Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yazo man ko baki son sa ne?"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a next page

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu* (💞milhaat💞)


Plz comments and share🙏🏻🙏🏻🙏🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 8️⃣5️⃣↔️9️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Kalfana ina kaunar sa sosai ma, shawaran da nake so ki bani shine kinga na Dade Ina karuwanci, in mukayi aure zai gane, shysa nake so na sanar dashi kan ya sani" ta karasa maganar cikin kuka Mai cin raai, tashi kalfana tayi ta zauna a gefenta, riko hannayen ta tayi sannan tace,

"Zeemah kar ki yarda kar ki kuskura ki fara sanar dashi Zaki say ya guje ki"

"Toh kalfana tell me what do I suppose to do, in bai Sani ba yanxu after marriage he will know and am sure that he will devorce me"

Kalfana hannu tasa tana sharewa Zeemah hawaye "look Zeemah zan taimake ki, kuma Insha Allah baxai gane ba"

Zeemah d'ago kanta tayi tana kallon kalfana cikin rashin fahimta sai tace "But Kalfana how will you help me a bud'e nake fa already"

Murmushi kalfana tayi tace "For now ki daina Sarki da ruwan sanyi, no matter what kiyi da warm water not hot water fa warm water, sannan ki nemi bagaruwa da ganyen magarya ki tafasa ya zama ruwan tsarkin ki, kiyi sit bath dashi"

"Kalfana are u sure of wat u r saying?"

"Of course, am 💯 sure about dix just try it and see and thank me later"

Zeemah rungumar kalfana tayi sai tace "Thank you so Much Mrs Maan🥰"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana tace "u are highly welcome Mrs Abdulazeez" dariya duk su biyun suke yi, suna cikin hiran ne Zeemah tace "Kalfana let me ask you something, Ina da wata qawa I Love her so much, ana so a cutar da ita is it proper na sanar da ita?"

"Eh mana Zeemah ki sanar da ita as soon as possible, in aka cutar da ita alhaki akan ki"

"Hmmm toh , kalfana qawar Nan tawa kece, kar ki sa hijab din da Momy ta dawo da shi, sannan ga wannan, (Wani d'an karamin kwalba ta Mika Mata) ta bani ne wai in Maan yazo na shafa a jikina don kar kato da hankalin sa a kaina, sannan anjima tana Shirin kawo Miki abinci kar ki kuskura kici"

"Zeemah Kenan nayi mafarki kwanaki naga Momy da hijab d'in na, da wannan kwalban tana Kiran suna na, ban fahimci mafarkin ba shys ban damu ba ashe ubangijina ya nuna min" sai ga hawaye wiwiwiwi

"Kalfana kuka fa bana ki bane , in so samu ne ki bar gidan Nan na d'an wasu kwanaki"

"Toh Zeemah nagode sosai Allah ya saka da alha.........."
Zeemah d'aga wa kalfana hannu tayi alamun tayi shiru

"Haba kalfana kin ceci rayuwa ta to me don na fad'a Miki halin uwata, kinga tashi muje mu Kona hijab din Nan bata gida kan ta dawo Mun gama"


Momy da tun shigar Azeemah d'akin Khalfana duk a kan Idon tane, lab'ewa tayi taji komai jikinta yayi matukar sanyi ganin yanda take son cutar da Kalfana Amma ita kuma kokari take ta cutar da ita, a ranta tace "Insha Allah zan rike ta da zuciya d'aya ba cuta ba cutar wa" jin suna Shirin fitowa yasa ta fita ta bar gidan cikin sauri.


Tashi tayi ta d'auka hijab din jiki na rawa, suna fita kero suka watsa akai, suka kyatta ashana, Nan da Nan ya kama kamar petir suka sa ,hayaki baki Kirin ne ya fara tashi ga Wani warin da yake, Zeemah ce ta koma ta d'auko wannan kwalban ta jefa a ciki a Nan take kwanban ya fashe, tiraren da akasa a ciki sai canxa kala yake, kalfana kam ta tsorata sosai don da zaka tsaga jikin ta tabbas baza ka ga jini ba lol😅😅.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Sallamar Momy ne yasa duk suka maida kallon su I zuwa mashigar gidan don tabbatar da muryar Wanda suke ji shin ita d'in ce ko ba haka ba, ganin Momy yasa suka tsorata ba kaliba hatta Zeemah ta tsorata.

Zeemah tace "Mo..... mom.......Momy welcome" "Ehen My Daughter ya kuke?" Tana saye ta d'aura hannu d'aya akan d'aya kamar Mai sallah.

"Muna lafiya Momy" kalfana kasa magana tayi don ganin take kamar Momy zata yanka ta, Momy tace "Kalfana ba magana ne?" "Na.....na...na'am Momy sannu da daw..... Dawo wa"

Kad'a Kai kawai Momy tayi sannan tace "ki shigo parlor Ina da magana da ku"

Tafiya suke a hankali kamar Kazan da kwai ya fashe wa aciki 😅😅

Bayanin sun shiga ne suka samu wuri suka zauna jiki a sanyaye Momy ta ce.

"Zeemah tun shigar ki d'akin kalfana akan idona ne, hatta maganganun da kuka yi I heard everything"

Kalfana da Zeemah kallon kallo suke yi wa juna.

Momy tace "Yes Naji komai, Kalfana Allah ya Miki Albarka, ya biya Miki bukatunki na alhairi, hakika na so na cutar da ke da mafi munin cutarwa Amma Allah Yana tsare ki, sannan kin San Ina nufin ki da sharri Amma ke da alhairi kike saka min, kiyi hakuri kiyafe min, hakika na cutar da Kai na sannan na you sanadiyar lalacewar 'yata, Azeemah ki yafe min Dan Allah" tana maganar idon ta cike yake fal da hawaye.

Cikin sauri Zeemah ta riko hannayen Momy tace "Momy kar ki yi kuka wlh na yafe Miki duniya da lahira"

Momy tace "Nagode Azeemah Allah ya Miki Albarka" kalfana da Zeemah suka amsa da Amin.

Ita dai Kalfana har yanxu gani take kamar Momy karya take kamar yadda ta saba.

Momy ce ta katse Mata tunanin da take tace "Kalfana kinyi shiru, ko da yake ba lallai bane ki sake yarda da magana ta ba,Amma wallahi wallahi wannan karon dagaske nake" jakar ta ta bud'e ta zaro wani chocolate sannan tace.

"kalfana kinga wannan don ke aka min had'in Nan nasan kina kaunar chocolate sosai shysa na nemi amin dashi , da zaran kinsha shkn naki ya kare don't ba b'ata lokaci Zaki zama cikakkiyar yar iska,Amma yanxu zan Kona shi" sai ta aje a kan jakar.

Nan Momy ta shiga Bata hakuri ta yadda hankali kalfana zai kwanta Amma Ina kalfana jin ta kawai take, a xuciyar ta kuwa cewa take "Chaaap wlh in ki ka ganni a lahira to kaini a kayi haka kawai, wlh gidan aunty Fatee ma zan koma da zama Kan matar Nan ta kashe ni"

Tana cikin wannan tunanin ne sai taji muryar Baby Nana na tari a tare suka maida kallon su inda take, ganin ta sukayi da wannan chocolate din da Momy ta kawo ta shanye shi tasss.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu had'u a page na gaba

*Daga Alkalamin Fadeelah* *Yakubu* (💞 *Milhaat* 💞)

Plz share and Comment🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 9️⃣5️⃣↔️1️⃣0️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
A tare suka nufi inda Baby Nana take cikin gudu, Momy ta gigice sosai, hannu ta d'aura a ka tana fad'in "Na shiga uku na kashe 'yata da hannu na" Baby Na tuni har ta fara Aman jini, kalfana zaro ido tayi "ashe dama abin da Momy take Shirin yimin knn, Alhamdulillah Allah nagode maka, Amma yarinyar Nan babu abin da ta sani" hawayen da ya ke sauko daga fuskar ta ta share sannan ta Mike da sauri ta nufi kicin, bud'e fridge tayi ta d'auko goran ruwan sannan ta zuba a Kofi.

Bayan ta shigo parlor ta zauna, Ta fara tofi acikin ruwan duk addu'ar da tazo ranta take karantowa, Momy da Azeemah aikin kuka kawai suke yi, Kalfana bayan ta gama tofin ne ta share wa Baby Nana jinin da ke bakin ta, sannan bata ruwan tasha ta shafe Mata jiki da sauran, ba a d'auki lokaci Mai tsawo ba ta fara Amaai.

Amaai take yi sosai bak'i Kirin ta dad'e tana Aman kamar zata amayar da Kayan cikin ta, daga bisani ta amar da wani abu kamar tsoka jajiir,Momy mamaki take tare da hamdallah, Baby Nana ji jiki acikin d'an kankanin lokaci hakan yasa tayi bacci.

Momy kuka take sosai babu abin da take cewa sai "Kalfana thank You, Thank you , Dan Allah ki yafe min, na tuba ki yafe min"

Azeemah ita d'in ma godiya take wa Kalfana, Azeemah kuka har da majina, Kalfana ce ta shiga basu hakuri basu daina kukan ba har sai da sukayi Mai isar su.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana tace "Momy Lokacin sallah yayi ya kamata muje muyi sallah, Zeemah ki je ki kwantar da Baby Nana a d'aki".

Tashi sukayi Momy d'akin ta tashiga, Zeemah da Kalfana Suma hakan sukayi.

Kalfana ma shiga wanka tayi Amma duk hankali ta ba ajikin ta yake ba bayan ta gama wankan ta yi alwala, tana fitowa doguwar rigar da take sallah dashi ta zurma sannan tasa hijab bayan ta idar da sallah, ta dad'e tana rokon Allah da ya Kara tsare ta da dukkan masharranta tare da yi masa godiya, bayan ta gama addu'ar Mai ta shafa sannan ta d'auko wata farar atamfa anyi Mata design da royan blue, powder kawai ta shafa da lip glow,ta kama gashin kanta da ribon sannan ta d'aura dankwalin atamfar, Hijab dinta ta d'auko tasa Shima ruwan Royal blue, sannan ta d'auki jaka da takalmi royal blue, wayarta ta d'auka taga tana da missed calls kacha kacha, tace "Oh gara ku ni mutuwa na gani yau k'arara mtwwwws".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Bayan ta fita daga d'akin ta ta tarar da Momy a tsakar gida tana zauna tayi takumi sai hawaye, kalfana a ranta cewa take "Hmmm kad'an ma kika gani ai wlh da ta ke ne bazan taimaka Mata ba, Allah da iko take ni dai nasan na karanta falaki da nasi da ayatul qursiyu, hakika qur'ani magani ne" a cikin maganar zuci da take yi take wannan zancen har ta karasa inda Momy take.

"Momy Zan shiga school" Amma shiru "Momy magana fa nake" shiru, sai da ta tab'a ta a firgice tace "Na'am" "Cewa nayi zan shiga school" "School Kuma yau ba Sunday ba?" "Eh Next week zamu fara exam shysa" "Okay Allah ya bada sa'a" Zeemah ce ta fito duk jiki ba kwari tace "Kalfana akwai maganar da nake so muyi Kuma naga kamar fita zakiyi" "Eh Zan shiga school ne,lfy Kuwa?" "Eh lafiya sai kin dawo kawaii" "Okay" zip d'in Jakarta ta zuge, Nikab d'inta ta Ciro ta shiga d'aura Sha a fuskar ta, Momy tace "Ohh su Kalfana yau weekend d'in ma baza ki hakura da Nikab din ba?" "Hmmm Momy knn sabo, nikam na tafi"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan ta fita Bata zarce ko Ina ba sai cikin Jami'a , wuri ta samu ta zauna a Mango garden Tana karatu Amma Sam bata fahimta, maida Handout din tayi a jaka ta d'auki wayar ta, duba missed calls d'in wayarta ta shiga you, taga harda Daddy dialing numb sa tayi, bayan sun gaisa suka fara Hira irin na Uba da yarsa bayan sun gama wayar tayi dialing Numb Alhj Maan, Yana picking yace "Bari Zan Kira ki" sai ya kashe. Bayan ya Kira ta suka gaisa sannan yace
"Baby na Kin manta Dani kawaii abunki,tun jiya na kasa gane kanki"

"Allah Sarki Hubbyna ba haka bane ba, kasan muna Shirin exams ne"

"Tsakani da Allah yau kwanaki 5 Kenan banzo na ganki ba Amma ko a jikin ki irin baki damun Nan ba ko?"

"Hmmm ban damu ba fa kace, nayi tunanin ayyuka ne suka maka yawa shiyasa"

"Toh ba haka bane" "To ya ya ne?" "Sai yanzu Zaki tambaya?"

"Ya Salam rikici kenan,Sai kace yaro d'an shekara 4"

"kin manta Hanif ne ni"
"Hanif waye Kuma haniif" "Umm umm 'Dan da zamu Haifa mana".

"Hmm toh Abban Hanif Amma fa ni , hanifah nake so tunkunna" "Babyna Kenan Nima haka ai,kawaii Allah ya tabbatar da alhairi a tsakanin mu"

"Ameen Abban Haneefah" Alhj Maan yace "Babyna Ina son sunan Nan gashi ya dace da bakin ki".

"Tunda kana so Nima Ina so,don hk da shi Zan Rika Kiran ka".

"Toh godiya nake Babyna, kina gida ne?" "A'a bana gida"
"Ina kika je nasan dai yau Sunday ba lectures" "Ina makaranta Amma yanxu Zan fita" "Okay hope gida Zaki koma?" "A'a gidan Aunty Fatee" "Gaskiya Babyna bana son yawo fa" "Bafa yawo bane gidan Aunty na ne" "okay ki jira ni Zan zo na Kai ki" dafe kirji tayi tace "Waaai Dan Allah ka rufa min asiri" shiru yayi Jin yayi shiru yasa tace "Hello!!! Hello!!! Hello" sai yace "Ina jinki" "Ya Ina magana Kuma kayi shiru?".

"Tunani nake" "tunanin me kake yi?" "Anya Kalfana Anya kina Sona kamar yadda kike ikrari?". Murmushin takaici tayi sannan tace "Kafi kowa sanin amsar tambayar ka".

"In dai hakan ne dagaske meyasa baki had'a ni da iyayen ki ba?".

"In ban manta ba munyi maganar Nan da Kai a baya"

"Hmm Kalfana kice kawaii baza ki aureni ba, su Zainab da Azeemah da me suka fiki ko kuwa da me kika fisu?"

"Me Kuma ya kawo sunan su acikin maganar da muke?"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Komai ma ya kawo maganar su" Yana maganar a cikin b'acin raai, "Hubby wai me ya kawo duk wannan b'acin ran?"
"Okay baki ma sani ba Kenan ko?"
"Eh ban sani ba da na sani bazan tambayeka ba"
"Akalla munfi wata 3 da had'uwa kan Adam da zainab su had'u yanxu haka har gidan su Yana zuwa kuma a parlor d'in gidan su suke Hira, haka ma Dr Abdulazeez da Azeemah, Amma ni kin ki bani dama iyaka Mom da kika had'a ni da ita".

"Ashe dai na had'a ka da wasu , tunda dai Mom mahaifiyata ce, sannan akan me zaka Rika had'a ni da wasu?" Cikin d'aga murya.

"Kalfana yau ni kike d'aga wa murya, eh, Ina magana kinyi shiru?"

"Toh me zance maka?" "Toh ni kiji abin da zance miki, Ina kaunar ki Ina son ki, Ina sha'awar ki kasance Matar Aure na Amma naga ke ba haka kika d'auke ni ba"

"Ya zaka ce ba haka na d'auke ba, na Riga na fad'a maka dad bazai tab'a amincewa nayi Aure yanxu ba a lokacin da mukayi maganar ka nuna min ka fahimce ni, to meyasa kake acting kamar baka San komai ba?"

"Adams ko yau yace Yana son auren Zainab za a bashi Amma ni fa waya San da zama?"

"Hubby kana jina Dan Allah mubar maganar Nan yanxu kaga ranka a b'ace Nima haka duk zamu ji ba dad'i"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Shikenan Babyna anjima Zan Kira ki" "Allah ya Kai mu" "Amin" katse wayar yayi ita Kuma ta bi wayar tata da kallo. Tace "Oh ni Yar su Jikan mutum had'u wannan shine ana wata sai ga wata,Allah shi kyauta".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tashi tayi ta fita daga cikin makaranta ta hau a dai daita "Malama Ina za a Kai ki" "Tudun Wada" Nan da Nan suka Isa dake ba nisa, Mika masa kud'in sa ta yi sannan naga ta nufi wani makeken gida Wanda aka kayata wajen gate d'in da flowers kala daban daban Kai tsaye ta kwankwasa kofar ba a dad'e ba Mai gadi yazo ya bud'e,Yana ganin ta sai ya hau washe baki yace "Aa'aaa yau manyan bak'i ne a gidan sannu da zuwa Bismillah shigo" har kasa ta tsugana ta gaida shi cikin ladabi da biyayya ya amsa ba yabo ba fallasa har yanxu dai bakin baba Mai gadi yaki rufuwa sai kace Mai tallan toothpaste.😁😁
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana Isa kofar palor Kai tsaye ta tura kofar ta shiga da Sallama Aunty Fatee da mijin ta na zaune a parlor suna kallon film, a tare suka amsa, zama tayi a kasa mijin Aunty fayya umaurce ta da ta tashi ta zauna a kushin, bayan ta zauna ta shiga gaida su, cikin Zolaya yace Mata "Ya Kishiyar ki?" Kalfana kallon sa take cikin rashin fahimta sai tace "Uncle Kishiya Kuma ni" tana Mai nuna kanta yace to me banbancin Kishiyoyi da ke da Matar gidan naku?" Dariya tayi sannan tace "Uncle Kenan wlh kana da abin dariya shiyasa na fi so idan na so na tarar da Kai a gida musha Hira" yace "Allah ko, to yau muna tare har sai kin gaji" Aunty Fatee tace "To kun had'u za a fara Hali, kalfana jeki d'ebi abinci kici" mikewa tayi tace to Aunty" bayan ta gama vin abincin ta dawo ta zauna tare dasu su kayi ta Hira Basu tashi ba har sai da aka Kira sallar la'asar, kalfana d'akin da ta saba sauka ta shige tayi alwala tayi salla sannan ta d'auki wayarta ta kashe ta hau gado ta fara shararrar bacci.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Mu had'u a page na gaba*


*Daga Alkalamin Fadeelah* *Yakubu* (💞Milhaat💞)

Plx Comments and share🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣0️⃣5️⃣↔️1️⃣1️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bata tashi ba har sai dab da magrib aunty Fatee tazo ta tashe ta bayan tayi sallah ta fito parlor da niyar komawa gida, Aunty Fatee tace "Ina zaki?" "Gida Zan koma Aunty" gyara zama tayi sannan tace "Aikin Zo knn,Deee kaga yadda yadda yarinyar Nan ta rame ga karatu ga takuran mayyar matar Nan" "Eh Wallahi My gaskiya ta rame sosai, kina jina Kalfana?" "Eh Uncle" "Ki zauna anan har ki gama jarabawar ki" cikin murna da farin ciki tace to Uncle nagode" Hira suka fara yi duk ai ukun suna cikin hiran aka Kira sallar isha, uncle ya tashi ya fita don yaje matsallaci kalfana da Aunty Fatee kowacce ta nufi d'aki tayi sallah, Aunty Fatee na idar da salla ta shiga kicin don had'a musu dinner, kalfana na fitowa ta shiga kicin don taya ta girki Basu d'au lokaci Mai tsawo ba suka gama girkin,tuwon semomivita da D'anyen kub'ewa suka yi da Naman saniya yaji man shanu sosai (ni kaina da nake d'auko muku rahoto sai da na had'iyi......😋😋😋🤣).

Uncle na shigowa dinning table ya nufa ya tarar sun gama shirya komai shi kawai suke jira, Nan suka fara cin abincin suna ci suna Hira sama sama,bayan sun gama suka nufi parlor suna kallo, mujeedat kasa sakin jikinta tayi gani take kamar ta takura su, mikewa tayi tace "Aunty Zan shiga sai da safen ku" uncle yace "Da wuri haka?" "Eh Uncle a gajiye nake shysa" "Toh mukwana lfy" Aunty Fatee tace "In Kuma zakiyi kallo sai kunna kayan kallon d'akin" "Toh Aunty".
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Ta na shiga d'akinta TV ta kunna ta kamo channel d'in Zeeworld , tana kallo tana chatting a WhatsApp, a ranta tace "Na Kwan 2 ban hau Facebook ba bari na leka na ga wata wainar ake tauya wa".

Ta Dade ta na karance karance, a Facebook kwasam tayi arba da post d'in da Alhj Maan yayi, hoton wata jarirya yasa sanan yayi rubutu kamar haka " _Allah ya Raya ki, abokina Ina Taya ka murna"_ murmushi tayi sannan tayi like tayi comment tace " _Allah ya Raya bisa Sunnah Kai ma muna jiran naka_ 😜"

Tayi sa'a Yana online sai ya Mata reply " _Nikam ai kin Riga da kun ga nawa_ 😎" dariya ma ya bata tace " _Za dai mu gani daai_ 🤣"

Wani ne Mai Suna Sani Ibrahim ya Mata magana yace " _Hajiya Mun gani dai, kije ki bin cika da kyau_ ".

Tashi tayi ta zauna ta karanta reply d'in sa yafi sau 5, tace a ranta "to me hakan yake nufi, Innalillahi kar dai Suleiman Yana da Mata na shiga uku" bata you kasa a gwiwa ba ta turawa Sani Ibrahim friend request Yana gani yayi accepting, bayan ta masa Sallama sai tace "Dan Allah bawan Allah dagaske Suleiman Yana da Mata?"
"Hmm ke kuwa lafiya kike tambaya?" "Eh lafiya Suleiman abokina ne a Facebook ya tab'a fad'a min cewar Yana da Mata Amma ban yarda ba shiyasa na tambayeka don na tabbatar"

"Eh Yana da Mata da Yara 2" zuciyarta ta hau duka uku uku sai taji Karan wani message tana dubawa taga Sani ne yace "Amma sun rabu da matar sa shekaru 2 da suka wuce".
Tace "Allah sarki yaran manya ne?" "A'a hanifah iatace Yar farin sa shekarunta 5 sai kaninta Hanif shekaran sa 2" hawaye ne masu zafi ya xubo Mata a kuncin ta, dakyar ta samu ta masa reply "Allah ya raya" yace "Amma kin tabbata ba ke bace Auntyn mu?" "uhmnn a a ba ni bace abokina ne kawai" "toh in tayi tsami zamu ji" sticker dariya kawai ta tura masa sai ta kashe wayar ta , duk ta rasa me yake Mata dad'i,tashi tayi ta kashe TV ta dawo ta kwanta bacci b'arawo ya sace ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Washe Gari*
Bayan tayi sallah ta gyara d'akin sannan ta nufi kitchen tasan Aunty Fatee da uncle da son cin Chips hakan yasa ta hau fere dankalin turawa tayi source din attaruhu da Kwai ta tafasa ruwan shayi ta say flask sannan tazo ta jera su a dinning table, ta hau sharen gidan ko Ina yayi tsaf bayan ta gama ta koma d'aki tayi wanka duk jiki ba kwari, bayan ta fito tace "chaapdi yau ake yinta bani da kayan sawa" tana cikin wanna tunanin ne sai ga shigowar aunty Fatee, Sallama tayi cike da farin ciki, tace "Sannu Kalfana kin taimaka min yau na makara " murmushi tayi "Ina kwana aunty?" "Lafiya Lau Kalfana, Yana ganki haka fuskan ki ya kumbura kuka kikayi?" "N....ni ...a a..fa Aunty banyi bacci da wuri bane" aunty Fatee taji ne Amma Sam bata yarda ba "ki sa kaya muje muyi breakfast" "Aunty ai ban kawo kaya ba" "okay jirani Ina zuwa" zama kalfana tayi ta zuba tagumi dai hawaye yake ta zubo Mata babu abinda zuciyarta bata Raya Mata akan Maan Mai kyau da Mara kyau, har Aunty Fatee ta shigo da kaya Niki Niki a hannun ta, ta dad'e a tsaye a kanta Bata sani ba, sai da ta dafe kafad"arta, "Kalfana tell me, me ke damun ki plx fad'a min, min dad'e muna abubuwa mu biyu babu Wanda ya sani so tell me damuwar ki" Nan kalfana ta shiga fad'a Mata yadda suka had'u da Maan da Kuma dalilin kukan ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Aunty Fatee Shiru tayi na d'an wasu lokuta sannan tace "Ki bi komai a sannu kar ki yanke masa hukunci ba tare da kinji me zai ce a Kai ba" "Aunty Amma ga alamu Nan na rashin gaskiya in da Yana Sona kamar yadda yake ikrari da zai Sanar dani Amma baiyi hakan ba".

"Kalfana knn sometimes something is better kept on sayed, akwai dalilin da yasa yaki fad'a Miki , just give him sometime okay?" "Okay Aunty kinga Zaki makara 7 saura?" "Ki sa kaya ki sauko kasa, shawarar da Zan baki shine ki d'auki rayuwar duniya a sannu sai kiga komai yazo Miki da sauki, sannan kar ki kuskura kiss tension na d'a Miji akan ki tun yanzu, focus on ur study for now" "I'll Insha Aunty".

Bayan Aunty Fatee ta fita , kalfana tayi saurin d'auko wani Atamfa Riga da sket Mai ruwan kasa an masa flower da ruwan Madara, kayan ya zauna a jikin ta kamar don ita aka d'inka ita kanta tasan kayan ya Mata kyau, a ranta tace "Ikon Allah har yanxu size d'in mu d'aya da Aunty Fatee, Allah ya saka Miki Aunty ya baki 'ya 'ya na Gari".

Aunty Fatee yau shekarar ta 5 da aure Amma

Please Login or Register in order to submit comment