Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kara sake Kuka Mai Cin Raina ta dauki 30mints kan ta Fara Bude Ido ta Bude Ido taga Kalfana Na kallon ta tace
"Kalfana plz tell me is not true" ta Fara Kuka sai d'ayan yace "mutuwa aka Muku"?

"Ayya waya rasu"

Tace "yayan mu ne"
Cikin muryan Kuka

"Allah sarki Allah ya jikan raai " "Amin Bari mu fita mu Kira Muku Mai nape" tace to "mun gode"

Tayi tayi zee ta Tashi Amma Ina a take jikinta ta d'au zafi tace "kiani wayar ki"
cikin Kuka ta tmbye " me Kuma zakiyi da wayar" "ki Bani in baza ki bani ba ki sanar Dani" ba musu Kalfana ta mikawa zee wayar ta sai tayi dialling numb Momyn ta tana picking ta Saki Kuka "Mommy Khalyd ya mutu, Khalyd ya tafi ya barni Dama Na fad'a Miki sun kashe Shi"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya rasu " Kalfana ta kwace wayar ta katse sai taga Mommy ta sake tayi picking "hlo Mommy " cikin shesshekar Kuka "Mujeedat, Wai Khalyd ya rasu" Kalfana ta saki Kuka tana toshe bakin ta tace "eh mommy ya rasu" "Allah ya jikan shi" ta katse wayar mommy ita ma mutuwar nan ya tab'a ta sai da ta xubar da kwalla harga Allah Khalyd ya Kwanta Mata a raai Amma Rai yy halinsa yaro yaron kirki kaai Allah yasa mu cika da Imani
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Kalfana sunfi awa d'aya a zube Anan wasu su tmby me ya same su wasu Kuma su wuce ta rasa yanda zatayi gashi nape din Shiru, sai ta d'auki wayar ta tayi dialling numb anas Yana picking tace
"Kaga mahaukaciyar nan tana Kiran zee ta fad'a Mata , ita Kuma ta fad'i"


"Kaai oh My God, Maryam Bata da hankali Na Dade da gane cewar wawiyace,yanxu Kuna Ina"?

"Muna cikin makaranta"

"Ta Ina"?

"Mashigar CS"

"Okay gamunan zuwa"
Zee Dai Kuka yaki ci Taki cinyewa Kalfana Kuma Bata gaji da rarrashin ta ba ana cikin hkn ne sai Taji karar Mota yyi packing a gaban su tana d'ago kai suka had'a Ido da Anas

Yace

"Kalfana Anan Kuka Zauna hba Dan Allah"

"Anas to yazanyi Na kasa d'aga Shine Kawai Nima Na biye mata"

Gigiza kai Kawai yayi ya dauki jakar Zee Mansur Kuma ya dauki jakar Kalfana, Sufyan Kuma ya Karbi wayoyin su suka sa a Mota Amma Ina Kalfana ta kasa d'aga zee da taimakon Anas suka sata a motar Suna Shiga Sufyan ya Jaa motar suka yi hanyar kagarawal, Anan Gidan su zee yk Dake Duk sun San Gidan shys Basu Dade ba suka Isa Suna Isa Kalfana ta rike zee suka fita

Anas yace.

"Naga yamma tayi kina nan ko gida zaki Koma"?

"A'a jirani"
Tasan halin Yan gidan Sarai Suna da Wani irin halin da sai Allah ne Zai Iya musu gashi zuwa yanxu sun San Suleiman Na nemanta a gate din Gidan ta tsaya ta Fara Kiran sunan, Amina da Nana, Suna fitowa suka ganta a zaune a kasa sai suka Fara dariya, Matar baffan nata ta leko Kalfana ta gaisheta ta ansa Sannan tace ita Kuma meyasa meta tk cikawa mutane kunnen"?

Kai a kasa Kalfana tace "Khalyd ne ya rasu" tace "ayya Allah ya jikan sa"

"Amiin" sai ta Mika musu jakar Zee da wayanta , ta matso kusa da ita tace "zee plz kukan ya Isa hk, Sannan ki toshe kunnen ki da Duk Wani abun da zasu ce Miki"

Amina da Nana dariyar Su suka cigaba da Yi ran Kalfana in yayi dubu to ya b'aci ta Tashi ta Shiga motar, a nan ne Amina da Nana suka shigar da ita gida"

Anas yace "Kalfana Amma Yan gidan su Zee Kan su d'aya kuwa ki dubu kiga dariyar ta suke"

"Hmm Anas Manta da su kai Kam"

Kalfana a Ranta cewa take "Anya Zan Iya auran Maan wannan Wani irin family ne" Duk abubuwan da ake Mata agidan zee Bata boyewa Kalfana Basu Dade ba suka Isa kofar Gidan su Kalfana, ta fita ta musu sallama
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Ranar sadakar 3*
Kalfana, Zeee, Azeemah da Maryam sukayi shirya don zuwa Gidan su Khalyd , Anas ta Kira ya musu kwatance , suka tare Mai adai adaita suka ce ya kai su Pantami, Suna Isa unguwar ta Kira Anas yaxo ya kai su Gidan suka gaida mami, Basu Tashi ba sai da suka mishi addu'a Anan ne fa Kalfana ta tabbatar cewa Khalyd ya mutu, Kan su Ankara zee Kuka, mahaifiyar sa Kuka, babban Auntyn su Kuka, Kalfana ta kasa jurewa ita ma kukan take nan Mansur ya Shiga Yi musu nasiha Akan Kuka wa mamaci Amma Kamar ba Da su yk ba
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Sukayi musu sallama Sannan suka fita , Basu fita Daga cikin Gidan ba zee ta suguna ta Bude Sabon Shafin Kuka , Bb Wanda yace Mata komai cikin Kuka tace

"Kalfana Na fad'a Miki kwanaki nayi mafarki Wai Naxo Gidan su Khalyd Ina ta neman sa aka ce yy tafiya Kuma ana taro a Gidan"? Kalfana tace
"Eh kin fad'a Min"..

"Kalfana wannan Gidan Na Gani a mafarki Na, kaico Na Khalyd kace kana da Magana Dani Naki Bari mu had'u, gashi yanzu ka tafi, Nima Insha Allah kwanan nan Zan biyo ka"

Sufyan yace

"Haba Zee sai kace ba musulma ba mu kanmu aboknan sa munyi kukan Munga ba riba mun hkr"

Anas yace "Kalfana calm down ki DaIna kukan nan kukun da kike Yi shys Zee take Kara Shiga tashin hankali"

Maryam da Azeemah suka Nufi inda Zee ta ke suka rikota suka Zauna a taburma sun Dade anan kan suka tafi,
Bayan sun Koma gida, Zee ta cigaba da Kuka, Kalfana tayi wanka ta girka musu macroni ta juye musu a babban plate Amma zee Taki ci, Kalfana ta Zauna a gaban zee ta riko hannayen ta tace..

"Zee, tunda aka sanar da ke mutuwar Khalyd kin Masa addu'a ki da sau d'aya"?

Ta girfiza kai alamun a'a

Tace "kina kaunar Khalyd soyayya d'aya ce ya rage Wanda mu zamuyi Masa shine addu'a,kukan nan da kikeyi zaki Kara Masa azaba ne ,irin kukan da kikeyi ya haramta" sai ta sa hannu ta share Mata hawaye Duk da ita Kanta kukan take sonyi sun Saba da Khalyd Sosai tana Jin mutuwar sa , "zee kimin alkawari baza ki sake Masa irin wannan kukan ba Daga yanxu Zaki Fara Masa addu'a" ta amsa Mata da "Toh" Sannan suka rungumi juna Azeemah da Maryam Yan Kallo suka Zama , suka Fara cin abinci Alhamdulillah zee ta Samu taci abincin Sosai Sabi da Yau kwanan ta 3 Ruwa kawai take Sha
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
A Gidan nasu ba Mai kwantar Mata da hankali Banda dariyar da suke Mata, Wai tana Kuka Akan saurayi ni ko Nace Suma Allah ya had'a si da Na nasu mutuwa akewa isgili😡
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
```Labarin Zee da Khalyd gsky ce , labarin soyayyar kawata ce da saurayin ta Mai Suna Muhammad, Na zabi Na sa Shi a cikin littafina ne sabida akwai Mata dayawa da suke rasa masoyan su Na gsky sai Daga Baya su zo Suna da nasanin```

Har gobe Zee Na nadamar wulakanta Masoyin nata da tayi, sanan Bata dainan kukan rashin sa ba Ni Kaina Ina Muku rubutun nan Kuka nk yi

Plz pray for him Watan sa 6 yanzu da rasuwa😭😭😭😭

*Allah ya jikan ka Muhammad yasa Aljanna ce makomar ka we love you but Allah loves u more, an Maka shaida Na Gari ,shaida Mutane Shi yk bin mutum, Allah ya kai haske kabarin ka we Really miss you* 😭😭😭😭😭😭
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*_CIGABAN LABARI_*

Kalfana Tashi tayi Zauna tana Kuka Maai sauti taka fad'in

"Allah ya jikan ka Khalyd, Allah ya kai haske kabarin ka tana cikin kukan ta sai wayar ta tafara ringing, da sauri tayi picking Kara a kunnen ta Amma Bata ce komai ba

Yace
"Babyna" tace "Na'am"

"Bacci kika fara ne"?
"A'a" cikin murya Kuka

Alhj Maan Dake zaune ya saurin Tashi ya Zauna

"Subhannallah My D Kuka kike"? Me aka Miki"?

Tace "babu " ta sake fashe wa Kuka Tashi yayi ya tsaya hankalin sa yyi matukar Tashi

"Hope Nine silan kukan nan naki ba"?

"A'a ba kai bane"..

"To tell me, me aka Miki"

Tace "Cikina ne ke Min ciwo" cikin muryar shagwab'a

Nan ya Zauna yace "kaaai Amma k ko da kina kusa sai Na cije" sai tayi murmushi yace
" Ya ciwon cikin"?
"Da sauki"
"Dama yana Miki hkn ne "?

"Eh"

"Kodai kodai ne"?

"Kodai kodai me"?

"Karshe wta mana"

Tace "Laaaaaa sai da safe"

Yace "no plz Na Bari"

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

"Babyna Dan Allah kiyi hakuri da abin da Na Miki d'azu sharrin Shaid'an ne"

A zuciyar ta tace "sai mutum ya gama tsula tsiyar sa yace shaid'an"

"My Princess Kinyi shiru ki Dai baki hkra bane"

"Na hkura ya wuce"
Nan suka Fara hirar su
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Washe Gari ta shirya Tsaf tayi breakfast da Noodles (indomie) da shayi ta d'auki Jakarta ta fita ta rufe kofar d'akinta Sannan ta Shiga d'akin Momy sai Taji Azeemah Na Mata Magana Daga kitchen
"Kalfana ki tsaya mu Karya"

Kalfana da tun jiya take cike da haushin ta tace Mata

"Wlh na makara ki bye" sai ta fita ba tare da ta Jira amsarta ba
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a next page

*FadeelahMilhaat* ✍🏻✍🏻✍🏻

Plxxxx comments and share

Matar Aure Nah group invite
👇🏻

https://chat.whatsapp.com/KRSQBsr9JJw6Qe8AzUT9lP

Mata zallah plx🙏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 2️⃣7️⃣↔️3️⃣0️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana tun jiya take cike da haushin Azeemah

"Wlh Na makara bye" sai ta fita ba tare da Jira amsarta ba

Azeemah tace "Hmmm yarinya in kin San wata baki San wata, ke in an barki ke ustaziya ce ko, to wlh sai Na Mai da ke karuwar gida" ta cigaba da aikin ta.....

Zee da Kalfana Suna had'uwa a makaranta Kamar kullum Wani lokacin Kuma su zo Gidan su Kalfana suyi sallah Sannan suci abinci, Alhj Maan da Kalfana sun shaku acikin sati 2 Kuma kullum sai yazo Hira, Maan (Yayan Zee) yaga canji sosai a gun Kalfana ta DaIna bashi kulawa Kamar yadda take yi da, hankalin sa yayi mugun Tashi sabida Yana matukar kaunar ta Amma tana nema ta Karya alkawarin da ta d'auka.......
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Wannan Kenan*
Kamar kullum Yau Maan yashirya Tsaf yayi hanyar zuwa Ganin masoyiyar sa, fararen Shadda yasa ,da Bakar hula sanan yasa Bakar Takalmi yayi matukar kyau, Sannan ya Kira ta ya Sanar da ita Yana hanya ta amsa da to ta Shiga wanka ta sa farin material Riga da skirt ta daura dankwalin kayan , Sanan ta yafa Bakar gyalle ta sa bakin Takalmi da bakin wrist watch, light make up tayi , tayi kyau sosai ta feshe jikinta da turare, ta dauki wayarta ta fito ta Shiga parlour gun su Momy , tana Shiga parlour ya gwaraya da kamshin tiraren ta, tana Shiga Momy tace
"Mujeedat irin wannan kyau haka, Maan yazo knn"? Tayi murmushi Sannan tace "eh"
"Dakyau Dama Ina so Na baki shawara Kinga mutumin nan ki rike Shi hannu 2, Kinga Mai kudi ne Zai d'auke Miki dukkan nauyin ki, kingane ko"? "Eh Na gane Momy Amma Nifa ba Ruwana da kud'insa" "Kinga matslaa ta Dake knn, ke Wai baza ki waye bane"? , Kuma mutumin nan Daga Ganin sa Yana da Mata" Kalfana tace "Momy Mata Kuma kai da Kamar wuya" "ki Karbi Wayan sa in kiga pic Na Yara to Yana da Mata" "Amma Momy kulkum fa sai yazo, Kuma mukan raba dare Muna ways" "it doesn't matter my dear ki dai bincika" Kan ta am sai suka ji sallaman Azeemah Duk suka amsa, sai ta Zauna kusa da Kalfana ,tace "Kalfana akwai gist fa" tace "Allah ko,Bani insha......
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Akwai Wani abokin Bashir yaga Hoton ki a status Dina yace Yana sonki , sanan gobe zasu zo" Kalfana tun da Azeemah ta Fara maganar Taji ta Fara b'ata Mata raaai

"Azeemah tace Kinyi shiru"?
"Toh Ni Kuma mezance miiki"?
Momy tace "Mujeedat ba a Zama da saurayi d'aya fa" "Hmm Momy knn Ni da ba Aure zanyi yanzu ba me amfanin Tara samarin, Maan din ma wlh nacin sa ne yy yawa Har ya sa Na Saba dashi"

Nan wayar ta ya Fara ringing Tana dubawa taga Hubbyn ta ne, Bata Yi picking ba ta Tashi tace "Momy bari nazo" Azeemah tace "plz in kika shigo Ina da Magana Dake" "okay to"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana fita ta Nufi inda yk ta Shiga motar sanan ta Masa sallama suka gaisa to her surprise sai taaga sun sa Kaya matching colours, Shima kallon kayan jikinta yk, yace "Waye yace ki sa Kayan nan" "Wa kuwa Zai ce Min, zuciya ta man" " Naji Dadi sosai zuciyoyin mu sun shaku" tace "Tabbas" tana dariya nan suka Fara Hira sun Dade Suna Shan hirar soyayyar su Sannan yace Mata "My princess in Allah ya kai mu gobe zanyi tafiya" tace "tafiya Kuma, xuwa Ina"? Yace "Anambra State, Akwai shagon mu a wurin so Na Kwana 2 banje ba zanje Naga ya abubuwa suke tafiya achan" "yaushe Kuma zaka dawo"? "Ina ga Zan kai 1week" "Allah ya kai mu" murya a Sanyaye " look Babyna Kar ki damu kinji in fa bakya so Zan fasa"? "A'a Ni bance ba, kana nufin in muka Yi auren ma Hk xaka Rika tafiya hk"? "In ta kama hkn zanyi man" " chaaapdi Aiko da sake" yayi dariya sosai sai da yy Mai isar sa yace "kin bala'in Bani dariya"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Sai ta turo baki "Ni ka Daina Min dariya" cikin muryar shagwab'a" Shi ko shagala yy da kallon ta da ta lura da lips dinta yk Kallo sai ta rufe fuskarta da gyallenn da yafa a kafad'ar ta , nan ne ya dawo hayyacinsa yace "Amarya ta, Amarya ta d'an Bude fuskar mana" ta d'aga kafad'ar ta alamun naki, sai yayi murmushi, tace "Muga wayar ka"? "Wayata Kuma me zakiyi da ita"? "Picx Zan kalla" "Babyna sai hotunan shinkafa Amma dai gashi" ya Mika Mata Sannan ya fad'a Mata password din tana budewa taga pic dinta a ne gaban wayar sa taji dadi sosai hkn ya tabbar Mata da cewa Bai da Mata sai taji hankalin ta ya kwanta, nan ta Fara kallon pics din Kuma hkn ne pics din shinkafa ta Gani sai hotunan gidaje, Har ta iso Kan Hoton ta sai ya Ce "Kinga wanannn Hoton kyau yk Min sosai Kinyi kama da sabuwar Amarya, musamman lallen hannun ki inason lalle sosai"
Murmushi Kawai tayi Bayan ta gama kallon picx din ta Mika Masa wayar sa ya karb'a yasa a aljihun rigar sa ,
"Babyna Zan tafi sai munyi waya" sai Taji ba Dadi ta amsa da "Toh"
"Babyna Na lura in Na Miki maganar tafiya ta Duk sai yanayin ki ya sauya" ,Na fasa tafiyar"
"A a Kayi tafiyar ka" yace sai Kinyi murmushi sunkuyar da kanta Kawai tayi yace "Babu wata matslaa ko"? "Eh babu" "baki fahimce Ni ba, babu Wani abinda kike bukata"? Tace "Eh babu" "Hmmm matsalaar kud'i fa nk Nufi" "Ni Bani da matsalaar komai" "Na lura Dake kina da kyaliya , Amma ba komai ban acct numb ki" "A'a ba sai Na Baka ba" yce "Toh shkn, Ina wayar ki ne"? Tace "gata" ta Mika Masa yace "pin" sai tasa thump dinta ta cire, nan ya Shiga contact list dinta ya duba ya ga My Acct Numb sai ya d'auka yasa a a wayar sa Sanan ya Mika Mata wayarta,
"My princess Ina so Na bude sabon acct, a Wani banki ya dace Na Bude" tace "Wanda Kk so"? "Inda kika da acct nl so a Wani banki ne"? Tace "Ecobank"
"Alright Amma savings kika Bude ko"? " Eh savings ne"
Sai Taji Karan msg a wayar ta tana dubawa taga Bank alert Na 100k abin ya Bata mamaki da taga sunan Suleiman Baba Suleiman, tace "Hmm kai gaka Mai wayo ko"? "Toh Gani nayi nema kike ki wahalar Dani" tace "Nagode Allah ya Kara bud'i" "Amin Amma Kar ki Kara yimin godiya babu godiya tsakanin Mata da miji" tace "Toh yallabai" ta kasa fatan Allah ya kiyaye hanya sanan ta Shiga gida
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana Shiga ta tarar da Azeemah a kwance a d'akinta tace "Azeemah Ashe kin shigo"? "Eh wlh jiranki nake" "da alama maganar nan Mai muhimmanci knn" tana Magana ta yaye gyallenn ta sai ta Zauna a Kan kushin, Azeemah CE ta matso kusa da Kalfana sai ta riko hannayen ta tace "Kalfana plz am really sorry, plz forgive me da abun da Na Miki ranar, Na Saba da rayuwa da Maza Wanda Idan nayi Kwana 2 ba tare da Na Miji ya kusance Ni ba, Bana Jin dadi, Na d'auka kema irina ce , Amma sai Naga akasin hkn"
Kalfana tunda Azeemah ta Fara Magana take kallon ta tasan cewa maganar nan Duk Karya Ce "Amma Bari Na bita a haka" a zuciyar ta sai tace "shkn Azeemah, Na hkra but plz kiji tsoron Allah ki sani kina cin Amanar mijinki, da Na 'yan'yanki, sanan kin muhafurci addininki, Allah ya shirye mu yasa mana tsoron sa a zukatan mu" ta amsa da Amin nan suka Ci gaba da hirar su, Amma Azeemah a Ranta cewa take "sai kin gane baki da wayo Allah ya kai mu gobe"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan sun gama hirar su ta Hau online tana chat sai Taga Anas ya Mata Magana nan suka Fara chat tun Bayan rasuwar Khalyd Kalfana ta Fara Kula Anas, yakan Kira ta Har Gidan su yk zuwa su Sha Hira, tana cikin chat da Anas Sai Alhj Maan ya kirata ya Sanar da ita ya Isa gida lfy suka Sha hirar su ta Masa fatan Allah ya kiyaye hanya ya katse wayar, sai Azeemah tace zaiyi tafiya ne"? "Eh" Azeemah tace "Alhamdulillah ya cika naci wlh" Mujeedat ta Tashi ta Zauna tace "Duk nacin sa Bai kai wanchan Dan iskan saurayin nan naki ba"
"Wanne knn fa"?
"Aww Zeemah Ai Na Manta samarin nakin Allah yy su dayawa, KumaDuk Yan iska ne"?
"Kuttmelessi Kalfana Amma wlh ban da Tanko"

"Wani Tanko knn"
"Tk mana d'aya Wanda kika sani"
"Mtwwww wanchan Dan iskan ai wlh Karuwan Na Miji ne Shi" ran Zeemah ya b'aci sosai Amma Sabi da akwai abin take Shirin Yi in ta biye wa Kalfana Duk sai ransu ya b'aci
"Hmmm Kalfana knn me hujjan ki"? Hujjana shine ranar Naga iskanci da rashin kunayar da kukayi a Motan sa"
"Innalillahi Kalfana abin naki ma sharri kika Fara yi"? Tana yarfa hannu
"Sharri Kuka ke kinsan wlh Kinyi kad'an Na Miki sharri da idanuwa Na ganku babu Riga a jikin ki"
"Shegiya Kalfana ai ban ganki ba" "laaaaaa laaaa Kul Kul Kar ki sake cemin shegiya Bana so ehe, in ba Haka ba Rai Zai b'aci" Zeemah dariya Kawai ta Mata
Sai ta canxa hirar Suka Yi ta Hira ranar a d'akin Kalfana Zeemah ta Kwana
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*Washe Gari*

Kalfana ta Tashi da ciwon kai, hancin ta ya toshe, muryarta Bata fita in zata Yi magana Ga zazzabi Mai zafi, a ranaar Bata Shiga makaranta ba, tunda suka gaisa da Daddy , Bata sake waiwayar wayar ta ba sai da Ya Maan ya kirata Jin muryarta hka yaji tausayi ta sosai yy Mata fatan Allah ya Bata lfy, Alhj Maan Har ya Isa Airport Kan ya kirata ya Sanar da ita karfe 10 zasu Tashi yaji muryar ta ya canxa hankalin sa yayi mugun tashi Har yaji Kamar ya fasa tafiyar Amma bazaiyu ba sabida tare da babban yayansa Mai suna Aliyu zasu Yi tafiyar Amma a ransa bazai kai Satin ba princess Dinsa ba lfy.......

Momy Ce ta sa Afra da Afnan suka sayo Mata maganin Mura Tasha tun da ta Sha take ta bacci Har sai karfe 4 Shima din ma don zee ta shigo ne ta Sanar da Ita Mahir yazo ya gaishe ta da jiki hkn yasa ta fito kofar gida don su gaisa Mahir Dan ajin su ne tun Suna Rabin ajin Na Jami'a (Remedial) su ukun sun shaku sosai Amma da suka Shiga Aji d'aya sai suka rabi sabida Kowa da department Dinsa Kalfana Medicine, Zee Pharmacy, Mahir Computer science, Mahir ya ha'du Iya had'uwa gashi da son mutane Shi kadai Kalfana ta kulla Abota dashi, ba kamaar Zeee ba ita Kowa ma kulashi take Yi
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Suna zaune su ukun Suna Hira sai Ga dawo war Momy Daga kasuwa a adaidaita, Duk suka gaishe ta, ita Kuma Momy Mahir take Kallo bud'an bakin ta "wannan fa hulan baban sa yasa ne, Kuma motar nan ba nashi bane ko"? Kalfana Duk takaici ya isheta Taji Kamar ta nitse kasa, Zee Kuma haushin ta Taji Duk babu Wanda ya Amsa Mata sai ta shige tana tsaki, tana shige Kalfana tace "Mahir am very sorry....." Ya d'aga Mata hannu Kar ki damu, Zan tafi" sai ya miko Mata wata Leda tace "Mene ne"? "Ke Dai ki karb'a mana" ta karb'a ta Masa godiya ya shige motar sa ya tafi, zee kasa magana tayi Yana tafiya tace "Kalfana kin sake wa Matar nan dayawa, ya za'ayi ta Yi disrespecting bakonki"? "Zee kema kin San....." "Nasan me Kalfana wlh tun wuri ki taka Mata birki Mata babu abinda ta Iya sai gulma da sa Ido mtssw" tana kad'a kafa Kalfana tayi murmushi ta riko hannun ta tace "mu Shiga Ciki plz ki daina b'ata ranki akanta" "Kalfana kodai tsorata kike Ji ne"? "a a ko kad'an Kar ki Manta ta haifeni fa"? "Yaushe ta haife ki"? "kaaai zee ki Rika daukan Abu da sauki plz" "Bazan Yi dinba" ta fizge hannun ta ta Shiga cikin Gida Kalfana Kam dariya tayi sananan tana Ji da ciwon Kan da ya dame ta, tana Shiga ta tarar dasu sun shimfid'a taburma , Zeemah da zee da Momy, ita ma Zaman tayi ta aje ledar da Mahir ya Bata Momy tayi sauri ta d'auka ta Bude sai ta Fara wage baki tana dariya tace "kaai madallah Ashe d'an arziki ne" Kaji me gassassu dasu yoghurt"ta umurci Zeemah ta dauko plates da cups sai hau ci ta dad'e tana ci Kan tayi musu Bismillah Kalfana tace ta Koshi , zee tace baxa ta ci ba ta Tashi ta Shiga da'ki Kalfana tabi bayanta..
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana tace "Zee lfy" "Oho ban sani ba, tafiya zanyi Bazan Iya kallon kayan takaicin nan ba" ta d'auki Jakarta ta fita da kamar Kar ta musu Magana sai tace "Momy sai da safe" dakyar Momy ta Amsa sabida ta cika bakinta da nama.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana tace

"Zeee tsaya mana Na Miki rakiya"
"A'a barshi, baki da lafiya ta fita "

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*_At Night_*
Azeemah Allah , Allah take dare tayi gashi tayi tashiga d'akin Kalfana ta Samu ta idar da sallar Isha tana zaune a Kan sallaya tana waya tana cikin farinciki sosai, Zeemah ji tayi Wani Abu ya soke ta a kirjinta, in akwai abinda Bata son Gani to farin cikin Kalfana ne ta Samu wuri ta Zauna Har sai da Kalfana ta Gama ways da Maan, Zeemah tace "Kalfana Bashir fa Suna hanya"
Kalfana tace
"Waye Kuma Bashir"?
"Hmm Harkin Manta Bashir saurayin d'an hajiya"
"Oh Na mance ai"
"Toh Na tinatar dake Tashi ki shirya"
"Me Zan shirya yadda kika ganni hka a HK Zan fita"
"Haba Kalfana jiya fa da Maan Zai zo kwalliya kika masa Na musamman" Rai a b'ace
"Toh Zeemah kema fa Maan kika Ce" Kan Zeemah ta Amsa saiga shigowar Kiran Bashir, tace "Kalfana Tashi mu fita" Suna fita suka Shiga mota Bayan sun gaisa Sai Bashir ya tada Mota, Kalfana tace "Ha'ah Ina Zamu Kuma"? Bashir yace "Outing,Babyna baki fad'a Mata bane"? Yana tmbyr Zeemah ta Ce "eh wlh Na Manta, am sorry Kalfana" Bata Ce Mata komai ba suka five Daga unguwar Wani wurin da ake sayar roasted Fish suka je s, Zeemah da Bashir ne a gaba sai Kalfana da abokin Bashir mai Suna Faisal a Baya suna Saya suka bar wurin, Wani makeken gida suka nufa da motar Kalfana Duk hankalin ta Tashi gashi Haryanxu zazzabi take Ji gashi sun kawo ta Wani gida unguwar ma shiru ita Kanta Bata San Wani unguwa bane nan , Faisal ne ya fita ya Bude gate din Sanan Bashir ya shiga yy parking Gidan babbane sosai gashi shiru alamun ba Kowa, Kalfana kirjinta ya Fara bugawa uku uku,

Please Login or Register in order to submit comment