Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batace komiba,
Mami tace "tashi kije zanzo insameki, sannan ta kalli Kabir "Meyasa ne Kakeson canza Hali Kabir daga yanda nasanka zuwa wani daban, Naji Nafisa k'anwar kace kana da daman hukuntata, anma inaga abun baikai har da Mari ba,


Murya asanyaye yace "I'am Sory Mami anma inason ta maimaita duk abunda ta fad'a min da bakinta inaga ta cancanci abinda yafi mari awurina, dan niba sa'anta bane, da Harara ya kalleta "ki maimaita abunda kika gayamin kalma d'aya inkika canza sai nafasa miki baki, atsorace ta maimaita muryanta na sark'ewa,

Mami ta jinjina kai "anma da bahaka kika fad'aminba Nafisa komi zakayi kayi gaskiya, rashin gaskiyan bayi da Amfani, nan tayi ta musu fad'a da Nasiha,
mik'ewa Nafisa tayi tace ma Mami zata gidansu, "adawo lfy ta mata ta rakata da ido sannan ta kalli Kabir

"Anyah Kabir haka zakuje kunayi da Nafisa agidan aurenku, sam kai baka iya rarrashi ba, haka zakuje kana mata abu kad'an ta d'ibi jiki tayi gida kaikuma kana kallo, gaskiya da sake zama da mace sai da hikima,

Kabir ya had'e rai "Mami wlh nifa na fara tunanima akan aurennan wlh na lura har yanzu rashin kunyanta na nan,

Mami ta zaro ido "karma ka fara Kabir ko da wasa sai da komi ya kankama zaka tsiro wani abun, ko kamanta nan shekaranjiya muka fafata akan wannan Engagement d'in naku, Nace ku barshi fir kabi bayanta cewa anriga angama tsara komi, kadinga ban baki, shine yanzu zakace mene
to ahir d'inka kar kajangolomin abunda yafi k'arfina, tashi tayi ta nufi d'akin Khadijah shikuma yafita rai ajagule,


Da Daddare Kabir yana zaune ak'asa a falonsa ldonsa na kan T. V amma sam zuciyansa tana can wani wajen Nocking yaji anayi, Nana ya bada izinin shigowa, hakanan ya tsinci zuciyansa, da fad'in Allah yasa Khadijah ce, dan ko ba komi zai d'an rage zafi, idonsa k'yam akan k'ofan ta tura ta shigo da sauri ya janye idonsa yana k'ara muturk'ewa, ahankali kaman wanda k'wai ya fashewa aciki, ta zauna daf dashi kaman zata shige jikinsa,


Ganin ko kallonta baiyibane yasa ta d'an fara shsshek'an Kuka tana kallonsa zuciyanta sai harbawa yakeyi tana tunani wannan karonkan inta rasashi, Mutuwa zatayi, sai dai inta tuno da maganganun Mamanta sai tasamu releif, "Ya Kabir dan Allah kayi hak'uri da abunda na maka d'azu, sharrin shaid'an ne da tsananin sonka, na tuba bazan sakeba tafad'a tana fashewa da matsanancin kukan Makircin da aka training d'inta akai, tun yana sharewa har yaji kukan ya isheshi danshi sam baya son yaga ana kuka, d'an kallonta yayi sai rok'o da Magiya take masa,

"is ok Nafisa har ga Allah kin b'atamin Rai sosai dan nasha jan Kunnenki akan yarinyan nan anma baki ji, Inkin cigaba da shiga sabgan Khadijah kece da wahala, dan nalura da yarinyan wata irin mutumce da Nasara ajininta yake, dan haka rabuwa da ita shiyafi, sannan babu wani abunda zakiyi ma Khadijah ta hak'ura tabarki, inbaki Mantaba kekikafara Marinta Ranan, nahanata ramawa dama nasani wannan Marin akwai ranan biyansa, kinmata d'aya ta mimi biyu, ahakanmafa Khadijah tayi sanyine Girma na canzata inda dane baki ma isa kifaraba, dan zata miki shirmen da bazaki iya dashiba,

So Maganinta kawai shine kifita hanyanta, i know her, inbaki shiga sabganataba, bazata shiga Nakiba, Amma ke baki gane hakanba, na miki magana kuma kin tashi zaki min rashin Kunya,

"wlh Nagane kurena Bazan sakeba dan Allah ka yafemin kaji? Ta fad'a araunane, ajiyan zuciya yayi, "Shikena is not my cornsen, inkinsakema nawa ido bazaki sha da itaba dai i'm talling u, anma ni karkisakemun haka agaban freinds d'ina dan ni abun kunyane a wurina,

Haka taci gaba da masa kissa da kisisina, har ya sauk'o, suka fara Hira ta d'an shagwab'e "pls dear Muje inkarb'o gawn d'ina da zansa Gobe, kuma dan Allah cake d'in pertyn nan kasa Khadijahn gobe ta karb'omana Allah daga yanzu na daina fad'a da ita, dama kishinka nakeyi dan sai inga kaman kana sonta,


Tab'e baki yayi "kibari sai Gobe duka sai akarb'o yanzu dare yayi, kima tashi kije ki kwanta, sai da tagama iyayinta kafin ta tashi,


Washi gari Dijah tagama shirinta tsaf tace ma Mami zataje Gidan Bintalo kallonta Mami tayi na d'an lokaci, kwanan nan tana ganin damuwa afuskanta, sai dai tayi ta tambayanta saidai tace Babu, cikin zolaya tace "Guduwa zakiyi Khadijah bazaki tsaya ayi hidiman dakeba, ko kina kishine? Turo baki tayi "Mami nidai ba ruwana dasu dukansu dan Allah kibarni inje,

Dariya tayi tace to shikenan Khadijahta, saidai sun d'auramiki wani abunda bansan daliliba, wai kikarb'o musu cake wai ko batananne kuma zasu tashi kafin ta dawone oho nidai banma ganeba, kidaije drever yakaiki yasan da maganan, Sam hakanan Khadijah taji aranta da akwai wani makircin da aka k'ulla anma saboda Mami tafi k'arfin ta aiketa ta mata tawaye yasa ta amsa badon ta soba, saidai tasa aranta koma meye tana dai2 dasu, dan haka ta tafi, sai dai abunda yabata mamaki shine wai ba'amayi cake d'inba inji matan wai tazauna ta jira, wani d'aki ta kaita ta zauna wasa2 har akayi la'asar lokacin gidan Mami yacika da 'yan perty angama decoration wajen kafin Matan ta kawo mata haka Dijah ta dawo acike dam kaman zata fashe dan takaici,


Nanfa akafara gudanar da Hidiman, Kb d Nafisa suna cikin shiga ta Alfarma, cikin fararen kaya sol kaman dai yanda yahudawan keyi 😁

Yau Ranace mai matikar muhimmanci agun Nafisa Ranan Farin ciki.

Bayan angudanar da matakin farko da akeyi a wajen irin wannan bikin abu nagaba shine yankan cake
Shi yafara yanka cake d'in dai2 wajen sunanta yasamata abaki itama ta yanko dai2 Sunansa tasa masa a baki, nan gurin ya kaure da tafi raf raf, sannan akaci gaba gudanar da abubuwa cikin Farin ciki, sai dai a b'angaren Kb yana cikin wani Hali tun bayan cin cake d'insa da kaman minti10 yaji wani abu na tasowa tundaga tafin k'afansa har cikin k'ok'olwansa,


Tin yana daurewa yana jin abun sama2 har abun ya faskara, can dai ya yunk'ura ya tashi ya d'auki excuse da k'yar yana karad'a hanya ya fita awajen pert d'in Mami ya nufa saidai kafin yakai ya yanki jiki ya fad'i awajen kumfa na fita ta bakinsa,


😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


*Ummu Fatima ce*
[7/23, 9:55 PM] β€ͺ+234 806 450 9198‬: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š

*Abunda yake ban Mamaki shine kusan Kullum sai nasamu mutum kusan goma koma sama da haka, a prvt wai inbasu Dijah Qaya daga farko, shin wai da kun makarane baku bin buk d'in sai yanzu kome?* πŸ€”

*pls wlh abun da Wahala my sisters kumin uzuri sanan akawai wa'inda suke min complain wai yanzu buk d'in baya zuwan musu, bansan meke faruwaba,?* πŸ€”

*Komasu tura musune suka gaji oho, pls fans ku taimaka kucigaba da tura musu* πŸ™πŸΌ


4⃣6⃣


Dai2 Lokacin Dijah ta fito cikin shirinta na fita dan bazata iya jure jin wannan kid'aba kaman zai d'aga Gidan, wani tuk'uk'in bak'in ciki takeji, Hakanan ta tsinci kanta da jin haushin kowa na Gidan, dan haka ta yanke a ranta intaje gidan Bintalo sai gobe ta dawo,


Tayi kwanan Fita kenan tayi karo da Kb kwance agun, atsorace ta durk'usa tana lek'a fuskansa dantasan ba lfy ba zai yasu awajen,

idonsa abud'e suke tarwal sai dai sun canza kala sun dawo yellow, ga kuma kumfa na fita abakinsa, Wani razananne k'ara tasake tana Jijjgashi Likita!! Likita!!! Ganin kansa kawai yake juyawa yasa takoma ciki aguje ta tarar da Mami agaban Mirrow tana make up,


Cikin Kuka ta rik'o Hanunta tana fad'in "Mami Likita zai Mutu, zai Mutu Mami gashi can akwance ak'asa,

*Innalillahi wa inna ilaihirraji'un* Mami take ta maimaitawa tana sa kaya cikin sauri, kusan atare suka jero da Dijah Gudu2 suka fito, Tuni Har Sani da Habib dasuka biyo bayanshi ganin yanayinsa, sun sashi a Mota, suna shirin fita Mami ta k'arasa jikin Motanta ko takan dariver da Dijah da take biye da ita, batayiba, ta rufa musu baya, saidai duk gudunta saida suka shiga Asibitin har suka shiga dashi d'akin gaggawa kafin tayi perking, tafito, Daga can ta hango Sani tsaye nan tagane d'akin aka shigar dashi, Addu'o'in da take ta karantawane yasata Samun nitsuwa,

cikin takun ta na Kamala ta iso wajen, da sauri Sani ya mik'o mata kujera ta zauna tana kallonsa, "Sani meke faruwane kam? Kansa na k'asa yarasa ta inda zai fara, sai kame2 yakeyi,

Kallonsa kawai tayi bata kuma cewa komiba, xuciyanta na ci gaba da harbawa, Har Habib da Dr Na'im suka fito, kai tsaye gun Mamin suka nufo, suka gaidata, nan take tambaynsu matsalansa,

Habib ya tsuguna daf da ita, cikin sanyi ya fara mata bayani "Mami poising yaci, kuma abinciken likitoci ya nuna poising d'in shine abunda yaci na k'arshe, sai dai ni abunda yaban Mamaki shine asanina dai Cake d'in Engagement d'insu shine abunda yaci nak'arshe,
Kuma tare sukaci da Nafisa, anma ita ba abunda yasameta, Anma yanzu na tura azo da cake d'in dan abincika, na kuma yi waya na sanar dasu Dady wanan karonkam duk wanda yake da hanu wlh sai ya fuskanci Hukunci, Mungaji da wannan al'amar. Yagad'a cikin b'acin rai.

Shiru Mami tayi tana Nazari na lokaci, sannan ta sauk'e ajiyan zuciya, "to yanzu dai ya yake?
"Anmasa Alurai har yayi aman sa, dake Allah ya tak'aita bai cii da yawaba, kuma bai jima ajikinsaba,

"To Allah yabashi lfy Mami ta fad'a tana jingina bayanta da jikin Kujeran, yace "Amen ya tashi yana barin gurin,

Motocine kusan guda Uku suka shigo Asibitin, tun ba agama perkingaba, Nafisa ta b'alla murfin Motan ta fito cikin tashin Hankali, tanufo inda ta hango Mami, kallo d'aya Mami ta mata ta kalli seceurityn dake wajan tace kadakatar da wancan tawagan kar kabar wani ya iso nan gaba d'ayansu, bama san hayaniya, da sauri ya isa dan cika Umurni,

Nan Nafisa tace bata iya jiba, dan ita Matarsa ce, sai da yamata jan ido tukun ta koma hefe tana kuka tak'ira Mamnta tasanar da ita

A fusace Maman ta ce "yana Asibiti fa kikace, "tace Eh Mama anma ai ba poising mukace abamuba meyasa zai mana haka?

Yanzu Mama me zance da Mami? Bani da bakin kare kaina Mama, a fusace Maman tace "ke kam ina Ruwanki? Ince dai ita wannan yarinyance ta karb'o cake d'in? To kizuba ido kiga yanda komi zai gudana ni nagama shirya komi, duk da ba lbrn danaso ji bakenan,

cikin Kuka Nafisa tace "Mama kina nufin da saninki aka samasa poising? Wlh in Kabir ya mutu sai na fallasa ki, kuma wlh sai na kashe kaina bazan iya Rayuwa ba Kabirba, wlh bakimin Adalciba, kin cutar da Mutumin da nakeso fiye da raina, tana fad'in haka tayi jifa da wayan tana cigaba da kuka,

"Helo Helo Nafisa Alhaji ya'u ne yafauce wayan ahanun Mamantan yana Huci, "ke wata iriyar mara hankaline? ya zakice mata Kina sane poinsing kika bata tasa, shin bakisan irin son da take masa bane? Wlh inna rasa yata bazan barkiba, kuma sai na tura Asibitin an kashe Kabir, koda me zai faru, saidai in har Nafisa ta salwantar da kanta kema kiyi kuka da kanki, ya sake wayan ak'asa, yafice a fusace.


Mami ce tsaye akan Kabir da yake Bacci tana kallon yanda yake fitar da Numfashi, Sai danne zuciyanta take ga abin da take sak'amata, a fili tace Manzon Allah S. W. A, yace zato zunubine koda ya kasance Gaskiya, ya Allah kaciremin wannan zargi da nakeyi azuciyana dan banida yak'ini akai duk da naga makamancin Hakan da idona, sai dai wannan d'in banda masaniya akai, Kabir Allah yaga wanda yamaka wannan Abun shi zaibi maka kadi,

Tabbas da ace d'an Adam na hana wani abu yasamu bawa da hakan bai samekaba, dan nasaka jami'an tsaro sosai ciki da waje dan baka kariya sai dai, abunda nake tsoron bashi ya samekaba, kaima danaka Kabir wasu lokuta da dama kana da sakaci da Addu'a, inba inayi ina tunatar da kaiba,

Ya Allah ka kawomana d'auki tafad'a araunane,

Ahaka aka turo k'ofan aka shigo Uncle Musa ne da Abban Habib da iya,

kujera Mami ta jawo ma lya ta zauna tana kallon Kabir, ta fashe da kuka tana fad'in

"Anyah wannan yaro Me yatsare ma Mutane ne kam? Fatima kumin bayani wai ame akasa masa guban? Nakasa fahimta,

"Acikin abunsu na shirmen lya, Mamin tabata Amsa atak'aice, "aciki akasa masa?, Uncle Musa ya amsa da cewa,

"lya abu guda sukaci shida 'yar gidan ya'u anma ita ba abunda yasameta, hankali zai d'auki wannan abun?

Hab'a iya tarik'e da Mamaki, tace "abu d'aya?, kuma itama taci? "k'warai kuwa cake d'in yana asibitinnan anbincika a iya gaban Kabir d'in kawai akasa guban ita gabanta babu, Inji Abban Habib, yad'ora dacewa nayi magana da sas zasu gobe dole yarinyan tamana bayani waye yayi cake d'in? daga ina cake d'in yafito? Nan ne zamu samu daman kama duk wani mai hanu a kan Kabir, dan na lura inmunyi sakaci zamu wayi gari wataran sun cika Mummunan burinsu akansa, insha Allah daga wannan asirinsu ya tonu,

"Kun min dai2 iya tafad'a, tana sharan k'ollah,

Mami ta kallesu, "to anma inaga da anbari akaga yanayin sauk'in jikin nasa da binciken zaifi tafiya, dai2 lokacin Kabir yad'an motsa duka sukayi kanshi, a hankali ya bud'e Idonsa yana kallonsu d'aya bayan d'aya sai sannu suke jeromasa, dakai kawai yake Amsawa, ahaka Likita yashigo ya k'ara dubashi, sanann ya fita su Uncle Musa suka bi bayansa,

Mami tace "lya Ya Khadijah na? ina nan inata Tunaninta, lya ta rik'e Hab'a aidama inason inmiki Magananta, Indai anan zaki kwana to sai dai akawomiki ita, danni har tsoro tabani kinga kukan da tayi bayan tahowanku? fuskanta gaba d'aya ya kumbura, Yanzu haka akwance nabarta inaga ma zazzab'ine ya rufeta, ina tsoron kar ciwonta ya tashi dan naji kuna cewa tanada ciwon zuciya, tunda tafara Maganan ldon Kabir akanta yake har tagama, Mami tace "Tun d'azu Sani yake cemin intafi shi zai kwana anan, zan tafi kawai wlh tuntuni hankalina na gunta,

Cikin shak'ek'k'en Murya irin ta Mara lfy Kabir yace "Mami akwai Maganinta acikin drowern Gadona inkinje kibata tasha, Sannan Wannan yawan kukanta zaike haifar mata da Matsala, Bansan meyasa kwanan take yawan koke2 ba, yakamata ki binciketa kiji matsalanta,


Mik'ewa Mami tayi tana kallon Agogo tace "to zan bata bata da wata Matsala lllah nason Ganin iyayenta, tacemin tanason takoma nikuma nace tabari ta kmalla Karatunta tunda sauran kad'an ne ya rage mata, iya mutafi, Nan suka masa Sallama suka fita bin Mami da kallo ya dunga yi har ta b'ace ma ganinsa, da k'yar ya fitar da ajiyan Zuciya.


*Ummu Fatimace* 😘
[7/28, 8:31 PM] β€ͺ+234 906 696 4247‬: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


_Jin jina gareku Masoya Dijah Qayah lallai Masoyi abun Alfaharine ina matik'ar Alfahari daku da soyayyarku gareni ina kuma k'ara baku hak'urin jinkirin da ake samu na wannan littafin wlh banda k'oshin lfy ne ankusa gamawa insha Allah_

_Gaisuwa gareku jigajugan Masoya *Dijah Qaya*_

*Jamila katsina*
*My Namecy Hajiya nenne*
*Mariam Tijjani Adam*
*Aysha*
*Mmn Ahmad* kd
*mmn ilham*
*Nafisa* Namcyn kishiyan *Dijah*

*Fatimas* _kuna da yawa da kuke k'irana awaya bazan iya banbancekuba, Yarana Ga tarin Addu'an da kukeyi ma takwaranku wlh ku na daban ne awajena_
*i luv oll masu wannan suna* 😍😘

_Dukanku na sadaukar muku da wannan page_ πŸ‘Œ


*_page d'in baya nayi mistake zansa 46 nasa 40 duk kun rud'e kuyi hakuri kainane yayi zafi_* πŸ˜…

4⃣7⃣

Mai da ldonsa yayi ya Rufe hoton fuskan Dijah da take kuka kaman kanta zai fashe namasa yawo lokacin da ta ganshi kwance ak'asa, yanajin shigowansu Abban Habib da shugaban ss, suna ta Magana akan harin da akayita kawomasa zuwa kan guban da yaci,


A Falo Mami tasami Dijah ta takure akan kujera alamun kaman Sanyi takeji, zama tayi agefenta ta d'an tab'ata tana k'iran Sunanta, ad'an Razane ta tashi Fuskanta ya Kumbura tsaban Kuka, "Sannu da dawowa Mami, ta fad'a tana sauk'e ajiyan Zuciya, "Sannu Khadijaah tashi muje Dining ki d'anci wani Abu kisha Magani,

Tea kawai ta iyasha tasha Maganin taje ta kwanta,



Washi gari Mami tana gama Abun Karyawa tayima lya sallama tare da bata Sallahun Maganin Dijah ta nufi Asibiti,

Da Sallamanta ta tura k'ofan tashiga Sani da Habib suna zaune akan Kujeru suna d'an hira k'asa2 shikuma Gogan yana kan Gado ldonsa Alumshe kaman Mai Bacci, dukansu suka tashi suna Mata sannu tare da karb'an kayan Abincin datashigo dashi, Sani yayi saurin tura mata kujera ta zauna Baki bud'e ta kalli Habib "kardai kaima anan ka kwana? "Eh Mami tare muka kwana,

"cab! Ina ka baro Matar taka? Dariya suakayi dukansu, Sani yana sosa k'eya yace "Mami nifa?

"a'a gwanda kai ai Kun far tsufa sufa Amarya da Angone, dariya suka kuma yi har da ita, sannan suka gaisheta ta tambayesu mai jiki,





Sai lokacin ta kalli Kb tace "Bacci yakeyine ahankali yabud'e ido ya kalleta, tace "Oh idonka biyu? Ya jikin? Alhamdulillah Mami, to Allah ya sawak'e ta kalli Sani tace had'a masa tea yasha yasha Magani kuma kusamu ku karya kuje kuga matayenku inyaso sai kudawo anjima nikuma intafi,




Yana Jingine da Pillow yana kurb'an tea a hankali ya kalli Mami, yace "Mami ya Khadijah da jiki? Da sauk'i ta amsa atak'aice kaman zai sake cewa wani abin sai kuma yayi shiru gudun karsu Habib su zaci yadamu da itane, daga waje sukaji anyi nocking kafin ayi izini tuni anturo anshigo, Alhaji ya'u ne da Matarsa, gaba d'aya d'akin ba wanda yamusu kallon Arzik'i sai Mami itace tayi ta musu sannu da zuwa gami da basu wajen zaman, Alhaji ya'u kam atsaye ya tsaya itace ta zauna, Nan suka fara jajanta Al'amarin Musamman Maman Nafisa, tadage sosai wajen Maganan dole abinciko masu Hanu wajen salwantar mata da d'a kuma siriki,





Kwanan Kabir Uku a Asibiti aka sallameshi, Duk dacewan Har yanzu jikinsa ba k'arfi, yawancin wasu abubuwan sai anmasa,




Da Misalin k'arfe 10 :00am suka shigo gidan su Sani ne suka taimaka mishi a hankali yake takawa har cikin pert d'inshi, kai tsaye toilet yace akaishi ya watsa Ruwa, jimawa kad'an yafito cikin tree quater da Amless masu santsi koraye, da ratsin fari, ya kwanta akan doguwar Kujera, nanda nan bacci yayi gaba dashi, dai Azahar ya farka,


Bayan ya idar da Sallah yana zaune akan sallaya yajiyo lya daga waje tana fad'in "Sani Kabirun ya farka?

"Eh yabata Amsa, tatura tashigo, kusa dashi ta zauna akan kujera tana kallonsa, "Maza ya k'arfin jikindai?

"Banso aiba yanzu nadawoba,

"Kai kaji d'an nima sawuna nawa ina zuwa kana Bacci?




"Mhmm ai nafi haur da shigowa kafin nayi baccin,

"Oh nima ai baccin nake lokacin dawowankun saida Khadijah ta d'agani, natashi nayi sallah,



Tab'e Baki yayi ya jingina Bayansa da Kujera, dai2 Lokacin Mami tashigo, Hira suka dingayi har akayi la'asar, suka shiga ciki, lya ta kalli Dijah da take ta danne2 waya, tace "Banga kinje kingaida Kabir Khadijah, ko bakisan ansallameshi bane?


Dijah ta turo Baki "to ina Ruwa na dashi?


"Ina Ruwanki dashi? Iya tafad'a tana rik'e hab'a, "Dan Allah lya kirabu dani inkuma so kk inbarmiki d'akinki to,

"Ke Khadijah kirabani da lyayi kitashi kije kigaida Mijinki, ince nan da aka kaishi Asibiti kika dinga Kuka saida Fuskarki yadawo kaman Gauta,



"Allah ya kiyaye Mijin masu Miji dai niba dai Mijinaba, tafad'a gamida mik'ewa tafita ta shiga d'akinta, yaye labulen Window tayi kaman mai niman wani abun tajima tsaye awajen har aka k'ira Magriba, sannan taje tayo Awala tayi Sallah.



Yau pert d'in Kb Mami da lya suaka kai Hira, suna zaune Nafisa da Ka'wanta suka shigo, can kusa da Kabir ta wuce tazauna tana d'ari2 datasan zata samu su Mami da batashigoba dantana kyautata zaton Mamince tasa aka hanata ganin Kb a Asibiti, Asanyaye ta d'ago ldo takallesu sud'inma itan suke kallo, ta gaishesu Mamice kawai ta Amsa fuska Sake, tamaida Kallonta ga Kb da yake mata kallon tuhuma dan yahanata mu'amala da Meena,

Saukar da kanta k'asa tayi tana gaisheshi dai2 Lokacin Su Uncle Musa suka shigo, nan guri yad'an kaure da gaishe2 ananne Kabir yasamu daman Mata Magana k'asa2 yace yana tuhumanta na ganinta da Meena,



Ta tab'e baki ni ai agidanta ma nake yanzu, zaro ldo yayi cike da Mamaki, yace "Saboda me?




"Saboda Fushi nakeyi da kowa can gidanmu Mama tamin laifi shiyasa na gujeta har sai sun gane kurensu, Nanma anmin laifi wai nice za'a hanani dubaka a Asibiti saboda rashin yarda ni yanzu ba Ruwana da kowa zaman jiran dated'in bikinmu kawai nakeyi amana aure indawo kusa dakai daga yauma baza kasake ganinaba sai bayan ammana aure, mukasance agidanmu duk dan bak'in ciki sai ya mutu.


Tsananin Mamakin lafuzantane ya hana Kabir koda k'ifta ldo yasaki baki yana kallonta,


Sallaman Sani da yashigo yanzu da kayan buk'atun kb da ya aikeshine yadawo dashi duniyan Mamaki dayatafi, nan yamaida kallonsa ga Sanin da yake ta jibga Kayan Drinks a frich,

Yana gaida su Abban Habib, Kallonsa tayi

tace "sai munyi waya, daga haka ta mik'e ba tare da tayima kowa sallamaba suka tafi,

Da ido yarakasu har suka fice.


"Sani ya kamata ace ka koma gida haka kasancewan unguwanku da d'an Rata, cewan Uncle Musa, Mami ta d'ora da cewa, "Wlh kuwa tunda yamma nace masa ya tafi inyaso sai ak'ira isma'il d'aya daga cikin seceurity ya rik'a kwana dashi, saboda laluran cikin dare, da safe shikuma inyazo sai ya karb'eshi,


Abban Habib yace, "Banganeba Fatima yaza'ace wani yazo yana kwana dashi wai ina Matarsane? Uncle Musa yacab'e danima maganan nata yaban Mamaki, ba dai ace duk tsawon wannan lokaci kina rik'e masa da Mata ba Fatima, indai kuwa hakane sam baki kyautaba, a'ina aka tab'ayin haka? Mutum da Matarsa har kina nima masa wani mai tayashi kwana?




Kan Mami ak'asa tace a gani nayi yarinyace kuma itama ba k'oshin lfy ne da ita sosaiba shiyasa nace shi lsma'il d'in ya kwan da shi,





"Wani irin k'oshin lfy ne bata dashi da zai hanata zama kusa da Mijinta? Maza ki turota tazo tayi masa abunda zata iya, wanda bazata iyaba sai ataimaka mata, Sani ya koma ga iyalinshi haka ai yayi k'ok'ari yabarta gida ita d'aya,





"Aifa naji dad'in

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment