Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaya, Mujeedat na Mujaheed, M²"

Khalfana jin haka yasa ta kware , Khaleel Kuma dariya yake shirinyi ganin Momy na kallon sa yasa yafasa Dariyar.
Dady yace "Kaaai Khausar ba a raba ki da shiririta"

Momy tace "ai ko da had'in Nan zaiyi da nafi kowa Farin ciki Alhaji"
Murmushi kawai yayi.

Khaleel Tashi yayi yace "Momy bari na watsa ruwa naga Lokacin sallah ya gabato"

"Abincin fa"?
"Na koshi"
Momy tab'e baki tayi ta cigaba da cin abincin ta, bayan sun Gama ci Khausar ta rike hannun Khalfana suka haura d'akin ta, alwala sukayi sannan sukayi sallah.

Suna zaune suna Hira kamar sun dad'e da sanin juna.
Kiran wayar Khaleel ne ya shigo wayar Khalfana, tayi picking dariya ya shiga yi yayin da Khalfana shiru kawaii tayi tana sauraron sa sai da yayi Mai isar sa yace "Hello Mi Amor" "hmm ka Gama Dariyar da kake yin ne"?

"Eh na Gama"
"Toh sannu da kokarin"
"My Princess nagode wa Allah da ya bani ke a matsayin Masoyiya ta, Khalfana naji dad'i Sosai, kinga tarbiyan ki Mai kyau ne, shi ya had'a ki da mahaifiyata har ta kwana a gidan Ku,Allah ya Miki Albarka"

"Nagode Sosai Mi Alma, Allah ubangiji ya barmu tare"

"Amiin Matata, a gaskiya kalaman ki suna dad'ad'a min shiyasa kika sace zuciya ta"

"Nima ai ka sace min zuciya, ba zuciya ta kawaii ka sace ba, har da tsinken sokan tsiren zuciya ta yasin da sake mu had'u a kotun masoya"

Dariya ya shiga yayi Sosai sannan yace "Ya mai girma mai shari'a inaso a kori wanna kara domin Wacce take kara ta kasa gabatar da wasu kwakkwarar sheda Nagode ya mai girma Mai shari'a"

Ita ma Dariyar ta shiga yi har da rike ciki, sun dad'e suna Hira suna aika wa zuciyoyin su sakon Ni daban daban, Khausar kallon ta kawaii take, a ranta "Ina ma ace Ya Khaleel zai samu soyayyar Khalfana tana da kirki Sosai"

Muryar Khalfana ne ya katse mata tuankn da take"Khausar Bari na Koma gida Zan shiga school"
"A GSU kike ne"?
"Eh a GSU nake"
"Nima hakan ai Kuma Ina da lectures 4"

Khalfana Tace "Okay to mu wuce kawai"
"Bari nayi wa Momy magana"
"Amma Khausar sai mun biya ta gida na shirya"
"Shiri Kuma me ya Sami kayan jikin naki"?
"Bazan iya shiga school da gyalle ba"

"Lallai Khalfana ke d'in ta dabance"
Murmushi kawai tayi, har d'akin Momy suka shiga suka Mata Sallama sannan suka fice, Duk abubuwan da suke yi Khaleel na kallon su, sai Hamdallah yake yi.

Suna fita motar Khalfana suka nufa, Khausar Tace "Khalfana Motata na wurin gyara"
"Kar ki damu muje kawai" suna tafiya suna Hira har suka Isa gidan su Khalfana, Aunty Fatee suka tarar ita da Yan twins d'inta suna wasa ita Kuma tana kallo, da Sallama suka shiga bayan sun gaisa ta gabatar da Khausar wa Aunty Fatee, Aunty Fatee ta amsa ba yabo ba fallasa.

Khalfana Tace "Khausar Tashi muje kiga d'aki na daga Nan muyi sallar la'asar Kan mu wuce"
"Toh"

Suna shiga Khausar sai yaba kyawun d'akin Khalfana take, bayan sun yi sallah, Khalfana ta kawo musu abinci suka ci sannan suka wuce school, Khausar Tace "Khalfana Ni dai Banda Aure banga dalilin da zai sa nasa Nikab ba"
"Hmm haka ko Khausar kin San shi ra'ayi Riga ce"
"Hakane a Gaskiya Khalfana duk Wanda ya same ki a matsayin Mata tabbas ya Samu aljannar duniya, 'ya'yan sa Kuwa sun Samu Uwa ta gari, surkuwarta ta Samu 'ya ta gari Wacce zata kare mutuncin ta, Khalfana d'azu da kike waya banji dad'i ba sabida naso ace yayana ne zai samu soyayyar ki ba wani ba, Amma duk da hakan Ina Miki fatan Alhairi"

Khalfana tuki take tana murmushi ita dai Khausar mamaki take Bata.

"Ban da ke da abunki Khausar you barely know me, Amma kiji yadda kike ta yabo na har kike so yayan ki ya Aure Ni, kwatakwata bamu fi 6hrs da had'uwa ba fa"

"Ai shi hali zanen dutse ne halayyan ki masu kyau shi ne silar had'uwar mu, Gaskiya Koma wane ne wannan ki fad'a Masa na Miki Miji" Khausar ta karasa maganar ta b'ata fuska.

Khalfana a ranta Tace "Yau naga iyayi"
Sai Tace "Shi Ya Khaleel yace Miki baida Wacce yake sone"?
"Baida shi sabo da yace har yanxu bai ga Wacce ta mishi ba, sai kuma gashi naga sai wani irin kallo yake Miki Kuma wallahi kallon so ne"

"Khausar baki da dama wallahi, A wani department kike ne"?

"Pharmacy nake"
"Masha Allah aji nawa"?
"Aji 3"
"Ai ko Akwai Aminiya a department d'inku, Kila ma kinsan ta"

"Wace ce ya sunan ta"?
"Zainab ana kiranta da zee"
"Chaaapdi na santa haka kawai jinin mu bai had'u da it's ba wallahi"

"Hahahaha ai ko zee tana da dad'in zama da saukin Kai"
"Inaa Ni banga haka ba wallahi"
"Maybe don baku saba bane ba Amma Insha Allah zata burge ki don Wallahi ba ruwanta"

Tab'e baki kawai Khausar tayi, Khalfana Kuma dariya ma Khausar d'in ta Bata, a ranta Tace "Taya za'ayi jinin ki yazo d'aya ita rawar Kai kema haka"

Amma a fili Tace "Khausar mun iso" ta Mika Mata wayar ta "samin numb ki in mun fito sai na maida ke gida ko"?

"Toh nagode" karb'an wayar tayi tasa Mata number sannan tayi wa kanta flashing, fita sukayi ko Wacce ta yi hanyarta.

Karfe 6 suka Gama lectures, Khalfana na fita tarar da zee da Azeemah na jiranta a jikin mota, zee Tace "Yau Ina kika shiga ne yau tun safe baki shigo ba"
"Is a long story,na sama Mana sabuwar qawa"

Azeemah Tace "Toh Khalfana sarkin kwashe kwashe a Ina kika samo ta"?

"Kinga gata tana Kira na" tana picking ta ce "Hello Khausar kin fito"?
"Eh na fito"

"Okay Ina Nan a inda mukayi parking"
"Toh gani Nan zuwa"
Ta katse wayar, Bata b'ata Lokaci ta iso duk su h'udun suka nufi commercial area, abinci suka ci suna Hira, Amma zee Bata fiye sa musu baki ba.

*Bayan Wata d'aya*

Khalfana,Zee, Azeemah da Khausar sun zama qawaye gwanin sha'awa, Khaleel ya Koma bakin aikin sa a Abuja , Khaleel ya nemi auren Khalfana alhamdulillah an bashi aurenta, Daddy da Momy da Kannen Khalfana duk sun dawo gombe, a fad'in Dad yafi so ayi auren Yar a gida, Amma har yanxu Khalfana na tare da Aunty Fatee.
Iyayen Zee Suma sun dawo Gombe.

Maan ya bi Khalfana har ya Soma karaya, ga Yusrah tasa shi a gaba tsiya daban daban take shuka Masa.

Zuwa Yanzu Mama da Khausar sun gane Soyayya Ce tsakanin Khaleel da Khalfana. Mama tayi murna Sosai burinsu ya cika.

Alhamdulillah yau Ne Emmatan duk su 4 suka Gama makaranta, saura bautan kasa NYSC.
Khalfana da Azeemah Bauchi aka tura su, Zee da Khausar Kuma jahar Adamawa d'aki d'aya suke Basu d'au lokaci ba suka zama aminai.

*Bayan sun Gama Bautar kasa*
Khalfana ta Tura wa Ya Maan Sako kamar Haka

```"Ban San ta inda Zan Fara maka zanchen Nan ba Maan Amma Ina so kasan Komai kaddara ce daga Allah kima ba Wanda ya Isa ya chanza. Maganar Gaskiya Akwai Wanda Nake so na aura, kayi hakuri Dan Allah ka nemi wata Allah ya had'a ka da ta gari Wacce zata baka kulawa fiye Dani, nagode da soyayya da kulawar da ka nuna min,Allah ya saka da Alhairi, kasa a ranka Ni Masoyiyar kace har a bada"
```
Tana typing tana zub da hawaye, Ya Maan na ganin sakon ta ya kirata,

"Khalfana na Taya ki murna Sosai, naji dad'i da kika fad'a min Gaskiya Ina Miki fatan Alhairi"
Yana maganar kuka yake yi, Amma kun San zuciyar na miji bai bari ta gane ba

Ita kanta Khalfana shasshekar kuka take, sai ya shiga Bata hakuri, yace "Khalfana tunda kin ki Ni sai ki nema min Mata"

Dariya tayi had'e da kuka
Tace "Ana haka ne dama"?
"Eh ana haka in ma ba'ayi sai mu Fara yanzu"
Tace "Aiko Ina da Wacce Zan baka"

"Dan Allah dai"?
"Allah kuwa sunan ta Khausar kanwar Wanda Zan aura ne, Bari na Tura maka picture d'inta ka gani"
Yace "okay Ina jiran ki"

Tura Masa pic d'in tayi yace "Masha Allah ta had'u Amma fa hakuri zanyi don Wallahi Bata Kai ki ba"

"Maan Hali zaka Duba ba kyau ba, sai ka shirya kaje gidan su"

"Toh Zaki min jagora ko"?

"Ba ka da case Kai Kam, Ina ce maganar aurene"?
"Eh, ai ban fad'a Miki ba na Samu aiki, yanxu Ni lawyer ne Mai zaman kansa"

"Wow na Taya ka murna wallahi fatan Alhairi.
"Nagode"

Wannan kenan

A yau ne aka sa ranar Auren
Khalfana da Khaleel
Zainab da Adam
Azeemah da Dr Abdulazeez
Khausar da Suleiman
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻



Ina kuke duk ku fito muna gaiyatar ku Biki don za a yi bikin Kece raini.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a page a na gaba

*Milhaat ce*💞💞


please comments and share🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*LAST PAGE*

*PAGE* 1️⃣7️⃣5️⃣↔️1️⃣9️⃣0️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Dukka Family 8 shiri akeyi Sosai ta ko Ina

Khalfana da qawayen ta raba IV suke wa Yan Uwa da abokan arziki haka ma mazajen.

Khaleel ya nemi transfer, Ya dawo Gombe.

Zee Tace "Khalfana duk min raba katin wa duk Wanda ya dace, Allah yasa dai bamu Manta kowa ba"

"Munyi mantuwa Akwai inda ya kamata muje"


Khausar Tace "Toh Wallahi Ni bazan yi driving Yanzu ba"

Khalfana Tace "Kar ki damu Ni zanyi"

Azeemah tace "A'a wallahi idan Khalfana Tace Kar a damun Nan Akwai tsiyar da take shukawa don wallahi ban Manta tsiyar da ta shuka mana ba"

Khalfana dariya ta Fara yi tace "haba Zeemah yanzu fa maganar Nan ya kusan 4yrs Amma baki manta ba"

Khausar Tace "ku shafa min inji, me tayi"?

Nan zee ta kwashe labarin abinda Khalfana tayi wa Yusrah.

Khausar Tace "kin min dai dai Matar Yaya kinyi maganin Yar iska, Amma wallahi Zan so ganinta"

Khalfana a ranta tace "haaaa yarinya yanzu Kuwa Zaki ganta"

Tashi sukayi suka fita don dama a gidan su zee suke,motar Khausar suka shiga Khalfana ke jaan motar , Azeemah Kuma na zaune a gefenta , a yayin da Khausar da Zainab suna baya, ana Hira ana shewa.

Ganin kofar gidan da Khalfana tayi parking ne yasa Azeemah fad'in "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Khalfana Nan ba gidan Maan ba"?
Khalfana tsaki ta jaa Tace
"Dan Allah me haka wallahi har kin tsorata Ni me haka haba"
Zee Tace "Khalfana Dan Allah na roke ki, ki rufa Mana asiri Kinga kinci nasara akanta waccan karon, Kuma Kar ki Manta Mummy Tace fa mu daina Shiga Rana , sabida Kar gyaran jikin mu ya lalace"

"Gafara matsoraciyar banza tun last week Muke yawon raba IV baki San muna yawo a Rana ba,sai yanxu"?

"Khalfana Dan Allah kiyi hakuri Kar ki Sa amin illa Adam ya Shiga uku"

Khalfana Tace "zee wallahi babu abunda zanyi ku Tashi mu Shiga ciki yau anan za mu bar motar, Khausar yau Zaki ga Yusrah" ta karasa maganar tana dariya

Sannan Tace "duk kusa Eye glass d'inku Kar ta gane mu, in ta gane mu mun kad'e don ba yanxu ya kamata ta gane ba"

Yadda ta fad'a haka sukayi

Suna kwankwasa gate d'in maigadi ya fito bayan sun gaisa yace
"Bari na Kira muka ita"
Tab'e baki Khalfana tayi,bayan Mai gadin ya tafi Tace
"Irin yanxu Ansa tsaro a gidan" duk sukayi dariya, ba b'ata lokaci Yusrah ta fito Hannu a kugunta tana tauna cingam, kare musu kallo tayi sama da kasa sannan Tace "Malamai daga ina"?
Khalfana ta nuna Zee tace "Sunanta Zainab itace Wacce Adam zai aura" sannan ta nuna Zeemah "Sunanta Azeemah itace Wacce Dr Abdulazeez zai aura, da fatan kin San abokanan mijin naki"

"Oh Allah Sarki bismillah ku shigo"suna Shiga a parlor suka zauna Yusrah da kanta ta kawo musu abun sha,sun d'an tab'a Hira kad'an Khalfana ta zaro IV guda uku, ta mikawa Yusrah, Yusrah ta duba taga tabbas na auren Adam da Dr ne, sai Kuma na Suleiman da Khausar, sai Tace "D'ayan da na waye"?

Sai Khalfana ta nuna Mata Khausar Tace "Nata ne"

"Ke Kuma Ina naki"?
"Allah bai kawo mijin ba tukunna, da fatan Zaki halarci bikin nasu"?

"Eh Insha Allah"

Yusrah tunda Khalfana ta shigo take Mata kallon sani, sai tace
"Amma kamar na San fuskar Nan"
"Eh Zaki iya sani, don da mu akayi bikinki sannan Lokacin da kikayi rashin Lafiya munje har asibiti"
"Oh ayya shiyasa, Allah ya bar zumunci"

Khalfana ta Miki Tace "mu zamu wuce"

"Wai su sauran kurame ne Kece kike ta zuba tun d'azu"?

"Oho musu fa Kila duk kunyar amarcin ne"
Dariya tayi,har gate ta rako su ta Koma ciki abunta.

Zee Tace "Khalfana Khalfana kedai Allah ya shirye ki, meyasa baki Bata IV d'inki ba"?

"Sabida nasan zata nunawa sokon mijinta Ni Kuma na fiso sai yaje ya gani, shiyasa nace muku Kar ku fad'awa Adam da Dr"

Khausar Tace "Khalfana kin Fara goge min hadda"
Azeemah Tace "Ai kad'an ma kika gani Nan ma baki ga yadda ta canza Mata halitta ba"

Tada motar Khalfana tayi suka bar unguwar, wayarta ta d'auka tayi dialing numbi Wanda banji me sukace ba ji nayi tace "Jirani a gun Zan kawo maka kud'in sai na karb'a"

Basu dad'e ba tayi parking Tace Wa su Zee "inazuwa plz " ta fita Bata dad'e ba ta dawo, ta jaa motar gidan su Aunty Fatee suka nufa, Kai tsaye d'akinta suka Shiga

Zee da Khausar suka Shiga d'akin Aunty Fatee, a yayin da Khalfana da Azeemah suna d'akin Khalfana, wani bakar Leda ta mikawa Azeemah, Azeemah Tace "Mene ne wannan"?

"Maganin matsi ne, Da Karin Ni'ima zai maida ke kamar budurwa idan kinyi sa'a Kuma har da jini zai zuba an rubuta yadda zakiyi amfani dashi a jikin"

Azeemah kuka ta shigayi tana yiwa Khalfana godiya.

Tun Ranar Monday Aka Fara occasions
Monday Friends Day
Tuesday Arab Day
Wednesday Bridal Shower
Thursday Qauyawa Day

Adam yace "Zainab tunda aka Fara hidiman bikin mu banga Khalfana ba,lafiya Kuwa"?

"Tana tare da Azeemah ne shiyasa"
Dr yace "Azeemah duk yadda kuke da Khalfana Amma Bata halarci hidiman bikin mu ba lafiya Kuwa"?

"Ai tana tare da Zainb ne, tunda za'ayi Dinner Saturday tare zata halarci dinner d'in"
."okay naji ance Akwai wasu da suka Kama Hall d'in tare za'ayi ko"?

"Eh ai bikin har 4 ma Kenan"
"Allah ya Kai mu"
."Ameen"

Khaleel Dake yasan auren Zainab da Azeemah ake shiyasa bai tambayi dalilin rashin zuwan su ba , sai dai Khausar da Khalfana tare sukayi hidiman su.

Friday aka d'aura Aure, ana d'aura Aure Khaleel ya Kira Khalfana tana picking yace "Alhamdulillah Allah mun gode maka da ka cika Mana burin mu, Koda na mutu yanzu Khalfana ta zama mallaki na, *Matar Aurenah*"

"Dan Allah na roke ka ka daina Kira Mana mutuwa yanzu"
"Amma Babyna kinsan mutuwa dole ko"?
"Na Sani Amma ba yanzu ba sai mun aje kamar yadda aka aje mu Insha Allah"

"Iyee Khalfana yaushe Mika zama Mara kunya haka ban Sani ba, waya b'ata min ke"?

"Ba wani rashin kunya in ma Akwai Wanda ya koya min ta Kaine"

"Da nayi me"?
"Da koyawa zuciya ta soyayyar ka"
"Naji Dad'ina kina ji Dani Sosai"

"Ai wani abun ma sai mun xauna a inuwa d'aya zaga ka Soyayya kalakala don na maka tanadin da Ni kaina ban San adadin su ba"

"Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ‘karuwar farin ciki na ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari. Duk wani abu da zan furta yau a gare ki ba zai wuce, ina Son ki ba, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannan kuma kina d’aya daga cikin mutanen da ba zan ta’ba mantawa da su ba har abada a rayuwata"

"Ba zan iya musalta adadin yadda sonka yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana Ina son ka mijina"
"Nima Ina sonki"
A haka sukayi Sallama cikin fari ciki da kaunar juna.


Saturday aka shirya Dinner,
Adam da Dr ba karamin mamaki sukayi ba ganin sunan Khalfana da wani wai Khaleel sunyi matukar mamaki.

Angwaye da Amare ansha kyau, iya kyau, Khalfana da Khaleel wankan fari da Royal blue sukayi,(Da alama dukka su biyu. Favorite color d'insu kenan🤔) Zee da Adam, wankan black and white, Azeemah da Dr wankan, Purple and white, sannan Khausar da Suleiman wankan red and white sunyi matukar kyau shagali ake Sosai ana shashewa sai ga shigowar Maan da Yursrah.

Maan gani yake kamar idon sa gizo yake Masa kamar Khalfana yake gani, sai da ya matsa kusa da su ya tabbar da Cewa Khalfana ce, tsuman tsaye yayi , Adam duk Hankalinsa na gun Maan don so yake yaga reaction d'in sa. Wuri zuka Samu suka zauna, Khalfana da sauran abokanan cin mushenta dariya suke kasa kasa, MC yace Yana bukatan Amare su fito su taka rawa don nuna irin Farin ciki da suke ciki.

Khalfana ce ta Fara tashi sauran Kuma a biye da ita wakar Umar M Shareef aka sa musu Mai taken share Hawayenki Amarya Share hawayen ki. Angwaye Kuma suka Tashi suna yi wa matayen su liki na dubu dubu.

Maan Ji yake kamar ransa zai fita, bai San sanda ya Tashi ya kashe kayan kid'an ba Hankalin jama'ar gun duk ya Koma Kan sa, ya Fara ihu Yana kuka Yana fad'in "Khalfana kin cuce ni kin cuci Rayuwata, Khalfana me na Miki da Zaki min irin wannan sakaiyar"?

Khaleel yace "kaai kana da hankali Kuwa Matar tawa kake wa magana in my presence"? Cikin tsawa abun ka da jinin Soja har Idon say yayi jawur.

Khalfana Tace "Hubby na barni dashi"
Karasawa tayi inda Maan yake Tace "yanzu Kai sabi da Kai Wawa ne jaki, har Kai ka Isa ka min maganar na cuce ka, Kai har ka Isa ka min magana, Maan ka cutar Dani ka yaudare ni sai da kasa na fad'a tarkon sonka kaje kayi auren ba tare da na Sani ba, Kuma a yanzu kace min na cuce ka"?
"Khalfana ke shaida ce kinsan ina kaun.....?

"Yi min shiru Kar ka kuskara ka furta kalmar so a gareni"
Yursrah Jin wannan kalmar yimin shiru yasa ta d'auki muryar, itace Wacce ta Mata duka.

Da sauri Yusrah ta taso tana nuna Khalfana Tace "Kece kece Kece Wacce kika Shiga har cikin Gidana kika min duka"

Maan kallon Yusrah yake sannan ya maida kallon sa ga Khalfana don Jin me zata ce.
Khalfana tafi ta Shiga yi Tace "Ashe kwakkwalwar ki na jaaa, Toh nice na Dake ki,Kinga wa'anchan" tana nuna zee da Azeemah dasu mukaje"

Maan yace "Khalfana meyasa kika Mata haka"? Cikin muryar kuka
"Gani nayi Kai lusari ne ka kasa controlling gidan ka, amfanin ku ya kare anan" sai ta riko hannun Khaleel Tace "Deee Dan Allah kasa a fita dasu ,bana bukatar ganin su"
Khaleel yace "your Wish is my command" Kiran sojojin da suke waje yayi ya umurce su da su fitar da Yusrah da Maan, Maan sai magiya yake wa Khalfana Amma ko a jikinta.

Adam da Dr Basu ji Dadi ba Amma tsuntsun da ya jira ruwa......

Anyi Biki Lafiya kowa ya watse , ko Wacce ta tare a gidan mijinta.

Ko wani ango ya bud'e amaryasa sabuwa gar a Leda
Abun mamaki harda Azeemah da alama maganin da Khalfana ta Bata yayi aiki, don babu angon da yasha wahala kamar Dr ita kanta Azeemah ta Sha wahala lol🤣🤣

Bayan Wata Tara
Zee Ta haihu ,ta samu 'yarta ta ci sunan Khalfana, Amma ana kiranta da Ameerah.

Bayan haihuwar zee da Wata 2, Azeemah tasamu 'yarta, itama taci sunan Khalfana, suna kiranta da, Islam.

Khalfana tayi murna Sosai sannan ta musu kayan takwara,abin ba a Cewa Komai sai dai ace Masha Allah.
Rana d'aya Khausar suka haihu da Azeemah, Khausar ta haifi d'anta yaci sunan Ya Khaleel.

*Bayan Shekara d'aya*

Allah ya Albarka ci Khalfana da Khaleel da Twins, duka Mata, sunan Zainab da Azeemah suka ci Amma ana Kiran su da Anisa da Anila.

Yusrah ta yarda makaman yakinta, Tana biyayya wa mijinta sannan ta rike 'ya'yan sa tamkar itace ta haife su ana cikin haka ta Samu ciki ta haifi d'a na Miji shi kuma sunan Adam yaci.

Haka rayuwa ta kasance wa duka iyalan cikin Farin ciki.


*THE END*
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️


Alhamdulillah a yaune na kawo karshen Littafina Mai Suna Matar Aurenah.

Ya Allah Nagode maka da ka bani ikon kammala littafin Nan sannan Ina Mika godiya ta ga dukkan mabiya Littafin Matar Aurenah Allah ya bar kauna, Fatana shine Allah ubangiji yasa sakon da na keso na isar ya Isa inda nake so ya je , Yasa kun d'auki darasin da ke cikin ta, dukkan abubuwan da na fad'a ba dai dai Ina rokon Allah ya yafe mana Dani daku baki d'aya.

Ya Allah kayi wa iyeye na Albarka, ka biya musu bukatun su na Alhairi ka kare shi daga sharrin masharranta Dan darajan annabin mu, masoyin mu annabi Muhammad S.A W.

Allah ya bamu qawa kamar zee duk da daai Ina da tawa Ina kaunar ki My Habibty Ummu Khultum Musa Bari, Allah ubangiji Ya bar mu tare, amiin.

Ummun Nana ban Manta Dake ba Allah ya bar Kauna.

Maman Afnan (matar fire) 🔥 Allah ya bar Kauna
Nagode Sosai da shawarwarin da kuka bani, Ina kaunar ku



Mu had'u a Littafina Na gaba
Mai Suna

*Sarah da Saira*
Labarine na Yan biyu masu abun mamaki, labarine Wanda zai nishad'antar daku, ilmantar, ya Kuma kayatar daku, ku cigaba da bibiyana don Jin Wanna sabon labari.

Taku A kullum Fadeelah Yakubu Wacce kuka fi Sani da *Milhaat*

Nagode Ina muku Son So fisabilillah🥰🥰😘😘




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment