Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 3⃣5⃣



*Nafisa*
Tunbayan da Kb yalallab'a Nafisa ya Maidata Gida, a Farfajiiyan Gidan ya hango Alhaji ya'u da Kila suna tattaunawa da Alama Maganan nasu Na sirrine.

Tare suka fito da Nafisa tashiga ciki shikuma ya isa inda suke azaune, tunkafin ya isa yaga yanayin Dadyn nasu ya canza sai mammatse ido yakeyi kaman Mara Gaskiya.

Kujeran da yake gefen Kila yajawo yazauna, yana Fuskantan Dady, yad'anyi k'asa da Kansa suka gaisa, ko kallon lnda Kila yake baiyiba yayi ma Dadyn Sallama ya fice, aguje ya figi Motan ya bad'e wajan da K'ura Maigadi ya bud'e masa yafita Alhaji Ya'u wanda yabi Motan da Mummunan Kallo ya dubi Kila.


"Anyah Yaronnan bai fahimci wani abuba? Shiyasa nace maka inzakazo wajena kadinga b'adda kama karink'a yinshiga na Mutunci yanda bawanda zaiganka awajena ya zargi wani Abun.

Kila ya kece da Dariya yana nuna Alhaji da Hanu "Alhaji ai kamala Afuska take ba arigaba lndai dan wanna banzanne da yazo yana wani Hura Hanci k'amshin Mutuwa ya jiyo, karakadamu tunda ya gagari Bindiga bazai gagari mai kwana Abuzuba.

Murmush Alhaji ya'u yayi sannan ya mik'e yana gyara Babban Rigansa, ya kalli Kila

"Ni zanshiga ciki Kila zan turo maka Kud'in kayi iya k'ok'arin ka komi yazama Normal kar asamu wata Matsala ko kad'an ne.


"ai Alhaji wanna karon Ko Kabir bai bak'unci Lahiraba, Malam Mai Buzu zai nakasashi yazamo bashi da Amfani, daga Haka ya shige Mota, Shikuma yayi cikin Gida.


Nafisa Kuwa tun fitanta a Motan Kb da kuka ta k'arasa Cikin Gida lokacin Mamanta tana kitchen, jin kukanta ne yasa tafito bashiri, tafara Tambayanta, tana kuka tana dukan Kujeran da take zaune take fad'in "Mama Kabir da Maminsa sunci Amanata duk jiransa da natayi yatashi Abanza, Aure! Aure
Akamasa, da sauri Mamanta ta Rufe mata Baki, "yanzu sai da akasamu Munafukin da ya gayamiki wannan Maganan, to bud'e kunnenki kiji, Kwanaki Dadyn ki yazomin da zancen wai... wai... Yaje wajen.... Fatima...take cemasa wai... Akwai wata yarinya..Aliya. da .. Iyayenta... Sukazo suka sameta.. Wai zai aureta... Ke intak'aice miki dai yanzu ba wannan maganan tuni naje wajan ... Malam anwatsar da zancen dama tana da saurayinta wai bayi da san'ane amma yanzu Ita Uwar kad'ad'in Fatima tasama masa aiki a Campanin Sugern Kabir.

Ki Kwantar da Hankalinki Kabir nakine ke kad'anki.

Nafisa ta kuma Rushewa da Kuka "Wlh Mami Wannan Bazan 'yar k'auyen da take gidan Matarsa ce, Nan ta kwashe duk yanda Mami ta gayamusu tafad'a.


Cike da tsoro Maman ta Rafka Salati tana tafa Hanu.

Dai2 Lokacin Dadyn ya zauna Fuskansa a murtuk'e yake kallon Nafisa dan yaji duk abunda ta fad'a.

"Nafisa d'ago ldonki kikalleni, Meyasa bazaki Hak'ura da Kabir ba ga samarukanki dayawa suna sonki da aure.

Da sauri tad'ago tana Kallonsa, "Dady wlh bazan iyaba inasonsa wlh sai nakashe yarinyannan kotawani Hali tafad'a tana wurgi da pillows d'in kujeru.

Ganin da yayi tana
Shirin Rikicemasa ne yasashi kwantar da Murya, "ya isa Nafisa inkinason Kabir bazan Hanaki aurensab, amma tunda Abun yazo da Haka zan d'aga aurenku daganan zuwa watanni biyu, sab'anin Sati Ukun da akasa.

Dai dai Lokacin komi ya zama Normal.

Sannan zanbaki abunda zakiba shi kitabbatar yaci, Muddin kinason Yazamo naki ke d'aya, Amma kinsan Hakan bazaiyiwuba har sai kin kwantar da Hankalinki, kinnuna baki damuba, Mamanta ta d'ora da kw'arai kuwa saikin had'a da Makirci, kafin aci Nasara, waye Kabir? Wlh namiki Alk'awari sai kin Mallaki Kabir fiye da Tunaninki.

Waro ldonta tayi tana sharan Hawayenta tace "Wlh zan iya Komeye kuma nima Nafison ad'aga auren harsai wannan Banzan takoma Gidan Ubanta, dan abun kunyanema ace wai na auri Mutum mai mata.

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Washi Gari ya kasance Laraba, wanda yadai2 da Ranan Kamun Sauda, da sassafe tazo dan duba jikin Khadijah, Bayan sun gaisa da Mami afalo kai tsaye d'akin iya tashiga, zaune tasamu Dijah abakin Gado ta jingina kanta a fuskan Gado, Har Sauda ta zauna agefenta bata saniba, saida ta tab'a kafad'anta kafin ta Kalleta, ta lumshe ldonta ta bud'e gami da sauk'e ajiyan Zuciya.

Sauda tace Khadija "Meyasa kikeson Jefa kanki cikin damuwane kinga fa ance dama kina da' matsalan zuciya baki ganin yawan tada ma kanki Hankali da tunanin da kikeyi zai Haddasamiki Motsawan ciwonki?


Sannan yawan Ganinki Hakan Agun Mami ba k'aramin tsahin Hankali take shigaba, Mami ta cancanci sakamako mai kyau a wurinki Khadijah inkiyi la'akari da so da k'aunan da ta nuna miki na zab'inki da tayi amtsayin abokiyar Rayuwan Tilon d'anta guda d'aya, ta tsallake Kaf Matan Familyn ta da na Familyn mijinta, ta zab'oki.

Dijah tasa Hanu ta share Hawayen da yagangaro mata ta gyara zama tana kallon Sauda,

"Aunty Sauda yaushe kika shigo?

"Yanzu na shigo, tun jiya nake sa Ran ganinki bangankiba nayi ta k'iran Wayanki akashe, na k'ira Mami shine take gayamin Abun da yake faruwa.

Ki kwantar da Hankalinki Khadijah kidaina sa damuwa aranki, Yaya Kabir Mutum ne Mai sauk'in kai da sanin yakamata Wlh zaki ji dad'in zama da shi Uwa Uba Allah yabaki Sirika ta Gari mai so da k'aunanki.


Dija tayi ajiyan zunciya tana k'ara Share Hawayen da yake bin Hancinta, tace " yau Mami tace min inna gama Makaranta na zata maidani Gidanmu, Sauda Ni Gidanmu zan tafi.

Wai nice za'ace Matan Kabir? Wlh bani so, Bani sonshi kaman yanda yace bayi sona yatsanane ni, nima na tsaneshi, yaje ya k'arata da Nafisansa kawai.

"Shi yace miki bayi sonki ya tsaneki?

"Eh jiya inajinsa acikin Gerding ina kwance anan bayan ya maidata gida, Shine da ta k'irashi awaya, yake cemata wai Shi dama tun asali ya tsaneni baya sona, lta zai aura. Ta k'arasa maganan tana sharan k'ollan da suka gangaromata.

Kuma nasha ji yana cewa bazai tab'a son wata mace aduniyaba bayan Maminsa, ko aure zaiyi to badai dan soba, wai shi bai ma yarda akwai wani soba bayan na d'a da Uwa.


Sauda tayi Murmushi "Habib yabani lbrn Irin Game d'in da kukayi tayi da Kbn naki tun farkon Had'uwanku, kuma duk games d'in ke kike Nasara k'arshe Har ya hak'ura, ya sara miki, Mai zai Hana ki Kwantar da Hankalinki Ku buga Game d'in k'arshe kigani na tabbata zakiyi Wining ni zan taimaka miki sosai Khadijah ki kwantar da Hankalinki, Zamanki Gidan Mijinki shine Kwanciyan Hankalin iyayen naki, kidaina Kallon wata Nafisa kedai ki Fuskanci Rayuwan Aurenki kawai.

Ko baya sonki yanzu, agaba zai soki, shi da Kansa wataran zai k'aryata furucinsa, zai yadda cewa bayan son d'a da Uwa Akwai wani Salon son na daban.

"Nifa Bana sonsa.

"Banyarda ba Khadija, Sau
nawa kike bani Labarin Abunda kike ganin Sunayi da Nafisa?
Inbaki sonshi ina Ruwanki?

Dijah ta turo baki "nifa Haushi kawai suke bani ai abunda sukeyi ne sam bai daceba"

Sauda ta kwashe da Dariya yanzu dai zo muje ki karya, dan Mami tace min baki Karya ba, Ga mai Gyaran jiki can tana jiranmu tare za amana komi k'arfe 4:00 za'aje kamun a can Distinatoin Hotel, kisaki jikinki wannan yana daga cikin plan d'inmu zan gaya miki sauran, ta rik'o Hanunta suka fito falo,

Mami tana ganinsu ta fara tafa Hanu Oyoyo Yarinya na ta warke, tana isa ta fad'a ajikinta tana Murmushi,

Mami ta Rungumota ko kefa My Khady, Amma har yanzu jikinki da zafi, barin kawomiki abun karyawanki ki karya kisha Magani da sauri Dijah ta mik'e "a'a Mami zan d'auko da Kaina.


Tea kawai ta Had'o tazo ta zauna tana d'an kurb'a ahankali.


Kabir ne yashigo Cikin takunsa na lsa yau shigan Manyan Kaya yayi na sky Blue d'in shadda sai Maik'o yakeyi ya Murza Hula zanna Bukar wanada aka sak'a da zare sky blue da dark Blue idonsa Manne yake da Farin Glass wanda kake iya Ganin fararen ldonsa fes daga tawajen glass d'in, ga wani Dadda d'an k'amshi da yake tashi ajikinsa.

Kallo d'aya Dijah ta masa ta yi k'asa da ldonta k'irjinta na Bugawa.


Fuskansa d'auke da Murmushi ya Zauna kusa da Mami dai2 lokacin ldonsa ya sauk'a kan Dija da take kurb'an tea ahankali sai tururi yakeyi, aransa yana mitan k'in bin dokan Likita da takeyi dan yana cikin dokan da akamata banda cin abu mai tsaban zafi.


"Inakwana yaya Kb Muryan Sauda ya ziyarci Kunnensa, ya dawo da Kallonsa gareta yad'an tab'e Baki Ashe dama kina nan ne Habib yake min wani dabara, Biyoshi kikayi dan tsaban Rashin Kunya ko?

"tad'an dara tace "Haba dai yaya Kb nanfa Gidanmunne kaga shi ya biyoni ba nina biyoshiba, watk'ila yaje Gidane akace masa lna nan,
Hararranta yayi "to sannu parot Inba biyoshi kikayiba me kikayi? Shida ya kwana anan, keda yanzu kika zo waye yabi wani?

"Wlh Bani daga cikin masu Bin maza gidajensu yaya Kb, wasu matan fa ma tarewa sukeyi a gidan samarukansu basu da shamaki a ko ina hatta da d'akin sa kullum suna nanik'e, "Hey Is Ok ya katseta yana Muzurai "Mawa kike mai da Magana haka?

Tana dariya tace "Sory yaya na.

Mami da take ta k'ok'arin Maida Dariyanta tace "Kabir ince aiki zaka tafi? Ai gara ka tashi kar ka makara.

Dija kam d'an Murmushin gefen baki tayi ta Mik'e da Cup d'inta, tashige d'akinta, Saida tasha maganinta mai gyaran jikin ta fara da lta, Suna cikin yi Sauda tashigo tana dariya,

Tace Khadija tak'ira Jamila ita zata musu kwlliya.

kafin yamma an yarfa musu tsantsararren Lalle da kitso, Jamilace ta tsantsara musu Kwalliya.

Dija tafito cikin fitet gawn d'in codeless pouple mai Silver, Head Sillver aka nad'a mata takalmi da Jakanta ma Silver, sark'a da warwaranta ma Silver. Tafito kenan Bintalo tashigo falon Baki Bud'e Bintalo take binta da kallo har ta k'araso inda take, ta rik'e Hanunta tana dariya Haba Matan Yaya Sani irin wannan Kallo.

"Ba dole inkallaba Khadija kinganki kuwa?

Bafa ke bace Amaryan irin wannan zak'ewa,

"Amaryance tabani wannan Dama, tafad'a suna zama abakin gadon lya,

Bintalo ta kalleta "Dija kinyi ciwo ne?

"Mhmm me kika gani?

"Naga Kind'an ramene.

"zamuyi maganan, yanzu Muje ki gaida Mami Bintalo Kinga ana ta tafiya, Af! Sory Aunty Binta zance, tana dariya suka fita,

4:00 dai2 su Dijah sukafito ajere da Amarya Sauda ba k'aramin kyau tayiba komi nata pink ne, Daf da zasu fito aka k'ira Dija awaya, haka suka fito su Uku agaba Amarya da k'awanta agefnta d'aya gefen kuma Jamila sai Dijah da take bayansu bayanta kad'an kuma Bintalo ce sai zabgamata Harara takeyi jin tana waya da Auwal, sai sauran jama'a dasuke tashiga Motoci, haka suka fito har bakin gate.

Kabir yana tsaye ajikin Mota shida Ango shigan Ash d'in dakakkiyar shadda Wanda Abbane yayo musu ordensu daga Dubai, sukayi hatta da aikin shaddan iri d'ayane huluna takalma duka iri d'aya, ba k'aramin kyau sukayiba, Gefensu Sani Suna d'an Magana akan yanda zasi tsara tafiyan sai Abokansu dasuke gefe suna bada Umurnin Motocin da za'a shiga.

Sani ne yayi ma Bintalo alama da tawagan Amarya Motansu zasu shiga.

nan suka nufi Motan d'agowan da Dijah tayine sukayi ldo Biyu da Kb wanda tun fitowanta ya murtuk'e Fuska yana Kallonta, abayansu ta tsaya tana cigaba da wayanta.

Sani ya bud'e Musu Mota suka fara Shiga, ahankali tad'an ti taku biyi tayi baya sannan tajuya ta nufi Motan wani abokin ango da tun fitowansu yake mata tayin Mota datazo tashiga su tafi.

Ke Khadijah! Taji an k'irata tana juyowa Sani yamata nuni datazo tashiga Motansu, sai da tad'anyi gajeren tsaki ta fara zuwa, Haryanzu ldon Dr Kb yana kanta k'are mata kallo yakeyi tundaga sama har k'asa, cikin matsanancin takaici nafarko kasancewanta Faran Mace anzana mata Bak'in Lalle daga can nesa shi zai fara d'aukan hankalin mutun zuwa gareta, na biyu Rigan jikinta ba k'aramin manneta yayiba ga Khadijah da Sharp na bugawa amujalla sanna ga d'an gyalantanma akafad'a kawai ta ratayashi, Uwa uba gawani Kwalliya da akamata nafad'a na Musali takalmita mai tsinine Sosai, sai k'ara yake yi duk inda ta taka, Ga Khadijah da wani irin tafiya mai matik'ar d'aukan Hankali, Ga wani sassayan turare da yake tashi ajikinta, kasancewan shine afarko tafi kusanci dashi a tsayuwan datayin, Har cikin k'wak'walwansa yakejin K'amshin.

Gani yake duk mazan gurin ma ita kad'ai suka zuba ma ldo, Sannanma da wa take lrin wannan waya da tun fitowanta har yanzu bata gamaba.??

Daga d'an nesa dasu tace ma Sani "Yaya Sani nayi mantuwane barin je ind'auko, yace "Ok barin kaisu sai indawo inkaiki da ragowan k'awayen naku, juyawa tayi batare datace komiba tayi cikin gida, Habib yad'an dunguri Kb "Man yadai?

"Mtss Dr Kb yaja guntun tsaki,

"zo mushiga Muje inyaso sai mudawo mu d'auketa Habib yafad'a da sigan zolaya.

Hararansa kawai yayi yashiga, Khadija data ke mak'ale tana lek'osu tana ganin sun tafi tafito tashige Motan Abokin Habib suka tafi.



*Anayinta Fa* πŸ€”
*Wai meke damun zuk'atan Ma'uratanne?*

Ummu Fatima ceπŸ€—
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬

*_Soyayya dad'i idan har dani zakuy inbaku wazana kalla Abayan Raiiiiiiii!!!!!!!!_* 🎢🎢🎡🎡 πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½
_Gaskiya ina shiga matsanancin farin ciki ldan aka k'ira wayana nad'aga akacemin Masoyiyarki ce mai bin Noveld'inki, ................. Wannan Kalma yana Matik'ar Burgeni ko karantawa nayi nakan shiga cikin shauk'in kalma saboda haka na sadauk'ar da wanna page gaba d'ayansa gareku masoyana, Masu k'irana awaya da masu min Massage wlh nima ina Son ku Fatana a Kullum shine Allah ya sadamu daku a Firdausi_ 🀲🏻
Allah yabar k'auna🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 3⃣6⃣


Kabir suna tsaye shi da Abokin sa Nura suna d'an tad'awa.

Gani yayi Nura ya sake baki yana kallon wani guri, ganin haka yasa Kabir bin inda yake kallo, Dijah yagano ltada Jamila suna shiga cikin Hotel d'in, taku take d'ad'd'aya mai kama da rawa.

Kabir ya juya bayansa baiga Motansa da Sani yatafi dashi dasunan d'aukotaba, tabbas bai kai ace har ya isa yadawoba.


Yad'an furzar da lska yana Kallon Hanya waje,
Nura yace Muje naga amfara Shiga,
Nan suka rufa musu baya, dai2 Lokaci aka saki kid'a nan aka fara jera Amarya da Ango da wa inda zasu bi bayansu, Gani da Kb yayi ana shirin had'ashi da Dijah ne yasashi yad'an kauce a wajen Yayi gefe yana waya.

Wani magigincin k'amshi yaji abayansa, Ahankali yajuyo yasauk'e idonsa akan Nafisa, juyawa yayi yacigaba da wayansa, sai da yagama yasake juyowa.

Tana tsaye sai wani mayaudarin Murmushi takeyi Rintse idonsa yayi ya bud'e cike da Mamki, dandai yasan Fushi takeyi dashi ko jiya da dare daya k'irata k'in d'agawa tayi, Sannan yasan ko suna shiri sam batashiri da Habib bare uwa uba Sauda da datake zargin wai saudan tana sonsane dan haka tatsaneta.

Cike da kissa da Makirci ta langab'ar dakai "sweet kaman bakayi farin ciki da ganin tauraruwan kaba.

Yad'anyi Murmushi, "no nadaiyi suprised ne daganinki sam banyi zaton ganinkiba By this time,

"Why?

"Cus nasan kina Fushi dani ne, akan laifin da ba nawaba.

Tad'an k'ara narkar da ldonta, "Wlh sonkane yasa sweet nashiga damuwa dalilin kishinka, to amma daga baya nayi tunani, Kuma Mama da Dady sunmin fad'a, bawanda ya isa ya wuce K'addaransa dan haka na mik'a Wuya sai dai inason kamin Adalci Kabir kar ka Wulak'antani lnasonka sonda ko kaina banayimasa haka. Tafad'a da Sigan makirci Kaman zatayi Kuka.

Gaba d'aya tagama Sakar masa da gwiwa, dan bai yi tsammanin haka daga garetaba, yanda suka rabu dak'yar.

Wani lrin farin ciki tashiga ganin Hak'anta yana shirin cimma Ruwa.

"Naga ana tashiga kaikuma kana gefe.

Ya d'an yamutsa Fuska dan har yafara manta abun da yasashi fitowa,

"Bazan shigaba ne yasa natsaya anan.

Ta zaro ldo haba dai? Kana babban Aminin Ango? To inbakashigaba su waye a High table d'in? Kazo kawai Mushiga mune a sama ai.

A Jere suka jero suna taku sai taunan Cingum takeyi k'as k'as suka shiga, har yanzu shirya masu taka ma Ango da Amaryan baya akeyi kasancewansa Babban Aminin Ango anbarmasa wajansa shine abayan Ango, tuni Sani yasanar ma Masu shirin cewa Kabir da Matansa Dijah zasu shiga, shiyasa ma akahanata shiga tatsaya jiransa.

Suna lsowa wajen yayi dai2 da Juyowan Dijah ranta ajagule dantsarin da akayi nacewa ita da Kb ne zasu shiga sam bai mataba, ldo Biyu sukayi da Nafisa, kowacce sai da K'irjinta yaba da Rass, Nafisa kam har wani jiirine ya d'ibeta dan sam bata tsammaci Khadija bace tundaga nesa ta hangota amma bata kawo ita bace,

batayi tasamanin yarinyan kalabace haka, Amma dayake ta shiryo fad'an ne cikin sunk'uru sai ta d'auke kanta ta mayar kan Kb tana Murmushi.

Haka yake ga Dijah wani irin bak'in ciki da ya tokareta saida ta dafa Jamila da take gefenta suna Magana da Sauda k'asa2 zamewa tayi gefe jin wayanta na Ringing can wajan Amsa wayan ta Lalace har suka shiga, ita kad'ai ta bi bayansu dai2 Lokacin aka saki kid'a, Akaba ma Amarya da Ango daman su fito Fili don anason ganin Masoyansu, Dijah ta shiga Fili ta bud'e post d'in ta da Mami ta cikamata shi ta d'auko Bunch d'aya na y'an Dubu2 tafara Lik'a Ma Amarya, Nan Dj yafara sanarwa, Babban Abokin Ango yafito shima ya nuna tasa Bajinta dan wannan k'awar Amaryan ta nuna son Kai dayawa, Ma k'awarta tafi yin Mannin.

Nafisa da ldonta yagama Rufewa da Bak'incikin Ganin Dijah ji take kaman tafito tashak'eta, ta kalleshi "Kb yakamata ka Tashi mushiga Filinnan mun gwada ma k'ananan k'wari cewa Wannan ajininmu yake, inma anyi awajenmu aka dangwala, cikin Rashin fahimtan inda zancentan ya nufa, yace ba inda zanje.

Magiya ta shiga masa har ta shawo kansa suka taso Hanunta sak'ale da nashi suka fara manni ma Ango, cikin dabara Dijah tazame tabar Filin, tafita can waje dan Amsa k'iran Auwal.

Zaune tasameshi akan Mashin ya Rafka tagumi, Sallamanta ne ya dawo dashi, ya Amsa yana mata wani mayataccen kallo ji tayi gaba d'aya ya d'aureta da Jijiyan jikinta, ta ware mayafinta ta Rufe jikinta, tace lna Wuni Auwal, yasauk'e Ajiyan zuciya yace "Haba Khadija kusan Awana guda anan, sai yanzu aka tuno dani?

Khadijah lna sonki, ki dubi girman Allah kidubi son da nake miki, ki sanar dani matsayin soyayyanmu naga kina niman kijefa zuciyata a wani Hali pls Khadija karki b'oyemin komi.

"Auwal dan Allah ka ajiye maganan wata soyayya tsakani na da kai, yanzu duk babu ita baran tab'a mance taimakon da kamin ba tafannin Karatuna inason muyi tsaftataccen Alak'a kuma Halacacce nida Kai.


Cike da Mamaki Auwal yake kallonta, Sannan ya juya ya Kalli Motan Kb da yake perke a Gefesu,
"Khadijah Wannan wanda Ranan naganku dashid'innane ko?
saurayinkine ko? Naga Alama don yayi niyan salwantar da Rayuwana, Nayarda da Maganan Abokaina dasuke gayamin cewa ke kalan Matan manyane ba irinmu 'ya'yan Talakawaba..

''Haba Auwal kadaina fad'in haka itafa soyayya Rayayyiyace kuma zuciyanta yafi na d'an Adam tsada, kud'i baya sayanta, Arashin Sanin ni wacece na Amsa tayin soyayyarka yanzukuma dole in ajiye badon kowaba, badon komiba, sai dan tsoron sab'ama Mahaliccina, kayi Hak'uri Auwal.

Gaba d'aya jikin Auwal yayi sanyi dajin kalamnata yasan koma meye tanada Uzuri mai k'arfi, dan haka yayi shiru yakasa cewa komi, tana shirin yi masa Sallama ta hango Mutuminta, ya kafa ma Wurin Kallo, Nafisa tana gefensa cike da Farin cikin ganin hakan duk da bataso Kbn yanuna wani damuwaba sai K'ok'arin janye Hankalinsa takeyi Abu yagagara, kalma d'aya biyu ne yake masa yawo akansa, _"Matarkace ta Auren Sunnah Khadijah bata shigo gidannanba sai da lgiyan Aurenka ya Hau kanta,_

Wani b'angarenkuma na tuno masa maganan Dijah Ranan da Auwal yazo ya tambayeta waye wannan tace masa _"Saurayina ne_ cikin Zafin nama ya shiga Motansa cewa yayi ma Nafisa ina zuwa daga nan yayi ma Motan Wani lrin key, ya fice Aguje Badon Allah yasa tayi saurin Matsawa ba, watak'ila, daya cire mata hak'ark'ari, dai2 Lokacin Jamila ta iso Gurin tace mata wai taje lnji Bintalo tana tafiya, Jamila ta kalli Auwal, Ashe Khadijah tana da Aure? Cike da tsoro Auwal yazaro ldo.

"Wlh matar Aure ne kaga wannan da ya wuce kaman yabanke kan? Wlh shine Mijinta.

Afalo Kabir yasamu Mami da Wasu Mata ya wuce Bed Room, Ganin yanayinsane yasa Mami bin Bayansa, zama yayi Akan kujera ya bud'e frich ya d'auko goran Ruwa mai tsaban sanyi, saida ya kusa shanyewa ya ajiye gami da jingina Kansa da Gini, yana mai tuhuman Kansa wai Shin ina Ruwansa da Sabgan yarinyan ne?
Meyasa yaji kaman yadamu da Abunda takeyi?

"Dole ka damu tunda ance wai da lgiyan Aurenka akanta, duk Randa Akamayar da lta lnda aka d'aukota shikenan taje can tayi yanda taga dama, mtss yaja gajeren tsaki wanda yayi dai2 da shigowan Mami, kallo take ta binsa dashi har ta zauna, tace "Yadai Kabir? any problem? Rausayar da Kansa yayi yana d'an dube2 yace Wlh Mami yunwa nakeji,

"Af! To bari akawo maka Abinci mana,

Har ta mik'e shima yatashi no Mami Barinje indawo, kafin,

Tad'an kalleshi cikin son Harbo Jirginsa, Sannan tace "lna lbrn Khadija?

Nandanan yahad'e Rai, ''Tana can Mami Amma bakigantaba lokacin da zata fitaba ko? "Wlh bata da Maraba da 'yar Arna sai sokuwa takeyi cikin Maza, wani Abun Mamaki ma Kaman Hira takeyi da wannan k'azamin data k'irashi dasunan Saurayin ta awajen to inbanda Rashin Hankali Mutum ya wuce Gidansu yaje koraro yana irin wannan.

Cikin son b'oye damuwanta tace "Tuntuni nake tunaninta lokacin Shan maganinta yayi batashaba.

Maza je ka d'auko mun lta yanzu tasha kar tawuce time diin da yawa.



Koda yadawo, Zaune yaganta Akan wani Kujera ita kad'anta ta dafe kanta tana danne2 awaya, d'an Gaba da ita kad'an yayi perking, ya fito lokacin har anfara fitowa, hawa saman Motan yayi yana kallon k'ofan da Jama'a suke Fitowa, ahaka Har Habib dasu Sani suka iskoshi awajen, Suna isowa ya Wurga ma Sani key yana yamutsa Fuska, d'auki wannan Yarinyan kamadaita Gida, yafad'a batare da ya dubi lnda takeba,

Sani yace "Wata yarinya?

"K'anwar Matarka yafad'a atak'aice.

Dube2 Sani yashigayi, ''d'azu kaman naganta anan ko lna tashiga oh?

Kabir ya juya ya Kalli inda take zaune, Wayam! Babbu ita, kallen shima yashigayi bai gantaba.

Azafafe yace "Sani kanimota duk lnda tashiga kamayar da ita, Habib yana Dariya yace "Mutumina yadai kaman tun ba aje nan da canba 'yar manune zata nuna,

Ya murtuk'e yana Had'e Gira, "ka lyama Bakinka kaima kasan bantab'a yin Magana biyuba ince No indawo ince Yes,

Daga kai har wacca kake Magana akantan baku isheni Kalloba Mami ce Ta aikoni, dai2 Lokacin Nafisa ta iso Wajen,

"Sweet mutafi tuntuni nake Jiranka,

Yashafi kansa yana Kallonta "Barin Had'a ki da wanda zai mayar dake anjima nima zanzo,

Tad'an b'ata Rai baga Motanka ba mezai Hana ka mayar dani,

"Wlh Kb Nagama iya bincikena banga Khadijah ba, Muryan Sani ta katse musu Maganan,

Shiru kawai yayi yana ciza Lip d'insa na k'asa yana jujjuya kansa yana d'an dube2, bako Alamanta.

Yadawo da dubansa ga Nafisa da tayi Mugun Had'e Fuska, cike da takaicin jin cewa Khadijah za'a kai amotan shiyasa yace zai had'ata

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment