Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waye zaiyi nasarane agun Mami na wannan case d'in*?? πŸ€”


*Dan Allah kusani a Addu'a bani da lfy seriously* πŸ™πŸΌπŸ˜­


_ummu Fatima ce_ 😘
[6/29, 8:43 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


3⃣9⃣


Ahankali Mami ta mai da kallonta kan Kabir da yake satan kallonta ta wutsiyan ido da sauri ya mayar da idonsa k'asa,


Zama tayi abakin kujera shiru falon yayi bakajin komi sai gunjin kukan Khadijah, ita adole ga wacca akayiwa fyad'e.

lya kuwa tasaki baki tanson ganin tayaya za'a yanke wannan hukunci? Don ta lura Mamin tanason biyewa sakarcin Khadijah tayi hukuncin Rashin gaskiya,

ita kanta Mami rasa nacewa tayi mamiki abun yabata dan zuwa yanzu bata tsammaci Kabir yafara kallon Dijah amatsayin Maceba da har zai mata fyad'e injita da fada.

Saboda yanda yake nuna k'yamanta a fili, kullum shikenan complain akanta.


d'an gyaran Murya tayi tace "Kabir Meye gaskiyan Maganan?

Kansa ak'asa yace "Mami kinfi kowa sanin Halina kinsan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba.


"No karma kace haka sau nawa mutumin kirki yake sauyawa yazamo na banza lokaci guda, sannan mutumin Banza ya sauya yazama nagari?

Tashi katafi dare yayi yanzu gobe insha Allah zamu k'arasa.

Da sauri ya mik'e ya fice kaman k'afansa zai burma acikin tiles.

"Khadijah tashi kije ki kwanta kukan ya isa haka kinji? Mami ta fad'a, cikin tafiya mai kama da gudu ta fad'a d'akinta dan sam bahaka taso ba.


Iya ta tab'e baki tana Murmushi "tofa yau ga wacca akayiwa fyd'e tana gudu.

Mik'ewa Mami tayi tana dan sauke ajiyan zuciya, "wlh lya Khadijah da Kabir suna bani ciwon kai,


Kwance take kan Gadonta sai juyi takeyi zogi da rad'ad'in da Bubs d'inta suke mata yahanata Bacci, hoton fuskan Kabir yak'i d'aukewa a idonta Musamman lokacin dasuke gaban Mami yanayin da Fuskansa ya koma yak'i b'ace mata wani nauyi takeji a zuciyanta yana tasowa, dak'yar tasamu tayi Bacci da asuba kuwa tana tashi kafin tashiga toilet sai da taduba Mirrow ga mamakinta Bakinta ya sab'e sumul ba kumburin.

Tana idar da Sallah kaman yanda tasaba kitchen ta nufa sai da ta gama tana jerawa a dining Mami ta fito cikin shirin fita aiki,

Cikin jin dad'i da fara'a tayima Khadijah sannu,

Agurguje ta karya ta fita dan tana da Meeting,


🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴


Boka wannan itace 'yata Nafisa dana maka bayani awaya, kamar yanda nagaya maka d'an'uwata ne Kabir tun suna yara suna son junansu sai gashi kamanza'ayi aure sai zancan ya shiriri ce da munyi zaton daga yaronne sai daga baya muka fahimci uwarsace bata son abun,

Yanzu haka danake maka bayani taje ta auramasa wata yarinya,

Wani irin tsawa boka ya daka mata "Kees fad'i abunda kk so ayi kawai, duk munsan wannan abunda kike fad'an yanzu ya kukeson ayi yanzu yanzu ayita ta k'are.

Cikin sabo da halin bokan tace "So nake asa Kabir yazamo mai bijire ma Mahaifiyarsa duk abinda tace yak'i yi Sannan asashi ya k'ara tsanan yarinyan dan dama yanzu haka ya tsaneta, saboda tsaban yanda yake bin maganan Uwarsa ne kawai yasa baiya nuna wa uwar,


Nasan da yadaina jin magananta zai saki yarinyan dan dama ba sonta yakeba,


"Ya isaaaa!!! Bokan ya fad'a yana kallon Nafisa da take ta takurewa ajikin Mamanta dan dai ita wannanne karo na farko da ta tab'a zuawa wajen Bokan.


"karbi wannan K'ullin Maganin d'aya kitabbatar ita yarinyan da yaron da Uwar tashi sunci, d'aya kuma kitabbatar shi kad'ai yaci sannan kisamasa ahanya ya tsallake d'ayan kuma....... hahhhhhhh ya fashe da dariya kutashi kutafi tsinnanun Allah, da sauri Nafisa ta mik'e har tana tuntub'e Mamanta ta rufa mata baya suka tafi.


Suna dawowa suka zube a falo, Nafisa sai haki takeyi ta kalli Mamanta, "wai dama kinsan Bokan ne?

Yatsa tasamata abaki alaman tayi shiru tace "kedai kiyi abunda yake gabanki kawai,

Nidai nagama nawa tunda na tasaki gaba na kaiki saura ya rage naki kisan yanda zakiyi Amfani dashi kisamusu.


"ai Mama sama Kabir da Maminsa abu suci shi yafi komi sauk'i ita wanccan banzanne dai bansan yanda zanyi da itaba, dan ko fitowa cin Abinci acikin mutane batayi.

Wlh Mama na tsani yarinyan wai nice za'ayiwa kishiya,

Kai nama tuna wlh ko shak'eta sai nayi na d'ura mata muddun zai sake shegiya.


"Ato? Gara dai kiyi kisama ma kanki farin ciki tunda kinmatsa kina sonsa ahakan.


Ta mik'e tana kallon Agogo Barima intashi intafi, zan koma gidan da zama Mama.

"baxan hanakiba Nafisa saidai kidinga yawan zuwa ina ganinki, kinsan ke kad'ai muke dake Nafisa, Anyima d'an'uwanki asiri ya fad'a yawon Duniya ko labarinsa bama ji.

Yauwa d'ayanfa nayanda zaki mallakeshi yanda bazai kuma kallon wata mace bane, dan haka shi ranan yin Baikonku ne zaki samasa.

"Gud Mamana Nagode miki Allah yabarmin ke, daga haka taje ta fara tare kayanta,

D'akin Dadynta Maman tashiga tsaye ta ganshi a gindin Window ya dafe Windown,

Zama tayi abakin gado ta kalleshi "ka kwantar da Hankalinka Dad yau saura sati biyu ayi baikon Nafisa da Kabir ko?

To iya wa'adin daya saura ma Kabir kenan a duniya, !

Da sauri ya kalleta "Nafa ji duk shiriritan da kukeyi ke wai so kk ta mallakeshi ni kuma dukiyansa nakeson Mallaka, kiduba kigani duk kadarorina sun k'are talauci na Barazanan afkamin abunda nafi tsana arayuwata.


Dariya tayi tana kad'a masa gira bakakaini tsanan talauci ba wlh kasan yaranta nad'iban Nafisa bazata tab'a yarda da k'udurinmuba shiyasa namata rufa rufa, ai Guba nabata tasaka masa Ranan baikon,

Dasauri yamik'e Gu.. What? Kina da Hankali kuwa so kk kiwurga mu cikin masifa? Kabir wasane? Dazata bashi poisin cikin dauk'i, Maza bita kikarb'o tun baki jefamin "ya cikin Musiba ba.

"Haba kaikuwa! Me ka maidani? Nagama shirya yanda komi zai tafi kwantar da Hankalinka, matso kaji,

Ya mik'o kunnensa ta masa magana gaba d'ayansu suka kece da Dariya.

( *To Allah ya kyauta* )

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Yau kwana biyu kenan da faruwan Lamarin Dijah da Kabir, Mami bata wani sashi a ido sosaiba, dan haka tana dawowa daga aiki ko cikin gida bata shigaba, tashiga pert d'inshi, Akwance tasameshi yana rik'e da maransa sai nuk'ursuwa yakeyi kallo d'aya tamasa hankalinta ya mugun tashi dan ganin tsaban rama da tayi a idonsa,

Akid'ime ta dafa kansa "Kabiruna! Meya sameka? Meke damunka? D'ago kai yayi suka had'a ido, yaski murmushin k'arfin Hali, Ya tashi da k'yar yana tattaro Murmushin dole "Mami na Barka da dawowa!,

"Meyasa meka Kabir? Fad'a min inji,
"kar kidamu Mami ciki na ne ked'n min ciwo,

"subahanallah tun yaushe?

"yau da safe ne Amma yanzu da sauk'i nasha magani,

Taxaro waya tana fad'in Gaskiya ban yardaba Kabir nasan Halinka sarai,

Habib tak'ira bugu d'aya yad'auka batagama Amsa sallamanba, tace " Maza zoka dubamin d'an'uwanka da sauri,

"to Mami dama gani ahanyan Zuwa gidan tun safe nake k'iranshi baya d'agawa,
"to maza hanzarta,

Baifi 5 Minutes ba yashigo yasamu sai sannu Mami take jera masa, agefe Habib ya zauna suna gama gaisawa da Mami ta tashi barin shiga Habib inkagama dubashin sai kasanar dani komi.


Habib ya matso yana kallonsa,
"Man meke damunkane?

Gyara zama Kabir yayi ya d'an ware idonsa, yana yamutsa fuska cikina ne yake min ciwo,

Gwade2 Habib ya shiga masa sai da yagama ya xauna agefensa, kai "Man wlh k'arya kakeyi Ba ciki bane marankane yake ciwo, Mhmmm ka d'an tsokano ko?

Wlh ka ajiye komi kab'arji angoncinka inkak'i kaine awahale baruwana,

"Dallah can Malam banason maganan Banza meya had'a ciwon ciki da Mara?

"Ok to barinje ingaya ma Mami abunda nagani, da sauri Ya jawoshi baya pls Habib karufamin Asiri kar fad'a mata dan Allah,

"amma kayarda matsalanka kenan?
"Eh nayarda pls kar kafad'amata.......



*Bahaka nasoba my Luvky Fans 😘 haryanzu banda lfy karkugaji damin Addu'ah kunji ni takuce ku nawane* πŸ€πŸ»πŸ˜‰

Gadai Nafisa wannan karon ta tink'aro gidan Mami da niyan raba d'a da Uwa dakuma mata da miji tofa koya zatakaya ???

sai naji daga gareku
.
Ummu fatima 😘
[7/2, 9:05 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬

*Nagode Matik'a da Addu'o'inku gareni, masu k'irana a waya ku kuka sani typing badan nayi lfyba,* 😰
*Musamman ta kwarata*
*Asma'u daga sokoto*
*Munira*
*Aysha jos*
*Billy...*
*Hajjaju....*
Some thing Kaduna πŸ˜‰
*da sauran wa inda bazan iya tuna sunanba, wa innan suna K'irana kaman sau cikin babban Bokiti biyar a kowani rana* 😰😰


🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


4⃣0⃣

"Ok Bazan fad'aba amma sai kamin Alk'awari,

Afusace KB yace "Wannane kuma baka isaba! Bawani Alk'awarin da zanmaka, Don't Waist your time!,

"Amma ai Kb naga kana da mata Bai kamata ace Haka ya faru dakaiba,


"Karka damu yau sauran Sati biyu ayi Engagment d'inmu anayi da sati d'aya za'ayi aurenmu, so kaga atleast sauran sati Uku in angonce,

"Kabir kar ka yaudari kanka ka hanama Zuciyarka abun da takeso, Khadijah kakeso ba Nafisa ba, da Harara KB yake kallonsa,

"Bantab'a son wata Khadijah ba kuma har abada bazan sotaba, sam kasan wannan yarinyan tsarina da nata ba d'aya bane bata dace da Rayuwana ba.......


"Inawuni Yaya Habib! Muryan Khadijah wacce sam basu lura da shigowanta ba, ya katse musu magana, gami da ajiye flaks d'in da tashigo dashi ahanunta, Wani irin d'aci takeji a mak'ogoronta, dan kaf taji abun da KB ya fad'a.

"Lfy Khadijah ya school... Habib ya Amsa adiririce, "Alhamdulillah! Wai inji Mamy inkagama kasameta, tafad'a cikin wani lrin sanyin dayasa Kabir yabita da kallo, ta mik'e zata tafi, Habib yace Khadijah pls d'an zo ki had'a masa tea d'in yasha, komawa tayi tajanyo Cup ta fara had'a masa,

"Barinje wajen Mami Habib ya fad'a sannan ya fice, Binta da kallo Kabir yake tayi har tagama ta ajiye agabansa ba tare da ta kalleshiba, ta mik'e zata fita, har takai tsakiyan falon yace "Ke Khadijah!
Tayawa tayi cak ba tare da ta juyoba, Kunnuwanta sai tarayo mata kalamansa sukeyi.

cike da Mamaki yataso ya sha gabanta yana kallon Fuskanta, dan bai tab'a ganinta hakaba, da yatsunsa biyu ya tallafo Hab'anta, Hawayen da suka taru A ldonta suka gangaro kan Kumatunta, da sauri ta k'wace Fuskanta gami da share hawayen tabi gefe zata wuce ya fizgota yamai data baya.

"Meye yasaki Kuka? Yauma wani Makircin kika shiryo? Yau kuma inkinfita mezakice namiki wanda yafi *Fyad'e* muni?

Yak'ank'antar da ldo Ki rubuta da Alk'alaminki ki ajiye akwai Ranan da saidai wani Yagaya miki cewa namiki fyad'e bama ke zaki fad'a da Bakinkiba, ya fad'a yana shafo Bubs d'inta, ta bayansa ta kuma yunk'urin wucewa ya rungumota jikinsa, kaman abun gayyah sai ga KB yana shirin fita ahayyacinsa, a tsorace ta k'wace kanta jikinta har yana b'ari ta fice da sauri, tanufi cikin Gida saidai Har yanzu lafazinsa yana mata yawo, dai2 lokacin kuma Nafisa tafito a Mota, bak'aramin fad'uwan gaba Nafisa tajiba sakamakon ganin fitowan Dijah a pert d'in Kb ta dafe kanta ta jingina ajikin mota tana tambayan kanta, Anyah! Ban sake da yawa ba? Yaushe wannan jakan tafara shiga wajen Kb dam taji gabanta ya fad'i "to koma wani abu ya shiga tsakaninsu, a fili tace k'arya ne..... Wlh bazaiyiwuba da sai na halakata, fuuu! Tabi bayan Dijah da kallo d'aya ta mata ta shige ciki abunta.

Dab da zata shiga ciki wata zuciya tace " Haba Nafisa ke da kikazo da babban Al'amari ai fushi banaki bane ahankali zakibi ba a galaba da fitina, wani muguncaccen Murmushi tayi sannan ta shiga.

A kwance Habib ya dawo ya tarar da Kabir yayi ruf da ciki ya damk'e maransa ya ciza lips d'insa yana juya kansa a Hanun kujera, dasauri Habib ya rik'oshi "u see Kabir zakaje ka illata kanka da ganga alhali kafi kowa sanin illan hakan kana da cuta sannan kana da maganinsa a kuturinka,

In nauyin Mami kakeji kaifa namiji ne ka lallab'a yarinyanan ka d'auketa ka kaita Gidanka ka sauk'e laluranka ka dawo da ita inma kai bazaka iya fita da ita ba, nizan kawo maka ita nasan dabaran da zanyi ma Mami, Amma kana da mata ka zauna ciwon Mara na Sha'awa ya illataka?

"Habib ya dai ciwon cikin ya motsane?
Nazaci ai kaje sayo maganin ne? Inji Mami ba Habib da yayi maganan ba Hatta Kabir saida Hantan cikinsa ya kad'a tsaban tsoro mai gauraye da Kunya!!


Dukansu suka d'ago suka kalleta Fuskanta wasai ba Alamun taji wani abun da akace, Cikin in ina Habib yace "Naba ma Sani ya tafi sayowa... Mmnn dama.... Tafiya zanyi ... Inya kawo Mami abashi biyu da rana biyu da Safe...

Ganowan da KB yayi Habib d'in yana son arcewa yabarshi da tarin kunyane yasa ya rik'o Hanunsa yana kallon Mami,

.... Mmnm ka jirashi ya dawo man... Da k'yar Mami ta gimtse dariyanta tana kallonsu sai tsilli tsilli sukeyi da ldo kaman sunci kud'in aika, "Mhmmn Gaskiya kam kabari ya dawo kafini sanin kan abun naku, ta fad'a tana fita,


Kuyi hak'uri da wannan in Allah ya bani lfy zanke muku yanda nasaba,

Ummu Fatima ce 😘
[7/4, 9:39 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


4⃣1⃣


Tana fita Kabir ya k'wace Hanunsa yana Hararansa

Habibb ya dafe bakinsa "kai da Allah tajine?

"Bansaniba aikai tsaban magananka sai ka fad'i abunda yafi karfinka, Har da cewa Kaba Sani yaje sayo magani,


Habib ya mik'e yana gyara Hanun Rigansa, to kai wani Magani ma za'a sayomaka? Bayan ga Maganinka acikin gida, kana k'i.

Ni kaga tafiyata, zanje wajen Mata ta dama Bak'ine suka cika mana gidan suka hanamu sakat, inba hakabama ba abunda zai fito dani ina shan Maik'on Amarci, kb dai komawa yayi ya kwanta ba tare da yace komiba,

Ak'ofan Fita sukayi karo da Nafisa tana shigowa, ya matsa mata ta shiga ba tare da sunce ma juna k'alaba.


Kwanan Nafisa Hud'u da zuwa Gidan duk yanda takai da son ta takali Dijah da fitina abun ya gagara dan Dijah sam bata yarda su had'a inuwa, iyakacinta idan tana d'aki taji motsinsu ta baya ita da Kabir ta tashi tayi ta lek'ensu tana tirrr!! Dan wannan karon like masa da tayi yafi na kullum dan har Abinci tare suke ci wani zubin har a baki take bashi musammanma intaga Dijah tafito zata shiga kitchen

Da Dijah Nafisa taso fara aikinta saida ta kasa gane wani lokaci Dijahn take cin Abinci??

Wani tunanine yazo mata akan ta saka musu maganin kawai a Abincin gidan gaba d'aya da haka ta d'auko ledan Maganin ta fito da duru2 kai tsaye kitchen ta shiga, Alokacin Dijah tana tsakiyan aikinta sauri2 takeyi dan yau tana da Lactur 7:00, Wani kallon sama da k'asa Nafisa tabita dashi tana wani yatsina Fuska, Dijah yi tayi kaman bata gantaba tajawo wayanta ta yake gefenta ta kunna k'ira'a ta ajiye ahankali take bin karatun tana aikinta, har sai da ta tabbatar ta gama komi sannan tafita da niyan yin wanka anan ta bar Nafisa tana ta bincike kaman mai niman wani Abun, tana fita Nafisa tayi wani Dariyan mugunta ta ciro maganin da ta tusashi a maranta ta bud'e kayan Abincin ta barbad'esu da Maganin da Sauri kuma ta mayar ta cusa, tana k'ok'arin Rufe Kulan Dijah ta shigo d'aukan k'aramar wayanta da tamanta,


Cike da tsoro Nafisa ta kalleta itama Dijahn ita take kallo da mamaki, "mhmm ke Wannan irin Kallonfa? Ko dan kinsamu na Bud'e wannan kucakin Abincinki,


"mhh to ai banga dalilin da zaisa ki bud'eba tunda naga bake kika girkaba.

"Eh Amma ai Gidan Ubana ne inada daman yin abunda naga dama tunda Gidanmu ne, ke kuma 'yar aiki ce baki da Hurumin hanani abinda nayi niya, banza kawai 'yar k'auye daga haka taja dogon tsaki ta fita,


Nan tabar Dijah tayi sakare tana k'are ma Hanyan da tabin kallo Lafuzanta sai dawomata sukeyi da k'yar taja k'afanta ta fita da tarin takaici, ta nufi d'akinta agurguje tagama wanka ta shirya ta fito tana kwaso Abincin daga kitchen zuwa daining, Mami ta fito cikin shiri, "Sannu Khadijah ta Allah ya miki Albarka,

Tana Murmushi ta Amsa sannan ta gaisheta, dai lokacin Dr Kb ya shigo Shima cikin shirin fita aiki, ganin shine yasa Khadijah ta shige kitchen kaman mai niman wani abun,

" Sannu Mamita!,
"mnh Sannu sarkin Latti? Ta fad'a tana jawo kujera ta tura masa, ya zauna Sannan itama ta zauna, yana Murmushi yace "Mami na kinyi kyau

Itama Murmushin tayi "Baka da dama Kabir, kaje ka gaida iya kuwa?

"ai Dole na Mami daga d'akinta nake,
"ok Addu'a fa? Kayi?
"Eh nayi,
" na dai gayamaka karka dinga wasa da Addu'a domin shine Babban Makaminka koda wani abun zai sameka to indai kana Addu'a xai xo da sauk'i, dan haka kar kayi wasa Kabir nasanka da Himmah Amma ka k'ara, kana idar da sallahn Asuba kar katashi a wurin sai kayi Addu'an safiya, sannan inxaka fita kayi Addu'an fita agida inka dawo kayi, kana idar da la'asar kayi na maraice, indai ka rik'e wannan da kyau tofa ko wata Annobace ta shigo gari banda kai aciki.

Cikin jin dad'in samun Uwa tagari yake kallonta yana Murmushi "Hak'ik'a Nikan Allah ya zab'eni Mami ta da ya azurtani dasamunki amatsayin Uwa sam Boko bai sakin manta da makomar kiba Mami na, sab'anin wasu da basumakai ki zurfi acikintaba, suke jifa da tsarin lslam su d'auki tsarin ya hudanci susa ma kansu.

Dai2 lokacin Nafisa ta iso wajen, fuskanta d'auke da Murmushin Nasara tajawo kujera daf da Kb tazauna, tana gai da Mami da Hankalinta yake ga Dijah da tafito daga kitchen sauri sauri takeyi tanason ta wuce d'aki, Mami tak'irata asanyaye ta Amsa ta iso, Kujeran da yake tsakaninta da Kb ta jawo mata, "Maza zauna ki karya dannasan k'aramin aikinkine kitafi haka baki karyaba, xama tayi dan tasan duk abunda zatace Mamin ba yarda zatayiba, plate 4 ta jawo zatayi saving nasu Cikin farin ciki Nafisa tace "Ni yau ina azumi Khadijah karki zuba da ni

"Azumin me kuma yau laraba? Mami ta tambaya cike da Mamakin irin walwalan da tagano afuskanta,

"Wlh Azumin dana shane nakeson inrama shi.

Dijah dai zuba Abincin takeyi batare da ta ko kalletaba har tagama ta tura ma kowa nasa agabansa.



*Wayyo Mami da yaranta* 😭😭

*Allah sarki Dijah ko ka'arshen zaman gidan Mamine yazo?* 😭😭


*Kuyi Hak'uri kunji k'awayena* yaumma ba yawa 😰😰😰


Ummu fatima ce πŸ¦‹
[7/11, 3:25 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


4⃣2⃣


Zama tayi ta jawo Abincin sai yatsina fuska takeyi dan sam taji bata sha'awan ci, ta d'iba zata kai bakinta kenan wayanta ta hau Ruri ta maida spoon d'in ta d'auko wayan ta zuba masa ido har ya yanke, sannan ta fara daddana wayan,


"Khadijah! Mami ta k'ira Sunanta tana jujjuyan Abincin da spoon, Meye haka acikin Abincinnan?

Da sauri Nafisa ta lek'o "Mmnn Mami kinsan halin ka da mutumin k'auye, inaga curry ne ta barbad'a bayan ta gama Abincin,

K'urama Abincin ido Dijah tayi tana nazari cike da tsoro ta d'ago ido ta kalli Mami da Kabir gaba d'ayansu ita suke kallo cike da tuhuma,

"Tambayanki fa nakeyi Khadijah!
Kina zaromin ldo, wani garine kala- kala nake gani haka aciki?


"Wlh Mami bansan meye bane.


"curry nefa Mami Nafisa tasake maimaitawa,

K'ura mata ido Mami tayi tana karantan yanayinta sannan ta nisa tace "curi? Ta yaya akayi kikasan curry ne Nafisa? Ko tare kukayi girkin?

"a'ah bana gurin tayi Girkinta, na dai ga kalanne kaman na curryn, to Allah dai yasa ba wani abun ta barbad'a,ba Nafisa ta fad'a adiririce ita dai burinta suci kar tayi asaran wannan daman,

d'an Murmushin gefen baki Mami tayi ta kuma kallon Khadijah data kafe Abincin da ldo kaman maison ganin wani sabon abin aciki,

mik'ewa Mami tayi ta d'ebe duk plates d'in gabansun ta juye a food flaks ta d'aga cak ta kai kitchen.

Cike da tsananin ta kaici Nafisa ta kalli Kabir da gaba d'ayan hankalinsa yana kan wayan Dijah dayake ta ruri akan table *My Friend* suna da yake yawo akan screen d'in kenan,

Azuciyanta tace yanzu kun tsira akwai gaba wlh bazaku taba tsere ma tarkon gaba ba Magani yananan wlh sai kunci daga haka ta mik'e ta tafi,

Cikin kasala Dijah ta mik'e tabi bayan Mami a k'ofan d'akinta tasameta rataye da jaka tana rufe k'ofan murya na b'ari tace "Mami wlh bansan..... "Shourt off, baki da bakin kare kanki Khadijah tayaya zakiyi Abinci sannan kice bakisan abun da akasa acikiba? Hakan bazai yiwuba, kinaji?, daga haka ta wuceta ta fita.


A falo Mami ta tarar da KB yana shirin fita tace, " Kabir kaje part d'inka kasha tea kar kafita

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment