Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar tab'a haihuwa ba sai dai tayi sa'a mijin ta na mutukar sonta haka ma dangin sa musamman mahaifiyar sa, duk da Kun San baza a rasa wa'anda basically sonta ba, (Kun San wasu dangin Mijin acikin 100% 99.9% hatred a jinin su yake nayi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️).

*Cigaban labari*

Bayan ta shirya ta d'auki Jakarta ta sauka kasa, kan ta Kara said dinining taji Aunty Fatee na waya tana dariya, tana fad'in "haba Daddy is kwantar da hankalin ka kalfana tana gida na Kuma baza ta koma ba sai bayan ta Gama exams d'inta " daga d'ayan bangaren Naji ana Cewa "Hakan yayi kinga hankalinta zaifi kwanciya anan, Ina take har yanxu bacci take ko?" "A'a ta tashi itace ma ta had'a Mana breakfast ta shiga wanka tana.......aww gata Nan ma ta fito" karb'an wayan tayi suka gaisa kamar yadda suka saba, suka gaisa da su Momy da Kannen ta bayan sun Gama ta katse wayar, har kasa ta durkusa ta gaida Uncle da Auntyn ta, Nan suka fara ci abinci, aunty Fatee cikin sauri ta d'auki makullin motar ta ta fita don ta kusa ta makara, Uncle babban Business man ne in bai Zo a na 2 ba tabbas zai Zo na 3 a cikin manyan Yan kasuwan gombe, bayan kalfana ta tattara kayan abinci hijab d'in ta tasa Uncle "Muje nayi dropping dinki" ta amsa da "To".

Suna tafiya suna Hira har cikin makaranta ya aje ta kan ya fito ya nufi shagon sa.

Lectures sukayi har 6pm kamar yadda suka saba tare suka fita da Zee suka tari a dai daita sukayi dropping d'in kalfana a Tudun Wada sannan aka wuce da Zee kagarawal.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Haka rayuwa ta kasance wa kalfana a gidan Aunty Fatee tana cikin farin ciki Kuma ta maida hankali Alan karatunta, Alhj Maan Kuma ko kad'an Bata nuna masa tasan sirrin da yake b'oye Mata ba, yakan Zo su had'u a makaranta lokaci zuwa lokaci, Sani Ibrahim sun zama frnds sosai yasan komai a kanta zuwa yanxu yasan soyayyace a tsakanin su, Maan da ya Lura da haka hankalinsa ya kasa kwanciya tabbas yasan wataran sani zai fad'a Mata dole ya nemi mafita.

Yau kwanaki uku knn baya Kula ta baya kiranta ko text ta tura masa baya Mata reply haka a WhatsApp bazai bud'e ba.

Tana kwance taga ya hau online yafi minti 30,cikin b'acin raai ta tura masa sako kamar haka "Wanna wani irin wulakanci ne Ina ta binka ka ki kulani, Shikenan in dai ni Yar halakce bazan sake kula ka ba.

Yana ganin sakon yayi saurin kiranta ya dad'e Yana Kira Bata d'aga ba sai da ya Kira kusan sau 5 ta d'aga da Sallama "Babyna wai me ke faruwane?" "Babu" "ya Zaki ce babu kince Shikenan a nufin ki mun rabu kenan?" "Eh Mana mun rabu" "Wallahi baki Isa ba" "Ban Isa ba kace to Zan nuna maka na Isa" zata kashe wayar yace "Dakata Babyna please karki kashe wayar" "Toh me Zan maka?" "Babyna ai tambaya ta zaki yi" "wani tambaya bayan Wanda na maka?" "Toh kiyi hakuri, Amma maganar gaskiya in fushi dake" "Da nayi me?" "Waye Sani Ibrahim?" "Friend d'ina a Facebook " "Shiyasa kika fad'a masa komai naki hattta makarantar da kike?" "Ai wannan ba sabon abu bane ba" "Haka ne to bana so kina kulashi" "Kawaii?? shine kawaii kake so?" "Eh shine kawaii" "Indai hakane Facebook d'in ma Zan goge" yace "Allah yasa" Nan suka fara hirar su, suna Gama wayar ta goge Facebook d'in ta.

bayan Yan kwanaki ya Sanar da ita ya tab'a aure Kuma Yana da Yara 2 haneef da Haneefah ta nuna masa Bata damu da Hakan ba har ta nemi ya kawo Mata su Hakan kuwa akayi yayi mamaki sosai sam baiyi tunanin zata so 'ya 'yan sa ba.

Wannan kenan
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Alhamdulilah Yau su Kalfana suka kammala second semester exam, zee da Adam an musu baiko, Azeemah da Abdulazeez Dady ya shiga maganar su like zuwa yanxu ta Gama TP d'in ta, har ta fara neman admission a GSU, kalfana tunda take ta d'auki hijabanta a gidan su Momy Bata sake komawa ba, Kalfana da Zainab Shirin komawa gida suke yi don an Basu hutun wata 1, kamar da wasa ta hau WhatsApp sai taga Maan yayi blocking d'inta , dubawa tayi da kyau don ta gane ma idon ta ko gizo ne amma Hakan ne da gaske Maan yayi blocking d'in ta, kiranshi ta shiga you a waya Amma yayi rejecting daga bisani ya kashe wayar, kalfana taci kuka sosai har hawayen sun kafe, yafi sati bai kirata ba Kuma baiyi unblocking ba, abin ya dame ta ta rasa wadda zata fad'awa damuwata, tashi tayi ta shiga d'akin Aunty Fatee tayi sa'a uncle baya Nan, Aunty Fatee hankali linta yayi mugun tashi ganin kalfana a haka, "me ya same ki mutuwa akayi?" Kasa amsawa tayi kuka ta fara yi Mara sauti hawaye Kuma kamar ankunna fanfo, Aunty Fatee kyale ta tayi sai da tayi Mai isar ta sannan tace "Aunty Suleiman ya daina kula ni, har blocking Dina yayi a WhatsApp" ta karasa maganar cikin kuka "blocking d'in ki Kuma have kila mistake yayi" "Aunty wallahi ba mistake bane, yau sati d'aya" "Haa'ah ko laifi kika masa" "Haba Aunty laifi Kuma shine zaiyi blocking d'ina dama ba so na yake ba , Allah ya Isa bazan yafe ba" "A'a kar ki ce haka daina kukan ,bani number saved shi Kuma ya zaiyi haka tun ranar da yazo ya gaishe ni Naji ya shiga Raina, Ban number" karanto numb ta shiga yi Mata, duka d'aya ya d'aga da Sallama Aunty Fatee ta amsa sannan tace "Aunty Fatee ne Yar uwar Kalfana" "Aunty Ina wuni?" "Lafiya ya aiki" "Alhamdulilah" Ina so nayi magana da kai in da Hali" "Okay bari na Kira ki" bayan ya kirata aunty Fatee take Tambayar sa "me yake faruwane" "Aunty bakomai kawaii naga Bata da niyar aure yanzu Kuma ni gaskiya bazan iya jiranta har tsawon shekara uku ba, in ta yadda ni Mai aurenta ne Amma fa idan zata shigo a Matata ta biyu" "Yanzu dai ka bani lokaci zanyi wa Mahaifinta magana" "A'a ba sai kinyi ba don lokaci ya kure" "lokaci ya kure aure zakayi Kenan?" "Eh to bazan ce gashi ba, don ita da kanta tace min in Zan cutar da Kai na nayi aure kawaii to meyasa zata tashi hankalinta?" "Ba dole ba ka cusa wa yarinya sonka ka daina kulata Kuma kace kar ta damu, ai da sai ka fad'a Mata ba kayi shiru ba zaka karya Mata xuciya" "haka ne nasan ban kyauta ba Zan kirata Insha Allah".
Aunty Fatee ta shiga rarrashinta da kyar ta samu ta yi shiru tashi tayi ta shiga d'aki ta yi wanka ta kwanta Amma bacci yaki d'aukan ta datan ta bude Taki WhatsApp d'in ma ba dad'i , a fill tace "mtwss bari na bude Facebook d'ina" play store ta shiga tayi downloading app d'in Facebook , ta seta komai ta fara chat d'inta Sani ibrahim na ganinta ya Mata maga am a network ya Hana su chat number ta, ta aje masa sai ta kashe datan ta , Yana ganin number ya kirata bayan sun Gama gaisawa yace "lafiya kin b'uya kwana 2?" "Eh wallahi , kasan bokon ne sai a hankali" "haka ne yau kamar Kun had'a baki da mutumin naki" "Meyasa kace haka?" "Ai Maan yafi wata baya nema na ko na mishi magana baya kulani" "subhannallah Meyasa" "sai Allah a tunani ne Alan ki ne don ya min warning na fita harkar ki" murmushin takaici tayi sannan tace "Allah ya shiryi Maan"ya amsa da "Amin".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tashi tayi don yin sallar isha , bayan ta idar ta sauka kasa ta samu su uncle suna kallo a parlor ta zauna Kenan sai ga call d'in Maan tashi tayi ta Koma d'akin ta, bayan sun gaisa ya shifa Bata hakuri, ta hakura sannan ya tabbatar Mata da cewa "Insha Kalfana nine mijin ki, Amma fa in Zaki auri Mai Mata" Shiru tayi yace "Kinyi shiru" "Hmm Allah ya tabbatar da alhairi" "Amiin" suka yi ta Hira Amma kalfana duk Taki sakin jikin ta suyi Hira kamar yadda suka saba, hakura yayi ya Mata sai da safe, Yana katse wayar ta bud'e data sai taga message d'in Sani a WhatsApp tana bud'e wa taga message kamar haka "Ashe Kiran da mutumin ki ya Kira ni IV ya turo min Alan na Zo na Karb'a na rabawa abokanan mu" zaro ido tayi ta dafe kirjin ta ta ce masa "IV kamar ya IV?" "Invitation card nake so nufi" "Allah Sarki har an sa auren nasa Kenan" "kamarya auren sa, ba dake za a yi auren ba?" "A'a ba Dani ba ce" "Naga ya turo min bari na tura miki ki gani" bayan ya turo Mata taga tabbas Auren Suleiman ne da Wata Wai Yusrah Hassan. Kalfana kasa motsi tayi want message d'in Sani ya sake shigowa "Yace fa kar na tura Miki sannan Kuma kar a sa a social Media" "To Meyasa yace make haka?" "Kila Yana so ya fad'a Miki da kansa ne" "Amma fa d'azu mukayi waya" "kar ki damu zai fad'a Miki" "To nagode".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
(Chakwakiya Yau ake yinta Maan da Aure ba Kuma ba kalfana zai aura ba)😭

Mom Arpat
Ummu Haneefah
Baby Haruna
My Salma
me zaku ce Maan fa yaci amanar Kalfanan ku😭😭😭😭

*Mu had'u a page na gaba*

*Daga Alkalamin Fadeelah Yakubu* (💞 *Milhaart* 💞)

Plz comments and share🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻.
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣1️⃣5️⃣↔️1️⃣2️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana takaicin duniya ta ishe ta, ta ma rasa me zatayi don har kukan ma ta kasa,Ban d'aki ta shiga tayi alwala sannan ta fara jero nafiloli tafi awa 2 sai jero su kawaii take bayan ta idar ta fara jero addu'o'i kamar haka "Ya Allah na roke ga bawan ka Nan nasan a iya xama na dashi ban cutar dashi ba, na so shi so na hakika, Amma ya cutar Dani ya yaudare ni ya Allah ka Masa abin da ya min" cikin kuka ta karasa addu'an nata, kalfana duk sanda tayi sallah sai ta jaa Masa Allah ya Isa da tsinuwa.


Rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya yau an d'aura auren *Suleiman* Da *Yusrah* , (Allah ya bada zaman Lafiya)😒😔.

Zainab da Adam
Azeemah da Abdulazeez soyayya suke Sha ba kakkautawa.

Zainab hankalin ta yayi mugun tashi jin Maan yayi Aure tunanin halin da masoyiyar ta ke ciki ne ya Kara tada Mata hankali, Kiran Azeemah tayi a waya a kan su shirya suje gidan Aunty Fatee, anyi sa'a Momy bata Hana ta ba Hakan yasa sukayi Mata zuwan ba zata, tana kwance a d'aki taji Aunty Fatee na kiranta jiki ba kwari ta sauko, tana saukowa taga zainab da Azeemah da gudu ta karasa inda suke, rungumar juna sukayi a tare, Aunty Fatee murmushi kawaii take yi, kalfana jaan su tayi suka Koma d'akin ta Nan suka shiga Hira Amma Zainab wani irin kallo take yi wa kalfana, kalfana da ta Lura da Hakan tace "Ke ya da kallo haka bashi ko Tara"?
Ajiyar xuciya tayi sannan tace "Kalfana Ashe Maan zaiyi Aure shine ko ki Sanar damu" "Zee Kenan to me zance muku Dan Allah,Aure dai yau za a d'aura ko ince an d'aura tunda karfe 10 na safe akace za a d'aura"

Azeemah tace "Kalfana wallahi na ji Miki haushi Ashe Maan mayaudari ne ban sani ba" Zainab tace "Kalfana kiyi hakuri duk mu muka jaa Miki da ace ba muyi convincing d'inki ba na tabbata baza ki amince ba Sabi da Tara samari ba halin ki bane, kalfana na fara tunanin ko haka Adam yake"

"A'a Zee Taya za'a yi halin su yazo d'aya"?
"
Azeemah tace "Please ask her na fad'a Mata haka tun a napep but she refused to listen"
Kalfana tace "Zee kar ki damu ku cigaba da soyayyar ku, Allah ya kaddara ta dalilin Maan Zaki had'u da Adam, Azeemah Kuma ta dalilin Rashin lafiyar ta suka had'u da Dr,So kar ki damu na d'auki wannan a matsayin kaddarata"

Zainab tace "Shikenan kalfana tunda kince haka, Amma wace ce ya aura"?

"Wata Wai Mai suna Yusrah, a manawachi take"

Azeemah tace "Anya baza muje wurin bikin Nan ba"

Kalfana tace "Muje Muyi me, baza a yi komai ba, Amma Kun San me, ranar da mukayi waya na karshe ya tabbatar da min da cewar satin su 2 da had'uwa,Amma bai fad'a min exact date d'in bikin ba shine abin da ya fi b'ata min raai"

Azeemah tace "Nifa wallahi ban yarda da zancen Nan ba ta ya za'a yi yace in 2 weeks suka had'u Kuma a d'aura aure in 2 weeks, da Wata a ka sa"

Zainab tace "Nima nayi tunanin hakan, Amma kalfana Maan ya nuna Miki duk wato so da kauna, nafi tunanin don ya ga ba yanxu Zaki yi Aure bane yasa yaje yayi auren sa, kuma ke ma da na ki waya fad'a Miki a na bawa na miji go and head da maganar Aure"?

"Zee Kenan ai gara yayi auren nasa da yazo ya lalata ni, zuwa yanzu soyayyar da nake yi Masa yayi yawa anything can happened, duk abinda yace min nayi Zan yi ko da Kuwa bana so"

Zee tace "kema kince wani Abu"

Muryar Aunty Fatee suka ji tana fad'in " Ko Kuma already Yana da wacce zai aura ba,ganin ki da yayi yasa yaga kece irin Matar da yake so ya aura sai ya canza shawara da yaga bazai samu damar auren ki ba ya Koma mata, Amma ta Yaya za a ce daga had'uwa haba"

Azeemah tace "Aunty gane min hanya sai dai fa idan iyayen ta basu son ta ai ko auren bazawara iya ka"

Kalfana tace "Ni dai abinda na sani Allah ya Isa yanxu na fara ja Masa Kuma wallahi bazan tab'a yafe Masa ba" Aunty Fatee dariya tayi kalfana ta d'aura da fad'in "Wallahi aunty salloli 5 da nake yi (Yatsanta ta d'aga tana nunawa Aunty Fatee) sai na jaa Masa Allah ya Isa da tsinuwa da Kuma fatan Allah ya yi Masa abin da ya min,Insha Allah auren Nan tashin hankali ne a gare shi"

Aunty Fatee tace "Haba Kalfana ban sanki da Hakan ba kiyi Masa kyakkyawar zato"

Zainab tace "A'a aunty wallahi ki barta tayi don na tabbata shine kad'ai zai sa taji sanyi a ranta."

Azeemah tace "Ko Kuma ta cire shi da ga ranta ba."

Kallon Azeemah kalfana tayi tace " kema kin San Abu ne Mai wuya, Amma Insha Allah , bazan bari Hakan ya shafi rayuwata ba"

Aunty Fatee tace "na nawa Kuma ke da abinci Mai kyau ba ki iya ci"

"Haka ne Aunty shiyasa nake jaa Masa Allah ya Isa Kuma Zan ci gaba da tsine Masa har izuwa ranar da naji na daina Jin haushin sa"

Aunty Fatee tace "Da dai kin bar maganar tsinuwar Nan, Ina ji a jikina zaku shirya Kuma shine mijin Auren ki."

"Aunty Rufa min asiri Dan Allah, Allah ya Raba Ni da auren Mai Mata kin fa San yadda na tsani auren Mai mata."

"Ina Miki fatan Alhairi kalfana, yanzu ku tashi muje muci abinci ko."

Kalfana tace "Laaa Aunty har girki kikayi Kuma baki kirani ba" tana turo baki.

"A a naga kinyi bak'i ne ku tashi kawai." Tana Kai maganar ta fita daga d'akin, duk su ukun suka tashi da niyar Rufa Mata baya, sai sukaji wayar zee ya fara ringing, zee na dubawa tayi tsaki, kalfana da Zeemah dai kallon ikon Allah suke kan su sauka kasa an Kira yafi sau uku, kalfana tace "Kaaai zee Dan Allah kin Dame mu ki d'aga call d'in Mana" zainab tace "Ke malama bazan d'aga ba."

Azeemah tace "Anya ba Adam bane, don d'azu kan mu iso yayi ta Kiran ta but she refused to pick up the call."

Kalfana tace "Haaa'ahhhhhh haba zee wannan wani irin abune." Kwace wayar tayi, tayi picking call d'in ta Kara a kunnen ta a dai dai lokacin sun Isa dinning room, duk su ukun suka zauna, Adam ne daga d'ayan bangaren yace "Haba haba Sweetheart Meyasa kike min haka laifin wani sai ya shafi wani" murmushi kalfana tayi tace "Assalamu alaika" "Wa alaii.....kiss....Salam, Zainab"
"Ba ita bace" "toh Dan Allah wace ce"? "kalfana ce" jikin sa ne yayi sanyi don shi wallahi kunyarta yake ji "Kalfana ya naji muryar ku yazo d'aya"?

"Eh haka ake Cewa muryar mu na kama" "Zainab d'in fa"? "tana sallah"

"A'a fad'a min gaskiya daai, tun d'azu fa nake kira" "eh ta shiga wanka ne d'azu,yanzun ma na d'aga ne don naga Kiran yayi yawa."

"Alright,kin kai Mana ziyara Kenan"?

"A'a ta dai kawo min ziyara"

"Okay gidan ku"?
"A'a gidan Aunty na" "please yimin kwatance" Nan ta shiga yi Masa kwatance ya tabbatar Mata da yanxun Nan zai zo,ya katse wayar Kalfana tace "Zee this is not fear haba Dan Allah ya kamata ki dawo cikin hayyacinki" Amma zee taki har sai da Aunty Fatee tasa baki tukun ta hakura.

Wannan Kenan

bayan sun gama cin abinci, suka zauna a parlor suna kallon tashar Zee world, a Lokacin an sa *Mehek* Kalfana da zee na bala'in son series d'in haka ma aunty Fatee, Jin horn d'in da ake a gate d'in gidan yasa kalfana saurin mikewa don ta tabbata Adam ne, already dama abaya ce a jikin ta baka, an jera musu shinning Stones Golding color sannan tayi rolling da d'an kwalin rigar, tana Isa bakin gate ta Sanarwa baba Mai gadi cewar bakon tane ya bud'e Masa Yana shiga yayi parking kalfana na tsaye tana jiran sa bayan sun gama gaisa wa ta ce Masa su shiga parlor, suna shiga zee ta b'ata raai, bayan ya zauna kalfana ta ce "sannu da zuwa me bakon namu zai ci ko zai Sha"? murmushi yayi yace "ruwa ma ya wadatar" tace "to ka samu" nan ya shiga gaida Aunty Fatee,Azeemah ta gaishe shi,bayan sun Gama gaisawa ta tashi ta shige d'akin ta, fridge ta nufa ta d'auko roban ruwa da na lemo ta jera a tray sannan ta sa glass cup a tebur d'in gaban sa ta aje masa ta Koma mazaunin ta, babu Wanda ya sake magana, Azeemah tace "haba jama'a ya shirun yayi yawa haka"? Kalfana tace "Tashi zamuyi mu basu wuri" har ta Mike sai Adam yace "Zauna kalfana please" komawa tayi ta zauna sai ya fara bayani kamar haka

"Kalfana nasan abokina bai kyauta Miki ba ko kad'an nasan kuna son juna ke dashi Amma matsalar karatun da kike ne ya......"

Zee ta katse shi tace "ya sa bazai iya jiran ta bako meyasa Kai da Abdulazeez ba kuyi Hakan ba, meaning Kenan a gaba Kuma zaku guje mu"

Azeemah tace "Gaskiya zee maganar ki dutse nifa na fara tunanin ko na fasa ma"

Kalfana tace "Haba Dan Allah ku bar wannan maganar babu abin da zai Raba ku da masoyan ku, shi d'in dai dama yayi niyar yaudara na ne , ba lallai bane Suma suyi muku Hakan"

Adam yace "Wallahi Kalfana Maan na kaunar ki, kawai dai kema kin San komai bai da hakuri ne ko kad'an shegen jarrabar tsiya ce dashi"

Zainab tace "Wace ce ya Aura"?

Adam ya maida kallon shi gare ta

"Sunan ta Yusrah Hassan, 'ya ce ga Alhaji Hassan Mai Kud'i."

Kalfana,zee,da Zeemah kallon kallo suka fara Yi wa juna, Azeemah tace "Hassan Mai Kud'i fa kace, d most richest man in Gombe state"

Yace "Yes, Alhaji Farukh baban wa ne ga Suleiman babu Wanda yake iya tsallake maganar sa a familyn gaba ki d'aya, Alhaji Farukh na auren Hafsat Hassan Mai Kud'i, shi ya umarce sa da ya auri kanwar Matar sa."

Zainab tace "kace kawai auren jari yayi"

Adam yace "kamar ya auren jari"?
"Ahhhh eh Mana if not ace duk suna auren Yan gida d'aya." Kad'a Kai kawai yayi yace "Allah shi kyauta, Kalfana kin fahimce Ni Kuwa"?

"Adam ai magana indai akan Suleiman ne bazan tab'a fahimtar ka ba a yanxu, tukunna ma kace umarni aka Masa da ya Aure ta, toh me ya hanashi fad'a min zaiyi aure"?

"Nima tambayar da na masa Kenan ,ya je ya auri bazawara mtwwwws" Rai a b'ace ya Fadi maganar

Zainab da Azeemah dariya suka shiga yi Mai sauti, a tare suka ce "Bazawara" Nan suka sake fashewa da dariya kalfana ganin dariyar yayi yawa ita ma ta shiga Taya su sannan tace "Girls Girls ya Isa haka Dan Allah, Adams kana so kace min bazawara ya aura"?

"Eh bazawara ya aura , kalfana dukkan nin abokanan mu sun ji haushin auren Nan ,shi Kuma sai wani rawan Kai yake"

Zainab tace "dole yayi rawan kaii zai zama surki ga Hassan Mai Kud'i"

Azeemah tace "Banda Maan ma me zaiyi da Kud'i bayan irin dukiyar da Allah ya Masa mtwss" kalfana tace " 'Dan Adam Kenan"

Zainab tace "Kace kawaii sauran wani kawai ya d'auka"

Kalfana tace "to ai shi d'in ma sauran Wata ne kin manta"?

"Ina Kuwa Zan manta,d'an rainin Hankali Mtsww BZ kawai"

Adams ya shiga bata hakuri akan kar ta kullaci abokin sa , godiya kawai ta Masa Amma ko kad'an maganar bai shiga jikinta ba a haka ya tashi ya tafi fa sanyin jiki.

*Bayan Sati daya*

Kalfana da zee shirye shiryen zuwa Abuja suke, Don yanxu saura sati 2 a Koma.

Bangaren Maan da Amaryar sa amarcin su suke ci ba ji ba gani.

Azeemah da Abdulazeez soyayya ba ace wa komai sai Masha Allah.

A yaune Kalfana suka sauka a garin Abuja.

Family 2 sunyi shirye shirye da dama wurin tarbar Daughters d'in su sunyi farin ciki sosai.

*Bayan kwana 5*
kalfana na kwance zee ta Kira ta,ta Sanar da ita cewar bata da lafiya jiyama a asibiti suka kwana , kalfana zuwa tayi ta Sanar da mummy, mummy tace "Allah Sarki ki gaishe ta zuwa anjima Nima Zan Zo na duba ta ,Amma please kar ki dad'e kin San daddyn ku a baya son fitan Nan" "To mummy yanxu Zan dawo" hijab d'in ta tasa dogo har kasa purple color tasa takalmi purple ,tana tafiya a hankali Kai a kasa, tafiya take cikin nitsuwa.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Wasu samari su 2 na gani suna zaune a wani garden, kayan marmari ne Kala kala a gaban su, d'aya daga cikin samarin ya d'auki apple zai sa abaki Amma ya kasa, bai aje ba sannan bai ci ba, tab'a shi yace "Mallam ya haka, me kake kallo ne"? Ganin bai amsa Masa ba yasa ya maida kallon sa ga inda yake kallo, yace "In dai wannar ce zaka yi ka gama" Jin Hakan yasa ya juyo ya kalle shi sannan yace "Kasan ta ne"? "Sosai ma Yar General Mujaheed ne" "Masha Allah Kace Mai suna na" "Eh haka" "Amma ya sunanta"? "Sunan ta Mujeedat Amma ana kiranta da Khalfana" d'aga hannu yayi sama yace "Alhamdulillah Allah na gode maka yau ga Matar Aure Nah, Mujeedat na Mujaheed, sannan Nick name d'ina da nata kusan d'aya Khalfana na Khaleel wow, mutumina had'in nan fa ya yi dai dai" dariya ya fara yi harda rike ciki "in mafarki kake gara ka farka, don sunayen ku na kama Hakan ba Yana nufin zata aminta da Kai ba " Mujaheed yace "mtwwwws kaga matsalata da Kai Kenan Idris Kai komai sai ka sa wasa "
"yi hakuri abokina naga day dreaming kake ne shiyasa" "Day dreaming Kuma kaji ka da shirme, kana wasa da ikon Allah ko"? "A'a wane Ni ka gwada sa'an ka Amma wa anda suka fika da Wanda Basu Kai ka ba sun kasa" "ya akayi Kasan da Hakan"? "Mujeedat fa Auntyn Sufyan ne abokina" "kana nufin Sufyan Wanda na sani"? "Eh shi" "kace abun yazo da sauki, Insha Allah Zan Mata magana" "Allah ya baka sa'a" "Ameen"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bata d'au lokaci ba ta Isa gidan su Zee, sun dad'e suna Hira ,alhamdulillah jiki da sauki, sai ta tashi ta mata Sallama da fatan Allah ya Kara sauki, tayi wa Mummy mahaifiyar zainab Sallama zata

Please Login or Register in order to submit comment