Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sokon mijin naki ya dawo kice Masa wacce ta San darajar 'ya'ya tazo ta d'auka wa Haneefah fansa" bud'e kofar tayi ta fita a hanyar ta ta fita suka had'u da Haneefah na tafiya da kyar shafa fuskar ta tayi, Haneefah Tace "Laaah Aunty Khalfana" sai ta rungumeta "Haneefah ya kike" "Lafiya kalau" "Sannu ko Haneefah Zan tafi, anjima Zan kawo Miki chocolate Kar ki fad'awa kowa nazo Nan kinji" "Toh Aunty" sannan tayi murmushi da sauri ta fita, Lami na Mata magana Amma Bata juya ba, ganin jinin Dake hijab d'in kalfana yasa ta haura d'akin Yusrah da gudu, Khalfana na shiga ta tada motar mai gadi ya bud'e musu gate, gudu Khalfana keyi sosai sai da ta tabbatar sun yi nisa da unguwar kan ta rage gudu, Azeemah tace "Oh My God Khalfana you are bleeding"

Zainab tace "Khalfana muje asibiti"

Murmushi tayi tace "Gaskiya Ina Jin dad'in yadda kuke nuna min kulawa,Amma banji ciwo ba."

mikawa zee wayar ta tayi ta Mata playing video dukan da ta yi wa Yusrah, Zainab tana Gama gani ta Mika wa Azeemah, Azeemah tace "Khalfana kin kashe ta" "a a ban kashe ta ba, tana da raai ai bazan so ta mutu ba, don nafiso ta wahala tukunna in ma muturwa ce Kullu Nafsin za'ikatul Maut, bare ma sai dai ta Suma ba mutuwa ba"

zeee tace "Dakyau Dan Allah bani hannun ki musha tafi sukayi duk suna Dariya, Azeemah tace "Khalfana sai kace kin samu sakwara sai kirb'anta kawaii kike" duk sukayi ta dariya, Khalfana tace "Zeemah gida zamuje na watsa ruwa na canxa kayan Nan in Aunty Fatee ta ganni a haka na kad'e, Allah yasa momy Bata Nan"

"ai Kuwa Bata Nan tayi tafiya"
Khalfana tace "Masha Allah,yau fa sai sa'a kawaii nake" suna Hira har Suka Isa gidan.

Wanka tayi ta canxa kaya suka fita don zaga gari.
Wurin shakatawa suka je suna ci suna Sha suna hirar su, kwasam wayar Khalfana ya Fara ringing tana dubawa taga sani ne da Sallama tayi picking ya amsa sannan yace "Ya na jiki Shiru ko kin fasa zuwan ne"? "eh Wallahi na fasa yanzu haka ma bana gari" "Ina Kuma kika je"? "harkar makaranta ce suka tura mu Bauchi" "okay Allah ya taimaka" "Ameen Nagode".

Zee mamaki take tace "Khalfana yaushe kika zama haka ne?,ni wlh kin Fara bani tsoro"

Zeemah tace "Nima haka mamaki kike bani, Khalfana u know all this tactics Amma baki d'auki mataki Akan mu ba?"

"Look zeemah abinda ya faru tsakanin mu is a pass so just forget it ki daina ma d'auko zancen plx"


Wayar Khalfana ce ta Fara ringing Amma wannan karon message ne tana bud'ewa taga private number ma'ana an b'oye number karanta sakon ta Fara yi kamar haka.

" ```Assalamu Alaiki, kyakkyawa son Mai so kin Wanda bai Samu ba da fatan kina lafiya sarauniya ta.```"??

Mamaki ta shiga yi a fili tace "Waye Kuma wannan"?
Zee tace "Mene ne"?
"Bakomai"

Karar wani sakon ta Kuma ji

Ta bud'e ta Fara karanta shi kamar haka,

" ```My Queen please karki tsorata ni masoyin ki ne ba makiyi ba sannan bazan cutar da ke ba"```

A ranta tace "tsoro dole"
Aje wayar tayi sukayi ta hirar su Amma hankalin ta na kan Mai turo Mata sako.

Sai tace "Zeemah a Ina ake sayar da, tab'arya"?

Azeemah tace "Khalfana tab'arya kuma, me Kuma zakiyi dashi" a tsorace dariya Khalfana ta farayi tace "Dallah chan matsoraciya ,ba kiga na bar na aunty na a gidan bane ya kamata na maida Mata kar ta gane"

"Okay daga Nan sai muyi kasuwa kawaii"

"Okay"

Bangaren Yusrah Kuma Lami na shiga ta tarar da ita a sume, da gudu taje wurin Mai gadi Akan ya tsayar dasu Amma Ina sunyi nisa, Kiran Maan Lami ta shiga Yana ganin call d'in kirjin sa ya Fara duka uku uku, don idan yaga Kiran Lami to tabbas wani abun ne
Ya faru, picking yayi hannu na rawa ya Kara a Kannen sa, yace "Assalamualaikum" lami da ke tsoro duk ya mamaye ta kasa amsa sallamar tayi tace "yallab'ai, yallab'ai Aunty" Tashi yayi ta tsaya "Aunty Kuma me ya same ta?" "Suma tayi" "gani Nan zuwa" ya katse wayar Adam da ke zaune a gefen sa kallon sa kawaii yake.

Maan yace "Na shiga uku, Adams tunda nayi Auren Nan hankalina kullum a tashe yake"

"Me Kuma ya faru"?

"Yusrah ce Wai ta Suma"
Mikewa Adams yayi yace "Muje gidan Amma Bari na Kira Dr Abdulazeez sai mu had'u a chan"

Hakan Kuwa akayi, a tare suka Isa Kai tsaye d'akin ta suka shiga Lami na rab'e a jikin bango don kasa kunce ta tayi, Maan yace "waya d'aure ta haka"? cikin rashin fahimta , kunce ta ya shiga yi bayan ya Gama kunce ta ya d'agata ya kwantar da ita a akan gado hannun ta na Lilo da alama ta karye haka ma kafar ta , masifa ya shiga yi wa Lami "Ina magana kinyi shiru wa ya mata haka"? Adams yace "Abokina calm down Mana baka ganin kana tsorata ta ne, Lami fad'a Mana me ya faru"?

"Yallab'ai wasu Mata ne su 2 suka shigo, bayan sun fita sai wata ta shigo, a lokacin Ina sallah ita ce ta Mata haka"

"Kinga fuskokin su"?
"A'a ban gani ba" Maan yace "ya Zaki ce baki gani ba" a tsawace

"Duk laifin Tanimu ne ai shine Mai gadin gidan Nan" fita yayi Yana ta balbale Tanimu da masifa, Tanimu sai hakuri yake ba dawa tabbas ya bada guduwa gun cutar da Matar Mai gidan sa, tunda shi ya bud'e musu gate.

Abdulazeez yace "Guys duk ba wannan ba mukai ta asibiti tukunna taji ciwo sosai Kuma ban fita da kayan aiki ba, gashi ta zub da jini sosai za ta iya rasa ranta"

Sata sukayi a mota, sai asibiti emergency aka kaita , an Samu hannayen ta duka biyu sun karye da kafar ta d'aya ma ya karye.

Maan burinsa ta Tashi don yaji Wanda ya Mata aika aikan Nan, duk da irin rashin kunya da wahalar dashi da take Yana Kaunar Matar sa tunda dai auren soyayya sukayi.

Dr Abdulazeez ya Sanar dashi irin raunukan da Taji ya tabbatar mishi da cewar "zata dad'e Bata warke ba ga karaya , ga yankan wuka, da Kuma ruwan zafi".

Maan kansa ne ya d'aure ya rasa ma me zaice, Abdulazeez da Adams kokarin kwantar Masa da hankali suke,
Abdulazeez yace ya kamata ka d'auko Mata Kaya don wannan ya b'aci da jini"
"Okay Bari naje na kawo Mata"

Adams yace
"Bari naje pharmacy na sayo Mata magani" Kai kawaii Maan ya d'aga Masa , a Hanyar su ta zuwa pharmacy Abdulazeez yacewa Adams "kana ganin ba Mahaifiyar su Haneefah bace ta yi Mata haka"?

"Anya kuwa, Bata kasar fa tana Aure a Ghana, Kuma tunda ta tafi Bata tab'a waiwayar Nan ba"

Abdulazeez yace "Allah shi kyauta".

Adams ya Amsa da "amiin"

Maan na komawa gida d'akin Yusrah ya shiga, Waldrop ya nufa ya Fara neman kayan da zai d'auka Mata, sai ya ga wani Abu na sheki karasawa yayi don yaga ko me nene, wuka ya gani duk jini, sai yanxu ya Lura da flask da tab'aryan da ke kwance a wurin, waya ya d'auka ya Sanar da Yayan sa, ba b'ata lokaci a asibitin suka had'u, ganin yanda take ya same ya Sanar da Matar sa da tazo.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Washe gari*

Khalfana na Tashi da asuba tayi alwala tayi sallah, bayan ta idar ta d'auki wayar ta sai ta ga sako tana bud'ewa sai taga wannan private number ne yace
```"Assalam Farin cikina da fatan kin Tashi kinyi sallah ko,toh Dan Allah ki Mana addu'a, I LOVE YOU"```

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un nikam ko nayi gamo da aljani ne"?

Karar wani sakon taji tana bud'ewa taga
```"Ni ba aljani bane mutum ne kamar Ki"```

Khalfana kashe wayar tayi ta Tashi ta nufi kitchen, ta Fara had'a musu breakfast, ta na gamawa ta Koma tayi wanka ta shirya don yau 7 take da lectures, Khalfana har tsoron kunna wayar ta take, bayan sun Gama karya wa ta Tashi ta fita bayan tayi wa Aunty Fatee da uncle Sallama, Aunty Fatee tayi nauyi duk da cikin wata 5 ne amma kamar tana cikin watan ta.

Yursrah kwana tayi a sume sai da asuba wurin karfe 4 ta farka, wani Kara tasa tana fad'in "Dan Allah kar ki cutar Dani, Dan Allah kiyi hakuri" Maan da bacci ya d'auke sa a zaune da sauri ya nufi inda take, yace "Yusrah Yusrah Ina Nan babu Mai cutar Dake ki kwantar da hankalin ki" hannun ta take kokarin d'agawa Amma ta kasa zafin da Taji jikin ke Mata yasa ta Fara kuka, ya shiga rarrashinta Kiran Nurse yayi a ka Mata alluran bacci.

Tana driving ta kunna wayar ta aje , wayar na Fara ringing ta tsorata, parking tayi ta d'auki wayar hannu na rawa taga zee ce da sauri tayi picking" Hello Khalfana kina Ina ne na shigo ban ganki ba" "Gani Nan Ina bakin gate yanzu Zan shigo"

"Ya naji muryar ki haka " "ke dai gani Nan" ta katsewar zata maida wayan ta aje taga wani sakon

Hannu na rawa ta bud'e

```Amincin Allah ya tabbata a gare ki Masoyiya ta, hasken idaniya ta na kanyi farin ciki matuka idan Ina tare Dake, na kan manta dukkan want damuwa idan Ina tare da ke, barka da safiya.```

A fili tace "Tare Dani, yaushe ya sanni har ya ke fad'in hakan"?


Motar ta tada ta shiga school.

Yusrah ta dad'e tana bacci ta da kuka ta farka Maan ya shiga rarrashinta, bayanta tayi shiru ya ce Mata "Yusrah waya Miki haka"?

"Wata ce"
"Wata wa kin santa ne?"

"A'a ban Santa ba" cikin kuka ta kwashi yadda sukayi ta fad'a Masa.

"Shikenan ki daina Kuka Zan d'auki mataki akai".

Adam na shiga d'akin yace "look kabi abun Nan a hankali, ka maida hankalin ka akan rashin lafiyar ta"
"Toh Shikenan"

"Yusrah ya jikin" da kyar ta amsa "da sauki" Adam Dariya yaso yi amma ya danne, a ransa yace "Amma naji dad'in lamarin Nan ,Allah yayi Miki Albarka koma wace ce, ji yadda ta zama sai ka ce ba masifaffiyar da na sani ba" (Adam mugunta Kenan)🤣

Sai yace "Amma Yusrah Zaki iya gane ta"?
"Eh Zan gane ta"
"Toh da sauki, Allah ya baki lafiya"
"Ameen"

Haka rayuwa ta kasance wa Khalfana da wannan Mai b'oyeyyen Number kullum sai ya tura Mata sako, tun tana Jin tsoro har ta daina Jin tsoro yanxu kimanin Wata 4 Kenan.


Wata ranar jumma'a dawo warta Kenan daga makaranta taga Aunty Fatee ta zube a kasa tana fad'i "wayyo cikina" da gudu Khalfana ta karasa inda take tace "Aunty lafiya me ya same ki" dakyar ta Samu ta ce "Khalfana Kai ni asibiti Ina ganin kamar nakuda ce" a daddafe ta sa ta a mota sannan ta d'auki duk wani abun da suke bukata a d'akin aunty Fatee ta jaaa motar a hanyar su ta tafiya ta Kira uncle ta Sanar dashi halin da ake ciki, ya ce Mata su had'u a asibitin, asibitin da Abdulazeez ke aiki ta kaita suna Isa aka Kai ta d'akin haihuwa, Khalfana sai safa da marwa take, Ba a dad'e ba sai ga shigowar uncle ,shigowar sa yayi dai dai da shigowar Dr Hassana, tace "Kece kika kawo ta ko"? Tana nuna Khalfana"Eh nice" "Ina mijinta"? Uncle yace "nine" "Masha Allah congratulations Matar ka ta sauka lafiya, an Samu Twins mace da na Miji" Khalfana tace "Alhamdulillah" uncle yace "Ita Kuma fa tana lafiya"? "Eh duk suna lafiya" yace "toh toh Masha Allahu" Khalfana tace "zamu iya shiga yanxu"? "A a ku d'an jira kad'an " sai ta Koma ciki.

Khalfana tace "Uncle Bari naje na Mata girki"

"To Shikenan" wasu makudan kud'i ya Mika Mata, yace "ki Kira Mummy ki Sanar da ita, ki tambaye ta duk abubuwan da akeyi sai kije kasuwa"
"Toh" kawaii tace Masa, ta Tashi ta fita a kan ta Isa motar ta Taji an Kira ta, ta baya juyawa tayi don ganin Wanda yake kiranta , Adam ta gani da Abdulazeez suna murmushi, ita ma murmushin tayi, tace "kaga manyan mutane" adam yace "in baku Nan Kenan ko" Nan suka gaisa, Abdulazeez yace "Waye ba lafiya"? "Aunty na ce ta haihu" "Masha Allah me aka Samu"? Murmushi tayi tace "Twins" Adam da Abdulazeez suka ce "Allah ya Raya" ta amsa da "Amin Nagode, sai anjiman ku"

Adam yace "mutumin ki na Nan fa" "mutumina wa Kenan"? "Suleiman Mana" "oh Allah sarki, me Kuka Zo yii"? "matar sa ce ba lafiya kullum sai anzo wanke Mata ciwo" Khalfana tace "har yanxu Bata warrrr...." Sai Kuma tayi shiru Adam yace "Bata me ba"?

"Yi hakuri hankalina baya nan, Bari na tafi sai anjiman ku" da sauri ta shiga mota ta fice daga asibitin.

Abdulazeez yace "Anya" Adams yace "Anya me"?
"Akwai abinda Khalfana ke boyewa" "Nima nayi tunanin hakan" muryar Maan sukaji "Ina kuka shiga nake ta neman ku"? Adams yace "Khalfana yanxu ta barnan"
"Dan Allah dai dagaske kake"? "Eh dagaske nake" "ta Ina tayi Bari na bi ta" Abdulazeez yace "zata dawo ai" Maan yace "Okay".

Tambayar su ya shiga yi me ya kawota, Adam ne ta fad'a Masa Auntyn tace ta haihu yace "Masha Allah"

Khalfana na fitaa tayi parking Tace "chaaapdi saura kiris da na tunawa kaina asiri" Kiran Mummy tayi ta sanar da ita sannan ta Sanar da ita abubuwan da ya kamata ta sayo.

Bayan sun Gama wayar ta nufi kasuwa tana driving sai taji kamar tayi mantuwa, "me na manta, tabbas akwai abinda nake son yi" sai ta tace "Na tuna Mr Unknown yau bai tura min sako ba" acikin wannan tunaninin ta Isa kasuwa ta sayi duk abubuwan da mummy ta fad'a mata sannan ta Koma gida tayi girki, Kirin zee tayi ta Sanar da ita aunty ta haihu farin ciki tayi dama tana school tace "Gamu Nan zuwa nida Azeemah ki jira mu" "a'a mu had'u kawaii achan" "okay to sai mun Zo"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Khalfana na tuki a fili tace "Ya Allah Wai me ke Shirin faruwa ne, tun Jiya bai turo min sako ba, Allah yasa lafiya" (ni ko nace khalfana kina ruwa soyayya da aljani Tabb)

Tana isa asibitin parking tayi ta riko food flask a hannun ta , tana tafiya a nitse wani mutum ta gani a gaban ta Yana tafiya tace "Kamar na San mai wannan tafiyar but who"?

Kan ta karasa inda yake har ya shige wani d'aki,tab'e baki tayi ta shiga d'akin da Su Aunty Fatee suke, Uncle ta gani rike da jariri, murmushi tayi tace "uncle duk Wanda ya gan ka ya ga sabon shiga"

Dariya yayi yace "Toh ai Daman hakan ne Yar qanwata shekaru 6 fa ba wasa ba"

"Haka ne Uncle Allah ubangiji ya Raya Mana su"

"Ameen" "Aunty haryanzu tana bacci"
Aunty Fatee tace "Ina Jin ku Khalfana ai na dad'e da tashi " "sannu Aunty ya jikin" "Alhamdulillah" "sannu" "bara na Sa Miki abinci" "a'a Khalfana bani yoghurt d'in in mun Koma gida na ci" Mika Mata yoghurt d'in tayi suna Hira uncle na rike da jaririyar Khalfana Kuma na rike da jaririn.

Zee da Zeemah suna shiga asibitin, sai suka ga motar Adam , kiransa zee tayi "Hello Sweetheart kana Ina"?
"Ina asibiti" "me kazo yi"?
"Nazo duba Matar Maan".

"Okay muma muna asibitin"
"A ta Ina"? "Parking area" "okay gamu Nan zuwa"

Zee da Zeemah fita sukayi da ga motar suna tsaye a jikin motar, Maan suka Fara hangowa sai adams da Abdulazeez, Maan burinsa ya ga Khalfana Amma yaga Bata Nan, bayan sun gaisa dukkan su suka nufi d'akin da su Khalfana suke, tun da ga waje suke Jin Dariyar su.

Zee ce ta turo kofan da Sallama a bakin ta, dukka suka amsa, zee na shiga da sauri ta rungumi Aunty Fatee Dake zaune a kan gado, tace "congratulations aunty am so happy for you" aunty Fatee murmushi tayi Tace "thank you zee" Zeemah ta gaida su duk suka amsa ,Maan ,Adams da Abdulazeez suka shigo da Sallama duk suka gaisa sannan suka musu barka da samun karuwa, kallon Maan uncle yake yi Yana Masa kallon sani, shi Kuma Maan kallon Khalfana yake, Khalfana Kuma kallon jaririn take, Adam yace "Khalfana har kin dawo "? "Eh tun d'azu " "okay yayi kyau".
Kalon Maan tayi a ranta Tace "Ashe shi na gani d'azu" sai ta kau da kanta

Uncle yace "Kamar na Sanka ko"? Yana nuna Maan "eh yallab'ai, Suleiman Baba"

"A a kace Alhaji Suleiman zaka ce"

Dariya Maan yayi Yana tsotsa keya.


Uncle yace "Ya Matar ka naji ance ba ta da lafiya tsawon Wata 4 "

"Eh wallahi jiki da sauki, za a ce"

"Kai Abu baiyi dad'i ba ace a shiga har gida a Mata jina jina, Allah ya kyauta duk suka amsa da Amin Amma Banda Khalfana.

Zee Tace "Maan Muje mu duba Matar taka" yace "Toh muje" Khalfana na zaune tana buga game a wayar ta zee Tace Khalfana muje ko "ni fa babu ind......." Aunty Fatee ta katse ta "Khalfana kuje Mana kinga yanxu muma za a salleme mu kinga sai mu tafi ko" Tashi tayi Amma ba don ta so ba, suna shiga d'akin da Yusrah take wani wari suka ji duk suka toshe hancin su, Maan Dake ya saba har ya daina Jin warin.

Khalfana kallon Yusrah tayi sama da kasa sannan Tace "kamar ma bacci take" Maan yace "eh shiyasa bamu tafi ba jira nake sai ta Tashi" Khalfana Tace "Adams ya jikin Haneefah"?

"Haneefah ta warke ai kinsan jikin yaro" "haka ne Allah ya kare Mana su" duk suka amsa da Amin , Maan a ransa yace "wato Adams ya fad'a Mata,ko ba komainaji dad'i tunda ta damu da jini na" Maan burinsa Khalfana ta kalle shi Amma Khalfana Bata ma San akwai mutum a wurin ba.

Khalfana Tace "Zee mu tafi ku ko"?
"Okay" suna fita suka fashe da dariya har sai da Wata nurse Tace "lafiya Kuwa"? Zeemah Tace "Yi hakuri" tsaki ta jaa ta bar wurin.

Su Adam da sauri suka fito, suna kalle kalle Adam yace "lafiya ihun me kuke"?

Zee Tace "ba mu bane wasu ne sun wuce ma".

Kalfana karan shigowar sako ne tasa ta duba wayar ta, burin ta taga massage d'in Mr Unknown Amma sai taga Alert na kud'in da dad yace zai turo Mata, duk Taji ba dad'i.

Tafiya tayi ta bar su Zee a wurin ta Koma d'akin da Aunty Fatee take, ta Samu wuri ta zauna, Aunty Fatee kallon ta kawaii tayi ta kad'a Kai uncle yace "Qanwata Ina qawayen naki"?
"Suna zuwa"

Datan ta ta bud'e sai taga sako daga wani sabon Numb
" ```Assalamu Alaiki kyakkyawa"```

Wani farin ciki taji , a ranta tace "Alhamdulillah ya Fara bayyana min kansa"

Ta Masa reply da ```"Wa alaikassalam"```
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Mu Had'u a page na gaba*
Milhaart 💞 ce

Please comment and share🙏🏻🙏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣4️⃣5️⃣↔️1️⃣5️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
```"Barka Da war haka Tauraruwa ta"```

```"Yawwa barka daai"```

```"Na San baki gane ni bako"?```

```"Eh ban gane ba"```

```"Ni masoyin ki ne,Ina so ki bani da ma na nuna Miki irin so da Kaunar da nake Miki"```

```"Taya za a yi na baka wannan Damar bayan ban San ka ba"?```
```"Kar ki damu"```

```"Na damu"```

```"Hahaha a gaskiya kina da abun dariya, Za ki San ko ni waye Amma Dan Allah kar ki tsananta bincike sannu a hankali Zaki San ko ni waye, sannan Dan Allah ki bani Damar Kiran ki"

```

```"Toh Shikenan na baka"```

```"Nagode sosai anjima Zan kira ki"```

```"Amma Dan Allah ya sunan ka"?```

```"Zan Sanar Dake Amma for now please kiyi Saving da Mr Unknown"```

```"Mr Unknown wannan wani irin suna ne"?
```

```"Sabo da ni ba komai bane, Kuma ba kowa bane sai lokacin da na Samu soyayyar ki"```

```"Ikon Allah, Allah ya tabbatar da Alhairi"```

```"Amin naji dad'in addu'ar ki"```

```"Hmm Nima haka,bye"```

```"Alright take care of yourself for me"```

```"Insha Allah, and you too"```
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kashe datar ta tayi sannan ta Fara tattara kayayyakin su, tana cikin tattara kayan sai ga shigowar zee da Zeemah, Suma suks shiga tayata Basu dad'e ba su ka tattare kayan duka.

Zee Tace "ya tafiyar zai kasance ne, motoci har uku"

Zeemah Tace "Bari na rike jariran a motar Uncle, Ina Taya aunty Hira, ku Kuma drivers ku jaa motar ku" cikin zolaya.

Aunty Fatee Tace "eh hkan yayi"

Suna fita gidan Aunty Fatee suka zarce , zee da Zeemah Basu Koma gida ba sun tsaya Taya khalfana aikin gida, zee Tace "Khalfana yau fa anan zamu kwana kawaii" Khalfana Farin ciki har da tsalle.

"Dan Allah dagaske zaku kwana"?
Zee Tace "Eh Mana,na Kira gida na Sanar dasu, Zeemah Kuma ta Sanar da Momy"
Khalfana tace
"Zeemah amma Momy Bata gari su Afra they are All alone"

Azeemah Tace "Kar ki damu they can handle it"

Aikin su suka cigaba da yi har sai dab da magrib suka Gama, wanka sukayi sannan sukayi sallah, bayan sun idar suka ci abinci sanan suka shiga d'akin aunty Fatee don su tayata Hira, hirar su suke sosai har uncle ya shigo, Tashi sukayi zasu fita yace
"A'a ku zauna ai yau Dani za a yi hiran" duk suka Fara Hira anayi ana dariya.

Suna cikin hakan ne wayar Khalfana ya Fara ringing tana dubawa taga Mr Unknown, zuciyar ta ne ya shiga duka uku uku, Tashi tayi ta Koma d'akin ta sannan tayi picking, muryar ta na rawa Tace
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikissalam Masoyiya ta dafatan kin wuni Lafiya"?
"Lafiya Lau Alhamdulillah"

"Khalfana Dan Allah kar ki tsorata kinji ni mutum ne kamar ki Kuma wallahi bazan cutar Dake ba, burina shine ki karb'i Soyayya ta Dan Allah"

Khalfana Tace "Mr Unknown, Soyayya da Wanda ban sani ba"?

Murmushi yayi yace "Zaki sanni ki amince plx daga baya Zaki San ko ni waye"

"In Kuma na amince daga baya Kuma naga baka min ba Kuma fa"?

Dariya yayi yace "Insha Allah Zan Miki Khalfana, ki bani Damar shiga Rayuwar ki, na kauda duk wani bakin ciki da kuncin da aka Miki"

"Aka min kana nufin kasan abinda ya faru da ni, kana so kace min kana bibiyata Kenan"?

"Sosai ma Khalfana son da nake Miki ne Sila, na San gidan ku na Gombe harda gidan ku na Abuja, in takaita Miki nasan Yan uwanki duka"

"A Gaskiya ka Fara bani tsoro"


"Haba barrack girl, kina Yar Soja Kuma da tsoro, Zaki sanni Kuma Insha Allah baza kiyi Dana sanin kasancewar ki a tare Dani ba"

"Yanxu me kake so na maka"?

"So nake ki bud'e min kofofin zuciyar ki, ya zama ni ke mulki a cikin fadar zuciyar ki"

Khalfana shiru tayi a ranta tace " Shin amince ko Kar na amince, ban San meyasa naji hankalina ya kwanta dashi ba"

"Hello, hello, Khalfana kina jina kuwa"?

"Sorry me kace"?

"Please accept me as ur lover and I promise you will never ever regret it"

"Toh shkn na amince"

"Nagode sosai Zan shayar da ke da salo na Soyayya daban daban Wanda baki tab'a samun irin sa ba"

Murmushi tayi Tace "Allah yasa"

"Ameen"

Jaan ta da Hira ya shigaya tun Bata amsawa har ta Fara biye masa, Hira suka sha Soyayya yadda kasan kamar sun dad'e da sanin juna, duk da dai yafi watanni 6 Yana tura Mata sakonnin Soyayya.

Zee da zeemah ganin Khalfana taki dawo wa yasa suka Tashi sukayi wa su aunty Fatee Sallama, Khalfana Hira yayi dad'i Bata San sanda su zee suka shigo ba dundu zee ta Kai wa Khalfana, Wani Kara ta sake har Saida ta yarda wayan akan gado, sai da wayar ta katse.

Rai a b'ace Khalfana Tace "Haba zee wannan wani irin abune baki ga waya nake yi ba yanxu duk Karan ihun Nan a kunnen sa"

Zeemah tace "Toh Khalfana anyi new catch Kenan"?
Zee Tace "ga alama Nan "

"Mtwws Dan Allah ni Kar ki sake min haka"

Wayar ta ya Fara ringing har kusan sau 2 Bata d'aga ba, tana ta aikin masifa wa zee Kira na uku tayi picking yace "Lafiya naji d'azu kinyi ihu"?
"Eh Lafiya Lau"
"Ba Lafiya ba kam, ko b'era kika gani ne"?
"Hmm eh

Please Login or Register in order to submit comment