Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hijabi ne ajikinta ta tattareshi ta d'ora akan wuyanta, tun daga sama Har k'asa yake kallonta, Maganganun Mami na d'azu na masa yawo akai, wata zuciyan tace kai Man ya kaman ka damu? Mezakayi da wannan k'wailan? No badamuwa nayiba, Mamine banason taga banmata biyayyaba bata cancanci haka agareniba,


jin kaman ana kallonta ne yasa ta juyo da sauri ta juya tana gyara Hijabinta, ahaka ya tako yazo yatsaya abayanta yayi Huging nata, "yan mata meya kawoki nan? Da izinin wa kika shigamin kitchen Har kike girki?

Cikin in ina tace "Mami ce tace inzo in dafa maka,

"mhmn shine ba niman lzini? Ko kin manta yau matata tana gidannan,

"cikin b'acin rai da tuk'uk' tace matarka ko 'yar iskanka?

Murmushi yayi ya zago gabanta yad'aga Hab'anta, yana kallon Fuskanta, kallo d'aya tamasa tayi saurin kauda kai ta juya, da k'arfi ya kuma juyo da ita ta sake sinne kanta sai lokacin ya tuna gajeren wandone ajikinsa yasan duk yanda yakai da son tsokananta tayi ta tsiwa bazata sake tayiba dan haka yasaketa yafita,


Tree quater ya canza yazo yazauna a falo haka nan yajishi bayajin dad'i,

Yana zaune ta fito da k'aton plate Dankali tasoya da kwai sai ta dafa masa indomie da yasha d'anyen kifi da vegatables sai k'amshi yake.

Agabansa ta dire ta mik'e zata, "Ke zonan ina zaki?

Ta turo Baki "Naga ai nagama abunda aka turoni inyi,

"No dasaura zoki zauna anan, Zama tayi agefensa ya mik'a mata spoon "Bismillah
"Ni nak'oshi!
"Baki isaba yarinya kiyi abinci kice bazakiciba, Me kika barbad'amin Aciki? Ko kinsa wani gubanne?

Ta tab'e baki tana kallo sa da zan samaka wani Abu a Abinci da tun a Ruganmu a Gidanmu nasa maka kaci inma mutuwanne da yanzu wani ake zance ba kaiba Likita.

"Mhmm naji karb'a kici yafad'a yana maamki furucinta ashe ta iya magana haka,

Wani spoon ya d'auka yasaka yafara ci loma uku tayi ta ajiye,

"Saifa muncinye tare
"ni nak'oshi d'azufa kikayi Alk'awarin kindaina musu dani

Mai dakai tayi suka cigaba da ci.

Mami ta shigo da sallama tana kallonsu Khadijah yanajiki shiru baki gamabane? ta k'araso dasuri Dijah ta ajiye spoon d'in Kb yace tanacin Abincine

juyawa Mami tayi inkingama maxa kizo ki kwanta dare yayi inajiranki yanxu




UMMU FATIMA 😘
.
[7/19, 8:20 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š

4⃣4⃣


Mami tana fita Dijah ta tashi asanyaye zatabi bayanta,

kabir ya Harareta gami da d'anjan tsaki yacigaba da cin Abincinsa, "Malama kikawomin Ruwa, kinba wa Mutum Abinci ba Ruwa",

Wurin da freach yake tayi ta d'auko masa goran Ruwa ta ajiye agefensa,

"Oya zauna waye zai tattara miki wajan innagama? Komawa tayi ta zauna,

tana zaune har yagama ta tattara wajen ta kai Kitchen ta wanke duk abunda ta b'ata ta maidashi ma'ajinsa, ta Goge kitchen d'in.


Tana fitowa kai tsaye hanyan fita tayi,

"Ke Khadijah zo nan Kb ya fad'a a Gadarance, kaman Bazata dawoba sai kuma ta dawo a d'an gefenshi ta tsaya tana tura Baki "Gani
"D'an zo kimin tausa ya fad'a yana mik'e k'afafunsa, Hararansa ta shigayi sama da k'asa ta juya yayi saurin finciko Hanunta ta fad'o k'irjinsa, da iya k'arfinsa ya matseta, tana kiciniyan k'wacewa yafara kissing d'inta, lumshe idonta tayi ta kwanta luf ajikinsa tana numfashi ganin haka yasa ya birkitota yana shirin..ciremata Riga dama tuni ya rabata da Hijabinta... Kawai sukaji ana knoking. "Khadijah! Suka jiyo Muryan Mami daga waje tana k'ira, arazane Dijah ta zare Bakinta acikin nashi tana k'ok'arin tashi, ya manneta ajikinsa, Murya na b'ari tace "pls pls Likita Mami ce dan Allah kasakeni zata shigo, k'ara k'ank'ameta yayi yana kallonta da birkitattun idanuwansa, "So What in Mami ne? Akwai abun da zaki b'oye matane? Keda kika ce mata anmiki Fyad'e? Gwanda kibarta ta gani da idonta basai kinje kina b'ata bakinki wajen Bata lbr ba,

Yasake k'ok'arin Manna Bakinshi da nata yana tura hanunsa Cikin Breast d'inta, dai dai Lokacin Mami ta tura k'ofan ta shigo, a birkice Dijah ta tureshi ta zame k'asa tare da fashewa da Kuka, dan kunya Kam tagama jinsa, "Khadijah baki gama cin Abincin bane? Mami ta fad'a cikin dakewa, tana kallon Kabir da yake ta Sissine kai, tarik'e Hab'a "lfy kuwa Kabir wani muguntan kamata take kuka? Batajira abunda zai ceba tajuya tanacewa, "Inkingama cin Abincin dai Khadijah kizo ki kwanta haka kema ki huta ma Ranki dare yayi, tana fita Khadijah ta mik'e dasauri tana kuka tayi hanyan fita shima da sauri ya mik'e yabi bayanta tana shirin antayawa da gudu ya rungumota jikinsa, zubewa tayi ak'asa ta had'a hanunta Biyu tana kuka "dan Allah Likita kabari Mami cefa take k'irana dan Allah kayi Hak'uri baniso wlh,


Ya lumshe idonsa ya bud'e yana kallonta, sannan ya tsuguna ya sake rungumota, "fad'amin mene ne bakiso? Kafin tasake cewa wani abu, yafara k'ok'arin fitar da ita a Hayyacinta, tuntana Tirjewa har taji yana shirin cin nasara akanta, Saboda Kb Namijin Duniyane na Gaske ba na Wasaba, k'ok'arin ciremata Riga yafarayi nan ta ankara tadage iya k'arfinta ta tashi da k'yar ta fice anan tabarshi yana maida Numfashi, tsawon Lokaci sannan yaja tsaki yad'ago Hanunsa yana lissafin sauran kwanakin da suka rage aurenshi da Nafisa,


A k'ofan shiga Falo Dijah ta tsaya tana share Hawayenta ta kama Bakin Hijabinta, tayi ta Goge Bakinta tana zubar da yawu, sai Allah ya isa take jerawa ba k'k'k'autawa, ta gyara Riganta da aka kusan ciremata tayi, Sannan tashiga, atsaye tasamu Mami a Falo tazuba ma k'ofan shigowa ido, wani irin kallo ta dinga Binta dashi, sannan ta juya ta shige bed room d'inta ba tare da da tace mata komiba,

Akasalance Dijah ta shige d'akin lya alokacin iya tana shirin kwanciya, Dijah ta haye Gadon ta kwanta luf tana sauk'e ajiyan zuciya, wani irin yanayi takeji ajikinta, gaba d'aya takasa Fahimtan meke damunta, "wlh bazan tab'a yafe masaba, ta fad'a asnyaye batare da tasan yafito filiba,

"Keda waye kuma? Iya ta tambaya tana k'are mata kallo,


"To kekuma lya me Ruwanki? Nayi da kene? Ta fad'a da Muryan kuka.

Iya tayi Murmushi "a'ah a'a Maida wuk'an, Khadijah am bani nakar zomonba, Ratayanma ba abaniba, Amma dai kid'an matsamin agadona kwanciya zanyi,

Ta turo Baki "yanzu lya duk filin nan bai lshekiba sai namatsa?

"Oh yau Naga k'arfin Hali Nida gadona, akan kebaki dashine kodai akaina zaki sauk'e fitinanki, baga d'akin kiba can.


Mik'ewa tayi Fuuu ta fita lya tayi Dariya tana girgiza kai, "Oh Dijah Manya" Allah dai ya kyauta

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Lokacin da Nafisa ta shiga Gidansu tun daga falo take ta rafka ma Mamanta k'ira da sauri ta fito kafin tace wani abun Nafisa ta fad'a ajikinta, "Mama ya wuce wlh ya tsallaka naci wannan Game d'in ya fad'a tarko d'aya", ta fad'a cike da tsantsan farin cikin samun Nasara,

Maman ta kamo hanunta tana dariya suka zauna, "To yabatun Abincin? Sunci?

"Basu ciba, Nan ta kwashe yanda akayi ta gaya mata,

"Inbandake Nafisa yazaki barbad'a musu garin Magani akan Abinci? Ai dole su gani, acikin tukunyan Abincin zakisa tun yana wuta ya nuna dashi duk iya muna funcinta bazata ganiba,

"Ai yanzun haka zan musu, inta d'ora zanje inzuba dole suci, Haka suka dinga tattaunawa har sukaje suka kwanta,


Washi gari kusan Azahara, Nafisa tace bari ta fara gwada aikinta ta gani bayan ta shirya, tak'ira, Kb alokacin yana zaune a Office shi kad'ai yana Brawsing, yana d'auka ta kashe Murya "Helo Kb kazo gida ina niman ka yanzu2

Dum yaji maganan ya cire Wayan akunnwnsa ya sake duba sunan Nafisan dai ya sake gani, ya mayar Kunnensa, Yace "Helo sake maimaitawa tayi, sosai yayi mamaki anma kasancewan bata tab'a mishi irin hakaba sai yayi tunanin ko wata matsalance, mik'ewa yayi yana fad'in "Wani Gidan?

"Nan Gidanmu man"

"Ok gani zuwa yafad'a yana gyara necked tied d'insa,

Ganin ba abunda zaiyi yanzu a Office d'in yasa ya shiga Motansa ya nufi Gidansun,

Tanaji anbud'e gate ta lek'a ai tana ganin Motan Kb ta daka tsale ta shiga d'akin Mamanta ta fad'a jikinta, bata tab'a k'iransa yazo ya d'auketa yazo akan kariba lokuta dayawama kai tsaye yake cemata shifa ba driver bane, sai dai yasa azo a d'auketa, "Mama Magani yaci wlh gashi ina k'iransa ko 10 minutes baiyiba ya iso,

"Mamnta tana dariya tace "aifa Nasan Boka sam baya wasa indai zaki sakar masa kud'i zaki ga aiki,

Tam bud'e kunnenki da kyau kiji abinda zance miki, ta fad'a tana k'asa da Murya, "karkiyi wasa bawai kawai kisashi ya rabu da Matarshi shikenanba, kud'i ki dinga karb'o mana mak'udan kud'ad'e ahanunsa, saboda bazamuyi sanyaba zamuke yawan zuwa gun Bokannan yana bamu magunguna,

Dai2 Lokacin wayan Nafisa ya hau Ruri, ta d'aga yace
"Ganifa na iso,

"Haba Kb kashigo mana sai kace Gidan Bak'onka? Ok ta fad'a, Sannan ta kashe wayan, a Falo ta sameshi ta zauna Gefe tana Murmushin Kissa, "My Luv ko nimana bakayiba yau da safe why?

Ciki dakewa yace
"Na nimeki mana duba wayan kigani cikin kissa tace Oh nabar wayanma acan Gida, nasan wancan Layin ka k'ira,

Kallonta yayi "Naji kin k'irani any problem? "Nothing kawai inason inkoma can gidanne yasa Nak'iraka ka maidani, sannan Gaskiya nayi missing naka sosai jinayi kaman na shekara bangankaba.

Ya sauk'e ajiyan zuciya cikin yarda da Magananta, "Oh nazaci wani abunne,

"Ba komi barin fito Mu tafi, kar inb'ata maka lokaci my luv, ta mik'e tayi ciki shima mik'ewan yayi
"Kisameni a Mota, ya fad'a atak'aice,

Suna tafiya sai kallonsa takeyi ta gefen ldo aranta tanaga tagama yin sa'a ace ta mallaki Kb ita kad'ai a Duniya.

D'an gyaran Murya tayi tana kallonshi, "Kb Maganan Kud'in pertyn nan,

"Oh bance kiyi list ki fad'amin nawa bane,

"Eh nayi naga zai ci kaman Dubu d'ari 4

D'an jim yayi yana Tunani, sai kuma yace
"Ok Gobe zan turomiki,

"Gud My Husband i luv u Murmushi yayi sam Hakanan kawai yaji bata Burgeshi, Magananma basonyinta yakeba,

suna tafiya tana jansa da Hira, jifa2 yake amsawa, har suka isa,

A bakin gate ya Hango Dijah Ta rako K'awanta Jamila suna Gaisawa da Saurayinta daya kawota,

Dukansu sai Murmushi sukeyi Musammanma Dijah, wani lrin takaicine ya ziyarceshi, aranshi yana tunanin tsawon zamanta dashi bazai iya tuna Rana d'aya da ta masa Murmushiba, sai dai yaga tanayi ma wani, shidai tsakaninta dashi tsiwa da Rashin Kunya,


Wani lrin Horn ya dinga dannawa ba k'ak'kautawa, har sai da Mai Gadin ya razana aguje ya fito ya Bud'e gate d'in,

Nan ya bad'esu da k'ura ya shige, ranshi kaman Wuta yanasane Wannan Jamilance ta kawo mata wani yaro da ta k'irashi Da surayinta yauma gashi ta kawo wani, "I hate this Girl ya fad'a afili, yana Huci,
Wayyo Nafisa ji tayi kaman tayi Hauka tsaban Murna, a tunaninta Dijah ya tsana, har yakasa B'oyewa,

Lallai Bokannan ya iya aiki ta fad'a tana Bud'e Motan, kusan tare suka fito a lokacin Idon Dijah yana cikin Gidan, nan idonta ya sauk'a akansu, tsananin B'acin Rai taji, dan haka tayi saurin janye ldonta, tanayi ma Jamila sai anjima ta shiga cikin Gida, ji tayi kaman kar ta shiga ciki ganin nan sukayi, sai dai tunawa da tayi yanzu zaya fito taje Gidan Sauda yasa da sauri ta shiga,


Ko Kallon inda suke a falon batayiba ta shige d'akinta ta d'auko mayafi da jakanta, taje tayi wa Mami sallama,

"Khadijah karfa kidad'e kigayawa driver ana la'asar yaje yad'auko ki, ki gaisheta, ta amsa da to tafito,

Wannan Karon Nafisa kad'ai ta tarar a falon ta fita.

A k'ofan falo sukayi karo da Kabir da sauri tarab'a ta wuce ganin alaman fita zatayi yasa yabi bayanta, yana Magana "ke ina zakije?" cigaba da tafiyanta takeyi bata ko nuna alamun tajishiba,

Mayafinta ya jawo yana kallonta hawaye taf idonta, "Ba magana nake mikiba, k'wace mayafinta tayi dai2 lokacin hawaye yafara zirya a fuskanta, ta juya binta yayi niyanyi, wani sashi na zuciyansa kuma yana mamaki Hawayen da yagani afuskanta, Wayarsa ce ta hau Ruri.

Yakoma gefe yana Amsawa yana gani driver yafita da ita,

Har bakin gate ya isa ya lek'a da niyan yadakatar darivern har sai ya san inda zata,


Sai dai ko alamansu bai ganiba,haka ya dawo ya shiga pert d'insa,


Yau Juma'a yakasance Gobe ne Ranan Engagment d'insu,

Yana Zaune a k'ofan pert d'insa yana tunani Rabonda yaga Dijah a idonsa tun Ranan da tafita tana Hawayennan, "ko ina taje?

Yafad'a a fili, yana zaune awajen Motan wasu daga cikin freinds d'insa guda 2 suka shigo da 'yan Matansu, kai tsaye gunsa suka nufa,

Cikin Murna ya taresu gami da ba wa Mazan wajen zama, Wayansa ya d'auko da sauri yana fad'in barin k'ira Nafisan ta shiga daku ciki ya fad'a yana kallon 'yan Matan dasuke tsaye,

Tana d'auka yasanar da ita tazo tashiga da Bak'i,

Cikin tsantsararren kwalliya ta fito tana taku d'ad'd'ai cikin farin ciki yayi dai2 da shigowan Dijah, kanta ak'asa take tafiya, Dai2 zata shiga cikin falon Nafisa da 'yan Matan suka iso suma zasu shiga,

Nafisa ta ciza Baki aranta tace "b'uyanki agidannan nabanzane yarinya nasan bakin cikin bikinmu yasa kike k'in fitowa yanzu zan k'aramiki bak'incikin inyaso kiyi Bindiga,

"Ke Dije Maza ki had'a min abun Motsa baki kikawo ma bak'ina in akasamu matsala ina mai tabbatar miki yau tsohon k'auyennan zaiyi Mummunan Gani.

Har Ranta taji Maganan anma ta d'auke kanta kaman batajiba zata shiga, jawota Nafisa tayi tayo baya da ita "Bakiji.... Aibata fad'i abinda zata fad'anba taji sauk'an Magigitan Mari har biyu a fuskanta, "Kafin tsohon k'auye yaji Mummunan labari na Birni sai yafara ji, daga haka ta wuce cikin matsanancin Borin Kunya tayunk'ura tayi bayanta "wlh yau sai na halakaki, d'aya daga cikin 'yan Matan ta rik'o Hanunta "No Nafisa ba girmanki bane pls stop it, ince k'anwar wanda zaki aurane?

"yar aiki ce daga k'auye aka kawota, sam ba a dangin mu take ba,

'yar aiki? Suka fad'a dukansu suna kallon juna, d'ayan tace "tokoma yane kiyi Hak'uri Mukanma daganan zamu koma dama bazamu samu attending Hidiman bikinku bane, zamu koma school abroad shine suka matsa akan muxo mu gaisa, Muna muku fatan Alkhairi ga wannan ba yawa, suka mik'a mata k'atuwar Ledan da sukazo da ita, cikin Matsanancin Kunya ta karb'a tana fad'in "Dan Allah kuyi hak'uri mushiga pls

"No karki damu dama ko munshiga ba dad'ewa za muyiba, akwai inda zamuje, tsaban Kunya kasa Rakasu tayi, ta tsaya awajen,
A haka suka k'arasa wajensu Kb da shima gaba d'aya kunya tagam lullub'eshi, dan tun shigowan Dijah yabita da kallo, yana son yace mata takawo masu abun tab'awa dan Ruwa kawai ya d'auko musu, saidai yanayin da yake ganin fuskanta ya dakatar dashi, kallonta kawai yakeyi, kaman yau ya fara ganinta, akan idonsa Nafisa ta tareta, baiyi auneba sai sauk'an Maruka ya gani kan fuskan Nafisa, nan Hankalin abokansan da suke shan Ruwa yayo wajen, ji yayi kaman k'asa ta tsage ya shiga, tsananin kunya,


Kanshi na sunkuye yaji suna masa sallama, asanyaye ya tashi, yana jan dariya,

"Haba har zaku tafi? Baku ko shiga bafa, yafad'a yana kallon Matan,

"Wlh sauri mukeyi suka bashi amsa,
Ya mik'a wa Mazan Hanu, "ok guys thanks so much, sai when?,

"Mukan ai damu gobe za'ayi komi, har jikin mota ya rakasu, yana d'aga musu hanu har suka fita,


Tun ahanya yake k'iran watan Nafisa tana d'agawa cikin kakkausan Murya yace "maza ki fito ina jiranki,

Sai kaiwa da kawowa yake agun tafito aranta tana fad'in yau zaman Dijah agidan ya k'are,

Yana jin motsinta abayansa ya juyo, yanayinsa ba k'aramin tsoratata yayiba,

"Ke Nafisa ashe baki da Hankali bansaniba? Ashe ke mahaukaciyace nake miki kallon mai hankali, Meye Had'inki da Khadijah? Ina Ruwanki da ita?

Cikin jin zafin Maganansa tace "Kai Kabir ya haka kake niman kazageni akan wancan banzar 'yarqauyen? Kasan me tamine? Daga ce ta had'a ma Bak'in mu Abinci sai tanimin min Rashin kunya? Meye amfaninta agidan? Wlh bazan bartaba ta rainaniba nida gidanmu sai naci Ubanta, nibana tsoronta dan naga ka maidata kaman wata ita tahaifeka, sai na halakata shegiya 'yar matsiyata tasss taji sauk'an Mari afuskanta,

yanuna ta da yatsa "yaushe kika fara rainani irin haka? Wace ce ke dahar zaki furtamin magana haka? Nidake waya riga wani sanin Khadijah? Ni nafiki sanin wace ce ita, duk da nasan akwai bashin Mari atsakaninku inda baki shiga sabgartaba bazata kulakiba, zakice ta had'o miki Abinci ma Bak'i ancemik 'yar aikice ita? Ko dakike cemata 'yar qauye yanzu keda ita wace ce tanuna qauyanci da dabbanci ma? Kin kunyatani kin kunyata kanki, Khadijah yarinyace k'arama agabanki ko a'ina kukayi haka ansan kece bako da hankali, sannan da kike wani fiffik'an sai kin mata kaza2 ke kin isa da Khadijah? In abaku guri da ita sai kin raina kanki ke kanki kinsan wannan, shine dan tsaban rashin kunya zakicr min nad'auketa kamar uwata, to ba Uwata bace ita, Mata tace ta aure ko dakike yawan cewa sai tabar gidan saidai ke ki bari dan kinsan ayanzu nine mai gidan kuma zaman aure takeyi, ko kina tsammanin matsayinki na k'anwata yazarta na mata tace, ko kina tunanin dan ansa ranan aurena dake shikenan har kinfara bearing matata ce? Nonses kawai, yafad'a tana jifanta da wulak'ancaccen Kallo, yajuya kaman kumurcin Maciji yayi nufi pert d'insa zuciyansa sai suya yake masa,


Nafisa da ta daskare awajan dafe da k'uncinta da tunda taji sauk'an mari idonta gaba d'aya sukayo waje tana kallon Kabir da take kokonton anyah kuuwa shine? Tasan Kabir tuntuni in Ransa ya b'aci yakan zama abun tsoro amma bata tsammaci hakanba,

Musamman ita da tasan aikin Boka na jikinsa,


Tana jin ya rufo k'ofa ta juya aguje tayi bayan d'akin Mami ta dirk'usa kaman mai niman gafara tana kuka kaman ranta zai fita tana fad'in "Wayyo Na shiga Uku aikin ya karye Boka aiki ya karye ya karye kalman da take ta maitawa kenan kaman sabuwar mahaukaciya.



🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣
*Tofa Mari Uku ana Gobe Engagement* wai yazata kasance ne?


*shin Kabir ya manta ne yayi irin wannan hukuncin wa matan da yake ta lissafa ranan aurensu?*

πŸ€”πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…



Yaukam sai kungaji da karatuπŸ˜‰


*Ummu fatima ce* 😘
[7/22, 7:21 AM] β€ͺ+234 816 155 6998‬: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


4⃣5⃣


*Dijah* da tun fara maganan *Dr Kb* ta ke kallonsu ta Window ne ta sake labulen tana tab'e Baki taja tsaki ta koma ta kwanta tana jiyo kukan Nafisa,


"Ke Nafisa" Mami da tun tana toilet take jiyo tane ta lek'a Window ta k'irata, da dauri tasa Hanu ta toshe bakinta tana mayar da kuka da maganganun da yakeyin tana Mai Addu'an Allah yasa Mamin batajiba,

"bada ke nakeba ne Nafisa tashi kishigo yanzu2 inajiranki,

Asanyaye ta tashi tana had'a hanya ta shiga, a fallo tasami Mami ta zube a jikinta tana sake sabon Kuka ita sam ba Marin da aka matane ke damuntaba, illah aikin bokan da baiyi tasiri ba tanaganin samu sai gashi taga rashi, yanzu haka ita sam basan makoman aurenta da Masoyin nataba, tabbas da tasan cewa Asirin bai yiba ko da gigin wasa bazata tab'a gigin d'aga harshenta ma Kabir ba mutumin da ta d'auki lokaci tana dakon soyayyansa bata da buri da yawuce taganta matsayin Matansa, kuka take kaman Ranta zai fashe, tun Mami tana k'o'arin binta da lallami har ta fusata tafara fad'a,

'inbazaki sanar daniba shikenan tashi kije ki cigaba da kukanki inkina ga zai miki Magani, Mami ta fad'a tana k'ok'arin tashi, ta rik'o Hanunta tana fad'in "Kabir ne Mami Kabir ne baya sona ya tsaneni bansan me na masaba, Nan ta kwashe duk yanda sukayi ta fad'a mata sai dai bata sanar da ita cewa ita tafara tsokano Khadijah ba,

Hab'a Mami ta rik'e tana kallonta tace "Mari? Khadijah ta mareki shi ya Mareki sunyi Haukane? Ko ke 'yarsuce?

Ta jawo Wayanta ta k'ira Kabir alokacin har yayi Wanka ya shiryo zai fita, yana d'agawa tace "Maza ina nimanka yanzu2

Nafisa tana sheshek'a ta kalli Mami "wlh Mami na lura yarinyannan bata bar Kabir hakaba, wlh Asiri suka masa mai k'arfi,

Cike da Mamaki Mami ta kalleta, tad'anyi Murmushi ta gyara zama,

"Nafisa Rayuwa da kika ganta wanda ya d'auketa da zafi da zafin take zuwa masa, Babu wani Riba cikin sab'on Allah sai tab'ewa da wahala, aduk cikin sab'a ma Allah kuma ba kaman had'a Allah da wani, danshi laifine da matik'ar ka mutu kanayinsa Allah bazai tab'a yafe makaba, sai ya hukuntaka akai,

Kuma bakisan wani abuba inma niman wani abun kikayi awajen wani yamikishi ta hanyan sihiri In Allah yaga dama sai ya miki talala, sihirinki yaci anma kisani akwai ranan k'arshen abun watak'ila kuma k'arshensa yazo miki da matsaloli fiye da wanda kika guda kiyi danasani mara amfani, inkuma yaga dama sai kiyi tayi amma bazaki tab'a ganin biyan buk'ataba, sai akasin hakan,

Ta d'an k'ara muskutawa tana kallon Nafisa da gaba d'aya jikinta yayi sanyi, danji takeyi kawai da ita Mami takeyi,

"ldanma Su Khadijah asiri sukeyi ma Kabir to da da Hali ki dakatar da ita ta hanyan bata shawara dani da Kabir sam bama wasa da Addu'o'i da yardan Allah bawani sihiri da zai kama waninmu ta hutar da kud'inta, ta fad'a tana nazartan yanda sak'on nata ke shigan Nafisan, dai2 lokacin Kabir ya shigo da sallama, fuska a murtuk'e yazauna a kujeran dake fuskantan Mami, "Tashi ka shiga d'akin Khadijah ka k'irata Mami ta bashi Umurni, tura k'ofan yayi ya shiga da mak'alalliyan sallama yatsaya yana kalle2 can ya hangota a kan Gado ta takure waje d'aya acikin Bargo, ahankali yak'arasa jikin Gadon yana kallon Fuskanta da hawaye ke ta sintiri,

Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauk'e aransa yana Mamaki duk da tayi marin bata Huceba kenan ko me? Kodayake kwanan nan duk haka yake ganinta kaman tana cikin damuwa, "To meke damunta? To ina Ruwanka da abunda ke damunta Wani sahin na zuciyansa ya kwab'eshi,

"Khadijah tashi ki zauna, batayi Musuba ta tashi ta zauna tana kallonsa da jajayen idonta, ahankali yasauk'e idonsa k'asa kaman zai tambayeta abunda ke damunta sai kuma ya fasa ya juya yana tafiya yace "Mami ce take k'iranki daga haka ya fita,

Saida ta wanke Fuskanta, ta fito a k'asa ta zauna kusa da Mami,

Ita Mami ta fara tambaya, dalilin da yasa ta mari Nafisa,

Kanta Na k'asa tace "Babu,
"Haka kawai kika mareta Khadijah? Shiru Dijah tayi

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment