Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai Amrah ta haihu twins. Ya tayashi murna kafin kace me labari ya bazu Sokoto, ana gama fadar na Amrah aka koma na Nimrah domin ta sauka lafiya itama da kyakkyawar babyn ta. Murna wurin kb ba magana, bayan ta gama shirya yaran tayi Asibiti tareda Nazir domin ganin Nimrah da baby. Harda fadan ta, " yanzu kinajin nakuda kema kika kasa fada kawai sai inneme ki in rasa toh meye amfani na da zamana tare daku kenan?. " ga amfanin ki zamu sha wanka. Ana sallamarta Nazir ya shafawa idanun shi Toka yace zaije da kanwar shi gidan shi tasamu kulawa a gaban hajjo saboda haihuwar fari gashi zasu kasa mata hankali. Harara ya watsa mai " haba wasa kakeyi ko?, " am serious.
Saida yayi jayayya yaga bazata yi aiki ba ya hakura, suka tafi gidan Nazir yace ai bakomai gidan ba bakona bane muje. Tayi farin ciki sosai y'an da Yayan ya nuna mata kulawa, daki guda aka ware mata harda gadon baby da komai na bukata, Amrah ma taji dadi, kosu Mami sun ji dadin abun da sukaji, labari. Tuni Mami tafara hada kayan ta tace wannan karon zataje ta kula da ya ranta. Nazir sai dare yazo ya ga yaranshi da kyau, masu kama da Abulkhair ya rungume macen kamar zai mayar cikin shi, sai kissing dinta yakeyi. Kallon shi Amrah tayi " yaya dama kasan twins zan Haifa ko? Kuma kasan watan haihuwa na yace " yes kinsamu ciki tun ranarda kika dawo garin nan yau watan Abina goma sha daya gashi da kanni biyu am missing my boy wallahi. Shiru tayi kawai don batason nuna nata damuwar, y'an da yamakale Y'ar yasa tace " me yasa kafi daukarta? " because I love her, she is just like you kina kamar ta. Murmushi tayi tareda gyarawa namiji kwanciya, ta dawo tareda rungume shi ta gefe yace " slowly madam kar Hajjo ta ganmu kinsan ta fa, oh I deserve it irin wannan yaki da nayi na zuba miki biyu once dole a soni......... 🖊


" very soon da Y'ar dar Allah zamu kammala a wuce wurin.


*Matar Soja*
[8/21, 1:05 PM] SAFIYYA: NAMIJIN DUNIYA


🌻🌻🌻🌻🌻



Page 4⃣7⃣




.............. Dariya tayi tareda kara shigewa " ba ruwana da zancen hajjo bazata raba soyayya ba saboda Al Adar ta. "Uhm madam wato na kara shigewa zuciya, lallai zankara himma in zuba triplets next kenan. D'an dukan shi tayi a kirji, "aa sai sunyi wayau gaskiya baza ayi musu irin na Abulkhair ba. Ya tayata suka shinfide yaran a gadajen su ya kunna musu heater don akwai sanyi a garin na kaduna, sukaje dakin Nimrah tana kwance Hajjo na jijjiga babyn yaki bacci, Amrah ta karbe shi tana taya ta. " lallai harke Kinyi kwari kina taya wani ke mai biyu?. " ai Hajjo ita ta saba ni na farko ne. " ke haihuwa batada sabo Y'ar nan Allah dai yasa ku gamata lafiya. Suka amsa da Amen. Shidai yana dubasu ya koma wurin yaran shi ta dan tsaya hira kadan tace zataje ta kwanta. "Aikam ansha fama kina bukatar hutu kafin zuwan baki gobe.

Tare ta kwanta a kirjin mijinta ba wani fargaba domin shi da kanshi tausayin ta yakeji bata shekara ba ta sunkulo biyu dole ya bita a hankali, ya bata dumi tayi bacci lukum, ko yaran da suka farka shiya jijjiga su suka koma saida Asuba ya bude musu nono yafara basu, macen ya fara bawa ta bude idanun ta, tareda D'an matse fuska, " Yaya yada haka?. " Ayi mana hakuri yunwa mukeji Momy. Gyara wa tayi tareda tashi ta rungume ta tana bata, tana gamawa ta mikamai ta karbi yaron shima ta bashi. Kwantar da ita yayi tareda mikewa ya je ya hada mata ruwan wanka yadawo ya karbeshi yace " oya kije kiyi wanka kafin Hajjo ta gama da Nimrah tazo tayi musu nasu. Da taimakon shi tayi wanka ya danna mata jiki da towel da ruwa masu zafi sosai, taji dadin jikinta, ta fito ta shirya cikin sabuwar atamfa taji umbrella style tafito a Matar so abinta. Sai zabga kamshi takeyi. Ya zuba mata ido cikeda so " Matar Nazir kina siye zuciyata baki daya bansan irin kyautar da zanyi miki ba?. Matsowa tayi ta rungume shi tareda manna mai kiss a kumatu, " bana son kyauta sai dai ina so in mallaki mijina nikadai domin zanyi kishin inga kana bawa wata irin wannan kulawar da kake bani mijina. "Ai ni nazama mijin Hajiya. Yes nasan me zanyi miki. " menene? " surprise ne ba yanzu ba. Ya fita zuwa kitchen. Da kanshi ya hada musu breakfast, ya kaiwa su Hajjo ya kai musu nasu daki, ita kanta Nimrah ya burgeta lallai Amrah tayi dace da miji nagari,
Saida Hajjo tayi mata wanka ta wanke yaron sannan tayiwa y'an biyu.

Da kanta ta gare dakin tasa kamshi ta canja bedsheets kafin ya dawo, ya kalleta " bansaki aiki ba fa malama. "Ai kawai wannan ne nayi. " ki huta you deserve some rest. Ajiye mata tray yayi ta kalla harda pepper soup din da Hajjo tayi musu jiya na kayan ciki, ya hada mata tea tareda mika mata " oya sit down and eat kinsan kina jego kici Abinci da kyau yafi wanka inji doctor. Murmushi tayi tareda da mai kallon I love you. Yace " me too tayi dariya. " ai bance komai ba Yaya. " I understand the look basai Kinyi min bayani ba. Ya shige yayi wanka tafara shan tea, kafin ya fito ta hadamai nashi, yana Shiryawa ya zauna ta mika mai cup, ya karba yana cewa "tank you Momy. " nazama Momy kuma? Yes Maman twins dina". Saida ya masu Hajjo sallama yatafi hajjo ta zo ta musu wanka ta shirya su suma, tace zataje ta kwanta don D'an su ya hanata bacci da dare. Da taimakon mai aiki ta hada musu abinci domin zuwan Mami, dayan dakin ta gyara tasa sabon zanin gado ta zuba drinks a karamin firijin domin Mamin ta, misalin karfe daya suka iso, Kb ya kawo su, Dukan su sunyi murnar ganin Mami da Farha, Abulkhair na manne da Mami ko Kallo Amrah bata isheshi ba, ta mika hannu yaki zuwa. Tace " ai gaka ga Mami tunda kayimin snatching uwa. Zama sukayi a falon hajjo ta taso tana masu sannu da zuwa, Mami na yimata sannu. " Allah sarki uwata wainnan ya'yan sun wahalar min dake. " kedai bari kar wannan gudan yaji labari. Nimrah ta kwaso Abinci Mami tace ai sai tayi sallah. Farha dai sai fama take da jarirai, jitake kamar ta gudu dasu, tanata yi musu Tsiya " wai su Nimrah anzama Mama. Dakin Nimrah suka je suna ta hirar su suka bar Mami da Hajjo. Sai karfe hudu ya shigo gidan shida kb. Suka yiwa Mami sannu da zuwa, yayi matukar farin cikin zuwan nata. Saida duka D'an taba hira yace zaije ya watsa ruwa. Amrah ta bishi. Yana shiga ya rikota zuwa kirjin shi. Ya rungume ta gam. " Yaya wannan farin cikin fa?. " Alhamdulillah, Baby ina farin ciki domin nasan da bake nake Aure ba Mami bazata taba zuwa gida na baby, yau gata har zatayi kwanaki dole inyi farin ciki. " tank God kasan saboda ni tazo, wama yace maka mamanka ne? Ummin ka na Sokoto. " yes nasani basai kin fadamin ba, Amma karki manta Abi ya kwace miki ita. " Hmm kana gani yaro yaki zuwa wurina. "Nima yaki yarda dani duk naci na da kewar shi da nayi.

Zuwan Mami da Farha ya taimaka wa Hajjo sosai domin sun dauke dawainiyar gidan baki daya, har wankan Nimrah Mami keyi Amrah kuwa mijinta ke mata safe da yamma idan yadawo aiki.
Kb na zuwa shima ya duba Matar shi da yaron shi, sai Abinda sukeso Mami ke dafa musu, harda shi yanzu yana manne da Mami kafin suyi bacci, itama taji dadin zuwan nata farin cikin ta baya boyuwa ganin yaranta cikin kwanciyar hankali yasa taji dadin zaman nata ga shi dakin ta daban ba takura. Ko kb yana jin dadin yanda Nimrah ke samun kulawa da babyn shi yakan raba dare wurin su kafin ya tafi gida. Kafin suna sungama siyan duk Abinda suke bukata. Sunga mutane makota wainda suka sani da wainda basu saniba a kullum suna shigowa. Ana gobe suna y'an Sokoto suka iso. Harda FARIDA Fahad ya barta wanda hakan ya taba zuciyar Amrah domin har yau bata taba zuwa nata gidan ba saboda Nazir da kishin shi. Sadiya da Momy da farida harda y'an uwan Momy dana Ummi sunkai kusan su goma. Kb ya basu key din gidan shi domin su zauna acan shi ya canja sheka. Sun kwana suna girke girke da soye soye na gobe suna tareda taimakon makotan su Amrah. Raguna shida Nazir ya kawo kowa biyu kb ya kawo rangadeden sa, hajjo tace " Zainabu wainnan ya'yan naki basu san ciwon kudi ba, ina zamu kai nama ni Hajara. "Allah dai ya saka musu da Alkhairi ya kara budi. Momy tayi farin ciki sosai da ganin y'an da Nimrah take samun kulawar D'an uwanta da yanda take tsoma biyar ta wanke goma, a gidan mijinta, ko FARIDA ba Abinda zata nuna mata, hankalin ta ya kwanta ta saka hannu sunata kula da jikokin su, washe gari suna aka sha shagali kowa yaci yasha yayi hani'an nima dai irin garar Arzikin da nagani naki gayyatar kowa naje nikadai na kwaso namomi da drinks don an dade ba ahadu ba, makota ma sun sheda sunan y'an uku, domin rana daya suka diro duniya. An sanyawa D'an gidan nimrah Nazir wanda kb yace dole yawa Aminin shi takwara, hakan ya burge kowa har Amrah tace ai dole taji da mai gidanta kuwa, su kuwa y'an biyu aka saka ma macen Aisha wato Ummi sai namijin Suleiman. Ummi da Abba babba sunyi takwarori. Don yaso ya kuma saka Zainab Mami tace akul ita an dade da yimata takwara batason kari. Yawa uwar shi.
Hajjo sai Hamdala takeyi domin Allah ya mata duk Abinda ta roka hadin kan iyalin ta da kuma kwanciyar hankali ba Abinda ya rage mata sai cikawa da Imani taje ta hadu da tsohon masoyi Alu.

Anyi taro lafiya an watse lafiya sun kimtsa ko ina sungyara sun soye musu namomin su sunraba na rabawa sun Ajiye musu nasu kamar yanda akeyi a al adance. Momy tace sufara shirin komawa gidajen su gobe tunda angama suna. Nazir yace bai yarda ba. Suyi sati kafin su koma. "Mami ta ce ai in kanada iko da Sadiya bakada iko da farha da kuma farida sannan gida munbar Aisha kadai dasu Abba kaga ba dadi kabar su su koma ni na kara sati daya. Bai soba haka ya hada musu shatara ta arziki washe gari ya mayarda su ta sama,.......... 🖊




*Matar Soja*
[8/21, 1:05 PM] SAFIYYA: NAMIJIN DUNIYA


🌻🌻🌻🌻🌻🌻





Page 4⃣9⃣



............. Farin cikin shi baya boyuwa domin da a tsorace yake karta botsare akan cikin wannan karon sai ta shayarda shi mamaki, don haka hankalin shi ya kwanta. Mami da kanta tace " Zainab cikine dake ko?. "Eh Mami. " toh Allah ya inganta, gashi zakije hajji zaki ji jiki duk da bakya wani laulayi. " ai Mami ko inayi sai na girgije Allah ya kiramu ai gwara mu leka." Farha ita tanada karamin ciki tafiya sai badi inji mijin nata. " Allah ya kaimu ya kuma Y'ar da. Abulkhair ya shigo da rigimar zaisha ice cream. Kamar sabon D'an yaye, Mami ta tashi da Sauri ta ce "aa muje akwai sauran da Abba ya siyo maka ai. " Mami yanzu haka yaron nan ke wahalar dake? Gaskiya ki rika Zane shi. "Saboda laifin me? Kawai don yaro na son Abu yace abashi kuma akwai sai in dake shi?"Mami bakiga irin shagwabar da yakeyi bane? Momy ce ta shigo tareda cewa " toh kisa adakar min miji kisha mamaki Amrah, karkizo ki takuri yaro a gidan su. " aa Momy gidan mu dai shida ke karere. "Aa kin so kanki dayawa in kikace ba gidan subane ai. Karbar Ummi tayi ta goya tace " bari in ara kafin da'na yagani ya hau ihu. Mami tace "gaskiya kuwa kema kinsani indai baba ne.

Sati biyu sukayi ta koma kaduna ita kadai cikeda kewar ya'yan ta da Hajjo domin tace zata tsaya sallama kafin lokacin tafiya don har shagari sai taje. Gidan yadawo daga ita sai shi, kamar sabbin Amare suka dawo, soyayya sabuwa, ya more y'an da yakeso. Kwance suke a gadon su bayan sun gama shakatawar su, yana nanuke da ita, " baby zanyi kewar ki kafin kidawo. "Wata daya nefa Yaya. "Wata daya ai ba sati daya bane, kinsan wahalar danasha bayan tafiyar ki Sokoto? And ba yarana baki, gaskiya inkika dawo zan dawo dasu har Abi bazan iya zama basu ba. "Zakaje kacewa Mami me tabaka yaranka kome?.
" yes zata fahimta ai. "Hmm bandamu ba ni yanzu domi nasan ko mu bazamu basu kulawar da take basu ba, bazan iya karbar suba domin ina ganin irin y'an da take farin ciki idan suna tareda ita. "Allah ya raya mana su toh.


Alhamdulillah sunje aikin hajji su uku Itada Hajjo da Nimrah, wanda tabar Nazir little a wurin Ummi itama don Momy tace bazata karba ba D'an ta nada kishi sai dai ta kaiwa Ummin su. Ummi kuwa ta karbe ta yaye itama. Sun gudanarda ibadar su cikin koshin lafiya, bakace tanada ciki ba, tayiwa mijinta Addu'a sosai ta neman kariya a gaban ka'aba, tayi Addu'oi dayawa harda kukan ta, ganin ta gaban dakin Allah, muma Muna fatan Allah ya kiramu in munada rabo. Sunyo tsaraba kamar ba gobe domin y'an uwa, Hajjo kuwa Nazir yasha Addu'a ganin ta koma gaban wannan babban dakin domin tun da jajayen sawu taje sai gashi jika yakai ta, don haka tace ko yanzu ta mutu ita tagodewa ubangiji.

sundawo gida lafiya, cikeda tarbar y'an uwa, domin a sokoto suka tashi, don haka Nazir bai samu zuwa ba, saboda yana busy, kiranta yayi yace barka da dawowa Hajiya ta. "Tace yauwa Alhaji na, Allah ya kaimu tare next time. "Insha Allah, ina shigowa gobe yau naso in kasance nine wanda zai tarbeki ya kwashi tabaraki.
"Karka damu nayima tanadi babba sai kazo. "Allah kice in shigo da karfi na kenan ?. " sosai karka manta dai da babyn ka dake ciki. " Suma sunyi kewar Dady ai.
Washe gari gidanta tasa aka gyara mata kafin zuwan shi da taimakon kamal, ta kwashe duk kayanta takoma, shirya mai girki tayi mai rai da motsi tasha wanka taci ado cikin wata irin Oman jallabiya datazo da ita hadaddiya. Ga cikin ta yad'an fito, tayi wani irin kyau ga hakorin ta guda daya data saka yana walwali.

Misalin karfe biyu ya shigo Sokoto, gida ya fara zuwa a gurguje yaga su Hajjo ya mata sannu da zuwa, ya kwashi Albarka ya tsaya yad'an ga yaran shi ya wuce gidan shi. Yaga tarba kuwa domin bayarda shi tayi kamar wani Abi don tattali, har Abinci a baki ta bashi ya saki jiki ya kwashi gara, kafin su kule tamai sannu da zuwan dayafi muradi. Ai kuwa ya yaba, bayan sun natsa ta fito mai da katuwar akwatin shi datayo mai na musamman, jallabiyu turaruka dadduma da kuma iners masu Aji. Yace " kaga mijin hajiyar ba. Ya yaba sosai har tagani a bayyane. Ta nuna mai tsarabar kowa tundaga su Abba dasu Mami da yaran su, ya gyara zaman shi yace " madam dama ina jira kidawo ne muyi shawara, nagaji da wannan aikin yanzu inaso insa takarda idan muka samu major this year indawo inyi business dina anan, lokaci yayi da nakeson hada kan iyalina wuri daya kuma ku samu lokaci na banaso yarana su taso ba agaban mu ba don haka zamu dawo Sokoto baki daya, ko ya kika gani?. " hakan yayi Amma kayi shawara dasu Abba first kaji daga garesu. " Insha Allah ina zuwa anjima zamuyi maganar.

Kb ma ya zo ya kwashi Matar shi suka tafi da D'an su daya saba da Ummi sosai, Amrah ma saida ta kara kwana biyu tabi mijinta bayan ta sallami kowa sukabar su Hajiya Hajjo, batada labari sai na zuwa makka yanzu tana mamakin komai ya sauya. Yasamu su Abba da maganar dukan su ba wanda ya hanashi domin shiga aikin ra'ayin shine don haka tunda yace yanaso ya Ajiye bazasu hanashi ba sai suyi mai fatan Alkhairi. Yayi farin ciki, Mami harda murna domin tunda yasamu accident aikin ya futa mata akai. Don haka tuni yafara gina musu wani tafkeken gida mai hawa daya, zuwa wasu y'an watan ni cikin Amrah yayi girma sosai don haka Abba yace bazai bar uwar shi tazo ba Amrah tadawo Sokoto harta haihu. Baida zabi dole yabarta ta tafi duk da taji tausayin shi da Nimrah da batada kowa sai Amran. Wanda ba dadewa ta kuma sunkuto Y'ar ta mace wannan karon mai kama da Amrah, ai kuwa kamar nazir ya cinyeta saboda so taga gata wannan haihuwar ma wurin miji da ya'n uwanta saidai ta godewa Allah.


************************
Alhamdulillah bayan shekara biyar

Gidan na nazir ya cika da iyali domin yaran shi shida maza uku mata uku, Abulkhair yayi wayau sosai yana zuwa makaranta, burin Nazir ya cika yanzu ya hada kan iyalin shi saidai a cikin wannan shekarun sunyi manyan rashi a family guda biyu Hajjo da Abba Wanda ba wani dadewa tsakanin su , wanda mutuwar ta jijjiga wannan zuri'a ba kadan ba, wanda bayan rasuwar Suka dawo da Mami gidan su, part dinta daban, kullum tana cikin jikokin ta masu debe mata kewar mijinta abin sonta.
Rayuwar tanayi musu dadi harkokin su na kara habaka daga shi har ita, a cikin wannan lokacin har ta samu hada digirin ta a D'an fodio wato UDUS.
Sai dai tace Alhamdulillah domin duk wasu buruka nata Nazir ya cika mata su a rayuwa.
Hangota nayi cikin D'an kareriyar motor, taci ado kana ganin ta kaga Matar so tana walwali cikin gwala gwalai da tsadadden leshin ta, ta faka a katon harabar gidan nata, tana zuro kafarta yaran suna fitowa da gudu, Baban su na biye dasu, rungume ta sukayi suna Oyoyo Momy. "Kiyimin a hankali nagaji karku yadani, Ina Mami na da Abulkhair?. Ummi ce tace " yana can wurin Mami a dakin ta yana bacci.
"Kumuje ciki. Suka karbi ledar data ciro musu suka karba suka ruga aguje suna murna sunga sweet da su ice cream.
Yana tsaye nade da hannu yana binta da kallon so, saida yaran suka shige ya karaso tareda rungume shi ba ruwan shi da masu aikin gidan da mai gadi. Tace " idanun yaranka fa Oga. " I don't care, naga kina kara zama young ne saboda kin kwana biyu ba ciki, don haka muje daga ciki yau zan zuba miki y'an uku ba twins ba. " Dole inkoma young ina tareda NAMIJIN DUNIYA ya rikemin kai macici ina wasa da bindin. "Yeah you deserve everything my life. Kissing dinshi tayi suka shiga ciki. Wurin Mami suka fara shiga tayi mata sannu ya aikin dai? " ai Mami kamal na mugun kokari wallahi yau kawai dana D'an zagayasu nagaji. " toh ai wurin ne da girma Kinyi kokari Allah ya sa Albarka.
Anan suka bar yaran suna hayaniyar su suka wuce dakin su. Shiya tayata tubewa shima ya tube yace suje ya wanke ta domin yaga Alamar ta gaji. "Zankoyi farin ciki idan nasamu hakan habeebi na. Ya sunkuceta suka shige..........


Ni kuma na dasa Aya domin kar in zake da yawa tsegumin ya isa haka sai muyi kokarin komawa wani gidan da izinin Ubangiji, mun kammala da Y'ar da da Amincewar shi don haka sai ince Alhamdulillah, inda mukayi dai dai Allah ya bamu ladan, inda muka kuskure Allah ya gafarta mana, wainda muka batawa Muna baku hakuri wainda mukayiwa dai dai kuma hakan mukeso domin faranta muku shine burin mu a rayuwa. Sai mun hadu a wani labarin Insha Allahu nagode.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment