Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take shirin shiryamasa in ya dawo daga tafiyansa,



Da dare Kabir yana zaune afalon Mami suna Hira Habib yashigo da sallama Mami ce ta amsa cikin fara'a tanamasa Sannu gefe ya zauna suka gaisa, ya kalli Kabir da idonsa yake kan T.v yace Wai kai har yanzu baka canzaba? Yanzu dirowana garinfa nazo dubaka kana wani shanmin k'amshi,


Kabir ya harareahi yana tab'e baki, "tom ni nak'ira kane? Kona ce kazo ka dubani?

"kadai ji dashi gurgu kawai, yafad'a yana mai da dariyansa, ya mik'e yana kallon Mami da take musu dariya, "Mami yau me aka dafa agidannan?

Kabir ya manna bayansa da jikin kujera yanata murmushi, ta wutsiyan ido Habib yake kallonshi yana cin abinci.


Ikon Allah ne kawai yakai Alhaji ya'u gida dan baimasan irin tuk'in da yakeyi ba, ko gama perkin baiyiba ya bud'e murfin Motan ya fita a fallo ya tarar da Matarshi tana ganinsa ta mik'e cikin damuwa take tambayansa,

Ko sauraranta baiyiba ya ciro waya bugu d'aya kila ya d'auka,

"Kai Kila nagaji da rainin Hankalin da kakemin dama baka kashe Kabir ba kacemin ka kasheshi?,

"What? Meka ke nufi Alhaji? Kodan baka gama bamu kud'inmu bane yasa kafito tanan? Kamar yadda nagayamaka ai Kabir saidai uwarshi ta haifi wani, amma shikam yayi nisa,

Cikin zafi ya katseshi da kai kar kawomin maganan banza zanyi maganinka, daga Haka ya katse wayan, ya zube kan kujera,

Rabi ta k'araso tazauna gefensa tana tambayansa, nan ya gayamata komi,

Tad'an kalleshi to Alhaji ka kwantar da hankalinka mana kuyi magana na fahimta kai da Kilan wlh nikaina na matsu ayita ta k'are muci dukiya musha dukiya mu kwanta akan dukiya,


*Oh Allah Duniya budurwan Wawa Allah yasa mufi k'arfin zuk"atanmu*

Kar kugaji kubiyoni har yanzu ba afaraba,πŸ˜‚

*Ummu Fatima*

Comments /corection πŸ‘‡πŸ»
.08065091824.
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣2⃣



Batarufe Baki ba sukaga wasu k'arti sun kewayesu da bindigogi zata kurma ihu Kila yadaka mata tsawa,

"Yimana shiru Munafuka inkink'i yanzu infasa wannan k'aton kannaki,

Cikin takun isa da izza ya k'araso gaban Alhaji ya'u da yaransa suka kewayeshi da bindiga,

K'afansa yad'aga yad'ora akan cinyansa, yana kallon fuskansa "kace kasan maganina ko? To gani nazo kayi maganina gani agabanka,


Kai wlh kacika d'an Rainin wayo inmaka aiki ka k'i biyana? Sannan kanimi ka gayamin maganan banza?

Cikin zafi Alhaji ya'u yace "Nabaku kud'inku kad'anne yarage ba gana biyankuba, Amma aikai ka ha'inceni kasan baka kashe Kabir ba kazo kacemin ka kashe yanzu Haka daga gidansu nake, da idona naga Kabir haba wannan abu dame yayi kama? Shekara nawa ina farautan wannan yaro abu ya gagara kumama yanzu sai dana gama asaran dukiyata kafin ya b'ullo baziyuwaba!!! Yak'arasa maganan cikin k'araji yana taune Hak'ora,

Kila yarik'e hab'a yana ksllonsa cike da kamaki, "ya'u bansanka da shaye2 ba nadai san ka k'ware wajen son kud'i,

Anya ko dai kayi gamone?

Kabir d'in da na fatattakasu da bindiga shi da drevernsa Sannan a idona suka afka cikin k'atuwar Gada wlh ko akan laya yake kwana bai isa fitowa har yataka doron k'asa ba,

"Wlh dagaskene Kila uwarsafa bak'araman shu'uma bace yanzu haka wani tsatsubenta tayi masa kafin yafita me zai hana kuma kufara bin Bokaye kawai akashe shi da Magani, inji Rabi,

Shiru Kila yayi yana nazari tabbas ya yarda akwai sihiri acikin wannan lamari inba hakaba Kabir basu isa su tsiraba,

Alhaji ya'u ya mik'e yana zagawa a Falon cikin tashin hankali ya k'araso gaban Kila, "yau nine ka d'ibo yaranka zaku kasheni? Bismillah ku kasheni koma na huta fa wannan bak'in ciki, dai ga Nasara sai asamu fail!! Why??? Yak'arasa cikin shouting yana jijjiga Kila,

Rabi ta k'araso ta dafa kafad'ansa, "ka kwantar da Hankalinka Alhaji badai kace yasamu matsalan k'wal'walwaba? Aini inagama angama wannan, ta matso fa bakinta dai2 kunnen Kila ta mishi maganan da shikad'ai yaji, wani mahaukacin Dariya yayi yadafa kafad'an Alhaji ya'u "Dama kana da mace irin wannan agidanka kasamu muke tashan wahala? Bani 2 days, daga haka ya juya yaransa suka rufa masa Baya,

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Washi gari Kabir suna zaune a garden shi da Habib daSani mafi yawancin Hiran Su biyu ne sukeyi jifa jifa ne Kabir yake ansawa yafi maida hankalinsa kan Lap top d'in dake gabansa, Sani yana ta latsa wayansa cikin sa'a yasamu no. Da kusan Kullum sai yanima yajita akashe, harsaida yakusan tsinkewa kafin aia d'aga, bako sallama yace "waye?
"kai lro baka iya sallanaba, to Sani ne meyasa Kullum inna k'ira inji akashe?

"Ayyah Sani wlh kuwa inazuwa gona ne shiyasa nake kasheta in ajiye agida, dariya Sani yayi sosai sannan yace "to da Allah ka kaima Fatima wayan,

"to barin kaimata kuna lfy ko?
Ya Likita yak'ara ji da jiki?
"Alhamdulillah yanzu yatashi daga gurgu yadawo mai k'afa yafad'a yana dariya yana kallon Kabir da yanayinsa ya canza,

Cikin sanyin murya suka gaisa da Bintalo, sai janta da magana yakeyi tana sharewa, "ok tunda kin k'i muyi Hiran ba ma Khadijah mugaisa,

"Dijah bata da lfy tana kwance amman dai barin kaimata,

"Subhanallahi meya sameta?
"wlh wai ciwontane yatashi,

Asanyaye yake Amsa gaisuwan ta jin yanda Muryanta yake fita, yad'ago yana kallon Kabir da yake kallonsa bako k'iftawa,

Yace "to ga mutuminki barin bashi kugaisa, yakara masa wayan akunnensa,

Zuciyan Kabir sai bugawa yakeyi da sauri2 amon Muryanta nazagawa duk sassan jikinsa, Hello kalman da take ta fad'a kenan,

Dak'ya ya iya cewa ke kincikamin kunne da Allah kiibawa Fatima wayan, shiri yaji tayi sai sautin numfashinta da yake fita ahankali,

Sani yacire wayan a kunnensa yana magana jin baiji amsabane yasahi ya kashe, Habib kam saibin Kabir da Ido yakeyi yana son fahimtan wani abu,

Kusan minti biyar gurin yayi shiru can Kabir yace ma Sani wai waye Ba lfyn?

"Khadijah yabashi amsa tak'aice, shiru yayi sannan yace "Wai meyasa meta?

"gaskiya ban saniba,
"k'iramin lron kace yaba ma Fatima muyi magana, cikin sa'a da yak'ira Bintalo ce ta d'auka ya mik'amasa,

"Hello mamata kina lfy?
"lfy Likita ya Mamo?
"lfynta k'alau wai tun yaushene yarinyannan bata da lfy?

"takai Sati akwance,
"Ankaita Asibitine?
"Eh, shiru yad'anyi ya sauk'e ajiyan zuciya,

"ciwontannane? Ko wani abunne?

"Eh naji Baffah yana cewa wai ciwon tane,

Cire wayan akunnensa yayi batare da yakuma cewa komiba, ya mik'a ma Sani yacigaba da opreting system d'in dayake gabansa,

Cike da zolaya Habib yace "Gurgun birni wai waye ba lfy naga duk kawani diririce, Anyah kuwa Gurgu baka shiga tarkon *Dijah k'aya* ba kuwa?

Afusace Kabir yad'ago yana masa wulak'anceccen kallo, "Look Malam kar kagayamin maganan banza kanaji?

"Sory man meye maganan banzan? Dan nace ka kamu da soyyayan Khadijah sauran muje musha biki kawai,

"God for bit ko kamanta he is my petient, daga Haka ya mik'e ya tafi don ua lura inyaci gaba da zama agun zasu b'ata masa rai don yanaga ko mata sunk'are badai Dijah bakam.


Yana dab da k'ofan Falo ya cikaro da Nafisa, wani wawan tsalle ta daka zata hau jikinsa yayi ta maza ya kauce ya bata guri da wowa tayi tana k'ok'arin mannewa ajikinsa yana nunata da yatsa, "hey stop! Haba Nafisa yaushe zakiyi hankaline? Swagwb'ewa tayi kaman zayayi kuka haba Kb kabarni inyi murna na watanni nawa rabon da inganka? Kaga halin danashiga na rashinka?

D'azu nadawo kawai naji su Dady da Mamanmu suna magananka duk da ban gane me suke cewaba na fahimci ansamu lbrnkane, shine nazo inji awajen Mami yanzu takece min wai kadawo kana gaden,
Ganin bazata gama surutunba ane yasashi bin ta gefenta ya wuce ya shige ta rufa masa baya sukaje suka k'arasa agaban Mami,
Washi gari yakama Ranan Asabar aran ne kuma zasuyi tafiyansu aggagauce ya shiga kasuwa ya sayi magun gunan Khadija ya dawo yaba ma Sani yace lallai yakaimata ayau Don yak'ira Baffa jiya ya mishi bayanin jikinta nan sukayi sallama shikuma ya wuce air pot, misalin 12:00 na Rana, jirginsu Kb ya d'aga zuwa England sai muce ayi seminer lfy,

Bayan tafiyan kabir da kwana biyu akasa bukin Bintalo da Sani sati biyu cif akasa,


Muje zuwa......


*Ummu Fatima ce* 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬

*Jinjina Gareku My Fans wlh inajin dad'in Addu'o'inku gareni ba kad'anba Allah yabarmu tare*

*Don Allah inkuji wani kuskure kumin gyara k'ofa abud'e take zaman tare kenan in d'an'iwanka yai ba daidaiba ka guaramsa, Nagode sosai,* 🀝🏻🀝🏻🀝🏻🀝🏻🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣3⃣




Dijah! Wai gashi inji Baffa ki k'arasa shan maganinki,

Dijah da take kwance akan k'atuwar katifan da ta gada awajen Kb πŸ˜† yitayi kaman batajiba, dataga Bintalo zata matsamata sai ta d'aga k'afanta kaman irin agigin Baccinnan ta d'oramata awuyanta,


Bintalo ta ture k'afan, Dijah tasake d'agawa ta d'oramata akanta,

Afusace ta saiti cinyanta ta d'akamta duka "iyi kinga kin fara farfafad'owa Rashin mutuncinki yafara dawowa aifa banmanta abun da kikamin d'azuba.

Azabure Dijah ta tashi tana sosa wajen, ta tak'ark'are ta k'walla uban k'ara,
"Wlh bazan yardaba sai na rama tana kuka takama Bintalo da kokuwa,

Nanfa kokuwa ya kaure, tun Bintalo tanabiyemata ta maida abun wasa har ta gaji tafara Bata hak'uri,

"Kiyi Hak'uri Dijah na kinga baki gama warkewaba, "Nidai sai na Rama ko kuma inje ince ma Baffah jiya naji kuna iskanci a waya keda yaya Sani.

"wai ke Dijah meyake damunkine? Don kawai nace nima inasonshi shine iskancin?

"A'uzubillahi sake maimaitawa kikayi? 😳 narantse sai nafad'a tunma bakije birninba kin fara iskanci, ta fauce Hanunta acikin na Bintalo zata tafi Bintalo ta rik'ota kiyi Hak'uri Dijah ki rama dukan ince shikenan, "nafasa Ramawa zanje kawai ingayama Inna kar akaiki Birni kije ki kwaso abun kunya.

Dariya Bintalo tayi sosai har tana sunkuyawa, kije kifad'a nima sai nafad'amata Hiran da naji kunayi keda Jebu jiya, daga Haka tafice tabarta agun.

Gyara kwanciya Dijah tayi akan katifa ta d'ora kanta akan pillow tana shak'an k'amshin turaren Kb dayazamo mata jiki, Don tun tafiyan su Kabir tamayar da d'akin wajen zamanta kwanane kawai batayi a wajen k'anshin turaren da yake fesawa har yanzu yana d'akin kaman yanzu ake fesawa itakuma a duniya k'amshin yana mata dad'i.


Tun ana biki saura kwana Biyar Mami sukazo da kayan sayan baki dakuma d'inkunan da Amarya zata saka dasuran abun buk'ata kafin akaita, don dama Baffa yace a ajiye mata lefenta acan tunda nan za'a kawota.


Tun Randa Mami ta dirk'o take fafatawa da Baffa akan yabata Dijah sutafi fir yak'i amincewa.

Suna zaune da Dijah tana nunamata sakamakon Karatunta tafara wani tunani itadai tanason yarinyan aranta, tanason ta taimaka mata tasamu karatu mai inganci, "khadijah kinason kicigaba da karatunki?

Dijah ta d'ago tana kallonta, tace "Eh inason incigaba Hajiya wlh inason in zamo mai aiki gidan T.v Mami tad'anyi Murmushi tace nifa Mamin kece ba Hajiyaba, kinji?

Ta gyd'a kai,
"Kinason intafi dake kije kiyi karatunki acan?

Dijah tazaro ido "Eh inaso amma Baffana bazai yardaba, "Karkidamu nasan Hanyan dazanbi lnsha Allah zai yarda dake za'azo bikin Fatima kinji?

Kayan da tazomata dasu ta bata sannan ta nunamata yanda zatayi amafani da wasu.

Washi gari Mami da zata tafi tashiga wajen Baffa tajima kafin tafito jiki ba k'wari, Dijah tana ganin haka tasan Baffanta bai aminceba.

Ahaka tamusu sallama Har jikin mota suka rakata tafi.


*Ranan Juma'a* shine Ranan da Baffa yasaka d'aurin auren Bintalo awannan Rana mutanen Rugan Juma sunga Abun Mamaki dayawa wasu kam sun sadauk'ar cewa Baffa yasayar da "yarsa mai Hankali yabar Mashiririciya agida sakamakon Irin Motocin dasuka shigo garin wanda tsawon Rayuwansu da yawansu idonsu bai tab'a Ganinsuba, gasu fa tsaban yawa nanfa akafara gutsiri tsoma hatta matan dasuke cikin Gida lbr yakaimusu haka wasu sukazo sunayima Bintalo kallon k'arshe kallon muhad'u a darussalam, wasu sai lbrai sukeyi wata wani yazo daga birni ya kashe kud'i mai yawa ya aureta asai ba'asanta d'an yankan kaibane ana kaitan shikena haryau shekaru kaza ba lbr.

Ire2 labarun da akeyi kenan agidan bukin wannan tanagamawa wancan taba dana ta, Inna kam yitayi kaman batasan me suke nufiba dondama tasan za'afad'i abunda yafi haka.


Hakadai har 'yan kai Amarya sukafara shiga motoci, nanma ba kowa bace tayarda tashiga don sunce basu shirya kai kayikansu ma 'yan Birniba.

Sai Daf Magriba suka isa Gidan Mami aka kaisu kai tsaye, wani k'aton pat aka ajiye Amarya da Bak'inta, Hidiman da aka musu ba'a magana, Mami tana idar da Sallahn Magriba ta shiga pert d'in Bintalo tana ganinta ta lullub'e fiska dariya tayi tace kwantar da Hankalinki Amarya ba gunki nazoba nazo niman 'yatace, tazauna agefe suka gaisa da jama'a annantace musu Ina Khadijah? Can ta hangota suna zaune dasu Ma'u Taje ta kamo Hanunta suka fita, bata ajiyeta ko inaba sai part d'inta,

Wani d'aki dayake cikin Falon k'asa ta kaita da alamu kayan ciki basufi sati dasawaba komi sabone dal ad'akin abakin k'ayataccen gadon dayasha gyara ta zaunar da ita,

Ta jawo stool d'in Mirrow ta zauna tana fuskantan ta.

"Haba Khadijah uwata!! Kinzo konimana bakiba kinacan cikin 'yan'uwanki kin shareni nikuma inannan ina d'okin ganinki,

Murmushi Dijah tayi tana bin d'akin da kallo zuciyanta sai Harbawa yakeyi da sauri2 Haka kawai yau kuma taji wani iri game da Mamin Anyah kuwa Maganan mutanen garinsu bazai tabbataba irin wannan Gida? Ashe haka suke rayuwa shine har suke iya zuwa Rugansu suna zama.

Gaskiya itama yaukam tana ganin sayar dasu za'ayi dukansu,

Mami ta kamo hanunta kaman tasan abun da take tunani tace "ki kwantar da Hankalinki Khadijah Bazamu tab'a cutar dakuba insha Allah.

kusa aranku kowa da yanda Allah ya tsaramasa Rayuwansa wannan shine banbancinmu daku ba wani abuba, kinji ko?

Dijah ta gyad'a kanta tana cigaba da kallon d'akin a tsorace Mami tace ina zuwa ta fita Dijah ta tashi tana k'are ma d'akin kallo ahankali tana taku, har ta iso gaban Mirrow ta lek'a azatonta taga fuskanta sai kawai taga wata matashiya atsaye ta hard'e Hanunta tana kallonta gefenta kuma watace atsaye amma bata ganin fuskanta, arazane tasa tafin hannayenta ta Rufe Fuskanta ta tsala ihu mai tsanani da sauri Mami da sauda sukayo kanta Mami ta rik'ota "Khadijah menene?

"wayyo Allah na don Allah amaidani wajen Baffana wlh bazan sakeba Don Allah ku maidani,

"wai meye kimin bayanimana khadija??

Aljanu nagani acikin Madubi don Allah kukaini Baffa yamin Ruk'iya.


Mami ta dad'a rik'e Hanunta "ba Aljanu kika ganiba Khadija mune,

"wlh banyardaba waima kud'in ta ina kuka shigo waiyo na shiga ukuna.

Duk maganan da takeyi idonta arufe takeyinsa cikin kuka,

Sauda ko me zatayi inba dariyaba,

Dak'yar Mami ta shawo kan Dijah har ta yarda ta bud'e idonta, "Munshigo munsamu kina kallon d'kinki Khadijah shiyasa muka tsaya muna kallonki, Mu kika gani a madubin ba Aljanuba kinga wannan tanumata Sauda ita kikagani a mdubin ko ba itaba?

"itace to amma ta ina kuka shigo?

"ta k'ofa muka shigo Khadijah ki kwantar da hanakalinki,

Nan d'akinkine ke kad'anki na kawomiki k'anwanki ta gwada miki yanda zakiyi wasu abubuwane, kallon sama da k'asa tayima Sauda sannan ta kalli Mami "Wannan gundu memiyance k'anwata?

"Af Addanki ce na manta, Sauda ki nunamata yanda zatayi amfani da bayan gidan tayi wanka ga kayanta akan gado intafito tasa sai kuzo muci Abinci, daga Haka ta juya ta fita.

Sauda tana Murmushi tace "zomuje Beutiful girl kina da kyau Amma don Allah karkisake yin irin wannan k'aran daga gani kinsaba da shine ko? Kanta ta girgiza har yanzu atsorace take cikin 'yan mintuna kad'an, sai ga Dijah ta koma Khadijah tare suka fito suka tarar da Mami akan Dinining suna waya da Kabir,

*Kuyi hak'uri Fans bayawa wlh inacikin damuwa pls pray for me* πŸ™πŸΌπŸ˜­
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬

*Masoya masu k'irana sumin Addu'a da masu min massage na gode sosai kuma Allah ya biya muku Buk'atunku na Alkhairi nagode sosai Ummu Fatima taku ce* 🀝🏻🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣5⃣



Sauda ta jawo mata kujera ta zauna tafara saving nasu, sai da tagama zuba na kowa ta zauna dai2 lokacin Mami ta gama wayan ta kalli Dijah ta ke takure acikin kujera "Kici Abinci Khadijah, nanfa gidankine kidaina d'ari2,


Haka suka ci Abinci Mami tana musu Hira jifa2 takansako Dijah aciki dak'yar tad'an saki jikinta,


Rana ta farko arayuwan Dijah data kwanta dasunan Barcin dare ad'aki ita d'aya gaba d'aya jitayi d'akin yamata mugun girma Allah sarki Bintalona ta fad'a tana share guntun Hawayen da yagangaromata, juyi ta dinga yi ahaka har bacci yayi gaba da ita.


Washi gari akaci gaba da shagalin buki yayinda Mami tad'auko masu Gyaran Amarya nagaske duk abunda akyi wa Amarya Mami tasa anyima Dijah,

Kafin yamma inkinga Amarya da k'anwanta bazaki ganesuba gaba d'aya kamanninsu ya canza, aharaban Gidan aka gudanar da tsararren Walima daya d'ibi maza da Mata,

Angoda da Amarya sai Haska waje suke kaman wasu taurari, sai daf Magriba aka tashi,

Duk abunda akeyi Dijah tana takure akan kujera dama ita ba gwanan shiga taroba, gawani Kwalliya da akamata gaba d'aya tana jin fuskanta yamata nauyi, tun daga nisa tajiyo Muryan sani yana k'wala mata k'ira ta tashi ta isoshi sai Kallonta yakeyi yana murmushi "Khadijah kece haka gaba d'aya banganekiba? Murmushi kawai tayi tace " ya Sani kaima ka ganka kuwa da muryanka kawai naganeka,

Kai da Bintalo sai kace ansakemu ku wani k'ira. Sani yad'an had'e rai "ke Daga yau nasoke wannan Sunan Aunty Fatima zaki dinga cewa ba Auntynki bace ba,

Dijah ta k'yalk'yale da Dariya "ok dariya ma nabaki? Insake jin sunan abakinki,




Zo muje kigaisa da su Hajiyata, yana tafe tana binshi abaya suka shiga pert d'i n da 'yan'uwansa suke, sosai Hajiya taja Dijah ajiki, tajima awurin suna Hira,

Harsaida Mami tanimeta.

Bayan Walima ba abunda aka kumayi awajen don Mami tace Albarka ake nima baza'ayi abunda yasab'a ma shari'a ba,

Sai washi gari aka kai Amarya gidanta tare da Rakiyan 'yan'uwata, Bakaramin kokari Mami tayiba

Wajen tsara gidan Amarya komi yaji saidai fatan Allah yaba da zaman lfy,

Washi garin kai Amarya ne 'yan'uwanta da 'yan'uwa Ango sukayi shirin komawa Garinsu, lokacin dasukazo tafiya and'an fafata da Dijah don tace sam Baffanta bai Amince ta zaunaba,

Harsai da Mami ta k'irashi awaya aka bata yace mata ta kwantar da Hankalinta zai zo ganin d'akin Amarya daganan sai su dawo tare (kamar yanda yake a Al'adan garunsu bayan Amarya tacika Sati BabπŸ™πŸΌπŸ˜­
anta yakanje ganin d'aki,)

Da kad'an kad'an Dijah tasaki jikinta da Mami sosai yanzu take jin dad'inzaman gidan haka tafannin abubuwa Sauda tana koyamata Sosai, tare suke shiga kicin da Mami suyi Abinci kasancewan dama Dijah bata da son jiki shiyasa ta dage kafin tacika wata uku ahanun Mami tuni ta goge ta iya abubuwa da dama, time to time takanbi Sauda suje gidansu nanma bak'aramin Experians take samuba, Mahaifiyar sauda tana bata kulawa sosai don haka tazamo bata da matsala


Dijah tana da wata Hud'u cif Mami tasamamata gurbiny karatu a Polytechnic,

Ita da kanta tad'auketa a mota takaita har cikin makaranta wajen Aminiyanta da take koyarwa a wajen takaita Malama Sadiya, a Office tasameta ta tareta da fara'a suka gaisa,

''yau wata Rana Hajiya Fati kece a Office d'ina?

Gaskiya baki da kirki gaba d'aya kingujeni,

Mami tayi dariya tace "yanzumma bahaka kawai nazoba nakawo miki Amanar 'yatace, gatanan tana nan Depertmen d'in Mass communication,

Malama Sadiya ta kalli inda Dijah take "Masha Allah Hajiya Fati 'yar waye?

"yatace pls don Allah inaso asamata Ido kinga Bak'uwace batasan kowaba kar abarta da k'awayen Banza,


"Ok bakomi akwai 'yata Nana zanhad'asu surik'a zama tare,

To nagode Mami ta fad'a tana mik'ewa dukansu tare suka fito suka tsaya ajikin Motan Mami,

Malama Sadiya tak'ira wayan 'yarta, ba'a jimaba sai gata tazo wajen, kallo d'aya tayi ma Dijah tahau yatsina fuska saidai tagai da Mami cikin girmamawa,

Nan mahaifiyarta tagabatar mata da Dijah amatsayin Sabuwar k'awa sannan ta gargad'eta da kar tabarta tayi k'awance da wasu shashashun k'awaye,


Mami tadafa kan Dijah tace "Khadijah kikula kinji? Kiyi abunda yakawoki, inkuntashi Driver zaizo ya d'aukeki akwai no. sa awayanki sai kik'irashi, cikin girmamawa tace mata "to"


Nana tana gaba Dijah tana baya ahaka suka isa ajin,

Nana tak'arasa wajen K'awayenta tad'an sukuya ta musu magana akunne gaba d'aya suka kwashe da dariya suna kallon Dijah suna nunata da yatsa,

Wani irin malolon bak'in cikine ya ziyarci Dijah.


*pls Karku manta dani cikin Addu'o'inku inkayi ma d'an'uwanka musulmi Addu'a mala'iku zasu maka kutaimaka 'yan'uwana*


*Nagode Nagode Nagode*πŸ™πŸΌ



Mmn temah 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment