Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dik da har yanzu bai gane inda ta dosaba, shin tana sonsa koba tasonsa, bata yarda suyi hira ko yaje k'ofar gidansu gudunsa takeyi,

Duk dahaka ya kasa rabuwa da ita don Dijah one in townce kykkyawace na bugawa amujalla duk rugan juma ba "yar data takaita kyau, tana da fasali mai kyau sosai, samaruka da yawa sunyi yunk'urin niman Dija saidai basu samun fuska ladone kawai daya nuna yana sonta bata balbaleshi da masifa,


Lado d'an gidan Hard'on garine Hard'o afualatanci yana nufin sarki, lado yayi zaman Birni dan haka kaf Rugansu ba saurayin da yakishi gayu dawayewa, shiyasama Dijah takesonsa don tanason d'angaye arayuwanta, saidai shiriritanta, yahana lado ya gane tana sonsa, Dondai Dijah ba dai shiriritaba,


Washi gari da dafe Dijah tunda ta idar da sallah take takiciniyar ayyukan Gidansu kamar yadda tasabatayi sharanta fes ta ttara wanke wanke tayi tana kife kwanuka Baffa yashigo da keke da jarkan ruwa akai da gudu tanufoshi tarik'e masa keken tana ta jero masa sannu sai k'ok'arin sauk'e jarkan takeyi Baffa yace "a'a mamata barshi bazaki iyaba, "Allah Baffa zan iya "to barin kama miki, tare suka kama suka juye aranda, ya juya yana kallonta da wutsiyan ido, yana d'aure jarkan ajikin keken tazo tarik'e kamar zatayi kuka

Baffa dan Allah karka koma zamu je mud'ibo ni da Bintalo,

murmushi yayi daman yasan za'ayi haka, sam indai Dijah tana gida bata barin Baffa yayi komi ko itace saitace zasuje suyi shikuma tausaya musu yakeyi amtsayinsu na "ya"ya mata baya son suke wannan wahala,

shiyasa tunkafin tatashi daga barci sai yaje yadebi ruwa yayo iatace, inta tashi tayi tamitan batason yake wahala sunanan.

Cikin sigan Rarrashi ya dafa kafad'anta karkidamu mamata sawu d'aya zank'aro kinga fa zaku tafi makaranta, inkince sai kun d'ebone zakuyi latti amuku bulala, a'a Baffa kabarshi wlh bazu d'ebo ganin tan shirin yin kukane yasashi ajiye jarkan, dai dai lokacin Bintalo tafito donyi musu abun kari, ita kuma Dijah ta d'auki tulu ta tafi d'ibo Ruwan,

Tafe suke cikin Unifoam Riga da wando da hijabi Blue du hud'u kamar yanda suka saba ko ina zasuje Bintalo da ma'u dune agaba Dijah da jebu suna baya hiransu sukeyi harsu ka iso gida su jebune da yarta ma'u sukafara shiga gida sai su Dijah tunda tacire unifom take kwance, inna ta shigo tasameta "Dijah kifita kuci Abinci tund'azu Bintalo take k'iranki kinyi burus, ta yatsina fuska "inna mekika dafa? "Shiinkafa da miya, "nidai nak'oshi tafad'a tana turo baki "mhmm dama nasan za'arina inna tafad'a tana fita,


Sai da tagama kwanciyanta tafito anan tasamu Bintalo tana zaune gefenta kwanon Abincine arufe tabud'e kwanon taga Abici ta kalli Bintalo ina Aaabincina? gashi naci nabarmiki, wani mugun kallo tamata ninema zakici abinci kibarmun dankinrainani, wlh bazam yarda ba kibiyani Abincina, "kefa kikace bazakiciba kuma aigefe naci baduka na tab'aba, "wlh nidai bazanci k'azantankiba saida kika jagwalgwala zaki barmin? Nanfa Rigima yakaure tun Bintalo batakulata har tagaji ta amsa mata ganin da gaske Dijah fitina take nima yasata tashi da niyar barin gurin da sauri Dijah tasha gabanta bainda zakije sai kin biyani Abincina "Dijah kinga kifita ahanyana zan marekifa, wani kallo raini ta mata "basai kimaranba wlh yarinya barganin kinfini tsayi ai baki fini karfi ba, dai2 lokacin inna ta fito daga d'akin Baffa, tana tambayansu Bintalo tamayar mata dayanda akayi

inna ta rik'e Hab'anta da hanunta "Anyah Dijah meyasa kk da fitinane damman tun shigowanku nagano rashin arzik'i a idonki to inda gaske abincin zakici kije kitchin akwai akula kid'iba ta turo baki inna ni wlh nawakawai zata biyani,

Inna takalli Bintalo "kinga wuce kiyi tafiyaanki kibarta tak'arata Baffa dayake d'aki yakejinsu yayi saurin fitowa don in akwai abunda yatsana to kukan Dijah ne

yasan yanzu zata fara don daga jin yanda case d'in yake fitina kawai take nima don inba fitina take nimaba in anyi shinkafa dayake ranta bayaso yawanci gunsa take zuwa yabata gassasun zabi taci da madara ko nono musamman yake ajiyewa sabo da ita,

Hanunta yakamo kai tsaye sai d'akinsa sai da yararrsheta, sannan yabata taci,

Bayan tagama ci yabata wani magani " Dijah karb'a kije

can wajen masu karaya Akwai wacce nayima d'ori dasafe kije kishafamata yanzu kizo muje can gida musa matanshi takarye ke zaki d'orata.


?🌴🌴🌴🌴

*A BIRNI*
Dr Kabir na gano zaune a office d'insa ganin baida abunda zaiyi yanzune yasashi duba wasu tsofffin files da suke cikin drower yajima yana duba wani file guda d'aya dayasha bamban da sauran files d'in watanni kusan 10 kenan daganin mara lfyn case d'inta sereous ne da yakamata ace yanaganinta akai2 to amma gashi sau d'aya kawai yaganta meyahanasu dawowa? To ko mutuwa tayi ras yaji gabansa ya buga daida lokackin sister mena tashigo, tazuba masa ido har ta matsoshi, file d'in yanuna mata "kinsan wannan mara lfyn? Karb'a tayi tana ta dubawa nad'an lokaci tace "Eh naganeta yarinyan bafulatanin nan dasu kazo mai cronic typortdi'nnan ka tuna? Shiru yayi na tsawon lokaci amma bai tunotaba, " sir yarinyannan dai wanda mama jumai tazauna da ita acan E P U, "Gaskiya ban tunataba haka tak'arashi kwatancenta, yakarb'i file d'in yana dubawa, *Khadijah Abubakar maid'ori*



Hahh muje zuwa Dr Kabir πŸ€£πŸ‘πŸ»


*Ummu fatima* πŸ‡³πŸ‡¬ 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡³πŸ‡¬

*ISLAM MY RELIGION* πŸ˜˜πŸ•‹





🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 8⃣



Mai mai ta sunan yake tayi abakinsa ahankali yafara tunota

"ok yarinyannane mara kunyannan wai suna ce mata *Dijah k'aya* tabbas yatuno sabida tsaban haushinta ma baice ma Babanta yadawo da itaba,

Wani dogon tsaki yaja ya ture file d'in gefe cikin takaici yana tuno abunda yarinya k'arama ta masa abunda yakasa mantawa,

Bazaitab'a manta wannan ranaba don tamasa abunda bawanda ya tab'a masa arayuwansa,


Wataranan lahadi da rana misalin 1:00 yana dawowa daga wani Ruga can gaba da Rugansu Dijah,

Inda suke kiwon dabbobinsu tun mahai finshi yana raye yana da garkunan shanu a garin,


Bayan Rasuwansa ne Mami takesa Kabir yaje yadubo su jifa2 awekend,


Tun Ranan monday Mami tace zaije awannan wekend d'in don haka yashirya tun safe yatafi don yana son yadawo da wuri,

bayan yagama duk abunda yakaishi yakamo hanya,


Yana dawowa Da misali 11:00 Ruwa ya tareshi ahanya gangarawa yayi, yayi perking a gefen hanya harsai da Ruwan ya d'auke kafin ya kamo hanya.

Adai2 Rugan juma ya wara idonsa yana kallon garin sosai yanayin garin yamasa musamman ma dayaga yara "yan makaranta suna wucewa har aransa yaji dad'in wannan cigaban da akasamu na karatu a Rugagen fulani,

yana ta kallonsu wasu suna tafiya wasu suna dawowa,

Ahaka ya iso kusa dasu Dijah ita da k'awarta jebu sanye da Unifom da Alama su sai yanzu suke tafiya, suna k'ok'arin tsallakawa,

Dijah batayi auneba Kawai sai jin Ruwan kwata tayi duk jikinta har fuskanta anwanketa dashi, d'ago idonta da tayi ta sauk'esu akan wata dank'areriyar mota,

sai sharara gudunsa yakeyi hankali kwance baisanma yayi wani Abuba,

Donshi baima san ya wuce su Dijah agunba Bin motan da kallo tayi,

Cikin takaici batasanma mezatayiba ji take kamar tabishi da gudu,


Cikin sa'a taga yatsaya ajikin wani shago dake gefen titi zai sayi Rechart cad,


Gyad'a kanta tayi ta nufi wurinshi da sauri Jebu ta kamo hanunta, "Don Allah Dijah kiyi Hak'uri kirabu dashi kingafa
Wannan d'an birnine irinsu ne masu shan jinin nan kirufa mana asiri karkijawomana wani fitinan,

Afusace Dijah tak'wace Hanunta tana masifa "wlh koma wayene shi sai naji dalilin watsamin kwata da yayi,

Alokacin data isa yana loda card awayansa, tasaya agefensa tana kallonsa, tace "Malam kaga yanda kab'atamin Jikina?

Allah sarki Kabir, hankali sa yana kan wayansa sam baima lura da Dijah ba,

juyawa tayi afusace,

Saida yagama abunda yakeyi awajen yanufi inda motarsa take,

Batare da b'ata lokaciba Yakama handle d'in motan da niyan bud'ewa yaji ya cab'a hanunsa akan wani Abun dasauri yabi gurin da kallo kashin shanune da yahad'u da kwacab'in tab'o gabad'ayan murfin motan da glass d'in anshafe dashi cikin matsa nancin mamaki yakebin wuraren da kallo ahankali yad'ago ya kalli gefen damansa, Dijah ce tsaye rik'e da kunkumi tana jijjiga bai kawo komi aransaba ya kalli hagunsa ba kowa awajen sake maida hankalinsa yayi wajen da Dijah take tsaye Dariya tayi tace "kaima kaji inda dad'i, cikin rashin fahimta yanunata da yatsa "kina nufin kice min kece kikam wannan aikin? Cikin isa tace "eh Ramukon Gayya, motarka ai baifi jikinaba tafad'a tana nuna jikinta da Ruwan kwata ya b'ata, cike da tsiwa tayi maganan,

Binta kawai yakeyi da kallo baki bud'e ko k'yafta ido bayayi, ta juya tana tafiya yaji andafashi,


"Ranka yadad'e kayi hak'uri, wlh yarinyan sam bata da dad'i, cikin wani irin fushi had'e da takaici yabi saurayin da kallo, sannan ya kalli hanunsa da yake dumu dumu da k'azanta, yasake kallon saurayin zuciyarsa sai zogi yake masa ganinsa har d'aukewa yakeyi tsaban b'acin Rai,

Muryansa har b'ari yakeyi yace "waye Uban wanna yarinyan?
Me ta taka?
Metake tink'aho dashi?


Saurayin yace "kayi hak'uri yallab'oi kar kasako uban mahaifinta mutumin kirkine wlh da zaiga abunda tayi sai yayi kamar ya had'iye ranshi dan haushi,


"wai ni mahaukaciya ce ko Aljana? KB yayi tambayan azafafe,

*Dijah Bukar maid'ori kenan yarinyace mai Hankali sai dai Akwaita da tsiwa inkashiga hark'anta bata da hak'uri komi kamata sai ta Rama ko ta d'auki fansa*

Inaga tayan motan kane ya watsa mata kwata dan naga jikinta duk kwata zaiyi wiya ta maka wannan abun batare da wani daliliba gaskiya,


Wani irin tsawa KB ya daka masa, "kai kacikamin kunne,
wace ce ita? Dahar zakazo kanamin bad talk akanta?


Dai dai lokacin mai shagon dayake bakin hanyan ya iso da bokitin Ruwa da omo,

"kayi Hak'uri malam zan wanke maka motarka, Nandai sukayi ta lallb'ashi, ya wanke Hanunsa, ya je gindi Bishiya yazauna suka farawanke motan,


Yana zaune awajen yayi tsaki yafi abunda yafi, zuciyansa sai rad'ad'i yake masa amon muryanta, da fuskanta ne yake tamasa kai komo,

Wayarsa datafara Ringing ya d'auko *Mami na* yagani akan wayan ya d'auka sallama kawai yayi ta fahimci yana cikin b'acin rai

Cike da damuwa tace "yadai Kabir?
Me ke faruwa ne?
Kana inane ?


"wlh Mami ina wani Rugane, "mekakeyi ?

Na had'u da wata Nonses yarinya ce nan yabata lbrn yanda abun yafaru, sauk'e ajiyan zyciya tayi,

"Wlh na tsorata danaga har yanzu baka dawoba,
Shiyasa nasamo maka sojojin da zasu dinga fita da kai dan tsaronka fir kak'i, kaga dasu na wajen ba yanda za'ayi tasamu daman tab'a motarka ,

Allah Mami yau sainasa anyi maganinta,

Atsorace Mami tace "Rufa min asiri Kabir banyardaba kasan halin fulani kuwa?

Kar kayardaka kafara,

Barin turo azo a dawo dakai,

Yamik'e yana fad'in no mami basai kinturo kowaba ganinan dawowa,

Duk da sunwanke motan tas harda blech baidaina jin yankyanin motarba

Kud'i ya ciro mai yawa yabasu bai saurari godiyan dasuke masaba ya finciki motan da gudu yabar wurin,

Tunda yake aduniya wani mahaluk'i baitab'a b'atamasa rai irin yauba,

Kodaya iso gida Mami tasha wahala wajen rarrashinsa da k'yar yasaki ransa,

Yanagama tunanin nonses girl d'in inji da fad'a yad'aga file d'in yamayar yadawo yazauna acikin kujera cike da haushi, kamrayanzu abunyake faruwa haka yaji.

Ahaka yaji ana nocking yabada ixini ashigo wani cosmone yashigo "Tanka yadad'e kana bak'o, "ok tambayeshi wayene? Jim kad'an yadawo, "wai yace ace maka Alhaji ya'u ne k'anin Alhaji Mahmud, dukda maganan yabashi mamaki da kansa yatashi ya bud'e k'ofa cike da girmamawa, yace "Bismillah Dady shigo,


Cikin isa da izza yashigo Kabir yajawo masa kujera ya zauna, "Sannu Dady lfy kuwa kazo da kanka? Madadin kamin waya inzo?

Da wutsiyan ido yakalleshi, "k'iranka kuma na nawa?
Nak'irka yafi abunda yafi,

Kabir yada'uko wayan yana dubawa "i'm sorry Dady ina wordne banashiga da waya word,

Tab'e Bakinsa Dadyn yayi "naga ka rufe acount din Campanin nanne gaba d'aya komeyasa?


KB yagyara zama yana fuskantansa, "satin da ya wuce naje nad'anyi bincike akan cigaban da campanin yasamu abun takaici sai na tar da b'arnan da akayi acampanin yazarta na kullum da akeyi, a iya binceken da nayi akai bansan wayee yafitar da kud'ad'e masu yawa hakaba

Cikin zafi Alhaji ya'u yafara magana


" lallai Kabir na yarda cewa niba kad'aukeni abakin komiba,

Ace campani yana hanuna amma karufe acount batare da kasanar daniba?

Dame za'a biya ma'aikatan?
Dame za'a sayi duk abubuwan da campanin yake buk'ata?

Tun mahaifinka yana raye nike gudanarda duk wani abu na campanin nan, bai tab'a samin ido akaiba,

Tunda yafara maganan kan KB yana k'asa yana nazartan kalamansa d'aya bayan d'aya,
Sosai yayi mamakin k'anin mahaifin nashi campani na hanunsa? Amma baisan yaciri wani kud'i dan developing campaninba?
Kuma kenan yana sane da b'arnan da akeyi a campanin?
To meyake nufi?
Yanasane da irin kud'ad'en da shima yake wawusa amma yayi kaman bai saniba, muryanshine yakatse masa tunani,
"kayi gaggawan bud'e acount d'innan nagayama,
Ajiyan zuciya yayi yad'ago ya kalleshi
"zan bud'e insha Allah amma sai na dawo daga tafiyan da zanyi,
"ina zakaje?

"zamuje Abuja wani seminner ak'arshen satinnan,
Wani dariya KB yaga Alhaji ya'u yayi da baisan ta mece ce ba, sai dai ya fahimci jin dad'i sosai acikin dariyan,

"dayaushe zakuyi tafiyan?
"Da safe,
Gyad'a kansa yayi alamun anzo wurin,
Tashi yayi batare da yak'ara cewa komiba, yafita gida yakoma kai tsaye tun ahanya ya k'ira kila yace yasameshi agida,

Sai kaiwa da kawowa yakeyi a falonsa kamar wanda yakai mai haihuwa asibiti,


Bai ko ji shigowan kila ba sai muryansa yaji abayansa

"ya akayine Boss? Tunda naji kamin irin wannan k'iran nasan tasamu,

Da sauri ya juyo ya dafa kila,
"Kabir zai tafi Abuja ran asabar, banaso asamu wata matsala kila kasan duk yanda zakayi ka hala yaronnan acan kar yadawo,
Kila yafashe da dariya anzo wajen Boss namaka Alk'awari baza'a tab'a samun matsalaba,
Gobe juma'a don haka gobe zamuje da yarana zamu rarraba kai acikin Daji mujira zuwansa wlh sai dai wani ba Kabirba yafad'a yana datse hak'oransa,


Kud'i mai yawa yabashi yace su sha mai da haka kila yafita zuciyan Ahaji ya'u fari tas don yana ganin mafaekinsa zai zamo gaskiya,



*Allah sarki Dr Kabir shin yaza takayane*?
*Ku biyini*












*ummu fatima* 😘😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡¬
_Sis safiyya nayarada da soyayyanki gareni wlh nima ina sonki Dijah tana gaisheki_
*ALLAH yabar k'auna*🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 9⃣


Tun bayan fitan Alhaji ya'u Dr KB yake zaune agun kaman andasashi tunani kala2 yakeyi akan k'anin mahaifin nashi, baifitoba saida akayi k'iran sallahn la'asar, daganan gida yawuce kai tsaye,

Yau yakama Asabar shine ranan da Dr KB zai tafi Abujah, tun dawowansa daga sallahn Asuba yazauna afalo yayi karatu Alk'ur'ani sannan yayi azkhard'in da yasaba, sannan yafito,

Kaitsaye sashin Mami ya nufa yana k'ok'arin shigewa bedroom yaji motsi akitchen yadawo da baya ya lek'a Mami yagani tana had'a break yak'arasa ya langab'ar da kanshi haba Mami keda yakamata aganki akwance shine kika shigo kitchen,

Mami tad'an zaro ido Akwance kuma Kabir? a haba ai tunda akayi sallahn asuba bacci kuma yak'are ai ko ka manta Hadisin manzo Allah (s a w) da yace baccin safe yahana arzik'ine

Kuma ma ai ba asan mace da Baccin safe ba,

"Mnnmm duk da hakadai is too early Mami,

Ina early d'ana zaiyi sammakon barin gida?

"Kina son wannan d'anaki da yawa Mami Mezan miki insa ka miki da wannan soyayyan ya fad'a yana nad'e hanun rigansa,

"kayi aure Kabir kazauna da matanka da Aminci ka hayyayafa inga "ya"yanka aduniyannan kafin inmutu, inkayi haka kasakamin Kabir, cikin sanyi jiki yake kallonta har yagama nad'e hanun rigannasa ya matso yakarb' firan dankalin da takeyi,
Yanad'an murmushi yace "insha Allah Mami zan cikamiki burinki,
Tayaya kenan Kabir d'ina? Anata gumu dakai ga mata nan suna sonka kai baka sonsu? Tafad'a tana lek'a fuskansa da yake ta sinne shi k'asa yana matik'ar jin kunyan wannan lamarin aduk lokacin da Mami ta d'ago Maganan wai ace Mamin sa mai sonsa da k'aunarsa amma yakasa yin abunda takeso,


Cikin jin kunyanta yace Mami to ke waccece ta kwantamiki arai?
"Nikuma? Haba dai Kabir nizan zauna maka da ita ? Kazab'i wacce kaleso dai acikimsu,

"yand'anyi mumushi yana kuna gas yakalli Mami da take tace gyad'an kunu fuskanta k'unshe da murmushi yace "Mami ai indai dan sone zanyi aure bazan tab'ayiba don inaga bayan son ki Mami innace inason watama k'aryane yak'arasa maganan yana d'ora mangyad'a akan gas,

Shiru Mami tayi tana nazarin maganansa, Kabir yajima yana fad'an wannan kalma, saidai ita takan alak'anta hakan da yarantace,

Murmushi tayi tace " To shikenan nizan auramaka wacca nakeso dama jiya yarinyannan Aliya ta zo tagaisheni,
Ahaka sukacigaba da hiransu irin na d'a da uwa harsuka gama, Mami tana zubawa shikuma yana kaiwa daining yana shiryawa, yana gama jerawa ya wuce sashinsa dan shiryawa,

Da waya kan wayan da Mami take ta masa yasamu yashirya cikin suit bak'ak'e da farar shirt taciki takalmansa ma bak'ak'e da farar socks aciki, idonsa manne da farin glass agogon hanunsama na bak'in fatane Sai k'amshi yakeyi kaman sabon Ango Afalo yatarar da Sani yana had'a masa abubuwan dazai buk'ata,
"Sani ya kalleshi cike da zolaya "Mami tana ta mita wai ita kam ta gaji da halinka kullum sai ta tsaya akanka kake shiryawa kaman k'aramin yaro ita kam aure zatamaka ta huta,
Da k'afa Kabir ya wurgoshi da wani cup, Sani yakauce da sauri yana dariya
Atsaye yasamu Mami tana kallon agogo, tana ganinsa tazabga masa harara, kansa ak'asa yana murmushi yak'arasa wajen dining yaja kujera yazauna, tana zuba abincin tana tura mishi gabanshi, tana mitan k'in yarda dayayi yatafi ajirki, "mmn Mami nifa nafison intafi amota indai k'asannane, yafad'a yana mik'ewa to Allah ya kare Kabir kayi Addu'a kuwa?
" Eh nayi,

Tana rik'e da hanunsa kaman wani yaro d'an shekara uku, har sukafito Sani yana tsaye rik'e da murfin mota, cikin kulawa Mami ta amsa gaisuwansa, tad'ora da Sani kunyi Addu'ah? "Eh Munyi Mami, tajuyo tana kallon KB da shima ita yake kallo ko k'yafta ido bayayi ta rik'o hanunsa taturashi cikin mota tana takoro musu Addu'a, moto ci biyarne hud'u cike da sojoji biyu agaba biyu abaya na Kabir a tsakiya Sani yana tuk'awa harbakin gate Mami ta rakasu tana kallonsu harsai da suka b'ace ma ganinta, ta koma cikin gida, ji tayi gidan yamata fad'i dayawa gashi yauba aiki, dahaka ta k'ira wayan Hajiya Rabi matar yayanta da suke uwa d'ya uba d'aya tace ta turomata yaranta su rage mata zaman kad'aici,

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Cike da nishad'i suke tafiya suna hira suna tuna zamanin yarantansu jifa jifa suna dariya,

Wannan na d'aya daga cikin abunda yake k'arasa Sani k'aunan KB da respecting d"inshi sam bai d'aukeshi matsayin wanda yake aiki k'ark'ashinsaba, dagashi har Mami,

*Bari muje waye Sani*
Sani dai ada mak'ocin su Kabir ne tare suka taso suna primary Allah yayi ma mahaifin Sani Rasuwa,


. Mahaifiyarsa ta d'aukeshi suka koma Gombe da zama kasancewan dama yar can ne, anan yacigaba da Rayuwa har ya kammala duk karatunsa daganan yafad'a aikin soja Sai kuma wata jarabawa ta fad'omasa Gwamnati ta dakatar dasu sakamakon wani matsala da a kasamu Sojoji dashi, bak'aramin damuwa Sani da mahaifiyarsa sukayiba, ana haka Allah yakawo Kabir garin Gombe duba wani campani dayakeso yasaya, kwatsam Allah ya had'asu ba k'aramin murna sukayi da ganin junaba nan sukayi ta hiran bayan rabuwa anan Sani yake gayama Kabir halin da yake ciki ba k'aramin tausayasa masa Kabir yayiba, Baiyi k'asa agwiwaba, daya tashi tafiya ya tafi dashi dazummar nima masa aikinyi, tofa alokacinne kuma Alhaji ya'u yad'aura d'amaran ganin k'arshen Kabir tahanyoyi da dama da ya ajiye motarsa za azo asama sa bom, bak'aramin tashin hankali Mami ta shigaba, ahakane tanima masa masu tsaronsa ciki har da Sani wanda yakasance ogansu kuma shine drivern Kabir duk inda zaije duk da wani lokaci Kabird'in yakan k'i fita dashi,


🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
"Hello Kila Kabir fa yataso ina fatan dai kuna cikin shirinku, pls kila wannan karon kar kabari asamu tangard'an da yaronnan zai kub'uta bai mutuba,
"Ka kwantar da hankalinka Boss gamunan adaji muna jiran shi yau kam Kabir saidai uwarshi ta haifi wani,
Cikin jindad'i Alhaji y'au yace

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment