Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasha Naji sauki"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Allah ya Kara sauki" "Amin ngd"
Nan suka Fara Hira Har ta Manta da Duk wata Damuwa sun Dade Suna Hira don sunfi awa d'aya Chan sai taga Yana kokarin matso kusa da ita ya rike hannun ta , tayi sauri ta zare, ya Kuma rike hannun ta Yana kokarin ya rungume tayi sauri ta ture Shi tana zub da hawaye Mai zafi ta fice Daga motar ya bi bayanta " Babyna plz am sorry, ya Na kokarin riko hanun ta ta wanke Shi da Mari taaaas ta ce Kar ka kuskura Kar ka sake ta Nuna Shi da Yar yatsa yaji zafin Marin Sosai Amma burinsa ta hkra Dai Kawai Kan ya hankara ta Bude kofar gidan ya karaso da sauri Zai sa kaai Jin Wani Kara nayi Gaaaaau, goshin sa ta buge da kofar irin Kofa Na karfe ne yaji zafin Sosai ya rike wuri yaga ko ya fitar Jini ya Ga babu Amma ya kumbura tiiiim, sai ya Koma ya Shiga Mota ya bar unguwar.....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu hadu a page Na gaba

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu* *(Milhaat*)

https://chat.whatsapp.com/KRSQBsr9JJw6Qe8AzUT9lP


Plz comments and share 🙏🏻🙏🏻 🙏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 2️⃣1️⃣↔️2️⃣2️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Yana barin unguwar su Kalfana Bai zarce ko Ina ba sai Gidan su Adamz , Adamz shine babban abokin Alhj Maan, Yana zuwa gate din yayi horn Mai Gadi ya zo ya Bude Masa Yana Shiga yayi parking din motar sa kai tsaye ya shiga cikin Gidan , parlour ya Shiga ya tarar da Hajiye a zaune ya durkusa ya gaida ta ta amsa ba yabo ba fallasa, "Hajiye Adamz fa" " Yana Dakin sa" yace "Toh Bari Na Shiga" Har Fara tafiya tace "Suleiman zo nan" tana Masa Wani irin Kallo so take ta ga abin da take Gani a fuskan sa hkn ne ko a a
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Na'am Hajiye" "kai ko d'an nan me ya same ka, ya Na ga ga goshin ka ya kumbura" nan ya Fara Sosa kai "Ina Magana kayi Shiru" "Hajiye dazu ne Na fito wanka sai Na buge " "Oh Suleiman Har yanxu Baka San ka girma ba" sai ya murmushi ya Tashi ya tafi, Hajiye mamaki take " Hmm lallai yaran nan mutumin da yk da yara Har 2 Amma sai Shiririta, Allah ya shirya mana Ku" sai ta cigaba da Har Kar gabanta...
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Yana Shiga ya tarar da Adamz Har ya Fara bacci, ya yaye bargon da rufe jikin Sa dashi ko Zai Tashi Amma Ina yayi Nisa sai da ya kai Masa bugu ya Sa ihu ya Zauna yace" Wayyo Ku kuke Ganin mu ba mu muke Ganin Ku ba"
Maan ya Fara dariya Har da rike Ciki sai da yy me isar sa Sannan ya Zauna a Kan kujera, yace "kai Wani irin matsoraci ne hka, baza ka Kira sunan Allah ba ka Fara Yi Wa mutane ihu, hba sai kace ba Na Miji ba"?
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Adamz da tun da ya farka yake ta share zufar da ta keto Masa ba shiri yk sai da ya gama yace " Maan Amma kai d'an mugun rainin hankali ne wannan ai mugunta ne, kasan Wani irin mugun mafarki nk Sannan Ga uban Duka da ka kai Min mtwwww"
"Yi hkri abokina Ni Dai yanzu ba wannan ba shawara Nazo ka Bani" adamz ya gyara Zama yace " me Kuma ya faru, wait Yana ga Kamar goshin ka a kumbura"?
"Maganar da ya kawo Ni gurin ka knn" "mtss to Ni me Zan maka? Likita ne Ni"? " Kaga matsala ta da kai knn Baka more zance"? "Toh Ina sauraron ka" nan ya kwashe komai ya fada Masa tun Daga had'uwar sa da Kalfana Har da yanda goshin sa ya kumbura" nan fa Adamz ya Fara dariya Har sai da ya ga ran Maan ya soma 'baci yace " Ai ta Min Dai Dai Ina ma ace har da bakin ta buga , kaga dama bakin yayi kankanta dayawa" ya karasa Maganar cikin dariya" Maan ya Mike Zai fita Rai a 'bace Adamz ya Yi saurin rike hannun sa "Mal Ina Kuma zaka, yhkri ka Zauna" ya Koma ya Zauna Baice komai ba Adamz yace "Maaan kayi kuskure babba yanzu kayi hkn don ka gwada ta gashi ta Nuna Maka cewar ita din ba hka take ba , ka samu amsar tmbyr ka , Amma ita Kuma a yanzu take da tambayoyi a Kan ka"
"Abokina Na sani wlh na San nayi kuskure Ina kaunar ta Sosai ,Ganin halin yarinyar da suke tare ne yasa nk zargin ta, kuma akwai inda Na tab'a Ganin Azeemah but gsky Na mance a Ina Na ganta" "in ko Hk ne Maybe ita Kafana ko kafarka ne sunan ta"? "Bana son iskan ci Malam sunan ta kaniyar ka" Adamz ya kyalkyale da dariya yace "wlh sunan nata da wahala tuno Min" "sunan ta Kalfana" yace "Awww to Kalfana yanxu kila ita din ma hkn ne first attempt kayi ai " yace eh Kuma hkn zaiyu, Amma fa tun 'dazu nk kiranta ta ki picking sai rejecting take" "sake kiranta muji" yayi dialling Amma Taki d'agawa hkn yasa ya sake shiga tashin hankali ya dafe kansa sai "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" yk ta fad'a Adamz shidai mamaki yk "My Man yaushe Kuka had'u da yarinyar nan da Har ka Dami kanka Har hk"?
"Shejaranjiya muka had'u a auren Auwal" "kaaai Hb Kar ka Raina Min hankali mana shejaranjiya shine kk santa Har hk"? Yace "wallahi gsky nk fad'a mka Ni kaina mamakin yanda ta Shiga Raina a kankanin lokaci nk" Yace " hmm ai ko dole kayi fighting soyayyar ka ,ka samu ka shawo kanta"
"Adamz tell me how, how ta Ina Zan Fara, she isn't picking my calls, look here, Yana nuna Masa wayar Na Kira ta more than 20 tym" Adamz yace "kasan ya xa ayi Tura Mata text" ba musu ya Tura Mata text
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bangaren
Kalfana tun da ta Shiga cikin Gidan Dakin ta ta wuce ka tsaye tana Shiga ta kulle ta Ciki, ta fad'a Kan gado ta Fara kuku wiiiiwiii tana Fadin " Me Na Maka Maan sai da Na Fara jin soyayyar ka ta Kamani, Ashe kai d'an iska ne", Allah ya Isa ta" cigaba da kukan ta wayar ta sai ringing yk tasan shine yasa Bata Duba ba Shi Kuma yaki ya hakura sai Taji karar message tana dubuwa taga shine sai ta Bude sakon Kamar haka
, "Babyna plz ki saure Ni Dan Allah pick my call" tajaaa tsaki ta Kwanta ta cigaba da kukanta, ya cigaba da kiranta Amma Taki ta d'aga sai ta sake Jin Wani msg din ya shigo ta Bude "My princess nasan nayi Miki laifi bazan Iya ce Miki komai ba Illa hakuri ,Dan Allah kiyi hkri ki yafe Min Babyna wlh kaunar da nk Miki ne ya Sanya Amma plz ki Bani Dama Bazan sake b'ata Miki raaai ba" har Kamar zata Masa reply sai Ga call Dinsa Kuma nan ma Taki picking ya Kira kusan sai 5 sai ya kuma turo Mata Wani msg din "hba Mata ta Kar ki Zama d'aya daga cikin mutanen da Basu yafiya mana, dan Allah kiyi hkri Na chanchanci hukuncin Amma Kar ki Hana Ni Jin muryarki, sai da safe Amma plz Kar ki Kwana da b'acin raaina, Kar na mutu acikin Daren nan ba tare da kin yafe Min ba" tana Ganin sakon jikin ta yy sanyi Amma Bata kirashi ba Sannan batayi Masa reply ba ta Koma ta Kwanta wata zuciyar Nace Mata Kar ta hkr Sannan d'ayar Kuma Nace Mata ki Yi hkri Har kin Manta kuskuren da zee tayi kema so kike sai Daga Baya kizo kina da Na sani???
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a page Na gaba

Milhaat🖊️✍🏻

Plz comments and share

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 2️⃣3️⃣↔️2️⃣4️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kar ki tafka kuskure Kamar yanda Zee tayi kizo kina Dana sani nan ta Fara tunani da jimamin kuncin rayuwar da Zee ta Shiga
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Wace ce Zainab?
Zainab'diyace ga Major general zayyad Zaid Hamid, ita Yar farin sa da kannen ta 5 Suna zaune ne a Garin Abuja barrack dinsu d'aya da Kalfana, sanadiyar admission din da ta Samu ne yasa ta Koma Gidan baffan ta yayan mahaifinta da Zama a cikin jahar Gombe, Mahaifin Kalfana da Zee Abokanai ne sun Shiga aikin soldier tare shys qawancen nasu yy karfi
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zee Na soyayya da wani Mai Suna Khalyd sun had'u ne a wurin dinner bikin wata qawarta Daga nan suka kulla soyayya Mai tsafta, Khalyd Na kaunar Zee Sosai ita ma Hk Amma bb Wanda take wulakantawa Sama dashi a fad'in ta Idan yasan tana san Shi Sosai Zai Raina ta

*3 Months back*
Zee ta sanar da Khalyd tana bukatar su had'u Amma a unguwar su Kalfana Bai Musa Mata ba Bayan sun dawo Daga lectures yaxo Suna cikin Hira ta Karbi Wayan sa ta hau bincike sai taga text message din wata Ranta yy mugun baci ta fita Daga motar a fusace , da gudu ta Shiga Dakin Kalfana, tana Shiga ta kife da Ciki akan gado sai Kuka take wiwwi , Kalfana Na wanka tana Jin Kumar qawarta ta Yi saurin d'aura zani a kirjinta jikin ta Duk kumfa tana fitowa ta dafe kafad'ar ta
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Tace
"Zee lafiya? Me ya faru"? Cikin tashin hankali..


Zee ta Tashi ta Zauna tana share hawaye da hannunta Sannan tace

"Ni Khalyd Zai Raina wa wayo"?

Kalfana kallon ta take cikin rashin fahimta

"Me Kuma ya Miki? Ku da ba a Raba Ku da complain"

"Text message fa wata shegiya ta Tura Masa Kinga kalaman da take Masa kuwa"?


"Zee knn Ashe ba Dadi"

"Kamarya Kalfana"?

"Kefa Har waya kike da samari a gaban sa, Kuma kin san yanda yk kaunar ki, kice Kula wannan Kula wanchan , a Ganin ki Yana Jin dadin hkn ne, wlh Zee ki nutsu ki rike Khalyd hannun bibbiyu don Wlh baxa mi tab'a samun Kamar sa ba"


"Ke dadina Dake in an Fara Magana sai kice ana ka Maza, kin bi kin makale wa Yaya Maan"


"Ohhhh so kike Na Rika Kula Kowa ko, wlh Na wuce nan ke Dai da Azeemah Allah ya shirya Ku"



"Ameen , Ai farin jine"


"Toh a barni da bakin Jini Na Ina wanka kika tada Min hankali,Mtsww? Sai ta shige ban d'aki Zee kuwa ta cigaba da kukan ta Hk rayuwa ta kasance wa Khalyd da Zee Yau Zuma gobe mad'aci don kusan kullum sai sunyi fad'a Amma sai Bayan sun rabu tayi ta Kuka

Kalfana tace


"Ke Ni wlh Kar ki Kuma shigo Min d'aki kina Min Kuka "

Bata Kula ta ba ta cigaba da kukan ta ita Dai Kalfana ta gaji da lamarin Zee sai kace Mai Aljanu


♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Wannan Kenan

Zee da Kalfana suka Je Hutu Abuja ranar tana Hawa online Khalyd ya Mata sallama a WhatsApp nan suka gaisa sai yake ce Mata Yana da Magana da ita Amma sai ta dawo

Tace

"Maganar Zee ce ko?

"Hmm ke Dai Bari Kawai"

"Khalyd, Zee Na kaunar ka Sosai Amma ta kasa Baka kulawar da ta dace"

"Kalfana Na sani tana kaunata Amma wasu abubuwan nata Na d'aure Min kaai"

"Sai hkri Zee miskila ce, Sannan Ga Kule Kule"

"Kule kulen nata shine Babbar matsala ta da ita, Ga su Yara, nifa Na Raina capability din su"



"Hhhhh capacity fa me kk Nufi da hkn"


"Ke Dai Bari Kawai, sai kin dawo din"


"Okay gud nyt"

"Amma Kalfana kinayi wa abokina wulakanci"


"Ni Kuma Wani abokin Naka"?..


"Anas mana kinsan fa yanda yk kaunar ki Sosai but sai ki nuna Halin ko in Kula"...


"Khalyd Ina da Wanda Nk so Kuma soyayyar da ke Raina Bazan Yi Mata kishiya ba, ko so kk mu rabu da Maan"?...


"Awww Dama Kuna tare da Yayan Zee Har yanxu"?...

"Laaaaaa Na Gano ka da so kk mu rabu"?


"A'a wane Ni my In law kai Na a kasa"

"Da ka kyauta wa kanka"...


"But plz ki sake Nazari Akan Anas mutumin kirki ne "...


"Toh zanyi, bye"

Da safe zee taxo Gidan su Kalfana , Kalfana ta nunuwa zee chat dinta da Khalyd Zee tayi dariya tace

"Maybe Maganar Anas din Zai Miki"


"A'a maganar ki Dai, ke Dai Allah ya shirye ki Ina gudun Miki ranar da Khalyd Zai guje Miki nan be Zaki gane baki da wayo"

Zee tace
"Kan Ku ake Ji"
Nan suka cigaba da hirar su
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*After Holiday*

Zee da Kalfana suka Koma makaranta , Zee da Khalyd Dai suka daura Daga inda suka tsaya
Bayan Yan kwanaki suka Yi chat fa Kalfana take sanar Masa cewa ta dawo ya tabbatar Mata da in ya Samu lokaci Zai zo sabida aiki Na Masa yawa a asibiti Amma Insha y in ya Samu sarari zata ganshi, Khalyd Dentist ne(likitan hakori)

A ranar da ya shigo cikin makarantar tasu Kalfana ma lecture Basu Samu damar had'u waa

_Bayan Sati 2_

Zee, Kalfana da Azeemah ne a zaune a d'akin Azeemah, zee tace

"Kalfana munyi chat fa Khalyd last week yace Min Yana so muyi Magana Mai muhimmanci Amma yanzu Zai Je asibiti in ya dawo Zai kirani in Bai dawo ba sai wataran"


"Kamarya sai wataran, nifa nakasa ganewa Khalyd din kin nan sai kiji Yana Magana Kamar zaiyi tafiya Mai Nisa Kuma Kamar ba ranar dawo wa"


" Kalfana me Ganin hkn ma kike nifa cemin yk Swthrt Zanyi tafiya Kuma in Na tafi Bazan dawo ba"

Azeemah Duk zancen da suke tana Jin su Kawai Dai chat dinta tk Ganin ba a Sakota cikin zancen ba


Kalfana tace

"Yaushe kukayi chat din"

"Kwana 4 knn Yau"

"Toh kin kirashine"?

"A'a ban kiraba"

"Matsala da ke knn,plz ki Kira Shi"

"Kalfana Ai Maryam tace Min , Sufyan yace Mata Khalyd Bai da lfy"

Sufyan abokin Khalyd ne Kuma abokin Anas me

"Plz kirashi, zuwa asibiti ya kama mu"

"A'a Kalfana plz ga Wayan ki kirashi"


"Sai akace Miki bazai gane muryata ba"?

"Bazai gane ba kin manta Basu banbance muryar mu"

Ta karba tayi dialling bugu 2 aka d'aga da sallama sai Taji Kamar ba muryar Khalyd bane Bayan sun gaisa tace

"Plz Ina mai wayar"?

"Yana bacci"

Tace

"Okay ngd, Amma ya jikin nasa"

Yace

"Da sauki Alhamdulillah"

"A Wani asibiti kuke plz"

"FMC"

"Okay ngd Allah ya Bashi lfy" ta katse wayar
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zee Kuka ta Fara Yi tun da Taji ance bazai Iya waya ba

"Zee me Hk cuta fa ba mutuwa bace addu'a Zaki Masa,in Allah ya kaimu gobe sai muje asibitin mu Duba Shi"

Ta amsa Mata da

"To"

Suka cigaba da hirar su Dake Yau Saturday be lecture d'aya suke dashi Kuma da safe me

Suna cikin Hira Kalfana ta Bude data ta Fara chat sai taga Anas yasa Hoton Khalyd a status ya rubuta "Plz pray for Dr Khalyd Rashid"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Ta Masa reply "me ya Sami Khalyd din"?

"Kalfana tsautsayi"...

"Kamarya tsautsayi accident yyi"?

Yace

"A'a an Masa aiki a hancin sane, so a process din ne infection ya Shiga ,daganan ya daina gane Kowa Bayan Kwana 2 barin jikinsa d'aya sa ya Yi paralyze (barin jikin Sa ya Shanye) yanzu haka kwanan sa 5 a ICU"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un , Allah ya Bashi lfy,Insha Allah xamu zo gobe Zan Kira ka"

Sai ta kashe fatan jikinta yy sanyi ta rasa ta yadda zata fad'awa zee maganar nan

Sai Ji sukayi ta sa ihu tana "Allahumma Ajirni Fi musibati", Kalfana Khalyd, Khalyd wayyo Na shga uku" ta daura hannu aka ....

" Waya fad'a miki"?....

Tace "Anas"

Tajaaa Dogon numfashi tace "haba Anas Ai ba hka ya kamata ya fad'a Miki ba, kiyi hkri Zee Allah Zai Bashi lfy"

Azeemah sai hkri take ta bawa Zee, zee Kamar ce Mata ake ta Kara kukan sunyi rarrashin Duniya sun kasa sai, kallon hotonsa take tana Kuka

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zee ranar wuni Kuka tayi, hatta abinci ta kasa ci sai karfe 6 Kalfana da Azeemah suka rakata tashiga adaidata ta Koma gida jiki a Sanyaya
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan sallar Isha Kalfana ta hau online sai ta turawa Anas Sako Kamar HK

"Anas plz ka daina fad'awa zee komai game da rashin lfyn Khalyd ka fad'a Min Zan San yanda Zan sanar da ita'

Yace

"Ko meyasa"

"Sabida d'azu tafi awa 4 tana Kuka bayan ka fad'a Mata Yana ICU"

Sai Ga Kiran Zee tana picking Taji tana shasshekar Kuka

"Haba zee Haryanxu Baki daina kukan ba"?

"Kalfana, Anas yace in yace Min jikin Sa da sauki ya Min Karya" tana Kuka Mai Cin raaai

Kalfana tausayin qawarta tk nan Fara Kwantar Mata da hankali Sannan ta Mata sai da safe
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Next morning*
Kasancewar Yau Sunday zee sai 10 ta zo Gidan su Kalfana nan suka shirya tsaf Azeemah, Kalfana,da Zee Duk simple dress suka Yi Sannan suka Dogon hijab Har kasa, sukayi da Maryam su had'u Kawai a asibitin nan suka wuce FMC
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Suna Isa Kalfana ta Kira Anas yazo ya Shiga dasu, ba a Shiga cikin d'akin da yk Yau kwanan sa 6 baci ba Sha sai da taimakon nakura hatta numfashi Na inji ne ya kai su gun Mami suka durkusa suka gaisheta ta amsa kana Jin muryata Zama San tana cikin tashin hankali
Mami Tace

"Gashi kunxo ba a Shiga"

Kalfana tace
"Eh Mami , Allah ya Bashi lfy"
Tace
"Amin" nan ta Riki bakin hijab dinta ta Na share hawayen fuskarta, zee Ganin hkn itama ta Fara nata kukan, Maryam ce tace Mata

"Zee lafiyan ki kuwa ki daina plz Zaki sake d'aga Mata hankali"

Mujeedat tausayin qawarta tk don Duk Sanda taga tana Kuka ita ma sai ta Taya ta hkn yasa ta kauda Kanta itace ta Fara mikewa

"Mami Allah ya Bashi lfy " suka Tashi suka fita jiki a Sanyaye

Basu Yi Nisa ba Anas,Sufyan da Mansur suka bi Bayan su Suna musu Godiya Kalfana tace

"Bkm mun Zama d'aya" Anas yace HK ne"

Anas suka jera da Kalfana Suna tafiya Kamar wasu masoya

Maryam da Sufyan..

Azeemah da Mansur

Kalfana hankalin ta yy Nisa Anas Na Bata lbrin yanda abun ya faru sai sukaji muryar Zee Na Kuka da karfi da sauri Duk suka Nufi inda take a tare sukace "lfy me ya faru"? Hankali Kalfana yafi Na Kowa Tashi
Zee tace

"Ga Anas da Mansur da Kuma Sufyan Amma ba Khalyd Dina" sai ta fashe da Kuka wannan karon Kalfana kasa controlling Kanta itama kukan ta Fara yi Mansur yace

"Haba Kalfana ke da Zaki rarrashe ta Kuma kema kike Kuka"?

Azeemah tace
"Kalfana,Zee plz Ku daina Kar Nima Na Fara"

Maryam tace
"Lallai zamu Tara Yan Kallo, Duk muyi hkri Insha Allah Zai warke"

Zee tace "Ina Ji a jikina Khalyd ya mutu Kawai boye Min Kuke" Haryanxu Bata daina kukan ba

Anas yace

"Kuyi hkri Ku Tashi mu Maida Ku Gida"

Sufyan yace
"Kuyi hkri addu'a zamu mishi" sai suka Nufi parking area

Kalfana , zee da Anas da Azeemah Mota d'aya suka Shiga Anas ke Jaan motar Kalfana ce a zaune a gaban motar, zee da Azeemah a Baya, d'ayar motar kuma Maryam ne da Sufyan tafiya suke babu Wanda yace komai Har suka Isa Gidan su Maryam suka sauke ta Sannan suka Nufi Gidan su Kalfana Suna Isa suka musu Godiya suka shige

*After 3 days*

Khalyd Dai jiki Shiru Haryanxu Kullum sai Anas da Kalfana sunyi waya sabida Taji ko akwai improvement Amma Shiru kwasam sai Anas ya Kira Kalfana Yana sanar da ita cewar Za a kai Shi Aminu Kano tayi murna Sosai kai tsaye ta sanarwa Zee Duk sunyi farin Ciki da fatan Zai dawo da kafansa ranar laraba aka kaishi Garin Kano Anas yaso binsu Amma mahaifiyar sa Dr Maimuna Khamis ta Hana sabida itace take Kuka dashi ita Kanta rashin lfyn Khalyd Na tada Mata hankali Abu Kamar Wasa Bayan sun Isa ne Anas yk sanar da Kalfana cewar a Daren laraba Za a Masa aiki
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Karfe 2 aka Shiga dakin tiyata da Khalyd likitocine Har 5 akansa an Samu damar yin aikin saura tube d'aya akayi ta nema aka rasa sanann Dr Yazeed Malik Baya Gari likitan kwakwalwa ne da aka sanar dashi Halin da ya me Ciki ya sanar dasu insha asuban fari Zai shigo Gari.....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a next page

```Sis Fareedah💞
Sis Rufeey💞
Sis Ummu hanifa💞

A gsky Ina Jin dadin comments dinku🥰🥰 Allah ya bar kauna
```

Afuwan Fans Nayi typing Amma network dinmu ya dauke

A gafarce Ni musamman
@⁨Baby Haruna⁩ da
@⁨Asma'u Lawal Magini⁩

Babyn mu network din Garin ku ya b'ata Min raaai😡😡

*Plz Comments and share*🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻✍🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 2️⃣5️⃣↔️2️⃣6️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Karfe 5 Na safe Dr Yaxeed ya shigo cikin Garin Kano, Bai zarce ko Ina ba sai asibiti zuwan ke da wuya aka cigaba da aikin Amma shikan sa ya tsorata Sosai sun fi awa 6 aka San karfe 2 da rabi Na Rana


raaii yy sa kullu Nafsin Za'ikatul maut Khalyd bb rai😭
Ba a d'auki lokacin ba aka Fara sanarwa Yan uwa da abokan arziki nan da nan garin Gombe ya d'auka sabida Khalyd matashi ne mai hazaka Ga son mutane,

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana da zee ne suke tafiya acikin makaranta Suna Hira Amma ba Sosai ba sai wayar Kalfana ya Fara ringing tana dubawa taga Anas ne tayi saurin picking ta amsa da sallama Bayan sun gaisa Anas yace Mata

"Kalfana, Ina Zainab"?

"Gata Muna tare"

Yace "Toh Khalyd ya rasu"
Kalfana tsayawa tayi chaaaak
Tace "Na'am"

Yace "eh Khalyd Allah ya Masa cikawa"

"Toooooh yaushe hkn ta faru"?

'dazun nan Allah yamasa cikawa" sai ya katse wayar

Kalfana idon ta Duk sun Ciko da hawaye Amma ta rike Kanta ta rike hannun Zee ta Fara jaàaan ta da Hira , zee tunda Kalfana ta Fara wayar hanakalinta kasa kwanciya yy,
Tace

"Kalfana me Anas din yace Miki"?

" Babu komai" ta kauda Kanta gefe don hawaye ne yk kokarin sauka Zeee tace
"Kuka kike Yi "

"Kuka Kuma Akan me Abu ne ya ya fad'a Min a Ido Suna tafiya Suna Hira Amma kwakwata Kalfana hankalin tabaya jikin ta
"Taya Zan Fara fad'a Mata cewar Khalyd ya rasu sun fi mint goma Suna tafiya acikin makarantar security office suke son zuwa karb'an Id card din su

Suna tafiya wayar zee ya Fara ringing tana dubawa taga Maryam ce tana picking tace
"Hloo Maryam" Kalfana Jin zee ta ambaci sunan Maryam a tsorace ta juyo don tasan tabbas Taji lbrin mutuwar ne kuma tafi so sai sun Samu wuri sun Zauna Kan ta sanar da ita Amma Ina Kan ta kwace wayar sai ji tayi Maryam Nace wa

"Zeee Wai Anas ya mutu"?

Zee ta zaro Ido "ya mutu" sai ta Yanke jiki xata fad'i Kan ta kai kasa Kalfana tayi saurin riko ta tana Kiran sunan ta

"Zee!!! Zee!!! Plz wake up , Dan Allah ki tashi" Maryam ta sake Kira Kalfana tayi picking "ke Maryam wannan Wani irin rashin hankaline ,Haka ake fad'an mutuwa"? Tayi tsaki ta kashe wayar

Ranta Kuma cewa "take wlh sai nayi maganin ta Bari ta gani"

Side din da suke yy Baya Sosai ba mutane sunfi 5mint a Haka wasu Maza 2 Suka wucewa Ganin halin da suke ci suka karso inda da gudu Dayan ne yk tambayar Kalfana "me ya same ta"?
"Suma tayi" sai suka Fara Mata Fifita"
zee ta fara Wani irin numfashi Kamar Ranta Zai fita Kalfana ta

Please Login or Register in order to submit comment