Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake Rik'e da Wayan tana sheshshek'a ya d'ago suna kallon juna d'an ciza gefen lip d'inta na k'asa tayi idonta taf Hawaye, tana girgiza kanta Ahankali tanason tayi Magana amma takasa dan duk abunda za'ayi sam bata son tasako Mami aciki, wani lrin tausayinta yaji yana ratsashi ta ko ina, ya ajiye wayan agefe ya jawota jikinsa, "Wlh Khadijah bani da Hanu cikin cutar da ke kiyarda dani kuma na miki Alk'awari insha Allah bazan bari ki cutuba, Banason Kuka arayuwana ko k'aramin yaro banson inga yana Kuka, pls take it Easy, ba abun tada Hankalibane.



Yayi shiru yana Kallonta So yake yaga ta saki ranta, wani dabarane ya zomasa dan yasan da haka zai sha kanta, yad'anyi Murmushi yana Kallonta yace

"Ga wani Albishir game da Baffanki, yasa bakinsa dai2 kunnenta ya fad'amata wani Magana, ta d'ago ta kalleshi tana Murmushi da gaske Likita? D'agamata Gira yayi yanajin wani abu nayawo cikin jikinsa, wanda yarasa gane meye, wani irin Murmushi tayi ta kwanta ajikinsa, ahankali tace "Kayi Hak'uri bazan sakeba da mamaki ya lek'a fuskanta, yanason tabbatar da cewa Khadijahnce kuwa tayi Maganan, har yanzu Fuskanta na d'auke da Murmushi aransa yayi tunanin wani lrin sone haka Khadijah takeyi ma Baffanta,


"Ina zuwa yace sannan ya fita ya dawo da Kwalin fresh milk ya tsiyaya mata ta sha sannan ya b'alli Maganinta yabata, Ya tashi ya tafi massalaci dan anyi k'iran isha'i, bayan ya idar sai da yaje ya sallami Mami kaman yanda yasaba, yadawo alokacin Khadijah har tayi wanka tayi shirin Bacci tana zaune ak'asa, Shima shirin yayi sannan ya had'a Alluranta yana zaune abakin gado yace "Khadijah Bismillah, ta zaro ido "Gaskiya Likita bazakamin Alluraba pls banso wlh, kallonta yakeyi yasani yanzu abune mai sauk'i tafara masa Kuka dan haka ya ajiye Alluran, yace "to shikenan inbakiso zo kiji, ba Musu ta taso, d'an nesa dashi ta zauna, ya kwanto da ita jikinsa yana d'an Romace d'inta, ayanzu ta saba da irin wa innan Abun nashi,
dan haka ta lafe ajikinsa, cikin dabara ya janye Riganta ba ta ankaraba sai jin shigan Allura tayi ta zabura zata sa ihu ya had'e bakinshi da nata, tsawon lokaci kafin ya ajiye Alluran ya gyaramata kwanciya ya rufa musu Bargo.




*Ummu Fatima ce* 😘

[8/9, 9:11 AM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


5⃣1⃣

Yau Laraba, yaune Ranan da Kb yace zai kai Dijah Office d'in Ss,

Misalin k'arfe 8:15am Mami ta k'irashi, Cikin yanayin Bacci ya d'aga Wayan ya kara a Kunnensa, yana fad'in "Helo!
"Au Bacci kukeyi Kabir? Kamanta yaune wa'adin daka d'auka? Kallon Dijah da tayi luf kwance a k'irjinasa yayi, Baccinta take bil hak'k'i, yad'an Matsar da ita ya d'ora kanta akan pillow, yana k'ok'arin tashi Mami tace "Ina Khadijahn? Cikin in ina yace "Barinje ind'agata,
"Oh yanzu saboda Allah sai da kadage ga koyamata Baccinka na Safennan? Yayi kyau tafad'a gami da kashe wayan,


Tashi yayi yashiga wanka, batare da yad'agataba, yana fitowa yatsaya yana dubanta, d'an juyi tayi jin batajita ajikinshiba yasa ta bud'e ldi, ya kauda Kansa yacigaba da shiri, ta maida Kallonta kan agogo, zunbur ta mik'ewa da Sauri ta shiga wanka,


shirinsa yayi cikin, Fara k'al d'in shadda yasa Riga da wando wanda tasha aiki da bak'in zare yasa Ba'ikin Hula, Yad'aura Agogo mai Bak'in Fata, ya d'ibo bak'ak'en cover shoe d'insa a hanu ya fito falo ya zubasuu agefe sannan ya haye daining, yana cikin karyawa, Khadijah ta fito cikin fararen Leshi da aka musu kwalliya da bak'in zare d'ad'd'aya ajiki, iya powder kawai ta shafa, sai kwalli da ta zizara sai kuma d'an Man baki da tashafa, Tun fitowanta ya kafeta da ido har ta isoshi, sadai yafi mayar da Hankali sa kan hanuntan da take Rik'e da Bak'in Gyale, ta kalleshi kaman mai ciwon baki, tace "Zanje Gaida Mami, wani wulak'ancaccen kallo yabita dashi ya kau da kansa, adak'ile yace "kizo kiyi Break tukun kaman tace ta k'oshi, sai kuma taja kujera ta zauna, d'an cakala kawai tayi ta tashi zuba mata ido yayi aransa yana girmama taurin kai da rainin da ta masa, dan inba hakaba ba abinda zaisa ta d'auko gyale, rai ab'ace yace "meye wannan ahanunki? Kallon Hanuntan da yakallan tayi, sannan ta warware gyalen ta yafa akanta, kansa ya gyad'a Sannan ya mik'e yana fita yace "Idan kin isa ke Mara Kunyace, Dan Allah ki fito da wannan Abun, daga Haka ya bud'e k'ofa ya fita, Yanufi pert d'in Mami,


Tsayawa tayi agaban sif ita kad'ai sai surutu takeyi "Danma yaga ina biye mishi shiyasa yake wani takuramin, Gaskiya Aunty Sauda bazan iya abunda kika saniba, haka kawai mutum yadingamin Abu kaman shi ya haifeni?

B'ak'in Hijabi ta zira ta d'auki Takalmi da jakanta bak'ak'e ta fito ta shiga pert d'in Mami, a Falo tasamesu dukansu har da iya suna Magana, Kusa da Mami ta zauna ak'asa ta gaidata, "Khadijah wato kin biyewa Kabir ya koyamiki Baccin safensannanko? Abunda sam baki iyaba,

d'an Murmushi tayi tagaida lya, Mami ta tashi tana kallonsu nikam barin wuce sai kun iso, ta d'auki jakanta tafita, Kallon Dijah yayi da ta gyara zama tana kallon T.V wani b'angare na zuciyanta cike da fargaban abunda ke gabanta, ko ya zata k'are da wannan Sharri da akeson d'oramata?


Mik'ewa Kabir yayi yafita ba tare da yace mata komiba,

"Ke Khadijah tashi kutafi, indai kinje kisaki ranki sosai kiyi bayani banda wani kame2 kinji? Iya ta fad'amata,


Tashi tayi tana Amsamata da kai, tabi bayansa, zaune tasameshi cikin Mota ya kifa kansa da sityari, ta bud'e ta zauna.

Jan Motan yayi ba tare da ya kalletaba, dan Zafinta yake ji aransa, Zuwa yanzu ya kamata ace ta ajiye Maganan sa gyale ba sai yayi Maganaba, tunda yajima yana mata Nasiha akan hakan,


Sai da Sukayi nisa sosai, Kabir yace "Yanzu inkinje me zakice? Adak'ile tace "Abunda suka tambayeniman, tab'e Baki yayi gami da d'an Murmushi, bai sake ce komiba har suka isa, yayi perking, sannan suka fito atare suka jera, Tunda ga Nesa Nafisa ta hangosu wani lrin fad'iwan gaba taji Kabir d'inta da Wannan yarinyan da ta tsana Aduniya, Kallon shigansu takeyi cikin tashin Hankali, Anyah Kabir bai fara son yarinyannanba? Ta tambayi kanta,


Cikin girmamawa Kabir ya gaida su Uncle, kowa ya hallara a wajen su kawai dama ake jira, kusa da Dijah ya zauna, yana d'ago idonsa suka had'u da na Nafisa, kallon tuhuma sukeyi wa Juna dukansu biyun,


Mintuna kad'an da isansu, mai Binciken ya zauna, d'an gyaran Murya yayi ya Kalli Kabir " Ranka ya dad'e Barka da Zuwa ya k'arfin jikin?
"Alhamdulillah Kb ya Amsa, mutumin yacigaba,


"Ankawomana wannan case yau kwana 8 kaman yanda kasani, anma bamusamu gudanar dashiba sai yanzu saboda Rashin lfynka, duk da Mun Gudanar da wasu Bincike, akan wanda abun yashafa ita wannan kad'ai muke jira dan mu cigaba,

Idan Munyi Nasaran gano komi zamu tarkasa masu laifin Kacokam mu mik'asu kotu,

Yad'an gyara zama ya Kalli Dijah, "Yan Mata meye Sunanki, "Sunana Khadijah Abubakar mai d'ori,
"Munsamu lbrn kece kika karb'o cake d'in Bikin Kabir da Nafisa, ko zaki gayamana meye tsakaninku da shi,
"Yayana ne ta Amsa a taka'ice,
"To meye Wannan yayan naki ya miki da har kike sha'awan salwantar dashi ta hanyan sa masa Guba?

D'ago idonta tayi da d'an tsoro ta kalli Kb shima itan yake kallo ido waje da kai yamata Alama da ta Amsa, ta dawo da kallonta ga tambayan.

Tace "ko d'aya bansa wani abu acikin cake ba hasalima ni idona baiga cake d'inba,

Aranan da abun ya faru, har na shirya zan fita Mami tace sunce inkarb'o musu cake, saboda Amaryan ta fita, kuma inba aje yanzuba mai yin cake d'in zata fita, bansan meyinba bansan inda takeba, akace wai Driver yasan komi, shi yakaimu me cake d'in agabansa tacemin bata gamaba injira ta shigar dani wani d'aki har bacci yad'aukeni wayan Driver ne ya d'agani na fito ko kallonta banyiba dan b'acin ran jiran da nayi bansamu naje inda zanjeba, kai tsaye gaban Mota na shiga nace masa mutafi kobata gama ba insun matsu zasuzo su karb'i abunsu, nikam na gaji da jira, ita da Kanta ta bud'e baya ta ajiiye tana ban hak'uri, ban ko kulataba muka tafi, muna isa nafita na shiga cikin Gida ba tare dana waiwayi wani cake, ban san ya akayiba suka d'auki abunsu,


Jinjina kai kowa ya shigayi a wajen Banda Nafisa da iyayenta da suka kusa bushewa, mai tambaya ya gyad'a kai ya kalli Mata meyin cake yace "Haka akayi? Cikin tashin Hankali ta gyad'a kai alaman Eh,

Gud "Yanzu ina Drivern?

Mami tace "yana waje shi ya kawo ni,

Nan yasa aka shigo dashi, Yanda Khadijah tafad'a game da yanda cake d'in yazo haka shima yafad'a

Ya tambayeshi waya d'auki cake d'in?
Yace Khadijah tana shiga Nafisa da k'awarta suka iso wajen Nafisan ta bud'e Motan k'awan ta d'auka suka tafi,


Tun Kafin mai tambaya yakuma cewa komi, Alhaji Ya'u yace "k'arya takeyi ba abinda ya had'ata da Kabir, Kabir ba yayanta bane, Mijintane da aka musu auren dole bayi so bata so, Uwansa ta had'a,


Da sauri Mai tambayan ya d'ago kai yanabin duk 'yan gurin da Kallo cikin Mamaki, Alhaji Ya'u sai Murmushin Mugunta yakeyki Musamman da ya hango tashin Hankali a fuskan Kabir da Mami,


Cikin Rud'ewa Kabir yake kallon Dijah so yake ta kalleshi duk da baisan me zaice mataba, Itakuwa idonta nakan Mutumin yana ta Rubutu, jim kad'an yad'ago ya kalli Dijah,

"Kikace min Yayankine? Ashe ba hakabane,

D'an Murmushi tayi tace "Amatsayin k'anwa, Dr da Aunty Nafisa suka aikeni ba amatsayin Mata ko kishiyaba, in hakane ai kishiya bazata aiki kishiyaba, tunda Mami ta kawoni ahanunta nake amatsayin 'ya ba sirikaba, dan haka naje ma Aunty Nafisa aikane amtsayin k'anwarta kuma k'anwar wanda zata aura, Kuma ta yarda dani bazan cutar da ita bane shiyasa ta tsallake sauran 'yan'uwanta har da k'awayenta duk da ansan a Al'adan biki k'awayen Amarya suke da Hakk'in irin wannan abubuwa, anma dan tasanni tasan cewa bazan cutar da ita ba yasa ta aikeni, irin wannan aika me muhimmanci,


Gyad'a kai Mai tambayan yayi cike da Gamsuwa,


Kabir ya sauk'e b'oyayyen Ajiyan Zuciya, Burinsa d'aya Kar wa inda suka had'a wannan abu suci Nasara musanman yanda aka had'a dashi, dandai yasa cewa daga Dijah har Nafisa ba wacce zata sa Guba dan ta cutar dashi, dazasuyi hakan da tuni sunyi,


Alhaji Ya'u zai kuma Magana, ya d'aga masa hanu, "Malam kabari inmunzo kanka kafad'i abunda zaka fad'a,

Ya dawo da Kallonsa ga Dijah "Khadijah anmyanzu munsallameki zamu cigaba da Bincike in buk'atan nimanki yazo zamu nimeki,


"Ke Nafisa duk da Abinciken da muka gudanar bamu sameki da Hanuba, zamu cigaba da bincike dake sabida kece jigon komi, Sannan zamu gayyato wannan k'awa taki da sunanta ya fito har sau Uku acikin cased'in zamu zauna da ita Azama na gaba,


Kabir ne yayi saurin mik'rwa, yace ma Khadijah "Lest go, ta tashi suka kama hanyan fita, har wani tsima Nafisa takeyi, ji take kaman ta tashi da gudu ta Mangaje Dijah,


A bakin gate Kb yayi perking bai shigaba dan yau yana son ya lek'a wajen aiki, ya juyo da Kallonsa ga Khadijah da take ta fushin da baisan dalilinba, Yad'an tab'e Baki "yau hankalinki ya kwanta? Kin gane cewa Kabir da Nafisa basu da niyan cutanki?


Turo Baki kawai tayi tace "Mhhmm,
Ya kamo bakin da yatsunsa, yace "Anmafa kin ban Mamaki banzaci zaki iya kare kanki hakaba, Ashe kin iya Magana, ya fad'a yana mik'a Hanunsa ya bud'e mata k'ofa, "Ki shiga Gida nizan fita, da sauri ta wurga k'afanta waje ta fice,



Kabir bashi ya dawoba sai yamma, agajiye yashiga pert d'insa, Bai samu Khadijah ananba har yayi wanka ya fito cikin Jallabiya bak'a dai shek'e takeyi kaman anyi b'arin Mai, sai Sassayan k'amshi ke tashi ajikinsa, ya nufi sashin Mami, a d'akin lya yaji Muryan Mami dan haka ya nufi can da sallamansa, dukansu suka Amsa, Mami tana zaune kan sofa iya tana zaune abakin gado Khadijah tana kwance ta d'ora kanta a cinyan lya tana mata susa cikin gashin Kanta,

Kusa da Mami ya zauna yana fad'i "wash! Mamina,
Mami takai Hanu ta shafi Gashin kansa, tace "Sory Son! Kaje Office ne?

Hakanan yaji Bakinsa na fad'in k'arya, "A'a Naje Midical chekup ne,

Mami tace "olrigth ince dai ba Wani Matsala? "Nothing, ya fad'a gami da mik'ewa haka nan ya tsinci kansa da jin kunyan k'aryan da yayi, dan Haka yaji yabar gun tun ba'aganoshiba, Iya tace "yanzu ina zakaje? Ya shafi cikinsa yana fita yace "Yinwa nakeji,


A falonsa ys zube yana tambayan Kansa dalilin k'in sanar da Mami aiki yaje,


Ahaka Khadijah ta shigo da kayan Abinci ta jera sannan ta nufoshi, agefenshi ta tsaya, kaman mai shirin komawa tace "Ga Abincinka, da Hannayensa biyu ya kamo k'ugunta ya d'orata kan cinyansa, yana kallon k'irjinta, "Me kikaje yi a sashin Mami? Yayi Tambayan cike da tsarguwa, kallonsa tayi itama batasan ya akayiba taji bakinta nacewa "Nazaci kafara zuwa aikine shiyasa nakoma,


Kafeta da ldo yayi hakanan yaji zuciyansa cikin Rashin jin dad'in Magananta, ahankali ya zamar da ita gefe "jeki kawomin Abincin nan, ya fad'a Ransa adagule, tunawa yayi zuwansa Office, hakanan ya tsinci kansa da yawan tunaninta, sai gashi ita har Murna take zata barshi,


"Allah Nagode maka da ban tab'a Son yarinyannanba, dan da nayi k'oshin Wahala,

Allah kasa kar na tab'a sonta,

Gobe zance Mami zan koma aiki ki tattara kikoma abunki nima inhuta ba ahunda kk min sai sa Ciwon kai,
ya fad'a yana lumshe idonsa,

Ajiye masa Abincin tayi sai tura baki takeyi tana Kallonsa yana loma, ajiye spoon d'in yayi ya kalleta yace "lfy kuwa khadijah?


Tab'e Baki tayi "ai nazaci bazakaci Abincin Gidanan bane dakaje can bata bakabane?


Da Mamaki yace "Can ina?
"Mhmm ai nagane gurin Nafisa kaje ba wani Medical chekup, duk takardun ka na Asibiti sunan ba kad'auki ko d'ayaba, ai dama naga kallon dakukayi ma Juna acan inda mukaje,



Mamakine ya hana shi furta komi illa kallo da yake binta dashi, itakuma sai k'ik'kifta ido takeyi tana jiran mezaice dan tsaban wani irin kishin da takeji ji take kaman k'irjinta zai b'alle,


Ahankali yasauk'e ajiyan Zuciya ya tsiyayi Drink yasha, ganin bazaice komibane yasa tashige bed room, shidai ldo kawai yake k'walalowa, yana tunanin irin badak'alan da sukayi da Nafisa d'azu awaya akanta,

"Cab Ni Kabir yaushe zan iya irin wannan?



*Ummu Fatimace* 😘
[8/11, 3:51 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š

πŸ’™β€πŸ’›πŸ’šπŸ’œπŸ§‘
*Zuwaira Ummu Maryam Nagode Nagode Allah yasakamiki da d'umbin Alkhairi yaba da Lada Bazan iya kwatanta miki lrin farin cikin danajiba, na wannan kara da k'auna da kika nunamin saidai ince Allah ya Raya mana Su Maryam da imani Allah yabar zumunci* 😘
β€πŸ§‘πŸ’›πŸ’šπŸ’™πŸ’œβ€


_Hausawa sukace so me sonka koda karene_ _wannan haka yake anma inkaren ba mai cizobafa_ 😳😳

*Group d'in Sawwama AG bazan gaji da jinjina mukuba da fatan Alkhairi agreku baki d'aya* 😘
_Mumy Manal gataki_πŸ‘πŸ»

5⃣2⃣

Yau take Juma'a Haji Babban Rana, Ranan Maza da Mata, Ranan da Allah yake sanya wani d'an lokaci yazama Bunus ga bayinsa duk abunda Karok'a awannan Lokaci Allah yakan Amsa, wannan lokaci ana son Mutum ya dukufa nimansane tun daga bayan la'asr zuwa Magriba zaka dace da lokacin.

Haka anason A karanta Suratul Khahfi,akwai falala mai yawa acikinsa yakan taimaka wajen tsaren Mutum acikin qabari daga fitinan Dajjal.

Abunda Mami ta d'aura Tilon d'anta kenan akai tun yana k'arami, haka bayan zuwan Dijah gidan sosai ta koyar da ita kuma ta d'auka, dam basa bari wannan garab'asa ya wucesu.

Kabir yana ta shirin Zuwa Masallaci bayan yagama karatunsa, yayi wankan Juma'a kaman yanda sunnah yatanadar, ya goge jikinsa tas bayan yasa inner wears ya feshe jikinsa da Body spray, Yad'auko wani lallausan Boyel yasaka army Green, Ya sanya Hula kalan kayan da Ratsin farin zare da brawn ajiki ya d'auki turare ya feshe jikinsa gaba d'aya, kallon fuskansa yayi a Mirrow gami da d'aukan brush ya k'ara kwantar da siririn sajensa, bak'aramin kyau yayiba, yasa Takalminsa have shoe ya fita, tundaga falo yake jin wani daddad'an k'amshin Girki na fitowa daga kitchen kai tsaye nan ya nufa a k'ofan kitchen d'in ya tsaya yana k'aremata kallo, itakuwa ta duk'ufa ma yin Girkinta hakanan yau ta tashi da son yin Girke2 kaman mai shirin tarban wani, k'amshin turarensa da ya ziyarci hancintane yasata juyowa ahankali shiko ganin zata juyo yasa yashigo da sauri dan gudun kar ta dank'ara masa ihun da tasaba, kallonsa takeyi har ya k'ara Matsota ya hure idon yana d'aga mata gira, murmushi tayi gami da jan numfashi, ta maida dubanta ga Albasan da take yankawa, ya lek'a tukunyan da yake kan wuta, yana fad'in me kike dafawane haka yau gaba d'aya kinzama busy? Gida ya kaure fa k'amshi kala2,


Murmushi kawai tayi batare da tace komiba, ta d'ago suka had'a ldo, ya juya har yakai k'ofa ya juyo ya kamata tana k'are mishi kallo, dawowa yayi da baya yana wani taku ya k'araso gabanta, yad'an karkata tsayuwa yana d'an karkad'a harcensa acikin bakinsa, gami da d'an kanne ldo, "Ya dai 'yan Mata wannan kallonfa? In wankan ya miki kifito ki fad'a kar kibarshi acikinki, kallonsa ta kuma yi, Sannan tayi k'asa da kanta ta kunna fanfo ta wanke hanunta ta juyo har yanzu yana tsaye yana kallonta ta gefensa tabi ta wuce sai da takai bakin k'ofa ta juyo ta harareshi tana Murgud'a baki, k'afansa yad'aga yad'an buga ak'asa kaman xai bita, ta kwasa da gudu tayi d'aki, Murmushi yayi yana girgiza kai, yana duba agogon Hanunsa ya fita da sauri ya shiga Mota ya fita,


Sannu ahankali yake tuk'i yanabin k'ira'an Ayyubi cikin suratul khahafi, har ya isa Massalaci yayi perking, sannan ya fito gami da rufe Motan ya shiga ciki.

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Alhaji Ya'u na Hango da Babban Riga yana Rik'e da Sallahya ahanunsa ga dukkan Alama daga masallacin Juma'a yake, yana shiga Gidansa da sauri rai ab'ace har yakai falonsa anan yasamu Matar Gidan tana ninke kaya tana sawa acikin Sif, tana wak'an Uwaliya mai Amada na Uwar gida, kallo d'aya tamasa ta kau da kanta, dan inda sabo tasaba da wannan d'aure fuskan nashi tun bayan Rasuwan Mahaifin Kabir kullum acikin k'unci yake dan yakasa samun abunda yake buuk'ata, kullum acikin farlurer yake sai gashi kaman zai samu biyan buk'ata sai wani abun yazo ya gifta, shikenan kullum acikin bak'in ciki gashi d'an Arzikinsan da yake Rainawa duk ya k'are awajen niman Hanyan salwantar da Kb, gashi Kabir Arzik'insa sai dad'a bunk'asa yakeyi, yanzuma wani k'arin bak'incikin da ya k'unso shine bayan an idar da sallah amasallaci kabir ya biyo bayanshi, suna gama gaisawa yake sanar dashi cewa akwai wani capanin da ya saya a Lagos, zaije ayi lunching d'in.. tsabn bak'in ciki baima bari yagama jiba, ya shige motansa yana hararansa, yace "tsaban karaianani anan ne zaka tareni da irin wannan maganan, mts yaja tsaki gamida yi wa Motansa key kamanzai bankeshi ya bad'eshi da k'ura yayi gaba,


Murmshi kawai Kb yayi ya shige motansa yayi gida, dan tun ba yauba yasan tsatsan dake Ran Baffan nashi,

shi kuwa Alhaji Ya'u da k'yar ya iya kai kanshi gidansa, zuciyansa sai zogi take masa,


Wurgi yayi da Sallahyan hanunsa yana bankamata harara, sosai ya lura da ita yanzu sam bata mutuntashi ko dan taga yanzu baya da Kud'ine?

Cikin zafin rai ya kalleta, "banga kina wani shirin bikin Nafisa a gobe ba, ajiye rigan da ta d'ago zata ninke tayi, tana kallonsa da Mamaki dan daren jiya ba irin artabun da basuyi dashiba akan maganan auren anma fir yak'i yace Bazai ba da 'yarsa ga Mara kunya irin Kb ba,

"Na lissafa nayi shawara naga bai kamata ace duk mun taru mun Rasa abunda muke soba, ni nakasa mallakan dukiyan kb, sannan tilon 'yata ma ta rasashi amatsayin mijin da takeson aure,


Ya furzar da iska yaci gaba "Naji sunyi shiru basu ce komi akan maganan bikinba, hakan ya nunamin daga shi har Uwarsa da 'yan'uwanta basa son auren kenan, to Wlh muddin ina numfashi sai anyi kuma a Goben zan cika ma Nafisana Burinta, inyaso su had'iye ransu su mutu, kuma banga wanda ya isa ya hana wannan aurenba, ya k'arashe cikin k'araji yana ciza hak'ora, sannan wata Murmushi mai ciwo, "Kuma bazan bar farautansaba koda 'yata tana hanunsa,


Maman Nafisa tashi tayi tsaye cikin wani irin Farin ciki dandama tana shirin tagama abun da takeyine ta k'ira Nafiasan suje wajen boka, yabata maganin da zai yarda ayi bikin dan dahakan ta lallab'a Nafisan bayan tagama kuka kaman ranta zai fita,


Hanunsa ta kama ta zaunar dashi tana washe baki "Zauna nana muji dad'in yin batun, nagode ma Allah daka fahimceni inbanda abunka ai indai Nafisa ta auri Kabir mun warke ina mai tabbatar maka duk k'udurinka akan Kabir zaka cinmasa, ba b'ata lokaci, Sannan Dukiyanmu zai farfad'i ta Hanunta, zata Dinga Amsarmana da dabara, ta kuma washe baki,

" karkaga yanda tad'aga hankalinta datasamu lbrn kace anfasa bukin, yanzu zan k'irata in sanar da ita, wayyo Nafisana yau zatayi kwana zaune dan farin ciki, saidai wani hanzari ba guduba, Shin yaza'a b'ullo ma iyayen nasa? Tunda kaga har yanzu case d'innan ba agama bincikenba,


Wani uban tsaki yaja yana zabga mata harara, "yo duk ba ke bace da k'aramar k'wak'walwanki kika shirya wannan shirmen, Kabir d'an kazane? Dazaki shirya wannan shirmenki yayi tasiri? Wlh nagaya miki kisan yanda zakiyi ku cigaba da b'oye meena inba hakaba duk randa aka ganta aka bincika ba ta da hanu wajen samasa poising d'in to dole agano gaskiyan magana ananne kuma zan fito inwanke 'yata wlh saidai a hukuntaki ba itaba,

cikin firgici take tasharan zufa duk da taji zafin maganganunsa, ta dan zai Rina, takuma san tabbas Meena bazata cigaba da b'oye kantaba duk randa aka ganta kuwa gaskiya zatayi halinta, aranta tace "ai wlh kuwa xa'ayita dan kaima zan maka tonon tsilili bazan shiga risky ni kad'aiba.


Mik'ewa yayi yana zabgamata harara ya fice shi kad'ai yake sambatu amota yana tafiya gidan Abban Habib, "Barin je musu ta mutunci insunk'i wlh ayita ta tsiya tsiya ko

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment