Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa da"to ummi".



Har ta tafi ta juyo tace"Hafeeza zo ki taya ni ninke kaya",mikewa hafeeza tayi ta bi ummin, suka barni ni kad'ai ina karanta wasik'ar jaki.




Can kuma na mike domin tafiya d'aki, ina shiga nayi wanka na canza kaya sannan na fito na shiga kitchen har lokacin bani da walwala kuma tunani nake yi.




Haka har na gama abincin bani da wata natsuwa,kuma cikin sanyin jiki nake komai, ga tarin tambayoyi da nake dashi..




Koda muka zo cin abinci babu wanda yace mini wani abu ga ummi ta kafa ta tsare ta hana Abdul'azeez magana.





Muna gama cin abinci na mik'e,kamar jira Abdul'azeez yake yi shima ya mik'e kan ya biyo ni ummi tace"zo nan kaje ka siyo mini filawa gobe muyi d'an wake da safe".





Ni kaina sai da na jiyo na kalle ta,domin na san cewa komai ajiye mana ake yi kayan miya kawai muke siya shima ba kullum ba.




Juyawa nayi kawai na shige d'aki gaba na na kuma fad'uwa,ina zaune gefen katifar mu na zuba hannu biyu nayi tagumi,kira ya shigo waya ta.




Da sauri na d'aga nace"Rufaida wai meke faruwa ne? ",ajiyar zuciya tayi tace"Ki bari gobe zan zo nayi miki bayani", daga haka ta katse wayar.




Ummi tayi sallama ta shigo,jiki a sanyaye na amsa mata,zama tayi kusa dani tace"damuwa ba zata yi miki ba ki nemi waje ki kwanta".





Ban musa mata ba kawai na kwanta,tana gefe na tayi mini Addu'a, sannan taja bargo ta rufe ni tace"sai da safe".



Ina kwance shiru,,in sak'a wancan in kwance wancan haka har barci yayi awon gaba dani.





Ina zaune washe gari bayan na gama duk ayyukan da zan yi su hafeeza da Abdul'azeez duk sun tafi makaranta.





Nima kuma sai k'arfe goma zan tafi makarantar,hakan yasa na zauna b4 time ya cika.





Yaya Abdulkareem yayi sallama ya shigo,na amsa mishi sannan na gaishe dashi,kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa babu yabo babu fallasa.




Gaba na ya fad'i ganin yadda yake kallo na,ciki-ciki yace"ina mahaifiyar ki",sai da naji abin banbarak'wai wai namiji da suna hajara😀.






Cikin in-ina nace"tana d'a...... Ta...... Tana d'aki",tab'e baki yayi sannan yace"kice mata Baba malam na neman ta", daga haka ya fice ya barni zaune shiru wannan wane kalar fitina ke son b'allowa ta shigo gidan mu???.





Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,kaf gidan mu kowa da sunan da yake kiran mahaifiyata shine *ummi*, maman su yaya khaleel *momma*, maman su Rufaida *umma*,maman su Yaya abdus-samad *hajiya*, yaushe kuma abu ya canza????






Tashi nayi jiki a sanyaye na nufi bedroom d'inta, tana zaune tana duba littafin siffatus-salatin nabiy.





"Ummi baba malam ya aiko a kira ki",gani nayi jikin ta yayi sanyi,cikin sauri ta mik'e ta fita.






Sai da na d'an tsaya minti uku sannan na fito,ina fitowa Rufaida na yin sallama ta shigo, ajiyar zuciya nayi sannan na jata zuwa d'akin mu sai da na turo k'ofar sannan naje kusa da ita na zauna nace"Rufaida fad'a mini meke faruwa ne".





"Hmm jiya abinda ya faru ai yayi yawa wallahi Allah ne kawai ya tak'aita,bayan mun tafi kasuwa ashe wai khairiyya zuwa tayi ta fad'awa momma wai yaya khaleel ya baki kud'i da kuma waya".






"Shine fa ran momma ya b'aci taje ta fad'awa hajiya, ita kuma hajiya ta bata shawara akan ta aiko ayi ma ummi rashin mutunci a amshi wayar,ashe lokacin da suke maganar yaya Abdallah yana jin su".






"Ita kuma momma da d'aukar zuga ta kuwa tura khairiyya tunda ta san yaya khaleed ba zai je ba, aikuwa khairiyya tazo har nan part d'in tayiwa ummi rashin kunya".






"Ummi ita kuma bata kulata ba, tana fita ta had'u da yaya Abdallah shi kuma ya hau dukan ta".





"Yayi mata dukan kawo wuk'a kin san yana d'an busawa,yanzu haka ma tana asibiti, yaya Aliyu yaje ya fad'awa Momma gashi can Abdallah yana dukan khairiyya anyi a hanashi yak'i hanuwa".





"Aikuwa ta garzayo ta taho tana zuwa ta rufe shi da duka tana zagin shi, ita kuma hajiya tace bata san wannan ba,shine fa suka hau cacar baki".





"Ke in tak'aita miki har baban gida sai da ya tako cikin gidan nan abinda be tab'a yi ba,amma wai abin haushin suka k'i su dena,aifa shine ya tafi ya barsu".






"Momma ta kwaso 'yan sanda,akayi su rabu da maganar suka k'i ana haka sai ga Abba da baba malam sun shigo babu wanda ya sani fad'a musu akayi ko zuwa kawai suka yi oho,suna zuwa kuwa Abba yace, ya saki momma saki d'aya shima baba malam yace ya saki hajiya saki d'aya".





"Yace kuma idan sun so su kashe kan su, yanzu dai maganar da nake miki khairiyya na asibiti, momma na wajen ta hajiya kuwa ta wuce gidan su tun jiya, kuma baban malam yace duk wanda ya tada maganar sai ya tsine mishi ".






Wai ai fuskata kamar an watsa mini ruwa,jiki na gaba d'aya rawa yake yi,kuka na fashe dashi ina fad'in "na shiga uku".





Rufaida tayi dariya tace"wallahi kin shige su da tsoro to bari na k'arasa miki kiji ma wallahi su yaya Abdul kareem cewa suka yi sai sun halaka ki shine dalilin da yasa ummi jiya tace kada ki dawo".





"Ban san wanda ya kira ya fad'awa yaya khaleel ba sai ga kiran shi wai aje a d'auko ki wanda ya fasa tab'aki, shine fa yaya Abdulfatah akan yaje ya d'auko ki".





Ai ciki na har wani sauti yake bayarwa,ni juwairiyya naga ta kaina, yanzu ina zan saka rayuwa ta,abinda nake fad'a kenan a raina.





Kallon juwairiyya nayi nace"wato shi yasa yaya Abdulkareem d'azu yake harara ta kenan ashe nice sanadiyar fitar mahaifiyar su",rufaida ta mik'e tana fad'in"bari na tafi kada ummi ta dawo ta same ni".




Yadda ta tafi ta barni haka nake zaune ina tunani wanda ni kai na ba zance ga abinda nake tunanowa ba.





Ummi tayi sallama ta shigo, kallo na tayi tace"ga Abdulfatah can a waje yana jiran ki yace khaleel ya turo shi ya kai ki makaranta".





"umm....... "Cikin daka tsawa tace"bana son jin kai ba dai kin nace sai kin yi karatu ba,juwairiyya kad'an kika gani, oya wuce".





Kuka na saka nace"wallahi ummi na hak'ura",girgiza mini kai tayi tace"wuce tun kan na sab'a miki",haka na fita ina zubar da hawaye.





Ina zuwa na shiga shi kuma yaja motar,bance komai ba haka shima beyi mini magana ba,sai da muka isa makarantar sannan na kira shi mutumin babu dad'ewa sai gashi yazo yayin da shi kuma yaya Abdulfatah ya juya ya tafi.





Mun shiga duk wani clearance daya kamata ayi mini duka anyi da yake da kud'i kawai dai takardun ya banu dan tuni an riga da an gama komai.






Kallon takarda hannu na nayi faculty of information technology,shiga nayi domin tambayar 'yan course d'in mu.





Allah ya taimakeni ban sha wahala sosai ba na had'u dasu domin suma d'in ku san yau suka fara zuwa.





Lectures muka shiga k'arfe biyu zuwa hud'u,duk da banda wani kuzari amma fa naji dad'i yadda naga buri na ya zama gaskiya.





Muna fitowa muka nufi masjid domin sauke faralli,daga 4:30 muke da wani lectures d'in zuwa 6:30 hakan yasa hutawa kad'an muka yi sannan muka nufi hall d'in da muke da lectures d'in.






Ban wani fahimta ba saboda matsalolin dake gaba na,amma duk da haka a gajiye nake haka na fito, me mashin na samu ya fitar dani bakin get daga nan kuma na hau mota zuwa pz.




Ko a cikin motar dafe kaina nayi kawai,matsalolin gidan mu ya fara isa ta yanxu haka kaina har ciwo yake yi.





Muna sauka na sami motar zaria daga nan kuma muka tafi, tunda na hango k'ofar doka gaba na ya fad'i dan danan naji kanar ma kada naje.





Ana sauke ni na k'arasa gida, kasancewar magrib ta gabato wasu masallatan ma har sun fara kira.







Ko a bakin get 'yan gidan mu ne suke alwala ina zuwa suka bini da idanu, wayyo! Ni dama rud'ad'd'iya ai ji nayi kamar k'asa ta tsage na shige.





Saura kad'an muyi karo da yaya khaleed,"meye haka ke kuma, ki bi a hankali mana, har kin dawo",d'aga kai kawai nayi ina k'ara sauri.



Sai da na shiga part d'in mu sannan na samu relief,na san ba zan samu kowa ba domin ummi da hafeeza sun shiga sallah Abdul'azeez kuwa da abdul maleek da abdulhafeez suna masallaci.





nima d'aki kawai na wuce,ajiye hijab nayi da jakata sannan na wuce bayi nayo Alwala na tada sallah.





Sai da akayi sallar isha'i na tashi daga kan dardumar,ina fitowa ummi ta fito, sannu da gida nayi mata ita kuma tayi mini sannu da dawowa.





Su Abdul'azeez suka yi sallama suma suka shigo,zama muka yi domin cin abinci, sai da muka gama sannan muka koma saman sofa.






Muna zaune Abdul'azeez ya tashi ya dawo kusa dani,cikin sakin fuska yace"sweet ya lectures", dariya nayi nace"lectures Alhamdulillahi".




Nan na shiga bashi labarin makaranta duk da yanayin yadda na shige ta ba wani dad'i, duk wannan abin ummi bata saka mini baki ba.





Sai da na gama duk abinda na saba kafin yin barci kamar wanka da yin Alwala sannan nazo na kwanta.




Ina kwanciya waya ta tayi k'ara,Na d'aga baki na d'auke da sallama gaba na yana fad'uwa.





Amsa sallamar yayi cikin muryar shi me cracking kamar k'asa-k'asa,ya d'ora da cewa"ya lectures d'in da sauk'i ko".






Kamar yana gaba na, na d'aga kai ina fad'in"Alhamdulillahi babu wuya sosai",cikin kwantar da murya yace"juwairiyya,kin san dai yadda muka yi da baban gida da kuma irin abinda muke fuskan ta a dalilin karatun ki ko,Dan Allah ki tsaya kiyi abinda ya kamata,kada kisa nayi asarar kud'i ke kuma kiyi asarar lokacin ki, ki saka mutane suyi mana dariya".






Yana fad'in hakan ya kashe wayar,bin wayar nayi da kallo ina mai nazarin magan-ganun shi,tabbas hakane abinda ya fad'a.




Share hawaye nayi domin ko ummi bata zaunar dani tayi mini fad'a ba hakan ya tabbatar mini da har yanzu bata wani goyi bayan cigaban karatu na ba.






Ajiye wayar nayi na kwantar da kaina akan filo ina cigaba da zubar da hawaye, kafin barci ya d'auke ni.



________________________________________________________________________________________
*ASIBITIN TUDUN WADA*




Momma na zaune tana kallon juwairyya wacce har lokacin bata farfad'o ba,fuskar ta gaba d'aya ta sauya kamanni.





K'wafa tayi tace"aikin banza aikin wofi,ni za'a ja dani wallahi sai na rama kuma ba zan tab'a so tarayyar khaleel da waccen sadaka yallan ba",ta k'arasa tana jan tsaki.






Ga abu na neman ya kwance mata,sauk'in tama da 'yan kud'i a hannun ta, dan Abba ya hana kowa zuwa inda take.







Sai bakwai na safiya sannan khairiyya ta farka, sosai momma taji dad'i amma ita kuwa kuka ta saka haik'am.





Ganin hakan yasa likitan yayi mata allurar barci domin ta d'an huta, Allah yaso ma babu internal injuries.






Khaleel kuwa ya kasa kiran ta ma gaba d'aya domin yana gudun ya kira ta sauke mishi nashi.




Yau dai da safe ya d'auki aniyar kiranta bayan ya dawo daga morning exercise,hankalin shi ya tashi dan tak'i d'aga kiran shi gabaki d'aya ma.





Sosai ya shiga damuwa dan ma cingam d'in nashi yana lallashin shi,Abba yakira yayi mishi complain.




Aikuwa ya rufe shi da fad'a kan me zai kira ta,nan dai yayi mishi gargad'i kada ya kuma sannan kada ya janye daga karatun nawa.






Suna gama wayar ya zubawa wayar idanu yana tunani, ni kuwa nace su malam khaleel anyi gudun gara an fad'a zago 😀😀.




*TUDU WADA POLICE STATION*.




hajiya je zabga bala'i tun d'azu akan me sunk'i su bada belling gashi itama Baba malam ya hana kowa ya zo.


. data ishe su wani gabjejen police yace"ke kiyi mana shiru idan ba haka ba kema na jefe ki bayan kanta", ya k'arasa yana hararar ta.




ai jin bakin hajiya kayi gum😂😂?,sai zagi da take aunawa police d'in cikin ranta, da tsinuwa babu adadi.




ni kuwa nace hajiya kenan ai be san kinayi ba aikin b'ur inji tusa.🤓 ashe ana tsoron hukuma.






Ni kuwa gari yana wayewa na fara shiri domin yau k'arfe bakwai nake da lectures hakan yasa tun asuba na fara shiri.





Ina gama abinda nake yi nayi wanka,riga da siket na atamfa na saka,me kalar ja da green sai ratsin milk,hijab dogo na saka milk na d'auki jakata na fito, sallama na yiwa ummi sannan na tafi.







Sai da nayi 'yar tafiya sannan na isa titi,yau dai babu laifi dan inada walwala kad'an,mota na samu na hau wacce direct har samaru.






Sai da muka je main get sannan na sauka na d'auki me mashin ya shigar dani har faculty d'in mu.







Alhmadulillahi yau ban san tunani da yawa ba hakan yasa karatun na fahimce shi sosai, har kuma lokacin ban yi k'awa ba sai dai mukam gaisa domin irin wannan makarantar idan kace zakayi rashin mutunci da girman kai to akwai wanda suka dama ka suka shanye.






Sai hud'u na baro makarantar,mota na sake hayowa domin komawa gida, amma wannan karan dana sauka a pz sai da na biya banki ja ciri kud'i domin dai na hannu na daf suke da k'arewa ga siyan hand-out da sauran su.





Dubu goma kawai na cira sannan na sake hawa motar da zata sadani da gida, duk da raina a cunkushe yake.





Ina isa gida na tarar dasu Ammie sun zo hakan yasa na saki raina,mun sha fira sosai dan ma a nan zasu kwana, murna kamar na zuba ruwa a k'asa nasha.





Zuhra tace"wallahi juwairiyya zaria k'auye ce wai fa dan mun fito sanye da mayafi kawai aka fara bin mu da kallo, kamar basu tab'a gani ba"ta k'arasa tana dariya.





Murmushi nayi nace"to kun saka abinda ba shigar su bace,kema kin san bamu cika saka gyale ba dama-dama da sallah amma mu duk kwalliyar da mukayi hijab ne".





Shukra ta kwashe da dariya tace"nifa haka bikin nafeesa daya tashi nazo wai naga mutane sanye da zunbula-zubulan hijabi",suka kuma kwashewa da dariya.





"to ai mutuncin mace kenan,ki rufe jikin ki gaba d'aya kuma wannan aiba k'auyen ci bane".





"To meye shi d'in mutum ya saka hijab ya rufe kwalliyar shi, amma idan ka yafa mayafi kai kanka kafi shan iska",zuhra ta fad'a.




Ganin idan naja yi zamuyi ta yi yasa nace mata tazo muje wajen Rufaida,da yake ta santa yasa tace to.






Mun taso itama shukra ta biyo mu tace muje duka kawai haka muka dunguma zuwa part d'in umma.






Duk da gaba na yana fad'uwa hakan be hanani shiga ba,kusan dukan su suna zaune a falo muka yi sallama muka shiga.




Rufaida ta taso da gudu ta rungume ni,cikin murna take fad'in"oyoyo yan makaranta",sakina tayi ta koma kan zuhra da shukra tana fad'in "sannun ku da zuwa".






Sai da muka gaishe da umma ta amsa da sakin fuska domin dai ita irin mutanan nan ne masu fuska biyu.




Haka Rufaida ta jamu zuwa cikin d'akin su muka hau fira,sai wajen goma sannan muka ce zamu tafi.





Kayan da muka siyo a kasuwa ranar nan ta kwaso wasu daga ciki tace"gashi wannan naki ne dama ina taso na kawo miki".





"A'a haba Rufaida kada abin yayi yawa mana",dariya tayi tace"dallah can ni amsa kina tsaya wani surutu", haka ta tilasta mini na amsa.





Har bakin part d'in mu ta rako mu sannan ta juya,muna shiga sai da na kaiwa ummi kayan wanda har yanzu fira suke yi ita da 'yar uwar ta.





"An gode kawai tace Ammie ce ma ta yaba kayan, sanin halin ummi yasa na kwashi kayan da k'afa ta na wuce namu d'akin.




Can ma wata firar muka dasa sai wajen sha d'aya sannan muka kwanta.



*Yau ga page nan nayi muku da tsayi, ban muku alk'awarin update kullum ba gaskiya, dan muna da matsalar wuta ga kuma wani lokacin ko bani da data, idan kun jini kawai shikenan idan kuma baku jini ba kuyi hak'uri,na san dama kuna yi amma pls ku k'ara hak'uri, na gode sosai*.


#COMMENTS.
#LIKE AND SHARE



babyn Abdul, maman meenal,elham da farouk".





*YAR MUTAN ZAZZAU*.








♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)

(It's all about friendship)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*




*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*




~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13 deeja



*ADDU'AR DA MUTUM ZAI YI IDAN MASIFA TA SAMESHI*


innalillahi wa'inna ilayhir raji'u, allahumma ajirni fi musabati a'akhlifni khairan minha.




Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata agreshi yace"wallahi ko dai kuyi umarni da kyakkyawan aiki kuyi hani da mummunan aiki, ko kuma Allah ya dora azzaliman cikin ku akan ku(wato mulki)zab'ab'b'un cikin ku suyi Addu'a amma Ba za'a amsa musu ba.




*_12_*






Zaune take gefen swimming pool kan rest chair,kunnen ta sanye da earpieces,lumshe idanun ta suke a zahiri zaka ce waqar take saurara amma a bad'ini tunani ta tafi.





Daga jiya zuwa yau taimakon da yayi mata ta tabbatar tana son shi,to taya zata jawo hankalin shi gare ta.




Yanzu zaman ta anan kwana biyu basu had'u ba kenan domin yanzu daddyn nata baya gari, hakan yasa baya zuwa.






Gab'a d'aya babu wanda take son gani kamar shi,mik'ewa tayi zunbur, kamar wata mahaukaciya tayi cikin gidan da sauri.






Kan gado ta fad'a ta fashe da kuka,sai da tayi me isar ta sannan ta mik'e ta shiga bathroom, wanka tayi shaf-shaf.






Wata riga ta saka pink me ratsin blue,iya gwiwa sai kuma wando kalar blue da pink,d'ankwalin kayan d'an siriri shi ta yafa.






Takalmi flat pink ta saka sannan ta d'auki wayar ta da purse ta fice,mota ta shiga cikin sauri ta bar gidan.






Gidan shi ta nufa,amma abin ban haushi get man ya hanata shiga, tace"kaga ka barni na shiga i have sum message to your oga", girgiza kai yayi yace"oga ya hana a bari kowa ya shiga".





Tsugunawa tayi a wajen ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta, tana ajiyar zuciya,k'arar mota taji hakan yasa ta tashi da sauri.





Idanun ta ya sauka akan fuskar shi,murmushi tayi zuciyar ta na cigaba da bugawa,shi kuwa Khaleel mamakin ganin ta yake yi.






Ita kuma wannan me take yi anan??? Abinda ya tambayi kan shi kenan, da hannu yayi wa securities d'in magana suka bud'e mishi get ya shiga itama kuwa ta biyo shi.





Yana parking ya fito jikin shi sanye da complete khaki,wanda hakan ya nuna daga ko taro ko kuma duty yake.





Har ya fara tafiya ta tsayar dashi ta hanyar cewa"heys",juyowa yayi ya kalle ta sannan ya cigaba da tafiya, da sauri tabi bayan shi.





Ganin cewa idan ya nufi bedroom ba hankali gare ta ba itama bin shi zata yi yasa shi tsayawa,kallon ta yayi.




"Haba daga zuwa wajen ka kuma sai ka wani k'yale ni haka ake saukar bak'i a garin ku", duk da d'aure fuskar da yayi hakan sai da ya sashi murmushi.





Murmushin daya shagaltar da ita da kallon shi,sake d'aure fuska yayi yace"meye ya kawo ki? ".




"Nazo ganin ka ne, kwana biyu bamu had'u ba shine dalilin da yasa nace bari na zo na ganka",kallon mara hankali yanzu ya koma yi mata.





"Pls out",ya fad'a cikin had'e fuska, tab'e baki tayi tace"koma dai meye ai na ganka wannan ya ishe ni sannan gobe ka shirya zaka kaini shopping", daga haka ta fice.




Da kallo ya bita yana murmushi "wai zai kai ta shopping", ya sake maimaitawa lallai yarinyar nan bata sanni ba ne,ya fad'a yana girgiza kai.




Dafe kan shi yayi, ga matsalar gida ga wannan tana so ta saka mishi wata matsalar, k'aramin tsaki yaja sannan ya mik'e ya shige bedroom domin yin wanka ya kwanta.





________________________________________________________________________________________

Alhamdulillahi da yake yanzu komai kaga be tafiya to baka fara shi bane, yanzu haka mun gama first semester mun shiga second semester itama mun ci rabi, karatu fa ya fara zafi sosai haka kuma matsalar gidan mu tana nan.






Bangaren khairiyya kuwa zuwa lokacin har an sallamo ta daga asibiti, shima kuma yaya abdallah baban gida da kan shi ya tasa k'annen nashi suka je suka yi belling d'in shi.




Haka kuma ya sasu kowanne ya dawo da matar shi,abu fa sai gaba ya ci domin dai komai na gidan k'ara kwab'ewa yake yi.





Yanzu tsakanina da khairiyya babu eh babu a'a dan idan ta ganni ko a hanya ne bata ma kulani.





Momma kuwa har lokacin bata sauke makamanta ba, dan har yanzu ko gani na bata so.





Masu biki kuwa saura wata uku,wanda su kuma aunty fauza da sumayya har lokacin basu kawo nasu ba.





Ni da Rufaida kuwa sai k'ara mak'alewa juna da muka yi yayin da har lokacin ummi bata wani goyan bayan karatun da nake yi.





A gefe d'aya kuwa k'ani na Abdul'azeez shike k'ara k'arfafa mini gwiwa na yin karatun, wanda hakan ba k'aramin dad'i yake yi mini ba.




Yau sai bayan magrib na dawo kasancewar yau bamu gama lecture da wuri ba,ina sauka daga mota na fara takowa a hankali saboda yadda nake jin marata tan murd'awa kad'an kad'an domin period d'ina ya kusa.





Ina kusa isa gida marata ta murd'a wanda ya sani dole tsugunawa ina kiran sunan Allah,dafe cikin nayi ina jin wata azabar zafi.





Abin mamaki be tab'a yi mini irin haka ba, Amma wannan karan kuma ya zo mini da canjin yanayi.





Kaina har juyawa yake yi, gashi na kusa gida,k'ok'arin mik'ewa nake yi amma bayana ya rik'e hakan yasa dole na kuma komawa na tsugunna.




Yaya khaleel da shigowar su garin zaria kenan kamar ance ya kalli gefen titi,gaban shi ya fad'i kamar yarinyar nan da yake d'aukar nauyin karatun ta🙄.




Kaji yaya khaleel da wata magana irin bema gane ta ba d'in nan wo yaya khaleel mr pretender 🤓.





parking yayi a gefe,sannan ya sauko ya nufo inda nake,ni kuwa jiki nane ya bani kamar ana kallo na.





A hankali na d'ago idanu na na sauke shi akan fuskar shi, rabon dana ganshi wajen wata uku kenan da d'oriya.



Yaui haske sai dai ya rame, duk da halin fa dana ke ciki na iya gano hakan,shima ta b'angaren shi hakane.




Yarinyar ta k'ara girma cikin k'asa da wata hud'u daya ganta,kamar wanda baya son magana yace"tashi muje".




Cikin k'arfin hali na mik'e, yaya abdus-samad dake hango mu yana daga cikin mota yayi murmushi.




Jiri ne ya kwashe ni na tafi zan fad'i da sauri ya taro ni,d'auke ni yayi cak duk da bani da lafiya hakan be hanani istighfari ba domin nasan babu kyau.





Yaya Abdus-samad ya fito ya bud'e baya, shi kuma ya sakani,ya rufe k'ofar sannan ya koma mazaunin shi ya zauna.




Gida muka k'arasa,sai da yayi parking sannan ya bud'e ya fito, bud'e mini yayi na fito ya rik'o ni,k'ok'ari nake wajen k'arfafa jiki na domin bana son tab'ani da yake yi.




Cikin k'arfin hali na fara takawa,yana tsaye yana kallo na har na shiga part d'in mu.




Ajiyar zuciya yayi yayinda ya juya suka had'a ido da khairiyya idanun ta cike da hawaye tana tsaye tana kallon shi.





Harara ya banka mata sannan ya yi mata Alama tazo da hannu,jiki a sanyaye ta taho, shi dai Yaya Abdus-samad yana tsaye yana kallon ikon Allah.




Sai da ta gaishe su sannan yace"wallahi naji kin kwasa kin fad'awa momma cewar tare kika ganmu da juwairiyya sai na miki shegen duka, wuce ki bani waje wawiya kawai".




Yana fad'in haka ya juya ya tafi ya barta a wajen,Yaya Abdus-samad ne yace"Ya jiki", kanta a k'asa tace"da sauk'i",Allah ya k'ara sauki", shima daga haka ya bar wajen.



Da idanu ta bishi, ita tasan cewa ta more miji domin Yaya Abdus-samad yana da hak'uri sosai sai dai matsalar yaya Khaleel ya fishi rank sannan kuma ya fishi kud'i hakan ne ita kuma bata so wato juwairiyya ta auri wanda yafi mijin ta kud'i.





Yo khairiyya hassada game rabo taki ce, kibi a hankali😏.





Jan numfashi tayi sannan ta juya,jiki sanyaye tana sak'e-sak'e a ranta.







Ni kuwa ina shiga jakata kawai

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment