Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujera ya kalli Dijah da take ta aikin kallonsa cikin wani yayi, dan rabonta da pert d'in nata sati wajen Biyu kenan, tun randa KB ya tsokaneta daga baya yamata wayo yajata Sashinsa,



Sosai yaji tausyinta har ransa, ya kamota ya zaunar da ita ajikinsa yana shafa cikinta, kansa a kan kafad'anta, Yana goga Hancinsa a tsakanin wuyanta cikin yanayin lallashi, murya a sanyaye yafara cewa, "Inasonki Khadijah bazan gaji da gayamiki wannan kalmaba, Kema kar kigaji da Amincewa dani, Dan Allah Khadijah kar kijuyamin baya namiki Alk'awari nima bazab juyamikiba duk Rintsi duk wuya ina tare dake Ba gudu baja da baya, Kina sane da ku biyu ne a k'ark'ashina ya zamo dole inyi Adalci a tsakaninku dan in tsira agaban Mahallicina,

Ya d'an furzar da iska, "Yau Nafisa zata dawo daga tafiyan da tayi, shiyasa na dawo dake nan Badon nasoba Khadijah ina cikin Alhinin hakan fiye da tunaninki, Gobe insha Allah zan taraku dan kutsayar da adadin kwanan da kuke son inamuku,


Ya juyo da Fuskanta yana kallon tsananin firgici da Kishin da ya kwanta kan Fuskanta, Yana kumajin yanda k'irjinta ke bugawa,


Bak'aramin tashin hankali Kabir ya shigaba, ganin yanayinda ta koma, ciki damuwa yace "calm down Khadijah ki taimaki zuciyata kinga kina da hert problem! Kuma kina da juna biyu, sa damuwa aranki ba k'aramin matsalane a garemuba, Nafisa bazata kawo wani abu game da Soyayyarki A zuciyanaba, pls ki kwantar da hankalinki! ya k'arashe kaman zai samata kuka.


Kallonsa takeyi tana tariyo maganganun Su Yafannah gareta,

_karkiyarda ki nuna masa baki son Matarsa, muddin kina son darajanki ya k'aru a idonsa, Sannan karkiyarda kidinga kaimasa k'aranta, hakan zaisa ya rinka ganin baki da hak'uri, da haka har kifita aransa,_



Ta sauk'e ajiyan zuciya tana d'an Murmushin k'arfin Hali,

"Nifa ba wai na d'aga Hankalina bane Honey, kawai dai ina tunanin yanda zan iy bacci ba kai akusana ne ka sakaltani da yawa, anma ba yanda na iya dole in d'au na Annabawa, inbarma Aunty na dan nasan kunyi missing juna sosai


Yak'ura mata Ido ba ko k'iftawa yana kallonta yasan k'arfi hali kawai tayi na wannan Magana,

"Nima hakantake awajena my luv sam bsnson abunda zai nisantani dake kona Second ne, Kuma ..... Baiyi auneba yaji Dijah ta manne Bakinsu waje Guda tana kissing nashi, Hakanan taji maganan ta isheta,

KB kam ji yayi kaman zai sume da irin wasannin da tashiga masa, k'arshe sai Agado na hangosu, πŸ™ˆπŸ™ˆ

**********

Tsaye take ajikin Window tana kallon yanda KB ya Rungume Nafisa tsam a k'irjinsa kaman zai maidata cikin jikinsa, sai dariya suke k'yalk'yalawa, kaida ganinsu kasan Masoyan junane da sukayi Missing junansu, Cike da Kewa ya jata daga palourn suka shige d'akinta basu ko bi ta kan jakanta da tadawo dashiba,



A hankali take sake Labulen tana ja da Baya k'irjinta sai bugawa yakeyi, da k'arfi, ta dafe k'irjinta gami da ciza Lip d'inta na k'asa tana ta k'ok'arin mai da k'ollahn dake shirin fitomata, anma ina yanda take jin zuciyanta na bugawa, abun yafi k'arfinta, da gudu ta juya ta fad'a saman Bed d'inta, ta saki kuka mai k'arfin gaske, Cikin tausayin kanta da Rayuwanta ta dinga juyi kan gadon, sai da tayi mai isanta, tayi shiru ta dafe Kanta da taji yana mata masifaffen ciwo Fuskanta ya kumbura ya mata Nauyi,


"Meyasa maza suka kasance Munafukai?
Meyasa Likita yake mata haka? Meyasa agabanta yake nunamata bai son Nafisa yake nunamata cewa ita kad'aice aransa, Bayan ba hakanbane,


Wani irin kuka mai tsima xuciya takuma fashewa dashi, Tsawon lokaci tana ahaka, jin k'iran Magrib da akayine yasa ta tashi ta shiga bayi tayi Alola da k'yar take ganin hanya tsaban ciwon kai da takeji, bayan ta idar da Sallah ta d'auki Qur'ani tayi takarantawa,

Ahankali ta dinga jin sanyi na ratsa zuciyanta, Ana k'iran isha'i ta Rufe Qur'anin Ta jingina kanta da jikin gado, aranat tana tuhuman kanta,

"To mezaisa ind'aga hankalina akan abunda ba haramunba? Matarsace tana da hak'k'i kansa kamar yanda nima nake dashi, Inba son zuciyaba dan me zan d'aga hankalina,

Sai kuma tasake fashewa da kuka, tanajin wani sabon kishi yana tasomata, tasani Kishine kawai ke damunta bawani abuba, tana idar da Sallah ta haye Gadonta, tana Addu'an Allah ya sassauta mata irin wannan kishi a ranta,

***********

Kwance yake Nafisa tana kan k'irjinsa, ahankali yake shafa gashin kanta, ya kalli Fuskanta Baccinta takeyi hankali kwance yayinda shi kuma, Sam Baccin yakasa d'aukansa, yasani sarai Khadijah ba k'aramin kishine da itaba, yaso ya lek'ata adaren yaga halin da takeciki, anma hakan baisamuba saboda yanda Nafisa ta lik'emasa, yana son yayi Adalci atsakaninsu sam bai son ya nuna banbanci, duk da yanda yakejin Son Dijah a ransa, kaman bazai iya had'ata da wataba,

Cikin Bacci Nafisa ta d'anyi Juyi ta bud'e ido ta kalleshi, ta shafi gefen Fuskansa, "Sweet meyahanaka Bacci har yanzu? D'an Murmushi yayi ya k'ara rungumota k'irjinsa yakashe wutan d'akin, hoton Dijah ne yake masa yawo a fuskansa,

**********

Misalin k'arfe Takwas Dr KB Yagama shirinsa cikin Milk Colourn Suit dasuka amsheshi Sosai, Sauri2 yakeyi ya fita yaje ya duba Dijah Dan da ita ya kwana ya tashi aransa, ya fice a sashin nasa ba tare da yabi takan Nafisa da take kwance shame2 ba,


Cikin sauri ya tura k'ofan ya shiga da Sallamansa, a lokacin Dijah tana zaune akan Sallahya da Qur'ani agabanta, ta rafka tagumi,


Ahankali ta d'ago tana amsa Sallaman,

Cikin damuwa Kabir ya tsuguna agabanta, ya kamo Hannayenta duka biyu yana kallon yanda fuskanta ya kumbura yayi jah, tsaban Kuka, ya girgiza Kansa yana jin zuciyansa namasa zafi, "Why Khadijah? Meyasa haka? Kinfa min Alk'awarin bazaki d'aga hankalikinba, inasonki Khadijah koda bana tare dake Zuciyata tana tare dake,


Dijah tayi Murmushi tana kallonsa "Haba Honey, baka kobari mungaisaba, katashi lfy? Ya Auntyna?

Ya girgiza kansa ba tare da ya Amsaba, "Kin Kwana kina kuka ko?
Ta girgiza kanta "Kainane yakemin ciwo Honey kuma nasha magani yanzu, yasa hanu ya d'agota ya Rungumeta ak'irjinsa,

Sukaji wani irin k'ara da sauri KB ya juya ya kalli inda yaji K'aran ba tare da ya fitar da Dijah daga jikinsaba,


Gadan gadan Nafisa tayo Kansu ta shak'o Hijabin jikin Dijah ta baya, ta yaga ta xubar Ta kuma damk'o gashin Kanta,,

😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
Wayyo Dijan KB

*Ummu Fatimace* 😍😘
[10/9, 8:47 PM] β€ͺ+234 816 155 6998‬: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


7⃣0⃣


Dijah ta zuba ma Ruwan wankan ido na d'an lokaci haka nan ta tsinci kanta da rashin yarda da Ruwan, dan haka ta bud'e tub d'in Ruwan ya tsiyaye tas ak'asa, Sannan ta tari wani tayi wankanta ta fito,


Ba tasamu Nafisa a d'akinba ta lek'a palour nanma bata nan,

Ta k'arasa jikin k'ofa da sauri ta rufe harda sa key, Nafisa da take tsaye daga d'an nesa tana duba kazan da Dijah tayi wurgi dashi jiya tayi dariya cike da mugunta, a fili tace "yarinya dama kinbar k'ofankine indai dannice, Na riga nagama dake ba abunda zai sa ink'ara lek'a inda kike har ranan da zaki tare yanaki2 ki barmin Gida, ta maida kallonta ga ledan ta kuma kwashewa da Dariya, "Ashe dai sak'ona najiya ya shiga inda nakeso, kad'an kika gani yarinya, kafin kibar gidan sai zuciyarki ta fashe dan takaici ladan shigomin gida da kikayi, daga haka ta wuce sashinta cike da farin ciki.



(Rayuwa kenan) tundaga wannan Rana Dijah tashiga wani hali mara dad'i agidan aurenta, dan tsakaninta da Mijinta sai hange daga nesa ta gama fita ahayyacinta, ko d'an Addu'o'in da tasaba yanzu bata samu tayi Kullum tana zaune a waje d'aya bata da aiki sai kuka,



Yau tun tashinta daga Bacci take kewan ganin Mami, dan haka tayi duk ayyukanta da wuri ta shirya, tayi ta k'iran wayan KB bai d'aukaba, ta ajiye wayan ta dafe kanta tana k'ok'arin maida hawayen dake son sulmuyo mata,



Ta window Can ta hangoshi yana shirin bud'e Mota, da saurinta ta zira Hijab d'inta ta nufi wajensa, Gabanta na bugawa haka ta k'arasa gareshi, a lokacin yana d'aura Agogo a hanunsa, Jin k'amshin turarentane yasa yaji wani irin fad'uwan gaba,


A hankali ya karkato da kansa gareta a lokaci guda bugun zuciyansu ta tsananta, yayi saurin kauda kansa gareta yana maida numfashi wani irin nauyi yake ji a zuciyansa,

A sanyaye ta k'ira Suanansa, "Liktaaa! Bai d'ago ya kalletaba kuma bai Amsaba ya cigaba da d'aura Agogonsa,

Murya a dushe ta cigaba da "Dan Allah ina niman izinin zuwa gidan Mami,

saida yagama d'aura Agogon ya d'ago ya kalleta, Tayi saurin maida kanta k'asa, kallonta yakeyi daga sama har k'asa So yake ya tambayeta abunda ke damunta ta canza haka, saidai ya gaza yin hakan, ya juya ya kama Murfin Motansa zai bud'e tayi saurin dafe Hanunsa, wani irin shork sukaji a tare, Kabir ya kalleta ya d'age Gira a hasale yace "Malama lfy?


Cikin sheshshek'an kuka tace "Pls Likita izininka nake nima kayi magana man, Gidan Mami nake Son zuwa, ta k'arashe cikin d'an kuka,


Cikin sanyin jiki ya janye Hanunsa daga nata zaiyi magana, sukajiyo salati daga bayansu dukansu biyu suka juya suka kalleta ta koma kamar wacca ta kama kwartaye,


A fusace Nafisan ta k'arasosu ta hankad'e Dijah gefe ta shiga tsakiyansu tana mata kallon tsana, tace "Ke Banza meye tsakaninki da Mijina?
Wama ya baki daman zuwamin gun Miji?

Dijah ta d'ago a sanyaye zatayi Magana, tadakamata tsawa "Dalla can matsa kiban wuri daga yau sai yau nakuma ganinki a inda Mijina yake sai na kusan halakaki, tafi kiban guri nace, idiot!! Mtsss!!


Kabir yace "Wai zataje wajen Mami ne,

"To baxatajeba, ba inda zata,

Ta juyo ga Dijah "Ba inda zaki kika sake kika fita a gidannan wlh sai kin gane kurenki, b'acemin da gani,

Ga Mamakina sainaga Dijah ta juya sum sum tayi ciki tana tafiya tana sharan hawaye, πŸ€”


Nafisa ta juyo da Kallonta ga KB da yaxamo kaman mutum mutumi, "Waima meyasa ka saurareta, ban rabaka da itaba?


Wani irin harara ya zabgamata yace
"To Uwata ai Sai kidakeni kawai,

D'an kallonsa tayi aranta tana mamakin taurin rai irin na KB, Sam asirin yak'i yayi tasiri gaba d'aya a jikinsa, so take taga tana juyashi ta koina anma ya gagara, wani lokaci sai yaxamomata kaman daa, taja tsaki ta shige ciki, shima tsakin yayi ya figi motansa ya fice,


*************

Kwance Dijah take kan doguwar kujera, sai juya kanta take tana kuka kaman ranta zai fita abun duniya yamata xafi, Ji take kaman tafita da gudu, Ashe haka Rayuwan aure yake?
Ashe haka maxa suke?

Tunani ta shigayi Ta rasa me tayima KB dayamata irin wannan juya baya haka, Ta rasa mekefaruwa da rayuwanta, sosai ta lula cikin Duniyan tunani, Sam bataji sallaman da ake ta rafkamataba, xuciyarta sai Zafi yake mata,

Jim ba amsa Sallamanba kuma ga k'ofa a bud'e yasa Sauda turawa ta shiga, Sosai ta karaya daganin halin da Dijahn takeciki, ta zauna a gefenta ta d'an bugi k'afanta,

Dijah ta d'ago a d'an tsorace ta kalleta, Ta tashi ta zauna tana share hawayenta,

"Sannu da Zuwa Aunty Sauda,

"Khadijah meke faruwa dake haka? Tun d'azun nake sallama har na shigo baki saniba, Haka kika dawo,?πŸ˜³πŸ€”

Wacce iriyar Rayuwa kikeyi haka?


. Dijah ta kuma fashewa da Kuka ta fad'a jikin Sauda,

"Dan Allah Aunty rSauda ki taimakamin inbar gidannan ayud'innan bazan iya zaman Gidanba gidan yafi k'arfina pls Help me Aunty Sauda,

"Ya isa Khadijah gayamin meke faruwa dake? Meyasa zakice gidan aurenki yafi k'arfinki?

Cikin Kuka Khadijah ta warware mata komi, ta d'ora dacewa Allah Aunty Sauda tsoron Nafisan nakeji har cikin raina bansan meke faruwa daniba gidanma tsoransa nakeji dan Allah kitafi dani, inje ga Baffana shi kawai nake son gani,

"Ba abunda Baffanki zai iyamiki Khadijah tunda kinsa k'afa kinyi fatali da abubuwan da ake gayamiki,


Suka jiyo Muryan Binta abayansu gaba d'ayansu suka dawo da kallonsu gareta, Kusa da Sauda ta zauna tana kallon Dijah,

"Nakai Adnan Asibitine Riga kafi nace barin biyo in dubaki kwana biyu innak'iraki awaya nakanji muryanki cikin damuwa, inna tambayeki kice babu shiyasa nazo inganema idona dan nasan akwai abinda kk b'oyemin, tun d'azu na shigo naji duk abunda kika fad'a Dijah kina da taurin kai dole ki ga irin haka,


Sauda ta katseta da "No karkice haka Binta wlh ba sontabane Aikin Asirine wannan inba hakaba Nafisa bata isa da Ya KB bata isa juyashiba wlh k'aryane sanna Kinsan bata kai wacca Khadijah zataji tsorontaba wallahi wannan sharrin shaid'anu ne, kinko san wacece Nafisa da iyayenta?
Mhmmmmm

"Ita taso Sauda, nayarda Asiri na tasiri anma wlh inkayi sakacine yake tasirin meyasa tuntuni bai kamasuba? Ita da bakinta take cemin tasha ganin Nafisa na Binne2 a gidan Mami meyasa tun cana ba ayi hakanba,

Sabida Mami ta rik'e Addu'a sam bata sakaci dashi, Tanayi tanasasu yi dan haka Allah yake karesu da k'arfin Addu'o'insu,

Yanzu kuwa sunyi sakaci sun mance da irin jajircewan da Mamin tayi akansu, kinko ba abunda bazai samesuba sai dai Allah ya kyauta,

Ta kalli Dijah tace "ko kina Addu'a ko wani safe da yamma da lokutan kawanciyanki? Sanna kina rok'on Allah ya karemiki mijinki daga sharrin ma sharranci?

Dijah tayi shiru tana tunani tabbas Rayuwa ya mantar da ita yin Addu'o'in da tasaba wanda da Mami kesata gaba tanayinsu,

"Wlh Aunty Binta damuwan danashiga tasa nake yawan mata Addu'a inadaiyi anma ba kaman daba,


Sauda ta sauk'e ajiyan xuciya "mhmmm ke kuma irin naki damuwankenan madadin kinshiga wani hali kik'ara kusanci da ubangijinki sai ki nisanta kanki dashi kimaida Kuka shine makusancinki? haba Khadijah meyasa kikayi sakaci haka?

Kokinmanta fad'in ubangijine badun Addu'o'inkuba da dayawanku na halakar daku, shifa yace mu rok'eshi xai amsamana, ko bada irin Nafisa Allah ya had'akuba, Bai kamata kiyi sanyi wajen Addu'aba, wlh duk zaman lfy da kike da kishiya kiyawaita niman tsari daga sharrinta na b'oye da na fili, dan d'an Adam abun tsorone,


Binta ta rafka tagumi tana tunanin Rayuwa wai yau Dijah mai tsiwa da abaya ba'a tab'ata ashare itake furta cewa tana tsoron wata da bakinta,? πŸ€”

Kai Rayuwa abun tsoro itakam tak'ara karaya da wannan Rayuwa, tarasama ta ina zata fara yunk'urin taimakawa 'yar'uwar tata, tabbas tasan wannan yana daga cikin jarabawan Rayuwa da mutum yake iya fuskantansa ta kowace fuska batare da yashiryama hakanba ko yayi tunanin hakan na iya faruwa dashiba,


Allah kenan buwayayyen sarki sai yayi abunsa kagani Allamul guyub fa'aalun lima yurid,


Ta d'ago tana kallon yanda Dijahn ta koma a k'ank'anin lokaci kai kace bata tab'a Rayuwan farin cikiba, duk ta birkice tafita hayyacinta,



Sauda ta dafa kafad'anta, "Ki dawo Hayyacin ki Khadijah kimaida Qur'ani abokin hiranki Ki yawaita Addu'o'i ba dare ba rana, ki kai kukanki ga isashshe mai isarwa, Kiyi taniman tsari zaki ga canji da izinin Allah muma xamu tayaki kuma zanbi yanxu insanar da Mami nima daga awu nake nace barin biyo indubaki kwana biyu shiru, sai yanzu na gano abinda ke Faruwa da Ya KB wlh kwana biyu shima abirkice nake ganinsa ba nitsuwa a jikinsa idan na tambayeshi ke kallona kawai yakeyi kaman baisan waccan nake tambayansanba wlh nikam dama nasha jinin jikina,

Dijah tace Dan Allah Aunty Sauda kar ki gayama Mami hankalinta zaiyi mugun tashi, nagode dakuka tunatar dani, wlh zan dage insha Allah, hakanan na tsinci kaina k'iwiyan yin ibadan dana saba nasan wanna saharrin shaid'anne, ta k'arashe tana share k'ollah abun gwanin tausayi,


Haka sukayi ta k'arfafamata gwiwa da lafuza masu dad'i sannan suka mik'e a tare suka mata sallama,

Suna fita ta shiga bayi ta d'auro Alola ta haye sallayyah tayi ta Nafiloli tana karanta Qur'ani tana tawwasalli dashi, tana Addu'o'i, Sai gashi taji zuciyanta yamata sanyi,

******
Kusan satin ta guda kenan yau bata da aiki sai na Addu'o'i sosai ta koma ta mik'a al'amuranta ma Mahalliccinta, ko Bed room nata bata shiga hakanan taji zaman d'akin yafita aranta, kullum tana palour tana ibadanta, wanka da sanca kayane kawai ke shigar da ita, hatta kwana a palourn takeyi,


Bak'aramin natsuwa da kwanciyan hankali tasamu ajikintaba, yanzu ta daina jin tsoron gidan haka ta rage tsoron matan gidan, wani lokacima tausayi take bata dan tana kallon shiga da ficensu, ta lura har yanzu daga ita har mahaifanta basu samu yanda suke so arayuwanba, gashi sun nisanta kansu daga Allah da manzonsa,
(Allah ka tsaremana imaninmu) πŸ‘πŸ˜­

********
Tsaye take ajikin window tana rik'e da plate d'in d'anwake dan yanxu shi yazameta Abinci flour kawai take iya saya da d'an kud'in Hanunta, Kallon Kabir takeyi da ya shigo yanzu tana ganin sanda ya fito daga Mota, yana takowa kaman zai tsaga k'asa dan sauri ya k'ura ma k'ofan pert d'inta ido yana kallo kaman wanda yayi wani mantuwa awajen, har sai da yaji ya bugu da gini kafin yayi saurin daidaita kansa ya shige sashinsa, Khadijah ta sauk'e ajiyan zuciya ta zauna, tausayinsa da wani sabon sonsa ya dad'a mamaye zuciyanta da ruhinta, ta d'anyi Murmushi mai had'e da hawaye ta girgiza kai, Allah ya kub'utar damu daga wannan hali Mijina, mu dawo Rayuwarmu kaman da baya, 😭


***********
Yau Asabar kasancewan yau Ba aiki yasa Mami ta himmatu da zuwa gidan d'an nata da ya gujeta kwata2 tsakaninta dashi sai dai in tak'irashi awaya, nanma da k'yar yake d'agawa yata mata kame2 takanji damuwa fal voice nashi inta tambayeshi yace mata babu da tace masa yazo, zaifara kame2 ai zaije waje kaxane a'a tayi hak'uri zai zo gobe,


Haka yake ta fannin Dijahma in tak'irata tace tagayamata meke faruwa a gidansu? Sai tace babu, Shikuma KB dagaske Hidima ke masa yawa, dan haka yau ta yanke shawaran taje ta ganema idonta, tunda ta zuba idon taga ba wanda zaizo ya gayamata ga abunda ke faruwa.


Cikin nitsuwa da kamala take tuk'i har ta iso gidan tanayin Horn masu gadi suka bud'emata, tana perking kai tsaye sashin Dijah ta nufa tayi knoking, daga kan sallayah Tace "Waye?
"Nice Mami tabata Amsa,

Da sauri ta mik'e jin muryan Mami ta zo ta bud'e Tun kan ta shigo ta fad'a ajikinta tana murna, suka k'arasa ciki, mami tana zama tafara tunanin me zata bata dan bata da komi na Drinks a gidan bayan Ruwan da take tara a famfo ta cika Randanta,

Ta shiga kitchen ya kai sau uku tana fitowa iya zamanta da Mami bata tab'a ganin tasha ko peur water na Ledaba, bare Ruwan randa, Ruwan gora take ganin tana sha,

Gashi ko sisi bata dashi bare ta fita ta aika a sayomata, Duk kud'ad'en dake Hanunta ya k'are wajen sayan Flour tana d'anwake dan kaf anzo ankwashe kayan Abincinta batare da tasan wanda ya aikata hakanba, kuma ba tasan yaushe akayi hakanba, dubawa kawai tayi bata ganiba,



Danne2 waya Mami takeyi anma hankalinta naga Khadijhan tana karantan yanayinta,


"Khadijah bamu Gaisabafa, Mamin ta fad'a tana a jiye wayan ajaka,


Da d'an Murmushin k'arfin Hali, Ta k'araso daf da ita, ta zauna ta tank'washe k'afa, cikin girmamawa ta gaisheta,


Mami ta gyara zama dan son tabbatar da zarginta tace "Khadijah haka kuke tarban bak'inku ba ko d'an Ruwan sha? Bare wani abun motsa baki?


Cikin inina Dijah tace "Amm Wlh Mami duk Drinks d'in namu sun k'arene d'azu da mukayi bak'i anjimane za'akawo,


Mami ta waro ido waje, "Ku dakuke da Store guda na Drinks da Snaks shine har zaku bari Su k'are tas agidanku,


"Mmm ba haka bane Mami bak'ifa mukayi,


"To ina Kabir d'in? Naga motansa a gida,

"Eh yana d'akinsa,

"Ok k'iraminshi,

A hankali Dijah ta mik'e kamar mara laka tafara tafiya.





*Ummu Fatima ce* 😘
[10/10, 11:05 PM] Hauwa Jameel: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*Wai dan Allah yaushe za'a daina niman _Dijah Qayah_ daga farko ne? Har yanxu Kusan kullum sai na samu masu bina wai inbasu daga farko ko daga 37* πŸ€”πŸ€”πŸ€”

*Jinjina gareki Dougterna 'yar Albarka Hauwa ta kaina manajar Dijah Qayah ina godiya gareki tare da yawun dubbannin ma biya wannan buk da baki gajiya da basu duk page din dasuka nima* πŸ˜πŸ˜˜πŸ‘πŸ»


*Gaisuwa gareki Maman 4 ta gidan Huguma* *Masoyiyar Dijah da marubiciyan Dijah*

*My Hannah Rabi'u ma tana jinjina gareki tare da mik'o gaisuwarta gareki*


*Ummu Fatima conversation group wannan page gaba d'aya nakune ku dukanku wlh inayinku Nagode matik'a da irin so da k'aunanku gareni* 😍😘😘😘😘😘


7⃣1⃣



Tajima tsaye bakin k'ofansa cikin fargaba kafin ta k'onk'osa, tsawon lokaci tana k'onk'osawa taji anbud'e k'ofan ba tare da anyi maganaba,


D'aure yake da Towel iya kunkuminsa yayinda wani k'arami ke rataye a kafad'ansa, Ruwa na tsiyaya ajikinsa da Alamun daga wanka yafito yanzu, ganinta tsaye yasa yad'an yamutsa fuska yana kallonta alamun saurara,

Tayi saurin sadda kanta k'asa tanajin wani abu na mata yawo acikin jikinta,


Murya asark'e tace "Mhhmm dama Mamice taxo tana son ganinka, shiru yayi kaman mai tunani, Sannan ya maida k'ofan ya rufe ba tare da yace komiba,


Ta juya a sanyaye ta koma,

Mami tana zaune cikin kujera Bakinta d'auke da Addu'o'i kala2 Dijah ta shigo,


"Mami yana wanka, kai kawai Mamin ta gyad'a Tace kawomin Cup,

Tashiga kitchen ta d'auko mata ta bata,

Mami ta d'auko Ruwan Zam2 ajakanta ta bud'e ta juye a cup d'in, ta shiga karanto ayoyi tana tofawa aciki, har tagama ta ajiye Kabir bai shigoba, Mami ta tashi ta d'auki Ruwan zam zam ad'in takalli Dijah, "Muje ki kaini wajen nashi,

Dijah tana gaba Mami tana biye da ita,

Cikin kasada da k'undunbala, Ta tura k'ofan ta shiga ba tare da ta nimi iziniba, yana zaune a saman Kujera sanye da Jallabiya Ash ma dogon Hanu, Nafisa tana zaune kusa dashi ta d'ora k'afanta a kan cinyansa,

A zabure ta Mulmulo wani K'aton Ashar ta wurgoma Dijah ta d'aura da cewa "Ke iskancinkin har yakai haka? Yuashe Rashin kunyankin yakai har nan?
Da zaki shigomin d'akin miji kai tsaye haka,

Dijah ta wurgamata wulak'ancaccen kallo ta juya ta kalli Mami, "Bismillah Mami shigo,

Mamin ta shigo sannan Dijah ta maida k'ofan ta rufe ta Kujeran da yake Fuskantansa Mami ta zauna, Dijah ta zauna kusa da k'afansa ak'asa, Murya k'asa2 tace "Honey kasauk'o ka gaida Mami, a hankali ya zamo k'asa ya zauna kansa ak'asa,

Mami ta mik'o masa cup d'in da ta shigo dashi "karb'i wannan kasha Kabir kafin mugaisa, Dijah ta

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment