Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya. iya haka ya mik'e sumsun ya fita ya jima a mota kafin ya tayar ya fice ko da ya shiga Gidansama zama yayi cikin Motan na tsawon lokaci yana niman yanda zaiyi, ya bud'e Motan ya sako k'afafunsa waje yayi diling layin Dijah,


Dijah kuwa tun Sanda taji k'aran da yayi ta tsorata ta sake wayan a k'asa Sai zare ido takeyi cike da tsoro tsawan lokaci kafin ta d'auki wayan ta shiga d'akin Yafannah, Duk yanda taso ta shashantar da zance a zuciyanta ta kasa musamman dataga bai kuma k'irantaba,


Tun Bayan da ta idar da sallahn Magriba ta kifa kanta sai kuka take, Musamman data tuna wai Nafisa ta tare yanzu haka suna Gidansu,

Da yaya ta yakice tunaninsa aranta tun da tazo,

Gashi yau kuma tunomata, Gaba d'aya taji zuciyanta ya cunkushe,

Daga Bisani ta haye Gado ta lullub'u tananin kishi ya sauk'ar mata da zazzab'i tanaji wayanta yana Ringing har ya yanke bata d'agaba,


Yana zaune sai k'ira yake bata d'agaba anma hakan bai sa ya hak'ura da k'iranba,


Candai da ta gaji dayin wurgi da wayan ta d'auka a zafefe ta kara a kunnenta,


Cike da tsiwa tace "Wani Mara aikinyi d'inne yake son shiga Rayuwata haka?





*UMMU Fatima CE* 😘
[9/10, 10:41 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣2⃣



Lumshe Idonsa yayi ya jingina da Jikin seat d'in Motan yana sauraren tsaurin idon da takemasa,


Wani iri Sanyi na ratsa jikinsa, sai shafa kwancaccen Gashi K'irjinsa yakeyi, jin kaman zata katse k'iranne yasashi saurin cewa "Dakata inason kigayamin inda kike, Na miki Alk'awari indai a cikin k'asannane A darennan zakiga ko wani mara aikinyinne mai damunki da izinin Allah,


"Malam Dan Allah kafita arayuwata, plaes kar ka k'ara k'irana,

Cikin wani irin Murya yace "Pleas My Heart Khadijah bazan iya fita arayuwankiba, Bazanma iya Rayuwa bakeba, ki taimakeni Khadijah I really Luv U, kisanar dani inda kike in zo gareki tun zuciyana bai Bugaba kinji matata, ya k'arashe cikin wani irin sanyi Murya,



Ji take kaman tana yawo cikin Gajimare kalmomin da take karantawa a Novel Miji na fad'a wa Matarsa yau shine Kabir yake gayamata? Ashe zata tab'a jin irin wannan kalman daga gareshi?


Mik'ewa take tayi akan gadon tanajin yanda kalamansa suke yawo cikin jikinta, ldonta a lumshe zuciyanta na Harbawa da k'arfi2


"Helo Dijahna pleas tell me ina Mami ta tusamin ke tabarni da Raunin Zuciya?

Dan Allah Khadijah kar kibarni duk rintsi ki kasance dani wlh inasonki, ki yarda dani,


Wannan karon kam Kunnuwanta sunkasa d'aukan maganganunsan dan haka tayi saurin katse wayan, tayi jifa dashi gefen pillown da take kai, ta dafe k'irjinta da take jin kaman xai b'ullo waje.


"Da Gaskene yanzu yana Sona kaman yanda nakamu da sonsa?
Da Gaske yana Son indawo gareshi?? Anyah???

Kanta tashiga girgizawa kaman k'adangariya, "No Dijah kar kiyarda dashi mayaudarine kinmanta yaudaran da yadinga miki abaya? meyasa tun zuwanki bai nimekiba sai yanxu?
Meyasa ya tare da Matarsa da yake cewa ita yakeso abayanki?

*Bana Sonta kuma bazan tab'a sontaba har abada tsarina da na yarinyannan ba d'aya bane*

Kalamnasa na baya suka dawo mata komawa tayi ta kwanta Dafe da k'irjinta wani lrin kuka mai k'arfi ya k'wacemata, ita dai ta cuci Kanta da tabari xuciyarta ta kamu da Sonsa,


Rik'e yake da wayan sai juyawa yakeyi a hanunnsa tsawon lokaci kafin ya tashi ya shiga ciki,


Jiki a sanyaye yake taku har ya iso bakin Gado, nan yayi tozali da Nafisa tayi shame2 akan Bed d'in zagawa yayi tacan side d'in ya zauna yayi Addu'o'insa Sannan ya jawo pillow ya Rungume a k'irjinsa ya lumshe ldo, yana tuanin kalan taushi da turaren Dijah tun bayan da tabarshi bai kuma sake jin irin k'amshintaba, yana matik'ar son K'amshin a ransa,


Washi Gari da k'yar Kb ya iya kaiwa takwasa agidansa ya fito ya nufi Gidan Mami, Bed room d'inta ya isa gam yaji k'ofan Arufe, ya d'anyi knocking anma ina bai koji alamantaba ya sauk'0 ya lek'a kitchen batanan,

Ya dawo palour ya zauna yana kallo aransa yana tunani yadai san Mami bata barcin Safe,

Kusan 2Hours yana zaune a wajen kafin ta fito cikin shiri da alama fita zatayi yanzun,

Kallonsa tayi kaman bata san da zuwansaba tace "A'a My Hanson Boy kaine anan? Ya shafa kansa yana d'an Murmushi,

Ta zauna kusa dashi tana k'aremas kallo,
"Kabir Anya kuwa kana cin Abinci? Duk ka wani firgice ka fita ahayyacinka, kobaka da lfyne?


"Lfy na k'alau Mami inaga dai idonkine kawai ya nuna miki kaman na Rame, anam yaronki dai dai yake.

Tab'e Baki tayi tace "Zan turomuku Laraba ta dinga muku Girki nasanka sarai yanxu haka k'in cin Girkin Nafisa kakeyi shiyasa ka koma haka, ta wuce kitchen ta kawomasa Abinci, ba Musu ya fara Ci dan mugun yunwa yakeji, ta kalleshe da Gefen ldo "ni zan fitane inkagama ka rufemin pert d'in Kaba mai gadi key,


Cikin wani irin yanayi Kabir ya ture Abincin Gefe, ya kalli Mami da take shirin tashi,

Asanyaye yace
"Mami kinmin Alak'awari jiya, Akan Maganan Khadijah, pls Mami,

Mami ta yatsina Fuska, "Ni Alk'awarin me namaka?
"kince xaki gayamin inda take,

"Gaskiya ba muyi haka da kaiba Kabir, bance zan gayamaka inda takeba,


Ya Langab'ar da kai "Plaes Mami ki taimaka Kisanar dani inda take badan Halinaba,

"Mhmm nifa Kar ka nimi d'agamin hankali Kabir dan bazan yarda indawo maka da 'yar mutane gidanka ku had'u da Matarka ku wulak'antataba, Sam hakan ba zaiyiwuba,

Tunda baka Ra'ayinta kawai ka rabu da ita kayi zamanka da Matarka,

Kana sane da yanda take a gurin iyayenta,

"Mami Nidai Hak'uri nake baki, Dan Allah ki...

tayi saurin dakatar dashi ta hanyan d'aga masa Hanu "ya isa haka Kabir,

Gatafa na maka ka nunamin ban kyauta makaba, da yake Bakasan irin artabun da nasha kafin in samu nasaran karb'anta A hanun Mahaifintaba,

Sannan bakasa sisinka wajen aurenba, dai dai da Sadaki Biyamaka akayi kaidai kawai Ganinta kayi nice nasha duk wahalan, ahakama kazo ka watsamin k'asa a ido ko kanmatane?

Ceminfa kayi fa ba zaiyiwu Kahad'a Nafisa da wannan yarinya mara kunyanba,

Kuma nan ka had'o kayan Matarka anma ita dai2 da pant baka saya ka bataba, a hakane zanbaaka 'yar mutane kaje kuyi ta mata tasku a nunamata wariya a fili?


Matsowa kusa da ita yayi yana fuskantanta, cikin Magiya da Kunya abunda yadingayi abaya, yace "Allah Mami hakan da kike tunani baxai yiwuba, kema kinsan Nafisa bata isa da Khadijah ba, ke kanki kinsani Khadijah ba kanwan lasa bace, Wlh inta cije ko nisaidai inganta inbarta Balle Nafisa, Allah kuwa itama Nafisan shakkanta takeyi duk wani abunda kika ga tanayi mata wlh ldon mutane kesawa ta mata,

Na tuba Mami Nasan nayi kuskure abaya bazan sakeba kiyi hak'uri,

Maganan lefe Kuma Insha Allah Gobe za'a kawomiki Mami kiyi hak'uri,

Tab'e Baki Mami tayi tana kallon yanda ya hak'ik'ance da iya Gaskiyansa yana bayani, tace "Shikena kaje zan duba Inyi Naxari akan Maganan Nan da 2 Weaks zakaji Amsa, Daga haka ta tashi ta fita,

Kabir ya dafe kansa yabi hanyan data wuce da kallo, na tsawon lokaci, Sannan daga Bisani ya tashi ya fita kai tsaye Gidan Habib ya tafi, Bayan ya nimi order, ya tsaya a k'ofan palour,

Sauda ta lek'o ganin Kb yasa ta fito Tana Murmushi Yaya Kb yau kuma daga wajene?

"Mtss ina wancan Banzan yake kice masa yazo ina jiransa, ba abunda ya iya sai baccin Asara,

Ta toshe Bakinta tana Dariya "Ya Kb waye kuma Banza?
Ya zabgamata Harara gami da nunata da yatsa "Ke kifa kiyayeni, ta d'an turo baki "To ai ni bansan wani Banza agidannan bane,
kanta yayo zai kaimata masga tayi saurin shigewa ciki tana dariya, dai2 lokacin Habib ya fito gami da Rik'eshi Yana murmushi "Kai Gurgu kar atab'oka awani wuri kazo ka hucemin akan Mantaman, bakasan tana da juna bane? Ko niman ka jawomin wani Abun,

"Wannan kai yashafa inkaci gaba damin maganan banza kuma Ina iya had'aku da kai da ita da d'an cikinta duka in b'ab'b'alaku, kasan sarai niban Son Iskaci,

Habib ya Shek'e da Dariya har yana rik'e Ciki, tsaki Kb yaja ya wuce yaje ya shige Motansa ya zauna Habib yabi bayansa yana dariya,

Ya zauna a gefensa gami da dafa kafad'ansa "Man wai waya tab'omin kaine kam? Kb ya sauk'e ajiyan zuciya ya kalleshi,


"Habib Mami tak'i ta fahimceni akan Maganan yarinyannan, narasa ta inda zan b'ullomata, duk ta inda na fito sai ta zame,


Habib ya d'an Murmusa "to kai ka hak'ura mana tunda gaka da Masoyiyar ka agida, kaxuba ido sai lokacin da aka dawomaka da ita,

Kb ya d'ago Rinnanun idonsa yana yima Habib wani irin Kallo da yasa Shi jin Kunya,


Ya dafa kafad'ansa "Sory Abokina kasan dama nace xan mayarmaka da Martani akan Khadijah irin abinda kadinga fad'a akanta alhali Nasan itace Muradinka, shiyasa tun Ranan nake ta maka haka,

Kar kadamu zan samu Mami akan maganan yau d'innan in abun ya gagara sai musa su Dady acikin Maganan dan basu san bata gidankaba,

Kb ya sauk'e Numfashi yace "wlh nima naso asakosu Dan nasan Halin Mami in ta cije akan abu wai tana tunanin banson Khadijah batasan Khadijah itace Rayuwana ba,


Sosai Habib ya danne Dariyansa Dan yasan inya kuskura yayi to Mai Rabashi da Abokin nasa sai a hankali, Ya lura gaba d'aya baya hayyacinsa,

yace "Kar kadamu zanje da dare insameta, daga haka suka d'an tab'a Hiransu sama2 sannan sukayi sallama da Juna, Habib yana Allah2 ya shiga yaba Sauda lbr su sha Dariyansu,


Da daddare Habib yaje yasamu Mami Akan Maganan, Sosai Mami ta gargad'eshi kan ya rabu da ita, sanna tace "Nasan tunda ya nimoka baku daceba zaku iya turomin iyayenku maza to wlh kuka kuskura duk sai na sab'amuku, tashi kaban guri, Sum2 ya tashi dan baiga wasaba,

A washi gari Kabir yabada sak'on lefen Dijah a india, baifi kwana uku ba yazo ya jibge wa Mami anma ko kallon arzik'i bata masaba,


Wasa2 Mami ta gasa Kb tun yana binta har ya gaji ya hak'ura, ya zuba ido,

Bangaren Dijah ma acikin kwanakin inma yak'ira ta bata amsawa sai dai baya gajiya da tura mata text kala2 wanda ta d'auka amatsayin Yaudara,

Yanayin Dijah da lya take gani ya canzane yasa ta yau tak'ira Mami Bayan sun gaisa tace "Fatima Gobe lnsha Allah zan turomiki da 'yarki, Sadiya zata kawota, ai gyara da Hutun ya isa haka, Mami tace

"Eh lya nima yanzu ina buk'atanta kusa dani anma naso sai nazo bikinnan sai mudawo tare, lya ta zaro ldo,
"Oh wai yanzu gurinki zata dawo? Fatima wai meke damunki? Yazaki sa a auro yarinya kuma ki rik'eta awajanki ki k'i sadata da Mijinta alahali itadashi suna son junansu?

To wlh ban yardaba tunda kikace haka bari kawai ink'ira shi Kabirun yazo ya d'auki Matarsa,


Mami tace "Kiyi hak'uri lya Gidansa za'a maida ita yanzu haka nasa angama sayo komi na kayan d'akinta jibi dama za'aje a zubamata, inyaso ina zuwa inmundawo dama d'akinta zan kaita, lya tace "a'a Bazan bari tayi bikinnanba kinasane Nafisa da Uwarta zasu zo, me kike tunanin zai faru in sun had'u? Gobe Sadiya zata kawota kuma a jibin in ankai kayan a jibin nakeso itama a kaita, Danme za'a bari sai wani lokaci?
Mami tace "Shikenan Iya ya da kikace hakan za'ayi ta kawota Goben Insha Allah a jibin zataje d'akinta, Iya tace "Atou da dai yafi,


Ta ajiye wayan tana Mita haka kawi ki rik'e yarinya awajanki kisa yara suna tambad'ewa awaje? Gashi inama yarinyan kallon kaman mai shigan ciki,

"Ke Khadijah! Ta k'walamata k'ira daga waje Dijah ta amsa ta shigo,
Iya ta kalleta "oh har kincire lallene?
"Eh na cire, ta fad'a tana zama kusa da lya,

Iya ta kalli k'afan lallene da aka yi da yankan salataf yakama yayi jah mai kyau, lya tace ya kwayi kyau sosai yanzu sauranme?

"Auty yafannanh tace wai anjima zata kumamin Dilka Gobe in Allah ya kaimu zatamin zanen bak'in lalle, Iya ta gyad'a kai "yayi kyau Yanzu muka gama waya da uwanki Gobe Sadiya zata maida ke Gida, Sai ki gama duk abunda zakiyi a yau Goben sai ta miki zanen lallen da sassafe,


Nidai nayi iya baki k'ok'arina wajan nusar dake zamantakewan aure Kahadijah,

tun zuwanmu kullum in muna zaune na dinga.miki kenan, gasu Yafannah suma sundage sosai wajen fad'akar dake,
shawarata dake ki d'au abun da ake gayamiki, ki bi Mijinki dan shine Aljannahnki ba Ruwanki da Nafisa, inta takaleki ki tura mata aniyanta sannan ki dage da Addu'o'i karkiyi wasa dan Nafisa Gubace sai da Addu'ah, kinji ko? Ki rik'e ibada dan shine Ginshik'inki, banda wasa, tashi kije kicigaba da kimtsawa Khadijah Allah ya Albarkace Rayuwan Aurenku yabaku zuri'a mai Albarka,


Asanyaye Khadijah ta tashi ta nufi bed room zuciyanta sai bugawa yakeyi da k'arfi



Tabbas Dijah tasan Allah ya kawota cikin zuri'a da suke sonta da k'aunanta dan a daren Ranan duk ta inda ta zaga acikin Gidan kowa da irin Nasiha da fad'akarwan da yake mata gami da tsaraban danginsu Humra da turaren Wuta,

Tun Asuba Yafannah ta yarfamata Zanen Lalle mai tsaban kyau suna gamawa ta fara tsantsaramata kitso wanda su kayi tsagun da Allura, suna gamwa tashiga wanka duk a peart d'in Yafannah, tana fitowa ta turarata da turaren tsuguno sannan ta Ratsamata kwalliya na gani na fad'a, Yafannah ta mik'omata wata d'anyan shadda sabuwa dal wacca lya ta saya taba ma Baba gwani k'anin Yafannah ya watsamata aiki mai tsaban tsada da kyau,


Wayyo Yafannah sakin Baki tayi tana kallon Dijah da take jin Rashin dad'in Rabuwa da Yafannah dan ba k'aramin dad'in zama da ita tayiba, sun shak'u sosai, Yafanna ta gwada mata Son da ko Bintalo sai dai haka,


***********
"Kb tun Ranan nake binka cewa zamu tafi Maiduguri har yanzu bakacemin komeba tafiyan namufa jibine,

Kb dayake shirin shiga Mota cikin Ginsan Maganan yace "Nafisa Sai kindawo Allah yakiyaye, yana k'ok'arin yima motan key ta rik'o Hanunsa, "Haba Sweet bakason inyi Nisa da kai ko? Wlh nima dolece da ba indazanje,

k'wace Hanunsa yayi cikin nata yana watsamata Harara,
"kin iya magana kaman gaske da kike tare dani d'inma me kike tsinanamin common Abinci wannan bakisan Ki girka kiba mijinkiba, lafazi mai dad'i bayi fitowa abakinki sai in kud'i kike nima, inasane da yawace2 da kikeyi kawai na zubamiki ldone, A sannu zan d'auki mataki akanki,

"Haba Kb wai meyasa kake min hakane? Yanzu duk k'ok'arin da nakeyi maka baka gani? To yaushe zaka ban kud'in Mota da na tsaraba? Kasan har ankonmafa banyiba,

"Abunda kika iya kenan wannan shine Hud'uban da akamiki inkinzo Gidab Multi Milonia Kb,

ya zabaga mata harara yayi ma Motana key ya fita,

Tab'e baki tayi cikin rashin gano maganan da ya yab'amata ta shiga ciki tana fad'in oho sai dai ka bayar d'an rainin hankali duk mak'alemin da kake ajiki bai ishekaba sai kamin wani gorin banamaka Abinci, Zan tafi ai zanga wanda zata dinga rage maka Dare, dai2 indawo kayi hankali,


Mayafinta ta d'auka kai tsaye Gidansu ta nufa, nan ta samu Mamanta tana shirya kaya a Kwati,


Tana zama Mamanta tace "dama yanzu nake Son k'iranki d'azu Dadynki yake cemin wai Angama Bincike akan Meena angano ba ita tasa poising d'innanba, yanzu ana nimanmu Ran Lahadi,

Nafisa ta yatsina Fuska "Dai2 Lahadin ai Boka yagama aiki akansu, shegu matsiyata Maman tayi dariya Rabu da tsinannu nace Allah ya kaimu zasu gani, dukansu suka kwashe da Dariya,

Nafisa tace "yauwa Mama inaso Boka yaba ma Kb Maganin sam inaga yana da Matsala dan baya iya yin Sex sai dai ya dinga wani jagwalgwala Mutum, wlh yanada Matsala,


Maman tace "iko Allah daman Can haka yake ko daga Bayane?
"Ni tun kafin aurenmu ma inamasa kallon haka, Shiyasa duk karuwancin wancan banzan yarinyan har suka Rabu bai tab'a kusantantaba,

"Ke haba kin tabbata bai tab'a kwanciya da itaba?

Nafisa ta had'e Rai kaman wanda aka gayawa mutuwa tace "Cab Wlh da ya tab'a kwanciya da ita Mama Mutuwa zanyi, Dan ni kad'ai akayi Kb banda wata banza ni nan nizan haifar masa 'ya'ya Mama Boka ya sake ban Maganin da zan dinga rikitashi ya mance da akwai sauran Mata Aduniya,

"To wai wancan Maganin da aka baki bakiga aikinsabane? "Nagani karkiga yanda ya rud'e a first 9it d'inmu ya dinga Surutu daga bayane dai sam Baya iya Sex d'in,


"To karki damu zamu karb'o wani ni nafi damuwa ma da naga kinsamu ciki wlh,
Haka sukayi ta hiransu na son kai da Son Zuciya, har suka Rabu,

************

"Anma Abokina ba ka ganin Khadijah tare suka tafi maiduguri da Iya?

Da sauri KB ya d'ago ya kalli Habib, Sani ya d'ora danima wlh hakan nake zargi dan Ranan da lya ta tafi Ranan naxo da na tambayi Mami ina Khadijah sai cemin tayi bata nan tun daga Ranan bansake ganintaba inna Tambayeta sai tace min kawai bata nan,


KB ya gyad'a kai cikin Gamsuwa yace "Na yarda Anma meyasa baku tab'a gayanin hakaba? Wlh sam tunanina bai kawo hakaba, jikinsa na b'ari

Ya bud'e mota da Sauri yana fad'in na tafi, Sani yayi saurin rik'oshi Kb kanitsu Zamu tafi tare Har Gidan lyan,

Kb ya k'wace hanunsa "Barni kawai zan tafi ni d'aya indawo da Matata, Sani yayi ta magiyan yabarshi su tafi tare


Bai kuma sauraransuba ya shiga Motan da niyan zuwa Maiduguri, ya fita, Nan suma suka shiga motan suka Bi bayansa da niyan komawa gidanjensu Suana masa Addu'ah.

Dai2 kwanan Da zaibar Layin Gidan Mami Suka had'u da Motan su Dijah Rashin Sani har d'an kaucewa yayi ma Motan suka wuce kafin shima ya wuce dake bak'in Glass ne dasu dukansu ba wanda yaga wani, Ahaka ya d'auki hanyan Maiduguri da zumman d'auko Matarsa,

Yayinda ita kuma Matarsan ta shiga Gidan Mami Cike da Farin ciki ta fad'a jikin Mami,




*Allah sarki KB Allah dai ya kareka a hanyan Maiduguri* 😭😭😭😭😭



*Ummu Fatima ce* 😘
[9/19, 6:31 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣3⃣


Sannu ahankali yake tuk'i a hanyansa ta zuwa Borno, aransa yana Ayyana yanda zasu kaya da Wacca zai d'aukon dan ya lura ta d'au zafi dashi, duk da baisan Laifinsaba,



Kusan Magriba ya shiga K'waryan Maiduguri, kai tsaye ya danna Hancin Motansa cikin Unguwan Ngroji, ya isa K'ofan Gidansu lya lokacin an Shiga Sallahn Magriba a k'ofan Gidansu yana fitowa daga Motan ya d'aura Alola ya shiga Masallaci,




Iya tana zaune akan Sallahya tana Azkar ya shigo da Sallamansa, Ta Amsa tana binsa da Kallon Mamaki, har ya samar ma kansa Wajan zama,


"Kabir kaine da darennan? Ya shafi Sajensa, yana Murmushi,

"Bakin Gudo abayanaba keda kikamin Alk'awarin Sai na dawo ki taho kawai nadawo naga Wayam,

Iya tashafa Addu'an da takeyi Gami da cire Hijab tana Murmushi,

"Dana biyemaka da Bandawo Mahaifataba, da yanzu inacan, kazo Maganan Campaninkane ko? Sarkin Campani,

Kalle2 kawai ya shigayi kaman Mai niman wani Abun ba tare da ya Amsataba, Zuciyansa a cunkushe, Gani yake kaman ba nasara.

Nan Mutanen Gidan suka fara cika d'akin daga masu zuwa Gaisuwa sai masu kawo masa Abin sawa abaki,


Har aka k'ira lsha'i Yana fama da jama'ah ad'akin lya Har yanzu kuwa dube2 yakeyi baiga wacca yake nimanba, Cikin sanyi Jiki ya tashi suka shiga Masallaci,

Tun fitowansa yake cigaba da Amsan Gaisuwa Daga Bisani yashiga,

Bai samu lya palour ba, Dan haka yabita Bed room cikin zumud'i dan yasan anan zaiga Dijah, inma tak'i fitowane d'azun,

Saidai abunda ya k'ara rikitashi, shine Ganin lya ita kad'ai kwance kan Gado tana waya,

Ya tsata yana k'arema d'akin Kallo sam baiga wani abunda yadanganci Dijah ad'akinba, nan zuciyansa ya d'anyance da Tunani iri2.

Yanashirin fita ta ajiye Wayan tana fad'in "Dawo kaci Abinci tun d'azu na aika ayi k'iranka dan nasan mutanen naka baxasu barka kashigo da wuriba, musammanma sun kwan biyu basu gankaba, ta fad'a tana jere masa kayan Abinci kan shinfid'an da tamasa,

Zama yayi kan shinfid'an gami da tank'washe k'afa ya bud'e Abincin yana dubawa,

"Kai lya Wlh najima Rabona da Tuwon Biski, lnaso anma Mami bata cikayiba,

Iya tayi Murmushi Tana kallonsa Batace komiba, Saima mik'ewa da tayi dan kawo masa Ruwa,

Duk yanda yaso ya share yaci Abincin kafin yayi Maganan Dijah kasawa yayi, ji yai baxai iya koda loma ba sai yaji labarin Dijah,

Ya d'ago ldo araunane ya kalli lya, "lya wai lna Mata tace? Yayi tambayan batare da yashirya yiba,

"Matarka kuma agidannan?

"Eh lya Dan Allah karkicemin batanan kinji, ancemin tare kuka xo da ita,

"Tabbas tare Mukazo anma inaga kana cikin Yola ta shiga, Ma'ana inaga kana fitowa ita kuma tana shiga,

Zuru kawai ya mata da ido yana kallonta ko k'ifta idon yakasa, Zuciyansa na masa zafi Sam shi baiga laifin da yayiba da ake ta masa Horo haka Akan Khadijah, Dafe k'irjinsa yayi ya kalli lya da idonsa da suka canza daga farare zuwa jajaye, cikin shak'ek'k'iyar Murya yace "Inama Mutum yana iya cire wani abu a zuciyansa da Dahanuna zan yakice Son Khadijah inhuta tunda ku bakwa sona da ita, Wlh nayi2 in hak'ura da ita Nakasa pls lya kisa baki ki taimaka kiyi wani abu akai, kada kimin haka nasan kinsan inda Khadijah take kitamka kibani ita, ya karashe kaman zaiyi kuka,


Cikin jin tausayinsa lya tace "Kayi hak'uri Muhamdu Kabir, Da bamu Sonka da Khadijah ai baza'a aura maka itaba, Ka koma Gidanka zaka sameta lnsha Allah,

Ciza lips d'insa kawai yayi cikin takaici dan aganinsa itama bakinsu d'aya da Mami Ashe haka So yake?
Ya tambayi Zuciyansa ahankali kuma ya tashi ya fita bai kula da k'iran da lya take masaba, ya nufi Makwancinsa, Ba yadda bai Soba ya cire tunani aransa Anma ya kasa, Wayansa ya d'auko ya bud'e Missed call d'in Nafisa nan take yak'irata, yasanarda ita tafiya ta kamashi sai Gobe zai dawo, Mimirna tayi dan tasamu daman zuwa Gidan Meena Gobe da sassafe,


**********
Da Misalin k'arfe Goma Na safe 'yan jere suka Dira a gidan Kabir,
Basuyi mamakin Rashin ganin Matan Gidan agidaba, Kasancewan sun san Halin yawonta,


pert d'in kusa Da KB akayi Jeren Da Mami ta kashe Mak'udan kud'i Wajen sayansu,

Kafin la'asar sun gama tsara komi kama daga kitchen palour, da Bed Rooms,

Su kansu masu jeren Sun yaba da yanda side d'in ya

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment