Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

darewa tsabar tsotson ki don haka dole ki bawa yaro shima yasha ban son iya shege. D'an matsowa yayi tareda cewa " baby daure kinga yana kuka kibashi ya sha kinga ma ruwan na zuba. Ya tara hannun shi kasan nonon tareda mayarda bakin yaron yana lashe lebe kamar ya maye gurbi. Hajjo tace " kar inkuma gani kin cire mai sai ya koshi kinji ni ko?."baby ya Idan inasha bakya jin zafi ni dakeda hakori, shi gashi bakin shi bakomai kina jin zafi?. "Toh fadamin mara kunya kana zuke madarar Arziki ai ko baka fadaba ansan me zaka iya aikatawa yanzu kuwa daga hange sai leke kuma zoka fice kafin in ci mutuncin ka mara ta ido. "Kunnen kine ya jiyo miki da sa idonki kinzo kin kwakube kin hanani sakewa nida iyalina, baby zanje indawo zuwa anjima tareda yarona zankwana inga me hanani yau, tunda bani nace a raboni da gidana ba, wallahi ba wanda zai sani zaman maraici niba maraya ba. Yayi waje yabarta da salati da bambami, Amrah na dariya domin ta lura yayan ya karo wulakanci yanzu......... 🖊



Maji ma gani kuwa mu ai karshen rashin kunya.



*Matar Soja*

NAMIJIN DUNIYA


🌻🌻🌻🌻🌻



Page 4⃣3⃣



..............Ai kuwa ya bar mita saida ta Kira Mami tafada mata, " kijawa yaron nan kunne karya dawo min gida wallahi don naga take taken shi sarai bana arziki bane. "Toh Hajjo zanyi mai magana. Mami tace, kiran shi tayi tareda yimai fadan ya daina saka musu tsohuwa a gaba. " Mami ba Abinda nayi mata, kawai so take ta hana ni ganin iyalina saboda wata al ada tata ta tsufa. "Toh gwara ka fada inji, toh ka kiyayi sasan nan yarinya na jego kaga gobe gidan nan a cike zai wuni don haka inaso kayi nisa dasu banson rashin kunya.
Amsawa yayi kawai yayi mata sallama, kwanan nukufurci yayi ranar, bacci mai cikeda kewa da farin ciki, yanzu shima baba ne tanada D'an kanshi, wayar shi ya fitar ya rika kallon hoton yaron dana Amrah da ya dauke su tana bashi nono batareda tasani ba, tuni ya D'an saki fuskar shi, "don't worry baby zaki saba.
Anan dai gidan ya kwana sai da safe ya tafi gidan shi domin ya kwaso kayan su daya siya musu sababbi. Don haka saida ya hada da taimakon kamal ya tayashi debo wasu, part din Mami yasa aka kai aka jibge su, tayaba sosai da irin bajintar shi, wanda Hajjo data gani fada tafarayi, " saikace hauka ko akanka akafara haihuwar zaka kashi zarafi irin haka. " badon ke nayi ba don haka ba ruwan ki. Yafada yayi waje domin haushin ta yakeji.
Part din Hajjon ya tafi domin bayajin zai iya yin zuciya da ganin iyalin nashi. Lokacin ta gama cin Abinci tana shiryawa domin tana fitowa wanka mai kawai ta shafa ta fara cin dumamen ta da kunun sabara, don hajjo ta hana shan shayi tace tasha abu mai amfani da zai gyara nono na gargajiya yafi. Itama da yake Y'ar gargajiya ce bata damu ba, tayi shar tayi cikar jego, ta ciro breast pad zata saka ya rike hook din brah din ta baya yana Ajiyar zuciya, leko da fuskar ta yayi ta kafadar ta, " good morning Mrs Nazir, ya kike da baby na?. "Morning sweetie ya ka kwana?. " Alhamdulillah, meye wannan kike sawa yafada yana leka rigar Maman. Yana hango yanda suka ciko suna kyalli da shekin cika, " breast pad ne nonon na zuba karya bata min riga, yaya kaga ya cika da yawa yamai yawa duk hadamar shi baya iya shanyewa. " Hmmm babana ne mai hadamar? Ina yake? " Momy ta goyashi. "What Momy please karku bar ma Matar nan yarona ta cutar da shi please you no she is wicked. Juyowa tayi tareda cire hannun shi a kafadar ta, " please Yaya forget everything, momy ta canja wallahi tausayi take bani don Allah kaima kayi hakuri ka daina tuna komai. "Tunda kince haka shikenan, but naji tsoron halin Matar nan sosai she is very bad. Wani irin kallon stop it tayi mai yace "shikenan. Ya mayarda hankalin shi kan abun da takeyi tun farko, riga ta dakko zata saka ya rike, "what are you doing?. "Can't you see am wearing my shirt. "You are not supposed to wear it. "Why? " cos ina kan kallon su ban gama ba, please leave them like that. "Za a shigo karka manta muna dakin Hajjo ne fa. "Yeah of cos zata iya zuwa da fitinar ta, yanzu, Hmmm ok dole inyi hakuri zuwa lokacin da zamu kasance mu kadai, dole inyi son raina. "Meye a ranka? "Right now? A lot. Yana bata wani irin dirty looks. Dariya tayi domin ta gama karantar shi tsab, tayata yayi ta saka rigar amma baiyi aikin a free ba saida ya D'an latsa su har yabata mata brah tana ashh yaya akwai zafi yanzu. "Sorry am obsessed with them. Yafada yana jan numfashi, canja wata tayi yana like da ita ta mayarda rigar ta tareda daura D'an kwali ta feshe Jikin ta da turare, sai kallon ta yakeyi kamar maraya. "Zan lallaba inje wurin Ummi na inci Abinci don naga ni yanzu na zama marayan karfi da yaji haka kawai kun mayarda ni kamar Almajiri. D'an matsowa tayi tareda rungume shi kadan, " sorry dear lokaci ne zamu koma gidan mu bamai sa mana ido kaji. "Hmmm ok. Ya kara shigar da ita kirjin shi yana jan numfashi a natse. Salatin Hajjo ya janyo hankalin su, Amrah ta daure fuska taki fita a kirjin shi saida ya saketa don kanshi yace "let me go before she start shouting.
"Wallahi ubanka sama'ila zakaci ka dawo min gida mara kunyar karya, mango pa yaci uwashi engila taci gidansu kaida turancin, ke kuma kici gaba kece a ciki.
Shidai yayi gaba yana dariya, Amrah ce ta haye gado domin ta D'an huta kafin baki sufara zuwa tace " kin faya sa ido wallahi mutum da mijin shi ba kwarto ba kita damun shi. "Eh kije ki bude mai ya dirka miki wani cikin Jikin kine zai gaya miki, shi nashi siyayya wadda ko motsa mai Aljihu batayi ke kuma Jikin ki ne zaiyi motsi, wai miji, ni za afadawa miji, yaushe kika fara son mijin da har kya gayamun magana Y'ar kusun uwa. "Koma yaune ina son A buna kedai harda kishi Hajjo don haka kizo mu raba kwana kinji Uwar gidan Yaya naziru. " aa Allah ya kiyaye ni, ai nida malam Alu haka yake fa zaman mu baiyi karko har in haihu ubanki ba, wannan irin tsatsuba haka namiji like like kamar Ayu gaskiya yaran yanzu bature ya gama dagula muku kwakwal wa.
Juya mata baya tayi domin tariga ta saba da wannan mitar, ko bacci batayi ba Farida ta shigo da katon cikin ta rikeda Abulkhair data amso a wurin Momy. "Masu jego. "Kai Aunty da wannan nauyi kika fito kuma Yaya Fahad ya barki? Ai tunjiya naso inzo kamar inyi tsuntsuwa nakeji, Wayyo ji nake ina ma nice na sauke. "Allah ya raba lafiya Aunty kin kusa ai. Tace amen tana kwakube da yaron, kamar ta gudu dashi, "gaskiya Amrah Yaya yayi miki wayau babana duk shi ya kwaso ba Abunda ya rage miki. "Ko Aunty? Sosai har girar su iri daya ce, ke bari inkaiwa Fahad babana ya gani yana falon su Abba. Muryar shi tajiyo da Hajjo a falon ta, Amrah ma ta mike tareda daukar hijabi ta saka suka fito. Tsiya yafara yimata "kaga mai jego anyi mana wayau kin sauke kinbarmu. "Ai lokacine kuma ta kusa.
Shigowa Yaya NAZ yayi fuskar nan da magana yasamu gefe daya ya nade kafa akan kujera yana danna wayar shi. Kallon shi takeyi ta wutsiyar ido har Fahad ya mata barka ya dauki babyn tareda Ajiye mai bandir din y'an dari biyar biyar guda biyu ya fita, FARIDA tabi bayan shi bayan ta mikawa yayan shi. Tashi yayi ya shige ya kwantar dashi kan gadon shi na jarirai dake nan dakin Hajjo. Ta shigo tana kallon shi " Yaya what is that? Tafada tana daga gira tareda murmushi. "You no already, har yanzu bai mun ba wannan gayen wallahi. "Oh yaya why? " because ya bude banzan bakin shi yace yana sonki don haka na tsani ganin yana miki magana I hate it, tank God kin saka hijab baisamu ganin Abunda ya rasa ba. "Kai yaya kishi bayan kasan wadda yake Aure? Yes I know the fact that a rashin Uwa yayi uwar daki.
Tayi subutar baki tace "toh ya zakayi da Samir danaso shi fa? Shi wannan dako sauraran shi banyi ba. "What? Tuni idanun shi suka juya, yakasa cewa komai ya juya ya fita a zuciye, wanda bata taba ganin kalar fushin a fuskar shi ba.
"Na boni na taro ruwa ba lema.
Kafin kace me gidan ya cika, farha tazo Aunty Sadiya tazo, Nimrah na Hanya itama. Abba Mustafa ya sa an gasa rago domin y'an barka, suna hira suna zuwa suna yanko nama, ga Abinci kamar ranar suna, drinks kuwa NAZ ya kawo ba iyaka,
Da Nimrah ta iso gidan kuwa kamar su tashi sasan Hajjo, ranar Kamar kar dare yayi saboda farin ciki, Kb yazo suna tareda NAZ bai kuma lekowa ba tunda yayi fushi kb shikadai ya shigo. Ya mata barka tareda tsokanar ta ya fita wurin Abokin shi. Zuwa dare su Farha suka tafi gidajen su itada FARIDA, Sadiya dai taja daru tacewa kamal ba inda zataje sai angama suna kamar yayi kuka, hajjo tace "atoh duk tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa kan doka. Tafiyar shi yayi don baya iyawa zancen hajjo, kwana sukayi su uku suna hira basu kwanta da wuri ba. Can kasan zuciyar Amrah tana tunanin mijinta yaki lekowa da daren nan ma kamal yasa yakai mai Abulkhair dakin shi saida yaga yanaso yayi kuka tabayar aka dawo dashi, saida tabari kowa ya kwanta ta dauki waya takira shi, lokacin yana kwance yana kallon silin din dakin nashi, yaga kiran ta, yaki dagawa saida ta tura mai text, " I know you are not sleeping Yaya, please call me back. Saida yaja dogon numfashi ya dauka ya danna mata Kira, koda ta dauka baice komai ba, ita tafara magana, " am sorry for hurting you my lovely husband. "Sorry for what? Ni na isa in sauya miki zuciya ne Zainab, kinso shi tun kafin ki fara sona bayan ni na rayu da soyayyar ki a zuciya ta, bakiyimin Adalci ba yazaki so wani bani ba? Bantaba tunanin nayi sake har wani yasamu matsuguni a zuciyar kiba, inada kishi mai zafi akanki Zainab I try my best saboda inkauda duk wani namiji a hanyar ki amma duk da haka saida wani yasamu wuri yayi gurbi, gurbin da bazama ki iya mantawa dashi ba kina kallon Idona kina fadamin wai kina son wani akan fuskata.
"Hmm nayi kuskure Yaya na, amma maganar gaskiya zanfada maka yanzu. "Naso Sameer so na kuruciya, kuma nagano cewa ba sonshi nakeyi ba kawai kuruciya ce ta yaudare ni, domin bai dade ba na manta dashi a babin rayuwata Wanda, nasan yanzu kai na daban ne a zuciyata Yaya domin bazan iya hakurin rashin kaba koda na wuni daya, akanka nasan meye so da sadaukarwa, yau jina nake kamar mara lafiya saboda kana fushi dani bansaka a Idona ba, me zanyi da soyayyar wani namiji bayan inada NAMIJIN DUNIYA kamar ka, soyayyarka tayimin dabaibayi da daurin da bazan taba iya raba zuciyata gida biyu inbaiwa koda Abulkhair ba, zuciyata takace gangar jikina naka ne ruhina nakane mijina.
"Hmmm kin iya siye ni da kalamai koda ina fushi kinsan y'an da kike sakko dani, na huce na hakura I feel relief. Hira suka farayi suna farantawa juna har saida Abulkhair ya motsa yace "take care of my boy good night. Dariya takeyi domin wannan kishin nashi ma na banza bayan ya gama da ita harda haihuwa mezai dame shi.

Haka kwanakin kullum gidan a cike yake su FARIDA sai sunzo, yaro mai goshi tuni kakannin shi sunfara jero akwatuna kowa da nashi su Mami Da su Aunty Zuwaira suma sun kawo nasu, Hajjo tace NAZ yazo ya ragesu yana kaiwa gidan su, kayane basa faduwa Alkhairi tako ina yaro mai iyaye, ga abokan arziki. Kwarya kwaryar liyafa NaziR ya hada ya gayyaci abokan shi, a nan harabar gidan aka baje canopy raguna kuwa Kamar ana gasar siya, kb ya kawo biyu Abba Mustafa yasiya biyu da sa haka Fahad ma ya kawo zungure re ga Abban Amrah ya siyo na kauri shima, don haka hajjo tace in angama sauran akai ayima Abulkhair kiwo tunda yazama mai raguna, ta shiga ta fita ranar suna itada mijinta da yaron su, sunsha anko kala kala itada mijinta, duk kayan da zatasa kalar shi yake sakawa, tasamu Alkhairi har saida tayi kuka tundaga kan sutura da ruwan kudi, ga kyautar ban mamaki da Nazir yayi mata bayan suna ya damka mata takardaun shedar mallakin plazar daya dage ya gina yace domin D'an shi da ita ya gina su, yabar wa kamal kula domin yasa mata ido akan komai, tayi kukan farin ciki har idonta ya kumbura, Su Abba sun taya ta farin ciki tareda shiwa Nazir Albarka Mami tace mishi Saura mota, tata ta kwana biyu. Yace "haba Mami wannan fa bata dade ba ga ta farko da ko cika hawan ta batayi sannan tana daukar nawa motoci zasuyi mata yawa. "Rungume Mami tayi domin tasan samun uwar miji tagari sai an tona zuciyar ta fal Alkhairi ba kyashi ba kishi, " Mami nagode wannan ma Ina zankai su. "Akul karki nunawa namiji haka, idan mijinki nada hali ki fantama haka hajjo ta koyamin tafada mana muci Arzikin mazajen mu domin mu suke nema don haka kema ki yagi rabonki kici kibawa mabukata kinji, Allah ya muku Albarka. Shidai ya dade da fita yana dariyar farin ciki yasaba jin ana samun matsala tsakanin mata da suruka shikam Alhamdulillah domin yasan soyayyar Amrah da Mami bata surukuta bace soyayya ce ta ya' da uwa tun fil azal.

Bayan sati guda da suna ya tafi kaduna domin check up ya kuma yi report na komawa bakin aiki wanda yana dawowa zasu tattara su koma kd. Tana nan gida tana shan gata batasan wahalar goyo ba sai yayi kuka akawo mata yasha ya koma kowa daukar shi yakeyi, sati uku da haihuwar ta Farida ma ta sauka, wanda akayi akayi Fahad yaki Amincewa ta dawo wankan gida, su Abba Sukace a kyaleta ba dole tunda ba Addini bane ta samu Y'ar ta, wadda farin ciki wurin su Momyn Fahad ba a magana a duniya tanason ya mace sai gashi Allah yabata jikar farko, Amrah taso zuwa ya fake da cewa bata isa fitaba Hajjo ta goyi baya, duk sunje itace Kawai harda kukan ta, data matsa yace " me kikeso kije kigani wanda mijinki baiyi miki ba tell me Zainab? Don haka tayi shiru bata kuma tada zancen ba, don ta ganoshi baya kaunar taje gidan ne Kawai saboda Fahad.
Har Nimrah tazo ana gobe suna bata jeba, sai dai suyi waya tana bawa Aunty Farida hakuri, tace ai kema kinsan Hajjo bazata barki fitowa ba kina jego. Taso tayi fushi amma tasan fushinta zai iya tada balli don haka ta hakura tasa ido. Bayan sunan FARIDA su Abba babba suka saka Abba Mustafa gaba aka mayarda Auren shi da Momy wanda saida tayi kukan farin ciki tareda binsu tana gode musu, tareda yimusu Alkawarin zata kiyaye da izinin Ubangiji shima Abba yaga canji don haka bai yi kasa a guiwa ba wajen hade kan matan nashi, Aunty Zuwaira nada ciki don haka Momy ta hanata komai sai dai ita tayi, cewa take ki huta karki wahalar min da yaro.

Saida Amrah ta cika kwana Hamsin Nazir ya diro Sokoto bayan yafada mata ta hada kayan su zasu koma dayazo, Abul yayi bulbul dashi sai wayau, Uban yanata murnar ganin shi kamar ya mayarda shi ciki, ga Matar shi itama ta kara kyau tayi cikar hutu da jego sai D'an duhun ruwan zafin da tasha Kawai. Lokacin da ya ganta yace " madam Nazir lallai su Mami sunyi kiwonku keda my son nine dai sai a A hankali. Kallon shi tayi " bayan ka kara kyau da jiki zakace wai sai a hankali. "Uhm saboda zaman gauranci nakeyi I need my wife close to me. "Am all yours. "I know that yanzu ku shirya gobe zamu juya nazo da jirgi ne zamu tafi da wasu abokan aikina gobe. Wani irin kallon tuhuma take yimai, " Yaya harka koma tukin?. " yes that's my work Kawai ina bukatar Addu'ar ki. "Hmm Allah ya tsare mun kai my dear. "Amen my lady. Get ready nafadawa su Abba we are leaving.

Ba karamin shiri akayi mata ba ciki da waje har Ummi ta gyara abarta a sirrin ce tabata wasu sirrika nasu na sakkwatawa, tasan taji gyara ta kara ilimi ta hanyar karance karance so take ta nunawa mijinta ta kara wayewa suna karawa juna ilimi ta hanyar zaman takewar Aure itada y'an uwan ta group suka bude duk inda suka samu sabon abu zasuyi shearing don haka ta daura damarar rike Auren ta da hannu biyu har tafishi matsuwa su koma gidan nasu ta nuna mai sabon karatun ta don haka tayi farin ciki da baice su tare a gidan suba gwara sutafi can bariki suci karen su ba babbaka.............. 🖊


"Allah ya taimakeni anjima ku samu update domin na yarda bawa baya yankewa kanshi Abunda zai faru nan da second daya, na daina Alkawari sai dai innemi Y'ar dar Allah, idan kanada rai ba lallai kanada lafiya ba, idan kanada lafiya akwai wasu uzurori don haka sai muyi fatan gamawa lafiya. "kuhuta jama'ar Arziki Allah yasadamu da Akhairin sa.

*Matar Soja*

NAMIJIN DUNIYA


🌻🌻🌻🌻🌻🌻



Page 4⃣4⃣



................Tunda ya fita bata kuma ganin shiba saboda busy sai da dare ya shigo a gurguje yace mata zai fita early morning don haka kamal zai kaisu airport din idan sun shirya. Ya wuce da kayan su da daren. Tunda safe Mami ta wanke Abulkhair suka shirya shi cikin kayan sanyi tareda rufeshi da D'an blanket dinshi. Ta shirya cikin wani D'an datsetsen code less brown tafito as Matar Ogan da dinkin ta na abuja bubu taci dauri da katon farin gyale ta rataya Jakarta baka da takalmi have cover baki, duk sun fito suna mata Allah ya tsare su Momy sai tsokanar Abulkhair sukeyi " toh na robar zaka tafi ka barmu da na karfen zamuyi kewa sosai, Ki kula dashi Amrah, shine maganar su Mami, hajjo kuwa fadan abi a hankali takeyi kar a janyo wa yaro lalacewa gashi bulbul dashi kar kuje ku cutar da shi. Banza takeyi da ita Kawai, ai bakinta ne ba mai hanata fadar Abinda tayi niyya. Sunbar gida cikeda kewa, harda kwallar ta domin tasan ta tafi zama ne wannan karon sai dai in sunzo ganin gida.
Koda suka isa airport sun gama komai ita yake jira, kamal na tsayawa ya bude motar tareda karbar Abulkhair, yana cikin kayan Shi na tukin yayi matukar yin kyau a ciki sai wani kallon ta yakeyi a kai kaice saboda sha'awar adon nata. Y'an da taga yana kallon ta ya kara mata kwarin guiwa tafito cikeda y'anga tana kashe mai ido daya. " wait till we reach home madam, karkisa in zubarda mutane fa. Murmushi tayi mai burgewa ya karbi Jakarta ya rataya a kafada danshi na hannun shi ya sallami kamal ya tafi shi kuma yamata jagora har cikin jirgin ta zauna a inda yake so, ya saka mata belt tareda cewa "take care of my boy ya manna mata kiss a baki ya mannawa yaron shi ya wuce.
Tasha gaisuwa a matsayin ta na Matar Oga captain kuma jogaran matukan na jiragen nasu, abun ya matukar burgesu y'an da yake kulawa da Matar tashi, wasu suce ai dole yaki kula mata yanada peacock a gida. Wato dawisu sarkin ado da kyau.

KADUNA

Wato sun isa garin na gwamna lafiya, yana sauka ya Kira kb yace yazo ya tafi dasu kafin yagama clearance. Ba bata lokaci ya iso ya tafi da ita, tun a motar tafara tanbayar ina Y'ar uwar ta? Dariya yayi "ai Y'ar uwar ki ta shiga hannu bata moruwa sai laziness muje tana gidanku tana jiranki. Tasha mamaki dataga sabon gida ba wanda suka saba zama ba, ya fi na farkon an canja komai sabo harda wurin parking mota, ga gefe daya kayan marmari ne irinsu lemo gwaba ayaba mangoe duka dai abubuwan da kasar mu ke iya dauka, batayi magana ba kb yace " kinsan mijinki yazama babban mutum dole ku canja mazauni kubar mana mu kanana.
Murmushi tayi mai Kawai. Gidan ya matukar burgeta komai Masha Allah tundaga falon har cikin dakunan wainda sunkai guda hudu kowanne da magewayin shi ga katon kitchen wanda ta samu Nimrah tana musu girki. Tar bar ta tayi cikin murna suka rungume juna Abul na hannun kb a falon. "Finally kindawo zanji dadi ga ni ga Y'ar uwata. Matsawa tayi tareda bude tukunya taga stew yaji namomi ta runtse idanun ta ta shaki Aroma, "madam kabir kinzama chef bansani ba. "Badole ba kodan in burge mijina. Kwala mata Kira yayi yace tazo ta karbi Abulkhair zai koma aiki. Suka fito tayi mai godiya ya tafi, batazo da kaya ba sai Yaya NAZ ya dawo daga ita sai Jakarta.
Sunsha hira kafin dawowar mazajen su, ta Kira duk y'an gida tafada musu ta sauka lafiya. Karfe biyu ya shigo a gajiye shida kb, ya wuce cikin inner room din shi tareda kiran ta. Ta Ajiye Abul a hannun Nimrah ta tafi. Yana kwance a gadon kafafun shi a kasa ko takalmi bai cire ba, ta duka tareda fara kwance igiyoyin takalmin ta zare harda socks din tana mai sannu. Idanun shi a runtse yanajin ta har ta je ta Ajiye a wurin da yake jera takalman gasu nan birjik. Tadawo ta zauna gefen shi tareda shafa fuskar shi yaja numfashi ta gangara da hannun ta zuwa maballan rigar shi ta fara cirewa. "Yaya daga gani ka gaji sosai. "Hmm yes tunda nazo ban huta ba har nadawo, I need a shower. Karasa cirewa tayi ya tashi zaune yana kallon cikin idanun ta, "ina ganin kece yau zaki sarrafani domin nayi weak sosai. "No problem my heart. Tafada cikin salon rikita shi, yaja numfashi "please take it easy for me karkisa in susuce gasu kb y'an sa ido. Murmushi tayi mai "sai subar mana gida my husband want to rest. "Allah my wife?. Yafada cikin mamakin canjin ta. "Sosai kuwa. "Ok bari dai in watsa ruwa mu sallame su subamu wuri we have all night. Doguwar Riga jallabiya ta ciro mai da sabon singlet da shot nicker ta Ajiye ta kwashe kayan da ya cire tasa a basket din laundry yana fitowa ya goge Jikin shi tace "zauna in shafa maka mai. " no bakyaso infita a dakin nan ko madam. Dariya tayi ta fita saboda ya nuna bayason ta kureshi tun yanzu dauriya Kawai yakeyi. Tuni kb ya baje yanacin Abincin shi, tace "Yaya na ba jira?. " wazai jiraku ai cewa nayi muci mugudu kafin mijinki ya koremu don baida kirki sometimes. "Toh yana zuwa yanzu yana watsa ruwa ne. Da kanta ta shirya mai a plate da drinks da salad din da Nimrah ta hada ya fito yana baza kamshi. A kasan carpet ya baje ta matso da tray din tasaka mai spoon ya faraci, kb na gamawa yace " let go madam mubar ma wannan gidan shi sai harara ta yakeyi. "Kaji da sharrin ka kuje din haka nakeso. Tashi Nimrah tayi ta dakko gyalenta da jaka Amrah ta rakata tace "don Allah gobe kizo ki tayani shirya kayana. "Toh Allah ya kaimu idan sun fita aiki sai inzo.
Dawowa tayi ta zauna sukaci tare Abulkhair na gefen shi a kan Y'ar Karamar katifa, "ki gama mu hada mai gadon shi domin

Please Login or Register in order to submit comment