Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

b'ab'b'alakiba,


Aguje Dijah tabi ta bayan Kujeran ta nufi d'aki tana kuka tana maganan dabaya fitowa,


Sake jakansa da ke rataye a kafad'ansa yayi yabita cikin zafin nama, tana shiga d'akin yana biye da ita yakaimata cafka Tayi saurin Shigewa Toilet ta mayar ta rufe, ta jingina bayanta da k'ofan.

*Wannan Daru haka? πŸ€” Su Malam KB haka ake Tarban bak'uwa?* πŸ€”πŸ˜

*Ummu Fatima ce* 😍
[9/24, 5:49 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣6⃣


Shima jingina cikinsa yayi kan k'ofan yana son ya bud'e ta k'arfi sai dai yana tsoron kar yajimata ciwo,


"To waima meyasa kike guduna? Ko jarumtankin na k'aryane?

Jin bata Amsaba yasashi ya bar wajan gami da bud'e k'ofa jin yafitane yasa ta fito tana share hawaye, da sauri ta maida k'ofan ta Rufe harda murd'a key,


Tadawo ta sauk'o da Akwatinta a saman sif, ta fara jibge kayanta aciki, tana gamawa ta nufi mirow tafara tattare kayan kwalliyanta,

Tana cikin tattarewa ta hangi Mutun kwance asaman Bed d'inta Hannayensa nad'e akan k'irjinsa ya tsura ma Hips d'inta ido ba k'ak'k'autawa, ta cikin Mirrow,

Axabure ta juyo suka had'a ido ya kannemata ido d'aya yana Murmushin Baki da wayo, sauri2 tayi ta rufe jakanta batare da ta tuna Hijab ba ta fara jan jakan takai bakin k'ofa ta taso da Ximman bud'e k'ofa taga baki key ajikin k'ofan ta juyo sukayi ido hud'u da Kb yayi mutmushi gami da kad'a makullan a hanunsa, yana d'agemata Gira.


Wani irin kuka mai tsanani Dijah ta sake gami da kifa kanta a jikin k'ofan tana Bugawa da Hannayenta tana goga goshinta a jikin k'ofan, Tana jin kaman Zuciyanta xai fito waje,


A tsorace Kabir ya diro daga gadon ya nufota, a fusace ta juyo ta d'auki Kwalban turare ta kwad'ashi da k'asa ya tarwatse a wajan, ta nunashi da yatsa,

"Kar kasake ka matsoni wlh zan illataka ka bud'emin k'ofa infita daga wannan banxan Gidannaka,


Sosai jikin Kabir yayi sanyi, yasan ya tsokaneta dan Nishad'ine duk da yasan itad'in ba kanwan lasabace, saidai sam baiyi tsammanin hakanba,


Ya langab'ar da kansa a sanyaye yace "Yi hak'uri Khadijah, xan bud'emiki ki tafi anma kidaina wannan kukan,

"Ba Ruwanka da kukana ka bud'emin k'ofa kawai ta fad'a cikin k'araji,


Ya juya ya nufi k'ofan ya bud'e, ya juyo yamata kallon inkinsan wata baki san wataba,


Ta jawo jakan ta fita har takai tsakiyan palourn ya sha gabanta,
"Haka zaki fita ba mayafi Khadijah?

Sai alokacin ta tuna da mayafi, anma tayi kaman batajishiba, ya sake maimaita mata, d'an jim tayi ta kalli kanta, tasan bai dace ta fita a hakanba,


Dan haka ta sake jakan kayantan awajen, ta juya ta nufi Bed room d'in da sauri ya d'auke jakan ya fita dashi,

Ta dinga jijjiga k'ofan anma yak'i bud'ewa,

"Kash! na manta naja k'ofan ya rufe gashi key d'in na ciki, ta jiyo muryan Kb abayanta,

Ta juyo ta kalleshi da Rinnanun idonta,


Ta fita palour ba tare da tace mishi komiba,

Turus tayi tana kallon wajan da ta ajiye jakanta, babu,

Kabir ya rab'a gefenta ya wuce zai fita, Da sauri ta sha gabansa, cikin dashashiyar murya tace "Malam kaban jakana, xan d'au mayafina,

"Oh nasamiki jakanki acikin Mota, Muje inbaki, ta galla masa Harara, zatayi magana,

Ya d'an had'e Fuska, Yana kallon agogon Hanunsa, So nake na ajiyeki agidanku in wuce sauri nakeyi, Muje ko.

Wani irin kallon Rainin hankali ta masa, farin Sani ta masa wajan iya wasa da Hankalin mutum,

"Bance ka kaini ko inaba, ba kai ka kawoniba, kabani kayana, ta karashe cikin tsawa,

"Ok ba damuwa Muje ki karb'a ya wuce gaba ta bishi, wani Coridor Yabi sai gasu a wani tafkeken palour, suna shiga ya mayar da k'ofan ya rufe,


Ya kalleta, Yace "Ina xuwa,


Tsayuwa tayi a wajen tana kalle2 Duk da ba fahimtan komi datake kallon takeyi ba, tsaban b'acin ran dake jikinta, Har wani jiri takeji Sosai ta juye ta fito a asalin bafulatananta,


Kusan Minti biyar ta b'ata tsaye a wajen, bai fitoba, a fusace tabi hanyan da taga yabi, tayi tafiya kad'an taga d'aki ba b'ata lokaci ta hankad'a k'ofan tashiga,

System tagani da takardu barbaje a tsakiyan palourn alamun yanzu Mutum ya tashi a wajen, ta dinga bin d'akin da kallo daki2, ba motsin komi sai na na'urorin da suke aiki a d'akin,

Ta jah dogon tsaki ta juya, danbatasan d'akinma na wayeba,


Sai dai tana kaiwa bakin k'ofan tayi2 ta bud'e abu ya gagara,
Wani irin kuka ta kuma sakewa mai tsima zuciya ta sulalle a jikin k'ofan ta jingina kanta ta cigaba da rera kukanta, a haka bacci yayi gaba da ita,

wani irin nannauyan ajiyan zuciya Kabir ya sauk'e daga inda yake b'oye a bayan Sif yana kallonta, a hankali ya tako gabanta ya tsuguna, zuciyansa tana harbawa, sau biyu yana mik'a hanu zai tab'ata yana janyewa, saboda tsoron kar tatashi,

Ya tsura mata ido yana kallonta cikin Mutuwar jiki, a haankali ya shafi Gefen fuskanta,

"Khadijah Case yaushe zaki daina bani matsala haka?

A hankali ya d'auketa yana taku da ita kaman wanda ya d'auki k'wai ya kaita kan gado ya kwantar da ita, ya gyarata yaja tattausan Bargo ya rufeta dashi,

Sai ajiyan xuciya takeyi irin na wanda yaci kuka ya gaji shikuma ya xuba mata ido kaman zai cinyeta,


Yasa hanunsa yana shafan gashin kanta a hankali yana Murmushi, Xuciyarsa cike da farin cikin yau gashi ga Khadijahn sa dayake yawan Mafarkinta,

Yayinda wani sashin kuma yake cike da fargaban ya zasu kwashe intafarka? Yasan yariga da ya tsokanota yau Allah kad'ai yasan yanda zasu kaya.


K'iran Azaharne ya sashi ya tashi ya shige Bayi ya d'auro Alola yazo ya wuce Masallaci,

Har yadawo bata farkaba, ya zare Jallabiyan Jikinsa ya ajiye, ya juyokenan yaga tana motsi alamun zata farka,

Damm! Yaji k'irjinsa ya buga a hankali yafara Addu'a "Ya Allah ka kub'utar dani daga Rikicin Wannan baiwa taka,

A hankali ya tako ya k'araso bakin Gadon yatsaya yana Murmushi, dai2 lokacin ta bud'e idonta tana k'are ma d'akin kallo har idonta ya sauk'a a kansa Zunbur tayi ta tashi tana kallonsa,


Cikin wani irin Murya tace "Likita Wlh bazan tab'a yafemakaba duk Abunda kake min kabani kayana intafi Ruganmu, zata sa kuka ya zauna a bakin gadon ya janyota jikinsa ya rungumeta,

Nan tafara kiciniyar k'wacewa anma takasa, tasaki Ajiyan Zuciya mai k'arfi ta manne ajikinsa tana sheshek'a,


Kabir kan gaba d'aya Jikinsa ya d'au b'ari shi kansa baisan daliliba, yana jin yanda ta lafe ajikinsa tana ajiyan xuciya, yanason ya d'an fad'amata kalma koda gudane dazai k'ara sanyayamata anma yakasa,


Tsawon lokaci suna a haka yaji d'umin hawayenta, sai alokacin yasamu ya fitar da wani Numfashi mai k'arfi ya d'agota suka had'a ido, a raunane tace "Likita ka barni intafi dan Allah!

"Ba inda zan barki kije Khadijah, Wannan tafiyan da kikayi kibarni tsawon wannan lokacin bai ishekiba?

Ta tureshi tana masa kallon sama da k'asa, "Ko kazaci da Nafisan kake tare da zakace haka?

"Nasani da Khadijana nake tare Nan gindamunne Khadijah Ba inda xakije kibarni,

"Gidanku dai kai da Nafisa,

"Mu Ukune har da ke Khadijah kecefa Uwargidana, ko kinmanta? Kinzama Jinin jikina inbaki bazan iya rayiwa mai kyauba, dan Allah karkisake tafiya kibarni,


Kuka kawai Dijah ta sake don ta lura abunda yasaba zai mata wato yaudara,

Ya sake manneta da jikinsa tanason ta k'wace anma ta kasa,


Saida yagama jagulata san ransa yamatso saitin kunneta, yace "Zakiyi sallah? Kai ta d'agamasa alaman eh, yayi murmushi ya tashi da ita ajikinsa yamata rakiya har bayi,

wanka tayi sannan tayo Alola tana fitowa ta samu kayanta akan gado har da na kwalliya da hijabi, d'an Simple make up tayi dan yanzu bata iya zama batayi kwalliyaba, tunda ta zauna da Yafannah,
tana sa kayan ta gwada bud'e k'ofan anma yaki bud'uwa dan haka ta dawo tayi sallahnta,


Tana zaune kan sallahya ya shigo rik'e da Abinci ya direshi agabanta, ya zauna ya zare hijab d'inta ya ajiye agefe, yana kallonta, Cikin sigan Rarrashi, yace


"Zo kici Abinci my hert, ta turo baki
"Nifa tafiya zanyi ba abunda zanci,

Yad'an Murnusa ya zuba Abincin a plate ya jawota jikinsa, Tayi saurin k'wacewa tana shirin tashi, ya kuma jawota, ya kifata saman cinyanshi,

Nan ta saki kuka, cikin sanyin jiki KB ya d'agota suna fuskantan juna ya fara share mata hawaye, "Haba Khadijah ki saurareni kiji abunda zangayamiki, pls daina kukan haka,

"Nikabarni intafi Likita banson jin komi daga gareka, Ni garinmu zantafi,


Kabir ya furzar da huci tabbas yasan yau ya d'ebo Ruwan dafa kansa, da Kansa.

Nanfa ya shiga Rarrashi kala2 yayi wannan yayi wancan, duk shi kad'ai, anma mutumiyar tashi ta tubure ita dole sai ta tafi Rugan Juma wajan Baffah 😁

Da k'yar ya samu yasha kanta har ta yarda taci Abinci, ya d'auketa suka fita ganin gari sai kusan Magriba suka dawo,

Yanzuma sashinsa ya kaita badan tasoba,

Haka suka kwana kadaran kadahan tak'i yarda ya Rab'i jikinta, haka duk yanda ya kai da zak'uwansa ya hak'ura ya zuba ma Sarautan Allah ido,

Kwanansu biyu suna a haka, Khadijah tak'i Hausa,

Yau KB tunda ya fita yaje Gidan Mami Bashi ya dawoba sai da'akayi la'asar Hadarine agarin sosai da yahaddasa sanyi, sauri2 ya shige sahinsa,

A kwance yadawo ya tarar da Dijah tasha kwalliya kaman zata perty wayanta na hanunta tana cherting da Sauda da Bintalo,

Sallamansane ya katseta ta tashi tana Ansawa idonta akansa Fuskansa Ba wani walwala,


_Idan kika sabarmasa da yamiki laifi ya rarrasheki kik'i jin rarrashi kece da wahala, ba ayima na miji haka, inyasaba da hakan zai daina rarrashinki, dan yasan koya rarrasheki aikin Banzane, Bazakijiba,_

_kiyi k'ok'ari kija mijinki jikinki kafin Nafisa ta dawo, dan inta fuskanci rashin jituwa a tsakaninku zata kara samun kofa_ Sam fushi da Miji banakibane,

Ta tuno Abunda yanzu suka gama tattaunawa dasu Sauda,
Kenan har yagaji da Rarrashintan ne?

Ta sake Kallon inda yake yana cire kaya zai shiga bayi, Ba tare da ya nuna kulawansa garetaba,

"To ta ina mazan fara? Ta tambayi kanta, ta d'an zamo daga kan gadon ta tallafi hab'anta, cikin fad'uwan gaba,
.
Tana nan a haka har ya shiga ya watsa Ruwa ya fito ya shirya cikin kaya masu d'an kauri, dan yanayin garin, a hankali ya tako ya k'araso kusa da ita ya zauna, yana kallonta, baice da ita komiba, Dan baisan da Abunda zata maida nasaba, ya jawo System d'insa, yafara sarrafashi,


Ta tashi a sanyaye taje ta kawo masa Abinci ta dire agabansa, ta kalleshi "Ga Abinci, d'an kallonta yayi ya tab'e baki

"Kingama fushinne?
Ni naci Abinci a wajen Mami sai dai anjima,


Dijah ta sunkuyar da kanta tana goge k'ollan da ya fito mata,

Ya kalleta na d'an lokaci, Sannan ya zamo ya jawota jikinsa, "Haba Khadijah har yanzu baki huceba?

Ya kk son inmiki, yanzu meye na kukan? Eye gayamin yanzu Duk yanda kk so haka za'ayi Khadijah koda zan cutu zanmiki yanda kikeso banason wannan kukan Allah kuwa har zuciyata nakeji,


Ta lafe ajikinsa tana wasa da xip d'in Rigansa,

Tace "Bakai bane kak'i cin Abincin,

"No bahakabane na riga naci Abinci a wajen Mami dan bansan zakibani nakiba, naga kina fushi dani sosai,

"To ai kai ka jawo,
"To ai nima nabaki hak'uri my Luv kece kikak'i hak'ura, kike ta fushi dani,
" tom na bari anma kar ka k'ara cemin Wai Nafisa Masoyiyar kace nasan kana sonta basai ka fad'aba,


Yayi Murmushi ya juyo da ita yana kallon fuskanta da take ta b'oyewa a k'irjinsa, yace "Dama duk wannan fushin wannan kalmane sila?


Na daina My Beutiful wife kece Masoyiyata Khadijah Allah kiyarda dani ina sonki sonda bazan iya kwatantamiki Abakiba, Ki yarda dani Ni nakine ke tawace burina muyi Rayuwa na rai da Mutuwa, pls karkisake tafiya kibarni Khadijah,

Dan Allah ko namiki laifi ki daina Fushi dani haka bakiji yanda zuciyata ta shiga Damuwaba, ko har yanzu baki yarda kece Rayuwataba?

Mik'ewa tayi zata gudu dan jin yanda yafara k'ok'arin Romacing d'inta, cak ya d'agata ya direta kan gado dai2 lokaci kuma Ruwa mai k'arfi ya sauk'o,
wai su KB dama yaya? bare Dijah tafito daga hanun Yafannah kuma andad'e ba had'uba πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ˜œπŸ˜œ


Rungume yake da ita a k'irjinsa ji yake kaman Ya Maidata cikin jikinsa wani shauk'in abunda ya gudana atsakaninsu yakeji,


Jiyake kaman Duk Duniya ba kamanshi wajen sa'a da dacen Mace,


Ya d'agota yana son su had'a ido itakuma gaba d'aya Kunya yagama Lullub'eta, yau itace da Romacing Kabir!!! Ji take kaman k'asa ya tsage ta shiga,

Batasan lokacin da tasaki kukaba dan kunya musammna yanda taga shi ya zak'e Da yawa,

Sai Rad'a mata wasu maganganu yakeyi a kunne masuwuyan fahimta


Murmushi yayi ya manne Bakinsu Guri d'aya, Yana mata wani Sabon salon,


*******
Boka so nake ka k'ara Mantar dashi yarinyannan kar yakuma k'ara tunota azuciyansa, yazamo kawai Nafisa zai dinga tunawa,


Wani irin Dariya tsinanan Allahn yakece dashi Bayan ya Amshi mak'udan kud'in data damk'amasa, ya kalli Maman Nafisa, Bayan yagama surkullensa,

"Ke Mu munga mijin yarinyanki da Matansa Kwance guri guda suna Sha'aninsu, Afirgice Nafisa tazaro ido tace "Boka ba Mijina kaganiba, wlh bashi bane shi bai tab'a kwanciya da wata mace ba inbaniba, kasake dubawa wannan 'yar k'auyen Sun jima da koranta agidan shi da Mahaifiyarsa,


Dariyan yakumayi ya wurgo mata k'ulle2 magani "Karb'i wannan kutashi ku tafi zamu muku bayanin yanda zakiyi Anfani dashi a Mafarki,

Ya daka musu tsawa a firgice suka tashi suka fita awajen, Nafisa ta zube a gindin wani Bishiya tana haki, "Mama wlh wannan Bokan ba k'aramin d'an iska bane, Wai har dacewa Yaga Kabir kwance da wata Mace tsaban rainin Hankali?

Ta ciza hak'ora tana jijiga kai "Wlh da hakan zai tabbata Mama sai nakashe ko wata shegiyace inyaso akasheni,

Allah ma yasawak'e Mamantan ta fad'a cikin Mutuwan jiki itakam ta tsorata da jin lafazin Bokan dan tasan aikinsa ba wasa,


Cikin b'acin rai Nafisa zata kuma Magana Maman taja hanunta "Zo mutafi kinsanfa su da Aljanu suke aiki kar su d'auki Magananmu sukaimasa,

**********

Dijah tana zaune akan Mirrow tana kwalliyanta hakali kwance yayinda duk Motsinta akan idon Kb takeyinsa, har tagama ta matsoshi ta hura iska a fuskansa, cikin shagwab'a tace "Kallonfa ya isa haka, yayi Murmushi ya kamota ya d'aurata kan cinyansa,

Yasa kansa tsakanin Wuyanta yana shak'an k'amshin jikinta yana lumshe ido,

A hankali kuma yana dannan k'asan Maranta, dan tabbatar da abunda idonsa ya ganomasa yanzu, Yaji wajan yayi tauri, ya k'ara d'an dannawa, tayi zillo gami da sake k'ara ta rik'e Hanunsa,

Rungumeta yayi tsam a k'irjinsa, yanajin kaman ya ciro zuciyansa yabata dan farin ciki,

"Wayyo Mami meyasa kika raba tsakanin d'a da ubansa na tsawon lokaci, meyasa bakibarni da yaronaba tun bai kai hakaba,

Ashe ni uban wanine bansaniba, My luv Allah ya sauk'eki lfy Allah yakawomin yarona Lfy,


A tsorace Dijah ta zaro ido tana kallonsa,

*Ummu Fatimace* 😘
[9/28, 6:09 AM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹


*Jinjina Gareki Sis Batul y'ar Jattko mai Halin Dattako* πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» the Page is urs😍😘😘


🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣7⃣



Ya hure idonta yana dad'a manneta a k'irjinsa,


Tayi saurin zamewa a cinyansa, Tana turo baki, ya biyota k'asa yana Kallonta, "Khadijah kina da ciki anma naga kaman bakiyi farin ciki da wannan Bbabn kyauta da Allah yabamu ba,


Ta turo baki cikin jin wani irin nauyi, "Nidai banaso,

Ya zaro ido "baki Son d'an namu?
"Eh ni bansonshi, kuma kar kasake fad'a,

"To inbaki Sonsa ni ina sonsa ki haifamin shi kuma sai nagayamasa kince bakisonsa,

Ta harareshi, "To kai zakabashi No..n.... Sai kuma ta rufe bakinta da Hanunta, ta sinna kanta k'asa, Kb ya cire hanunta da ta rufe Bakinta dashi yana d'ago Kanta, "k'arasamana My Luv ni xanbashi me?

Ta janye Fuskanta zata gudu ya jawota, Yana mata cakulkuli, ai sai kin fad'a meye zan bashi, ta dunga dariya tana jan jikinta, da k'yar ta k'wace kanta, ya jawota ya zira Hanunsa cikin Riganta, "mhmm wato wa Babyn nawa zakiyi Rowa bakiyi ma Babansaba sai shi zan dinga bashi kar kidamu ki dai haifominshi kawai kingama naki,


"Nidai bana So, tafad'a kaman xatayi kuka,

Ya Kamo hanunta Cikin Happy "Zo muje inga lfyn baby na, bai tsaya ko ina ita ba, sai wani d'aki da aka sanya kayan Da suka shafi Asibiti, na'urorine kala2,


Ya sata ta hau Gadon Scaning, ya jawo na'uran ya Fuskanto mata da Screen d'in suna kallo dukansu,

Cike da tsantsan farin ciki yamata scanining sosai yayi mamakin cikin wai har ya kai 3 Monthns, ya jawota ya d'ora kanta a cinyansa, Yana shafa cikin, ta dafe Hanunsa, kaman xatayi kuka, "Likita Dan Allah....
"Menene Khadijah kar ki b'oyemin abunda ke ranki, fad'amin ko meye? Insha Allah zanmiki Baby na, banson ki dinga b'oyemin Komi naki,

"Mhhmm nidai banson ka fad'ama Mamine kaji,

"Ya xaro ido, "Khadijah inban fad'a ma Mami wannan abun farin cikinba ba mawa zan fad'a?

Kinsan tsawon lokacin da Mami ta d'auka tana jiran irin wannan lokacin?
A duk lokacin da Mami tamin maganan aure zanceta baya wuce insamu d'a ta samu jika, pls My Luv kibari insanar da ita, a k'alla zata tamakamana da Addu'a,
Ta mak'ale kafad'a "oh nidai kar karkafad'amata,

"Ok inbakison in fad'amata Zo kiji, yamata rad'a akunne, ya saketa ya tashi, ta harareshi ya kuma mata wani Rad'an a kunne, ta tashi da sauri ta suri Pillown dake kan gadon Tabishi dashi zata kwad'amasa ya bud'e k'ofa yafita da gudu ta rufa masa baya, Suka shiga kewaye gidan suna dariya,

*********

Washi gari Kabir yana xaune da System a gabanshi yana aiki, Khadijah tafito cikin shigan Shadda dark blue,Riga da sket ba k'aramin kyau tayiba k'amshi mai sanyi na tashi a jikinta, a hankali ta zago ta bayansa Tasa Hanunta ta Rufemasa ido, yad'anyi Zillo yana yarfe Hanu, yace "Wayyo My Luv Ga Dodo zai kamani yazo ya Rufemin ido kizo da gudu ki ceceni,

Me Khadijah zatayi inba dariyaba, ta tsuguna a wajen tanata k'yak'yatawa, yasa Hannayensa duka biyu ya jawota Gabansa yana Murmushi, Ashe ma Kece My Luv, nazaci Dodone,

Dariya takeyi harda k'ollah tace Likita Ashe kai matsoracine??

Dariyan yarantanta ya shigayi, Ya Rungumeta a k'irjinsa, Yana shak'an k'amshinta, "Da Gaske nazaci Dodone zai cinyemiki Miji, ya gyaramata zama a gefen cinyansa yana cigaba da aikinsa, yana janta da Hira jifa2 yana kallonta danba k'aramin burgeshi kwalliyantan yayiba,


Ta d'an langab'e ajikinsa, tace "Honey Dan Allah Ka kaini Gidan Aunty Binta, Cikin wani irin shork d'in jin Sunan da ta k'irashi dashi yayi Saurin d'ago kai ya kalleta, itakuma tayi Saurin b'oye Fuskanta A tsakanin kafad'ansa, tana Murmushi, Shima Murmushin yayi Ya maida kansa ga aikinsa, kusan 5Minut Dijah ta lek'o Fuskansa, "Kaji!!!,

Ya ture Systemam d'in gefe ya jawota suna fuskantan Juna,
"Banjiba Sai kin maimata abunda kika fad'a,
"Nace dan Allah kakaini Gidan Aunty Binta inason inganta inga Adanan,
"No ba wannaan d'in nakesonjiba, naji wani sabon Sunane da aka rad'amin Very nice & sweted,

Tace "nifa Doctor nace,
"Ok ashe bakison zuwa Gidan Aunty Binta,
"Inasofa Dan Allah kaji,
"Mhmnn to sake fad'a inji,
"Mnnnmm Honey fa nace, ta fad'a tana rufe ido,
"Ayyah My Beuty Bakishirya zuwaba inkinshirya kizo kisanarmin ya fad'a yana yunk'urin tashi ta rik'eshi,
"To ba nafad'a ba,
"So nake ki kalli cikin idona ki fad'a sai inyarda,
Ta saita cikin Idonsa tace "My Honey
Ya Huramata iska acikin idon yana k'yalk'yalewa da Dariya,
Ta kifa Fuskanta a k'irjinsa, tana kaimasa Duka, Saida yagama Dariyansa, yace tashi mutafi Luv Kin ci xuwan Gidan Aunty Binta dagananma har gidan Sauda, da Mami, ta tashi tana tsalen Murna. Ta d'auko Hijab.

************

"Gaskiya nidai Mama nagaji da wannan yawace2 zan koma gurin Mijina shi kad'aifa na baro, Wlh Inaji ajikina kaman wani abun yasameshi,

Kumafa kinaji d'azu yace yayi missing d'ina kullum da irin k'aryan da nake masa, na dalilin Rashin dawowana, anma wlh yau kasa cemasa komi nayi na'ajiye wayan inacewa banaijinsa,

Mamanta ta rik'e Hab'a cike da mamaki tace "Anma duk yawace2 da mukeyi ba dalilinkibane? Ko kinmanta cewa kikayi Kinason ki zauna dashi ke kad'ai ba tare da wataba? Ancemiki hakan zaiyiwune inba muntashi muntsayaba,

"Mama nifa nasan Kabir Wlh ba wata macen data isheshi kallo da har zai je niman aurenta dama damuwana wannan 'yar K'auyen kuma wacca ta yayimota ta mai da ita, Ayanxu banda sauran Matsala, dan Allah mukoma ina son Ganin Mijina,


"To shikenan Jibi sai Mukoma,

Shiru kawai Nafisa tayi cikin takaici dan ita kam Jibi yamata nisa, ba k'aramin shaukin mijinta takejiba, Sosai tayi Missing tattausan Fatansa da take kwana manne dashi, dan dai kawai ba yanda ta iyane,

***************

Dijah nagano Zaune Cikin Lilo Kabir yana Turata a hankali sai dariya sukeyi, kallo d'aya zaka musu ka karanci tsantsan So da k'aunan da yake tsakaninsu, jinsu suke cikin matsanancin Farin ciki,


Kabir ya xira hanunsa cikin Aljihun Wandonsa ya d'auko Wayansa da take verbratoin, "Dam! Yaji k'irjinsa ya buga ganin wacca take k'iransan, d'an kallon Dijah yayi da gefen ido yace mata yana zuwa ya gangara d'an nesa da ita yana d'aga wayan,


Binsa tayi da ido tanajin fad'uwan gaba musamman yanda taga jikinsa yayi sanyi tana kallon yanda yake maganan Fuskansa ba yabo ba fallasa, duk da bata jin abunda yake fad'a ko kad'an hakanan taji ba dad'i,


Ahankali ta zame daga cikin lilon tafara Tafiya, daf da zata shiga pert d'insa taji ya k'irata a sanyaye ta juyo tana maidamasa da Murmushin da yake mata, Sosai take son b'oye yanayin da ta tsinci kanta,

Da hanu ya mata Alama da ta dawo, ba musu ta dawo yana zaune a cikin lilon ya jawota ya zaunar da ita a saman cinyansa, yana juyasu a hankali, ya sako bakinsa dai dai kunneta, "Meyasa zaki gudu ki barni Luver?

Tad'anyi Murmushi "Ba guduwa zanyiba yama za'ayi ingudu inbar Honey na, ta ziro hanunta tana shafa sajensa, ya lunshe idonsa yana jin yanda wani abu ke masa yawo ajikinsa,


Ya d'agata ya kama Hanunta suka nufi sashinsa, makulli ya d'auka suka fito ta cikin wani k'ofa dake pert d'in, ya tsaya bakin sashinta ya bud'e k'ofan jiki ba k'wari suka shiga, Ya zube kan

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment