Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fira da dariya sai da naga alamar farinciki a tattare da ita idan akayi la'akari da kwanakin baya yadda na tsagwami kaina ga wulak'anshi da nake gani wajen yan gidan namu.





shi kan shi abdul'azeez daya dawo sosai yayi murna haka ya zauna a cikin mu muna ta fira, duk da rufaida tana da wasa haka kuma bata tsaya tayi karatu sosai ba sai da na fahimci yanzu kamar rayuwar ta ya fara canzawa.





Sai yanzu na fahimci dalilin da yasa baban gida ya had'a ta da yaya khaleed wato Allah yayiwa dattijon kaifin basira,ashe yaya khaleed zai iya saisaita rayuwar ta.





Har wayar da yaya khaleel ya bani sai da na nuna mata, ta kuma yi murna dashi sosai tana fadin sun sami ta yin selfie, data tashi tafi har bakin karamar kofar bangaren mu na kaita sannan na dawo.






Haka muka rink'a tattauna canzawar tata nida abdul'azeez ummi dai na jin mu bata ce komai ba.




Bayan munyi abubuwan da muka saba akowanne dare kafin mu kwanta sannan muka kwanta.



Ina kwanciya wayar tayi k'ara gaba na ya fad'i cikin rawar jiki na d'aga, "ki kawo mini coffee kawai yace ya kashe wayar.




Ajiyar zuciya nayi sannan na mik'e, kayan dake jiki na riga ce iya gwiwa ta barci hakan yasa kawai na d'ora dogon hijab a kai.







Kitchen na shiga na had'a masa sannan na bud'e k'ofa na fita domin kai mishi.




A farfajiyar gidan na had'u da Khairiyya da yaya abdus-samad bata ce mini komai ba inajin ganin yaya abdus-samad yasa nima kuma bance mata ba.






Ina zuwa bakin k'ofar d'akin nayi sallama sannan na shiga, yana zaune daga shi sai singlet da gajeren wando.




Runtse idanu nayi gaba na na tsanan ta bugu,rufe idanun da nayi yasa ban san nazo kusa dashi ba.





Kujerar dake kusa na daka kofin ya tarwatse ruwan ya zube a jiki na, saukar ruwan zafin a jiki na yasa na tsala ihu ina fadin"innalillahi".





Bud'e idanu yayi, yana tsaye rik'e da system d'in shi wanda na san gudun kada na b'ata ne yasa ya d'auke idanun shi tsaye a kaina.





Kallon k'asa nayi da kuma jiki na ga zafi yana ratsa ni domin rigar jiki na irin me santsi ce hijab d'in dake jiki na kuma yadin d'an Abba ne bashi da kauri sosai hakan yasa ruwan zafin ya tab'a ni sosai.




Yaya khaleel kuwa kallo na kawai yake yi a zuciyar shi yana ayyana abubuwa da yawa, anya wannan yarinyar bata da matsalar k'wak'walwa tun daga shigowar ta idon ta a rufe har zuwa zubar da coffee d'in duka yana kallon ta.




Ajiyar zuciya yayi sannan yaja hannu na muka shiga bedroom d'in shi,ni dai bin shi kawai nake yi, ganin ya shiga dani bathroom ya sa gaba na ya cigaba da fad'uwa.





Ji nake kamar na zuba da gudu,ban ankara ba naji ya cire hijab d'in dake jiki na,dogon numfashi naja ina jiki na ya hau rawa, nama kasa motsi gaba d'aya.




Bangaren oga kuwa tsayawa yayi k'am ya kasa motsi, kallo yake bin yarinyar dashi tun daga k'asa har sama lallai yarinyar nan ta fara wuce tunanin shi.






Zufa ya fara keto mishi gashi ya kasa k'wakk'waran motsi,miyau ma da zai had'iya neman fara gagarar shi yayi,a hankali ya fara lumshe idanu cikin sauri kuma ya bud'e su.





Bugun zuciya ta ne ya k'aru ganin yadda gaba d'aya idanun shi suka sauya kala,jikin shi har rawa yake yi, murya a dashe yace"ansa ki saka maza ki fice",ya fad'a yana mik'o mini hijab d'in.





Amsa nayi na fara k'ok'arin sakawa, shi kuma ya tsugunna yana dafe cikin shi, sai da na saka hijab d'in sannan na lura da halin da yake ciki.



Murya na rawa nace"yaya baka da lafiya ne",na fad'a ina k'ok'arin tab'a shi, cikin daka tsawa yace"ki fita daga nan nace", jiki a sanyaye na fice daga bayin.




Ina fita muka had'u da yaya abdus-samad sannu kawai nayi mishi na wuce, farfajiyar gidan babu kowa saboda goma ta wuce mata duk sun shige d'aki maza kuma wasu basu dawo ba.




D'aki na wuce har hafeeza ma tayi barci nima kwanciya nayi sai dai kuma tunani na fad'a meye yake damun yaya khaleel ne? ",ban samo amsan ba hakan yasa kawai na hutar da kai na ta hanyar yin barci.





B'angaren oga kuwa dafe da ciki ya baro bayin,gefen katifar shi ya tsuguna,yaya abdus-samad da ya shigo ya fara tambayar shi lafiya kuwa.




Nuni ya mishi da cikin shi, kasancewar shima gauro ne ya fahimci me yake nufi dan haka yayi murmushi yana fadin"bari na d'auko maka tablets d'in".





Koda ya kawo mishi b'alla yayi ya sha sannan ya kwanta,A hankali cikin ya fara lafa mishi haka har harci ya d'auke shi.




Sannan abdus-samad ya sami damar tashi ya fice daga d'akin zuwa shima nashi d'akon don ya kwanta.





Washe gari kuwa garau ya tashi,haka suka je sallar asuba Yaya abdus-samad nata yi mishi tsiya banza yayi dashi kamar be san me yake magana akai ba.





A ranar baba malam ya duro k'asar daga saudia,duk yaran gidan masu hankali sunje sunyi mishi sannu da zuwa, ciki kuwa harda ni.





Janyo ni jikin shi yayi kamar yadda ya saba yace"fatan babu wata matsalar? ",eh baba babu komai", na bashi amsa.






"To Allah yayi miki Albarka", na amsa da ameen, daga haka na mik'e na fice.






Kan na shiga b'angaren mu na had'u da rufaida da khairiyya da alamu magana suke yi,murmushi rufaida tayi mini tace"daga ina haka".





"Naje yiwa baba malam sannu da zuwa ne",hannu na ta rik'e tace"dan Allah anjima ina zaki je? ",nace"babu ko'ina".




"Pls ko zaki raka ni sabon gari",ajiyar zuciya nayi nace"zan tambayi ummi",yauwa dan Allah ki tambaye ta kinji sai muje", murmushi nayi mata nace"insha Allah",sannan na tafi.




Ina kallon khairiyya fuskar ta cike da mamaki ni dai ban bi ta kan ta ba na wuce,daf da shiga b'angaren mu na hadu da aunty fauza.





"Ke baki iya gaisuwa bane",Hajiya data fito b'ullo tace"ina fa zata iya gaisuwa ke kin tab'a ganin 'yan sabon gari sun yi gaisuwa.





Da idanu na bita gaba na yana fad'uwa, khairiyya me jiran kad'an inaji hango mu da tayi ne yasa ta taho ko kuma ba haka bane oho.




Harara ta tayi sannan tace"wallahi juwairiyya ki canza hali idan ba haka ba kina tattare da shan wuya, kuma ki sani kije ki fad'awa uwar ki asirin da tayiwa d'an uwana ta gaggauta warware sh........... ".





Bata k'arasa ba saboda saukar marin da taji,duka muka juya,sanye yake da yadi kalar fari haka ma chewing gum d'in shi.





Fuskar shi a d'aure yace"wallahi khairiyya idan baki fita harka ta ba sai na b'alla ki a gidan nan,".




Daga baya muka jiyo muryar momma tana fad'in"au b'alla ta zaka yi?, khaleel akan wannan zaka b'alla 'yar uwar ka uwa d'aya uba d'aya".






Abin ban haushi har wajen ya cika da mutane,ni dai gaba d'aya jiki na rawa yake yi domin kuwa na tsorata sosai.





"Haba momma baki ganin me take yiwa yarinyar nan ne zagin mahaifiyar ta fa take yi.... ",





"Yi mini shiru shashasha wawa wanda baya kishin d'an uwan sa,idan ta zage ta ai tayi abin zagi ne".





Kowa a wajen sai da yayi mamakin furucin momma idan akayi la'akari da yadda suke da ummi a da.





Kuka nake yi sosai gashi a wajen an rasa me hana ta,"haba momma dan Allah ki bari wannan ai cin fuska ne".





"Ah lallai khaleel dole ka nuna mini cewa fatima ta barbad'a ta baka ka sha",momma ki dena fad'ar haka ni bata bani komai ba".





"Ni nake magana kana maida mini ko khaleel",momma ta fad'a sai kuma hawaye ta fara kuka.




Yaya khaleed shi yazo ya rik'e yaya khaleel yace"khaleel meye haka kana gani mahaifiyar ka na zubar da hawaye akan ka".




Cikin b'acin rai yace"to yaya ya kake so nayi, tazo tana ci wa 'yar mutane mutunci a bainar jama'a",ya k'arasa muryar shi k'asa-k'asa.






Baban gida ya aiko duka muje, hakan yasa aka d'unguma zuwa falon hukunci yo falon hukunci mana tunda duk abinda ya faru can ake zuwa.





*masoya na kuyi hakuri saboda ban yi update da wuri ba, Abubuwa ne sun yi yawa love you oll😘*.






*LIKE*
*COMMENT AND SHARE*.




*BABYN ABDUL MAMAN MEENAL DA ELHAM*.



*YAR MUTAN ZAZZAU*.






♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*




~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja




*ADDU'AR SAKA KAYA*

_alhamdulillahil lazi kasani hazzas sauba warazaqanihi min gairi haulin minni wala quwwah_.





*Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi yace"ba zaku shiga Aljanna ba har sai kunyi imani, kuma ba zaku yi imani ba har sai kun so junan ku,shin bana nuna muku wani abu ba idan kun aika tashi zaku so junan ku*, *_ku yad'a sallama a tsakanin ku_*.



*_AL-MUHAYYMINU_*
*_9_*




Babu ummi a wajen hakan yasa aka aika aka kira ta, koda ta shigo k'ok'ari nake mu had'a idanu amma abu ya gagara.




Dan tak'i bari har ta sami waje ta zauna hajiya kuwa da mama idan ka kalli fuskar su ka san cewa suna cikin farin ciki.



Aunty ce dai ba zaka shaida ya fuskar ta take ba dan babu yabo babu fallasa.




Bayan baba malam ya bud'e taro da addu'a baban gida yace"wallahi kun bani mamaki,hajiya maryam kin bani mamaki ban tab'a kawo hakan daga gare ki ba idan ma zuga kike d'auka to ina baki shawara da tun wuri ki dena".






K'asa momma tayi da kai,baban gida ya juya ya kalli ummi yace"hak'ik'a fatima kin nuna halin girma duk da sanin cin zarafin da suke miki su da yaran su baki tab'a mai da musu ba haka baki tab'a kawo k'arar hakan ba".





"Tabbas kina nuna cewa ba duka 'yan sabon gari suke lalatattu ba kamar yadda cikin zaria akwai nagari akwai akasin haka to haka sabon gari ma akwai nagari akwai akasin hakan".





"Ku kuma ku sani duk abinda kuke yi yana dawowa kunne na,barin mama na tayi karatu ni na yarjewa d'an uwan ta khaleel dan haka duk wanda zai ci zarafi to ni ya kamata yazo yaci zarafi".





"Ku kuma alfarmar dana yi muku ta lokacin dana baku na janye ta ku nemo mazajen aure na aurar daku, wannan shine k'arshen magana zaku iya tafiya".




Daga haka ya mik'e ya bar wajen,sosai wajen yayi tsit domin kowa ya san ran baban gida ya b'ace ne hakan yasa kowa jikin shi yayi sanyi.





Rufaida dai ganin kowa yak'i mik'ewa yasa ta tashi tazo taja hannu na muka fice,sai lokacin kuma kowa ya fara samun k'arfin halin mik'ewa.




Muna tafe tana k'ara bani hak'uri kan abinda ya faru haka har muka je b'angaren su, direct d'akin su muka shiga muka zauna muna kallo a waya ta.




Mun ma manta da wani taro,ni kam dama ita ta d'auke mini hankali haka har wajen sha biyu sannan na tafi.




Ina shiga ummi tace"ina kika je sau biyu khaleel yana aikowa kija", kallon ta nayi nace"ummi ya isa haka matsalar da muke fuskan ta ya kamata ace ya wuce, babu inda zani idan abinci yake so ya aiki k'anwar shi mana khairiyy...... ".




Ban k'arasa ba ummi ta gwab'e mini baki tace"kada na kuma ji wuce kije kiran da yake miki, kuma yayan ki duk abinda ya saka ki bance kada kiyi ba".





Ba dan raina yaso ba na wuce sai da na shiga d'akin mu nayi wanka na canza kaya zuwa doguwar riga ta kanti na d'aura hijab sannan na tafi.





Da sallama na shiga as usual yana zaune a one seater yana operating system gefen shi kuma cewing gum d'in shi ne yana tapping waya.





Tab'e baki nayi sannan nace"yaya gani",be kalle ni ba yace"ki sama mini abinda zan ci",da to na amsa sannan na fice.




D'an wake na saka mishi da mai da yaji na jera a basket sannan na tafi kai mishi.



Wannan karon sun yi exchange domin dai yaya abdus-samad(cewing gum), shi yake operating system yaya khaleel kuma ke danna waya.




Ajiyewa nayi sannan na fara zuba mishi,hankalin shi duk na kan wayar sai da na gama shirya komai sannan ya d'ago ya kalla.




Dan-danan ya kuma had'e rai cikin fushi yace"meye wannan? ", murya na rawa nace"dan wake",kuma waye zai ci miki wannan d'in"?





Shiru nayi, daka mini tsawa yayi yace"ba magana nake yi miki ba",ji nayi fitsari na k'ok'arin zubo mini.





Hawaye ya gangaro daga idanu na cikin kuka nace"dan Allah kayi hak'uri",harara ya galla mini yace"kin kwashe tarkacen nan ko sai na miki shegen duka a wajen".




Ai kan kace meye na kwashe kayan, cikin d'aga murya yace"ki dafa mini wani abun me sauk'i na baki minti goma".





Ai harda gudu nake had'awa wajen k'arasawa bangaren mu,ina zuwa na d'ora indomie to ya zanyi idan nice khairiyya godewa Allah zanyi da aikin shi ya tsallake kaina amma tana nan tana hauka.





Tana dahuwa na juye da sauri na fice shima dai har gudu nake yi,sai da ya harare ni sannan ya fara ci.





"Ki shiga ciki zaki ga wani file da takardu a sama ki kwaso",amsawa nayi da to kamar yadda ya fad'a haka kuwa naga takardun duka na kwaso.






Sai da ya gama cin abincin sannan yace"kin samu addmission ranar monday jibi kenan zaki fara attending lectures dan na gama yi miki komai".




Duk da naji dad'in makarantar da zan fara amma sai da gaba na ya fad'i,cikin sanyin jiki na amsa da to.




Yana gamawa na tattara kwanukan nayi ficewa ta,ina komawa nayi sallah sannan nake fad'awa ummi.




"Wato juwairiyya ba zaki bar maganar karatun nan ba ko? ",k'asa nayi da kai nace"ummi addu'a zaki cigaba da yi mini".





Bata kuma cewa komai ba, Abdul'azeez yana dawowa na fad'a mishi murna kamar me,rufaida ma dana fad'a mata haka ta dinga murna kamar da ita a ciki.





Ita dai ummi bata kuma kula mu,da daddare dai be nemi coffee ba to ko nema na beyi ba hakan yasa kawai na cigaba da sha'anin gaba na.






Washe gari ranar laraba haka na tashi cikin d'oki gani nake kamar monday d'in tak'i zuwa ummi kawai kallo na take tana girgiza kai.





Misalin k'arfe tara na safe yayi sallama ya shigo cewing gum d'in shi na biye dashi,kamar na mik'e na gudu haka nake ji.




Gashi riga da skirt ne a jiki na kuma rigar ta d'an matse ni dan ummi ma sai da tace na cire a kyautar nace ina ni ina son kayana a haka.





K'asa nayi da kai kawai, b'angaren oga kuwa tunda ya shigo idanun shi ke kanta,har ya zauna.







Wasa nake da zoben da yake hannu na kamar me rad'a nace"ina kwana",shi kad'ai ne ya fahimci me nace shima dan idanun shi yana kan lip d'ina ne.





"Lafiya", kawai yace sannan kuma yace"ina ummi d'in",shima cikin sanyin murya nace"tana d'aki",fuska d'aure yace"to ba saki kije ki kira ta ba".





Wayyo kamar na d'ora hannu na a kai na kurma ihu haka nake ji,kallon shi nayi harara ya aiko mini da ita.




Kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki haka na mik'e,mutuwar zaune yayi yana bina da kallo, wani abu yaji ya taso mishi.




wato dalilin da yasa tak'i tashi kenan, kai daya sani be matsa mata ba, a hankali ya juyar da kallon shi ga Abdus-samad ganin hankalin shi naga wayar dake hannun shi yasa yaji wani sanyi wato be ganta a haka ba kenan.





Oh khaleel kishi ya rufe maka ido ka manta cewa uban su d'aya ne🤔.





Abdus-samad dake lura da abinda yake faruwa yayi murmushi yana cigaba da dannan wayar shi.





Ina shiga na kira ummin ni kuma daga nan na zame nayi d'akin mu, kwanciya kawai nayi ina tunane-tunane.






Ban san lokacin da suka bar d'akin ba ni dai anan barci ya d'auke ni, sai da na tashi ne ummi ta bani Atm da wata takarda tace yace a bani wai ashe ranar zasu koma wajen aiki.





Amsa nayi takardar ma k'amshin turaren shi take yi, na warware ta domin ganin meye a ciki.





*ga atm nan duk lokacin da kike buk'atar kud'i, sannan kuma ki dage kiyi karatu domin ki taimaka mini dan duk abinda kika yi nike da responsibility a wajen baban gida, ni na koma wajen aiki idan kina bukatar wani abu ki kira ni, sannan ga number d'in mutumin da zaki nema idan kin shiga makaranta, ga kuma pin nan*.





Sai number na waya da kuma pin number nashi,murmushi nayi lallai dole 'yan gidan mu suyi hassada dani, ni kuma insha Allahu sai na bawa mara d'a kunya.






____________________________________________________________________________________________________________________________________




Sanye take cikin riga da wando pensil duka kalar bak'i, gashin kantin nan ne aka nannad'e shi.



Kan rest chair take zaune wacce ke gafen swimming pool dake gidan sister d'in baban ta.





Hannun ta rik'e da glass cup ciki hollandia ne tana sha a hankali,idanun ta a lumshe kan ta sanye da head phone da alamu waqa take sha.





A zahirin gaskiya hankalin ta gaba d'aya naga wanda mahaifin ta yasa ya taro ta ranar data dawo.





Baban ta be samu lokaci ba balle ta zauna dashi ta nuna mishi cewa ita fa wannan take so ya zama permanent driver d'in ta domin kuwa gaskiya he is classy guy.




Dama tun kan ta dawo tunanin da take yi kenan na driver da zai dinga jan ta to amma daga saukar ta Allah yasa daddy ya turo mata wannan driver d'in kamar ya san irin shi take so.





Wata yarinya ce wacce ba zata gaza shekarun ta ba ta k'araso ta tab'a ta, firgigit ta dawo hayyacin ta.





"Haba zuby wai me yake damun ki ne, tun jiya da kika zo gidan nan na lura da kina yawan tunani amma kuma kin k'i ki gaya mini meke damun ki",yarinyar ta tambaya.





Ajiyar zuciya tayi tace"wallahi zuly wani driver ne ke caza mini kai,ya had'u sosai sai dai fa akwai isa gashi kwana biyu ban ganshi ba gashi daddy be zauna ba balle muyi maganar".





Bata damu da kallon mamakin da yar uwar tata take mata ba ta cigaba da cewa"shine fa tun shekaranjiya naji gidan yayi mini babu dad'i shi yasa na taho nan domin na samu sauki amma kin gani sai tunanin shi nake yi".






"Haba zuby kada ki bada mata mana driver fa kika ce?, yanzu akwai mutumin da zaki iya tsayawa ki b'ata lokaci wajen tunanin shi balle wani abu wai shi driver! ", ta k'arasa cikin matuk'ar mamaki.




Zuby tayi mata wani kallo tace"wallahi baki san meye ba, nifa kawai ji nayi yadda yake wani isa da iko birge ni yake yi, ina so na k'ara ganin shi koda sau d'aya ne".





Tafa hannu zuly tayi tace"shikenan zuby kin harbu, meye haka kinga mu bar maganar da ba zata amfane mu ba mu koma me amfani ya maganar fatin aleesha zaki je ko".





"Hmm zuly dan baki ganshi bane amma tunda kin ce haka shikenan muje d'aki ki bani wannan ragowar kayan aikin idan na farka anjima sai mu shirya mu tafi wajen partyn".




Jan hannun ta tayi tace"muje kamar kin san yanzu da zan dawo makaranta na biya na siyo domin na san halin ki baki da wasa", dariya suka yi suka tafa.




Wani irin hadadd'en flat ne me kyau,ciki suka shiga duk iya had'uwa d'akin had'u,jaka ta d'auko sannan ta bud'e ta zazzage.




Kwalaben magani ne na syrup, babu wata-wata zuby ta d'auki d'aya ta bud'e ta kafa kai sai da ta shanye tas sannan ta k'ara dauka a haka sai da ta sha hudu, sannan ta hak'ura.





Rigar jikin ta ta cire cikin maye tace"sis baki san me ba, ina son guy d'in sosai, kin san jin shi nake har cikin k'ok'on zuciya ta".






Zuly tayi wani munafikin murmushi,haka zuby ta cire kayan ta tas sannan ta kwanta tana cigaba da magan ganu marasa kan gado .





*babyn abdul maman meenal,elham da farouk*.

#SHARE
#LIKE AND COMMENTS.



*YAR MUTAN ZAZZAU*






♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*




~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja



*ADDU'AR SAKA SABON KAYA*

Allahumma lakal hamdu anta kasautanihi as'aluka min khairihi wa khairi ma suna'a lahu, wa'azubika min sharrihi wa sharri ma suni'ah lahu.




An karb'o daga abu huraira Allah ya yarda dashi yace"masoyina yayi mini wasiyya da abubuwa guda uku *yin azumi guda uku a kowanne wata da sallar walaha da kuma inyi witiri kafin na kwanta*.



*yaushe writers zamu sami yancin kan mu ne wallahi a duk lokacin dana ga ana zagin wata writer sai gaba na ya fad'i saboda nima gobe zan iya kasancewa hakan, readers wai me kuka d'auki writers mala'iku basu yi kuskure ko me, ku sani mutane ne kaman ku bayin Allah amma ku zauna kuna zagin ta babu kunya kuma ta rubuto novel ku karanta haba ku dinga yiwa mutum kyakkyawan zato*.




*wani lokacin kuma writers ku kuke bada kofar da ake zagin mu kama ta yayi ace idan ana zagin yar uwar ki writer kiji kamar ke ake zagi amma ba wai ki dinga jin dadi ba meye ribar ki idan an zagi wata what will dat owe you??? "*.

*_AL-AZEEZU_*

*_10_*




Ba ita ta sami kan ta ba sai bayan magrib,babu batun Sallah kawai shiryawa suka yi suka wuce party till down.





Waje ne kai daka gani ka san shagalallu ne,babu abinda ake a wajen sai watsewa da tanbad'ancewa.






Kid'a kawai ke tashi ta ko'ina,maza da mata cakud'e suna rawa,masu shaye-shaye kuma suna yi.






K'arar bindiga suka ji wanda ya hargitsa wajen, kowa fita yayi domin ceton ran shi, wa'inda suka sha suka yi tatul kowa suna tafe suna had'a hanya.





Cikin wa'inda suka sha suka yi tatul akwai zuby, gashi zuly ta tafi ita da saurayin ta gidan shi domin kwana.




Tafe take tana had'a hanya domin ba'a cikin hayyacin ta take ba tana zuwa ta hau kan titi, motar dake tahowa Allah yasa ma driver din yana jan motar a hankali ne.




D'an bige ta yayi ita kuma ta fad'i gefen titi, cikin maye tace"Who d who the hell is who d hell is dissssssssss? ".






Cikin sauri khaleel ya bud'e ya fito domin ganin waye ya buge domin dai da alamu mutum ne dan yaji magana.





Shi da farko ma ya dauka wani abu ne ko aljanu ke son tsorata su ganin yadda dare ya tsala wajen k'arfe biyu na dare.






Ganin kamar mutum a durk'ushe yasa gashi garin da duhu baya hango mace ne ko namiji ba zaka iya banbance waye ba.






torch d'in wayar shi ya kunna cikin sauri ya kautar da fitilar yana fad'in"Astaghfurullah",abdus-samad ya fito yana fad'in "meya faru ne my man? ".





"Wata na buge",ya bashi amsa a tak'aice,"to ka taho mu wuce mana na gaji da yawa ka taho mu tafi kawai ba dai tana da rai ba? ".




"Eh tana da rai amma kamar bata cikin hayyacin ta", ya fad'i haka yana juya wa domin ya tafi.





Cukuikuye rigar shi ta baya tayi tana fad'in"ba dai lahira zaka tafi ba to muje tare mana, daga nan har saudia".




Gaban shi ya fad'i, idan zai iya tunawa muryar wannan yarinyar yake ji 'yar major Aliyu kenan ita ce.





Kallon Abdus-samad yayi wanda

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment