Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komiba,

can anjima yaga ta kalleshi tayi murmushin da baisan nameyeba, Sannan yaga ta sunkuya ta d'auki k'aton Dutse a hanunta sam bai kawo komi aransaba, duk da Murmushin dayaga tanayi ahaka harsukazo kusa da gida,

da sauri Dijah ta k'arasa Jikin wata k'atuwar Bishiyan Kuka ta tsaya awajen tana dariya, kallonta kawai yakeyi har yak'araso wajen yana shirin tambayanta kotasamu matsalan k'wak'walwa ne,

Dutsen da yake Hanunta ta saiti Gidan Zuma da yake kan Bishiya ta wurgesu dashi, ta tsula da mugun gudu tashige cikin Gida, haba ai kan kaceme zuma sun taso gadangadan wajen Kb suka yo ga wani adabbaben turaren dayake tashi ajikinsa, ga k'afansa har yanzu batagama dawowa Normal ba,
Tashin HankaliπŸ€”

Gudu yafara mai kama da sassarfa, Sake fitowa tayi daga cikin gidan tatsaya abakin k'ofa tana tafi "Gurgu sai katsere, Gurgu sai katsere,

dai dai lokacin Motan sani tafaka awajen ganin haka yasa ta juya ta koma batare da yagantaba.

cikin zafin nama Sani ya Bud'e motan Kabir yashiga ya rufe baiyi auneba yaji Harbin ahanunsa Runtse ido yayi yana yarfe Hanun ya jingina kansa ajikin seat d'in motan yanajin yanda harbin yake ratsashi Sani ya had'a hannayensa yakashe zuman k'waya d'aya data biyoshi, yana kallon Kabir, yace

"Sory garin yaya Kb? Tunda nazo garinnan bantab'a ganin zumannan sun tashiba, ko turaren kane yad'agosu?


Bud'e idonsa kawai yayi ta glass d'in Motan yake ganin yanda zuman suke shawagi awajen batare da yace komiba,


Ahaka Baffah yafito daga cikin gida zai shiga gari dukansu suka fito Kabir yana goye da Hannayensa abaya suka k'arasa suna masa sannu,


"a Sani kadawone? Ya kabaro mai jikin?

"a jiki Alhamdulillah,

"to Allah yak'ara mata lfy
"Ameen,

Kallon Kabir yayi "yace Kabir har kundawone?

"Eh Nadawo ind'an hutane ya fad'a yana shafa kanshi,

"to barka inace dai ba wani matsala?

Sani yace Zumace ta harbeshi Baffa,

"Subahanallahi garin yaya Kabir? Yarane suka tab'osu ko? Dondai basu tashi hakanan,

Sunkuyar da kansa yayi tabbas da yasan Sani zai fad'a daya kwab'eshi,

Yana d'an murmushi ya kalli Baffa "nad'an zaunane ak'asan Bishiya watak'ila k'arfin da turarena yake dashine yasa,

"Ayyah to sannu barin dubomaka magani kashafa.


Tundaga wannan Rana Kabir yayi saranda wa Dijah yayarda da kirarin da mutanen garinsu suke mata, ya k'ara mata matsayi sosai awajen Hatsabibanci, yak'udura aransa bazai sake shiga sabgantaba,

To ab'angaren Dijahn itama hakane saida takoma gida gaba d'aya taji kunya yakamata sam taji bata ji dad'iba can kuma taturo baki ita kad'ai tace "to shima wayace ya shunamin Mage? Wlh inyasake nima Ramawa zanyi, ko da dare yayi bata yarda takaimusu Abinciba Bintalo ce takai tea d'in sama da tadafa wa Jebu tabayar takai masa wasan b'uya suka dinga yi sosai.



*Rayuwa kenan* yau take Alhamis ayaune Mami ta diro Rugan Juma da niyan komawa da Kabir.

Bak'aramin tarba Inna tayima Mami ba, dukda tamusu zuwan bazata, bayan ta hutane ta tambayi Su Khadjah, Inna tace sunje can gidan kakar su Goggoji,


Ayyah KB fa zai tafi yabar Dijah to ko yaya zata kasance
Kubiyoni


*Ummu Fatima ce* 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA*πŸ‡³πŸ‡¬

*Don Allah kuyi Hak'uri my Fans najina shiru da kukayi, Blood sister nane akamata cs ancire twins acikinta ina ta d'awainiyan asibiti Sam bana samun zama,*


🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣0⃣


Washi gari da safe Mami tashiga d'akin Baffa Bayan su Gaisa ta gyara zama tana kallonsa anitse tace "Baffa Bani da Bakin godiya agareku na irin d'awainiya da kukayi da Kabir, sai dai Addu'an Allah ya muku sakamako da Gidan Aljannah,


sannan ina k'ara Godiya game da Babban kyautan da akamana na amincewan Bamu auren Fatima, masu kawo kud'in aure sunkoma suna san barkan irin tarban da akamusu, naji dad'i sosai Allah yak'ara Girma,

"Ameen Baffa yace sannan yad'ora da "Hajiya Kabir yafi k'arfin Komi awajena sam babu godiya tsakaninmu, Haka banso Rabuwa dashi duk da dama nasan jinyane yakawoshi inyaji sauk'i zai koma amma Sam naji babu dad'i,

Mami tad'anyi Murmushi "a'a Baku Rabu da Kabir ba, Allah ne yahad'amu Baffa Insha Allah Muna tare,

Ya jinjina kai yace to "Allah ya taimaka, nagode sosai, kukuma haka Allah yayiku? Wasu na k'yaman 'yank'auye ku kina k'aunansu,

"a haba wazai k'yamaci tushensa? Mami tafad'a tana murmushi,

Baffa ya gyad'a kai yace "hakane ga mai tunani,
maganan auren Bintalo kuma Hajiya duk lokacin da kuka shirya kuzo kawai insha Allahu baza'a sammu wata matsalaba,


Mami tad'an k'ara muskutawa tana kallon shi tace "to Baffah nagode Allah yabar zumunci,

Shiru ta d'anyi sannan ta d'ago ta kalleshi, Mnnm Baffah karka gaji dani, nakuma zo da k'ok'on barana har iyau, inaso kataimaka kabani Khadijah intafi da ita, taci gaba da karatunta, don naga yarinyan tana da k'ok'ari sosai kuma tana son Karatu, ta k'arasa tana kallon idonsa, shirune yabiyo baya, sannan ya nisa yana jinjina kai ya d'an tura Hulansa baya yana shafa fuskansa, yace "to Hajiya Bank'i mikiba, sai dai kinsan munan karkakra bakaman Birniba, can rayuwa ne na kowa ya iya Allonsa ya wanke, ba Wanda zai sama ka ido cikin lamuranka, sab'anin Mu nan da duk abunda kayi idon wani na kanka, yanzu ina d'aukan Dijah inabaki, to ina mai tabbatar miki m da fita kuma sai dai inzan sa Abu intoshe kunnena, kowa da irin Abun da zai dinga fad'a akaina, nabbata akwai wa inda zasu iya cewama na turata karuwanci don dama idon kowa nakan Dijah, Kiyi Hak'uri Hajiya Ba hanaki Dijah nayiba sai dai ina gudun gutsiri tsoman jama'a,

Mami tad'anja numfashi, tace "to ai karatu zataje tayi kaga yanzu bai wuce saura wata d'aya da wani abuba tagama secondary kuma anan babu makarantan da zataci gaba inaga kaman hakan ya ishemu Hujja,

"Nasan aranki zaki tsammaci nine baniso, wlh karatun nand'inma karkiga yanda ake zagina akai, kawai dai na toshe kunnena, ayanzu koda auren Dijah nayi abirni sai nasamu masau zagina agaefe don komi indai akan Bintalo zai zo da sauk'i, sab'anin Dijah.


Shiru Mami tayi na lokaci sannan ta Nisa tace "to yanzu kana ganin ba wata hanya ko wata dabara da zammuyi? Tunda ga 'yar'uwanta basai in anyi bikin Fatima sai sutafi tareba, inyaso daganan sai tacigaba da karatunta,

Baffa kam rasa irin bayanin da zaiyi ma Mami ta fahimceshi yayi don haka sauk'e kanshi k'asa kawai yayi batare da yace komiba.

Aranshi yana tunani yaza'ayi ya d'auki 'yarshi mace yabada ita atafi da ita sannan ba dangi iya bare na Baba haka, duk da dai baya zatonsu da wani mummunan abu, bazai iyaba,

Ta hanyan aure ne kawai zai iya yarda yarabu da Dijah, bahaka kawaiba,



Mami tayi shiru aranta tana tunani tabbas tasan abune mai wahala dama Baffa ya amince yabata Dijah cikin sauk'i,

Don Haka ta nisa tace "karka damu Baffah zamu samu mafita insha Allah barinje inga Marar lfyn naka, tafad'a tana mik'ewa, sashinsu Kabir ta shiga kai tsaye.

Kabir yana zaune cikin kujeran Roba ya zuba k'afafunsa ackin guda dayake gabansa ya manna bayansa acikin kujeran kansa yana kan saman kujeran yana kallon Sani da yake taramasa abubuwansa masu amfani acikin akwati yanata masa shak'iyanci kala2

Shikuwa Kb kallonsa kawai yake bako k'ifta ido batare dayace komiba,

Jin motsi abayansane yasashi juyowa, yasauk'e idonsa akan Mami, Murmushi yayi har hak'oransa suka fito,
Yasauk'e k"afafunsa yana kallonta, "Welcome My Mum tun d'azu nakesa ran ganinki Mami,

Murmushi tayi ta juya tana kallon sani, tarik'e hab'a "Wai duk d'okine hakan yasa kukafara shirya kaya tun yau? Kabir ya langab'ar dakai "Mami inacefa yau zamu tafi, "Haba Kabir sai kace d'aukan wuta, sai mun k'ara sati nangaba, tayi maganan da zolaya, Sani yafito daga d'aki yana dariya,

Yaja kujera d'aya yazauna yana fuskanta Mami,

"Wlh Mami tun jiya yad'agamin Hankali daga jin isowanki yasani nafara perking sai kace yak'i,

Ni wlh yanzu garin yafaramin dad'i yafad'a yana shafa kansa,

Kabir ya wurgamasa Harara "to wayace dole sai katafi? Kayi zamanka tunda yanzu kazama mara kunya kaci gaba da rashin kunyanka, daga Haka yajuyo yana magiya ma Mami, dariya kawai take.




Tun bayan fitan Mami Dijah take zaune awajen gaba d'aya jikinta ba k'arfi tarasa meya kashe mata jiki ko aikin da ta sabayi yau kasawa tayi,

Ahaka Mami tazo tasameta agun ta zauna agefenta tace "yadai Khadijah? Dariya tayi tace "babu, sannan ta tashi tafita,

Tulu ta d'auka ta lek'a d'akin inna tece mata ta tafi d'ibo Ruwa, tana fita tashiga gidansu Jebu suka fito suka tafi Rafi suna dawowane Jebu ta rik'o gefen Mayafinta "wai Dijah meye yasameki ne yau naganki kaman baki da lfy?

"lfy na k'alau ta amsa atak'aice tana cigaba da tafiya Nima haka kawai tun jiya najini bani dai2


"To Allah dai yasa lafiya inji Jebu yauwa yau da safe naji Iron gidanmu yana cewa d'an birni zasu koma garinsu, dagaskene?

Dijah ta sauk'e ajiyan zuciya, "Haka dai jiya Mamin sa tagayamin, kinsan meye? Wai tace tanason tafiya dani, nasan kuma Baffa bazai tab'a yardaba nima kuma wlh tsoro nake ji,

Jebu taja ta tsaya agun tana kallon Dijah cikin damuwa tace Dijah tafiya zakiyi kibarni?

"yaushe Baffana zai yarda? Wlh nasan bazai yardaba,

Jebu ta yi ajiyan zuciya tace "wlh inason kije Birni ko don wata ran inje wajanki sai dai bani son kitafi ki barni inkin tafi shikenan bani da k'awa,

Dijah inason zuwa birni ban tab'a zuwaba inason inje inga yanda ake lbrn birni,

Duk maganan da Jebu takeyi hankalin Dijah baya wajen ta lula wani Duniya da bansan inabane,

Sosai Kabir ya tasa Sani da iro agaba sai da suka gama had'a masa duk wani abun da zai tafi dashi kafin suka kwanta Bacci,

Washi gari kan kace me sai gashi har Kb yagama shirinsa fes cikin k'ananan kaya blue jeans da farar shirt mai layin blue mai gajeran Hanu, bak'in socks yasaka da bak'in takalmi sau ciki, sai baza k'amshi yakeyi,

Duk tsokanan da Sani yakemasa ko ajikinsa, Burinsa kawai yaga Mami tashigo cikin shiri,

Yanatsaye Hanunsa d'aya na cikin aljihun wandonsa yad'aga d'ayan Hanun yana duba agogo mai cain d'in silban da yake d'aure ahanun,

Dai2 lokacin suka shigo ita da Dijah datake rik'e da flaks tana binta abaya,

Kallonsa takeyi har suka iso shikuma idonsa yana kan Mami, zai yi magana kenan, Mami ta dakatar dashi tana nuna masa flakcs d'in hanun Dijah "karb'a ka karya kafin kafaramin wani coplain,

Bin inda ta nunan yayi da kallo, sosai yayi mamakin yanda yaga Dijah so silent kaman wanda k'wai ya fashewa aciki take abu, jan kujera yayi yazauna ahankali ta durk'usa agabansa ta'ajiye flacks d'in dai2 lokacin Bintalo ma tashigo da kulan soyayyar doya da kw'ai ta ajiye tana gaisheshi,

Mami tace "Khadijah d'auko cups kizo ki had'a masa tea,

Tana had'a tea d'in shikuma ya tallafi hab'ansa yana kallon Hanunta, bai tab'aganinta cikin nitsuwa hakaba, saidai yasa aransa tana da dalilinta nayin hakan, watak'ila wani iban Albarkan takeson yi masa,

Tana mik'a masa ta had'a ma Sani sannan ta juya ta tafi, Haka Mami ta tasashi gaba har sai da Yaci ya k'oshi sannan ta koma sashin Inna alokacin Dijah tana zaune akan itace ta Rafka tagumi, "khadijah je ki tattaro abun da sukayi break d'in ki shigo dashi, tana fad'an haka ta shige toilet, don watsa Ruwa,

Zaune ta sameshi a inda ta barshi yana rik'e da goran Faro yana sha anitse gefensa Iro ne yana zabga godiyan irin kayan da Kb ya taramishi,

Kallo d'aya yamata ya kau da kansa, har ta iso bai kuma kallon inda takeba,

"Khadijah taji muryansani daga d'aki, amsawa tayi ta shiga da sallamanta duk da labulen ad'age yake,

Kallonta yayi yana Murmushi "K'anwata yadai naganki haka?
Ko kinajin Rabuwa da mutumin nakine Abokin fad'anki?

Turo baki tayi "wayene Mutuminan? Da bakinsa ya nunamata Kb, da Harara ta kalli inda Kabir d'in yake yayi dai2 da lokacin da yajuyo yana kallo cikin d'akin, shima Hararan yasakarmata, atare suka janye idonsu,

Sani ya kwashe da dariya, ya jawo wata Leda ya mik'a mata "Ga wannan wayan kiba wa Fatima kice mata tahad'a zank'irata,

Gaskiya zanyi Missing naku Khadijah, don Allah inma tak'i karb'a kihad'a zan k'ira,

Dijah ta gyara tsayuwa tana juya ledan ahanunta, "Yaya Sani ai dagani Har Bintalo ba mu isa karb'an wannan kyautaba,
Saidai ka kaima Baffah inya karb'a to, Amma nasan innina karb'a zaimin fad'a tak'arasa tana ajiye masa wayan akan akwatinsu,

Kai ya jinjina aransa yana k'ara yabama Tarbiyan Baffah

Afili kuma yace "Naga dai ni yayankune Khadijah yanzufa munzama d'aya,

"Duk dahaka wlh Baffah zai yi fad'a sosai,

"Ok to badamuwa zanbashi,

Tabi d'akin da kallo tace "Bayau zaku Kwashe kayanku bane? Cikin zolaya yace

"Kabir yace yabar miki duk kayan d'akin, har frich d'in ki dinga shan Ruwan sanyi,

Ta tab'e baki tace "baniso daga haka ta juya tafita,

Cups d'in gaban Kabir ta sunkuya tana kwashewa dagangan ya saiti Fuskanta ya matsa Goran Faron dake Hanunsa, Ruwan ya tsartu ya wanke mata Fuska, tana d'ago kanta ta juya tafita batare da ta kalleshiba, d'an Murshin Gefen baki yayi yarakata da ido,


Misalin 11:00 na safe suka fito kusan gaba d'ayan "yan unguwa sun Hallara ajikin Mototinsun, Sosai sukaji Rabuwa da Dr Kabir domin ba k'aramin amfana sukayi da zaman nashi, musamman wajen kula da lfynsu don tun kafin k'afansa ta fara warkewa duk wani mai cuta inyazo wajensa zai dubashi ya rubuta masa magani inkuma akwai awajensa zai d'auka ya bashi ya shashsha aikan Sani ya sayo masa magunguna acikin gari don mutanen wannan yanki,

Tsaraba kam Kabir har yagaji da karb'a daga masu bashi zabbine, k'wai ne fruit ne kai har da masu bashi naira d'ari, d'ari biyu, Baffah kam Saniya yasa aka yanka aka sa ad'ayan motan seceurity,

Sosai ya matsu Mami tafito su tafi, k'asa2 yake ta tsaki Gashi ko yak'irata bata d'auka, ahankali wasu suka Fara Raguwa, ahaka ya hango Mami rik'e da Hanun Dijah gefensu Bintalo ce da Ma'u da Jebu,

Har suka iso bakin Motan yana kallon Fuskan Dijah ko ba'a fad'a masaba yasan tayi Kuka sai dai bai san dalilinta na Kukan ba,

Kwantowa Mami tayi dai dai Kunnenta ta gayamata magana sannan tasake Hanunta ta shafi gefen Fuskanta ta shige Mota, ahankali ta tako kusa da Kabir da yake k'ok'arin Bud'e Murfin Mota, murya k'asa2 tace masa "Yaya Kabir Allah ya kiyaye hanya ku gaida gida,

Kai kawai ya jinjina yana kallon k'wayan idonta, ya shiga Mota, gafen Sani ta Matso tace "yaya Sani Allah ya kiyaye hanya,

"Amen k'anwata Baffa yak'i karb'an wayannan anma zan k'iraku da na wajen Iro. Yafad'a yana kallon Bintalo datake ta b'uya abayan Ma'u

Ta gyad'a kai tana juyawa, Motansu ta fara juyawa zata tafi kenan sukaji ana buga Motan alamun su tsaya, Goggoji ce ta k'araso wajen, ganinta yasa Kabir saurin zuge gals yana dariya, "kai tsohuwa yau danafi bamu ganaba danamiki saki tara,
"waneni Kabiru wlh natafi can waje gyatumace tarik'eni da tad'i, zaka tafi baka bani magani naba Kabiru,

"na isa? Ai nabama Fatima ta kai Inna ta ajiye miki zata miki bayanin yanda zaki sha inya k'are kigayama Iro yagayamin awaya zanbayar akawomiki wani, Gogoji takamo Hanunshi tace Kabiru Allah yamaka Albarka yabaka zuri'a mai Albarka ta kunce bakin zaninta ta ciro gudan naira Hamsin tasa masa ahanunsa, da zobe mai kyau na azurfa "wannan Zoben ka adanashi duk lokacin da Allah yasa ka auri matan da kake sonta kaba ta wannan zoben nima Mijinane Allah yajik'an Rai yabanishi adaren amarcinmu,

Kabir yana murmushi yace to Goggoji na gode sosai Allah yasaka, Hamsin d'infa? Kasha Ruwa ahanya, daga haka ta juya ta tafi, motansuma tayi Ribas tafara tafiya tacikin madubi yake kallon Fuskan Dijah da yake ta ambaliyan Hawaye, d'ad'd'aikun Mutane dasuka saura agun sai d'aga musu hanu sukeyi har suka bar wajen,

Kwantar da bayansa Kabir yayi yana murza Zoben da Goggoji tabashi yana tunani magananta, yad'anyi Murmushi a fili yace "indai don so ake aure to har abada bazanyi aureba Goggoji don bawata mace dazan so har abada, bayan Mami ta.





Tofah masu karatu kunji furucin KabirπŸ€”

Wai ya zata kaya gadai Kabir zai koma gida ga kuma Alhaji ya'u babban mak'iyinsa waishin yazaiyi randa sukayi ido hud'u da Kabir??...
Kubiyoni

*Gamasu buk'atan comments ko gyara ma wannan labari k'ofa abud'e take ga no. ta :08065091824: sai naji ku taku Ummu fatima* 😍
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣1⃣





Sani yayi kamar bai jishiba aransa yana addu'an Allah ya nunamasa randa zaikama Kabir da wannan furucin dayadad'e yanayi,


Kwanciya yayi luf acikin sit d'in yana kallon motan Mami da yake tafiya kaman bazai tafi, Don sam Mami bata yarda ayi agudu da ita, shiyasa har yau tak'i canja tsohon drivernsu, juyawa d'ayan gefen yayi yana kallon motan seceurity sum airin tafiyan sauran motan sukeyi, yaja d'an gajeren tsaki afili yace "Wlh na matsu inganni acikin d'aki na gaskiya nayi missing Bed d'ina over,

Sani ya kalli agogon Hanunsa, ka kwantar da hankali Minti goma kacal ya rage insha Allah,


Wai Kb wani mataki zamu d'auka akan Alhaji ya'u ne?

"kafa iya ma bakinka nagaya maka banison Mami tagane cewa yana da Hanu cikin maganan har sai kungama binciken ku kun gano kome.

Sani ya d'an kalleshi "kana nufin har yanzu baka gamsu bane? Duk hujjojin dana baka basuyi bane? Najima ina zargin Alhaji ya'u cikin son ganin yaga bayanka, sai gashi zargina yazamo gaskiya yanzu da abunnan yafaru wlh ranan da suka tsare motocinmu da idona naga gayannan lokacin da yabi Motanmu yana Harbi sannan kuma da idona yanzu nake ganinsu tare da Alhaji ya'un,


Sannan naji da kunnena suna hiran bayan maganan da Nafisa tagayamin yagaya mata,

Bai kamata azuba masa idoba Kabir yakamata ada'auki mataki,

Kabir yad'an Murmusa yana kallon waje yace "Tun kafin ka gayamin wannan magana nida Habib munsan komi, sai dai inason abi komi ahankaline, ko bakomi ubanane shi sannan kuma ina sa ran auren "yarsa don inason cikama Mami ta Burinta, don bata da Burin da yawuce haka.

Tunda mai gadi ya wangame Gate d'in gidan, Kabir yake ta murmusawa har suka faka aka bud'e masa k'ofa yafito pert d'insa ya shige kai tsaye, komi na part d'in agyare yake fes dashi har yanzu k'amshinsa yana nan kaman koda yaushe, afili yace "wannan aikin Mami tace, uwa ta gari Allah yabani daman cika miiki burinki koda Hakan yana nufin Bak'in cikinane, indai ke zakiyi farin ciki shikenan,

Yana shiga Bed room ya zube akan gado ya lumshe ido yana shak'an iskan dake shiga da fita ad'akin, photon Dijane yazo masa idonsa siraran Hawayenta da yake sintiri akan fuskanta yake gani da sauri ua zabura yatashi ya zauna afili yaja tsaki yace "stupid girl, ya mik'e yana k'ok'arin rage kayan jikinsa aljihunsa yaji abu ya ciro zobe da Hamsind'in da Goggoji ta bashine yayi Dariya yana girgiza kai ya zubasu akan Mirrow, ya shige toilet,


*Bayan sati d'aya*


Zaune yake akan kujeran k'ofan shiga part d'insa ya d'ora k'afansa d'aya akn Table d'in dayake gabansa yana waya da abokan aikinsa, kan yanda tafiyansu zata kasance, nan da sati biyu, Motoci ne guda biyu suka shigo gidan kusan ajere, d'aya nasu Abban Habib ne da uncle Musa d'aya kuma na Alhaji ya'u maida kansa yayi yaci gaba da wayansa batare da yakalli fitowansuba,

Yana gama wayan ya tashi yashiga lambun gidan yana zagawa, jin wani abu yakeyi aransa mai kama da kewa, Sannan wani sashi na zuciyansa yana kamomasa photon irin shak'iyancin da Dijah takeyi yarasa meyasa hakan ke damunsa, yana cikin wannan Tunani yaji wayansa tana Ringin yana dubawa yaga Mami ya kara akunnensa, "kasameni afalo ta fad'a atak'aice sannann ta kashe batare da taji me yaceba,


Zaune suke su biyu akujera d'aya Alhaji ya'u yana fuskantansu, yayin da Mami take tsiyaya Ruwa agaban Alhaji ya'u, ta koma ta zauna shikuma ya d'auka yafarasha yana d'an mata wasan da suka saba (wasan k'anin Miji, ) dai2 Lokacin ne kuma Kabir yashigo da sallama, har ya iso tsakiyan Falon Alhaji ya'u yana shan Ruwa, Kabir yasami guri ak'asa daf k'afan Mami yazauna, tas sukaji k'aran fashewan cup agurin gaba d'ayansu dama shi suke kallo ban da Mami da take kallon Kabir, Gaba d'aya ya dirieice har yafara tunanin ko magarki yakeyi, wani irin zufane yake ketomasa ta ko ina, jiya2 yagama narka mak'udan kud'i wajen canja takardun cpanin Kabir d'in yana mafarkin campani yazamo nashi sai gashi yayi mafarkin ganin mai campanin,

Cikin tashin hankali yanuna Kabir "Dama kanan ataye?

Kallon2 Abba sukayi shi da Uncle Musa, Mami tad'an Nisa tafara magana "kayi Hak'uri Dadinsu tun randa muka dawo da Kabir nake k'iranka awaya, dama nafidon sai kazone gaka gashi inshaida maka yanda akayi, Kabir yana raye bai mutuba dam..

Dasuri Uncle Musa ya katseta ganin zata ruguza musu plan, "Eh tabbas Kabir yana raye Dama hatsari yayi ahanyan Abujah likitoci suka tsinteshi kasancewan sun sanshi yasa suka rik'eshi agunsu basu sanar da kowaba, kodayake sun kaffa hujjan hakan dacewa yasamu matsalane ak'wak'walwansa,

Har saida sukaga yafara warkewa suka sanar damu, tunda aka dawo dashi aka k'ira akan kazo kaga d'anka yana raye bai mutuba, baka samu zuwaba sai yau.


Cike da mamaki Mami ta kalli d'an'uwanta dan batasan dalilinsa na b'oyema Alhaji ya'u zancenba, a ganinta ko za'a b'oye ma wani shi bai cancaci a b'oye masaba.


Shikuwa tsaban Rud'anin da yashiga daga farko bai ji abunda akecewaba, sai kalman k'arshe yaji wato Karbi nada matsalan k'wak'walwa,

Ganin irin kallon dasuka shiga masane yasa yawayence cikin k'arfin Hali yafara fad'a ta inda yake shiga banan yake fitaba, ya tashi yana fad'in shikenan tunda kunnunamin niba kowabane awajen Kabir saidai kurik'e aranku ina da rana zaku nimeni komin jimawa, haka yafice ko gani baya yi da kyau, yana karad'e hanya ya isa Mota,


Kan Kabir nak'asa yanajin yanda Mami take complain d'in sam basu kyauta masa ba sosai suka fahimtar da ita cewa hakan duk a rarrashin kar yad'auka da zafi ne,


Bayan sungama ne Mami tasanar dasu Waliman

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment