Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yan bad'o har anata yabonsu wai suna da ladabi, basuyi tawayeba.

Habib yayi k'asa da kansa yana Dariya "Allah Mami k'arya yakemin ni bansantaba.

"To Allah dai yasanya Alkhairi tafad'a tana Duba l.V cards d'in dayake gabansu.


"Mmmn yauwa Kabir kaje kad'au komin Khadijah da Allah yanzu dare yayi, tafad'a tana shiga ciki.

Dukansu suka mik'e Kabir yace "Habib muje gidan Sani daganan ka rakani wajen wancan fitinanniyan, wai ltama yau zata dawo gidannan, Jiya Dady yadawo.

"ka manta ne tun d'azu Abbana yake min waya zanje inji, wai ni yaushe ne aurenkune kai da Nafisan?

Hararansa kawai yayi ya Shige Motan ya rigashi Fita.

K'wank'wasa gate d'in gidan yayi ya koma gefe ya tsaya can Dijah ta lek'o tana fad'in "waye?

Ganin Kabir ne yasa ta fito tana kallonsa wa kake nima?

Dogon tsaki yaja "lnkin ga Dama kizo in mayar dake inada abunyi,

Jujjuya ldonta tayi sannan tashiga can kuma sai ga Bintalo Bayan ta masa sannu da Zuwa tace "yaya Kabir na zaci zata kwanane, inyaso Gobe sai muzo tare.

"nifa Mami ce ta aikoni duk basan wannanba, inzata zo tafito ina da Uzuri.

"Ok bari tafito, tana shiga Dijah ta fito ta d'an tsaya tana langab'ar da Kai "Ayya Likita da kabarni da safe sai mudawo tare tsayawa yayi yana bin bakinta da kallo duk ta inda ta motsashi,

Ya Kalleta inkimgama sai kishigo mutafi karkiyarda ki b'atamin Rai wlh.

*Cab Nasan yau da magana* 😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳


Ummu fatima ce
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡¬

*ALLAH yabar k'auna*🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 3⃣3⃣


Bud'e Motan yayi ya shiga ya kifa kansa akan siriyarin motan yana jiranta, yana jinsu suna magana da flatanci, da Alama fad'a Yartata take mata.

Har saida ya k'osa aransa yana Mamaki wai shine yau yake jiran wata ba Maminsaba? Kodayake hakanma Umurnin Mamin ne.

Yana ji ta Bud'e ta shiga bata gama Rufe motanba ya figeta a guje dan ta gama k'uroshi.

Sai da ya hau titi kafin ya tsagaita Gudun.

Sun Nisa sosai akan Titin Dijah tasake Salati gami da d'ora Hanunta akai,

Agaggauce ya sauk'a akan Titin yana kallonta, tun kafin yayi Magana cikin Muryan Kuka tace Likita Don Allah kamai dani na Manta ban karb'i no.ba ka maidani inkarba ko ka ajiyeni in koma.

"a'ina ne zaki karb'i no.?
"awajen Bintalo.
"no. Meye?
"Numbern Wayan Baffah na.
Wani dogon tsaki yaja ya Figi Motan aguje, yana fad'in nazaci maganan naki mai Muhimmanci ne.

Buga k'afa tafarayi,
Sanin da yayi kad'an da aikintane ta tara masa jama'a, yasa ya sassauta Murya, "indai Numbern Baffah ne in munje Gida Mami zata baki..

"Bazata baniba Lilita ka ajiyeni kawai inkoma.

Yad'an Lashi Lips d'insa cike da takaici wai yanzu indai yana son zaman lfy amotannan sai ya lallab'ata? Shi da Motansa? Sannan shima ba tuk'a kansa yakeyiba, Amma ya d'ukota, Ga mari ga tsinka jaka ke nan.

Tajjuyo tana sharank'olla tace "Likita!
"Khadijah kiyi Hak'uri inma bata bakiba zan baki, Dan Allah kibarni Haka.

"Kayi Alk'awari? Ta tambaya tana Rausaya kanta.

Yad'an ciji Lip d'insa yana furzar da lska yace "Eh. Atak'aice

"Kuma kishare Hawayennan ba abunda namiki wai meyasane halinki yazamo wani irine?

Mai da Bayanta tayi ta kwantar ajikin seat din Motan tana share Hawayen.

Yad'an kalleta da wutsyan ido ahankali yace Silly Girl.

Tuk'insa yaci gaba dayi cikin Nitsuwa Ba sautin komi amotan, sai na Numfashinsu kowa da abunda yake nazari, sunyi Nisa Wayansa tafara Ringing, d'auka yayi ya kara a kunnensa "wai kungama Dinner ne? Yanzu kina Hotel d'inne? Ok gani zuwa daga Haka ya ajiye wayan, yana shirin juya kan Motan yaji anja Dogon tsaki abunda yatsana arayuwansa, wani irin Burki yaja sai da Dijah ta tsorata, ya juyo suka had'a ldo mawa kikayi wannan tsakin?
"Nikam ka maidani gida kafin kaje duk inda za kaje wlh ni ba wani Hotel da zanje ta k'arasa maganan da Muryan kuka,
"Inkuma ban mayar dakeba fa akwai wani abunda zakiyi?
Kin ishenifa.
Kikasake kikasake kikamin wani Rashin kunya Ranki zai b'aci, bamani zaki dinga sakarcinkiba.

"to ni kamai dani Gida kawai.

Jan Motan yayi ba tare da Ya kuma kallontaba, abakin Hanya ya Hango Nafisa ita da k'awayenta, tana ganinsa suka nufo Motan tana isowa ta bud'e inda Dijah take kasancewan Bak'in glass ne sam bata ga mutumba,wani d'an tsalle tayi ta matsa baya kaman wacca taga abun tsoro, Ta fara Wurga mata Harara ta yatsina fiska "Kabir wannan fa?

Ya kalli Agogon Hanunsa "Nafisa shiga Mutafi sauri nakeyi,

"wah inhad'a Hanya da wannan Abar wlh k'aryane, tasake Murfin Motan, tatsaya agefe tana jijjga.

Cikinb'aci rai ya kalli Dijah "Ke Rufemin Mota, tun kafin ta ida Rufewa ya finciki Motan yayi Gaba, suna daf da lsa wayanta ta Hau Ringing a Fuskan wayan taga Auwal da kamar bazata d'agaba sai kuma ta d'auka, "Hello Khadijah gani a k'ofan Gate d'in Gidanku, tad'an Murmusa kajira gani zuwa daga Haka ta kashe, ta gefen ido Kabir ya Kalleta ya tab'e Baki, suna isowa a lokacin Auwal yana Zaune akan Machin d'insa, tace "Sauk'e ni anan, wani irin takaicine ya ziyarci zuciyansa, aransa yana tunanin irin rainin da yarinyan tamasa sake kan Motan yayi gadan gadan yayi kan Auwal wani lrin lhu ta sake tana kallon yanda Auwal d'in yadira yayi gefe, Kabir kuwa ko ajikinsa saima Huci da yakeyi yana Horn, masu gadi suka wangame k'ofan yana perking tafara kiciniyar bud'e Motan amma ta kasa sabo da Rufewa da yayi,
"Meye tsakaninki da wannan kucakin yaron? yafad'a yana tsareta ldo.

"saurayi na ne, ta amsa azafafe, wani lrin bugu yakai ma Bakinta, yana Huci "kundace dashi Sosai, Amma ba a gidannanba wlh kika kuskura ki ka fita saina karyaki sai kibari sai kin koma can k'auyenku yabiki.
Cikin kuka tace wlh sai na fita kuma k'auyen mu ai... Bata k'arasaba ya fincikota bai tsaya da ita ko inaba sai gaban Mami ya wurgata gefe yana huci Mami ta dafe kai,

"Oh ni Fatima wlh tuntuni lna zaune anan ina tunanin wata wainar ake toyawa mancewa nayi nace kad'auko ta, na had'a Wuta da Auduga, Haba Kabir meyasa ne kake biye ma Yarinya k'arama haka?

Zama yayi a kujeran dake gefen Na Mamin, "Mami bana biye mata da ina biye mata da tuni na karyata.

Wano k'azamin yarone yazo wai Saurayinta wannan ai zubar da Mutuncine takeson yi ma Mutane, 'yar wannan yarinyan yaushema aka haifeta gata da sakarci Mami wannan ba wuya wani ya yaudareta yajefata wani hali, bata da wayo ko kad'an, ta bari sai ta koma can k'auyansu, sune suke aurar da jarirai inyaso tayi duk yanda taso Amma ba agidannanba.
Ya k'arashe magannan yana nunata da yatsa, wani lrin zafi darad'd'i yakeji ak'irjinsa shi kansa bai san Daliliba jiyake yanason ya tattakata, Dam Dam Mami tajii k'irjinta yana bugawa, karfa tayi gurguwar dabara.


Ta Kalli Khadijah da take ta sharan Hawaye sosai kalamansa suka k'ona mata Rai.

Asanyaye Tace "Khadijah a'ina kikayi saurayi?
Ina kike fita da har kikayi Saurayi?

"Mami a school d'inmu yake, kuma...

Bata kai ga fad'in abunda zata ceba suaka jiyo karad'in Nafisa da k'awarta Meena a falon,

"Wlh Kabir yau sai kagayamin Matsayin wannan kucaka k'azaman yarinyannan agidannan, tun safe na maka waya zan dawo bayan mungama Dinner n k'awata a aroma Hotel.

tunda a kagama nake ta k'iranka baka zoba sai da ka b'atamin lokaci sannan katashi kazomin da wannan Banzan?

Mintunanka nawa da dawowa? Shine ka shanyani acan?
Yau sai nasan waye Uban Wannan Banzan ta fad'a tana Nuna Dijah cike da Wulak'anci.

A fusace Dijah ta mik'e itama tana mata Wulak'ancaccen kallo, "Sam bani Mamakin lrin lafuzan da suke fitowa a bakinki, Innayi la'alari da watsatstsen tarbiyanki, yo ai wanda yake da Tarbiyan mutunta iyayensa ne yake tunanin Mutunta na was...


Kukan kura Nafisa tayi takai mata shak'a, cikin Zafin nama Mami ta finciki Nafisa tayi baya da ita,

"Mami wlh yau sai na kashe yarinyannan kuma sai ta koma gidan Ubanta indai anason zaman lfy, inji Nafisa


"Naga kema dai ba zumuncin gidan d'an'uwan Ubanki bane yake kawoki,

yawon lskancine da tab'ara yake kawoki kinzama bishi zai zai kizo kugama lskancinku... Dijah bata rufe baki ba Nafisa ta k'wace da k'arfin tsiya tayi kanta, itama kantan tayo,

A fusace Kabir ya jawo Dija ya yarfa mata Mari ya nunata da yatsa yana kallon Mami da kamanninta yagama canjawa dan ji tayi kaman Fuskanta ya Mara.

Pls Mami kimai da yarinyannan garinsu Ni kaina abun ya d'auremin kai bansan meya kawota gidannan ba bansan zaman me takeyi agidannanba,

For giveme Mami bayanda za'ayi ahana Nafisa zuwa gidannan, Sannan bazasu tab'a zama wuri d'ayaba Wlh bani son tashin Hankali Mami yanzu Haka kaina ciwo yakemin bazan iyaba, ki mayar da ita Gidansu yak'arasa zancan Kaman zaiyi Kuka, Zuciyarsa cike da tsoron Kallon b'acin rai Kwance Afuskan Mami,


"pls Mami kiyafeni Fitinnan da Hatsabibancin yarinyan yayi yawa.


Cikin matsanancin b'acin Rai Mami tayi taku ta zo gaban Dijah da takifa kanta akan gwiwowinta tana kuka mai tsima Rai ta kamo Hanunta ta wurgata kan k'irjinsa,

"Kasheta Kabir! Kasheta!! Daga nan sai amai da gawanta ai lbrn zaifi tafiya yanda yadace.


Kuna son Sanin Matsayinta ko?
Kanson Sanin zaman me takeyi agidanku ko?
Kanson Sanin Meya kawota ko?

To ku bud'e Kunnuwanku da kyau kuji,

Ta sake kamo Hanun Dijah da tazame a jikin Kabir ta tsuguna tana cigaba da Kuka,

"Wannance Ka k'ira Da Hatsabibiya Kabir Zaman da Khadijah takeyi agidannan Zaman Aurene Kabir, Aure ne ya kawo Khadijah Gidannan Khadijah Matarkace Ta Auren Sunnah Matar kace kake k'ira da Hatsabibiya.

Cikin Matsanancin Rud'u Kabir yace "Mami Mata nawa zaki auramiin? Kince lna England kinsa an d'auramin Aure da wata, Sannan Kince zan Auri Nafisa, Mami lnaga kaman sun isa basai ank'aramin ba.

Mami ta kalli Nafisa da tayi suman tsaye cikin Rashin Fahimtan zancen.

ta koma kan Kujera ta zauna Ta Kalli Kabir da ya bud'e kunne da baki yana Kallonta.

"Khadijah itace Matar da aka d'aura muku Aure da lta lokacin Kana England Kabir ka Nitsu abun yana da sark'ak'iya bata haka naso sanar daku batunba, saidai Naga Abunne yana niman yazamo wani Abu daban Ba haka kawai lyayenta suka d'auketa suka bani itaba har sai da lgiyan Aurenka ya hau kanta, da Aurenta tazo gidanku, Aure kuwa shike raba kowace mace da gidan Ubanta ta dawo gidan Uban wani.


Sai yanzu Nafisa tasamu daman d'aga k'afa ta iso gaban Mamin ta tsuguna, dan sam Har yanzu bata fahimtaba, ta dafa k'afan Mami, "Mami baki tab'a mana irin wannan Wasanba.

Ni kad'aice Matar da Kabir zai aura bayana ba wata macen arzik'ima bare wannan Kucakan ta nuna Dijah da tazama mutum mutumi.

Mami kidaina fad'a kar 'yan Amin su Amsa bazan iya zama da kishiyaba Mutuwa zanyi.

Mami tadafa kafad'anta Nafisa Kidaina wannan Furucin Matan da suka fiki Daraja Matan Manzon Allah (S. A. W) da Matan sahabbai sun zauna da kishiya Kada kiyi jayyaya da Abunda Allah ya Halalta.


Khadijah Matar Kabir ce Ke bakisan komi game da lyayentaba, Amma kai Kabir kasan irin kara da karamcin da suka maka, dan haka naso Rama musu ta wajen son d'aukan Khadijah dan ln bata lngancaccen llimi Musama lura da nayi yarinyan tana da Hazak'a da baiwa.

Bayanda banyi da Mahaifintaba akan yabani ita fir yahanani ita har Manyan garin nabi ta hanunsu surok'anminshi yabani ita, yace bazai tab'a bada 'yarsa Mace atafi da itaba, koda kuwa ma 'yar'uwansace, ban tab'a sha'awan ace ina da wani d'a na miji bayan Kabir ba sai awnnan lokaci dan sam ban kawo had'a auren da Shiba saboda sanin Halinsa na nuna ko oho akan auren, naji araina da ina da wani d'an dana nima masa auren ta dan nasan tahanyan aurenne kawai zai bani ita.

ammadai tunda nadawo na duk'ufa da Addu'ah da istihara akan abun kullum sai inji lnak'ara son hakan danhaka nayi shawara da Yayana da Abban Habib, suka bani goyon baya d'ari bisa d'ari kan aura ma Kabir Khadijah.

Nan dannan suka wuce gaba bak'aramin daga akashaba lokacin da suka sami Baffanta da Maganan, kasancewan Khadijah ta dabanne awajensa.

Ahaka dai da Allah ya k'addara akayi, Rana d'aya aka d'aura dana 'yar'uwanta aka kawosu tare saidai na rok'i lyayenta kar su sanar da lta kasancewanta k'araman yarinya ko dasu suna aurar da yaransu da wuri Dai tayi k'ank'anta.

Ahaka aka kawota amatsayin tayi ma 'yar'uwanta Rakiya ankawo amarya da ita.

Tad'an Nisa takalli Kabir da zufa yake ta d'iga daga goshinsa, "Abban Habib shine Waliyinka lnkana niman k'arin bayani kaje gurinsa zakaji.

Da Rarrafe Dijah ta matsota "Mami kin mantane kiiyi Hak'uri bani bace naji da wanda aka musu Aure Aliya Sunanta Ranan naji kin fad'a wlh bani bace tafd'a tana fashewa da kuka.



"Wancan auren bai yiwuba zanbaku lbrn yanda abuun ya kasance.


Sai Alokacin Nafisa tasamu daman k'wallah k'ara tafita a guje kamar Mahaukaciya sabuwar kamu




*Tofah inajiran Comments d'inku zafa ayita* πŸ˜³πŸ˜‚


MMN Temah😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 3⃣4⃣


Cikin zafin nama Kabir yabi bayanta, tana daf dakaiwa jikin gate, Daga inda yake tsaye yayi Umurni Ma Mai Gadi Da ya rufe Gate d'in kar yabarta tafita.

Agagauce Mai Gadi yacika Umurnin Ogan nasa, tana kaiwa Jikin Gate d'in Ta kifa kanta ajiki tana Bubbugawa Da Hannayenta Duka Biyu tana Kuka kamar kanta ya fashe.


Ahaka ya iskota, yatsaya abayanta Zuciyansa Kaman yafita, sam baya son tashin Hankali, Murya araunane yace "Nafisa! Cool dawn pls Kidaina irin wannan kuka, "Kabud'emin k'ofa intafi kabir".


"inazakije awannan yanayin ki nitsu Kar kiyanke Hukunci cikin Fushi manzon Allah (S. A. W) yayi hani dahaka.


"No Kabir banison jin komi kabarni inatafi gidanmu, bawani abunda zaka gayamin anriga anmin Illah" tayi maganan cikin k'araji.

"Look Nafisa zo muje Part d'ina Muyi magana inyaso sai inmaidake Gidan, ya rik'o Hanunta, sannan yayi umurni ma Driver ya maida k'awarta.

Rarrashin Duniya Mami tayima Dijah Amma fir tak'i tayi shiru, tahad'a kai da gwiwa sai k'iran sunnan Baffa takeyi.

Iya wacce tayi jugum ad'aki tana jin irin badak'alan da yau akeyi agidanne ta fito, jin abun yak'i ci yak'i cinyewa.

Kamo Hanun Dijah tayi cike da Matsanancin tausayi, don duk abinka inkaji irin kukan datakeyi sai zuciyanka ya karye.

Abakin Gado ta ajiyeta ta d'ago kanta tana kallon Fuskanta, "Kiyi Hak'uri Khadijah ki kwantar da Hankalinki da yardan Allah kece da Nasara.

"lya Baffah na, lya zanje wajan Baffahna, kitamakamin lnason Ganin Baffah da lnna ta, na hak'ura da Karatun dan Allah lya kisa amidani Gidanmu kinji? Ta fad'a cikin raunanniyan muryanta da ya Dishe.


"To kiyi shiru za'a maidake amma kidaina kukan haka kar kija ma kanki ciwo.

Dak'yar ta lallab'ata tayi shiru.

Gidan Mami dayake cikin walwala kowani dare yau sai gashi yazama kaman ba kowa aciki,

Dan tunda Dijah tayi Sallan Magriba da Isha'i ta haye Gadon lya ta k'udundune, Zazzab'i Mai Zafi ne yarufeta, ko Abinci takasa ci, Ahaka Mami tashigo ta sameta, Bak'aramin Damuwa tayi ba Lokacin data tab'a jikinta taji zafi rau, data mata Magana cikin Kuka da dashshiyan Murya take cewa "Mami Baffahna!


Iya tace "Fatima ki k'ira Kabir man yadubata". Ko zai bata Magani zazzab'in ya sauk'a.

"Rabu dashi Kawai lya yaje yayi ta Faushinsa zan k'ira adubata da Safe lnsha Allah.

"Fushi kuma?
"Eh Fushi yakeyi da ni bakiga tunda yafita bai dawoba?
A'a karkice Haka, kinsan tunda suka fara maganan bukinnan dama bai cika dawowa da wuriba,

Kabir bazaiyi Fushi dakeba dukda anmasa abunda yaran yanzu bazasu lamuntaba.

"mhmm kawai Mami tace tafita.

A falo tasamu Kabir yana zaune akan kujera ya Dafe kansa yana Kallon T. V kallo d'aya zaka masa kagane Hankalinsa baya jikin Kallon, Jin motsin dayayine yasashi kallon Wurin, Mami yahanga tana hauwa Sama.

Jim kad'an yatashi yabi bayanta, Waya yasamu tanayi da Dr Asma'u dan haka yazauna gefe sai da ta gama, Shiru ya ziyarci d'akin.


Kabir yayi gyaran Murya yana kallonta "Mami na naga Kaman Fushi kikeyi dani.

"Nikuma Kabir?
Taya za'ayi inma laifi Sannan inyi Fushi da kai? ...

"Laifi Mami? Wlh bakimin Laifiba, kiyi Hak'uri kimin Uzuri.

"Namaka Aure Kabir Shine laifin danamaka.

"Subahanallahi.

"Mami mungama wannan maganan ai, yafad'a yana zaro ido.

"daa kenana kafin kasan wacce aka auramaka, Yanzu kam kagano cewa Hatsabibiya mara kunyace, tafad'a tana k'are masa Kallo.

"Bahakabane Mami ninafi kowa Sanin yarinyannan wlh bata da dad'i Mami, amma ban isa jayayyiaya da Umurnin kiba.

Saidai Mami ya maganan Nafisa? Bazai tab'a yiwuwa inhad'a Nafisa da wannan yarinyanba Muddin inason zaman lfy.

Kuma ba hali ace za'a fasa Auren Nafisa.

Shiru Mami tayi tana nazarinsa can ta nisa tace "Karkadamu Ka Auri Nafisanka da zaran Khadijah tagama makarantanta zan maidata ga iyayenta kaman yadda ka buuk'ata inkuma tasamu miji anan shikenan sai na aurar da ita.

Dumm!! Yaji maganan ya daki zuciyansa.

Shiru yayi cikin Mutuwan Jiki, Kalaman suna masa yawo a Kansa can ya nisa Mami badai Fushi kikayi bako?

"Ko d'aya banyi fushiba Kabir saidai kafinnan lnason Kasani duk yanda ka kai da k'inta Tana da Hak'k'i kafin wa'adinmu yacika.


Kallon Mamin yakeyi da wannan dunk'ulallen maganan nata.

"Kaci Abinci ne?
"Wlh Mami nakasa cin komi ne.

"yanzu zaka iya ci ai tunda nabarka da zab'inka, baki bud'e yad'ago zaiyi magana, tadakatar dashi da Hanu tashi kaje kaci Abincin ka ni Kwanciya zanyi.

Mik'ewa yayi cikin Mutuwan jiki, Har yakai Bakin k'ofa tace "ln kagama cin Abincin ka kawomin Maganin Zazzab'i,

Yad'an Rausayar da Kai "Zazzab'i kikeji Mami?

Kaman bazata Amsaba tace "Bani bace, Khadijah ce, inka kawo ka kaima lya zand'an watsa Ruwane.

Juyawa yayi yafita kaman Mara laka, kodaya Haye daining ba yanda baiyiba yaci Abinci Amma yakasa.

Tashi yayi kaman wanda aka tsakaleshi, ya nufi pert d'insa, Baiijimaba yadawo da magani yashiga d'akin lya,

Akan gado ya hango Dijah kalle kalle yashiga yi baiga lyaba saidai yaji Motsi abayan gida.

Ahankali yatako Har gaban gadon jin irin Numfashin datakeyi.

Ya bud'e Bargon da ta rufe Fuskansa dashi, yak'ura Ma Fuskan ldo Bacci takeyi amma fuskan yayi fayau dashi alamun akwai damuwa akansa sai sheshshek'a takeyi da Alama taci kuka har ta gode Allah, Yasa yatsunsa Biyu ak'asan Wuyanta, saikuma ya janye da sauri yasake Bargon yajuyamata baya.

Dai2 Lokacin lya tafito kallonsa takeyi har tazauna akan Sofa, "Kabir! Yanzu kadawone? Kazo dubatane?.

Yatako ya k'araso gabanta yana yamutsa Fuska "Mami ce tace inkawo kibata, yafad'a yana Mik'a mata, karb'a tayi tana bud'ewa yana mata bayani yanda zata bata.

Ya juya zai fita Har yakai Baki k'ofa yajuyo ya kalleta, "Wannan Numfashin yanzu tafara ko tuntuni? Ina nufin kafin tayi bacci tanayi ko sai datayi Baccin?


"a'a Gaskiya sai da tayi Bacci naji tanayi, inaga Ko Kukan datayine yasa haka Don tayi kuka sosai.

Ya yamutsa Fuska "ai dama ita ba abunda ta iya sai koke2, kuma tasan cewa itan ba kaman Normal Mutane bane, daga haka yafice.


Iya ta tab'e Baki tabi hanyan da yafice da Kallo tace "kaji dashi dai Gulmammen Yaro.

Washi gari da safe Dr Asma'u tazo duba Dijah kaman yanda sukayi da Mami, Bayan binciken datamatane sukafito a falo suka zauna ta kalli Mami inaga kaman yarinyannan matsalan zuciyane da ita,

Sai daima Abunma yazo da sauk'i ga ku da Likitan Zuciya agida Dr Kb sai yadubata,

Mami tajinjina kai "da nayi zaton ko matsalanta ya shafi Fanninkine.
Dahaka sukayi sallama ta tafi.


Atake Mami tayi waya ma Habib tana nimansa,

Kabir yana zaune ad'kinsa duk yanda yaso da yacire duk wata damuwa da matsala aransa abun ya fasakara


Ba abunda yafi tsayamasa aransa irin furucin Mami nacewa In Khadijah tagama Makaranta zata maidata Garinsu ko ta aurar da ita shin hakan yana nufin tayi fushi dashine?

Kuma to meye matsayin Aurensa akanta?

Abunda yake tayi kenan yasak'a wancan ya kunci.


Ahaka Yaji ana niman ordern shigowa, nan yaba da ordern Habib ne yashigo yazauna Kujeran gefensa yana kallonsa "Man yadai? Tun jiya banganemakaba any problem?

Tab'e baki Kabir yayi gami da ajiyan Numfashi mai k'arfi yad'an kishingid'a acikin kujera, Habib ya d'anyi Murmushi.


"Yauwa Mami ce ta k'irani ashe Khadijah bata da lfy ne? Kabir ka bata Midicine mana.


Hararanshi Kabir yayi "a wani dalilin?

"Dalilin fanninkane kafini k'warewa a fagen.

"Eh amma ai wainda suka nimokan sunfika sanin hakan ko sokake inyi shishigi?

"Mamice fa tagayamin,

"Eh Mamin, watak'ila tafi yarda dakaine akaina.

"Amma Kb ai kaine....


"Shittt! Malam kaje kayi aikin ka kawai kar kasani aciki.

Habib yayi dariya sannan ya yagi takarda yazaro Biro a Aljihun Kb yana Rubutu d'an karkato kai Kabir yayi yana lek'awa ta wutsiyan ldo Habib d'in yake kallonsa yanagama Rubatawa ya mik'e Kabir ya ja tsaki "Amma dai bakasan mekakeyiba Midicine d'in da Mai hert Disease yakamata yasha kenan?

"Eh asanina shi yakamata Malam banson shishshigi.

"mtsss kb yakuma jan tsaki ya finciki takardan yayaga nan yashiga gayamasa Abunda zai Rubuta shikuma yana Rubutawa.

sai da Habib yanimo Maganin yakai ma Mami Sannan yadawo wajen Kb.

Alokacin har yawatsa Ruwa ya canza kaya, a k'ofan falo suka Had'u, sannan suka koma tare suka shiga Mota, Har sun fara tafiya Habib yajinjina kai "Gaskiiya yarinyannan tana jin jiki, Kb yayi kaman baijiba.



Can anjima ya nisa yana kalon Habib "kasan wai yarinyannane Mami ta had'amu da ita?

Habib ya gimtse Dariyansa yace "Wata yarinyafa?

"Wannan mai rawan kan tsiyannanman.



"Wai Nafisa kake fad'a?

Azafafe yace "Khadijah dai Nafisa kuma tana da rawan kai ne?

Habib ya shek'e da dariya yace "Af zancen yazo kunnenka kenan, yaushe kasamu labari? Ya ciro wayansa ya d'auko masa vidion Auren yace "gashi kaima ka shaida wlh Kb aurenku yayi Albarka kaga jama'a karkaso ka ganni Ranan wlh kaina sai huruwa yakeyi munzama manya, Kabir da ya k'ura ma waya ldo ko k'iftawa bayayi yanajin yanda sunasa yake tayawo a bakin mai shela abun daya k'ara bashi mamaki shine yanda yaga abokansa kaca2 a wajen amma arasa murum d'aya da zai gaya masa.

Dogon tsaki yaja ya wurgo masa wayan acinyansa, Gaskiya kai ba k'aramin Munafukibane shine ko a fuska baka tab'a nunaminba, Gaskiya angama dani yandama naji anata k'iran sunana ana had'awa da nata.

Hahh shiyasa a Ranan kak'irani kakw ta min dariyan iskanci kana hausa.


*Kuyi hak'uri da wannan wlh abubuwane suka sha kaina basonabane bana typing akan kari, sanna kuyi hak'uri da typing Errow masu k'irana awaya da masu min masdage a inbox nagode* 🀝🏻

Ummu fatima ce 😍😳
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment