Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saving da *SOJA NA* ƙara ciro wayar yayi daga kunne ya sake duba wanda yake kira *Raheela*.




Katse kiran yayi sannan ya juya ya kalle ta,gaba ɗaya ta haɗa zufa sai juya idanu take alamar mara gaskiya.



Sake kira yayi wayar tata ta kuma ɗaukar ƙara,a tare suka kuma kallon wayar kan su kalli juna,gaban ta na dukan uku uku saboda kallon da yake jifan ta dashi.




*kuyi haƙuri da wannan,Ku dai ku cigaba da bina,nusram hajajju fatima bala,salma,meera ta annabi,zainab bala,fatima zahra Ruqayya imam,Aishatu babyo da khadija ta group ɗin yaya umar dukan ku ina godiya da sauran wa'inda ma ban ambata ba*.



#LIKE
#SHARE
#COMMENTS


*babyn abdul maman farouk,elham da meenal*





*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.



*_Luƙumanul hikmata yayi wa ɗan wa'azi ko ince nasiha shi inda yake cewa"ya kai ɗana kada ka haɗa Allah da wani_*".


*_Ya kai ɗana ka tsaida sallah kuma kayi umarni da kyakkyawa ka kuma hani da mummuna ,ka kuma yi haƙuri akan duk abinda ya same ka_*



*_kada ka ɗaga kan ka akan mutane sannan kada ka tafi a ban ƙasa kana mai girman kai ko alfahari_*.




*_ka ƙanƙan da kanka wajen tafiya kuma ka dai dai ta muryar ka,domin mafi abin ƙi shine muryar jaki_*



*_~suratul luƙman aya ta 13,17,18,19~_*.

Ku sani littafin one love babu na siyarwa a ciki group nace na buɗe me so yayi mini magana naji wasu sun fara tambaya ta banki za'a tura kuɗin ko kati,a'a nifa bana siyarwa bane littafi na kyauta ne duka.


*_24_*



Ɗauke wayar tayi da sauri tana mazurai,kashe wayar yayi yana kallon ta cikin ɓacin rai sai yanzu ya gane abubuwa da yawa.

Wato itace take mishi wasa da hankali kenan??,cikin rawa jiki ta miƙe,shima haka yana binta da wani irin kallo.

Daburcewa tayi,cike da fushi yace"Wallahi kin bani mamaki,haƙiƙa kinyi wasa dani kuma kin raina ni,to amma ki sani ko a mafarki ba zan taɓa auren ballagaza me bin maza hotel me shaye-shaye ba,ban taɓa zina ba na san ubangiji ba zai sa na auri mazinaciya ba,ina so ki sani tuntuni na tsane ki na tsani halin ki kuma ki sani wannan shine gargaɗi na ƙarshe da zan miki shine kada ki sake ki kuma shiga harka ta da rayuwa ta idan ba haka ba kuwa zan barki da abinda har abada ba zaki manta dashi ba".

Cikin borin kunya tace"me ka isa kayi mini,ka sani cewa har gobe ina son ka kuma ba zan taɓa denawa ba,kuma idan har ina da rai ba zaka taɓa samun farin ciki dauwamamme ba matuƙar ka auri wata bani ba".

Kan ta rufe baki ya wanke ta da mari,dafe wajen tayi,cikin matuƙar ɓacin rai yace"baki da hankali kenan,idan baki ji ba kuma ki cigaba da shiga al'amura na wata rana sai na zama ajalin ki".

Cikin kuka tace"yanzu soja na zaka iya halaka ni",ba tare da wani tunani ba ko damuwa yace"tsaf kuwa saboda na tsane ki".

"ban taɓa ganin masoyi ya zama maƙiyi ba,kuma shiga harkar ka yanzu na fara....",ganin yadda ya zuba mata idanu yasa ta kasa ƙarasa maganar da tayi niya.


Zai sake magana major ya fara saukowa hakan yasa yayi shiru,file kawai ya amsa sannan ya juya ya fice ranshi a ɓace.

Zuby ta taɓe baki a ranta tana faɗin"zaka san kayi da Zuby,kuma ko wacece ba zata taɓa samun kwanciyar hankali ba".

Daga haka ta juya ta haye sama,major ya zuba mata idanu kafin ya girgiza kai kawai yana nema mata shiriya.

Khaleel yana isa gida ya zauna yana huci,lallai yarinyar nan ta raina mishi wayo,hannun shi ya dunƙule yana huci.

Koda Yaya Abdus-samad ya shigo bebi ta kan shi ba tunda ya lura ranshi a ɓace yake.

Wayar shi ya ciro ya nemo number ta ya fara kira,ni kuwa a lokacin ina kwance hannu na riƙe da wani handbook na information ina dubawa.

Ganin me kiran ya bani mamaki,sai da na dai dai ta natsuwa ta sannan na ɗaga wayar da sallama ɗauke a baki na.

Ajiyar zuciya yayi sannan ya amsa,cikin ladabi harda duƙar da kai nayi sannan na gaishe dashi.

Be amsa ba yace"me kike yanzu",kallon littafin dake hannu na nayi sannan nace mishi"karatu nake".

"ki kunna datar ki zan kira ki",da to na amsa,shi kuma ya katse wayar,murmushi nayi ina faɗin "halin yaya Khaleel wallahi sai shi".

Ina kunnawa kuwa sai ga messages suna shigowa bata su nake ba,dan haka ban buɗe ko guda ɗaya ba.

Kiran yana shigowa na ɗaga,yana kwance ya ɗora system ɗin akan cikin shi,jikin shi sanye da t shirt kalar brown.

Kallo na yake yi haka nima shi na zubawa idanu,ta ɓangaren shi kuwa ji yake kamar yana zubawa zuciyar shi ruwan sanyi,wato duk ɓacin ran da yake ciki ya kwaranye.

Kyau yake gani ta ƙara masa kasancewar yau fuskar tawa tayi fayau dan ko hoda babu a fuskar haka kuma ido na fari yake fat.

Alamu nayi mishi da ido akan lafiya kuwa,lumshe idanu yayi alamun babu komai,murmushi nayi kawai.

Shi kuwa ajiyar zuciya yayi yace"kun fara attending lectures ne?",da ido nayi mishi nuni da a'a.

Gefe ya kalla yace"ji nake kamar na dawo zaria na fara gajiya",a hankali nace"dame yaya",baki ya taɓe yace"da aikin nan mana,gashi akwai wa'inda a koda yaushe nake son kasancewa dasu ko wankan tsarki?",ya ƙarasa yana kashe mini ido ɗaya.

Rufe fuska nayi ina dariya kamar me raɗa nace"uwar gida kuma",shima kwaikwayo na yayi yace"sarautar mata",zaro idanu nayi ina mamakin ya akayi yaji me nace.


Yayi dariya sannan yace"Allah yarinyar nan yanzu kinga gadon barci na,anya kuwa zaki barni nayi aure",na turo baki nace"sai dai ka jira idan nayi nawa sai kayi".

Lips ɗina ya zubawa idanu,ɗagowa yayi ya jingina sannan yace"na rasa yaushe kika maida ni kakan ki?",bance komai ba banda murmushi da nake yi kawai.

Abdus-samad dake gefe yana kallon ikon Allah yayi murmushi yana jinjina wannan soyayyar da wa'inda keyi basu ma san suna yi ba.

Ya Allah!,ka bani soyayyar gaskiya nima,tuno da Khairiyya yasa shi jan tsaki sannan ya miƙe ya fice.

Ina muka san da wani halittan Allah a wajen ta junan mu kawai muke yi,gyara zama yaya Khaleel yayi yace"yauwa baki siffanta mini kalar mijin da kike so ba".

Rufe idanu na nayi nace"ko wanne kala ina so",kallon da yake yi mini yasa nayi saurin sauke kaina ƙasa domin yanzu babu kalar kallon yaya Khaleel da ban san me yake nufi ba.

"kin san ina so na fara nemo miki mijin da zaki aura ne,na san kamar yau lokaci zai yi",ƙasa-ƙasa na kalle shi kan nace"kai yaya kace dai kawai ina so kiyi aure ko nima na samu nayi".

Da mamaki yake kallo na domin beyi tunanin zan iya faɗa mishi haka ba,jinjina kai yayi yace"lallai kin fara wuce tunani na,yanzu dai faɗa mini wane kalar miji kike so".

"a siffan jiki kalar ka,me tsafta irin taka me barkwanci irin na yaya Al'ameen me haƙuri irin na Yaya Khaleed me sallolin dare kalar na yaya Abdus-samad me yawan azumi kalar naka",na ƙarasa ina rufe idanu na.

"hmm anya kuwa akwai kalar wannan namiji kin san mutum tara yake be cika goma ba,amma baki son miji kala ta",shiru nayi ina murza yatsun hannu na,ɗagowa nayi na kuma kallon shi ni ya kafe dai da idanun shi,rasa me zan bashi amsa nayi domin na lura so yake ya ƙure ni,can wata dabara ta fado mini,nace"kai kana son mata kala ta ne",murmushi yayi kawai.

Can kuma ya ɗago ya kalle ni,ni kuwa ban san me yasa gaba na ke faɗuwa ba addu'a nake akan yace"eh,duk da ban san dalili na,na son hakan ba.

Ya buɗe baki zai yi magana Ummi ta shigo,gani na na tasa laptop a gaba ta ɗauka danne-danne nake yi dan ina facing ɗin ta ne yasa tace"ke kam sai nace Khaleel.ya amshi abar nan kullum baki da aiki sai kallon ta kina faman surutai da shi mishi da Albarka amma kuma ɗauke hankalin ki take,oya kashe ta ki kwanta".

Kallon jikin screen ɗin nayi har ya kashe hakan yasa nima kawai na rufe nayi ɗaki.

Shi kuwa murmushi yayi har sai da haƙoran shi suka fito farare tas,wata iska me daɗi yake ji tana kaɗa shi,ga wani abu dake zagaye cikin ɓargo da jijiyar shi.

Ni kuwa ina shiga ɗaki na faɗa saman bed na lumshe idanu fuska ta ɗauke da murmushi,ba wai na dena jin tsoran shi bane a'a kawai dai na rasa meya saka kwana biyu na kan sake muyi fira dashi sosai.

A haka Rufaida ta shigo,ɗaka mini duka tayi,da sauri na buɗe idanu ta galla mini harara tace"wallahi dai kin cika nawa kiyi sauri ki shirya shine kika kasa,kin kuma san Baba malam zai yi faɗa sosai.

Zaro idanu nayi sam na manta cewa zamu je gaskiya lay out tare da Rufaida,Baba malam ya aike mu.

Cikin sauri na miƙe nayi bayi,ban daɗe ba wajen yi wankan na fito,simple make up nayi wani material kalar coffee na saka,sai farin hijab.

Da sauri nace"tashi mu tafi",ita ma Rufaidar miƙewa tayi kawai muka tafi,a waje muka tarar da Khairiyya tana tsaye sai ƙunƙunai take.

Ni dai bance mata komai ba,tana ganin mu tace"shine kika wani shanya mutum",ta ƙarasa tana kallon gefen da nake ta ƙasan ido.


Rufaida tace"to waye yayi miki dole,dallah ni idan zaki je ki wuce mu tafi kawai",matsa hannun Rufaidar nayi alamun tayi shiru.

A hankali muke takawa muna yafe muna fira har muka iso bakin titi,nan muka tsaya domin samun mota.

Wata farar mota end of discussion new model 2019,har ta gifta ta dawo a hankali,ni dai kauda kai nayi domin indai kalar wa'innan motocin ne to na saba ganin su idan na fito domin tafiya makaranta.

Zuge glass ɗin aka yi,kyakkyawan saurayi baƙi dai dai kyawun mu na arewa,Rufaida da Khairiyya kuwa baki suka saki suna kallon shi.

Ni kuwa tunani nake ina na san wannan fuskar,Murmushi yayi wanda yasa suka kuma buɗe baki,yace"hi Juwairiyya Mahmoud ko?".

Mamaki na fara yi ina kuma wannan ya sanni,ɗan lagwaɓar da kai yayi yace"ya ilahi,wato tsabar iya taimakon ki har taimako kike ki manta waye ma kika taimaka to sir Abubakar hall,yanzu kin tuna".

Sai a lokacin na tuna shi,lokacin da muka yi jarabawa a hall dake sir Abubakar wanda ya zauna kusa dani har bashi da lafiya na taimaka mishi.

Idan ban manta ba sunan shi Jabeer Ibrahim kyari,Ɗan katsina ne aiki ya kawo mahaifin shi zaria shine shima yake karatu anan ABU zaria.

Ƙatse mini tunani yayi ta hanyar kaɗa hannun shi ya kaɗa yace"yauwa kin tino ni ko?",ɗaga kai nayi ina murmushi.

"to yanzu dai ku shigo na rage muka hanya,",girgiza kai nayi nace"a'a ka barshi na gode haka ma".

Kallon Rufaida yayi yace"wai haka ƴar uwar mu",dariya tayi tace"to wannan dai tsakanin ku ai",riƙe baki yayi yace"da alamu wannan ƴar adawa tace",dariyar da babu shiri muka yi.

Khairiyya taja tsaki tace"dallah ni kuna ɓatawa mutane lokaci idan zaku shiga kuzo mu shiga idan kuma ba zaku shiga ba kuzo mu nemi abin hawa".

Da sauri ya fito ya buɗe mata ƙofar baya yace"yauwa ƙawar mu shigo kinji ki bar su",bata ce komai ba shiga kawai tayi,ganin haka yasa ita ma Rufaida ta shige kawai.

Nazo shiga ya rufe ƙofar sannan ya buɗe ta gaba yace"gimbiya bismillah",kamar zanyi magana sai kuma na fasa kawai na shiga.


Shima zagayowa yayi ya shiga sannan ya tada motar ya harba ta titi,tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana.

Kallo na yayi yace"kinyi registration ne?",ɗaga kai nayi nace"eh nayi",dariya yayi kan yace"yayi kyau gaskiya babu wasa da karatu kenan?",murmushi nayi.

"kin ga dama na daɗe bana da abokiya a makarantar yanzu kuma Allah ya bani,sai a taimaka mini da number".

Ban san me yasa na kasa mishi musu ba number na kawai na saka mishi,kira yayi jin ringing ɗin ya kalle ni.

Ciro wayar nayi,murmushi yayi yace"ah lallai ke hajiya ce,wannan babbar waya haka",dariya kawai nayi ina kauda kai.

Dai dai bakin makarantar darul hadith dake maje road ya ajiye mu,godiya muka yi mishi yace"babu komai ƙawa ta kawai kuje,sai mun haɗu a school ranar monday".

Kai na a ƙasa nace"Allah ya kaimu",ɗago mini hannu yayi yana kuma nuna mini alamun sai ya kira ni.

Khairiyya kuwa zuciyar ta kamar zata fashe,wai meya saka komai sai wannan Juwairiyya ne?,haƙiƙa a rayuwa komai ta fita kuma tana samun nasara da duk abinda take nema meya saka ne.

*ai hassada ce kawai dama kuma meyi baya cigaba a rayuwa,Allah ka shirya masu yi amin*.



*kuyi haƙuri da wannan naso yafi haka amma kuma hakan be samu ba ku dai yi haƙuri*.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT
*babyn Abdul,maman farouk,meenal da elham*.


♥ ❤

♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)





https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*




*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



Wattpad 13deeja.


Daga wannan page d'in har zuwa k'arshe sadaukarwa ne gare ki *AISHATU BABAYO* saboda kaunar da kike wa *GOLDEN PEN WRITERS* ba muda abinda zamu biya ki dashi, dan haka *K'AREENATEEY* har zuwa k'arshe ya zama naki sis kiyi yadda kike so dashi, *JAKADIYA* ta baki wannan yan shafukan har zuwa karshe, muna godiya sosai da irin kaunar da kike mana.


Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace"me yanke ta ba zai shiga Aljanna ba",abin nufi me yanke zumunci.


A wani hadisin yace"duk wanda yake so a yalwata masa arziƙin sa kuma ya afaɗaɗa masa takun sa to ya sadar da zumunci".


*fatima zahra* na gode da kati sosai ubangiji ya bar ƙauna na gode na gode Allah ya ƙara zumunci.


*_25_*


Sai da muka amso saƙon,litattafai ne manya manya wanda aka siyo su daga sudan,jaka biyu manya-maya haka na ɗauki ɗaya Rufaida ta ɗauki ɗaya.

A bakin titi muka tari keke napep sannan muka hau,har cikin get ya shigar damu,sai da muka biya shi sannan muka ɗauki jakar.

Dai dai zamu shiga falon Baba malam ta Rufaida ta saka mini ƙafa,tafiya nayi gaba na faɗi jakar kaina ma tayi ƙasa,kaina ya bugu da jikin tiles ji kake qum.

Goshi na dafe sannan na kalli littattafan dake zube a ƙasa,ƴan ɗakin suka taso suna faɗin subhanallahi.

Baba malam har ya buɗe baki zai mini faɗa ganin yadda na koma,ga kaina dana dafe ga kuma yadda na maida fuska ta gwanin ban tausayi.

Dama ance tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah balle kuma ni ƴa mafi soyuwa a cikin ƴaƴan shi,fasawa yayi kawai ya ba ɗaliban shi umarnin su tattara littattafan ni kuma yace naje na kwanta a ɗaki Allah ya kyauta gaba.

Rufaida ta riƙe ni muka fita yayin da Khairiyya taja tsaki ta fice tana jin haushi ita ba haka taso ba taso ne Baba malam yayi mini faɗa a cikin jama'a.

Muna fita Rufaida tace"amma wallahi sai naci uwar Khairiyya dan ita ta janyo hakan tana kallo ɗauka saboda bana uban ta bane sannan kuma ta kusa ta janyo ayi asarar su dan bata san kuɗin su ba aƙalla fa sun fi dubu ɗari da hamsin".

Kallon ta nayi da mamaki nace"amma kuwa Rufaida kin bani mamaki wallahi ban ɗauka kema kina da wannan abin ba cikin ranki,bafa dalilin da ya saka bata ɗauka ba kenan ai Baba malam da Abba duka ɗaya ne a wajen ta kuma maganar faɗuwa tuntuɓe nayi ba wai ita bace ta janyo".

Tun daga kallon da take mini na fahimci bata yarda ba,tsaki taja dogo sannan tace"kin cika sanyi ki canza hali wallahi",tana gama faɗin haka ta juya ta bar wajen.

Binta nayi da idanu kawai ina murmushi,ita kuwa ko juyowa bata yi ba,sai da naga ɓacewar ta sannan hawaye ya zubo mini na goge nace"Allah yana nan",daga haka nima na nufi ɓangaren mu.

Zuby ta kalli Zuly taja tsaki tace"wallahi kina bani haushi sosai da sosai jifa yarda kika wani share ni kamar ni ɗin ba ƴar uwar ki bace".

Zuƙy tayi murmushi tace"wallahi baki san me nake tunani akai bane akan waccen ƴar iskar",Zuby tace"ni ina nan ina tunanin yadda zan yi da soja na ke kuma kina can kin tunanin wata yarinya".

Zuly ta riƙo hannun ta,ta zaunar da uta bakin gado sannan tace"nima ai tunanin da nake kenan amma kuma me a gaba da gaba yaƙin ba zai yiwu ba dole sai dai mu biyo masa ta ƙasa da sama da gefe da gefe".

Zuby tace"nifa ban fahimci inda maganar ki ta dosa ba,me kike nufi kenan?",Zuly ta buɗe murfin totulin ta kurɓa sannan tace"wani abu wanda yafi so zamu lalata shi".

Zuby ta ɗaga kafaɗa tace"har yanzu dai ban fahimta ba",Zuly ta kuma yi dariya sannan tace"wani lokacin kan ki baya ja,ina nufin kin san yaƙin gaba da gaba ba zai yiwu ba to muyi mishi kisan mummuƙe mana mu nemi wani na jikin shi wanda yafi so yake ji dashi mu lalata koma muyi sanadiyar barin shi duniya kinga shikenan".



Ihu Zuby tayi sannan ta buga tsalle ta rungume ta,hakan kuwa ya tafi da imanin ƙawar kuma ƴar uwar ta ta,shafa gefen fuskar ta tayi tace"kada ki damu sweet heart".

Miƙewa tayi tana mata wani kalar kalƙo,kafin tayi tsalle ta faɗa saman bed,cikin farin ciki tace"yanzu wa kike gani zamu fara akan shi".

"ai babu wani tantama kema kin san wacce zamu taɓa",miƙewa Zuby tayi tace"wa kenan kike magana akai?",Zuly ta juya idanun ta kalar na ƴan chinese tace"wace banda wannan shegiyar Juwairiyya".

Zuby ta jinjina kai tace"tabbas hakane domin na san sai yafi jin ciwo",Zuly tace"ai dama hakane dan wallahi so nake ya zubar da hawaye".

Zuby ta kashe ido tace"ina so yayi kuka amma kuma ba sosai ba gaskiya",Zuly tace"yanzu abinda ya fara kama ta shine mu sami hoton ta".

"Zuby tace"taɓ abu me wuya kenan sai dai bari mu duba instgram nashi ko zamu samu",Zuly tace"hakane duba mu gani".

Duk iya binciken su hoton Juwairiyya ya kasa samuwa,hakan ya sa Zuby kamar zata yi kuka tace"wallahi kota yaya ne ya ka mata na sami hoton yarinyar nan,domin kuwa ita zamu taɓa Khaleel yaji zafi".

"kwantar da hankalin ki,zamu san yadda zamu yi",Zuly ta faɗa tana dafa Zuby,ita kuwa bata ce komai ba domin kuwa abin ya koma bata haushi kuma.

Ni kuwa yau Monday na fara shiga makaranta,alhamdulillahi duk abinda zanyi clearing nayi sannan kuma karatun ya fara tafiya yadda nake so.

Yayin da graduation ɗin su Rufaida ya matso sosai haka kuma jarabawar su Abdul'azeez itama ta matso sosai da sosai.

Shirye shirye munyi shi sosai,dan har kasuwa muka je muka siyo duk wani abu da zamu buƙata,Khairiyya kuwa sai cika take tana batsewa mu kuwa kota kanta bama bi.

Yanzu haka gobe ne za'ayi musu graduation,munyi su dubulan da su doghnut da cin cin,muna gamawa Jabeer wanda yanzu mun fara sabawa dashi ya kira ni a waya.

Wajen da nake akwai mutane da yawa hakan yasa na miƙe na fita,ɗagawa nayi ina jiyo ajiyar zuciyar shi sannan yace"buddy anya kuwa?",kamar kin manta dani".

"haba buddy yaushe muka rabu ne kuma na faɗa maka gobe graduation nasu Rufaida shi yasa".

"to yanzu dai gobe zan zo na amshi assignment ɗin ki,sai kiyi mini kwatancen gidan ku".

Murmushi nayi nace"idan kazo gidan yari dake ƙofar doka ka kira ni",dariya yayi yace"insha Allahu kuma ki tabbatar suna ready dan ba zan daɗe ba zan tafi".

Idan hanci na be mini ƙarya ba turaren Yaya Khaleel nake ji,juyowa nayi a hankali,yana tsaye a baya na jikin shi sante da farin yadi ƙal.

Kasa cire wayar nayi daga kunne,ina jiyo Jabeer yana cewa"Allah ba zan jira ki da wani uzuri naki ba",da ƙyar na iya ce mishi"ok insha Allah,sai anjima".

Kan yace wani abu na katse,yaya Khaleel kuwa murmushi yake yi wanda hakan ya alamta mini cewa beji wayar nake yi ba.

Nima ƙaƙalo murmushi nayi sannan nace"yaya sannu da zuwa anzo lafiya",buɗe baki yayi domin yayi magana sai kuma ya fasa.

"da ido yayi nuni da yunwa yake ji",murmushi nayi kawai wato

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment