Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakya son gsky Amma dazu cewa kikayi baza kije ba mujeedat ko kallon batayi ba sai ta shige toilet tayi wanka Azeemah, zee da Momy hirar su suke Suna dariya Har ta fito sai zee ta Shiga ita ma ta watsa Ruwa mujeedat ta dauko Mai tashafa tayi lite makeup sanan ta dauko T-SHIRT dinta Na orientation tasa kalansa pink sai kolan rigar baki rubuta *KALFANA* a bayann rigar Shima da baki a karubuta ta dauki high waist baki tasa sanan ta dauko toms da baby himar baki tayi kyau matuka abunka daguwar mace☺️
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zee ta fito ita ma ta shirya tasa nata Duk Kala daya ne dake faculty daya suke Amma different departments ita Kuma *Zeee* aka rubuta a Baya ita din ma high waist tasa sanan tayi rolling da bakin gyalle irin Na abaya ita ma light make up din tayi da dauko bakin sandals irin Mai igiya fashion tayi kyau sosai nan suka fita suka Samu Azeemah ma ta shirya zata tafi makarantar da take teaching practice Tasha kyau tasa less fari ta yada gyalle Jaa Takalmi Jaa Haka jakar ta Jaa ta rike wasu littattafai a hannun ta zee tace "kyau knn" Azeemah tace "Na kai ki ne" Azeemah tace "kalfana fa "tace "tana Ciki ko me takeyi Oho"sai ji sukayi tace "malamai jakata Na dauko" sai suka Ga tana kokarin yada gyalle zee tace "ke haba yauma sai kinyi kauyancin not" Kuma wannan zee ta juyo "tace Dan Allah ki cire" mujeedat tace "in fita waje da figaggiyar rigar nan, Dama ace duguwar hannu ce Amma ki Gani fa hannu na a waje" Momy tace "Hmm Dix Mujeedat ko zee tafi ki waye wa dan Allah ki cire" mujeedat tace "Momy wlh bazan sake ba zanga kamar Duk Kallo Na ake", Zeee ta taso Kamar zata shige daki sai ta kwace gyallenn mujeedat tayi ta Hada ta da Allah Akan ta Bata Amma Taki , a Haka dai suka fita sukayi wa Momy sai anjima Azeemah tayi hanyar ATC sukuma GSU Duk da hkn Dai mujeedat Bata daina roko Zeee ta Bata ba dgaa Baya Zeee ta hakura ta bata Amma ba Wai don Taso ba, nan da nan Har sun Isa bakin 2nd gate Na GSU Suna Isa suka Ciro ID card din su suka Nanu security ya musu hannu akañ su wuce Suna Shiga suka Nufi CS Anan Za a Yi orientation din tun karfe 2 aka fara su kuwa Har 3 ta wuce suka Isa Suna Shiga suka nemi guri suka Zauna,.........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mujeedat ta zaro wayarta a jaka ta Bude datar ta sai Fara replying messages sai taga Hubby Na a online toast Dake ta G WhatsApp take amfani sai tayi searching Hubbyna❤️, Kamar tayi Masa magana wata zuciya tace share Kawai sai Gani nayi tayi Typing _Assalam_ nan da nan taga Shima yana _typing_ tace "wow yaga sabuwa numb Amma ba Jaan Aji", ya amsa _wslm_ tace _ya kake ya gida_ ya amsa Da _Alhmdlh_ tace Masa _ka gane ni_ yace _a a plz waye nawa_ sai tayi searching pic dinta sai ta Tura tace _Amma ka gane wanan_ sai yace _hmmmm ai bazan taba Manta wannar fuskarba_ _Babyna_ sai batayi reply ba tace "Zee kiga mutumin nan Har Babyna yake cemin" tace Muga sai ta karanta chat din su sai taga mujeedat batayi reply Na karshe ba sai ta Yi reply da _Hmmm Allah ko Hubbyna_ Yana Jin karar msg din ya Bude don a lokacin driving yake ganin sunan da ta Kira Shi dashi Yaa yayi parking yaji dadin sunan ya kira sunan a fili 'Hubbyna" sai yayi reply _Wow Naji dadin name din nan sosai_ zee Na ganin msg din ta Mika Mata wayar ta mujeedat Na Bude msg din tace "innalillahi kin kasheni zee"........
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Zee tace "Mtwssssss Kinga plz ki kyale ni, Dr Isma'il ya Fara Magana" Mujeedat tace "ban ga laifinki ba, ki Tashi mu Je muyi sallah, tunda naga su Basu da niyan Tashi" Zee tace " ai Yau har 10 ana nan za a yi party in malamai suka watse"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Hmm lallai Naga halama ba Dai Zama zakiyi ba ko"?
"Kalfana me za a fasa mutuwa ko hisabi"?
Mujeedat tace "ko d'aya, tashi mu tafi Naga malaman ma sun fita , Amma Ni fa Daga masjid LT5 nayi " "me Kuma zakiyi a Chan "? Karatu zanyi ina da test gobe karfe 8"
Zee okay mu tafi Amma fa Ni nan zan dawo" Mujeedat tace "zakiji dashi"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Nan sukayi masjid suka yi sallah sun Dade Suna azkar sanan suka Tashi suka fita, Mujeedat tace "yanxun orientation din Zaki Koma"? Tace "eh, ko da Magana ne"? " "Hmm babu Allah Bada sa'a" zee tace "Amin, zan zo Na same ki anjima kadan" Tace okay "sai mun hadu din"
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Nan Mujeedat ta Fara karatu almost 30 mints Bata fa zee ba tace " Hmm ko Bata ganin tym ne, yarinyar nan bata ji wlh" sai Taji an tab'a ta tna juya sai taga zee ce
" Ke hajiya Baki ganin Tym ne" tace wlh ina Gani, abun ne ya fara bda Kala, Baki Ga yanda ake shashewa bane shys" Mujeedat tace "jiman Malama kinga ki Tashi ki tafi gida Ni wlh in baffan Ku ya Zane ki ba Ruwana" "chaap Zane Ni fa kikace, ai in fada Miki Muna next level da knn wlh" "naji naji dai, Tashi Na raka ki gate, zan Je nayi sallan Isha" nan suka fita Suna hirar su wannan ta fada Waccan ta Fadi nata Dake Duka su 2 babu wacce a ka Barta a baya Har suka Isa bakin gate din sukayi sallama zee ta fita Mujeedat kuma ta Shiga Masjid, tana Shiga tayi alwala sanan ta dauko alqur'ani ta Fara karatu tana cikin hkn ne aka tada hikama, nan ta aje qur'anin ta Mike bayan sun idar da sallann ne ta jero addu'o'i Kamar yadda ta Saba, bayan ta Gama ta dauki qur'anin ta Maida Shi mazaunin sa tayi ficewar ta, ta Koma Lt din ta ci gaba da karatu don ita a al'adar ta sai 8 Zara fita Daga cikin makarantar, tana cikin kaaratu sai Taji karar wayar ta tana dubawa taga Hubbyna
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Nidai Allah ya shiryani, Na kasa canja sunan da Na sa Masa" tana picking " Assalam" yace "wassalam,Yar Jami'a ya kike"? "Lafiya kalau Dan kasauwa,ya gida"? "Haba hajiya nifa lafiyar ki Na tmbya ke Kuma gida kike tmby"? "Am sorry Sabo ne, to ya lafiyar ka"? "Yww ko kefe lafiyata kalau, ya Boko"? "Alhamdulillah" "kina gida ko makaranta"? "Ina makaranta" "Toh ina gate din makarantar Ku" haba Dai dagaske kake ko Wasa"? " Dagaske nake " tace "me kazo yi"? Ko kadan baiji dadin tmbyr nan ba "me zanzo yi in ba wurin sarauniya ta ba"? Tace "Uhmn Haka ne, akwai abinda nk yi gsky" yace "Kar ki dami Ni Mai jiran ki ne" tace "Toh Bara Na Gama" a Ranta kuwa zaka ga Jira ta cigaba da karatunta, tun karfe 7:37 ya kirata Har 8:30 ya ji ta Shiru yace "Hmm Anya ba son maso Wani nk ba kuwa ,yarinyar nan ta Manta Dani, Aiko in tasan wata Bata San wata ba, dole sai kin Soni Kalfana,Kuma sai Na Aure ki" ya fada a baiyane ita ko Har ta Manta da ana jiran ta karutun ya Mata Dadi don Yana Shiga yanda take bukata , sai Taji ringing din wayarta tana dubawa taga shine tace " hmm Mara zuciya kawai, Assalam, yihkri fa Na Shanya ka" yace "no Kar ki damu Duk a cikin so ne, ina fatan kin Gama"? Tace "eh kusan hakn" "ko Dai Na tafi ne? Tace "akwai inda zaka Je ne" "a'a Naga Kamar Na takura kine" a Ranta tace "takura kai" Amma a bayyane ce Masa tayi "a a ba takura ai ko ba komai ka so Mai sonka ko"? Amma "Anya kinsan da hkn"? "Nasanta man tun da gashi na fada Maka, yanxu Dai am sorry Gani nan zuwa , Amma fa da d'an Nisa" yace" indai bazai kai jiran da Na Miki a baya ba, ba matslaa" tace "To" ta katse wayar " iska Na wahalar da Mai Kara aka" nan ta Tattare littafan ta tasa a jaka ta fita a LT din
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana tafiya Kamar wacce Kwai ya fashe a aciki, a Ranta Allah yasa ma ya tafi, Shi kuwa a ransa cewa yk ina nan ina jiranki ba inda zanje sai Na ganki don in ban ganki ba bana tunanin zann Iya bacci"
Kalfana ta dauke wajen 20 mints Kan ta fita , ta dann tsayan kadan tana dubawa ko zata gane motar Amma ba ta Gani ba tace "kila ya tafi, but Lemme call him, bugu d'aya ya katse sai ya Kira ta , "hello ya ban gan ka ba" sai yafa Daga motar ya Duba sai ya hango ta yace " ina kallon ki" ta Fara Dube Dube Amma Bata gansa ba ,"ban ganka ba fa" yace " "Gani ina Daga Miki hannu" sai tace "okay Na gan ka" ta Fara tafiya Kamar an daure kafarta da igiya , Shi ko kallon ta yk Dake gun da hasken street light ta ko ina don ko allura ne zaka yi Iya dauka tsabgen hasken wurin,
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Maan sai kallon ta yake ita Kuma ta lura da hkn , "irin Matar da nk so Na aura Kenan slim to fashion" ita ma kallon nasa take Daga nesa, " hmm Ni wlh Dama Kaftan kasa Akan wannan dressing din da kayi"
T-shirt ne Navy blue da jeans Baki sanan yasa pea cap Baki , takalmin sa Baki, yayi kyau matuka ita Dai Mujeedat Duk munin Na Miji indai yasa kaftan Yana tafiya da imaninta, tana cikin wannan tunanin ne ta karaso inda yak, " Assalamu Alaikum" "Wa'alakkissalam sarauniyar kyau, barka da fitowa" tace "yww " alamun gajiya duk sun nuna a jikinta, yace "yada"? "Wlh Na gaji ne Sosai" yace "Ayya sannu naso Na Shiga Na dauko ki, aka hanani"? Tace "wa ya hanaka"? "Yan rainin hankalin nan mana securities dinku" "Ha'ah to me yasa"? "Wai cewa sukayi in 6 ya wuce Mota Mai tinted windows Bata Shiga" tace " oh ni ina ma nasan suna hk? Ta Kara maganar dakyar ya karaso da sauri ya Bude Mata gaban motar "sorry Bismillah Shiga ki Zauna" tace "Nagode" "Kar ki damu ki sarauniya ce a fadar zuciya ta kiyi Mulki yanda kike so " tayi murshi ta Zauna Shima ya xaga ya Zauna yace "Ina zamuje" tace"gida" Bata ma kalli inda yk ba, yace "no muje mudan Saya Miki Abu ko da fruits ne" tace" kar ka damu am Okay" "plx I insist muje mu Saya Miki ice cream, Dan Allah Kuma Kar kice a a" tace "okay muje din but baza mu Dade ba kaga dare yy ko"? Yace" yanxu xamu dawo" nan sukayi Havilla ice cream sukayi order suka samu wuri suka Zauna Suna Sha Yana Bata lbri tun Bata amsawa Har ta sake jikinta sukayi ta Hira tana dariya, Duk Wanda ya Gansu Zai Zan cewa masoyan nan Na cikin farin Ciki, Shi kuwa Dadi yk Ji Na ganin ta Fara sake jikinta dashi Basu bar wurin ba Har sai karfe 9:30 tace "plz ka Maida Ni gida" ya Duba agogon sa yace" am sorry my princess nasa kinyi dare wlh ban lura bane" tayi murmushi ta Mike " Kar ka damu mu tafi" nan suka fita Suna Hira Har suka Isa Parking space Shi ya Bude Mata motar ta Shiga sukayi hanyar Jauro Kuna unguwar su Mujeedat Suna tafiya taga ya tsaya" yace Ina zuwa plz" Bai Dade ba ya shigo da manyan leather guda 2 ya Mika Mata d'aya ya aje d'aya a baya ta karba ta Masa Godiya, Basu Dade ba suka Isa gida sukayi Parking a kofar gidan su Kalfana yace " Zan rabu Dake a Dai dai lokacin da idanuwa suke bukatar kallon ki, kunnuwana Na bukatar Jin zazzakar muryarki, hancin na Kuma Na son Jin kamshin tiraren ki" Bata ce dashi komai ba murmushi take yi Wanda ita kanta Bata San tana Yi ba tsintar kanta tayi ita kanta Bata son rabuwa dashi Amma dole su rabu,
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu hadu a next page don Jin yanda Zara kasance

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* ( *Milhaat)*
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

*Written and Story by Fadeelah Yakubu*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aikida da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.```🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PAGE* 1️⃣7️⃣↔️1️⃣8️⃣
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Zan rabu dake a Dai Dai lokacin da idanuwa suke bukatar kallon ki, kunnuwana suke bukatar Jin zazzakar muryarki, hancina Kuma Na son Jin kamshin tiraren ki" Bata ce dashi komai ba murmushi ta yi Wanda ita kanta Bata San Dallin yinsa ba, sai ta sinci kanta da Bata so ya tafi.......

Wannan kenan
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Babyna ya Naji Kinyi Shiru"?
"Uhmn bkm Na gaji ne sosai ga bacci"
"Ayya am so sorry Na wahalar dake ko"? "Umm Umm, ba kai bane, tun ranar Monday muke ta zirga zirga gashi Yau Saturday ana Abu daya"
" Haka ne Kam, shys fa Na ki Boko Na fiso a saku kudi yanxu yanxu"
"Aaa'a kace naku Na Manyane, in ba hk ba..........." Sai wayar Alhj Maan ta Fara ringing,


♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️

Ya Yi picking "Hello, Adamu ya akayi ne"? Adamu Yana d'aya Daga cikin ma'aikatan Alhj man yace "Alhj mutanen na fa Basu Tashi ba Haryanxu" " Basu Tashi ba"? "Eh wlh" "to me suke Jira"?
"Cewa sukayi Suna bukatar Ganin ka tukunna" " Gani Na , kaaai yanxu yaushe suka Tashi Daga Dadi Kowa Har suka Isa Adamawa, Amma tafiyar dare zasu Yi ko"? "Eh tafiyar dare zasuyi" " Okay Gani nan zuwa nan da awa d'aya zan shigo" ya katse wayar
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"My Princess, tafiya ta kamani yanxu yanxun nan"
"Zuwa Ina Haka da darenn nan"?
"Dadin Kowa"
Ta zaro Ido "Dadin Kowa,"? "It's late fa"
"Haba hajiya , yimin yaren da nk Ji , Ni ba bature bane" tayi dariya tace" yanxu Chan kayi knn"?
"Eh chaan nayi, Amma da ace da Rana ne da Na tafi Dake" " mu tafi man Kawai" "rufamin Asiri Dan Allah , bar Ni Na tafi Ni kadai hanyar akwai Yan iska, Bazan so Wani Abu ya tab'a mini ke ba,"
"Tunda kasan da hkn,y not ka Bari sai gobe mana"
"Babyna Zan so hkn amma bazaiyuba anyi order ne Kuma gobe suke bukata, Kinga ya Zama dole" "toh shkn Allah ya tsare Amma ban so hkn ba" "meyasa" "sabida Bana so Wani Abu ya tab'a Min kaaaa......" Ta kasa karasa Maganar,
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Maan ya kwantar da Kan sa Akan sit Yana shafa gashin kansa, Yana murmushi sai ya maso kusa da ita , yace" Babyna, plz ki karasa abin da kike Fara fada" ta sunkuyar da kanta kasa sai ya Sa hannun sa ya d'ago kanta, Dukkan su Saida suka ji Wani yaaaar ,
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Duk su 2 sun shagala da kallon juna sun dauki kusan mint 5 a Haka, sai ya Kara matsowa kusa da ita Har ya kai ga Suna shakan numfashin juna ,
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Sweetheart, Naga alamun chanji a Tattare da ke hkn Na nuna cewa kin karbi soyayya ta knn"? Zata Kuma sunkuyar da kanta yayi sauri rike Kanta da hannu 2 ," plx Kalfana kiso Ni Kamar yanda nk sonki ko da kuwa kwatan Wanda nk Miki ne"
Tayi doguwar ajiyar zuciya Wanda yasa Har yaji gaban sa ya Fadi Kuma Bata ce komai ba, "Dan Allah kice Dani kina so Na"
"Maaan" yace "Na'am kinji yanda sunan yayi Dadi a bakin kuwa, Kamar kice kika kirkiri sunan" tayi murmushi tace" karfe 10 saura ya kamata ka tafi" anan ne ya sake fuskar ta tun dasu ka Fara maganar ya rike yayi ajiyar zuciya yace " hkne korata kike ko, kin gaji da Gani Na Bara Na tafi , sai da safe" ta Bata raai Kamar Bai tab'a dariya ba tace" a a ba hk bane Kar ka Manta akwaii inda zaka Je " " hk be, yanxu daganan Chan nayi don in Alhj mu yaji Zai hanani tafiyar" sai ya fita ya zaga ya Bude Mata kofar ya rako ta yana rike da ledar ya Mata sayayya Har suka karasa kofar gidan, sai ya Mika Mata yace "sai da safe" tace " plz in ka dawo call me" " okay ki Kula Min da kanki My dear" " Insha Allah, take care sai ta shige cikin gida," ta Shiga parlour Assalamu Alaikum" Azeemah tace " Hajiya sai yanxu Ina kika Shiga ne hk"? " Ina makaranta, Ina da test gobe, Ina Momy ne"? Sunyi bacci" "okay sai da safe" ta fice ta Nufi kofar Dakin ta tasa hannu a jaka ta zaro key din Dakin ta.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Tana Shiga ta aje Jakarta ta Shiga toilet ta watsa Ruwa, tana fitowa ta sa sleeping dress dinta pink an Masa ado da fararen followers yy kyau sosai ya dace da jikinta sosai, Har ta rufe kofar ta sai Taji ana kwankwasa kofar ta, tace "waye"? Sai ta Ji muryar Azeemah tace, " mutum ce, dallah zoki Bude Min," tana budewa Azeemah ta shigo da tace "Gobe Saturday so nk ki rakani shagon Hassan Zan karbo dinki Na" " Allah ya kai mu goben" Azeemah tace" Good nyt" ta fita Kalfana ta Maida kofarta rufe....
Har ta kwantar ta dauko wayarta tana chat da frnds dinta Har wajen 12 da rabi sai ta tuna Bata Duba me Masoyin nata ya Saya Mata ta dauko ledan ta Bude taga chacolate ne kala Kala sai soft drinks , tana kallon su tana murmushi ta dauki ledar d'aya ta Fara Sha, bayan ta Gama Sha ne ta dauki soft drinks din tasa a Kamar fridge din da ke dakinta taje tayi brush sanan ta kwanta tayi addu'ar bacci bata Dade ba bacci yayi awun gaba da ita.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bangaren Maan Kuma Bai Dade ba ya Shiga Garin Dadin Kowa, zuwa karfe 12 ya dawo gida yayi wanka karfe 12:31 ya kirata ta bugu 2 ta dauka , idon ta a rufe ta dauki wayar ta Kara a kunnen ta, " Babyna kin Fara bacci ko" nan baccin ya watse tayi murmushi "Har ka dawo" cikin muryar bacci " eh Na dawo, da nasan Kinyi bacci da ban tashe ki ba" " da kuwa Baka kyauta minnba" yace" hmmm yanxu Na kyauta ko" tace " eh sosai " nan sukayi ta waya sun Dade Suna wayar Har ya kai awa d'aya ya ynk ya Kuma kiranta bacci take Ji sosai Amma ta kasa fad'a Masa Hira tayi Dadi Har bacci ya dauke ta Yana ta surutu Shi kadai sai Ji Hyo ta Na sauke numfashi a hankalin alamun bacci take you murmushi yace " Gud nyt sweetheart " Duk da ya San cewa ba Jin sa tk ba sai ya katse wayar yayi addu'ar bacci Bai Dade ba Shima yy bacci.
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Karfe 5 alarm dinta ya buga nan ta Tashi ta kashe tayi addu'ar Tashi Daga bacci ta shiga toilet tayi alwala tayi sallah tayi addu'o'i Kamar yanda ta Saba sanan ta Koma ta kwanta don Yau Sunday ranar Ce kadai tk samun Hutu , tana kwance idon ta a rufe Amma ba bacci Tk ba kwasam sai ta tuna jiya Suna waya Bata San ya suka Yi sallama ba "Kar Dai Na Yi ta Masa kwa'ba ko da to Wayan Yana recording" nan tayi playing Taji Har karshe Har Taji inda yac " Gud nyt sweetheart ya Sumbaci wayar" sai ta Rumgumi wayar tace " Wai me ke Shirin faruwa Dani ne"? A hk tayi bacci
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Bangaren alhj Maan karfe 5 Shima ya Tashi ya shirya ya fita masallaci Bai dawo ba ya Zauna Yana karatun alqur'ani ya Dade Yana rokon Allah da ya mallaka Masa kalfana yasa had'uwar su alhairi Ce in ba alhairi bace ya juya Shi yazama alhairi,karfe 6:30 ya dawo Yana shiga gida ya Shiga toilet yayi wanka ya Sa kaftan Royal blue Wanda yasha aiki Mai tsada ya Sa hula da takami Wanda ya dace da kayansa ya Sa agogo sanan ya Zauna Na a bakin gado ya dauki wayar sa Yana murmushi you dialling numb ta suka gaisa yayi ta dariyar ta " ke Kuma hk Ake Yi kika Yi bacci ba bankwana" tayi dariya tace" Shi bacci fa barawone" sun Dade Suna waya sai ya sukayi sallama ya Nufi kasuwa ita Kuma ta Koma bacci sai karfe 11 saura Azeemah ta kwankwasa mata Kofa Akan ta Tashi su Karya , ta Shiga toilet tayi brush ta fito suka Zauna a tsakar gida, chips ne da source sunci sosai bayan sun Gama cine Momy ta fito nan suka gaisheta Kamar kullum suka Yi ta Hirar su Har akayi sallar azahr ko wacce ta Tashi sukayi alwala sukayi sallah
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Azeemah da Kalfana Suna idar da sallah sukayi wanka , Kalfana Wani material royal blue doguwar riga aka Masa design da farin flower tasa farin takalmin ta kama Kanta da blue ribbon sanan tayi rolling da farin gyale light make up tayi Sannan ta feshe jikinta da turare ta dauki Jakarta fari sanan ta dauki wayar ta tanufi parlour ta tarar da Azeemah jiranta tk really Ga da skirt ta sa Na atamfa green tasa golden Takalmi Sannan tayi rolling da gyalle golden tayi Duk sunyi kyau sosai suka Shiga Dakin Momy suka Mata sallama sanan suka fita suka tare Mai adadidaita Basu tsaya ko Ina ba sai Bubu Shango, Suna Isa suka sallami Mai adadidaita sanan suka Shiga shagon dinki babba shaago ne Hassan yy Suna sosai hkn yasa wasu ke kiransa da ajebo, Suna Shiga ya Bata Rai sunyi da Azeemah ita kadai zata zo Na da Kowa ba Kuma shagon ma Shi kadai ne Yan aikin nasa Basu zuwa a weekends, Mujeedat tace" Ina wuni" Yana amsawa Chan Ciki Kamar an sashi dole yace "Bismillah Ku Zauna " Mujeedat ta Zauna ta ciro wayar ta ta fara chatting
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Azeemah ta San dalilin bacin ran nasa Duk da Bata fadawa Mujeedat ba,
Ta matsa kusa dashi tana Masa Magana Amma Yana amsa Mata da kyar, sai ta Rungume Shi ta Baya Sannan ta kwantar da Kanta a bayan Sa tace " Babyna meyasa kk 'bata raai tana ganinta Anan bazai Hana mu yin komai ba" Jin hkn ne yasa Mujeedat tayi sauri d'ago kanta tana kallon su mamaki take "Ashe dama hk Azeemah take"?a zuciyarta nan ta juya ya rungumota ya Fara shafa jikinta ta ko Ina ya Na kokarin Fara sumbatar ta Mujeedat ta kau da Kanta ta cigaba da chat din ta Amma Har Ga Allah Ranta ya baci sosai sun Dade a cikin wannan Yana yin Sannan Azeemah tace "Kalfana zamuje mu gaida mahaifiyar Sa zamu dawo yanxu" 'Daga mta kai kawai tayi alamun to suka fita Amma sun bar Kalfana ita kadai a shagon tana zaune Kamar wata Yar jiran shago, Wayan ta ya Fara ringing Tana picking
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
"Assalam Mijina" Maan ne Yayan Zee nan sukayi ta wayar su cikin kulawa sa kaunar juna Sannan suka Yi sallama ya katse wayar nan ta cigaba da chat din ta Azeemah Kuma da Hassan kusan awa 1 knn babu su babu lbrin su
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Mu hadu a page Na gaba don jin Wani Hali Azeemah take Ciki.

*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *Yakubu*🖊️

Plz comments and share 🙏🏻
💜💜💜💜💜💜💜💜
*MATAR AURE NAH*
💜💜💜💜💜💜💜💜

_*(A love and sympetic story)_*

```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```🖊️

*Matar Aure Nah, labarine Wanda ya kunshi soyayya tausayi fad'akarwa Nishad'antar wa gami da ilmantar*

*Note_* ```bamu yarda Wani ko wata su juya mana labariba ba tare da izininmu ba```


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah* *(Milhaat)*✍️✍️


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.

Please Login or Register in order to submit comment