Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motar Har sai da ta tsorata, Kuma Har yanxu Bata daina wayar ba ta Dade tana wayar Shi kuma driving Kawai yake, Bayan ta Gama wayar sai taga ransa a b'ace.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Hubbyna ya Naga kamar ranka a b'ace"? "Dawa kike waya"? Rai a b'ace don ko kallonta baiyi ba, tace "da Mahir" "waye Shi"? "Dan ajin mu ne" "mtswww matsala ta da Yanmata Yan Boko knn Duk Wanda ka tmby sai tace mka class mate ko Kuma course mate" dariya tayi sosai Sannan tace "Hubbyna da tafiya zakayi ka Barni ko"? Hmmm Kawai yace "Hubby Yau a Karo Na farko Na bude motar da kai Na" "Toh ba ke bace, ai kece Sila" "Naji am sorry" "Babyna ba Kya laifi fa" "Gashi kuwa Nayi" yayi dariya Sannan ya Ce "Bari Na sayi Magani a chemist din nan" sai yayi parking ya fita Har ya Yi Nisa sai ya dawo ya cire key din Sannan ya kulleta a Ciki..
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Ita kam Dai kallon Ikon Allah take, Bayan ya dawo ne sai yace " baki tmbyi dalilin da yasa Na dawo Na kashe motar ba"? "Eh Amma meyasa"? "Baki Ga Wani mutumi a tsaye kusa da motar ba"? "Eh Na ganshi Yana ta kallon motar" "Gud to wlh hankali Na ne bai kwanta dashi ba" "hmmm kai Dai wlh ka cika tsoro dayawa haba, sai m
Kace ba Na Miji ba"?
"Hmmm yarinya baza ki gane bane"
"Toh Kaka Sanar Dani mana" "Lallai Kalfana wato kin Raina Ni ko Kar ki damu akwai ranar da xan Sa bakin nan ya rufu" "hhhhh kamarya knn" "saurin me kike with time Zaki sani, kina jina"? "Eh" "Ina fad'a Miki an tab'a kidnapping d'ina, 3 days suka ajeni a Wani d'aki" Kalfana zaro Ido tayi tace "Amma Wasa kake koh"? "Hba Babyna Muna irin wannan Wasan da ke ne"?
"A'a ba muyi Amma Garin Yaya suka kama ka"? "A hanyar Taraba zamuje saro Kaya suka mana fashi sun kyale Sauran Amma Ni suka tafi dani, sunyi demanding 5mil in ba hka ba zasu kashe Ni" "innalillahi Allah ya tsare Na gaba" "Amiin shysa ai ma tsorata da mutumin nan, hka Kawai ya sace Min ke ya Je ya cutar Min da ke ai Gara ya sace motar" murmushi Kawai tayi Suna hirar su irin Na masoya Har suka Isa gida.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Suna Isa ya Ce "Babyna Ina so muyi wata magana da ke Mai muhimmanci" "Toh Ina sauraron ka" sai yayi shiru Yana Nazari "Anya in Na fad'a Mata baxa ta guje Ni ba, kaaiii Ina Bana so Na rasata, Zan Bari Na fad'a Mata a gaba" itace ta katse Masa tunani, "hubby Kayi shiru" "Babyna nifa hankali Na Bai kwanta da Zaman ki a Gidan nan ba, Nayi Wani mummunan mafarki dake, Dan Allah ki bar Gidan nan, tayi shiru Na d'an wasu lokaci Sannan tace "Hubby wlh Zaman dole nake a Gidan nan Ni Kaina bana so" "Toh me kike Jira" "Aji 2, in Na Shiga Aji 2 Zan bar Gidan" "look Babyna Ina kaunar ki sosai in Dai matsalar kud'in da kika Biya ne xan biyaki Sannan mu nema Miki Wani,Wanda Zaki Zauna ke kad'ai" "Ni kad'ai Kuma so kake axo a kashe Ni ko, sai Dai kazo ka Samu gawata" tsawa ya Mata "ke in ana Magana sai ki d'auko maganar mutuwa" "Amma hubby mutu........" Ya d'aga Mata hannu malama ya Isa hka, mutanen Gidan ba su sonki, Amma ke bakya gan, ban so Na Shiga maganar nan ba Amma tunda ya shafe ki ya shafe ni, Babyna a ranar da mukaje restaurant da ke da Azeemah, baki lura ta Miko Min wayar ta nasa Mata numb Na, Amma ban karb'a ba" gyara Zama Kalfana tayi tana kallon sa cikin mamaki, "Dan Allah dagaske kake"? "Eh dagaske nake" "hmmmm biri yayi kama da mutum, ba abun mamaki bane Zeemah zatayi fiye da haka" "babyna Na lura ke Mai biyayya Ce Ga maganar iyayen ki, shysa kike Zama a Gidan nan ko? "Eh hakane" "Toh ki fad'a wa daddy kinji Suna planning Na kashe ki" zaro Ido tayi Sannan ta Fara dariya "kashe Ni Kuma Hubby haba mana".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Yarinya ke Har yanxu yarinya Ce ana fad'a Miki yanda zakiyi Abu Amma kin ki"
"Toh kaka Na sharrin kisa fa kake so Nayi"
Rankwashin ta yayi ta Sa Kara tana dirza gun Kuka ta Fara Yi, ya Ce in kika sake Min kaka sai Na cije ki" Yana maganar Yana dariya, cikin muryar shagwab'a tace "Toh nima ka Daina ce Min yarinya" "ban Girme ki bane"? "Toh in ka girmeni ka haife Ni ne"? "Hmmm Lallai ma yarinyar Na" Ji yayi Duuuuum ta kai Masa dundu a Baya, yace "la la la la, Malama so kike ki karyani"?
"Oho Kaji in da Dadi" tana markwad'a bakin ta, "Ni kike murd'awa baki"? "Eh din Nayi" "Allah in kika sake sai Na ciza bakin" Kawai Gani yayi ta sake, Bude baki yayi Yana kallon ta Yana Jin kaunar ta Na Kara Shiga ransa, "hmmm Kar ki damu yanxu lokacin ki ne" ganin an dawo da wutan Nepa ne yasa tace Masa zata SA wayarta a chaji, sai ta Shiga cikin Gida don tasa chaji, tana Shiga muryar su Zeemah da Kannenta take Ji a parlour kai tsaye d'akinta ta nufa, tana Shiga taga abun mamaki.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Madara,bornvita, da sugar dinta taga an juye an bar Mata su empty turarikanta Kuma an tsiyaye, wuri ta Samu ta Zauna ta dafe Kanta, sai hawaye wiwiwiwi, "Ya Allah wannan Wani irin jarabawa ce, Daddy meyasa baza ka Bari Na bar Gidan nan ba"? Sai da tayi Kuka Mai isarta Sannan ta Tashi ta Shiga ban d'aki ta wanko fuskarta Sannan ta fita wurin Hubbyn ta, jiki Na kwari.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana Shiga ta Zauna , ya kunna fitalar cikin motar Sa don yaji muryar ta, ya canxa yaga idonta sun Yi jajir, hankali a tashe yace " Babyna me aka Miki kike Kuka"? Bata Ce Masa komai ba sai Kara fashe wa da kukar tayi, ko kad'an Baya son bacin Ranta bare ace har Kuka , Bai San Sanda ya rungumota jikin Sa ba sai rarrashinta yake Yana bubbuga bayarta a hankali, "Babyna kukan Na Mene ne haka, plz ya Isa" Amma bata sauraron Sa, Kara manneta yayi a jikinsa, a zuciyar cewa yake "kiyi Kuka Mai Isan ki kila ki Daina Jin zafin abun"..
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Ta Dade tana kukan Shi Kuma Bai Daina rarrashinta ba Shima Ji yake Kamar ya Fara kukan, yace "Babyna Dan Allah kukan nan ya Isa Haka in ba so kike Nima Nayi ba", Har yanxu Dai Bata daina ba, yace "Bari kiga Na kama baki Mai kukan nan Na tsotsa" saurin Tashi tayi taga jikin sa tana share hawayen fuskarta , ya riko hannun ta "Babyna Bana son tashin hankalin ki plz fad'a Min me aka Miki"? Sai hawaye Kawai ba Magana, fuskanta ya d'ago ya zaro harshen Sa ya lashe hawayen Dake fuskarta tass Sannan yace "Insha Allah Babyna Bazan Bari ki mana asarar hawayan ki ba in Dai Ina tare da ke" ganin ta Daina kukan yasa ya janye jikinsa ya shafa Kanta , Sannan yace "Kar ki boye Min komai nasan kukan nan bazai wuce matsalar Yan Gidan Ku ba ne, ki fad'a Min Duk abubuwan da suke Miki" ajiyar zuciya tayi Duk muryar ta ya dashe Sannan ta Ce "Hubby ban tab'a fad'awa Kowa Damuwa ta ba sai Momy ita din ma ba komai nake fad'a Mata ba, Sabi da Kar hankalin ta ya Tashi tana da hawan jini, dadyna Kuma ba yadda zaiyi ba, Hubby Ina cikin tashin hankalin Wanda ba Lallai bane Na iya fad'a Maka suba" "Toh Naji yanxun nan fa kika fita cikin fara'a Amma kika dawo kina Kuka" "eh sun Dade Suna Min d'auke d'auke , yanzun ma haka ne" "hmm ke Kuma Dake hawaye sun Miki yawa ko, ki shirya gobe muje shopping Kuma wannan umarni ne ba shawara ba kinji Na Gaya Miki" murmushi Kawai tayi tace "Allah ya kai mu , sun dad'e Suna Hira Sannan yace Zai tafi sin rabu Duk Suna cikin kewar juna musamman Alhj Maan da tun da ya rungumeta yaji Wani masifaffiyar sha'awa ta Tashi Masa Yana Isa gida lemon tsami ya matse yasha, Alhj Maan mutum ne Mai bukata sosai shysa Baya kallon film, a haka ya kwana cikin kewar ta, ita ma hka.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Washe Gari*
Kasance war weekend ne Duk Suna gida, dady Mahaifin su a Azeemah ya musu shigowar ba zata, Bayan sun Masa sannu da zuwa sai yace Azeemah da Kalfana su shigo d'akin sa, Bayan sun Shiga ya ce "Mujeedat ya karatu da fatan ana Maida hankali"? "Eh dady Alhamdulillah" "Mujeedat ki fad'a Min gaskiya tsakanin ki da Allah ya rayuwar Azeemah take"? Zeemah ta tsorata da tmbyr dady don batayi tunannin hakn ba sai kallon Kalfana take Taji me zata Ce, "Dady am sorry ban fahimce ka ba" Wayan Sa ya zaro ya miko wa Kalfana Ga mamakinta Hoton Zeemah ne da Alhj Tanko, yace "kin San Shi"? "Eh dady Na San Shi" Zeemah a Ranta cewa take "innalillahi wa'inna ilaihirra ji'un, Kalfana Dan Allah ki rufa Min Asiri Kamar yadda Allah ya rufa Miki Asiri.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️


Team Kalfana

Shin Kuna Ganin Kalfana zata fad'awa Dady gsky???

Mu hadu a next page don Jin yadda zata kasance


*Daga Alkalamin Fadeelah Yakubu Milhaat*

Plz Share and comment✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 4️⃣6️⃣↔️4️⃣9️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana tace "Eh Dady Na San Shi" a nitse, yace "Good Feed me more" "Daddy sunan sa Alhj Tanko" cikin Zeemah sai kuuuuuuuu yake "uhmn ina sauraron ki".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Akwai Wani connect da mukeyi Na matasan Gombe, Sunan kungiyar GAYF, (Gombe Arewa Youth Forum connect), to shine HOD, Azeemah Ce PA dinsan sa" "Toh Amma meyasa babu Wanda ya fad'a Min maganar nan" "Dady last week Muka Fara Kuma Duk Mun shafa'a ne kayi hakuri" "Toh Mujeedat bakomai Allah ya Bada sa'a, ke kuma Azeemah ki Daina d'aura hotunan ki a social media kina jina ko"? "Eh Dady Insha Allah Bazan sake ba" "Zaku Iya tafiya" Mujeedat Ce ta Fara fita, tana fita Dakin ta ta Shiga.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zeemah ta bi Bayan ta, jiki a Sanyaye ta Zauna , Kalfana kallon ta Kawai take, Zeemah tace "Kalfana emm......emm...emm Nace ba"? "Uhmn Ina Ji lafiya kuwa kike Magana haka"? "Kalfana gsky ke Yar Halak ce ban tab'a tunanin ko a mafarki Zaki rufa Min Asiri ba, nagode sosai Allah ya saka da Alhairi" "Azeemah knn ko kad'an banyi Hakan don tausayin ki ko Wani Abu ba nayi Hakan ne Sabi da addini Na,addina ya Koya Min yanda zaka rufa wa Dan uwanka musulmi Asiri,in ka rufa wa Wani Asiri kai ma Allah Zai rufa Maka, ba wa ke ba ko wane ne da ya Shiga irin wannan halin xan taimaka Masa" Azeemah Tashi tayi tana nuna Kalfana da Yar yatsa "mtwwww ke Kalfana Kar ki Ga Na shigo d'akin ki, ki d'auka xan janye kudirana Akan ki, Toh wlh yanxu muka Fara" Kalfana Tashi tayi ta tsaya tace " Toh Zeemah kina Ganin Ina so ki janye ne, shysa fa ban tona Miki Asiri ba" tunda Kalfana ta Fara Magana Zeemah mamaki take Wai Ashe Dama yarinyar nan ta Na magana, Ina Mata kallon wawiya, chaaapdi, " Toh me Zaki iya min" Kalfana dariya take sosai Har da tafi Sannan ta dauko wayar ta, ta kunna Mata Video din ta Mika Mata wayar "ko kin San wace ce wannan" Azeemah ta tsorata sosai ta fizgi wayar Daga hannun Kalfana, Kalfana dariya take tana Kara tafi Mai sauti, "Azeemah Kar kiyi tunanin goge wa ko da kin Yi kokarin Hakan bazaiyuba sabida a email yake, Sannan nayi saving a memory daban da ban gudu 3" tana nuna Mata yatsanta 3, ta sake fashe wa da dariya sai ta fizgi wayar ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Kince me Zan Iya Yi ko? , Toh barin fad'a Miki abin da zan iya kinga video nan watsa wa zanyi a Social media Shi wannan Dan iskan Khamal din ki fada Masa ya shirya don Na tabba Zai Rasa aikin sa.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Typing yayi kad'an ko☺️?

Iya yawan comments din da Na Samu Iya typing din da zanyi


Mu hadu a page Na gaba.

*Daga Alkalamin Fadeelah Yakubu (Milhaat)

*


💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 5️⃣0️⃣↔️5️⃣3️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Wannan page din sadaukarwa ne ga dukkan *_MANAZARTA WRITTERS_*

@⁨Binta NOVEL⁩
@⁨Fareedah MWA⁩
@⁨Nana MWA⁩
@⁨Rufaida MWA⁩
@⁨Ummuhaneefa⁩
@⁨Smarty 🥰🥰💝⁩
@⁨Maman Teddy🧸⁩
@⁨Mom Affan⁩
@⁨maman teemah✨🥰❤️🔐⁩
@⁨Jameela⁩
@⁨Soomeey⁩
@⁨Yar'mutan kankia ce✍️⁩
@⁨10k Returns✍🏻⁩
@⁨Typing.........✍🏻💅🏻⁩
@⁨Hijjiyyah💞💞⁩

```Love you All Allah ya bar kauna ya Kuma cigaba da had'a kawunan mu Ameeeen``` 🤲 🤲
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Ke Har kin Isa kisa a Kori Kamal, wlh Mujeedat Kinyi kad'an Yar iska Kawai" "hhhhhhh Ni ce Yar iska , Toh Sannu Yar guguwa karuwar banxa Shasha wacce Bata San ciwon Kanta ba" "Kutuman bura uba, Ni kike fadawa karuwa"? "An fad'a Miki Karya ne ba karuwar bace ke, karuwar Gida" hannun ta d'aga zata Mari Kalfana, sauri ta Yi ta rike hannun ta Sannan ta shafa Mata Mari guda 2 masu kyau Sannan tace "wlh Azeemah Kinyi kad'an kisa hannun ki a jikina da sunan Duka" "Kalfana Ni kika mara don ubanki" "ke Kar ki sake Sa mahaifana a cikin maganar ki, ko da yake ba a San darajar Na Gida bane" tana Mata kallon Sama da kasa.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Ke fice Min Daga d'aki" "Zan fita Kalfana Amma wlh wlh sai kin San kin mare Ni" "Eh Dai a fita" Azeemah ta fice fuuuuuu Har tuntube take tana fita Zeemah ta Shiga wanka tayi alwala tayi sallah Bayan ta idar da sallan ta kwanta knn sai ga Kiran Alhj Maan.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Ganin sunan sa a fuskar wayar ta taji Duk bakin cikin da take Ciki babu ita, tana picking yace "Gani hope kin shirya"? Cikin rashin fahimta tace "Shirya Kuma zuwa Ina" yayi Shiru bai ce komai ba, "hloo kana Jina kuwa"? "Burinki shine kiga kin b'ata Min raii koh"? "Haba Hubbyna Duk Duniya babu Wanda ya kaini son ganin farin cikin ka" "Toh in hakan ne da gaske meyasa kika Manta Yau zamu Je shopping"? "Wayyo am very very sorry ban Manta ba Na shafa'a ne My, Gani nan zuwa" ta katse wayar a gurguje ta Tashi ta dauko Wani atamfa Jaa da Yellow anyi Masa dinkin Borno style Riga da zani, Tasha daurinta irin Na Aisha Buhari, ta yafa bakin gyalle da Bakar Takalmi, powder Kawai ta shafa ta dauki eye glass baki tasa, da Bakar jaka,tayi mutukar kyau, ta feshe jikinta da tirare ita Kanta ta san ta had'u.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana fita Dama ya fito Yana tsaye a jikin motar, Kallon ta yake tana tafiya Mai d'aukar hankali Har sai da ya Bude baki Yana kallonta ta lura da Hakan sai da ta matso kusa dashi tace "yallabai mu tafi ko"?
Amma Ina Baya jin ta sai da ta Yi tafi ya a razane yace "Na...na.... Na'am" Kalfana Dai dariya take Har da rike Ciki, yace "Toh ya Isa hka Shiga Ciki" ya Bude Mata ta Shiga, Suna Hira Suna tafiya nan sukaje sukayi shopping Na Duk abubwan da suke so sun share kusan awa 3.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Suna Isa Gida yayi Parking a kofar Gida, sai hirar su suke cikin farin Ciki da kaunar juna, sai take Ce Masa tana son zuwa Mal Inna, ta gaida baffan ta Bai da lafiya, yace "ki aje kayan nan sai Muje Na kai ki Karo Na farko Zan had'u da dangin ki" tayi murmushi "Haka ne Kam Bari Nazo" tana Shiga ta aje kayan Bata b'ata lokaci ba ta Nufi hanyar fita kwasam sai ta sinkayi muryar Azeemah Na Fadin "wayyo wayyo wayyo Zan mutu" tsaki ta jaaa Sai wata zuciya tace Mata "Haba Kalfana mugunta ba halinki bane ba, mutuwa fa tace" wata zuciyar tace "Toh Kalfana in mutuwarce Ina ruwanki"? Girgiza kai tayi sanan ta Shiga parlour,tana Shiga taga Azeemah a kwance a kasa ta rike cikin ta sai juye juye take bakin ta Duk kunfa, hancinta jini, Bata hayyacinta, da gudu ta karasa inda take "Zeemah!!! Zeemah" plz talk to me" Amma ba magma sai Kallon ta take plz Azeemah kimin Magana" sai tace "kal...Kal...kalfa...Na Bashir ne" cikin rashin fahimta tace "Bashir me ya Miki"?
Na kai Mata ziyara ne, sai muka Samu sab'ani Ashe abincin da ya Bani yasa poison a ciki,Bayan Na Gama cine ya Sanar Dani" "innalillahi wa'inna ilaihirra ji'un Zeemah shine kika dawo Gida baki Je asibiti ba"? Amma alokacin jikin ta ya Fara kakkarwa, da saurin Kalfana ta Koma d'akinta ta dauko gongomin madarar da suka sayo, da gallon din manja ta Fara durawa Zeemah a baki tasa Mata Madara tasa man Jaa a tsorace don hannunta rawa yake Yi, nan take Zeemah ta Fara Amai Kalfana murmushi tayi tana share hawayen da ita Kanta Bata San yaushe suka zubo Mata ba, da sauri ta fita ba ko mayafi a jikin ta,ta Nufi inda Alhj Maan yake,tana Kuka ganinta a haka yayi bala'in tada Masa hankali ya kudiri niyya indai Zeemah Ce tasa Matar Sa Kuka wlh wannan Karon bazai Barta ba tunda Yana da karfin da Zai Sa a d'aure Duk Yan Gidan su.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana sai Kiran sunan Azeemah take yace "me ya Sami Azeemah" "Dan Allah kazo ta taimake Ni" ta Koma Ciki da gudu a nan ne ya lura babu Takalmi a kafanta, yace "innalillahi wa'inna ilaihirra ji'un Wai me ke faruwane Amma Bari Na Gani" bin bayanta yayi da sauri muryar kukanta ne yasa ya Gane inda take Yana Shiga yaga Halin da Zeemah take Ciki ya ya tsorata don Har Ga Allah ya d'auka ta mutu ne, sai Daga Baya ya lura Ashe tana numfashi, Kalfana tace "Hubby mukaita asibiti Dan Allah ka taimake Ni Kar ta mutu" cikin Kuka Mai sauti ,karasowa yayi yace d'aga ta mu tafi, Kallon Sa tayi tace "Bazan Iya ba" murmushi yayi ya d'ago ta Chak Kamar jaririya ya fice Daga d'akin bin Bayan su take tana share hawaye,taga ya tsaya ita sai ta tsaya yace "Haba yanxu a haka Zaki fita Duba kanki fa ba ko dankwali bare Takalmi, sauri tayi ta dauko hijab dinta, tasa slippers Wanda ita Kanta Bata San Na wane ne ba, Kuma daban daban, tana Isa ta Bude Gidan Baya ya Sa Azeemah ita ma ta Shiga ta Zauna da Azeemah tasa Kan Azeemah acinyarta sai Sannu take ta mata, Shi ko Maan mamaki yake "Wani irin zuciya Kalfana take dashi Wai ace Duk irin abubuwan da suke Mata shine Harda Kuka, wlh inda nice ko Kallo Basu isheni ba Mtsww" Suna Isa aka fito da Keke irin Na daukan marasa lafiya, d'akin taimakon gaggawa aka kai ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana sai safa da Marwa take, Maan Yana zaune Yana kallonta Har ta Fara Bata Masa raaai, yace "Dan Allah Malama ya Isa Haka ki Samu wuri ki Zauna" kallon Sa ta sayi Yi da idonta, Kamar Mai Jin bacci, Babin Kuka ta sake budewa, da sauri ya karasa inda take ya riko ta don su Zauna mutanen gun sai kallon su suke, rungumota yayi a jikin sa Yana rarrashinta, wata tsuhu Ce Tace " 'yata addu'a Zaki Mata ki daina Kuka kinji"? Kai Kawai ta d'aga Mata, "Allah ya Muku albarka ya Baku zuri'a dayyiba" suka Amsa da "Ameen" Magana ya Fara Mata a kunne yace, "Babyna kallon Mata da Miji fa suke mana" anan ne ta tuna tana kwance a jikinsa, Tashi tayi da sauri tana kame kame Kamar mara gsky murmushi Kawai yy.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Babyna Dan Allah kukan me kikeyi"? "My Zeemah bata tsoron Allah ta kasance a ko da yaushe tana Sabon Allah in ta mutu a hka fa"? ta sake fashe wa da kuka, "Babyna knn hmmmm Toh Allah yasa mu cika da Imani" "Ameen" sun fi awa d'aya Kan Dr Abdulaziz ya fito, ya Nufi inda su Kalfana suke Bayan sun gaisa yace su bishi office, Dr Abdulaziz yace "Alhamdulillah Allah ya bamu Ikon ceton Ranta kuje Ku Biya kud'in Aiki" Maan yace "Toh Dr Mun gode Sosai" "Amma Wani hanzari ba gudu ba ya akayi Tasha guba"? Kalfana ta ce "Sa Mata akayi a abinci" mikewa yayi yace "whaaaat Kisan kai fa knn"? Amma kun San Wanda yasa"? "Eh Na sani" Maan ya juyo ya kalleta "Babyna kin San me kike cewa kuwa"? "Eh Na sani" "Babyna Daga nan police station zamuyi" Rai a b'ace "My mu Bari ta farfado muji hukunci ta, Dr zamu Iya ganinta"? "Eh Bismillah muje Na raka Ku", Duk su 3 suka fita.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Suna Shiga sun Samu ta farka, tana Ganin Kalfana ta fashe da Kuka, da sauri Kalfana ta iso inda take, "Zeemah stop crying insha Allah you are safe okay"? Tana maganar tana share Mata hawaye, Zeemah tace "Kalfana ba kukan da nake ba Kenan Na cuci kai Na Na zub da mutuncina,Hakan Bai isheni ba naso Na d'aura ki Akan......" Da sauri Kalfana ta rufe Mata baki tana Mata Magana da Ido tayi Shiru Bai dace tayi Magana a gaban su ba, Bayan ta d'aga hannun ta sai zeemah ta cigaba da cewa " plxxxx Kalfana forgive me ki yafe Min kin Ceci rayuwa ta da Na Zama gawa" " look u r like a sister to me Zeemah, do u think Zan barki a wurin ki mutu ne never" sai suka rungumi juna Suna Kuka, Dr Abdulaziz ne ya katse su yace " Masha Allah da irin wannan kawancen kun burgeni gsky, Allah ya bar Ku tare Duk suka Amsa da Ameen Amma Banda Maan don Shi wlh ya tsani Zeemah din nan, yace "Dr Bari Na Je na Biya kud'in " tare suka fita, Bayan ya Biya kud'in 150k fitowar Sa knn suka had'u da Dr Abdulaziz Zai Je masalci sai suka had'a hanya suka fita.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bangaren su Kalfana tmbyr ta take meyasa ya ganta ita kad'ai a Gidan Ina su Dady da su Afra"? " Daddy ya Koma, ya Bani 100k Wai mu raba Dake, su Afra Kuma Suna islamiyya" "Ayya Dady Baya gajiya Bari nayi alwala Maghrib tayi, ban d'aki ta Shiga tayi alwala ta Fara sallah sai ga shigowar Maan da Dr da take away Na abinci, hira suke Sosai Kamar Dama sun San juna,Bayan ta idar ne ta cewa Maan ya kaita gida don ta Sanar da da su Afra " Nasan hankalin su a tashe yake" yace "okay muje ko"? "Amma Hubby Zeemah ita kad'ai" Kan Maan ya Amsa Dr yace "Kar ki damu Zan Kula Miki da ita" murmushi tayi "Nagode Dr" "Zeemah me Za a kawo Miki"? "A'a bakomai " "okay sai mun dawo".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Dr Abdulaziz labarai Na dariya yake ta bawa Zeemah ita ki dariya take Sosai, a ransa yace "Ya Allah tausayin ta nk Ji ne ko kaunar"???
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Fans Anya Dr Abdulaziz Baya Ruwa, Ruwan ma kusa da kada kuwa🤣😂 Ni Dai Ina kusa da Hamisu breaker😎😎


Mu had'u a Next Page

Ummu Haneefah
Sis Fareeda Yau nayi typing dayawa ko🥰🥰

*Daga Alkalamin Fadeelah* *(Milhaat*)

Plz comments and share👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS

Please Login or Register in order to submit comment