Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan magana dakukayi dan nima abun ya d'aure min kai, mutum da matarsa anma anmaidashi gouro da k'arfin tsiya ina natab'a jin wannan abun innayi Magana tacemin wai ai karatu takeyi, naga ince auren yazu kam baya hanaku yin kartunku, cewan lya,



Mami ta d'ago ta kalli Kabir da yake ta danne2 waya kai kace baima san wainar da ake toyawaba, alhali kuwa hankalinsa kacokam na wurinsu kunya ne sosai Maganan nasu yabashi,




"Mami tace shikenan Yaya tunda kunce haka zan turota anma akwai Maganan dazamuyi daku gobe in Allah yakaimu zan gayamuku abundake tafiya,




Sai lokacin yad'ago suka had'a ldo da Mamin, a hankali kuma ya yunk'ura zai tashi da sauri Sani ya zo ya taimaka masa nan ya musu sallama Sani ya rakshi Bed room, abakin gado ya zaunar dashi, nan ya masa Sallama wata k'atuwar Leda yad'auko wanda da dasunan Nafisa yasayi abun ciki, ya mik'a ma Sani ga wannan ka kaima Mamata, Sani ya karb'a yana godiya gami da Mishi sai da safe ya tafi,



Saida yagama Shafa Addu'o'insa sannan ya kwanta gami da jawo blancket ya shiga ciki, idonsa a lumshe yake ya fad'a Duniyan tunaani, nan ya jiyo su Uncle Musa suna sallama ya kalli agogo 11:00, ya sake rufe idonsa, gamida d'anyin juyi,




Atare Mami da iya suka fito Mami tadage sosai wajen son fahimtar da lya dalilin rik'e Khadijahn agurinta, lya tace "anma ke har yanzu baki gane cewa yana son matarsaba? sarai haline kawai irin na kabiru yasa yake hakan, kacokam Hankalinsa na gareta,



"mhmm lya ai tun farko tunbansama Khadijah ba, Kabir yana sonta taurin kaine da Rashin kunya, kuma wlh lya in nabarta atsakaninsu shida Nafisa zata sha wahala, shiyasa nakeson sai nayi training d'inta tukunna sannan inason sai ya d'an kod'u yazo gareni da kansa ya furtan cewa yana buk'atar ta kafin ya mallaketa,

"haka ne lya ta fad'a suna shiga pert d'in,


D'akin Khadijah Mami ta shiga kai tsaye, kudundune tasameta cikin blancket, tana Bacci, Yaye Bargon tayi kad'an ta d'an bubbuga k'afanta Tana k'iran sunanta, da k'yar ta bud'e ido cike da Bacci a idonta ta kalli Mami,



"Tashi kizauna Khadijah a hankali ta tashi tana Hamma,



"Shiga bayan gida kiyi brush yanzu ki fito ina jiranki, ince kinyi wanka? Kai ta gyad'a tana wani Hamman dan baccine sosai a idonta,

"Tashi mana,

Ta tashi tashiga bayan gida tayi brush din duk agigin Bacci, ta fito tatsaya tana fad'in nayi Mami inkwanta?


Mami ta mik'a mata Buter Mint "sa abakinki inaga idon naki zaifi warewa, ba musu tasa abakin dan batasan ainihin zancenba,



Mami tacigaba da zab'o kayanta da takeyi tana zubawa a kwati, sannan ta kwashi wasu kayan Cosmetic daga kan Mirrow ta zuba mata aciki, ta kalleta sai d'an tangad'i takeyi na bacci,


tace "Khadijah bud'e idonki kiji, bud'e idon tayi tana cigaba da tsotsan Mintinta,




"Zaki koma pert d'in Mijinki tunda kinga bayi da lfy, kid'an dinga taimaka masa inyaso inya warke sai kidawo abunki,



Firgit Khadijah ta ware idonta gami da furzar da Mintin Bakinta ta kalli Mami,



Atsorace tace "Mami waye kuma Mesuna Mijinki? Harara Mami tazabgamata, sannan tace "to ina nufin zaki koma sashin Kabir da zama dai2 yaji sauk'i ince yanzu kin fahimta?







Wani k'ugi taji cikinta yayi gami da wani jiri da ya d'ibeta saida tadafe jikin bango dan kar takai k'asa, Da Mamaki Mami take kallonta,





Gaba d'aya baccin dake idonta ya washe sai wani tsoro da yakamata, cikinta sai k'ululu yakeyi,


Araunane tace "Mami dan Allah kiyi Hak'uri kibarni anan dasafe zanke kaima sa Abinci ina gyaramasa pert d'insa, kinji? Tafad'a kaman zatayi kuka,



Mami tace "Khadijah wlh ba tsarinabane kinga Uncle d'inku ne suka tsara hakan inkuma kince bazakiba, sai ink'irashi yanzu ingayamasa, yanimo mai tayashi kwana, da saurinta tace "a'a karkifad'a masa Mami Uncle yana duka ya tab'a dukanmu nida Sauda, tafad'a tana faman share Hawayen dake mata zarya,



"Ato inbakison duka zo muje inrakaki dan nibacci nakeji nidai abunda zance miki shine kirik'e mutuncinki sosai danshi Namiji dakiga ganshi wasu lokuta da dama sai kaja ajinka kake samun daraja da k'ima agurinsa,


Sannan kinsani sarai basai nagaya mikiba Aljannanhnki tana k'asansa inkinbishi kinmasa biyayya kishiga dukda yanzu jinya zakije bazaman aureba amma dai ki kiyaye, kiyi gaba barin d'auko miki wani Humra naga nakin ya k'are,


Ta fita tashiga d'akinta, tafito da Humran a falo tasami Dijah tayi tirus sai Kuka takeyi, mik'amata Humran tayi tana k'ok'arin b'oyemta damuwanta tace jeki shafa ki biyoni barin kaimiki akwatin, ta sunguma tayi gaba tabar Khadijahn anan,




Lokacin da tashiga Bacci har yafara d'aukan Kabir Mami ta ajiye akwatin tana fad'in har kayi baccine? Bud'e ido yayi yana kallonta



Murya asanyaye yace "Wlh Bacci ya fara d'aukana,


Tace "to kaga dai yanda abun yakasance Dan haka Kahdijah zatazo gareka amma kasani zata zone amatsayin mai jinyarka ba matsayin mataba, kar kayarda katakuramata dan itama bason zuwan takeba gatacan ta tubure sai kuka takeyi wai bazata zoba, daba katakurata da bazatayi hakanba,

Nasanka da lzza dajin kai wannan shine abunda yake had'aka da Masoyanka ma bare wa inda bakaso,


D'an tab'e Baki yayi yace "Mami dama kin barta kawai dan nasan Halin Khadijah tunda aka tirsasata zata dinga samin ciwon kaine, Harara Mami tazabga masa "to ai agabanka akayi Maganan da tun lokacin kace musu subarta, banice zakamin Rashin kunya yanzuba,



Yad'anyi Murmushi kiyi hak'uri Mami wlh ji ba abunda nakemata Halintane kawai Hakan yanzufa kiduba na kwanta asibiti kwana Uku ko lek'ani batayiba, nadawo tun safe agidannan Masu aikima Maza da mata ba wanda baizo yamin yajikiba, anma kullum laifina kk gani,



Murmushi Mami tayi tace "ai ltama bata da lfy meyasa kai bakabaro Asibitin kazo gaishetaba? Koda kadawo kanimi inda take ka gaisheta?


Murmushi kawai yayi dan yasan Bazata tab'a yarda da Gaskiyaba,

Fita tayi takoma pert d'inta a Falo tasami Khadijah kwance kan kujera sai sharan Hawaye takeyi, da ido tamata Alaman ta taso,


Haka ta tiso k'eyanta har Bed room d'in wannan karon fuskansa rufe yake da Bargon, Mami tace "kifito da kayan Akwatin kisa a sif ta inda ba kaya, kizuba kayan kwalliyanki akan Mirrow, Randa yafara fita aiki Ranan zaki dawo gun Maminki, daga Haka tafice tare da Rufe k'ofan,


Tanajin ta rufe k'ofan falo tasaki Kuka mai d'an sauti,


Tun yana sharewa Har ya yaye Bargon da yarufa fuskansa dashi ya sauk'e idonsa akanta.


πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…

Tofah yau dai ga Dijah ga Kabir wai ya Wannan jinya zata kasancene?


Hahhh Mami kenan tayi tufka tayi warwara duk ita kad'ai,


Ku biyoni inna gamasu da coments dinku in muku typing.. GobeπŸ‘Œ 😜





*Ummu Fatima ce* 😘
[8/3, 5:14 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*Safiyya Abdullahi Huguma Allah yabaki lfy, Yasa babyn da kika haifa ta koma taceceku*

*Allah ya mayarmiki da mai Albarka* πŸ™πŸΌ


*Guys da fatan zakuyi hak'uri da duk yanda wannan page yazo muku*

Mmn Aysha ana tare🀝🏻😍

4⃣8⃣



Kallonta yake bako k'ifta ldo, da Fad'a yaso yamata dan yanuna mata shima bada yawunshi aka kawo masa itaba,


Saidai tunawa da yayi da Halin Mutuniyar tashi yasa ya cigaba da kallonta, dan yasan kad'an da aikinta tasa suyi kwana zaune ita batayi baccinba bata barshi yayiba, Ahankali take k'ara sautin kukanta,


D'an juyawa yayi kad'an ya gyara kwanciyansa, Murya asanyaye, yace "pls Khadijah darenefa, Dan Allah kizo ki kwanta kiyi Bacci,

Zamewa tayi ta zauna ajikin sif tana sharan hawaye, ta kalleshi ni bazan kwana ananba, cikin gida zankoma,

Yatsina Fuska yayi ya kalleta, "No ni bani nace ta kawokiba, so kibari da safe zan mata Magana sai kikoma abinki, anma inkin kwanta baki d'agamin Hankaliba, inkuma kincigaba da kuka to kinyi wa kanki.

Jin haka yasa tayi shiru ta goge Hawayenta tana ajiyan zuciya, gyara kwanciyansa yayi ya lumshe ido kaman mai Bacci,

Kalle2 d'akin tashigayi aranta tana tunani d'aki saikace na Mace? Har yafi na Mami tsaruwa, ahaka har Bacci yafara fisganta, ta jingina kanta da jikin sif, tana gyangyad'i inkanta ya zame ta d'an zabura ta gyarashi,



Shikuwa Kabir ldo ya zuba mata yana Mamakin ba hagon Hali irin nata,


Can da tagaji tazame awajen takwanta, "Ke Khadijah kb yak'irata ad'an zafafe, firgit ta tashi tazauna, ya had'a fuska "Kar kiyarda ki kwanta awajen kitashi ki hau gado ki kwanta,

Ta turo baki tace "ni anan zan kwanta, dogon tsaki yaja gami da d'an yaye bargon da yake jikinsa, Ya zaro ldo cike da fad'a "Karkiyi tunanin wani Dalili ne yasa nace ki haumin gado, nima bada son raina zaki haumin Gadoba,

Ko so kike ki sanyin talis ya kamaki ak'asa wa inda suka turoki su zargeni?

Oya tashi ki hau ki kwanta, ko yanzu Ranki yab'aci banacin mutane, koda ina cima, ke kin kasamin, yafad'a yana jawo Belt d'insa akan bed side drower,


Tashi tayi tana share Hawaye taje can k'arshen Gadon ta zauna, komawa yayi ya kwanta, yaja bargonsa, nanma saida tagama gyangyad'inta, ta dunk'ule agun ta kwanta, acikin hijabinta k'afafunta anad'e gwiwowin k'afanta takure ak'irjinta, tayi pillow da hanunta d'aya d'ayankuma ta damk'e hijabinta dashi ta k'asa,


Kallo Kb yabita dashi, yad'anyi Murmushi mara sauti, ya mik'a Hanunsa ya matsa makunin wutan d'akin ya kashe,


Ai arazane ta ta tashi tazauna, tana k'ok'arin Kuka tace "Likita dan Allah ka kunna Wutan wlh tsoron duhu nakeji, jin tana shirin taramasa mutane, ya mik'a Hanu ya kunna yana kallonta duk tayi wuki2 da ido, yace "Anma yaud'innane kika fara tsoron Duhun ko? Daganan ina hango Windown d'akinki bantab'a ganin wuta akunneba, Dan Allah Khadijah kibarni inyi Bacci nifa mara lfyne, pls kar kik'armin wani jinya, ya mik'a Hanunsa yana k'ok'arin sake kashewa.



Kuka tasake tanace "Nidai wlh kar kakashe banason duhu, dafe goshinsa yayi yace " *Yasalaam!* Why Mami kika had'ani da irin wannan Matsala, khadijah ban iya kwana da Haske, zaki hanani yin Bacci, Why?


Gyara kwanciyansa yayi ya rufe idonsa da Blancket yana mita "haka kawai nida d'akina ahani bacci? Yajima kanshi acikin Bargo har Bacci yad'an fara d'aukansa, ya bud'e ya kalleta, irin kwanciayan d'azu tayi, da Alama Bacci yafara d'aukanta, juyowa yayi sosai yana fuskantanta, jin motsinsa yasa ta zabura ta kalleshi,



πŸ˜† Ahaka dai kwanan nasu yakasance dukansu basuyi Baccin kirkiba, afannin Khadijah atsorace take dashi da yad'anyi Motsi xata zabura ta d'ago kai ta kalleshi, dan wani irin nauyi da takeji kasancewan yaune rana ta farko da ta kwanta d'aki d'aya da Namiji, shima gogan hakan take awajensa, jinsa yake wani iri gashi da Mace kwance agado d'aya sannan ga Hasken wutan da bai saba kwana dashiba, duk ya takurashi,


Ana k'iran Sallah ya tashi ya zauna, yana kallon agogo, jin Kansa yake ya masa nauyi sabo da Rashin samun Bacci da baiyiba,



D'an juyawa yayi ya kalli inda Dijah take a zaune yaganta tana matsa k'afafunta da suka mata tsami dan takuresu da tayi,


Ahankali ta mik'e tana yarfe Hanu ta shiga toilet, Alola tayi sannan ta fito, ta nufi wajen akwatin kayanta zata saka tayi Sallah,


Kallo Kabir yabita dashi yace "Kinsamin Ruwan Alola? Girgiza kai tayi tana kallonsa,


"Ok jeki had'amin Ruwan zafi zakisa,


Ta mik'e tana gyara hijabinta, taje ta had'a ta fito tace "Na had'a
"Ok taimakamin intashi, d'an jim tayi Sannan ta matsoshi, ya mik'o Hanunsa,


,,,, Da iya k'arfinta takama Hanunsa tana k'ok'arin wai zata d'agashi, d'an yunk'uri yayi kaman zai tashi, Nan ta afko jikinsa, yafad'a da baya akan gadon yana fad'in "Wayyo cikina! Wayyo Mamina!, yunk'urin ta tashi akansa takeyi amma yarik'eta Gam ak'irjinsa, Fusakansa nakan k'irjinta yana d'an goga Bakinsa kan niple d'inta yana "wayyo Mamina! zan mutu cikina?, wayyo Marana, gaba d'aya Dijah ta tsorata jikinta har b'ari yakeyi tana masa Sannu, atunaninta da gaske zafin ciwone yasa yake hakan, Ganin dabaran nashi yana kaimasane yasa yak'ara k'aimi har yayi nasaran zira harshensa cikin Breast d'inta, wai duk azafin ciwo, mutuniyar kam duk da irin wannan ciwo yad'an bata mamaki tana ta jera masa sannu gami da shafan kansa, ta Rud'e sosai har tafara tunanin k'iran Mami,

saida yayi mai isansa sannan yad'an nitsu, jin yadaina juya kansa kan k'irjintane yasa ta tazame daga rik'on da yamata ta tashi ta zauna sai alokacin ta lura ya cire mata hijabi ya mirgina akai,


Kallonsa tayi tana kare k'irjinta da Hannayenta, idonsa a lumshe kaman ba ita yake kalloba, tad'an tab'ashi "Likita! Ware idonsa yayi duka ya kalleta akasale, yace "Na'am kin had'amin Ruwan? Tad'an cuno baki "Gaskiya inaga ciwonkannan Aljanune nidai katashi kabani hijabina zanyi sallah,


Yad'an Marairaice Fuska, "pls inkin had'amin Ruwan taimakamin lntashi kikaini inyi Alola, kinsan jikina ba k'arfi, yafad'a yana mik'a mata hanu, tana rik'eshi ya tashi, ahaka suka shiga tazaunar dashi akan kujera zata fita yace baki ban brush ba, tasa Maclean ta bashi, ya rik'o Hanunta yana d'aga mata gira "tsaya mana kiyi Alola.
.
"ni nayi Alola yad'anyi Murmushi "ai wannan Alolankin yatashi a tutan babu, kodai Mami tasa ina biyan kud'in Malaman lslamiyannan a banzane? Baki fahimtan komi,


Harara tabishi dashi aranta tana tunanin wato abunda yamata d'azu da ganganne yana sanekenan?



Alola takuma yi tafita tabarshi anan, sauri2 ta canja kaya, tazo ta haye sallahya, shima yana fitowa yasa jallabiya ya yatada iqama,


Bayan yagama Azakar d'insa kaman yanda yasaba aduk lokacin daya idar da salatussubhi, ya juyo ya kalleta sai gyangyad'i takeyi,


K'afanta yad'an tab'a ta bud'e ido ta tashi yace "zo ki kwanta ki rama baccin dakika hana kankiyi kika hanani,

Ta girgiza kanta tana fad'in aiki zanyi, tashi yayi yacire jallabiyansa, ya kamo Hanunta, "zoki kwanta ki rama baccinki, Dodon naki yana zaune anan zaiyi gadinki, ki kwantar da Hankalinki,


"Ni kabarni infita Likita ban iya Baccin safeba,


"Karkidamu indai iyawane bakiyiba barin koyamiki yanzu, zama yayi abakin gadon yajawota ya cire mata hijabi yayi wurgidashi, yafara kiciniyar rabata da kayanta, da k'arfi ya ciremata kayan yasamata Rigan baccinta, ya kwanta yajawota ya kwantar da ita kanta yana kan k'irjinsa yadinga mata susa tundaga Kanta har gadon bayanta, tuntana mutsu2 har bacci yayi gaba da ita,


Basu suka farkaba har wajen 12:00 na Rana, wayan Mami ya farkar dashi, ahankali ya mik'a hanunsa ya d'aga yakara akunnensa, "Hello Mami,
Mami tace "Haba Kabir wannan wani irin Baccine? Kusan sau uku ana kawo muku abun break, anyi knocking anyi knokcing shiru? Ina Khadijah? Ahankali ya zare jikinsa acikin nata yatashi yazauna yana fad'in Wlh Mami jiya bansmu nayi bacci isasshe bane, nace "ina Khadijah? Yad'an kalli inda take tana motsi alaman zata tashi, yasa Hanu yana wasa da gashin kanta, yace "inaga tana falo Mami, batanan, Jinjijina kai tayi ta kashe wayan,

Ya gangara da Hanunsa ya shafo k'irjinta, dai2 lokacin ta farka, ta tashi ta zauna,

"Mn jeki ''had'a mana Ruwan wanka, hijabinta ta zira sannan ta shiga toilet, ta had'a tafito, narkewa yayi dole saida ta rik'eshi ya tashi, suka shiga bayan gidan tana k'ok'arin fita ya rik'ota "aike zakimin Wankan ni bazan iyayiba, zaro ldo tayi waje

"Ni kuma? Wlh bazan iyaba,
"To inbakiyiminba wa zaimin? Tunda kikazo jinya aikomi ya hau kanki,

"mnnn to barin cire hijabina, kar yajik'e
"to yace gami da saketa, tafara kiciniyar cire hijabin tana matsawa da baya tana zuwa jikin k'ofa tayi saurin bud'ewa ta fice da gudu ta rufo k'ofan,


kai tsaye bayan gidan falo tashiga tasa key sannan tahad'a Ruwan wanka tashiga tajima aciki kafin tayi wankan tafito, afalon tasameshi rik'e da remote yana kamo tasha, yasha kwalliya cikin jeans da Ash d'in shirt, sai baza k'amshi yakeyi, ta wuce, kwalliya tayi sosai tasa Riga da sket na jan Material, mai bak'in flawers, fashion din jajayen sark'a da abun hanu tasaka, bak'aramin kyau tayiba, tana zaune akan stool tana fesa turare kb yashigo, kallonta yakeyi har ya iso gabanta ya tsaya rai ab'ace yace "kar ki kuskura kisake shiga toilet d'in falo, kinajina? Yanzu inda kin fito kinsamu wani afalonfa? Ko bakijinane bazaki amsaba?

Ta dago Ido araunane ta kalleshi, tace "Naji bazan sakeba,

"Gud yafad'a ya juya har yakai bakin falo, yajuyo yace ana nocking, kizo kije ki bud'e, daga haka yafice,

Saida tasa Hijab taje ta bud'e mai aikin Mami ce ta gaida tare da tambayanta mai jiki, ta mik'o mata abun kari,


Tana ajiyewa tashiga kitchen ta d'auko cups,spoons da plates, ta dawo, ta zuba ta tura masa gabansa, ya kalleta "what do you mean? Aike zaki bani baby yafad'a yana d'agamata Gira, zatayi magana ya jawota jikinsa, ya mik'amata spoon ba yanda ta iya haka tayi tabashi kaman k'aramin yaro, sannan ya karb'a ya mannata a k'irjinsa yayi tabata,


Bayan sungama ta gyare pert d'in gaba d'aya, tasa turaren Wuta sai k'amshi ke tashi,


Ta dawo kusa dashi ta zauna kallonta yayi da Alaman magana abakinta ya jawota ya d'orata akan cinyanshi, yasa hancinsa wajajen wuyanta yana shak'an k'amshin dake tashi ajikinta, idonsa alumshe, yace "What is ur wrong baby?


D'an zamewa tayi daga cinyansa tayi k'asa tana kallonsa, shima kallonta yake yana lumshe ldo kaman wanda bacci mai tsanani ya kamashi,


Cikin marairaicewa kaman zatayi kuka tace "kace da safe zakasamu Mami kamata magana inkoma, shiru yayi na lokaci suna kallon juna, can ya nisa yana d'an yatsina fuska ya lalumo wayansa, yace "ba Mami bace ta creating Maganan, su Uncle ne barin k'irashi, yana danna waya, asanyaye, ta dafe Hanunsa idonta taf da hawaye, tace "Dan Allah kar kakira Uncle,

"To yaya kkson anyi? Dole shine zai san abunyi,

Ta girgixa kai hawaye nabin kuncinta, nasan Halin Uncle bazai barniba,

Hanunta yakama yana murzawa, "to meye na Kukan Khadijah? Indai bakison ak'irashi to kik'ara hak'uri mana, nan da 'yankwanki za'a d'aura Aurena, ana auren nasan zai sallameki tunda inada Mata, da sauri ta k'wace Hanunta acikin nasa, tasaki kuka mai sauti, k'irjinta sai bugawa yakeyi,

Jawota jikinsa yayi yana kissing d'inta tana zillewa, yasa bakinsa a kunnenta, "Tsaban kin tsaneni shine bazaki iya jiran wannan lokacinba?

Tureshi tayi tace "Bazan jiraba mezai hana yanzuma ta dawo ta zauna da kai?

"ina kikaga antab'ayin haka?
"kukan kunsaba har abunda yafi haka kusan ini takeyi ad'akinnan, kai zan iyacewama kwana akwai randa naga tafito ad'akinnan cikin dare ina duba agogo naga 1:19 na dare,


K'uramata ido yayi har takai Aya, yasauk'e ajiyan zuciya yana mamakinta, ya tuna Ranan da akayi hakan, Nafisance ta masa waya cewan takasa Bacci sabida tsananin ciwon ciki da takeye na piriod, yace mata ta bari da safe yamata Allura anma tak'i tazo ta dinga masa knocking dole ya bud'e k'ofa yamata, aggagauce yamata baiko bari ta zaunaba yace ta tafi dare yayi,

Wato yarinyannan takan samasa idone aduk al'amuransa? Ko kuma tsakaninsa da Nafisane kawai take masa hakan? To meye dalilinta nasamusu ldon?


Ganin tana shirin tashine ya jawota yazaunar da ita,


"Khadijah meyasa kike da zargi? Da kinga abu sai ki fassarashi yanda ba haka yakeba, Why? Meyasa kike min Mummunan zato, ban tab'a kusantan abinda kike zargina dashiba, inason wannan yazama Rana na K'arshe da zaki daina Zargina da Nafisa, Ya k'arasa maganan yana sharemata Hawaye, "Sannan idan dan zamanki ananne bakiso to ni nasan hanyan dazanbi ki koma wajen Mami, Amma sai kin kwantar da Hankalinki kin nuna ma kowa da son ranki kike zaune dani sannan kinbi duk Umurnin da nake baki,


Kisani duk irin son da Mami take miki indai kika fito fili kika nuna mata bakison Kabir tofa son datake miki acikin kashi d'ari zaki b'arar da Hamsin, dan haka ki kwantar da hankali, nan ba da dad'ewaba zaki tafi abunki, koda cuta zata kasheni cikin dare zan san yanda zanyi,



Sosai Jikin Dijah yayi sanyi da lafazinsa na k'arshe shima ya lura da hakan, dan haka ya jawota jikinsa suna shak'an numfashin juna,

Can sukaji ana niman order, d'agata yayi daga jikinsa yace ta d'auko Hijabinta taje ta duba,


Tana bud'ewa taga Sauda da Habib da murna suka rungume juna, Nan Habib ya wucesu yana Murmushi, sai da suka gama Murnansu suka shigo ciki, kusa da Habib Sauda ta zauna ta gaida Kabir, Dijah kuma kitchen ta wuce kawo musu abun tab'awa, sai da ta cikasu da fruit da drinks ta zauna ak'asa d'an nesa dasu ta gaida Habib,
Sauda ta d'auki kankana ta kalli Habib Honey ga mutuminka bakinsa ya mik'o tasa masa, yana sha, wani mummuna kallo Kb yajefesu dashi, da sauri Sauda ta b'oye Fiskanta abayan Habib, fito da ita yayi yana Hararan Kb "yi shiru abinki my Soul bud'e bakinki bud'ewa tayi ya d'ago kankana zai samata, Kb ya d'auki goran Ruwa da d'an sauran kad'an aciki ya wurgeta dashi, Habib yayi saurin cab'ewa yana Zaro ido, "Haba Man inda kasametafa?


"Ke tashi kifitamin anan, banson Rashin kunya kinaji?

Shagwab'ewa tayi "yaya Kb sakamakon zuwa gaishekan kenan?
"Eh bana son gaisuwan, "Allah daga yau konazo bani k'ara shigowa nan, "Naji tashi kifita karkisake shigowa, kuma inkika sake wani magana anan zan tashi intakaki, inkina gadaran aurene dake da auren da Mijinkin sai intakaku, Habib ya kwashe da dariya wlh Baka isaba yaya Kb, Sauda kam mik'ewa tayi ta kamo hanun Dijah da tayi Mutuwan zaune tana kallon ikon Allah, "muje mugaida Mami,


Suna fita Sauda ta kwashe da Dariya, "wai meke faruwane Mutumiyar naga duk kin wani diririce?

"mhhm Aunty Sauda wai dama kowa tayi aure sai tazama mara kunyane?

Dariya ta kuma kwashewa dashi "Rashin kunyan me Khadija? Ai dama zama da na miji sai da Rashin kunyan indai wannan shine Rashin kunya, to ai baki ga komiba, inyi kikayi sake yanzu sai wata can ta k'wace miki Miji,
Dijah ta tab'r baki "mhmm Allah ya kyauta,


Sauda ta rik'o Hanunuta "Khadijah yakamata ki tsaya ki fuskanci rayuwan aurenki wannan game d'in yatsaya haka, kinci wsan taurin kaine kawai irin naku, Dijah ta turo baki, "Ni bawani zaman aure da zanyi kina ga har yanzu yanakan bakansa na auren wancan Banzan, nidai badani za'ayi wannanba,


"Waya gayamiki za'ayi auren? Kuma ma in anyi sai me? Ai zamanta daban naki daban, kowa tata ta ficceta, ai zama fa kishiya ba wani abu mai tsananibane illa yakansa mace ta k'ara k'aimi wajen niman Alajannanta, "nifa bazan iyayin abun da kike saninnanba wlh,
"zaki iya harma fiye da hakan muje mufito yau zan baki wani Assigment guda d'aya tak, dai2 lokacin suka shiga ciki, da sallama d'akin lya suka fara shiga,
[8/4, 4:50 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment