Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

insha Allah Gobe zanyi mai yawa πŸ˜πŸ˜‰


*Ummu Fatima* ce 😘
[9/4, 11:15 PM] Hauwa Jameel: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH QAYAH*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣0⃣

Shida kansa yayi driving Har cikin Garin Rugan Juma, lokacin da Ya isa k'ofan Gidan Baffahne k'irjinsa ya buga sam baisan da wani ldo zai kallli Baffah ba dan baisan me Maminsa tace masaba da tadawo masa da 'yarsa, shin ta inama xai fara??



"oyo oyo Likita Iro ya katse masa tunani yana kiciniyar bud'e Motan,

Kb ya sauk'e ajiyan zuciya ya dawo da kallonsa ga iron har yanzu kiciniyar bud'e Motan yakeyi,

ya bud'e Gami da sako k'afansa yana d'an Murmushi, lro sai washe Baki yakeyi yana masa lale Maraba, Kb ya dafa kafad'ansa yana Amsawa Fuskansa asake,


Nan matasa suka fara kewayeshi suna Amsan gaisuwa, baiyi k'asa a gwiwaba wajen basu kyautan da yasaba idan yazo,

Da k'yar yasamu kansa ya shiga ciki da Sallamansa Inna tana zaune da Littafin arba'una Hadis tana dubawa cikin kad'aici wanda yazame mata jiki,


Jin saallamane yasata d'agowa gami da kallon hanyan wajen ta Amsa cikin fara'a gami da bashi izinin shigowa dan tuni tagane Muryansa,

Ta tashi da saurinta ta d'auko taburman Kaba da yasaha Kalal Green da pink da yellow, ta shimfid'a Masa tana fad'in lale maraba marhaban da zuwa,

Cikin kunya da surkantaka yale Amsawa, Ta koma ta d'auko Kwanon sha ta tsiyayo masa Ruwa mai sanyi A Randan k'asa, ta dire sannan ta juya nimo wani Abun,


Ba b'ata lokaci ya d'auki Ruwan yasha duk da bai jima da shan Ruwan Faro a Motansaba,

Ya ajiye kwanon gami da sauk'e Ajiyan zuciya yana kallon Cikin Gidan Sosai Gidan yabashi sha'awa, yanda tsakar Gidan yasha shara ga zanen tsintsinyan Gwanin sha'awa a tsakat Gidan sai k'amshi k'asa ke tashi, ya kalli Wani Rumfa da yake gefe tukwaneni a kife akai sai ka rantse ba a wutan itace ake d'aurasuba, k'al suke ba alaman bak'i ajiki, kalle2 yakeyi sosai, ko ina na Gidan tsaf yake gwanin sha'awa,


K'ara sauk'e ajiyan zuciya yayi aransa yana tunanin ba abanza Khadijah take da tsentseni wajan gyaraba,


Inna kam sai jera masa abubuwan ci da sha takeyi, Sannan ta zauna suka Gaisa cikin Mutunta juna, ta tambayeshi lbrn Mami Sannan ta tashiga Kitchen tana sabganta dan tabashi daman tab'a abunda ta kawomasa.



K'ura ma k'ofan d'akin lnna ldo yayi gani yake kaman Xaiga Khadijah ta fito, yakasa cin komi zuciyansa sai kaiwa da kawowa takeyi, Gaba d'aya yarasa Sukuninsa,

Ahaka Baffah yashigo ya tarar dashi,

Kusa dashi ya zauna cikin farin ciki yake marabtansa, gami da bashi Hanu suka gaisa,


Baffah ya gyara zamanasa yana Fuskantansa, yace "Su Hajiya suna nan k"alauko?
"lfy k'alau Kb ya fad'a cikin wani lrin yanayi, yana jiran Baffah ya tuhumeshi akan diyarsa,


Ya Dijah 'yar Rigima tana nan lfy?

Maganan Baffah ta katsemishi tunaninsa,
Arud'e ya d'ago ya dubi Baffah kaman bai Fahimci abunda ya fad'aba,

Nan Baffah yakuma maimaita Tambayansa, maida Kansa k'asa yayi cikin Matsanancin damuwa, ya Amsa da lafy k'alau take tace Agaidaku, Baffah yace "To Maddala Nidai bazan gaji da baka Baki akan Dijahba kasan xama da yaro sai Hak'uri Musamman irin Dijah na, Sai kayi Hak'uri Sosai, Kan Kabir ak'asa cikin damuwa da Kunya, Har ga Allah baisan banan Mami ta kawo Dijahba dan baiyi niyan sake zuwa Garin ba tare da itaba.

"To ina Khadijah tashiga? Ya tambayi kansa,

K'ara rikicewa yayi da ya tuno maganan da Mami ta fad'a na cewa iin Dijah tagama shcool dinta tana da zabi ko ta maidata ga iyayyenta ko ta aurar daita ga wani,


Mik'ewa yayi kaman Zautacce Baffah ya d'ago ya kalleshi shidai yau sam baiganema sirikinnasaba,


"Har zaka tafine?
Cikin k'arfin hali yace "Eh zanje ingaida Goggoji kafim in wunce, to sai kadawo,

Yana fita ya bud"e but d'insa yara suka kwashi tsaraban su kayan Abincin da ya kawo masa sannan ya wuce gidan Goggoji,


Zaune yasameta atsakar d'aki tana kankare goro tana afawa abakinta, da sallama ya sahiga ta d'ago tana tafi "oyoyo Mijin, barka da hanya,


Ya zauna yana mata yauwa ta lek'a bayansa tace "Oh Kabiru yauma kazo baka kawomini Dijahba?


"zankawomiki ita Goggoji karki damu, makarantane ya hanata zuwa,

Haka dai kake cewa wani irin karatune haka tun bayan aurenku inaga kai kazo yayi sau uku, anma ita shiru, 'yar'uwantama taxo yafi abunda yafi

D'an Dariya kawai yayai suka gaisa agaggauce ya a jiyemata tsarabanta ya fice sai godiya take masa, ita kanta yanayinsa na yau ya d'aure mata kai, ba kaman yanda tasaba ganinsaba,


A tsaye yasamu Baffah a k'ofan Gida,

Baffah na ganinshi ya hau k'orafi,

"Haba Kabiru irin wannan d'auniya yayi yawa Gaskiya aikin kenan ko kazo ko bakazoba, Kb yad'an Risina yana shafa Kai, yace "Baffa ai wanna shine hak'in d'a ga ubansa, ayitamana Addu'a kawai,


Baffah ya jinjina kai "Addu'akam kullum acikinta muke Kabir sai dai Muk'arata Allah ya Albarkaci zuri'anku gaba d'aya,

Ya Amsa da "Ameen ya d'an k'ara Risinawa "Baffah Maganan komawankannan dai ina k'ara niman Alfarma tuni angama gidan naku Baffah ka taimaka ka koma su Khadujah zasuyi farin ciki sosai su ganka kusadasu,


Wani Murmushi Mai sauti irin ta manya Baffah ya fitar, yana kallon Kb da yaga ya koma masa kalan tausayi,


Yace "Kabir bani da Bakin godiya gareka Addu'ance dai kullum nake binka dashi, Allah ya sakama da Aljannah,

Banak'i makabane da ace zan iyayin yanda kaso d'in danayi Kabir to anma banijin zan iya Rayuwa a ko'ina inba Wannan Ruganba, dana da can duk d'ayane Kabir muna tare, zaku zo duk lokacin da kukaso, ku koma sanda kuka so, so kaga ai bamu rabu,


Ba yanda Kb baiso yasha kan Baffah ba anma fir yak'i dan shi yanaganin ba k'arshen komawa baya irin ace yabi 'yay'ansa Mata garin da suke aure, da haka Kabir yayimusu sallama ya koma cikin Matsanancin tunanin inda Khadijah take,


Gidan Mami ya dawo kai tsaye ba tare da yaje gidansaba, anma wani k'arin haushin bai tarar da ita agidanba,


Dan haka ya dawo Gidansa, A falo ya tarar da Nafisa da Meena suna hira kwata2 basuji tsayuwan motansaba sai ganinsa sukayi kawai ya shigo ba k'aramin razana dukansu sukayiba sakamakon case d'insu da akadakatar acewa Meena tabar gari, Wani irin wulak'ancaccen kallo yabisu dashi, ya wuce a sanyaye Nafisa tabi bayansa k'irjinta yana bugawa, ta murd'a handle d'in k'ofan taji arufe ta d'an buga kusan minti biyar bataji ko motsinsaba, asanyaye ta dawo ta zube cikin kujera tana kallon Meena,

"Nashiga uku Meena nida nake ta murnan aikin bokan da kika samamin d'innan yaci wancan shegiya ta koma k'auyensu sai gashi kuma yau Kb ya ganki wlh ina tsoro kar agano guban da yaci ta hanunmu yafito, wlh inason Kb bani son abunda zai nisantani dashi,


Meena tayi 'yar dariya jin ta sake samun hanyan cin kud'in k'awar tata, tace "haba kekuwa? Inace dai bokan yananan da ransa bai mutuba, kar ki damu ke dai kikawo kud'i sai inkoma inmishi bayani a kashe case d'in,


Nafisa ta tashi jiki na rawa batare da tace komiba tashiga d'akinta ba b'ata lokaci ta fito mata da kud'i tabata ta fita,




Mutum yana nasa Allah yagama nashi akansa aranda nace muku zanmuku typing mai yawa aranan akayiwa Blood sis d'ita Cs aka cire Baby boy acikinta munata jelen Asibiti, bansamu lokaciba wlh yanzuma yawan k'irana yasa nace barin muku wannan kuyi hakuri Ban samun lokaci ne,


Anma inkunyarda zan ta k'aita labarin dan naga kun matsu a gama,


*Ummu Fatima ce* 😘
[9/9, 2:07 PM] β€ͺ+234 813 157 1274‬: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣1⃣

Yajima a kwance Saman Bed d"insa ba abunda yake tunani Sai ina Khadijah tashiga?

Juyi yakeyi asaman Bed d'in hancinsa na jiyomasa k'amshinta, da ya lumshe ido zaiga photon Fuskanta, nan tana masa Murmushi nan tana masa tsiwaannan nata,


Ya rufe idonsa gam k'wak'walwansa na tariyo masa tun Randa idonsa ya sauk'a kanta acikin Rugansu da zuwanta Asibiti, amtsayin pecaint d'insa, da lrin draman da sukayi tayi a lokacin da yaje jinya wajan Babanta, yanda yabarota da yanda yadawo yasameta acikin Gidansu, da irin Rayiwa mai dad'in da sukayi kafin Mami ta shiga tsakaninsu,


Juyi yayi ya Mirgina ya kifa k'irjinsa akan Gadon gami da dafe daidai inda yake masa zogi,


A hankali yafara cewa "Iluv her Mami ireally luve her plaes Mami help my life, Ki taimaka Mami wlh tun asali Khadijah jininane, ninasan irin wahalan danasha a london lokacin da na barta a rugansu, nashiga damuwa aduk lokacin da tuna nabarta da wani d'an k'auye wai yana niman auranta, nakanji kaman xuciyata xata faso, alokaci nakasa gane sontane yake min hakan na I zaton tsanace.


Nashiga matsanancin Farin ciki da nadawo nasamu kin kawomin ita har gida, nasani da gangan nake cusa k'iyayyanta araina, anma inasonta Mami ki ceci Rayiwan d'anki, ki dawomin da Hapiness d'ina, pleasss,


Buga k'ofan da yasakejine a karo na biyu yasahi yin shiru da zantukan da yakeyi, ya cusa Hanunshi cikin gashin kansa yana ya mutsawa, yana sauraron Magiyan da Nafisa takemasa a bakin k'ofa,


Baisan yanda akayiba yajita kwance saman bayansa, tana shafashi gami da Kukan kissa, "Haba sweet laifin me namaka? Zanyi ta knoking kak'i bud'eni sai da na wahala na tuno da k'ofan da yake ta cikin wancan side d'in da xai sada mutum danan,


Shauk'in Dijah da yake cikine yasa yadinga jin Muryan Nafisa kaman na Dijahn, Hanunsa yasa yadafeta sannan ya Mirmigina ya maidata saman cikinsa suna kallon Fuskan Juna, fuskan Dijah ya Gani A Fuskanta Cikin matsanancin Buk'ata ya dad'a Rungumeta,


Tayi saurin manne bakinta da nashi, tana kissing nashi kaman zautattiya, yanajinta sai lumshe ido yake yana shafa gadon Bayanta,



Cikin Dabara ta rabashi da Rigan jikinsa, sosai take Romacing nashi, har yashagala suka tsunduma wani Duniyan,




Har yafito daga Wanka tana kwance shame2 yanda yabarta, Kallo d'aya yamata ya nufi closet d'insa, Jallabiya ya zira mai guntun Hanu ya fesa turare, zama yayi a bakin Bed d'in yana kallonta, ya wurgomata tambayan dayasa cikinta yin k'ululu,

"Yaushe Meena ta dawo?
Arazane ta kalleshi, "Ba.. ba dawo... Shitttt!!! Ya d'ora ya tsansa kan bakinta "Amsan tambayana kawai zaki bani bani son wani Magana gayamin yaushe tadawo?
"Mhmm Jiya,
"Ok tana Gidantan danasani?
"Mnn Eh inaga agidan take, d'an Murmushi yayi yace "K'irata yanzu ki tambayeta tana gidan ko wani wajen tayi?

Bataga Alaman wasa a idonsa ba dan haka ta d'auko waya hanunta na b'ari tafara k'iran Numbern jawota yayi ya mannata jikinsa gami da sa wayan a hans free,

K'irjin Nafisa sai bugawa yakeyi da k'arfin Gaske, tana Addu'an Allah yasa kada Meena ta d'aga wayan,
"Hello k'awata muryan Meenan yakatsemata Addu'an da takeyi a zuciyanta, ta d'ago ido ta kalli Kb dashima ita yake kallo Fuska a murtuk'e ya zabgamata harara gami da mata alaman tayi abunda yasata, Murya a sakale, tace "Kina Gidane?
Meena ta amsa da "Eh yanzu shigowana naje Gidan Bok...... Da sauri Nafisa ta datse k'iran zuciyanta na Harbawa,


Kb yayi Murmushi gami da sakinta daga rik'on da yamata,


"Wai meya tsorataki hakane?
Cikin Muryan Kuka tace "Kb ina tsoron kada kasa a hukunta Meena akan laifinda batayiba, pleas nasan Meena tanasona bazata cutar da abunda nakesoba,

Kallonta kawai yakeyi yana latsa wayansa jim kad'an ya kara a kunnensa,
"Hello Yusuf yarinyannan Meena ta shiga Gidanta yanxu haka, Eh to ku hanzarta, Ok yafad'a Gami da kashe wayan.


Kallonta yayi sai juya kai takeyi "Haba Kb? Baka yarda danibane?
Ya firzar da huce yace
"Bincike shi zai bayyana komi ba yarda ko rashinsaba, tuhumanta akeyi da laifin ba wai anada yak'inibane idan bata da Hanu fine gaskiyanta zai k'waceta,
"Allah Kb ba itabace,
"Gud to fad'amin waye?
"Wlh bansaniba, anma har ga Allah ni nafi zargin wannan yarinya 'yark'auyennan itacefa ta karb'o cake d'in kasan halin ba k'auye bai iya samun wajeba,

Wani lrin Kallo da ya wurgamatane yasata saurin Had'iye maganantan ta sinna kanta k'asa, daga Bisani ta tashi zata fita yasa hanu ya karb'e wayanta batare da tasan dalilinsa nayin hakanba, yanan zaune a wajen cikin halin da yake tun farko wayansa ta d'auki Ruri nan akasanar masa da Meena ta shiga Hanu, ya tashi ya fito zaune yasami Nafisa ta Rafka tagumi tashin hankali kwance a fuskanta ya wurga mata wayanta gami da hayewa dining ba yanda baiyiba yaci wani sandararren jalof d'in shinkafa da tayi anma yakasa, haka ya mik'e ya fita da yunwan cikinsa,

Tana jin tashin Motansa ta k'ira wayan meena har sau biyu ba ad'agaba, ta k'ira Mamanta Ringin d'aya ta d'auka tana fad'in yauwa 'yar Albaraka kinyi yandda na fad'amiki?
Nafisa ta Rushe da kuka tace "Asirinki zai tonu Mama yau Kb yazo yaga Meena har yasanar da Ss cewa tana gidanta suje, nikam na shiga Uku wlh nasan kb yana gane cewa kekikasa masa guba zai sakeni wlh Mama inason sa kaman Raina yau ya zanyi? Bazan iya Rayuwa bashi ba, Tafad'a cikin tsananin Kuka,

Duk da Maman ta tsorata dajin maganan sai ta dake har da dariyanta na k'arfin Hali,

"kar kid'aga Hankalinki Nafisa, Boka na da rai bai mutuba, yanzu haka wani Maganin yabani zan aikomiki dashi ki binne a bakin gate sai yanda kikayi dashi sannan wannan yarinyan bazata sake dawowaba har abada, ta tafi kenan,

D'an sauk'e ajiyan zuciya Nafisa tayi dan ba k'aramin farin ciki takeyiba idan ta tuno cewa Asirinsu yakama Dijah Kb da Mami sukoreta agidan kuma basa ko Magananta sannan Boka yace musu yama manta da ita kwata2 ko yaganta bazai iya tunataba,


Maman tace "kina jina? Lami k'awata kuma ta samomin wani boka a can hanyan jos tacemin aikinsa kankat ne dan haka zamuje komi zai warware kar kidamu, dan haka kigayama Kabir d'in zamuje Maiduguri bikin Asiya daga nan in munje wajen Bokan sai Mu wuce Maidugurin, Yafannah ta miki gyaran jiki ko zata mutu sai tayi dan nasan ta inda zan b'ullomata intasan wata batasan wataba, Burina Nafisa inganki cikin fari ciki, kin mallaki Kabir angama.

Nafisa ta sauk'e ajiyan zuciya, "Gaskiya Mama ni inaga mu hak'ura da Maganan Bokayennan haka, anyi2 anma ba Nasara kullum cikin kashe kud'i ake kiga d'akinkifa yanda yadawo wlh ni har kunyan k'awayena suje gaisheki nakeyi,


"shiyasa ai nasamo wannan Bokan dan in munmallaki Kabir kakarmu ta yanke sak'a mujuya dukiya yanda mukaso, kedai kawi kishirya,


Nafisa tace "To shikenan yanzu yaushe zamuje?
"Sai bikin ya gabato nan da Sati sai mu tafi tunda dama ai kowa yasan da Bikin,


Haka sukayi ta Hiransu yanda abun zai kasance musu daga bisani sukayi sallama suka ajiye wayan,


*********************

Tuk'i yakeyi cikin damuwa duk yanda yaso ya cire ma Ransa tunaninta ya kasa duk yanda yayi tsammanin zuciyansa ya illatu da Rashinta abun yafi haka, yayi jelen zuwa gidan Mami fir tak'i sauraransa, Har ya gaji ya mata maganan bata saurareshiba,


Ak'ofan Gidan Sani yayi perking ya fito gami da Rufe motan ya tura gate d'in ya shiga yadinga sallama abakin falonsu, Bintalo ce tazo ta bud'emasa tana masa sannu da zuwa wani sashin na zuciyanta na mamakin yanda ya canza kaman mara lfy,


"Sani fa? Ya tamabayeta yana latsa wayansa,
Ta d'anyi Murmishi gami da bashi hanya "Kashigomana Doctor yana wankane,


Kansa na jingine ajikin kujera yana tunanin ta yanda zai fara abinda yakawoshin, Bai kula da abubuwan da ta kawomasaba tunaninsa kawai yake tayi yaji andafashi a hankali ya d'ago ya suka had'a ldo, Sani yace " Oga lfy kuwa kwana biyu gaba d'aya bana ganemaka kaman ba Angoba,


Harara Kb ya masa sannan yace "Niba surutu nazo kaminba, Mnnhnn Numbern yarinyannan zankabani, Sani ya kalleshi yana gimtse dariyansa kaman bai fahimceshiba,

Yace "Yarinya? wace yarinyan kenan?

"Mtss nifa banson lskanci ai kasan yarinyan da nake fad'a sarai, Dalla can Malam kaban Numbern Khadijah,


Sani ya d'an dake "Ni bani da Numbern Khadijah,

"Malam kar karainamin wayo mana ta yaya za'ace baka da Numbernta?
Sani ya yatsina Fuska "To akan me zan ajiye Numbernta awayana? Kaida kake Mijintama baka da No. Sai nine zan ajiye no. ta,

Cikin tsoro Kabir yace "pls Abokina maganan Gaskiyafa Dan Allah inkanada ka taimaika kabni pls, yayi maganan cikin sanyi Murya da Rarrashi, wannan karon kam Sani bai iya b'oye dariyansaba saida ya d'an Dara yace "Dagaske bandashi,


Wani irin ajiyan Zuciya Kb ya sauk'e kaman k'irjinsa zai b'alle a kasale yace "Dan Allah ka tambayarmin Fatima nasan ita bazata Rasaba,
"Kai gaskiya zaiyi wuya dan nadad'e banji sunyi wayaba,

Kafeshi da ldo kawai Kb yayi kaman mutum mutumi ko k'iftawa bayayi, Sani yayi Murmushi, har ransa yaji tausayinsa sannan inya tuna waye Kb agareshi bai cancanci hanashi No. Matarsaba duk da Mami ta gargad'eshi, ya dafa kafad'an sa "Sory Abokina barinje intambayamaka idanma bata dashi promise zan nimomaka a yau d'innan, daga haka ya shige bed room, Kb ya mik'e da k'yar yana karad'e Hanya, ya fita ya shiga Motarsa, ya zauna gami da kifa kansa akan sitiyari yana xaman jira,


Bayan 'yan mintoti, Sani ya lek'o da kansa gami da Mik'a masa wata 'yar farar takarda da saurinsa ya amsa ji yayi kaman kyautan Gold ya bashi, Sani yace "Gaskiya oga ka fad'a Rijiya mai zurfi, jan motansa kawai yayi ba tare da ya kulashiba dan yana ganin yanzu komi xaiyi dai2 indai ya k'ira Khadijah zai tsarata ta gayamasa inda take yaje ya dawo da Abarsa, yau d'innan basai Gobe ba,


Da yaso sai ya isa Gida ya k'irata anma ina yakasa daurewa yayi hakan, dan haka yayi perking a gefen hanya ya saka Numbern a wayansa yayi dailing yana jin yashiga ya saki murmushi gami da Kwantar da Bayansa ajikin seat sai lumshe ido yakeyi, har wayan ta tsinke ba ad'agaba,

Fitowanta kenan daga Sashin lya Ita da K'anin Yafannah yana bata labari sai dariya take yi taji wayanta yana Ringing a karo na Biyu, da Sauran dariyan a bakinta tad'aga Wayan ta kara a kunneta tana fad'in Helo!

Wani irin mummunan fad'uwan gaba yaji sakamakon jin muryan namiji agefenta sannan yaji tana dariya, ji yayi duk illahirin jikinsa yasake,

Numfashi kawai yake fitarwa, Rass Dijah taji gabanta ya yanke, dan kaman taso ta gano wannan Numfashin, canza wajen tsayuwa tayi tana fad'in "Hello inbaza'ayi maganaba zan kashe ta fad'a a d'an zafafe,

Cikin wani irin Murya yace "Karkiyadda ki kashemin waya,

Cikin fad'uwan Gaba Dijah ta dafe jikin gini dan ji take kaman zata fad'i,
"Sai yanzu ka tuno dani sai yau kaji ka nimi layina? Tafad'a a zuciyanta,

Da k'yar ta daidaita kanta cikn kasallaliyan Murya tace "Waye kai da zakace kar inkashemaka waya? Pls waye? Ta maimaita irin bata ganennenanba,

Ya sassauta Murya "kina inane gayamin inda kike yanzu zan isoki sai kiga waye ni,
"Mhm Malam ina da miji taya zakazo inda nake,
Cikin kad'uwa yace "Kina da Miji? Waye Mijinnaki? Mijina gashi muna tare yanzu haka inajin Muryan masoyina yana jin nawa,

"Noooo!!!!!! Kabir ya fad'a cikin k'araji gami dayin wurgi da wayan, yadinga Huci da muzurai acikin Motan shi kad'ai yana sharce zufa,
Ganin haka bazai ficceshiba yasa yayi ma Motan key, yadinga sharara gudu har ya iso Gidan Mami, baiko gama perking ba ya finciki Murfin Motan ya bud'e yafita taku yake kaman zai b'urma k'asa ya shiga palour a kitchen ya tarar da ita, ya jawo Kujera ya zauna, dan bazaima iya tsayuwanba, a d'an tsorace Mamin ta kalleshi,

"Pls Mami Mu musulmaine a ina aka tab'a aure akan aure? Da aurena akanta Mami Meyasa aka mata Aure? Haba Mami mufa Musulmaine,

Cikin Rashin fahimta take kallonsa, "Banganeba Kabir???

Da sauri ya karb'e "Mami Dan Allah ki taimakeni karkimin haka kidawomin da Matata Wlh Khadijah matata ce, D'an Jim Mami tayi tana tunani kodai d'an nata yafara zaucewane,


Ya Dafe kansa yana maida Numfashi ganin tak'i sauraransa,


Ta dafa kafad'ansa tace "Har yanzu baka fahimtar daniba, Waima to me xakayi da Khadijah bayan gaka tare da Matarka Kabir banson niman fitinafa kwanan nan kanason d'agamin Hankali kodai kagaji danine, ta k'arashe cikin d'an d'aga Murya,

"Mami wlh lnasonta kiyi hak'uri wlh inason Khadijah Mamina ki taimaka tacemin wai tana da Miji, dagaskene? Ya tambaya yana langab'ar da kai Sosai yaba Mamin tausayi anma ta share ta maida Kanta ga Girkinta, tace "To ance maka baka sonta kowa ma bai sontane,

Zaro ldo yayi "Kenan da gaske anmata auren? Tsoron yanayin da ya nuna yasa Mami tace,

"mhhhmm aina katab'a jin anyi hakan ai sai ka ware igiyan aurenka akanta kafin Asamu daman mata aure so nake sai sungama dai2 tawa da Mijin nata kafin insaka bani takardanta,

Wani irin ajiyan zuciya mai k'arfi Kabir ya sauk'e ya sadda kansa k'asa na d'an lokaci kafin ya d'ago ya kalleta,

"Kiyi hak'uri Mami kibarni da Matata dakika auramin wlh ina sonta Kinji Mamina,
D'an had'e rai Mami tayi "Yau Kabir agabana kake cewa kana son wata yaushe Soyayyar ka ya canza akala Daga na tsakaninka da ni ya koma kan wata ka manta cewa Zuciyarka ta soyayyan Mahaifiyarkace kawai?

"Kiyi hak'uri Mami da Gaske nake inasonta,

"Mmmh, kawai mai tace taci gaba da aikinta, bata k'ara bi ta kansaba, taci gaba da aikinta tana jin yanda yake ta ajiyan Zuciya,

Har ta kammala taje tayi wanka Kabir yana inda tabarshi ba abunda yake tunawa sai kalman da Khadijah tagaya mishi "Yanzu haka ina tare da Masoyina ina jin Muryansa yana jin nawa,

Tabbas yaji Muryan wani kusa da ita sannan da farko yajita cikin farin ciki da alama bata da wata damuwa, to waima a ina take? Yadai san ba cikin garinnan takeba, dan duk inda yasan zata je yaje,


"Ka taso kaci Abinci Kabir ka wuce Gidanka dare nayi, a kasale ya taso yafito palour ya zauna ak'asa ba yanda ba tayiba ya k'i cin komi duk da azaban yinwan da yake ji,

Magana d'aya yake maimai tamata Tabashi Khadijahnsa, ita kuma fir tak'i yarda suyi Maganan, ganin dare nayi kuma yak'i ya tafi yasa tace "to wai yanzu ya kakeson inyi?

Ya langab'ar da kai "Just Mami ki gayamin inda take kawai abunda nakeson ji kenan naje Garinsu bata can Dan Allah ki gayamin inda take plss,


Zuba masa ido tayi da alama yayi Nisa, "yanzu ka tashi ka tafi dare yayi Gobe in Allah ya kaimu za muyi maganan, zai kuma magana ta d'aga masa hanu,

"Kaga inka matsa xamu b'ata kaje Gobe sai muyi maganan,

Ba yanda

1 Comments On DIJAH QAYA
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

Please Login or Register in order to submit comment