Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Koma gida "Toh Kalfana ki gaida maman naku" "Toh Mummy zata ji"

Tana cikin tafiya kanta a kasa sai taji kamar ance d'aga kanki, tana d'aga kanta Idon ya sauka Akan wani kyakkyawan saurayi dogo ne, Mai dogon hanci bai da jiki sannan ba tsiriri bane ba, sannan ba fari bane,Yana da dimple ga d'an tsiriyar wushirya,🥰 wando wanda ya wuce gwiwarsa kad'an yasa kalan na kakin sojoji da bakar T-SHIRT Wanda ya kama jikin sa, hannu d'aya yasa a aljihu yayin da d'ayan hannun Yana rike da wayar sa yana lallatsawa, ganin ya d'ago kansa har sukayi ido had'u yasa ta sunkuyar da kanta da sauri, Murmushi yayi a zuciyar sa yace "Anya is it d right Time to talk to her?" har ta wuce sai yaga inaa ba zai iya barin ta, ta wuce ba tare da yaji ko da muryar ta ba, bin bayan ta yayi Yana Cewa "Malama!!! Malama!!!" Kalfana ko a jikin ta har ya karaso ta Yana Mata magana Amma Bata kulashi ba sa hannu yayi ya rike hijab d'in ta kalfana juyawar da zata yi sai naji Tasssssssss....
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

(Ikon Allah To Wai wa aka Mara ne, kar dai ya Mari Kalfana🙄🙄, ko Kuma itace ta mare shi)

Ku kasance tare Dani don Jin yanda labarin Matar Aure Nah zata kasance

*Mu had'u a next page*

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu*
💞 *Milhaart💞*
Please comment and share🙏🙏🙏
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣2️⃣5️⃣↔️1️⃣3️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zaro ido tayi don ganin Wanda ta Mara, shi kansa mamaki yayi don ko da wasa be yi tunanin zata Mara shi ba, tana huci tace "Mal Kai wani irin Wawa ne daqiqi ba a koya maka girmama mace a gidan ku ba Mtwws" ta tafi ta barshi ba tare da ya iya ce Mata komai ba, tsuman tsaye yayi sabida ji yake kamar Marin Sa da tayi ta cire zuciyar sa ta tafi dashi.

*Wannan Kenan*

Mujaheed kwance yake a d'akin sa ya kasa nutsuwa ya rasa yadda zaiyi ya kamu da son wacce bata San ma yanayi ba, shigowar Idris ne ya dawo dashi daga tunanin da yake, tashi yayi ya zauna yace "My Man Dan Allah ka taimake Ni ka nema min Numb Khalfana" "Mtsww Sallama fa nayi maka Khaleel baka amsa ba Amma kake min maganar Wata Wai Khalfana" "Afwan Dan Allah Dan Allah ka taimake Ni" "Khaleel kana lafiya Kuwa jibi yadda ka wani rikice" "Wallahi in ma lafiya nake to ba kalau ba Ni dai kawaii ka taimaka min na samu numb ta."

"Ka kwantar da hankalin ka yallab'ai in dai numb Khalfana ne ka samu,Bari naje gidan su Sufyan d'in"

"Kaje ko muje ai kafata kafar ka,Bari na watsa ruwa" tashi yayi ya watsa ruwa ba b'ata lokaci ya shirya kunsan Shirin maza Yar sharp sharp ne Lol🤣.

Wata farar Kaftan yasa wadda aka yi Mata zubi da ruwan bula, haka ma hular sa da takalmin sa duk Kala d'aya agogo yasa Mai ruwan Gold sai sheki yake, wayar sa kawaii ya d'auka da makullin motar sa suka fice daga quarters d'in.

suna Isa Idris ya Kira Sufyan ya Sanar dashi cewar Yana quarters d'in su ba b'ata lokaci Sufyan ya fito, bayan sun gaisa yace "Bismillah ku shigo Mana" Idris yace no Kar ka damu Nan ma yayi"Khaleel sai kalle kalle yake ko Allah zai bashi sa'a yaga abar Kaunar sa sai idea yazo Masa yace "Sufyan Kar ka damu Akan hanya muke restaurant zamuje" "Restaurant Kuma, a a bazaiyu ba kuzo mu shiga kawaii Ni d'inma abinci zanci yanzu kun iya noma" ya karasa maganar cikin zolaya.

Idris yace "Ai ko zanci Ina fatan girkin Mummy ne, Gaskiya Mummy she ia a great cook"

"Toh Long Throat, Big Aunty na Nan ai baza ta Bari mummy tayi girki ba"

Idris yace "Ai girkin Mummy da Na Big Aunty ba ban banci baza ka ma San Wacce tayi ba,mu shiga kawai."

suna tafiya suna Hira har suka shiga cikin gidan su Khalfana wani katafaren parlor na gani na fad'a Wanda idan na tsaya muku fad'a muku sai mu b'ata lokaci.

Haryanzu Khaleel sai kalle kale yake, Sufyan Yace "Oga lafiya Kuwa me kake nema ne"?

"Ba Komai ,Kawai daai tsarin gidan naku ne ya burge Ni" murmushi yayi yace "Godiya muke."

Nan suka fara haura saman stairs har suka shiga d'akin Sufyan,babu Wanda ya sake magana , d'akin Sufyan ya had'u iya had'uwa sai kace d'akin Mai mata🙄.

"Bismillah ku zauna Bari na Sa a kawo Mana abincin anan"

Fita yayi ya nufi kitchen , Wata mata na gani wacce baza ta haura shekaru arba in ba , Yana shiga yace "Baba sannu da aiki" "Yawwa d'an har ka fito" "Eh Baba abinci na fa"? "Abincin a had'e yake ai kasan Khalfana bata son rabiyan abinci tunda ta Gama ta sa flask " "Toh Dan Allah a samin nawa nayi baki" "Toh Shikenan je ka same su yanxun Nan za a kawo muku" "To Baba."

sai ya fita a hanyar sa ta komawa d'aki ya ga Khalfana na waya bata ganshi ba, Dake ta juya Masa baya,zuwa yayi ya mutsine ta ji nayi ta sa wani Kara , har sai da ta kusa yarda wayar a kasa shi Kuwa ya shiga aikin yi Mata Dariya harda rike ciki tace "Amma Sufyan Kai ko, zo Nan" nan ya Ruga a d'ari ya shiga d'akin sa ita ma bin bayan sa ta yi da gudu tana fad'in "wallahi ka tsaya sai na Rama" Kai tsaye ta shiga d'akin ,ganin sa tayi kwance a kan gado ba b'ata lokaci tayi kansa har ta Kai Masa bugu sau d'aya sai taji motsi ta gefen ta, taga Ashe bashi kad'ai bane a d'akin da sauri ta juya ta fita, dukkan su Dariyar ta sukayi.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Khaleel da tunda ta shigo ya kasa motsi har ta fita Yana kallon kofan, Idris ya d'an tab'a shi yace "Dad'ina da Kai Kenan haba Dan Allah" Sufyan Dariya yayi yace "Kanwata ce kana son ta ne"? Idris yace "Bari ta jika, Khaleel Sufyan kanin ta ne."

"haka ne ga kama Nan,Sufyan maganar gaskiya ina son Yar uwar ka Kuma da Aure Dan Allah ka taimake ni kamin way da zanyi magana da Mahaifin ku."

Sufyan tashi yayi ya zauna yace "Masha Allah naji dad'in hakan, don Kai mutumin kirki ne duk da magana bai tab'a had'ani da Kai ba Ina Jin yadda mutane ke yabon ka, gashi dai ka girme mu da kusan shekaru 10 ko fiye da hakan ma, shawara d'aya Zan baka a yanxu shine kar ka tunkare ta, sannan kar kayi wa Daddyn mu magana"

"To Amma meyasa kace haka"?

"A halin yanxu ta sani kalmar so, Mahaifin mu Kuma yace sai ta Gama Jami'a."

Khaleel a ransa yace "ta tsani kalamar so, to meyasa"?
"Sufyan Dan Allah ka taimaka min wallahi tallahi Zan iya samun matsala"

"Look kwantar da hankalin ka, Zan Kai ka gun mom don tafi dad saukin Kai, duk yadda tace hakan za'a yi"

"To nagode sosai"

"Bakomai Bro in law😁"

Duk sukayi dariya, Sufyan Yace "bani wayar ka plz", Mika Masa yayi, sai ya tura Masa hotunan Khalfana sama da hamsin sannan yasa Masa number ta, Mika Masa yayi sai yace "gashi kayi saving,ko don gaba " "Nagode sosai bara na yi saving" (ni ko Jin hakan yasa na leka don ganin da me ze yi saving gani nai yayi saving da *Rabbaitul Bait*, wow ,Mom Arpat kin San ma'anar sunan Nan Kuwa, Bari na fad'a Miki Yana nufin *Matar Gidana* maza ki fad'awa Abban Arpat ya canxa Miki suna ke Kuma ki sa Masa *Zaujul Bait*😁😁 nayi nan🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️)


Sallamar Ladi suka ji Sufyan ya amsa yace ta shigo, ajeyi mu su abincin tayi ta fice, Idris ne ya bita da kallo yace "mutumina Yarinyar Nan fa ta girma, ba ita ce jikar baba ba"?

"Eh itace " "Ina ciki" "kana cikin ruwa in fact kana teku" Khaleel Dariyar su kawaii yake.

Zuwa sukayi suka zauna a karamin table d'in da a ka jera musu abincin Tuwon sakwara ne da egusi soup😋 duk yawan abincin Nan sai da suka cinye shi tasss.

Bayan sun Gama ci Sufyan Yace "Tashi muje ku gaida mommy" da sauri Khaleel ya Tashi , Idris yace "innalillahi Kai ko irin kunyar Nan ma baka ji" "to kunyar me zanji ai harkar neman Aure ba kunya ko ya kace Bro inlaw"?

"Eh haka ne" suna tafiya suna Hira har suka Isa part d'in mummy Sufyan Yace "Kila ma Khalfana na ciki " da Sallama ya turo kofar parlor, Mummy ce ta amsa suna shiga suka zauna, Khaleel ya zauna Akan koshin d'in da yake facing na Khalfana kallon ta yake ta gefe, ita ko bata San ma sun shigo ba tana aikin kallon zee world d'in da ta saba , bayan Idris da Khaleel sun gaida mummy sai suka Fara Hira Dake dama sun saba da Idris tun Yana yaro suke tare da Sufyan, Khalfana duk sun Dame ta da surutu , Yar karamar tsaki ta jaa , Tashi tayi ta d'auki wayan ta ta fice Bata kalli inda suke ba, d'akin ta ta shiga ta kunna TV ta cigaba da kallon ta.

Sufyan ya kwashi duk yadda sukayi da Khaleel ya fad'awa mummy, mummy tayi farin ciki da Jin hakan don tana jin labarin sa, tace "zanyi wa Daddyn ku magana tukunna duk yanda mukayi zakuji" sun dad'e suna Hira duk da Khaleel bai cika sa musu baki ba bayan sun Gama sai suka Mata Sallama.

Bayan sun Koma gida Khaleel kamar a mafarki yaga pictures d'in Khalfana a wayar sa yayi murna sosai ko ba komai hotunan zasu Rika d'ebe Masa kewar ta.

Yace a "Aikin Sufyan ne"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Haka rayuwa ta kasance, Khaleel so da Kaunar Khalfana Kara hauhawa yake a zuciyar kamar farashin gold.😁


A yau ne hutun su Khalfana ya kare sun shirya tsaf suna jiran driver ya Kai su park Daddyn su Zee Kiran Mahaifin Khalfana yayi yace "a had'a su da sojoji 2 a Kai su har cikin school"haka Kuwa akayi, Alhamdulillah they have safely arrived.💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Gidan aunty Fatee suka Fara zuwa sukayi dropping d'in Khalfana sannan suka wuce da zee.

Zuwa yanzu Khalfana ta mata da wani Wai Maan, rayuwar ta take cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali , Rayuwar su acikin makaranta da ita kawayen ta Zainab da Azeemah sai dai ace Masha Allah, lokaci zuwa lokaci takan Kai wa Momy ziyara,(Momy nitsuwa ta Zo)🤣🤣.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Yau Saturday Khalfana ta dawowarta daga school a gajiye tana shiga parlor ta wullar da jakar ta akan koshin kana ganinta kasan akwai gajiya a tattare da ita, aunty Fatee ce ta ke saukowa daga matakala a hankali tace "Yar jima'a yaushe kika shigo banji shigowar ki ba"? "Yanxu na shigo Aunty, ha'ah d'azu kince akwai aikin da zaki karasa ba zakije bankin ya Kuma na ganki a gida"? "Eh dawo wa nayi bana Jin dad'in jikina ne"

Mikewa Khalfana tayi ta nufi inda aunty Fatee ke zaune tace "sannu ya jikin"?
"Da sauki Alhamdulillah, Khalfana ya kamata a nema Miki mota fa wahalar Nan tayi yawa"

"Aiko aunty kamar kin karanta abinda ke Raina, d'azun Nan mukayi magana da zee "

"Mayu kawaii, Zan fad'awa Dad" "to aunty mun gode"

"Khalfana albishrinki "
"Goro"

"Naje asibiti likita ya gwada ni ya Kuma tabbar min da cewa Ina da cikin wata 3"

Tsalle Khalfana tayi sannan tace "Oh My God aunty are you serious"? Kai ta d'aga Mata alamun eh.

Khalfana tace "Alhamdulillah Allah mun gode make , Allah ubangiji ya sauke ki lafiya yasa ki haifi mace Amin takwara"

Aunty Fatee dariya tayi sannan tace "Naughty girl , Ameen"
Nan sukayi ta Hira Aunty Fatee tace "ya kamata kije kici abinci " "ai Aunty labarin da kika bani yasa ya kosar Dan......" Kan ta karasa maganar da take yi sai taji wayarta na ringing Tashi tayi ta bud'e jakara ga mamakin ta sunan *Abban Hanifah* ta gani tana kallon wayar da mamaki Aunty Fatee tace "wane ne"? Kalfana tace "Aunty Maan ne fa" gyara zama tayi tace "wani Maan d'in "? "Alhaji Maan" "kiyi picking sa a handsfree muji me zai ce" picking tayi tace "Assalamu alaikum" ajiyar zuciya yayi yace "wa alaikissalam salam" bayan sun gaisa ya shiga Bata hakuri , "nasan na cutar Dake Khalfana Dan Allah kiyi hakuri" "laifin me kamin ni baka min laifin komai ba" nayi Aure ba tare da na Sanar Dake ba" "laaah Suleiman Ashe kayi Aure, ban sani ba ai yaushe akayi hakan"? Murmushin takaici yayi yace "My Khalfana nayi missing d'inki " "haka ko"? "Eh" "okay sai anjima Ina d'an aiki ne" ta katse wayar ba tare da Taji me zaice ba.

Aunty Fatee dariya ta shiga yi "Khalfana yau naga ikon Allah, yaushe akayi auren da har ya Fara neman ki"? "Ai Ina tunanin yanxu Wata d'aya Kenan"
"Lallai nasan dama zai neme ki Amma Wata d'aya yayi kusa" dariya sukayi Khalfana ta shiga ta watsa ruwa , Uncle Jin labarin Matar sa na da ciki yayi mutukar farin ciki, tasha kyaututtuka.

Maan yana wayan Kiran Khalfana Amma ko kad'an baya gane kanta, sannan bai gaji da bibiyar ta ba.

*Bayan Wata d'aya*

Kalfana da zee an saya musu sabbin mota iri d'aya Mercedes Benz baka motar ta had'u ba karya.

Wannan Kenan

Bangaren Khaleel an tura shi kasar waje don kwantar da Wata tarzoma da ta Parke a kasar Iraqi, a kullum baida aikin yi sai na kallon pic d'inta bayan ya dawo Nigeria, ya samu har ta koma baiji Dadi ba Amma ya zama dole ya yayyafa wasl zuciyar sa ruwan sanyi, bayan sati d'aya da dawowarsa ya nemi Idris ya rakashi gidan su Khalfana, Mummy Taji dad'in ganin sa "Khaleel nayi magana da Mahaifin Khalfana ya ce na ba ka hakuri in dai zaka iya jiranta tana aji 2 yanzu next year sai ka Zo ka gabatar da kanka" "Insha Allah Mummy Zan jirata" tayi Masa fatan Alhairi.


Yau weekend Zainab, Khalfana,da Azeemah sunyi Shirin fita outing sai Adam ya nemi su had'u da Khalfana,ta Sanar dashi suna gida , bai b'ata lokaci ba yazo bayan sun gaisa yace "Khalfana hakika Allah ba azzalumin bawan sa bane Maan ya auri bala'i,in fact ya auri mutuwar sa" "kamarya ya auri mutuwar sa " "Yusrah muguwa ce Mara imani tana wahalar da abokina bai tsaya akan sa ba har da 'ya'yan sa" wayar sa ya zaro ya nuna Mata wani hoto Khalfana na gani ta kama baki "innalillahi" sai hawaye wiwiwiwi sannan tace "kamar Haneefah" murya na rawa "eh itace " zee ta karbi wayan ta gani bayan ta gani ta mikawa Azeemah ita ma ta gani, Khalfana tace "me ya sameta accident sukayi"? cikin muryar kuka "a'a yusrah ce ta Dake ta da muciya sannan ta watsa Mata ruwan zafi da gishiri" "Allah Sarki Allah ya isar Miki" Adam yace naga kamar fita zakuyi"?

Zainab tace "eh fita zamuyi" Adam yace "Khalfana please find a place in ur Heart to for give my friend har yanxu Yana sonki, ki taimaka ya aureki,kece kad'ai Zaki gyara komai tunda gashi yace zai sake ta an Hana shi" Bata ce masa komai ba Sallama ya musu ya shiga motarsa ya fice daga gidan.

Azeemah tace "Khalfana meyasa kike kuka"?

"Zeemah baki ga yadda taji wa yarinyar Nan ciwo ba bayan ta karya Mata hannu ta watsa Mata ruwan zafi Kuma da gishiri haba rashin Imanin yayi yawa"

Zee tace "Allah ya Kara naso da shi tasa a tunkuya tasa man gyad'ata soya shi".

Murmushi Khalfana tayi ta share hawayen ta da bakin gyallen ta , tace da wani mota zamu fita ne"?

Zee tace "ai duk d'ayane ni dai bazan yi driving ba"

Khalfana tace "ni zanyi kar ki damu" mika Jakarta tayiwa zee sannan tace "ku shiga Ina zuwa" Kai tsaye kitchen ta nufa ta d'aura ruwa a babban tukunya ta d'auki ledan gishiri guda d'aya ta juye duka a ciki,sai ta haura d'akinta, hijab ta sa, sannan ta sauko ta samu ruwan har ya tafasa Dake a kan gas cooker ne, wani babban flask naga ta d'auka ta juye ruwan aciki, ta d'auko wuka har ta fita daga kitchen d'in sai ta dawo ta d'auki tab'arya.

Tana fita ta fara leke tace "Alhamdulillah aunty ta Tashi" tafiya take a Hankali daka ganta kasan Bata da gaskiya.

Tana fita ta nufi inda sukayi parking motar sai tace "zee bud'e min Booth" da mamaki zee ta fito ta bud'e mata tace Khalfana me za kiyi da wa'annan abubuwan"? Sai da tasa tab'aryan a booth saii ta kalleta tace "in munje Zaki gani,shiga mutafi" Zeemah na zaune a baya Bata San me ke faruwa ba gani kawai tayi Khalfana ta Mika Mata flask karb'a tayi aje, wukan Kuma ta aje a gaban motar, wayanta ta Ciro a Jaka ta shiga Kiran Layin Sani bayan ya yi picking sun gaisa sai tace "Dan Allah yimin kwatance gidan Suleiman" "gidan Suleiman Amma lafiya dai ko"? "Lafiya kalau na shigo unguwar ne shiyasa nace ya kamata na Kai wa amarya ziyara" murmushi yayi yace "to shkn" Nan ya shiga yi mata kwatance , bayan ya Gama tayi Masa godiya ta katse wayar wani iriyar murmushi tayi Wanda ita kad'ai tasan dalilin yin hakan, Wata bakar eye glasses ta d'auka tasa, sannan ta tada motar , baba Mai gadi bud'e Mata gate yace sannu " 'yata" ko kallon sa ba tayi ba zee ce ta amsa
Yace "Allah yasa lafiya".

Yana bud'e gate d'in ta fita fuuuuuu.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*Mu had'u a page na gaba*

*Daga Alkalamin Fadeelah Yakubu* (💞 Milhaart💞)

Please share and Comment🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣3️⃣5️⃣↔️1️⃣4️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Tunda suka fita daga gidan babu Wanda ya yi magana, don Azeemah da Zainab mamaki suke tunda suke da Khalfana Basu tab'a ganinta a cikin irin wannan yanyin ba, parking suka ga tayi a wani katafaren gida, gidan ya had'u iya had'uwa kud'i ya zauna.

Khalfana tace "Yes Nan ne gidan"

Zee tace "Wani gida"?
Khalfana tace "Ina zuwa" cire eye glass d'in Dake idonta tayi ,fita tayi ta nufi gate d'in ta kwankwasa wani mutumi ne ya fito da alama shine Mai gadi, bayan ta gaida shi ta Sanar dashi "gun Matar gidan muka Zo na Kira wayanrtaa bata shiga" yace "Bismillah ku shigo" komawa tayi ta jaaa motar xuwa harabar gidan, zee da Zeemah mamaki suke har yanzu Basu fahimci abin da Khalfana take Shirin yi ba.

Khalfana tace "Zee, Zeemah ku shiga cikin gidan Nan ku gaisa da Matar gidan idan tana Nan kimin flashing sannan ku Sanar da ita Abu zaku d'auko a mota,kin gane"?

"Eh na gane, Amma Khalfana me Zak......."

Buga siterin motar Khalfana tayi da hannun ta da karfi tace "Ohhhhhh Zee please this is not the right time kiyi abinda nace kiyi please" cikin tsawa,zee fita tayi da sauri don ta tsorata sosai Azeemah ita ma bin bayanta tayi, suna sallama Wata ce ta bud'e musu kofar zee tace "Matar gidan na nan"? "eh tana Nan Bismillah ku shigo" suna shiga, suka ga Wata Fara siririya, tana tauna cingam ta d'aura kafa d'aya Akan d'aya, daurin kanta ture kaga bala'i tayi tana kallon su sama da kasa Tace "bismillah ku zauna" bayan sun zauna zee Tace "Ina wuni" "lafiya" tana latsa wayar ta azeemah Tace "Dan Allah Yusrah muke nema, d'ago kanta tayi Tace "Nice Yusrah lafiya"? "Lafiya sako aka Aiko mu kawo Miki" "okay Yana Ina"? (Ni ko nace ji Jaka Bata ma tambayi was ya Aiko sakon ba mswwts) zee Tace "Yana Mota" sai suka Tashi suka fita, yadda Khalfana ta umurce su haka sukayi Khalfana na ganin Kiran zee ta kyalkyale da dariya harda tafi, fita tayi ta bud'e Booth d'in ta d'auki tab'aryan sannan ta bud'e bayan motar ta d'auki flask d'in sannan ta d'auki wukar zee da Azeemah na Isa inda take tace "Khalfana Dan Allah me kike Shirin yi ne"? "Zee zaku ji komai in na fito"

Zeemah tace "Khalfana mu biyo ki"?.
"A'a Zeemah ku shiga mota ku jirani"

Sallama Khalfana tayi taji ba a amsa ba sai ta tura kofar parlor sai ta hangeta tana haurawa sama, da alama d'aki zata shiga, Khalfana tace "Perfect"

Bin bayanta tayi a hankali Dake Yusrah ta sa ear piece a kunnenta shiyasa Bata ji shigowar ta ba, bud'e kofan d'akin ta tayi tana shiga zata maida kofar ta rufe sai taga inuwan mutum kan ta Ankara sai taga mutum a tsaye a kanta da sauri ta jaaa baya ta dafe kirji tace "Na shiga uku" Dariya Khalfana tayi sai tace "Yusrah kwantar da hankalin ki Nima mutum ce kamar ki, Innalillahi ya kamata kice ba kin shiga uku ba,in Kuma mutuwa ce fa? Zaki mutu da kalmar kin shiga uku Kenan fa" tana maganar tana sa Kai a d'akin ita Kuma Yusrah a tsorace take komawa cikin d'akin, Khalfana na shiga d'akin ta kulle da makulli ta cire ta aje a gaban mirror,

"Dan Allah wace ce ke, me na Miki Dan Allah kar ki cutar Dani" Yusrah ganin wukan Dake hannun ta yasa tayi shiru, Khalfana tace "Yusrah Yusrah, Kar na cutar da ke ko Amma kika cutar da wata"

"Ni wallahi ban cutar da kowa ba"

"Shhhhhshh yimin shiru"
tana matsowa kusa da ita har sai da ta Kai kusuwar d'akin, marin ta tayi Wanda yasa Yusrah har ta Fara ganin duhu, ba b'ata lokaci ta d'auki tab'arya ta Fara Kai Mata duka dashi ta ko Ina Yusrah ihu take tana neman agaji amma babu Wanda yaji ihun ta, Lami Yar aikin ta Kuma sallah take shysa Bata fito ba,

Khalfana sai da ta Mata jina jina, sannan ta d'auki wani zani da ta gani a yadde a kan gado d'auka zanin tayi ta d'aure Yusrah dashi, Yusrah rokon Khalfana take Amma Bata ce Mata komai ba , sai da ta d'aure ta sai tace "wawuya kazama dubi d'akin ki kina mace" Yusrah Tace "Dan Allah ki min raai me na miki"? "Tsawa ta Daka Mata "yimin shiru munafuka, Don ubanki ne nake bada raai, ki ka Kara yimin magana wallahi Zan yanka ki da wukan Nan" wani yawu naga Yusrah ta hadiye da kyar ya wuce makoshinta, (har Saida naji karansa😁)

Ji nayi wurin yayi tsit kamar ba mutane a gun, Khalfana yanke jikin Yusrah ta shiga yi Yusrah na ihu Amma baya fita Dake ta rufe Mata baki da zani, tace "Babu Wanda zai ji ihun ki, ki kwantar da hankalin ki bazan tab'a Miki fuska ba,sannan bazan kashe ki ba yanda kikayi wa Haneefah na Zan Miki".

Yusrah a zuciyar ta tace "wato itace Mahaifiyar Su Haneefah".

Flask d'in ta bud'e sannan ta bud'e Mata baki, tace "Yawwa ruwan zafi da gishiri kika watsa Mata ko,Nima ga nawa" Yusrah tace "Dan Allah kiyi hakuri kiga yadda kika ji min ciwo jini na zai kare" cikin muryar kuka "Ai so nake ya kare munafuka algungunma" maida zanin tayi ta rufe Mata baki ruwan ta Fara zuba Mata akai Yusrah ji take kamar zata mutu, so take ta tsosa Amma ba Hali an d'aure ta, sai da ta juye Mata ruwan tass sannan ta d'auki wayar ta da tunda ta shigo ta aje shi tare da key, tace Mata "idan Wawa

Please Login or Register in order to submit comment