Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"Ina?
"Ruganmu mana,

Murmushi yayi ya kurb'i Fresh milk ya ajiye "Wato baki mantabako? To ai baki cika sharad'in nakiba kinmanta jiyama kinyi taurin kai, ya fad'a yana d'aga Gira,

Kaman zatayi kuka tace "Banyibafa dai2 lokacin sukaji anyi nocking k'ofan d'akin anmurd'a handle d'in cikinzafin nama Kb ya tashi ya shiga toilet dai2 lokacin aka bud'e k'ofan aka shigo Mami tasaki baki tana kallon ikon Allah ga k'amshin turaren Kabir da yake yawo a hancinta,

ta kalli plate d'in ta kalli cups d'in dake wajan sannan ta kalli wayoyinsa Biyu da Hulansa da yacire ya ajiye awajan,


Sannan ta maida kallonta ga Khadijah da tayi suman zaune, kaman k'asa ya bud'e ta shige, Mami ta tab'e Baki tace "Ina Kabir d'in ya shiga?


Murya na b'ari Dijah tace "Mnnm babu,

"Dana d'aukoki daga d'akinsa shine kika kawoshi d'akinki ko Khadijah? Har kin iya b'oyeshi, yaushe kika iya irin haka? Tad'an sassauta murya k'asa gami da d'an ran k'wafowa yanda tasan bazaijiba,


Tace "wato ke dad'i miji ko? To kimayar da Hankalinki ba'ayiwa Namiji haka, Khadijah so nake nakarb'armiki 'yanci, baki ganeba,

daga haka ta juya sai da takai bakin k'ofa ta d'aga Murya yanda zai ji tace kuma kisanar dashi zamu had'une daga haka ta rufo musu k'ofa tana d'an murmushi Aranta tace Kabir d'an Duniya wato sai da yasan yanda yayi ya yaudareki har kika amincemasa zaman d'akinki batare da nasanaiba saidai dama na dade ina zargin hakan, nasan yanda zan b'ullomuku dukanku zanyi maganinku yara zaku gane baku da wayau,



Washi gari Kabir da k'yar ya iya zuwa gaida Mami saidai bata nunamasa komiba ta amsa da fara'anta har yafita batace dashi.komiba,


Ganin hakane
Yasa washi gari yazo takanas yasameta, akan kujera ya zauna itakuma tana bakin gado,


Bayan sund'anyi 'yar hirane ya gyara zama yana kallonta yace "Mami jibinefa zan tafi Lagos

Mami tace "Eh inasane Allah yasa kaje lfy kadawo lfy Kabir Allah ya katemin kai,

" Amen yace gami da kallonta yace "dama inason in ajiye Khadijah a rugansune sai inwuce inna dawo sai in d'aukota indawo miki da ita,


Cike da Mamaki Mami ta kalleshi aranta tace tofa gawani tsari ta inda ka bullo kenan? Har zakacemin wai kadawo min da ita, kama cire kanka, Ayyah yaro ka makaro nagano logonka yanzu zamaka mai gaba d'aya ayita ta ka're Kabir.



πŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ

*Wai shin da gaske Kabir Rugan zaikai Dijah ko dai akwai abunda ya shiryane?*


*to inma can zai kaita anyah Mamin zata yarda musamman yanda talura yaran nata namata wasa da hankali*

*To Ya Dijah zataji in Mami ta hanata wannan tafiyan dabatasan ingancinsaba ma'an Rugan xai kaita ko wani wajan?*

Ya Kabir zaiyi tunda yanzu baya iya barci hakanan?

Nidai nace in anhanashi Dijah yaje ya d'auki Nafisa mai nimansa ido arufe πŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ

Anmafa Shawaratace wannan ke meye shawaranki? Sai naji daga gareku


*Ummu Fatima ce* 😘
[8/30, 9:51 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š

_kai Gaskiya inashan k'orafinku kala2_ πŸ€¦πŸΌβ€β™€

_Sam kunk'i karb'an uzurina fans da gaske jikinrin littafin ba sonabane_ 😰

_Nasadauk'armuku da wannan page gaba d'ayanku masu k'irana fa masu min massage ta inbox da watsao grouo da prvt duka akan Rashin ganin sabon page_

Karfa kuce cin hancine πŸ™ˆπŸ™ˆ


Wanda ban amsamusu maganaba a prvt kuyi hakuri wayance tayi Rsetoring😰


5⃣8⃣


Wani kallon baka da wayo Mami ta bishi dashi tayi murmushin inka san wata baka san wataba, ta d'an muskuta suna facing d'in juna sosai,

Tace "ka k'osa ko Kabir? Ka k'osa tayi ta barmuku gida,

ka k'ara Hak'uri ina sane da Ak'awarin da na maka, duk yaushenema tagama makarantan?

Cikin wani irin yanayi Kabir yake kallon Mahaifiyar tashi, jin tamasa wani fasarra na daban,

ya girgiza kai "No Mami ba haka nake nufiba.. Da hanu ta da katar dashi, ta d'an had'e Rai "ya isa Kabir kai da zaka Lagos a jirgi mai xai kaika wannan Rugan?

Kayi tafiyanka kawai ni na d'auko Khadijah daga wajen iyayenta da Hanuna, kuma ni xan mayar da ita garesu da Hanuna, kayi tafiyanka kawai kabarmin abata.

Ahankali ya d'ago ya kalleta sam ba alaman wasa a fuskanta,

"Ayyah Mami baki fahimceniba, ba manufata kenanba, ya fad'a azuciyansa,

Yaso ya fahimtar da ita, anma Ganin bai samu fuskaba yasa ya mik'e jiki ba k'wari ya fita,


A k'ofan pertd'insa ya zauna ya rafka tagumi yana tunani da jin Haushin kansa na yanda ya bari yake shiga cikin lamarin yarinyan da yawa haka,


Can yayi tsaki gami da mik'ewa aranshi yana tunanin gara yayi tafiyansa ma shi kad'ai yasan kafin ya dawo ya manta ta kwata2

Da wannan shawara Kabir yayi shirinsa a tsanake, cikin kwana Biyun ko nimanta baiyiba, duk da yanda yake jin zuciyansa da gangan jikinsa nayi, na Rashin ta akwana biyun, anma ya dake gani yake da yatafi shikenan ya manta da ita

******************

Tun shida ya fara shirin tafiyansa ayau, dan da wuri yake son barin gidan sabida abinda yakeji na fizgansa game da Khadijahn,


Fararen tas d'in Suit yasa dw wandonsa, yayinda na cikin ya kasance coffe brawn, takalminsa ma Sau ciki cofee brawn yafito a asalin Likita Gogagge kuma wayayye sai da yagama had'a duk takardun da yake da buk'ata sannan ya manne idonsa da Glass mai fararen kwalba wanda kake iya ganin komi na idonsa tas tacikin kwalban yayin da Hanun galss d'in ya kasance coffe brown ya d'aura agogon fata ahanunsa shima brown ya d'auki brief case d'insa brown ya fito, sauri yakeyi sukayi kicib'us da Sani A falo, dukansu fuskansu da guntun Murmushi suka mik'a ma juna hanu,

Sani yad'an gyara tsayuwa yana kallonsa, "Haba Kb meyasa yanzu inzaka fita sam bakasanr dani kuma kasan aikina ne fita dakai,

Kabir yayi murmushi yaja Hanunsa suka fita yace "Abokina ta yaya zan dinga d'aukanka muna tafiye2 kullum bayan yanzu kazama nai lyali?

Tuni na canzamaka aiki abubuwanne basu gama kankama ba shiyasa bansanar dakaiba, Na mai dakai Campaninnan yanzu kaine Manerger,

zaro ldo sani yayi ya tsaya cak da tafiyan da yakeyi "Kana nufin Zaka karb'a ahanun Alahji ya'u kabani? Kb yayi murmushi gami da d'an dukan kafad'ansa "shirin da nakeyi kenan Abokina, kasan nidashi d'in kowa shiri yake akan d'an uwansa, ninawa shirin kenan akansa inyagama farautanan,

Daga haka ya wuce cikin pert d'in Mami, yabar Sani da tarin Mamaki yarasa hali irin na Kb sam bayada k'yashi ko Hassada, Burinsa wani yasamu ak'ark'ashinsa, yasan duk irin Abunda Alhaji ya'u yake shukawa akansa anma yayi burus ya zuba ido yana jiran sai yagama.


D'akin Mami ya nufa jin Motsi akitchen yasashi dawowa a tuanainsa Manince aciki,


Khadijah ya gani tana share Hanunta da Towel dan wanke2 datagama, Dam!! Sukaji zuciyoyinsu ya buga a tare,

Da sauri ya juya ba tare da yace komi itama da saurin ta yarda towel d'in da yake hanunta ta nufoshi gami da k'iran Sunansa, "Doctor!! Cak yatsaya ya juyo yana kallonta, ta matsoshi asanyaye daf dashi ta tsaya ido da ido suke kallon Juna,

Numfashinsu na turereniya, ta d'an girgiza kanta tana ci gaba da kallon k'wayan idonsa da shima ya bud'esu sosai yana kallonta dasu, yanajin wani abu na ratsa illahirin jikinsa, Cikin wani irin Murya mai d'auke da damuwa tace "Likita kafasa kaini Gidanmunne?

D'an ajiyan zuciya ya sauk'e yayi kaman zai juya tayi caraf ta cafko Hanunsa tana murza cikin tafin Hanunsa da yatsunta kaman yanda yake mata aduk lokacin da yake son shawo kanta akn wani abu ta d'an langab'ar da kai, Murya Asanyaye


Idonta taf da Hawaye tace "Baka tab'amin Alk'awari kacikaba Likita, meyasa kazamo mai magana biyu? Meyasa kake yawan yaudarana?


Cikin mutuwan jiki da kalamnsa da kuma abun da take masa ya jawota jikinsa yamanneta ak'irjinsa, yanajin zogi aransa harga Allah yaso tafiya da ita suje Rugansu suyi kwana biyu sai su wuce Lagos kafin su dawo, dan ayanzu ji yake kaman bazai iya Rayuwa ba itaba, duk da yasan ba sonta yakeyiba anma zuwa yanzu yasan tana da matik'ar Muhimmaci a Rayuwansa,

Anma ina Mami ta hana faruwan hakan.

Kuka tasake gami da K'ok'arin k'wace jikinta dan yanzu ta gama ganewa jikinta yakeso shiyasa yake yawan yaudaranta sai ya samu yanda yake so sai ya shareta,

shiyasa yanzu ya yaudareta dacewa inbata bashi kanta bazai kaita gun Baffantaba inkuwa tana Amincewa da shi zai kaita tayi sati ya dawo da ita,

bayan wata yasake maidata, Ashe duk yaudaranta yakeyi,


"Khadijah ba laifina bane ya fad'a Araunane, da sauri ta k'arasa k'wace jikinta ta kalleshi "Likita na dawo daga Rakiyanka bazan sake yarda duk wani furuci da zai fito daga bakinkaba,

Cak magananta ya tsaya sakamakon Had'e Bakinsu waje d'aya da yayi kissing nata yakeyi cikin k'warewa jin suna niman su fad'ine ya manneta da jikin Gini ya tura Hannayensa Cikin Riganta, Shiru tayi ta kasa Koda motsi ne sai k'ara lafewa takeyi ajikinsa tana fitar da Numfashi, tanajin kaman tana Son abinda yake matan,

Jin takun k'afa Alamun ana dosowa kitchen d'inne yasashi zare Hanunsa da Bakinsa ajikinta, ya d'anyi baya kad'an dai2 lokacin Mami ta shigo tana fad'in "Khadijah har yanzu baki gamabane?

Nan idonta ya sauk'a akansu kallo d'aya ta musu ta gano halin da suka fad'a da sauri ta janye idonta tana k'ara tusuwa cikin kitchen d'in cikin dakewa tace "Af Kabir kar dai har kagama shiri, ai nayi zaton kana Bacci ne inata k'iran wayanka baka d'agaba,


Gefensa Khadijah tabi ta fice cikin azama ji yake kaman yabita ya kamota ya maidata jikinsa,


Ya gyara tsayuwa kansa ak'asa yana facing Mami da tak'i yarda su had'a ido tana ta had'a abinci a Basket sai da yayi gyaran murya kusan sau uku kafin ya iya fara Magana duk da Maganan baya fitowa sosai, yace "Ni zan wuce Mami amana Addu'a sai lokacin ta d'ago ta kalleshi,

"zaka wuce bakayi Break ba Kabir?
"Nayi a pert d'ina Mami sauri nakeyi kar asamu matsala kai ta jinjina, tafara Jero masa Addu'o'i yana Amsawa da Ameen har ya fito a a falo yasamu lya,


Yamata sallama tace "Ayyah nima bazaka dawo kasameniba Kabiru Gobe insaha Allah zan wuce Maiduguri,

Yace Haba lya wai me kikeyi a Maidugirinnane haka da kika k'i hak'ura da shi?

Dariya tayi tace "abunda kakeyi a yola haba Kabir ni da mahaifata ga zuri'ata duk acan kace me nakeyi,

"to ki k'ara hutu anan sai ki koma
"a'ah gaskiya ina kewan gidanmu,
"Ok kibari to inna dawo nanda sati sai inmayar dake da kaina, tace "Anyah zan iya? Sati zakayi acan?
"Eh Ran ata yau zan dawo insha Allah,
"to barin gani dai,
Nan sukayi sallama ta masa fatan sauk'a lfy ya fice zuciyansa na ga Khadijah ya rasa wani irin Hukunci Maminsan takeson yankemasa,


Dijah kuwa tun shiganta d'akinta ta shige wanka dan tasaha Alwashin zatayi ma Mami Rikici ta barta taje wajen 'yar'uwanta ta wuni ko zata huce takaicin da Kabir ya d'ura mata tafito kenan taji hayaniya ta window, ta yaye labule tana kallonsa yanda sceuiritynsa suka kewayeshi yana tabasu hanu,


Zuciyantane taji na mata d'aci tana kallonsa har ya shige Motan ta saki labulen gami da fad'awa kan gado ta saki Kuka mai cin rai da irin yaudaran da yamata, sannan awani fannin tanaji ajikinta ya koyamata jarabansa, dan kwana biyunnan da yayi ba tajita ajikinsaba da k'yar take iya Bacci,


Tafi Awa biyu tana risgan kuka kafin ta tashi da k'yar ta shirya,

tana d'aurin d'an kwali Mami ta shigo, kallo d'aya tamata ta gano kukan da taci aranta tana mamakin yanada akayi nan danan ta hango tsananin zazzafan so da shak'uwa a tsakaninsu wato ita dai tana Gidan Sun maidata Hotiho tana musu kallon suna fad'a gami da sukan juna ashe akwai wani sirri tsakaninsu,

Dan ba k'aramin mamakin yanayin da ta gansu d'azu tajiba, dan dukansu fuskansu ya nuna tsananin buk'atuwa da k'aunan junansu,


D'an tab'e baki tayi aranta tace bazan janye k'udurinaba Khadijah inna janye wlh kece aciki muddin bangara Kabir akankiba Nafisa da Uwarta zasuyi saurin cin Nasara akanki,

anma inya garu yasan zafinki to ko zasuyi nasara ba dukaba zai nayi yana tuna cewa ked'in mai tsadace inkin kub'uce masa zai sha wuya, Ta sauk'e ajiyan zuciya awani gefen kuma tana tausayinsu, tace "Khadijah kizo ki karya Sai kije kiyi ma Fatima sallam Gobe in Allah ya kaimu zaku tafi maiduguri da lya kije kid'anyi Hutu akwai autar lya dazata miki gyaran jiki inkun gama sai kidawo kuje can wajensu Baffah,


Wani irin kallo Dijah tayima Mami sannan ta kau da kai aranta tana tunani "to kodai haka duk mutanen garin suke da yaudara?


"Kiyi hak'uri Khadijah nasan hankalinki ya tafi wajen son ganin mahaifanki zaki je lnsha Allah, ta fad'a cikin rarrashi kaman tasan abunda Dijahn take tunani,

Mik'ewa Dijah tayi tana kauda damuwanta ta fita.


Dama tuni Mami tagama tsara lya akan tafiyan takuma gama shirya yanda komi zai tafi dan haka washi Gari da safe suka wuce Maiduguri,

BaK'aramin Mamaki Dijah tayiba yanda aka dinga nan danan da ita agarin duk wanda ya shigo lya tace masa ga matan Kabir sai taga ank'ara karramata haka sukayi ta tururuwan zuwa ganinta, sosai tasake acikinsu,


Washi gari lya ta damk'ata ahanun Ya Fannah, kamar yanda Mami ta gayamata,

wayyo Nan ya Fannah ta fara aiki akan Dijah na musamman dan tuni tariga da tasan komi game da Dijah da Nafisa dama ba k'aramin haushin iyayen Nafisa takejiba akwai k'ulli tsakaninsu Shiyasa bayanda basuyiba kan ta gyara Nafisan fir tak'i,

abubuwa take koyamata tunda ga kan yanda zata zauna da Mijinta da kishiyanta, girki, tsafta kula da shimfid'an miji, da yanda k'amshi zai kama jikinta koda yaushe, kafin sati Dijah ta canza kala gaba d'aya dan wannan sana'an Yafannah ce na shekara da shekaru ba k'aramin k'warewa akai tayiba dan gari da gari ana zuwan mata,

*****************

*Kabir* tun fitansa agidan cikin damuwa yake ahaka har ya isa cikin garin Lagos ya sauk'a a hotel d'in da aka tanadar masa bayan yayi wankan gajiya ya haye kan gadonsa ba abunda yakeso da k'aunan gani irin Khadijah,

ya k'ira Maminsa sun d'au lokaci suna hira yana ta kasa kunne ko zaiji koda motsintane kusa da Mami anma baijiba da haka sukayi sallama, yana ajiye wayan k'iran Nafisa na shigowa,

bai d'aukaba sai da ta mishi missed call2 kafin yabita tana d'auka tasa kuka hans fre yasa Wayan sannan ya ajiye agabansa yanajinta sai da ta gama tafara magana sannan yace "ina jinki inkingama zan kashe wayana inci Abinci,

"hakama zakace kabir? Bayanda banyi zan bikaba fir kak'i yanzu kuma tun yaushe ka isa anma baka k'iraniba, ina k'iranka inajin kana waya, dawa kake wayan da yafini muhimmanci?

Ahasale yace "Uwata ko kina da magana? Nafa gayamiki muddin kinason mu shirya kidaina min magana gatse2 haka ba sa'ankibane nifa kingane, baijira ta cewantaba ya kashe wayan gaba d'aya yana jan tsaki,

Ba yanda baiyiba yaci Abincin anma yakasa dan damuwa,


haka ya hak'ura ya kwanta kalaman da tagayamasa su suka tsaya masa arai da hoton fuskanta irin kallon da take masa haka yadinga juyinsa agadon, sai dai yasama ransa nanda kwana biyu yamanta ta, daga nan kuma inyakoma bazai kuma shiga hark'antaba, in Mamin taga dama tabashi ita shikenan, inta mayar da itama shikenan, tunda kafin zuwansannan Alhaji ya'u ya k'irashi yatsaida ranan tariyan Nafisa nan da sati,

zai zauna da ita haka, Duk da sam bayajinta aransa, ita Dijanma yasan ba sonta yakeyiba, saidai ko ba komi tafi Nafisan sanin me takeyi wannan shine kawai Banbancin da yasa yake tunanin Dijahn fiye da ita Ba wani abuba.



Sai dai Duk yanda Kabir yayi ya cire Dijah arasa abun yaci tura, kullum abun k'aruwa yakeyi ahaka dai yayi kwana hud'u da k'yar rana tsaka ya tattaro ya dawo batare da yakammala abunda ya kaishinba.



Habib da Sauda yasamu da Mami a falo suna hira, kusa da Mami ya zauna yana yarfe hanu alamun wai ya gaji,


Mami ta kalleshi rik'e da Baki tace "yanzu kabir dakacemin gaka dawowannan da gaske kakeyi??

Ya shafa kansa yana murmushi yace "wlh kuwa Mami garinne ya isheni, ba dad'i
"Ikon Allah lokacin daka fara shiryan tafiyannan sati 2 kace zakayi, daga baya randa zaja tafin kace sati 1, kaje kuma kayi kwana hud'u kadawo,


Habib yace "wlh kuwa Mami nima yabani Mamaki dan randa ya isa nikanma cemin yayi sai kawai anganshi,


Sauda ta tashi ta d'auko masa Ruwa a frich ta ajiye agabansa, tana kallon Habib, "daga shigowansa bai ko hutaba yaya Habib zakamasa sharri,


"Rabu dashi sam bai da Kunya baya girmama nagaba da shi baya girma ma aurensa ko ba komi ai ni sirikinka ne, ya fad'a yana kurb'an Ruwan, sannan ya a jiye ya kwantar da kansa akan cinyan Mami da take ta kallonsa dan inba idonta bane yake mata k'arya kaman taga ya d'an fad'a,


Lumshe ldonsa yayi yanajin suna cigaba da Hiransu,


Mami tace "to tashi kaci Abinci Kabir dan inagama hala rabonka da Abinci tun randa katafi naga duk ka fad'a,

Idonsa a lumshe yace "later Mami,
"Mhmmn kawai tace sukaci gaba da Hiransu,

Har su Sauda sukayi ma Mamin Sallama suka tafi, ya tashi yace mata xaije yayi wanka yazo,


Bayan anyi lsha'i ya shigo yana cin Abinci hankalinsa nakan k'ofan Khadijah, ko zai ganta shiru har ya tashi bai gantaba, sun d'an jima suna hira da Mami har tafara gyangyad'i, ganin haka yamata sallama ya tafi wasa2 kwanansa kusan uku da dawowo baiga Khadijah ba, aranan na Ukunne da ya shigo yayi k'undumbalan shiga da saurinsa ya mayar da k'ofan ya rufe dan kar Mami ta ganshi ya kunna hasken d'akin bai gantaba bayam gida ya bud'e nanma wayam, cike da fargaba ya dawo yana bin d'akin da kallo zuciyansa na bugawa ya kalli gaban mirrow ba kayan kwalliyanta,



Nan bugun zuciyansa ya k'aru dan yanzu kan ya tabbatar da bata gidan da alama ma ta jima batananan, asanyanye yafito ad'akin yana jin d'aci azuciyansa.


cikin wani hali ya shiga d'akin Mamin, tana kallonsa ta gano wani abun tattare dashi,

Fita yayi ba tare da yace komiba, can anjima yakuma shiga, kallonsa Mami takeyi yana ta shiga da fita kaman mai niman wani abun, bata kulashiba.

Yana son ya tambaya yana tsoron jin Amsan da zai tarwatsa zuciyansa,


Washi gari Mami ta shirya tana shirin fita ya shigo ta kalleshi "zan d'an fita Kabir inbaka key d'in nanne?

Ya d'an gyara tsayuwa cikin kasada da k'undubala yayi k'arfi hali yace "Ina Khadijah ne Mami?

Saida ta zira hijabinta tace "ai Khadijah tajima bata Gidannan Kabir wlh duk kewanta ya dameni gidan bayamin dad'i sam,


Kansa na k'asa ya dawo kaman andasashi har ta ida magananta, ta rufe pert d'in tare suka jera har jikin Mota,

Sai da ta shiga tace "Ina dai maka tunin maganan gyaran gidankannan inkuma haka zaku shiga shikenan,


Daga haka driver yaja suka fice.

Hakanan Kabir yaji jikinsa gaba d'aya ya mutu ya dinga jan k'afansa har yakai falonsa ya zube cikin Kujera, Ya dafe kansa,

*Nadawo daga Rakiyanka Likita bazan k'ara yarda da duk wani furuci da zai fito daga bakinkaba,*


*Baka tab'amin Alkawari kacikaba*

Kalmomin dake ta masa yawo kenan yana tunano fuskanta da gangan jikinta yanda yakeji aduk lokacin da suka kasance,

Kafin kace me zazzab'i ya rufeshi gami da ciwon kai,

Jujjuya kansa kawai yakeyi acikin kujera yana cewa "why Mami why Mami meyasa kikamun hakan??????? 😭


*Ummu Fatimace* 😘
[9/1, 8:30 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


5⃣9⃣


Ahaka Habib ya shigo yasameshi cikin wannan Hali ya zauna agefensa yana kallonsa,

Cikin d'an damuwa da yanayin da yaga Aminin nasa yace " Man any problem? Me yasameka? Yajeromasa Tamabaya.

Ajiyan zuciya kawai yake ta sauk'ewa batare da ya Amsamsaba har sai da yakuma masa wani tambayan,


Ya d'an girgiza kansa ahankali yace "Nothing! Zazzab'ine kawai ya d'an tab'ani,

Habib ya k'ura masa ido, Sannan ya Numfasa "to kasaha maganiman,

Kb ya ya gyad'a kai Alaman yaji,


"Dama key d'in Gidanka zakabani wai yau zasuje Jere,

Da baki Kb yamasa Nuni da key d'in da yake kan Tv stand, Habib ya d'auka ya fita,


Wasa2 Kabir ya lula duniyan tunani na Rashin yarinyan da bayi tunanin sonta yakeyi,

Zaune yake a k'ofan pert d'insa yana kallon ma'akaitan Gidan ya zaro wayansa a Aljihu kaman mai Niman wani abu aciki Rana ta farko da yafara tunanin wai meya hanashi Mallakan No. Khadija? Nan danan yaji zuciyansa takamu da tsananin son mallakan No.ta Yak'irata dana yaji awani hali taje Rugansu. Ma'an meye matsayin da suke ayanzu?


Zunbur ya mik'e ya shiga side d'in Mami a falo yasameta tana kallo ya zauna yana mata sannu da hutawa, ta Amsa cikin kulawa tana kallonsa duk yafita ahayyacinsa, gaba d'aya ta tsinci kanta cikin Rashin jin dad'i,


"Kaci Abinci kuwa Kabir?

Sosa Kansa yayi yana kallon T.v
"Zanci Anjima,

Tashi tayi ta shiga kitchen ba tare da tace masa komiba,

Da saurinsa ya d'auki Wayanta, Rana na Farko da ya dinga mata Bincike a waya, Contact d'inta ya shiga yasa K letter nan sunan masu K suka bayyana kan wayan ya dinga sauk'a har yazo kan su Khadijah,
Suna khadijahn suna da yawa iri daban2 Awayan anma ba wani Abunda ya nuna masa No. Khadijan da yake nima,


Duk iya Bincikensa yakasa gano no. Da yake nima,


Jin Motsin Mamine yasashi saurin maida wayan inda yake, ya d'ago yana kallonta rik'e da plate da cup na Abinci,


Agabansa ta dire gami da bashi lzinin cinyewa yabata plate d'inta, nan ya hau ci a zuciyansa yana tunanin a ina zai samu No.?


Nan wani tunani yazomasa aransa,


"Binta Rugan zakayi ba No. Zakanimaba, Yesss yafad'a a fili dan jin gamsuwa da wannan shawara da Zuciyansa ta bashi,



Saida yad'anci Abincin ya tashi yana kallon Mami yace "Mami k'arshen Satinnan xanje induba Dabbobinmu na wajen fulanin nan,



K'uri Mami tayi tana binshi da kallo aranta tana mamaki duk da bata kawo cewa garin su Dijah xaijeba,

ganin yana shirin Angwancewa, Sannan kuma bai cika zuwa duba dabbobinba sai tayita Magana yake zuwa yasata Mamakin,



"An ma dai ba Rana da za a kai Nafisa zaka tafiba ko?

"Washi Garine zanje, ya Amsa atak'aice
"Allah yasa Muna Raye ta fad'a tana k'ara karantan yanayin sa,




Ranan Asabar aka kai Nafisa Gidan Kabir washi Gari Lahadi yayi shirin tafiya Rugansu Dijah, tare da tarin tsaraba.



Kuyi hak'uri da wannan wlh dan in farntamuku na takura kaina nayi wannan d'in Manage pleas

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment