Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RAHIM*

*PAGE* 6️⃣5️⃣↔️7️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Havilla ice cream suka nufu inda suka Zauna Na tsawon lokaci Suna ci suna Sha Kan suka dawo da emmatan gida
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Next Day

Kwanaki 2 knn Kalfana Bata Je lectures ba hkn ne yasa ta shirya da wuri Bayan ta Karya ne ta leka Dakin zeemah, Alhamdulillah jiki ya warware Kamar Na ita ba, sukayi wa juna fatan alhairi ta fice, Kalfana Bata dawo ba sai karfe 8 Na dare, ta tsaya a Na mata tutorial, shigowar ta knn ta sinkayo muryar Momy Na cewa, "Mujeedat ko lafiya Ina ta Shiga tunda yamma Na dawo ban ganta ba, bara Na Kira numb ta" Kalfana ta Shiga da sallama ta Na murmushi "Momy ba sai kin Kira ba Gani nan" Momy dariya tayi "Ja'iri Na kika Shiga hka?" "Momy Ina schl Muna Shirin Fara test" "Okay Allah ya bada sa'a" "Ameen Momy, Momy Azeemah fa?" Tsaki Momy ta Jaa Mai tsawon Kan tace "Tana waje Wani Wai Dr Abdulaziz yazo" "oh Allah sarki Dr Na Zeemah, Momy Bari nayi sallah Naxo Na Karbi sarabata" "Toh to a fito lfy" Kalfana Na Shiga da'ki Momy tabi Bayan ta da harara da Wani irin murmushi Wanda ita kad'ai tasan dalilin ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana Shiga wanka tayi tasa sleeping dress tayi sallah, Bayan ta idar da sallan ne taga Abun mamaki, hijab dinta da tade tana nema, "Ha'ah ya akayi hijab din ya shigo bayan kofar a rufe?" Shiru tayi sai tayi murmushi "Hmmm wato ta window aka jefo min dakyau" tana d'aga hijab din taga Duk dirty ga Wani uban wari da yake yi, Ranta ne ya b'aci sosai wato sun bata baza su Iya wanke Mata ba, kwanciya tayi Bata Tashi ba sai karfe 10 da rabi, Shidin ma Kiran Ya Maan ne ya tada ita, Bayan sun gaisa yake nuna Mata Baya Jin dad'in yanda take nuna rashin kulawa a gare Shi, hakuri Kawai ta bashi, Amma Har ga Allah tana sonshi Amma ba Kamar da ba, Bayan sun Gama wayar ne ta d'auko hijab din nan ta wanke ta Shanya a waje ta Koma tayi baccin ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
*Washe Gari*
Kalfana lectures dinta na yau sai yamma, Bayan ta idar da sallan asuba ta Koma bacci Kamar yadda ta Saba bayan ta Ga tilawar al-qur'ani , sai karfe 9 ta fito, fitowar ta knn bayan sun gaisa da su Momy Afra tace "Kafa kince baki ga hijab dinki ba Kuma gashi Har kin wanke" "Eh Nima dawo Wata jiya Na Gani a Kan gado, ban San ya akayi haka ba" Kan ta Kuma Ce Wani Abu Momy ta fito da masifa "Ke Mujeedat ki kiyaye Ni kin Maida mutane barayi Ni ban haifi baro ba, Yar iska Kawai" ta inda take Shiga ba tanan take fita ba
"Dan Allah kiyi ki Koma hostel kinxo kin takura Ni da 'ya'yana" cikin tsawa Kalfana tace "Ko Kuma Kuka takurani ba, kene zagi kene habaici Duk nasan da Ni kike amma Na Maida kai Na wawiya, Sannan tarbiyar da iyayena suka d'aura Ni Akai knn Girma Na gaba"
"Mujeedat Ni kike Yi Wa tsawa?" "anyi Miki din" yarfa hannu Momy ta Shiga yi tana sallallami, "Wallahi Na gaji da yarinyar nan kiyi ki tafi don Allah" "Kamar yadda Nima Na gaji Dake, kud'i kike Biya Nima Shi Nake Biya Koda ace nan Gidan ki be ba ki Isa ki koreni ba bare ma ba Gidan ki bane" momy Mamaki take "dama haka yarinyar nan take, Tabbas boye Halin ta tayi"

Ni ko Nace Momy zuciyar Mai hakuri ba kyau in baki Sani ba ki Sani.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Kalfana shegewa d'akin ta tayi, sai hawaye wiwiwiwi "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un Yau nice nakeyi Matar da ta Kai ta haifeni tsawa?"wayar ta ta d'auko ta Kira Dady Yana picking ta fashe da Kuka ta kwashi Duk abinda ya faru ta fad'a Masa yace "Shkn kiyi Shiru kukan ya Isa haka" Amma Ina sai abinda ya Karu "Ke don Ubanki baza kiyi Min Shiru" chiiiit naji Kamar anyi Ruwa an d'auke "ke tunda kiga hijab din me Na Kuma Na Magana ai da sai kiyi Shiru" "Daddy sun shigo da rainin hankali ne ya Za a Yi Na wanke Abu ban San ba a dawo Min dashi Duk datti, Naji mistake ne sukayi ta d'auka nasu ne,Kuma sun San Ina nema meyasa baza su fad'a Min sun Gani ba Amma suka ajiye min Shi and yet Har da zagina" "banji Dadi ba Kalfana yanzu mamar tasu take?" "tana waje" "Kai Mata wayar" "Toh" Kalfana nafi ta ta Mika wa Momy waya "Gashi babana Yana son yin Magana dake" "In baki matsa Min Annan ba sai Na wanka Miki Mari Bazan karb'a din ba ya Aiko da sojoji su kama Ni" cikin fushi da izza, Kalfana tasa Wayan a kunne "Daddy ka......." "Kiyi Shiru Kar kiyi magana Sannan Kar ki kashe" Momy sai ashariya take Yi marasa dad'i Daddy kashe wayar yayi sannan ya sake kiranta yace "Kina Ina yanxu?" "Ina tsakar gida" "Shiga da'ki Kar ki sake magana, inazuwa Bari Na Kira Auntyn Ku" ya katse wayar.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan ta Koma d'aki ne sai taji ana sallama Amma Momy Basu amsa ba da akayi Na 2 sai ta d'auki muryar Ashe zee Ce da sauri ta Taso ta bude Mata Kofa Sannan suka Shiga cikin d'aki, Zee kasa gaida Momy tayi don Jin yadda ta ke Ashar, Basu bi takanta ba suka farayin assignment din su, chaan sai sukaji Momy Na waya da Alama da mijinta take "Wallai tallai Dady am telling Kalfana ta zage Ni" Dady yace "Ya Salam habiba, Kalfana Ce ta zage ki, ban yarda ba gsky" Momy sai surutai take Dady yace "Look woman in baki da aikin Yi Ina dashi" sai ya katse wayar.
Zee tace "Kalfana Kamar da ke take koh?" "Eh mana Je da Duk kin d'auka da wa take?" "Kutccc shine kikayi Shiru?" "Toh zee me xance Mata?" Zeee tace "Dama Na fad'a Miki Mutanen ba sonki suke ba" murmushi Kawai Kalfana tayi Jin surutun Momy yayi yawa Kalfana tace wa "Kinga Tashi mu Shiga school baza mu Iya komai anan ba an Maida mana gida Kamar Gidan Yan giya" Shiri ta Yi cikin shigar jeans da T-shirt, tasa safa Sannan ta d'auki hijab Har kasa Wanda ya rufe har kafarta, ta d'auki Nikab ta rufe fuskarta tace "zee Tashi mu tafi" "Kalfana Wai ke yaushe Zaki daina dressing din nan sai a d'auka kina da aure " dariya ta Fara "Ai ma kin tuna Min kin San yadda mukayi da Saleem kuwa?" "A'a sai kin fad'a" "Ya tab'a cewa Yana Sona ban amince ba Amma Duk da Hakan Yana bibiyata, a lokacin da Na Fara sa Nikab ya tmbye Ni, Kalfana meyasa kika Fara sa Nikab?, Wanda Zan aura ne ya hanani fita a haka, kin San me yayi masallaci fa zamu Je Amma ya canxa hanya Ina ta Kiran Sunan sa bai juyo ba bare ya Amsa" ta Kara sa dariyar tana dariya da karfi zee ta Shiga tayata zee tace "Wannan Shi Ake Kira da Self respect" suka cigaba da dariya Har su Momy Na Iya jiyosu Har ji take Kamar da ita suke, fita sukayi Suna Hira Har suka fice Basu Kula Kowa ba.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Ba suyi Nisa ba sai ga Kiran Daddy tayi d'aga cikin farin Ciki Shi kansa yayi mamaki Amma Kawai ta batsar "Na Kira Auntyn Ku anjima zata zo, kina Ina yanxu"? "Na fito Zan shiga makaranta" "Toh in taxo fa Zan Kira ta yanxu sai Na fada Mata Kan ta Tashi ta Min Magana" "Okay yayi ya Matar Gidan naku?" "tana chaan sai Ashar take tayi" "Hmmm Ai Duk Naji abinda tace ban tab'a sanin haka take ba, da tana da hankali da zata Karbi wayar tunda Ni Na Aiko ki" "haka ne Kam" "Ya Labarin Zainab Kuna had'uwa kuwa ?" "Ai kullum Muna tare yanzun ma hka" "Okay bata mu gaisa" mikawa zee wayar tayi Suna tafiya Suna wayar Bayan sun gama gaisa wa ya katse wayar.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan ta Karbi wayar ta, ta Shiga Kiran layin aunty Fatee Amma Kan ya Shiga Kiran Aunty Fatee ya shigo ta d'aga , Ji tayi aunty Fatee Na dariya, Dake kalfana Na fad'a Mata Duk abubuwan da suke Mata Har da yadda Azeemah ta had'a baki da Faisal a Mata fyade, Aunty Fatee Daga wawwatan Kalfana tayi Mata fad'a sosai, "Kalfana Yau Kuma me ya faru?" ta fad'a Mata komai tace "okay Bayan sallar azahar Zan zo, Kar fa ki sake Amsa mata" "Aunty Ai Bana Gidan Zan Shiga school" "okay sai nazo" ta katse wayar.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Karfe 12 suka Gama Duk Wani Abun da sukeyi a makaranta ta , sai suka dawo gida abin su, Suna Shiga Dakin Kalfana sukayi Kai tsaye, Zeemah Na ganin su ta bi Bayan su, "Kalfana kiyi hakuri da abinda Momy ta Miki d'azu wlh banji dad'i ba" "Zeemah don't worry ai ba laifin ki bane" "laifina ne Amma Bazan Iya Gaya Miki dalilina Na fad'in haka ba, Amma in da nice ke ko Bazan sa hijab din nan" tayi saurin fita Zee tace "Something is definitely fishy, Kalfana are u thinking wat am thinking?" "Zee Dan Allah share su Na gaji da Jin maganar su, yunwa nk Ji me Zan dafa mana ne?" "Macaroni plz" Bata Dade ba ta Gama girkin ta juye musu suka cinye tass don girkin yayi Dadi yasha kayan had'i, a wurin bacci yayi awun gaba dasu.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
A cikin bacci taji Azeemah Na fad'in "Sannu da zuwa Aunty Fatee" Aunty Fatee ta Amsa "Lafiya Lau Azeemah ya kuke?" "Lafiya" "Toh Sannun Ku" d'akin Kalfana ta Shiga da sallama "A'a Yan Boko sanannun Ku Yan Boko irin Wannan bacci haka da Alama ba kuyi sallah ba" Kalfana Ce ta Tashi tana Miki "Sannu da zuwa Aunty baki Zauna ba" Zama tayi tace "ki tada Zainab kuyi sallah " "Toh aunty" Kalfana sai da tayi alwala Kan tazo ta tada zee, Duk sukayi sallah Aunty Fatee Na zaune tana chat, Bayan sun idar ne aunty Fatee ta Ce da Kalfana ta fad'a Mata yadda Abun ya faru, Bayan ta Gama Sanar da ita ta Tashi ta fita, "Azeemah Ina Maman Ku?" "Ta fita" "bara Na Kira ta" ta Dade tana Kira not reachable, Azeemah tace "Aunty Fatee Bari Na Aiko Zu Afra su Kira Miki ita" "Yawwa nagode". Zee baccinta ta koma
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Shigowar Momy da sallama, "Ina Aunty Fatyn?" "Maman Azeemah Gani" Tashi tayi suka gaisa ba yabo ba fallasa, Aunty Fatee tace "Maman Azeemah me yake faruwane Muna Jin dad'in Zaman Ku da Kalfana Amma Yau banji dad'i ba" Momy tace "hmmmm aunty Fatee Kalfana ta Bani Mamaki kullum sai ta mana sharrin sata, tace mana bamu da addini" "Ya Salam Abu baiyi dad'i ba Kalfana fito" wuri ta Samu ta Zauna Momy Karya take tsarawa kalakala ta fad'i Wannan ta fad'i wanchan, Aunty Fatee Ranta ya b'aci sosai ganin yadda take b'ata Kalfana,Bayan tasan Kalfana tun tana yarinya, "Kalfana meyasa kikayi haka?" "Wallahi aunty ba hka bane, Kiji fa Wai Muna gulmanta da qawayena" "su Waye qawayen naki?" "Aunty Duk kin San su fa, Zainab,Faty,hafsa,falmata da Zahra kin San mu tare mu 6 bamu rabuwa, in ba yanxu da jamb suka Hana Sauran admition ba" "Suna zuwa ne?" "Sosai ma bamu sati 2 bamu had'u ba in Basu zo ba Ni zanje Gidan daya Daga cikin su sai mu had'u Duk a Chan" "Maman Azeemah kin tab'a Ji Suna maganar ki ne ko Kuma d'aya da ga cikin qawayen nata ne suka fad'a miki"? "Sun Isa su tunkareni da irin maganar nan ne?" "Aunty zargina fa take Yi" "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un see this small girl Ni take fad'awa Ina zarginta" tana d'aga hannun ta Sama "Haba Maman Azeemah zargi Yana nufin Accuse nothing bad" "Aunty Fatee Wallai tallai Ina son Kalfana fiye da yadda nake son Azeemah" Kalfana saurin d'ago Kanta tayi ta Kalli Momy, zee Jin haka sai da ta Tashi ta leka ta window, a Ranta tace "lallai Matar nan Yar bariki Ce Kutt" Kalfana Kuma aranta cewa take "Taya Za a yi ta Soni fiye da yarta?" Aunty Fatee tace "eh ana hka" ammafa Bata yarda ba "Maman Azeemah to Dama Kuna samun matsala ne?" "A'a wlh ai Kalfana tana da respect ba ruwanta Duk abinda Nace tayi Shi takeyi,Ga ilimin Boko da addini AI tana karawa su Afra karatu yanxu be da abubuwa suka Mata yawa ta daina" "Toh Alhamdulillah, yanxu daai a bar tone tonen haka komai ya wuce Ku Koma yadda kuke a da" "Da wa Dani Wallahi a a kuje chaaan kuje chaaan Ku karata" tana d'aga hannun ta nuna ta inda unguwar su Aunty Fatee yake, "Haba Maman Azeemah sulhu Ake nema kice aje chaan, yarinyar nan da gatan ta fa Kuma Muna sonta in ba don makaranta ba me Zai sa ta Zauna a nan, Kuma Nace miiki Ku Koma din bawaii don baxa ta Iya kula da Kanta bane ba ,a'a yakamata ace akwai babba da yake sa Ido akanta, Amma tunda kince haka nasan irin hud'ubar da Zan Mata, Kalfana kina jini Daga Yau Kar ki Kara Cin abinci tare dasu ma'ana maciya, in sun Miki tayi in Kinga zaki Iya ci ki ci in baxa ki Iya ba ki Bari, Sannan Kar ki sake Zama acikin su Iya Kan Ki dasu Ina kwana Lafiya, Sannan Idan ciwon ki ya Tashi ki tattara kayan ki ,ki Koma Gidana, in takamarta tana kusa dake Kuma Zaki Iya mutuwa ne to ta Allah ba tata ba, haka Kawai Mata da girmanta d'auko Min jakata" tun da Aunty ta Fara magana Momy ta Rasa ta cewa, Kalfana zee sukayi hanyar fita zasu yiwa aunty Fatee rakiya, Aunty Fatee tace "maman Azeemah sai anjima" dakyar Momy ta Amsa "to Sai anjima".
Suka fita
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
```Wace Ce Aunty Fatee???
```
Mu had'u a next page


*Daga Alkalamin Fadeelah Yakubu Milhaat*


Plz comments and share👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 7️⃣5️⃣↔️8️⃣5️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*Wace ce Aunty Fatee???*

Aunty Fatee yar d'akin momy ce (Mahaifiyar Kalfana) sun zauna a barrack d'aya tun aunty Fatee na primary school suke tare da momy ta d'auke tamakar 'ya hakan yasa Aunty Fatee ta d'auki 'yan 'yan momy a matsayin kanne, sun zama family d'aya baza ka tab'a sani ba sai dai idan sune suka sanar da kai,Aunty Fatee Kanuriya ce mutanen borno, bayan ta gama makarantar jami'a sai ta nemi ai a d'aya daga cikin manyan Bankin da ke cikin garin gombe cikin sa'a ta samu aikin, sannan tayi aure.

Wannnan Kenan
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*Ci gaban labari*

Bayan aunty Fatee ta tafi Kalfana da Zee suka dawo cikin gida, momy jin salamar su yasa ta fara ashar, "Har ni karamar yarinyan chaaan zata ce wa da girma na, ban haife ta bane" ta maganar cikin d'aga murya, Afraa ce take ta bata hakuri, Zeemah kuma shigewa d'aki tana ala ya wadai da irin halin momyn ta. A haka duk suka kauna rai ba dad'i.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

*Washe Gari*

Dady ne ya Kira Kannen Sa Hafsa da Balaraba, Wanda su kalfana ke Kiran su da Goggo Hafsa da Goggo Balaraba, Hafsa suna uwa d'aya uba d'aya ne da daddy, ita kuma Balaraba suna 'ya 'yan baffanu ne.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Bayan Dady ya Kira su ne ya Sanar dasu duk abin da ke tafiya, ya nemi da suzo suji kan maganar sabida Aunty Fatee tayi fushi, don har cewa take kalfana ta dawo gidan ta da zama, Kiran Goggo Hafsa ne ya shigo cikin wayar kalfana a dai dai lokacin suna tare da kawayen nata, zee,Fatima,Zahra,falmata da kuma Hafsa, a gidan Aunty Mubarakha, yar uwar Fateema ce. Suna Shirin fita ne don zuwa gidan su khalfana kamar yadda suka saba.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Goggo Hafsa ta sanar da kalfana cewar gasu a hanyar xuwa gidan nasu, bata yi mamaki ba sabi da tasan duk bazai wuce maganar momy ba.

Kalfana tace "Zee ga makulli nan kuje gidan zan je na siyo Kayan miya, yau tuwo nake son ci" zee tace "Wallahi nima haka" Fatee tace kawata zan Miki rakiya" "Yawwa kawata shysa na fi son ki fiye da kowa anan" dukkan su tafi suka yi Hafsa ta ce " Dallah chan munafukai, ku tashi mu tafi" fita sukayi suna yi wa Aunty Mubarakha sallama.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Fateema da kalfana sukayi Hanyar Kasuwar mata don ba nisa da unguwar nasu suna tafiya suna hira.

Bangaren su Zee kuma bayan sun gaida momy ta amsa da fara'ah kamar babu abin da ya faru bayan sun shiga d'akin kalfana hira suke tayi cikin farin ciki, suna cikin hakan ne suka ji ana Sallama momy ta amsa sannan ta basu wurin zama, bayan sun zaune suka gabatar da kan su, ga mamakin su zee Momy Cewa tayi "ayya ai ban San ita yar gombe ce ba" Goggo Hafsa da Goggo Balaraba su kansu sunyi mamaki sabida Zeemah da kalfana sun sha Kai musu ziyara, ita Goggo Hafsa tun farko da Kalfana take ba da labarin matar bata shiga mata rai ba.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Goggo Hafsa ce ta fara bayani kamar haka

"Maman Azeemah wai me yake faruwane a gaskiya bamu ji dadi ba, Kalfana a ko da yaushe labarin ko take da irin kyautatawar da kike mata, sai kuma ga mumunan labari"

Goggo Balaraba tace "ai kuwa mumunan labari Mahaifinta hankalin sa ya tashi gami da bacin ran wasu maganganu da kikayi a lokacin da ya nemi yayi magana dake".

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Momy da tunda suka fara magana bata ce komai ba sai yanxu tace "Mama......" Goggo Balaraba ce tace "a'a kar kice min Mama ban haife ki ba" cikin zolaya, Momy tace "A'a ai girmamawa ne, na d'auki kalfana tamkar ni na haife ta , amma wlh ta bani mamaki, har ta iya bude baki ta zage ni, kuma wallai tallai da zan fad'a muku abubuwan da take yi Mahaifinta sai ya tsine Mata"

Dafe kirji Goggo Hafsa tayi tace " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Dan Allah ki dubi girman Allah ki fad'a mana abun da take yi".

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Momy tace "Hmmm Kalfana maza take kawo wa d'akin ta akwai Wanda yazo har ya kwanta da ita ina d'akina ina jin duk abubuwan da suke yi kuma tana mana sharrin sata wai an saw Mata kud'i gobe tace an sace mata BZ ko 'yan kunne " tunda momy ta fara maganar kallon ta kawai suke yi, Zee kuma In ranta yayi dubu to ya 'baci.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Goggo Balaraba tace "Ni dai a iya sani Kalfana itace ta ke saya wa 'ya 'yan mu yan kunne kuma tafi shekara a gidana ban tab'a ji tace an d'auke Mata abu ba, Goggo Hafsa ko kin tab'a ji?"

"A'a ban tab'a ji ba bar maganar sata ni maganar mazan da take kawo wane ya tada min hankali"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Goggo Balaraba Sam ita bata yarda ba amma Goggo Hafsa ta hau Kai ta zauna damas,momy taji dad'in hakan sabida uwa d'aya uba d'aya suke dole ya d'au maganar ta.

Goggo Balaraba tace "Uhmmn amma wasu mazan ne suke zuwa gun ta kin tab'a ganin su?"

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bangaren su Kalfana da Fateema suna isa Kasuwar Basu b'ata lokaci ba, ganyen alaiyahu suka saya, tare da timatir,attaruhu,albasa da duk wani abin da ya kamata, bayan sun gama ne suka nufi hanyar gida.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Momy tace "Sosaima ai lab'ewa nake ta window ba tare da ta gan Ni ba sun Kai kusan su 5 abun haushin ma yaran fa kanana"

Murmushi Goggo Balaraba tayi don tuni da gane yaran da Momy take fad'a.

Sannan tace "Maman Azeemah ai wa'annan da kike gani ai kann..........." Sai sukaji sallamar su Kalfana duk suka amsa amma ban da Momy da take ta rarraba idanu, a zuciyyar ta cewa take munafuka ai banso ta dawo yanxu ba mtwwwws".

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Bayan sun gaishe su ne Fateema ta Mike ta shige d'akin kalfana ta tarar da su duk sunyi shiru tace dasu "lafiya kuwa ya na ganku haka, da fatan kun yi tuwon?"

Hafsa tace "Ina kuwa mukayi munafukar matar nan muke sauraro tana fad'awa su Goggo karya da gsky"

"kamarya wani abun ta fad'a musu"?

Falmata tace " ke dai bari Ina mamakin halin wananar matar" nan ta kwashe komai ta fad'a Mata Fateema tace "Allah sarki qawata kina ganin abubuwa kalakala"

Gani sukayi zee ta Mike tana typing cikin sauri bayan ta gama fita tayi ta Mika wa kalfana wayar tace mata "Khalfy gashi an turo Miki sako" sai ta koma ciki, Kalfana fara karanta sakon kamar haka

```"Maman su Azeemah fa cewa tayi kina kawo maza kuma kina musu sharrin sata, ta fad'i maganganu da dama maras dad'i ji kiyi kokarin kare kanki Dan Allah"
```
Murmushi kalfana tayi

"Yanxu maman Azeemah zargin Kalfana kike Amma bari muji ta bakin ta"
muryar Goggo Balaraba ne ya dawo da ita daga tunaninin da ta shiga yi
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

"Mujeedat wasu mazan ne suke shiga d'akin ki"? Cikin kwanciyar hankali kan ta amsa Goggo Hafsa tace

"Haba ya kike Mata magana da sanyin murya?, Ke don ubanki ana Miki magana kina jin mutane baza ki amsa ba?"

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Kalfana murmushin takaici tayi sannan tace

"Anas,farukh, uncle Hayat ,hisbullah,Habeeb da sufyan in ya shigo gari"

Goggo Balaraba tace "Nayi tunaninin haka, yanxu dai duk a bar tone tone komai ya wuce, ke kalfana ki bata hakuri"

"Kiyi hakuri" kawai tace a takaice

"Maman Azeemah kiyi hakuri Dan Allah komai ya wuce, Amma dga yai kar ta sake amfani da wani abu naki gudun magana ko ya kika ce?" Ta mai da kallon ga Goggo Balaraba da tun d'azu jikin ta yayi sanyi akan yadda ta yarda da maganar maman Azeemah ashe duk sharri "Eh haka ne" Goggo Balaraba tace "Yawwa yanxu kuwa muna isa gida zamu Kira Mahaifinta mu sanar dashi duk yadda mukayi" Momy tace "Dan Allah ku bashi hakuri b'acin raine, zan ma Kira shi da kaina".

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mikewa sukayi Goggo Hafsa tace "kar ki damu ai haka rayuwar take dole ake samun misunderstanding,
Mu zamu tafi sai wataran" Momy ta amsa da "Mun gode fa Allah ya saka da alhairi" Goggo Balaraba leka d'akin Khalfana tayi tace "emmata ashe kuna ciki kwana biyu baku kawo min ziyara ba" murmushi. Sukayi suka shiga gaishe su , suka tabbatar Mata da cewa zasu zo kwanan Nan.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan sun fita ne suka nufi inda sukayi parking driver na jiran su, Goggo Balaraba ce tace kar ki sake tab'a Mata komai kinji maganganu da tayi akanki kuwa in Mahaifin ki yaji daga ke har mu kashin mu ya bushe, kina gani fa har Goggon ki ta yarda" Goggo Hafsa tace "eh wlh matar Nan yar duniya ce kibi ta a hankali kar ki rabuda da addu'o'in kare jiki,sannan hijab din nan ki Kona shi, da fatan kin fahimta?" " Eh na fahimta nagode soasai ku gaida gida sai nazo weekend" Bandir na dubu dubu zai Kai dubu hamsin Goggo Balaraba ta mikawa Kalfana, tace kiyi hakuri ba yawa ta karb'a tayi godiya wasu Bandir d'in Goggo Hafsa ta mikawa Kalfana Amma yayi biyun Wanda Goggo Balaraba ta bata, godiya ta shiga you musu sosai duk da tana da kud'i a hanunna ta.

♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bayan sun tafi ta shige cikin gidan Momy ce tace
"mujeedat zo Dan Allah, zauna" bayan ta zauna sai tace "Dan Allah kiyi hakuri mu yafi juna" Kalfana tace "Momy ban rike ki da komai ba" "toh nagode" tashi tayi ta shige d'aki Nan suka fara hira da qawayen ta suna girki suna Hira tuwon semomivita sukayi da miyar alaiyahu duk yawan sa cinye shi sukayi tass.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Bangaren Dr Abdulazeez da Azeemah soyayya tayi karfi haka ma Adam Da zainab.


Kalfana ce zune a d'akin ta dawowarta daga school knn sai ga shigowar Azeemah jiki a sanyaye. Bayan ta zauna ne tace da "Kalfana plx shawara nake so ki bani"
Tashi tayi ta zauna sannan tace "Ina sauraron ki" "Abdulazeez ne ya ke so ya zo ya gabatar da kanshi a gidan mu" "Masha Allah to mene ne matsalar ki bari

Please Login or Register in order to submit comment