Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsohon iskancin ki mu zuba. Ta katse kiran tayi gaba, kiranta Momy tayi cikin kwantar da murya tace " ke banson hauka da rashin hakuri ke bakibin abu a hankali, tunda kikaga bata tareba kinsan aiki yayi kyau, Kuma bansan iya shegen da yakaiki gidan shi ba batareda nafada miki ba, idan kina son kisamu zuciyar Naziru sai kinbini a hankali mu cika burin mu ba rashin kunya ba. "Wane irin hankali nifa namatsu wallahi kawai so nake mufara rayuwa tareda shi, koda yake ke girma yakamaki bakya sanin banbancin namijin duniya da lusarin namiji duk D'an kanoma ya gama da tsohon mijinki yazaki gano matsala?.
" eh Y'ar wofi ai ni bansan dadi ba ke kika sani, Kuma mijina karki manta uba yake ga Naziru duk Abinda kika gani a jikin shi yatada miki hankali nima shi nabi Kuma har gobe ruwa na wankin d'aud'a don haka idan bazaki hakura ba kije ki turmushe shi kimai fyade. Ta katse kiran tana cewa "shegiya Y'ar bariki mara kunya ni zaki fadawa zakin namiji nida ke cin halas kullum....... πŸ–Š



masoya seriously Ina matukar kaunar Momy wasan nata mugun burgeni yakeyi amma fa akwai sauran rina akaba, kujirani a next page muji ya Amri takeπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’–



*Matar Soja*

🌻🌻🌻🌻



Page 2⃣1⃣


........ Tunda wannan Al amarin ya faru take rayuwa shiru, haka kawai ta daina fita ko wurin Hajjo, Ummi ta koreta harta gaji haka ta hakura ta kyaleta, Mami har zuwa tayi ta tanbaye ta ko laifi tayi Y'ar ta ke gudun ta? Ummi tafara fada tace " ni ai don Allah Yaya ki dauketa kitafi da ita nagaji tazo ta takure min yaro. "Aa karki matsa mata Aisha batta kinsan tayi jinya kila jikin ne. "Ba wani jiki iya shege ne kawai. Itadai kanta akasa taki motsi haka suka gama hirar su suka kyaleta anan, Saida Mami ta tafi Ummi ta Kara rufeta da fada, kawai hawaye tafara yi bata iya cewa komai ba domin batada hujja ko dalili. "Ina kula fa dake wayarki ma a kashe take, Uban wa kike kashewa waya? Mijin naki da Aljannar ki ke dun duniyar shi? " eh lallai idan baki gyara ba zakici wuta daga yau zuwa gobe ki tattara naki ya naki kibar min gida kisan inda zaki koma bazakizo ki hanani sakewa da mijina ba. Ta mike tafice. Shiru tayi tana nazari ita batasan meke faruwa ba a rayuwar ta tarasa meke mata dadi a ranta haka kawai batada wani sukuni kamar ancire mata wani sashe na farin ciki a cikin zuciyar ta, kosu Farha sun gaji da tanbayar lafiya sun kyale ta.
Dole batada zabi haka ta koma wurin Hajjo, tana ganin ta tafara yi mata sannu tareda cewa zoki zauna anan ki kyale D'an banzan yaron nan karki damu kanki, ban so in sameki ne acan shiyasa na kyale ki, yanzu ya Jikin naki yake? " da sauki tafada tana dukar da kanta. "Karki wani sawa kanki damuwa kiyi hakuri zai shigo hannu na ne. Daga kai tayi tace "Hajjo zaki rabamu?. Wani irin kallo tayi mata domin tanaso ta tabbatar da gaskiyar zuciyar ta, "ki fadamin meya janyo wannan tsanar? Meya miki kikeso araba Auren ma da ba'a fara zama ba? " Hajjo nidai banason shine kawai. "Yaushe kiyayyar tafara? Ta tanbaye ta, "nidai naji bana son shi. "Kinji bakya son shi? Ko dama can bakya son shi? Shiru tayi tarasa amsar bata," toh indai ba wani dalili ni hajara ban isa in kashe sunnar ma aiki ba bani ba wannan zunubin. "Toh ni bazan zauna dashi ba. " toh kada Allah yasa ki zauna Zainabu ai shidai inma miyace saida ya shude tas yayi gaba yabarki da fanko, koki bishi ko karki bishi ya D'an dali roman arziki yayi pijo, ki zauna kina kallon Idona kina fadamin bakison jikana, sai kin fadamin munin dake gareshi ko abinki, yarinya don samun wuri yaron nan yayi shekara da shekaru yana dakon sonki yanzu yana farin ciki burin shi ya cika kizo kice wai ke bakyason shi. "Ke tsaya kardai kinfada mai wainnan munanan kalaman akan fuskar shi? Tura baki tayi domin ta lura Hajjo batada Alkibla, yaushe Kuma Yaya NAZ yazama jikan nata bayan kullum cikin wanke shi take kamar sabulu.
"Kya turamun baki wato abinda kikayi kenan? "Kai Allah ya narkawa D'an nan Albarka ya cika jinin hajara da Alu, ai yamin dai dai, da nasan iya shegen da kikayi dana kulle mai ke adaki yakara miki fiyeda Wanda yayi nafarko. "Ai kuwa kuka tasa mata wiwi harda buga kafa "eh lallai bakya sona hajjo irin wulakancin da Yaya yamin na dauka zaki dauki mataki yanzu kina goyan bayanshi saboda ni bakya sona. "Ai kalmar batada muni abakin ki shiyasa kika fadawa yaro toh kije kiji da tsiyarki yarage naki matsa bani wurin ko in tsula miki wannan casbahar.
Kin tashi tayi kawai kyaleta tayi tanata mitar da bata gajiya, Kuma ai inda sabo sun sabaji. Sallamar Momy kawai ya kashewa Hajjo baki, ta shigo tareda kallon Amrah tace "kedai an daura Aure tarewa ta gagara Allah ya kyauta meye ranar wannan Auren? "Toh Y'ar ayi meya shigo dake? Ai ni nariga nasan ke tauraruwace mai wutsiya ganin ki ba Alkhairi bane indai kin shigo tsegumin ki ne ya kawo ki toh idan kin gama ki kama kanki.
D'ana baki tayi kalar na munafukan mata tace "daga magana Hajjo kamar ni na hana tarewar tata kin fesomin duk yawun goro.
"Saratu bar dakin nan ko in mike in bubbuga miki wannan sandar. Ta janyo wata zungu reriyar sanda kusa da ita ta korar kajin ta da talo talo da take kiwo.
Mikewa tayi ba shiri ta tafi tana cewa "ai sai dai ta hango wasu a dakin miji itadai da dakin miji sai hange. "Oh toh ta Allah bataki ba kuma bakin ciki zai kashe ki bakar daga mai bakin hali nakusa maganin ki indai nice Hajara. Mikewa Amrah tayi ta shige cikin dakin domin Momy ta Kara jangwalo mata magana.

Ai su Abba na dawowa tace tana jiran su.
Saida sukayi ishai suka shigo tareda samunta tana hadiyar farfesun naman da Mami ta kawoma ta yayi lugub tada saka abaki take tamne abinta ta hadiye. Abba babba ne yafara magana " Hajjo lafiya dai ko? "Kalau gobe kasa kanin ka ya kaimu kaduna nida Zainab domin anfara zuwa ana jifarmin jika da habaici har agabana don haka zamuje banason kowa ya rakamu. Shiru sukayi saboda rigimar sabuwace. "Kawu Mustafa ne yace "ai bakomai sai inkaiku Hajjo, amma kuma Tafiyar nada nisa mai zai hana kubi jirgi saboda kafafun ki dake ciwo. "Toh koma dai meye gobe wurin jikana zan kwana. Taci gaba da cin naman ta, Abba kabir yace "toh Hajjo zan yanko muku tikiti in Allah yakaimu gobe sai ku tafi. "Toh Allah yayi Albarka kuje wurin iyalin ku.
Dariya suka fita sunayi domin sun san harda shekaru ke janyo mata wata rigimar, kuma yanzu suna tafiya zata uzzura zata dawo.


FARIDA

Tunda ga ranar da ta hadu dashi ya gasa mata magana a part din Momy ta daina Y'ar da su hadu bata lekowa sai yabar gidan take zuwa gaida Momy sannan ta nemi Abinci, duk tafada cikin kwana biyu saboda kad'aici da rashin sabo ga kuma zaman takura da take ciki.
Kwanan ta na uku ta fito zata nemi Abinda zataci daji muryar shi a bayan ta. "Ke"! Ta tsaya cak tareda juyawa gabanta na faduwa. "Ba a koya miki gaisuwa bane a gidan ku? Sauke kanta tayi kasa ta gaishe shi, hannun shi cikin pocket yana wani irin taku ya karaso kusa da ita, "wato akwai raini tsakani na dake ko? " me yasa zanbaki Umarni kiki bi? Shiru tayi tarasa ma mezata fada. "Look kin cuci rayuwata kin hanamin farin cikin zuciya ta, I will never forgive you for that, ki shirya zaman bakin ciki, yanda na rasa farin ciki na haka kema bazakiyi farin ciki ba, kuma kisani bazan taba yin hasarar sadaki naba don haka muje ciki. Ya nuna mata hanyar wani dakin da bata taba lekawa ba da Alama dakin shine. Wasu irin hawaye masu shegen zafine suka fara zubo mata tafara girgiza kai Alamar damuwa nadama da takaici, "i said go. Ya daka mata tsawa da Sauri tayi gaba ya bita. Yana shiga ta fashe da wani irin kuka ta durkusa a kasa, datse kofar yayi ya shige cikin dakin tareda zama bakin gadon ya kalleta yace " if you are done crying get up full your clothes zanga akan abinda na biya sadaki na. "Haba haba menayi maka da zafi kake cin mutunci na haka kawai saboda na nuna Ina sonka da farko? Toh na janye ba wata Soyayya please free me from this marriage na rokeka Fahad.
Zaburowa yayi "you are in sane, idan nayi free naki what about me? Ina nawa farin cikin? I love Amrah with all my life not only my heart amma me kikayi? Kunyi kutun kutun kun hana ni yanzu inaji Ina gani na rasata she is some body's wife not mine, kin cuceni, now full before I changed my mind. Ya buga mata tsawar da batasan lokacin da ta zuge zip din doguwar rigar da ke jikinta ba, ta saketa kasa, tana kuka jikin ta na rawa ya zuba mata ido kamar maye saboda gaskiya ba laifi tanada komai dai dai gwargwado don haka ya manta waye a wurin tuni ya shagala, nukuma nace gwara infito kafin abun yayi yawa in dakko na kanwa in dakko na Yaya? Ku kama mom ikram tabaku labarin ya akayi.


Washe gari

Tunda gari ya waye Hajjo ta Kira Mami tace ta hado mata kayan Amrah zasuje kaduna yau. Dariya Mami tayi har zuciyar ta tayi farin ciki domin ba abinda takeso irin taga Amrah gidan Nazir. Don haka ta koma ta shirya mata katuwar akwati cikeda kayanta na Aure komai ta hada mata har kayan baccin ta classic one.
Itadai tana can tana baccin ta har kusan karfe goma na rana Hajjo tasa su Nimrah tace suje su tasheta ta shirya. "Tana baccin ta mai dadi suka tashe ta " kitashi her highness Hajjo tace zakuje unguwa ki shirya. "Tashi tayi dakyar tace " Ina zamuje? " oho kedai ki shirya tana jiranki bata kawo komai ba ta fada wanka ta fito tareda shiryawa tsab cikin wata doguwar rigar atamfa glitter maroon da farha ta kawo mata sabuwa dal hade da farin gyale da plat white shoe, tafito as Amarya tana kyallin goshi farha tace ga humra ki mustsika Amaryar big bros. Tsaki taja tareda mikewa domin ta tsani ko jin sunan shi a kusa da ita, kawai turaruka ta fesa Nimrah ta miko mata Y'ar Karamar jaka tace "take Mrs Nazir. "Zamu samu matsala daku wallahi idan baku kiyaye niba. " oh keda zaki bamu tukuici duk Ina soyayyar da akeyi a ban daki?
Fita falon hajjo kawai tayi domin batason zancen. Tasamu hajjo tasha super dinta tsohuwar Ajiya kamar sabuwa saboda adani, tace " lallai yau duk inda zamuje dinnan na musamman ne irin wannan wanka hajjon mu. "Oho dai wuce muje.

Harabar gidan duk su Mami sunfito harda su momy suna so suyi mata sallama, Momy tace " wai hajjo Ina zakuje ne haka keda Amrah kuma? " inda kika aike mu uwar gulma, Zainabu ga kofata nan ki rife sai Allah yamun dawowa. Taja bakinta tayi shiru domin ita farin ciki ma take a zuciyar ta ko banza sa huta da fitinar tsohuwar. Abba kabir ya daukesu itadai bata ce komai ba, a yau ta dauki wayar data dade bata kunna ba domin Tafiyar da zasuyi. Saida sukaje airport ta kallo Hajjo tace " wai Ina zamuje harda jirgi kuma? " gidan y'an kan kai zankai ki su yanke kanki mai shegen tauri. Jan bakinta tayi shiru domin batason dogon surutu.
Saida suka shiga aka gama komai tacewa Abba kabir ya Kira mata takwaran shi ya taresu a can karsu isa suna jira. Tayi saurin kallon ta cikin tsoro hade da tanbayar ta "wai Ina zamuje hajjo me kike nufi? "Gidan mijinki zamuje sai Yaya? tafada hankalin ta kwance ko a kwalar ta.
Wani irin kallon tsoro "haba dai Hajjo yazaki yimin haka bayan nafada miki bana son zama dashi, so kike ki kaini ya kashe ni ni dai bazanje ba. "Dira ta jirgin toh tunda yafara tashi, shine kawai yau zai hana mu shiga garin kaduna....... πŸ–Š.

"Kuyi min hakuri mura ta hana ni posting jiya naso inbaku page biyu amma sai Allah ya kaimu gobe Asabar zaku samu wani fa izinin ubangiji.
*Matar Soja*

🌻🌻🌻🌻


Page 2⃣2⃣



......... Tunda ya samu lafiya ya koma bakin aikin shi sai dai gaba daya ya canja baya tareda walwala daka ganshi kasan yana cikin damuwa, kb ya tanbaye shi har ya gaji, ga mutanen Sokoto baya son waya da kowa sai Mami, Abba yasan inya kirashi fada zaiyi, wadda yakeso yaji muryar ta kuwa yasan bazata taba daukar wayar shi ba domin yasan ta tsane shi ga kuma abinda yayi mata kafin su rabu, Wanda ita ya bari da jinya shikuma yana jinyar zuciyar shi, ya karowa kanshi gubar soyayyar ta, domin yanzu jinta yake har cikin Ruhin shi idan ya runtse idanun shi ba abinda yake tunawa sai moment dinsu, wannan lokacin da wannan yanayin yazamo abu mafi dadi da muhimmanci a rayuwar shi, duk da yakan tuna kalaman ta akoda yaushe, idan ya tuna how sweet she is zaiyi wani irin murmushi har cikin zuciyar shi. Tundaga ranar ya canja mata suna a zuciyar shi "my little girl, domin ita din yarinya ce D'an ya sharab wadda kofarta take arufe ruf ko motsi batayi, ya tuna how hard he pushed before it open, irin sweetness dake ciki is inexpressible, baisan tayaya zai kwatanta yanayin da yake jinta ba a yanzu only tree days yaji zuciyar shi ta gaza, ya so tayimai adalci ya hakura da ita baki daya amma yaje ya karowa kanshi dafi mai mugun zafi.
Tunda ya taso aiki yau yake jin zuciyar shi tayi mishi nauyi ba abinda yakeso sai yaje Sokoto yana son ganin ta at any cost ko bazata kulashi ba, she deserve to be beg if possible domin takai macen da zai saka guiwoyin shi biyu kasa ya roketa, zaije ya roketa yaji wane laifi yayi da zata tsane shi lokacin da yafi kowane mahimmanci a rayuwar shi??. Tunda ya iso gidan nashi ya kwanta sai juyi yakeyi yakasa cire farin kayan shi daya saka yau na pilot beret din kawai ya cire. Kwankwasa kofar akayi da karfi yasan kb ne da wannan aikin, don haka saida yaga an buga sau hudu ya mike yana rangaji tareda fara balle boturan rigar shi singlet dinshi fara tas ta bayyana ya nufo falon yana tsaki tareda kudurin yimai warning yadaina damun shi.

Yana budewa yayi ido biyu da abinda bai taba tunani ba, Hajjo sai Amrah a bayan ta kamar zata tashi sama saboda cika da fitina. Ko kb bai samu gaisuwa ba daya dakko su daga airport, yace "madam ba gaisuwa? " kai kyale mata abarta ta hadiye da ruwa miskilar banza, Ina fata dai Abokin naka na gida? " eh yanzu mun tashi aiki Hajjo. Tunda Hajjo tasanar da ita inda zasuje ta hada rai bata kuma cewa komai ba domin fadar batada Amfani amma tabarwa zuciyar ta abinda duk zai faru. Wani irin bugawa zuciyar shi tayi lokacin da yayi ido biyu da ita, ga wani irin farin ciki daya bayyana lokaci daya akan fuskar shi. "Kabamu hanya mu wuce ko sai ka gama kare mana kallo?. Hajjo tafada cikin fada, ya sosa keya tareda cewa "na isa? Shigo uwar gida, gaskiya Kunyi min bazata, what a surprised. Kaucewa yayi Hajjo ta shigo sannan kb dake gabza mai harara, shidai fuskar shi a washe kamar anyi mai Albishir rabon shi da kalar wannan farin cikin tun ranar bikin su da bamusan y'anda ya watse ba.

Tsayawa tayi cak kamar dutse ta hade girar sama data kasa taki motsi kanta a kasa. Kallon ta yakeyi kasa da sama, tayi matukar yimai kyau da Alama ita batada matsala. Ajiyar zuciya ya sauke cikin wata irin kasala data lullube shi yace " you are welcome. Tareda nuna mata hanya yana D'an kaucewa, saida ta Kara second biyu ta rabeshi ta wuce, wani irin lumshe idanun shi yayi domin jin kamshin data wuce tabar mai, ji yayi kamar ta wuce da numfashin shi, saida yaji muryar kb yadawo hayyacin shi. "Malam wakake gadi a kofar da ka tsaya?. Shigowa yayi cikin sanyin jiki, idanun shi akanta, ta wani hakimce tareda daura kafa daya kan daya tana danna wayar hannun ta, hajjo mike kafafun ta tayi akasa tace "kai kabiru tafiya a jirgi inba makka zankoma ba baida dadi bazan kuma hawa ba. "Hhh Hajjo ai idan da mota kika biyo da haryanzu kina hanya baki iso ba domin Tafiyar doguwa ce. "Haka nan Mustafa yace min, amma kai bazaka bamu ko ruwa ba munsha tafiya ka zauna ka zuba mata ido kamar maye. Kallon ta yayi sannan yayi murmushi " Hajjo gidan gauro me zaki samu? Kawai bari muje mukawo muku abinci a waje. "Aa Allah ya tsari hajara da cin Abincin da babu bisimillah babu tsabta mudai kasamo kayan girki adafa mana agida ko bakada kitchen ne a gidan?. "Waye zai girka? Hajjo domin nasan kinfi karfin shekara talatin rabonki da girki. "Yoh ga Matar ka ai ita keda gida dole ta girka mana. "Nifa ban iya girki ba Hajjo. Mikewa yayi tareda kallon kb yace " let go to Mami. Ya mayarda maballan rigar shi yayi gaba, domin bayason tayi abinda kb zai gano tsakanin su. Yace "hajjo bari in nemo kayan miya akwai komai a ciki na kayan Abinci. Tace "toh madallah adawo lafiya. Suna fita Hajjo tace " mike kiga abinda zaki farayi kafin sudawo. "Nifa bazan yiwa kowa girki ba agidan nan. "Eh lallai wuyanki yayi kwari yarinya zaki kare iya shegen ki ne badai munzo ba? Toh zanga karshen kiyayya. Gyara zaman ta tayi bata kuma motsi ba, Hajjo tayi mitar ta harta gaji taki motsi. Haka ta mike tace " nidai bari in nemi masauki na inyi sallah kafin yadawo. Saida ta leka ko Ina taga daki biyu da kitchen sai falo dai dai zaman mutum daya, taga Alamar Wanda baya zama ta dauki Y'ar Jakarta ta wuce tana sana'ar tata. Sallah tasa dole ta mike ta shiga dakin da hajjo ta shiga, shine dakin da ta kwana lokacin da yakawo ta, a halin yanzu bata kaunar ta tuna duk wani abu daya shiga tsakanin su, so take tayi formatting komai a kwakwal war ta. Hajjo na tsaye ta rasa ta ina zata fuskanta tayi sallah saida ta shigo tace " sai ki nuna min gabas ai tunda kin shigo.
Wucewa tayi tareda bude drower ta ciro mata sallaya ta shinfida tareda cewa " ga gabas nan". Tayi gaba domin ita ma tayi Alwala.
Basu dade ba yadawo dauke da manya manyan ledodi ya wuce dasu kitchen kafin ya fito da Guda daya babba. Dakin da suke ya nufa tana zaune a gefen gadon sanye da hijab tana answer Nimrah dake mata tsiya. " Aa Amarya shikenan kinfa tare hajjo ta kaiki. "Ba inda natare, kamar y'anda akayimin na farko wannan ma haka ne kuma zan dawo ban shirya zaman Aure da kowa ba tunda ba'a dole yanzu.
Yana jinta tunda ya shigo ranshi ya sosu haka ya zauna gaban hajjo dake mike kan dadduma ya fito mata da take away mai gasashen naman kaza sai kuma wani dauke da gasashen kifi domin ya lura tana kaunar shi, sai kuma ruwa da drink's masu sanyi daya kwaso musu a firij yace " Hajjo bisimillah kafin adafa abinci.
"D'an Albarka irin wannan hidima daga zuwan mu?. Tafada tareda saka hannu ta debo cinya ta kai baki saida ta tauna tace " kai amma Naziru wannan gashin inji ne ko? Murmushi yayi kafin yace " meya faru? " ai jinayi kashin tama na taunuwa kamar kad'a. "Hhh hajjo ai itama kazar abincin kasuwace ya akayi kikeci kuma?. "D'an nema ko kabiru haka yake siyomin ita s yahuza spa. Harda ita dake waya saida tayi dariyar Hajjo. Yayi dariya har yagaji kafin ya mike ya fita bayan ya kalleta, ganin ta kishin gida akan gadon da akasha gumurzu last time.

Saida hajjo taci ta koshi ta mike tafita tareda cewa "ni nayi falo inyi kallo bazan iya zaman kurame ba. Zaman ta tayi aciki saida taji yunwa zata karta ta bude kifin taci ta kora da exotic ta kuma hayewa gado tasha baccin. Suna falo hajjo sai zuba mai hira takeyi yana dariya gaba daya ta yaye mai damuwar zuciyar shi, ganin ta a cikin gidan shi ma is enough. Kallon hajjo yakeyi a cikin yanayi na sonta domin ita din tana kaunar su fiyeda tunani domin tanason farin cikin su, karfe hudu da kanshi ya shiga kitchen ya dora musu girki, Hajjo batako saniba tana kallon gidan badamsi tana dariya. Ranta fess gata gidan jikanta. Saida hajjo ta tashe ta tayi sallah, ta kalleta tace " ki kwashemin kayanki kiyi dakin mijinki ina kallon ki sarai ki gama iya shegen ki ki gama. "Ni ba inda zanje ai bani nace miki zanzo ba. Tashi tayi ta dauki Jakarta tayi waje da ita ta Ajiye tareda cewa wuce ko in bugeki karki ganni haka da saurin kwarina ko Hadiza ta kama bugu zatasha bare ke.
Zuwa yayi ya tarar da rigimar ya kalleta tareda cewa hajjo " kibarta mana inda takeso. "Wallahi ban hada gado da ita sai dai ta kwan falo ba nan ba don haka kwashi kayanta ka kai mata cikin dakin ka. Ba musu ya dauka ya wuce domin ya matsu bai samu sarari ya saita mata hanya ba, ya daga mata kafa saboda hajjo bayaso ya bata mata domin ta faranta mai zuciya amma wannan hukuncin ya mai dadi dole ya nuna mata shidin fa namiji ne ba solo biyoba....... πŸ–Š

"Masu yimin sharri ko Oga yazo, to ai muna tareda abina shine ya janyo wannan murar don Kunsan ana sanyi daka yi wanka sau biyu a rana dole mura ta sarkafe ka bare ace abu ba sauki cikin wannan sanyin. Amma dai kuyi min Addu'a in yaye siyama na kafin akaini a barkπŸ˜‰


*Matar Soja*



🌻🌻🌻🌻



2⃣3⃣


............. Da kanshi ya kwashe kayan ya kaisu dakin shi tare da shiryasu a waldrop din shi, gefe daya ya ware mata yana wani irin murmushi, finally she is here with him, farin cikin shi baya boyuwa don haka baidamu da duk wani fushi da kunburin da takeyi ba, ya fito ya koma kitchen suna falon itada Hajjo, cikin minti kadan ya kammala girkin ya fito da plate da warmer Guda daya, Hajjo tace "wai kai kayi mana Abincin da zamuci? Amma ke Zainabu kinada aiki babba yanzu gaki mijinki ya shiga kitchen ya dafa abinci wannan wane irin zamani muke ciki? Batace uffan ba ya bude kular shinkafa ce, taji namomi ga busashen kifi tana zuba kamshi, "kai Naziru yaushe ka koyi girki? " Hajjo ai dole gauro ya koyi girki tunda bamai dafa mai. "Allah sarki Ashe haka kake rayuwa? Toh ba komai ai ya wuce da izinin Allah. Ta baje ta kwashi girki, yana kallon Amrah kasa kasa da kanshi ya dauki plate ya zuba mata tareda nufar kujerar da take zaune two seater ya Ajiye a gefen ta, "eat your food madam. Kallon Abincin tayi, ta kauda kai ya zauna a kasa kusa da kafafun ta ya sauke Abincin come down and eat kafin inyi miki dura. Hajjo tana gamawa ta mike tace zanje inyi Alwala naji ana kiran sallah. Tana

Please Login or Register in order to submit comment