Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa"? mujeedat tace "fried rice din muma zamuci"waiter din yace "shkn nan" sai Maan yace "ka hda da ruwa da smoove" mujeedat tace "ka kawo Min malt" Azeemah Kuma tace "Fanta" , Azeemah ce da Maan suke Hira Sama Sama ita kuwa game take ta bugawa abin ta Har aka kawo abincin suka Fara ci mujeedat kunya take Ji gashi Tana Jin yunwa Kuma Ga mutumin nan Yana ta kallon ta, Azeemah kuwa ko a jikin ta sai ci take Azeemah ta cikin spoon Wai zata Sawa mujeedat a baki sai ta Harare ta tace "Sabon salo Bana son iyayi"sai tace "shkn to tun da baxa ki ci ba "sai ta kai abincin bakin Maan Shi kuwa ya karba mujeedat tazaro Ido Tana kallon Ikon Allah😳 .........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu hadu a next page

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah*( *Milhaat)*

Plz kuyi comment da sharing🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣3️⃣↔️1️⃣4️⃣


Ina Mika Godiya ta Sisters

```Binta Umar Abbale
Ummu Haneefah
Fareeda
Rufaida
```
```Allah ya bar kauna ya Kuma ci gaba da had'a kawunan mu
Aminn summa ameeeeen```🥰
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️


Azeemah tace "to shkn tun da baza kici ba" sai ta kai abincin bakin Maan Shi kuwa ya karba , mujeedat ta zaro Ido tana kallon Ikon Allah,
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Maan kuwa sai ya dauki Can Malt ya sa straw yasa aciki ya kai bakin Mujeedat sai ta kau da Kan ta sai yayi Murmushi ya aje Mata a gaban ta sai ta dauka ta Sha, Azeemah tace "Hmm masoya" a Ranta kuwa so take ta ci Nama kajin nan son Ranta Amma Kuma Wai fashion sai da spoon da feck ta kasa hakuri sai Gani sukayi ta Tashi ta wanko hannun ta a washing hand basin tace "Kalfana, I can't cheat myself Bazan iya ba wallahi Haka Kawai" sai tasa hannu ta hau yagan naman nan son ranta😅
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mujeedat Duk sai Taji kunyan Maan daya lura Da hakan
Sai yace "kin san masana kimiya sunce cin Abinci da hannu yafi digesting da wuri akan Wanda Zaka ci da spoon sabi da hka aci abinci lafiya"ta amsa da "Amin" Amma fa dakyar ta amsa sabida ta cika bakin😂....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mujeedat Dai takaicin Duniya ya isheta karfe 9 saura wayar Azeemah ta Fara ringing Tana dubuwa tace "Kalfana Momy ce" , tace "chaapdi kiyi picking Kar ya Yanke" tana picking tace "Momy Muna hanya" tace "okay" Azeemah da Maan sun cinye abincin su tass mujeedat ko rabi ta kasa ci kasancewar ita ba Mai ci bace sosai.....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Maan yace "My Kalfana, Zaki Sha Ice cream"? da Har Zatace "a'a" sai Azeemah ta kashe Mata Ido akan tace eh sai mujeedat tace "Eh"Dama ita din mayyar ice cream ce yasa aka kawo musu sai suka fita suka zo in da sukayi packing Maan ne ya bude wa mujeedat Kofa ta shige yace "Azeemah sai hakuri fa" sai ta ce bakomai kuyi ta ci fuska na Zan Rama Ai"sai yayi Murmushi ya zaga ya shiga motar Azeemah ma ta Shiga Suna tafiya ana Dan hirar duniya mujeedat Dai Bata cika sa Baki a hirar tasu ba Har suka Isa Suna Isa Azeemah ta fice tace "Mr Suleiman sai da safe" yace "yww Allah ya tashe mu lafiya Miss Azeemah" , mujeedat tace "ki jirani mana" Maan yace "jeki abinki zata biyo ki" mujeedat tace a Ranta "oh ni Allah ya hada Ni da maye", Maan yace "Allah ya hada ki da maye ko Mujeedat"? ta Yi saurin cewa "a a Ni Dai bance ba" sai yace "Okay", so ki Bani labari sai tace "labari daya ne yanzu ina da assignment din da yake jirana" yace "Na takura ki ko tace no ba Haka bane kasan dare yayi Bai Kamata ace ina waje ba" yace "Haka ne to shkn Bara Na barki" tace "to", sai wayar mujeedat ta Fara ringing Tana dubawa sai taga "Habibty,Zainab Kenan don da Haka suke saving numb juna sabida amintakar mujeedat tayi picking tace "Emmata yane"?sai tace "kalau plx kimin snapping din Phy101 page 10 Nawa baiyi haske ba" sai tace "to in na Shiga Daki Zan Tura Miki" Zainab tace "Yanzu don wulakanci kina cikin gida ki Shiga Daki yanxu sai kice sai kin Tashi"? tace "no ina waje ne fa" sai Zainab tace "oh ke da Maan Mai Car ne"? sai Ji sukayi yace "eh shine" Ashe Duk maganar da suke Yana Jin su ta Kure Volume din wayar ta, Zainab tace "Kalfana Allah ya Isa" Kamar zatayi Kuka "don wulakanci a handsfree kika sa wayar Muguwa Kawai" sai ta katse wayar mujeedat kuwa dariya take Maan Shima Dai dariyar yake , Yana satar kallon ta yace "wow kinga yanda kika Yi kyau da kike dariya gaskiya dariya ya dace da fuskar ki" sai ta sunkuyar da kanta yace "Aww Wai ke kunyata kike ji"? "hmmm Baki San kunyan wa Zaki Ji ba,tun wuri ki daina, Bata ce komai ba yace "okay"sai da safe ko"? tace to "Nagode Allah ya saka" yace bakomai "ai Yi wa Kaine sukayi sallama ta fita Bai bar unguwar ba Har sai da ya ga shigewar ta yace "Masha Allah dubi yanda take tafiya Kamar dawisu" , ya Daga "hannu Sama yace ya Allah ka tabbatar da alhairi a tsakani Na da wannar baiwar taka" ya tada motar sa sai Abuja quarters,.......
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mujeedat ta tarar da Azeemah Har ta Gama Shan ice cream dinta sai "ta ce mayya Kawai" ta amsa da "Na kaiki"? Momy tace "to malamai Baku San mutum ba Ku kama Ku bishi in Dan yankan kai ne fa"? mujeedat tace "hmm Momy ai Duk Azeemah ce Yar rainin hankali" Ji mujeedat tai Azeemah takai Mata dundun Momy ta ce "look at those girls everybody will now know dat u people are back Allah ya shirye Ku" sai ta shige Dakin ta tace sai da safe.....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mujeedat tace "Azeemah bashi kika dauka" ita ma ta shige daki Azeemah ta kyalkyale da dariya itama ta shige mujeedat Na Shiga daki ban Daki ta nufa tayi alwala tayi raka'a 2 tana Mai rokon Allah daya Basu sa'a akan karatun da suka sa a gba sai ta dau jakar makarantar ta ta dauko handout din tayi snapping ta turawa Zainab ta WhatsApp sai ta kashe datarta ......
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana cikin assignment sai tace "nayi mantuwa akwai abin da nake son Yi Amma Mene ne" tayi shiru tana kallon Bob din Dakin ta sai tace "yaww Alhj Maan, ya Kamata Naji ko ya Isa gida" sai ta dauko wayar ta tayi dialling numbsa Har sau 2 Bai Daga ba sai ta ce ko lafiya , ta aje wayar sai Taji karar shigowar message ta duba sai taga Alhaji Maan ne ta Fara karanta sakon kamar Haka"Am so sorry Babyna ina driving ne shysa ban Daga call dinki ba but ina Isa gida Zan Kira ki" sai ta Masa reply da "to Allah ya tsare "sai ta cigaba da karatun ta....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Chaaj Sai Taji wayar ta tafara ringing tace "oh waye ne Kuma Ni kashe wayar ma zanyi haba" tana Daga wa sai taga Sahibin ta ne Maan dinta yayan Zainab sai tayi Murmushi ta Yi picking da "assalamu alaika mijina" cikin muryar shagwaba yace "hmmm wa'alakkissalam Mata ta , ya kike"? "ina lafiya, kai fa"? yace "ba lafiya gaskiya" ta Tashi ta zauna tace "lafiya me ya same ka"?yace "hmm Babyna, ba ke bace kika sa ina ta tunanin ki Na kasa karatu" sai tace "haba Mijina Har ka tsoratar Dani nadauka Wani Abun ne ya same ka"sai yace "Kya jiki wanan ba Wani Abun bane"? tace "Wani Abun ne"yace "me kike Yi"?tace Masa "karatu"yace "Kar Na dame ki Nima ina area class ne Nace ya Kamata Naji muryar Babyna" tace "hmm Nagode" yace "ki kulanmin da kanki"tace "Insha Allah ", "I love you" ta amsa da "love u more"sai ya katse wayar.......
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bangaren Maan kuwa Yana Isa gida yayi wanka sai ya kira mujeedat tayi picking "assalamu Alaikum" yace "wa'alakkissalam Babyna" a zuciyar ta tace "Wai meyasa Maan din ta da Alhaji Maan wasu abubuwan nasu iri daya ne"? Tana tmbyr kanta sai tace Masa 'ina wuni" yace "lafiya ya kke" tace "lafiya ka Isa gida lafiya"? yace "Alhamdulillah, Kar Dai Na tashe ki"? "a a karatu nake" yace "I'm sorry Na dame ki ko" tace "a a bakomai"daganan ya Fara jaaan ta da Hira Har suka kai 1hr Suna waya sai wayar ya Yanke ya sake kiranta yace "Ashe Mun kai awa daya"? "eh Nima nayi mamaki" "Bari Na barki hka, Amma ba don Raina yaso ba" "Toh sai da safe" yace "mukwana lafiya pls ki kulanmin da kanki" tace "Insha Allah" ya katse wayar ta cigaba da karatun ta Har karfe 2 sai ta Tashi tayi alwala tayi addu'ar bacci tayi baccin ta
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Karfe 5 Na safiya alarm dinta ya buga ta Tashi tayi alwala tayi Sallah tayi tilawar alqur'ani karfe 6 ta rufe qur'anin ta Koma bacci Bata Yi Nisa cikin baccin ba taji wayarta Na ringing tace "Dady ne in bashi ba Wa Zai Kiran da safe Haka" tana dubawa taga Alhaji Maan tace "Ikon Allah" tayi picking da sallama ya amsa yace da "fatan kin Yi Sallah" tace "eh nayi"yace "kin Tashi lafiya" tace " lafiya Lau Alhamdulillah" yace "jiya karfe Nawa kikayi bacci", "karfe 2" "kaai kaaai me kike Yi Haka" "karatu" sai yace "Baki da lecture ne"? tace "ina dashi Har 3"? yace "okaBan tea a gas cooker sai ta Shiga bathroom tayi wanka tana fitowa ta sauke Ruwan da ta daura, sai ta cire kaya material Lemon green ta shafa mai,sai ta dauko Bokaai ta fita ta rifu kofar , sai ta Shiga Dakin Momy ta gaishe ta , Azeemah kuwa tana kitchen , mujeedat ta Shiga a hankali Azeemah Ji tayi an Kai Mata dundu sai tasa ihu wayyo , mujeedat tace "Yar rainin hankali baza ki Kira sunan Allah ba Zaki ce wayyo, Dama Nace Miki sai Na rama" Azeemah tace "Hmm yau Bana jin Na magana", Mujeedat tace "Zan Shiga school", Azeemah tace "Har kin Karya"?tace "Laaah kin Ga Na Manta Na tafasa Ruwan tea gashi karfe 8 nake da lecture" ta ciro wayar ta a jaka ta Duba 7:45 tace "Oh My God"ta dafe Kai tace "Azeemah Nikam bye sai Na dawo Zan Karya"sai ta Ce "Momy Na tafi" Momy ta amsa da "sai kin dawo".......
♾️♾️♾️
Mujeedat Bata fita ba sai da ta yi addu'ar fita dga gida
_Bismillahi, tawakkaltu alallahi Wala haula Wala kuwata illa billah_
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tafiya take cikin sauri Har ta Fara hangen 2nd gate Na jami'a sai Taji wayar ta ta Fara vibrating tana Duba wa taga Excellency (mahaifinta) ta amsa "Assalamu Alaikum" ya Masa "wa'alakkissalam my daughter"tace Daddy "Ina kwana" yace "lafiya yau Baki fita ba" tace "yanxu haka Ina hanya ne" sai yace "okay Ina Jin Karan machine" kin Tashi lafiya"?tace "lafiya Lau Yasu Momy"? yace "Suna lafiya gasu Muna breakfast Wayan Na handsfree ku gaisa", tace "Momyna Ina kwana" ta amsa "My Kalfana ya kike" tace "lafiya Lau Momy ya gida"? tace "lafiya Lau ya karatu"tace "Alhamdulillah, ina kanne Na"? Maryam tace "Aunty Ina Kwana", tace "lafiya Lau ya kike"?tace "lafiya ya makaranta"? tace lafiya Lau, Sufyan yace "Big sis" tace "Hmm Big guy so ka Manta Dani ko"?"yace Na Isa ya kike,ya makaranta"? "lafiya Lau" yace "Allah ya taimaka" tace "Amin Nagode, Ina Hashim"? Maryam tace "gashi Yana Wasa" Hashim yaro ne Dan shekara 1 be Fara magana ba mujeedat tace "to sai anjiman Ku saura 4mints mu Shiga lectures Gani a bakin LT" (lecture theatre) Daddy yace "okay Allah ya Bada sa'a"ta amsa da "Amin" Momy tace "ki Kula da kanki fa" tace to momyna tace 'Allah ya Miki albarka" tace "Amin" Sufyan da Maryam suka ce "bye take care" tace "thank you, miss u guys alot".......
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana Shiga LT Taji ana Kiran ta "Kalfana!! Kalfana!! Kalfana, ta juya taga Salma ce tazo ta Mika Maka ta hannu tace "masoyiya kin Tashi lafiya"? Salma tace "lafiya Lau,Ina cincin Na amarya"? mujeedat ta kyalkyale da dariya Salma ta nuna mata sit zauna "Dama Na aje miiki sit"sai ta zauna a gefen ta kuwa sauran kawayen sune suka gaisa Suna cikin Hakan ne sai Dr Yusuf ya Shiga ya Fara gabatar da darasi karfe 10 ya fita.......

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Nan suka Nufi Science complex Su 6, Mujeedat,Salma, hafserth,fateema, Hassana,da Sarah Suna tafiya Suna Hira , sai Salma tace "Mujeedat Ina Zainab ne"tace "wlh rabona da ita tun jiya,tace tana da lecture karfe 10 a science complex, kila zamu hadu" Suna shiga cikin science complex Kan su Shiga lectures inda zasu Yi lecture sai Sarah tace ga chaan "Zainab din ai" mujeedat tace "a Ina" sai Salma tace "a LT A "tace "okay Na ganta Bara Na je Na same ta" Kan ta Kara sa inda take Zainab tace "yar rainin hankali Ina ta Kiran ki kika ki picking",
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
tace "ni yaushe"? Zainab tace "Duba wayar ki" Mujeedat ta Duba wayar tace "kassh I'm so sorry wayar Na silent ne Ina lecture,so ya akayi" tana magana tana kallon wayar sai taga 2 missed calls Na Maan sai 1 missed call Na Alhaji Maan sai taga 3 missed calls da Sabon numb "Zee tace Ina Miki Magana hankalinki Baya nan" tace "sorry xamuyi magana anjima sai suka Yi hugging Na juna" mujeedat tace "akwai labari fa"tana magana tana tafiya sai zee tace "zamuje orientation din ko"? mujeedat tace "bazanje ba" zee tace "wlh sai kin Je" mujeedat tayi dariya ta Shiga LT B Zee Kuma ta Shiga LT A karfe 12 suka Gama Mujeedat tana fita ta tarar da Zee tana jiranta sai suka fice suka Nufi hanyar gidan su Mujeedat Suna tafiya sai mujeedat ta Fara lambarin yanda suka Yi da Alhaji Maan da Azeemah zee tace "kuttmelessi a gaban idon ki ta bashi abin ci a Baki"? mujeedat tace "eh to Ni Ina Ruwana chaan musu"zee tace "Hmm lallai ma Bani ba Kam wallahi da Na Mata jahilci" mujeedat tayi dariya "Allah ya shirye ki" zee tace "Haka Kawai wallahi ke kika barta" sukayi ta Hira Har suka Isa cikin gida suka Shiga da sallama Momy ta amsa Azeemah Kuma tana parlour tana guga........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mujeedat ta Shiga Daki tace "yunwa nk Ji Momy, ban karyaba Na fita", tace "ke ko U dis girl taya za'ayi ulcer ya rabu dake" mujeedat tayi Murmushi, Zee ta Shiga parlour tace "Azeemah yane" sai Azeemah tace "emmata ya kike ta amsa da lafiya Lau" mujeedat ta dauko bread sai ta Debo Stew a plate ta Shiga ta zauna a parlour tace "zee ga bread" Azeemah tace "ita kadai kika Gani"? mujeedat tace "bismillahi al-masifatu", mujeedat ta dauko wayar ta sai ta Kira Maan Yana Gani sai ya katse wayar ya Kira ta Kamar kullum sunyi wayar Kamar yanda suka Saba cikin Farin Ciki da kaunar juna Dsun dauki mintuna 40 Suna waya sai ya ce Mata "Yana da lecture karfe 2 Bari ya shirya" yace Mata "I love you" ta amsa da "love you more" sai yace "Haba Babyna baza amin ba"?tace "me za a Maka"? sai yace peg (kiss) mana sai tayi dariya tace "ina tare da Zee da Azeemah" yace "waai Waai kice kina tare da Zee buga Duniya to Bara Ni Na Miki sai yace Muaaah😘" sai tayi Murmushi tace "Nagode Mijina" yace "bye", Azeemah tace "love birds" mujeedat ta Harare ta........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zainab kuwa chatting take tayi , mujeedat sai tayi dialling Sabon numb da ta Gani ta Kira sau 2 ba a Daga ba sai ta aje wayar , sai taga numb Yana Kira tana picking Taji ance assalamu alaiki sarauniyar Mata...........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu hadu a page Na gaba

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat* )🖊️

Plz Share and comments🙏🏻🙏🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣5️⃣↔️1️⃣6️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️




Mujeedat tayi dialling Sabon numb da aka Kira ta dazu, ta Kira Har sau 2 ba'a Daga ba tana aje wayar sai ta Ji Wayan ya Fara ringing Tana picking sai Taji ance assalamu alaiki sarauniyar Mata, ta zazzararo idon ta alamun waye wannan Kuma sai Taji ance hello sai ta dawo Daga Duniyar tunanin da ta Shiga, ta amsa da wa Alaikummussalam , yace barka da war hka anan ne ta gane muryar wane ne Ashe Dai Alhj Maan ne, tace yww barka daai, yace ya kike ya schl, tace Alhamdulillah sai yace kin gane ni tace eh Na gane ka,yace to wane ne ni sai tace hmmm ka yadda Na gane ka Kawai yace Amma kinyi kokari Na zaci baza ki day murya ta ba tace Hmm Daga nan suka yi ta Hira kusan Na 30 mints sai yace Mata lokacin sallah yayi Bari mu Shiga Masjid tace to a mana addu'a, yace me kike so a Roka Miki sai tace abubuwan da yawa Kawai Dai ka Roka min Allah ya cika Min Burina Na alhairi, yace to Nima kimin sai tace me za a Roka Maka yace ki Roka min Allah ya Bani Mujeedat a matsayin matata uwar 'ya'yana tayi juum Bata ce komai ba sai yace ko baza ki Iya ba tace a a zan Iya sai anjima yace to ya katse wayar.........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Ta aje wayar sai taga abin mamaki Zee da Azeemah sun cinye bredin tass, mujeedat tace kuttmelessi me zan Gani hka a Dai Dai lokacin ne Azeemah ta kai yankan bredin Na karshe ta cika bakinta Har kasa magana take zee kuwa sai dariya take Kalfana ta Bata Rai tace wannan ai mugunta ne Amma kunsan ban Karya ba Kuka cinya bredin ko????😡 Zee tace afuwan Matan Yaya Na dauka kin Koshi e kina ta cin soyayyar ki Naga Har sai da kikayi gyasa Azeemah kuwa sai dariya take........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana ta ce sai Ku Tashi muje muyi Sallah ko,😒 zee tace Wai da wa kike waya ne Azeemah ta amsa waye ban da Maan zee tace bashi bane mujeedat tace to Wai Ina ruwanku Dani ne kam zee ta matso ta rungumi mujeedat tace haba my Habibty fushi fa Bai dace da kyakkyawar fuskarki ba sai ta Fara Mata chakulkuli nan take ta Fara dariya Azeemah ita ma ta Taso taya zee Suna ta Yi Mata chakulkuli Mujeedat tace dan Allah Ku Bari ya Isa wlh nayi dariya sosai Cikina zaiyi ciwo hkn Bai sa suka Bari ba Momy tace me kukeyi a Dakin nan nan Dana suka nutsu mujeedat tace Momy Suna Cin Zali Na tace eh kin dawo ai ta cigaba da harkar Dake gaban ta nan sai mujeedat ta Shiga dakinta tayi alwala zee ma ta bi bayanta suka Yi Sallah........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan sun idar da Sallah ne Duk Suna zaune a Akan sallaya Bayan sunyi addu'o'i mujeedat ta Dade tana rokon Allah zee tace "Malama me kike Roka mna ne hka" sai mujeedat ta Harare ta sanan ta shafa addu'ar Nima Dai naso Na san addu'ar me take Amma tayi a zuci, Zee tace "zamuje orientation din nan ko"?, mujeedat tace "kedai in ta nan ne kin Fi karfi, ni bazan je ba" Zee tace wlh "sai kinje" mujeedat tace "to uwata sai ki Tashi mu shirya ko" Suna cikin hakan ne sai Azeemah ta shigo da food flask mujeedat ce ta Fara budewa taga farar shinkafa ne da stew da kifi tace "wow yunwa nk Ji wlh" nan ta dauko plate ta diba musu suka Fara ci Zee tace "kalfana kici a hankali mana" mujeedat "dallah Chan ba Duk kune Sila ba tun fa abincin da Na ci jiya a restaurant,banci komai ba" nan Azeemah tace "zeeeeee kinyi miss wlh" zee tace "bani Insha" sai Azeemah ta Fara Bata labarin yanda sukayi a restaurant din Zeee ta Fara dariya tace "haba yanzu Azeemah sabida naman kaza ki wanke hannu a gaban Alhj Maan, ai sai ya dauka Duk hka muke" mujeedat kuwa ko kallon su batayi sai Loma take burinta taga ta Koshi zee tace Kalfana ke Kuma ya kikiyi a daidai lokacin ta dauko Ruwa zata Sha sai da tasha Mai isar ta tace Alhmdlh gsky yunwa batayi ba, Zee tace kin Koshi Kennan tace eh man baki ga Har fuskata ta nuna ba Azeemah tace barnan kin bi kin Dami mutane da yunwa gashi kwakwata dakyar in kinyi loma goma Ciki Kamar Na jarirai mujeedat tace eh din zee tace baki ganta ba Kamar zata karye mujeedat tace iyeee Wai kare ne yake cewa Kura maye sai kuyi ta dariya mujeedat tace zee kinsan Azeemah Yar rainin hankali ce Azeemah tce me Kuma nayi zee tace shafa Min mujeedat tace hmmm a gaban idona fa ta bawa saurayina abinci a baki Zeee da Azeemah dariya suke ba kakkautawa mujeedat tace eh dole kuyi dariya Ashe Duk Momy Na Jin su tace haeeey Azeemah why ya Zaki bashi abinci a baki Shima Dan iskane sai ya karba mujeedat tce ya bazai karba ba tunda ni ban Basa ai ko don ya bani haushi Zai karba Azeemah dai dariya take tace Momy wlh tsokanace ita Kuma sai ta nuna Bata Damu ba Shi Kuma Har da Bude Mata Malt ya mata strow Wai Zai sa Mata a baki ita Kuma Yar kauyen sai ta karba tasha da kanta mujeedat tace oh haushi kika Ji da bai sa miiki a baki ba Zee da Momy sukayi ta dariya mujeedat tace in sonsa kike sai Na Hada Ku ai Azeemah tace ai ya ganni nice ma Fara gani Kan ya ganki Kuma be ce Yana Sona ba ke yace Yana so Wai tukunna ma ya kukayi dashi ne mujeedat tace hmmm my sister Daga haduwar mu jiya jiyan nan Wai Aure Na zaiyi before sallan azumi Kuma yanzu saura 4months a Fara azumi Ji mayaudarin sai sukayi dariya Momy tace wannan ake Kira love at first side ai ana Haka mujeedat tace kai Momy am finding it so very hard to believe him , Zee tace Plx ki amince kinga in Muka Je gidan ki ayi welcoming din mu da namomin Kaji da dawisu Amma Dan Allah me zakiyi da yayana mutumin da ko Mota Bai dashi bare Mota mujeedat Dai tunda zee ta fara magana ta Bude baki take kallon ta Azeemah tace kaaaai mujeedat rufe bakin ya Isa Haka mujeedat tace hmmm Ikon Allah Zee Haka kike ce zee tace eh mana me yayana yake Miki kun bi kin makale wa juna Kowa Maan din Kalfana mtswww mujeedat Yau Naga Yar bikin Ciki Ashe Muna tare da makiyiyar mu ba mu sani ba to a kunnen yayan ki zee tace to sai me ki fada Masa mana ni Dai Dan Allah kiyi accepting din Alhj Maan Momy tace Dix children ba u won't kill me tana dariya Azeemah ita dinma dariyar take sai tace kalfana tunda dai Kanwar sa ce ta baki shawara just accept him a just a wuce gun Momy tace Mujeedat my dear ki amince Masa ai Gara kiyi soyayya da Wanda Zai Biya Miki bukatunki Na Yau da kullum zee tace yww Momy fada Mata mujeedat tace hmmm tunda mun gama Cin abincin sai mu shirya fita Orientation din ko zee tace eh munafuka

Please Login or Register in order to submit comment