Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anduba Al amarin nan kafin azo aji kunya, kaga namiji ne ba ayimai Auren dole ba. "Hajiya Hafsa ki daina wannan maganar domin ni mutunci nane zai zube, ya za ayi Muna mulkin gari mu gagara mulkin gidan mu gaskiya banason jin wata magana akan Auren nan,
Shiru yayi kawai badon ta Amince da zancen shi ba Sai don tasan bata iya jayayya da shi, saidai kuma har zuciyar ta tanajin bazata Amince ba dole tayi wani abu akai. A ranar bai Kwana a gidan ba tuni ya nufi hotel ya kama ya kwanta yana faman juyi, fuskar ta yake gani a duk lokacin da ya runtse idanun shi, bai san wace irin Soyayya bace ta shigeshi, bayajin zai iya hakura da ita, don haka gobe zaije gidan ya tunkare su bazai taba iya bin wani zancen Dady ba a daura mai Auren dole yana namiji gaskiya bazai iya hakura da Amrah ba. Zabura yayi tunawa da sunan ta ya dafe goshin shi. " is all your fault baby, da kinfada min sunan ki da hakan bai faruba. Dakyar ranar ya runtsa don haka yayi mugun makara da safe, domin saida gari yayi haske, ya duba wayar shi yaga miss call birjik daga abokai da Momyn shi, saida yayi wanka ya fito tareda mayarda kayan shi domin bai dakko komai ba Sai wayar shi da mota, ya fara kiran Momy tana dauka tace " kai ina ka shiga inata kiranka kaki ka dagamin waya, ga Baban ka yasa andaura Aure tunda Asuba a masallaci. "What wane irin daurin Aure ne haka Momy? " wallahi nima na tanbaye shi ya rufeni da fada don haka Sai hakuri ka kuma dawo gida ina jiranka. Cilli yayi da wayar tareda fadawa gado ya kife na D'an lokaci, kafin ya zabura ya dauki wayar ta ya fara dialing number Aminin shi, "mu hadu a kofar gidan su Amrah please yanzu. Ya datse ya fita ranshi na tafasa, a daura mai Aure kamar kaza Auren shi ace wai da Asuba? No way.


Amrah

Fitowa tayi rikeda basket din Abincin ya Naz tana sanye da Hijabinta har kasa mai hannu kalar onion, tafiya take kamar wadda kwai ya fashewa, tsoranta daya karon su domin tasan tunjiya basu kuma haduwa ba, ko ya zata kasance?
"Baby". Taji ance a bayanta, tayi Saurin daga kanta tareda kallon fuskar Fahad da Abokin shi da ya tsayar da ita jiya, diriricewa tayi domin ta rasa me ma zatayi, wani irin marairaice fuskar shi yayi tareda matsowa kusa da ita, " Amrah Amrah Amrah ". Kallon su takeyi cikeda mamaki da tsoro, cikin rawar murya tace ina kwanan ku? Ko akira Aunty Farida ne? " no baby am here because of you, please listen to me. Abokin shi yayi Saurin matsowa tareda cewa " Fahad please don't scare her, look Amrah akwai misunderstanding da mukeso mu warware please give us chance.
"Yes please baby, saboda ya shafi rayuwata and is all because of you. Duk ta rude ta rikice bata fahimtar me suke fada, burinta kawai tabar wurin kafin Yaya NAZ yafito ta kara laifi, Sai dai kash ya fito daga falon Abba. Yana sanye da jallabiya, hannun shi cikin pocket din jallabiyar, a hankali yake takowa, wani irin kamshi ke fita a Jikin shi mai matukar dadin shaka da kwantar da hankali. Bata ganshi ba saboda tabashi baya, saida ya iso kamshin shi ya sanarda ita, tuni ta Kara firgicewa, yana matsowa ya bai tsaya yin wani abu ba ya riko hannun ta dake rikeda basket din Abincin ya karba tareda jan hannun nata ya juya da ita. Saurin tarar shi sukayi ran Fahad a bace " please ba nazo muyi sa insa da kai bane am here to talk. Tsayawa yayi ya bashi wani irin kallon da ya kasa fahimta kafin ya bude Baki kamar bayason yin magana yace " don't come here and make confusion, na saurare ka because you are part of our family, so idan kanada magana go and meet our elders . Abba Mustafa ne da Abban Amrah suka fito daga wurin Abba babba ya same su tsaye kamar zakaru ga Amrah tsaye Nazir ya damke hannun ta kamar zata gudu , ya matso tareda cewa "aa Fahad lafiya dai? Dukawa sukayi har kasa tareda gaida su, Sakin hannun ta yayi, tuni ta ranta ana kare don dama a matse take matukar matsuwa, "bismillah ku shigo yaya na ciki. Juyawa sukayi su Fahad suka bisu shikuwa juyawa yayi tareda nufar hanyar dakin shi.

Zama sukayi a gaban Abba bayan sun gama gaisawa Abba babba yace "Alhamdulillah Fahad yau dai an daura Aure bisaga Umarnin mahaifin ka, andaura Aure karfe shida na safen yau,Sai muyi fatan Allah yabaku zaman lafiya.
Su Abban Amrah suka amsa da Amen.
Abokin shi yayi gyaran murya tareda Zama yace " Abba akwai matsala ne akan Auren nan, ansamu misunderstanding wanda bamu ganoba Sai jiya, kuma munyi kokarin Sanar da iyayen mu tun Ajiyan domin asamu gyara gudun kar ayi Abinda zai janyo matsala aciki. "Subuhanallahi, meya faru kenan ??? Kuma yau muna tare da mahaifinka amma bai fadamin komai ba . Abba ya fada gyarawa Fahad yayi tareda cewa "Abba nafada mai jiya Amma ya nunamin inyi hakuri da Abinda yafaru, kuma gaskiya zan cutarda kaina ganin idan na Amince bazan samu damar Auren wadda nakeso ba. Dukan su Jikin su yayi sanyi su Abban, Sukace "toh wacece kakeso kenan inba FARIDA ba? Cikin dukar da kai yace "Amrah nagani nabiyota har nan gidan, Yayan su ya hana ni karasowa shiyasa na turo Dady na saboda yasan bawai wasa ko yaudara ta kawoni ba, Amma bansan FARIDA ba bantaba ma ganin taba saida aka fara shirin Aure. Tsit falon yayi kamar ruwa ya cinyesu, Abba ya gyara zaman shi kafin yace "Toh Fahad ina tunanin kamar kazo nan kafin Aure, meyasa baka yi magana ba saida lokaci ya kure??. Shiru yayi kawai domin baida wannan Amsar, Abba Mustafa kuwa da Abban Amrah kasa cewa komai sukayi saida sukaji Abba ya fara tanbaya, "Yaya abi a hankali mu fahimta da kyau.waya Abba ya dauka ya Kira Nazir yace "yazo nan yanzu. bai dauki lokaci ba yazo. Samun wuri yayi ya zauna gefen su Abba kamar yanda ya saba. Abba ya kalleshi. "Naziru akwai abinda kefaruwa anan wanda nakeso inji daga bakin ka, "toh Abba. "Kasan lokacin da Fahad yazo neman Zainab anan gidan??. Daga kai yayi kafin ya Gyada, " eh Abba. " meya faru da akazo maganar Auren baka fadi abinda kasani ba kayi shiru?? "Abba Idan nayi magana nima zan taba rayuwa ta shiyasa nayi shiru. "Ban fahimta ba kayimin bayani????. "Abba Amrah ya biyo fa. "Idan Amrah ya biyo fa? Basai kafada mana ba musani kana kallo agaban idanun ka andagula lissafi Baki daya yanzu ta ina zamu faro ya kakeso mu warware Al amarin nan yanzu??. Fahad ya kalli Abba tareda cewa "Abba ya Hana ni inyi magana da ita, yace min wai matar shice. Gaba daya ido suka zubamai suna kallon shi, Abba babba bai iya cewa komai ba, Sai Abba Mustafa ne yace " me yake fada ne Naziru? " Abba gaskiya ne, Amrah Nake so Hajjo tasani, kuma itace ke hana infada muku tun farko, Da ta Amince da mun dade da yin Aure, da kuma hakan bai faruba. Ajiyar zuciya sukayi Jikin Abban Amrah yayi mugun sanyi domin yasan wannan abun zaija rikici ba kadan ba don haka cikin sanyin jiki yace " Fahad kaga anan nine karami a cikin y'an uwana bayan kanwata karama wadda tana nan yanzu haka a gidan nan, so zan rokeka don Allah tunda hakan yafaru an riga andaura Auren kayi hakuri... "Kabiru ko yanzu kayi shiru wannan maganar akan ya'tace Amrah don haka ba ruwanka kabarmin maganar. "Yaya kayi hakuri nima maganar ta shafi Rayuwar ya'ta FARIDA don haka dole inyi magana. Abba babba yace " Toh dukan ku yanzu shiru zakuyi ni inyi magana, Fahad kaje zamu nemeka idan mun gama magana da mahaifiyar mu. "Gyada kai yayi tareda Addu'a komai ya tafi y'anda yakeso.


Bayan Tafiyar su Fahad Abba ya hada taron gaggawa a falon dukan su iyayen harda matan su, Momy dai hankalin ta kwance ganin andai daura Aure, saidai FARIDA dake faman kuka akan wannan abun domin hankalin ta bai kwanta ba.
Saida kowa ya zauna harda Hajjo tana hakimce akan kujera, a cikin yaran kuwa Nazir ne kawai. Hajjo tace " me ya faru kuka taramu kamar masu laifi kunki kuyi magana? "Hmm zamuyi Hajjo, abubuwa ne suka taso da yawa yanzu mukeso mu warware su agaban ku duka, Na farko akan maganar Auren Naziru ne?. " waya baku izinin sa baki a cikin Auren shi? Ko yakawo muku wata yarinya ne a waje zai Aura? "Aa hajjon mu, yafada mana Amrah yake nema. " eh gwara da yafada muku, toh bazan bayar ba, ku fadamai ban basuwa. Wani irin Ashar Momy ta Y'ar fa, duk suka juyo suka kalleta " eh ku kalle ni Tunda ni mahaukaciya ce, wato magana ta da tunani na suna kan hanya, wallahi Yaya Zainabu bakida tunani, kina kallo an kalallame D'an an zabga mai Asiri yace ba wadda yakeso sai Amrah duk ya'yan dake gidan nan uban me tafisu? Gwaggo Hadiza ce ta mike tareda nunata da yatsa " wallahi Saratu zakisha mamakina a gidan nan idan kika wuce gona da iri. "Hadiza nan ba gidan ki bane gidan mijina ne kuma inada damar inyi magana ehe. Gwaggo Hadiza zata kuma magana Abba ya hanata, Hajjo dai na tsuke da bakinta tayi gum. Abba Mustafa cikin kuluwa yace " Saratu Kinyi kokari kwarai, kin Kuma taka rawar gani akan duk abinda kefaruwa a yau din nan, kinzo Kinyi dibar Albarka agaban mahaifiyata akan zancen Auren da kinsani ba Y'ar ki yakeso ba. Tuni bakinta ya mutu. Hajjo tace " kai Mustafa meke faruwa ne bangane ba? Cikin jin zafi ya mayar mata da abinda ya faru duka. "Ai toh hakan yayi dai dai Saratu kin kyauta wa kanki, kin mayarda yarinya bazawara tun bata tare dakin miji ba, domin dai bazan yarda in kai jinina ya wulakanta ba, don haka kai babba ka karbo min takardar Auren jikata yau dinnan basai gobe ba, ita kuma Amrah inada Wanda zaku daurawa Aure yau din nan ya dade yana neman ta itama tana son shi fin karfi mukayi muka rabasu don haka Anjima y'an uwan shi zasuzo kuci gaba da taron ku tunda dama yau ne daurin Auren da kukayi garajen daurawa da Asubahi. Wani irin kallo Nazir kewa Hajjo yana Gyada kai, cikin hade rai, zaka iya hango bacin ranshi a bayyane, Momy kuwa kururuwa tasa tana tsinewa Ummi, " Allah ya isa tsakanin mu dake nida Yaya Zainabu kin cuce mu kin gogawa ya'yan mu bakin jini takice kawai akeso, nazirun ma dama shi kin dafe ya cinye wannan Kuma kin shiga kin fita Kinyi kutun kutun kin watsa ya birkice yace sai Y'ar ki, wallahi sai munyi hisabi dake agaban Ubangiji. Mami ta kalleta cikin jin haushin halayen ta tace "Saratu sai dai toshewar kwakwal wa, amma kowa yasan gaskiya Kuma ya fahimta don ba D'an da kika Haifa anan, nidai bansan asiri ba kuma banyarda da Aisha tana asiri ba, Abunda na yarda dashi shine dabi'ar ta itace ta janyo mata farin jini, ke kuma banzayen dabi'un da kike yi shi kike dora ya'yan ki, don ma Allah yana duba zuciyar iyayen su maza yana karesu badon haka ba Allah kadai yasan me zai faru.

"Ya isa Zainabu karki bata bakinki akan wannan sha shashar, ku kiramin yaran nan yanzu dukan su. Hajjo ta fada, sudai su Abba sai shiru saboda takaicin kwabar da sukayi, domin harda laifin su da basu tsaya dogon bincike ba,
Shigowa sukayi dukan su, suka zauna harda Amrah, Hajjo ta kalli Farida da taci kuka ta koshi, abinka da jini tuni taji tausayin ta, don haka batace komai ba sai " farida Allah ya kawo miki mafi Alkhairi kinji kiyi hakuri, kuskuren Uwar ki yaja miki a rayuwar ki., ke kuma Zainab ina son inji ko har yanzu kina son malamin ki daya koyarda ke? " dago wa tayi zata yi magana sukayi ido hudu da Nazir fa fuskar shi kamar gobara saboda bakin ciki, Tsabar tsoro batasan lokacin da tace eh ba. Mikewa yayi kawai yabar falon Hajjo ta bishi da bakar magana.
Saida ya fita Abba yace " kina son shi Zainab? Girgiza kai tayi tareda cewa "aa Abba ni banason kowa.
Mikewa Momy tayi tareda nuna ta " eh ai da izinin Allah bazaki so kowa ba, yanda kika hana ya'ya na Aure kema sai dai kigani a makota, mu zuba nida ku. Ta juya tabar falon hajjo tace" munriga munce Allah don haka Allah ya tsinewa Aljanu ma ba shi boka da kayan tsafin ba kinji shedaniya,ku kuma ku tashi ku tafi zamuyi magana.
Tunda yafita dakin ya nufi parking lot yafada motar shi tareda kifewa a sitiyarin motar yana fitarda wani huci kamar kumurcin maciji, zuciyar shi wani irin tafarfasa takeyi kamar wuta, wani zancen baza abashi itaba duk a shirme yake ganin shi, bakin cikin shi itace da ta kalli Tsabar idon shi tace wai wani takeso tana hauka ne?. Yana wurin bai motsa ba suka fito suna magana a tsakanin su "ni dai bangane meke faruwa ba wallahi. Farha tafada. Nimrah tace "ai kawai kibar maganar ta manyace bamu a ciki sai dai muce Allah ya kyauta, itadai Matar sarman inji Hajjo zamu sha biki kwanan nan. Duka ta kai mata "Allah ya kiyaye wallahi bana yayin shi na wuce da Ajin shi yanzu, da yana sona dabai shareni kusan shekara ba. "Karki fada haka domin bakisan wane irin gargadi yasha fa ya daina zuwa. Zata bude Baki tayi magana kwaram ya dira agaban su fuskar shi kamar wuta idanun shi sunyi mugun kadawa saboda azabar kishin ta dakecin zuciyar shi, he don't care itada su waye ya ce " Wani kikeso bare ko? Ni bakowa bane a rayuwar ki I don't mean anything to you right? Karya kikeyi baki isaba. Hannun ta ya fisga ya nufi parking lot da ita tana turjewa, bude wa yayi ya jefata ya rufe tareda juyawa ya shiga ta other side cikin zafin zuciya, tafara mutsu mutsun budewa, wata uwar tsawa ya buga mata dole ta koma ta natsu. Fisgar motar yayi kamar zai tashi Sama ya bar gidan, iya tsoro ta tsorata don haka ta takure a Jikin kujerar motar tayi tsit tana kallon hanya, kamar wasa yafara fita hanyar Sokoto idanun ta a waje duka gashi ba halin tanbaya............. 🖊



"Toh ko ina zuwa? Ku taimaka ku tanbayar min Aunty Aisha dahiru don nasan hudubar tace.


*Matar Soja*

🌻🌻🌻🌻

Shin kuna bibiyar littafin *DAUƊAR GORA!* Wanda *HAWA__B__KUMO (REAL-SMASHER)* ke kawo maku? Wai³ this is an emotional story ever,idan ba kya bi maza ki nema ki fara kada ayi babu ke,*DAUƊAR GORA!* Labari ne dake ƙunshe da sarƙaƙiya akan ƙaddarar wata baiwar Allah *AYSHATOU AYATULLAH* wacce tayi fama da matsalar yoyon fitsari at a very young age,she really went through tsananin rayuwa,ƙiyayyar Family'n uba,kowa yana ƙyamar zama da ita,saboda larurar data sameta lokaci ɗaya,ba kuma wai dan haifeta da shi ba,ku nema ku karanta kada ayi babu ku..

*DANÆŠANO*

Kallon ƙyama Inna Tabawa matar ƙanin Babanta data kama baki kamar an yi pausing ɗinta ta bita da shi dawani murya take cewa "toh! Yau muke ganin tsiya da wasali.. Ke yanzu da girmanki gotai² sai ki saki fitsari a jikin kayanki? O'ohh! Ikon Allah.. Ni Tabawa na ga abunda ya isheni bai ishi Allah ba" ta riƙe haɓa tana sake jinjina al'amarin,kamar an cillota kuma kamar me jiran ayi da ita,Inna Larai tai wuff ta fito daga ɗaki jin maganganun da Tabawa ke faɗa ta ɗora da faɗin "ai Tabawa in faɗa maki iskanci ne da kuma ganin ta samu masu ɗaure mata,amma babu wani rashin lafiyar dake damun yarinyar nan,samun guri ne kawai.. Allah na tuba yau aka fara yin ciki? Kou a kanta aka fara haihuwa da za'a raina ma mutane hankali ace ta gamu da wani larurar dake hanata riƙe fitsari.. Zallar taɓara ce dai ke damunta,tou kuma kin san abunki da goyon kaka,babu abunda baza tayi ba da sunan larura" hawayen da suka ciko idonta tai saurin sa hannu ta goge,da sauri ta wuce za ta bar gurin,Inna Larai ta kalli yara²n gidan tace "Kaiii! Kui mata ihu kou za ta ji haushi ta dena abunda take,kui mata waƙar me fitsarin kwance ni na saku,duk wanda yayi kuma zan bashi Nera 5-5,manya kuma zan baku 20-20" ihu da tafi suka hau yi,kafin kace me ƙananan yaran gidan sun ɗauko murafen languna da ƙananun gallon suka fara kiɗa. Kamar cikin watan ramadhan lokacin tashe,haka muryoyin yara da manyan gidan masu jin haushinta babu gaira ba dalili suke tashi cikin waƙe suna faɗin "me fitsarin kwance,amalaala! Wace ce? Me fitsarin kwance.. Amalala.. Me fitsarin zaune.. Amalala.. Me fitsarin kwance!" Inna Larai tace "baku kama sunanta ba,ku faɗa ku ɗaga murya kowa yaji,idan tai zuciya gobe ta daina" kamar Inna Larai ta zugasu kuwa suka ci gaba da kiɗa suna waƙa "wace ce? Aya me fitsarin kwance,amalaala! Aya me fitsarin kwance.. Amalala.. Aya me fitsarin zaune.. Amalala.. Aya me fitsarin kwance!!" Ba waƙar da suke yi ne yafi taɓa mata zuciya ba,yanda wasu ciki ke zagayeta har suna kama mata zani suna janta,wasu na dungure mata kai shi ne abunda yafi komai sawa taji ta muzanta a idanun duniya,da wani irin sauri ta durƙushe bakin ƙofar ɗakinta,banda kuka babu abunda take kamar ranta zai fita,bata taɓa jin ta yi loosing hope ba irin yau,zuwa yanzu kam gaba ɗaya rayuwar ma ya fice mata a rai,musamman irin tozarci da wulaƙancin da take kan fuskanta daga danginta,abun yai mata yawan da ciwon zuciya yake neman kamata nan take,daga jiya zuwa yau sosai take cikin barazana/walaƙanci da tsokanarsu,har tunanin fita take kou wani uzuri ya kamata da dole zaisa ta haɗuwa da wani cikin mutanen gidan ba Baba Wada kou su Inna Asama'u ba,wani lokaci har ƙofar ɗakin ake zuwa ai mata ɗan kira...


#Za ku samu littafin DAUƊAR GORA! Na ɗaya kyauta. For 2 & 3 shi ne na kuɗi akan ₦500,SP 1k,za'a tura kuɗin ta wannan account ɗin 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank,kou a tura zuwa 8165726609-Hauwa Usman Muhammad,Opay digital wallet. Mutanan Nijar/Mali zaku tura dala ɗari,SP jaka ɗaya,ku tura shaidarku zuwa 08165726609. Ku bi zazzafan alƙalamin #REAL-SMASHER domin samun cikakkiyar amsarku game da wannan matsala data taɓo wanda ya zama ruwan dare a ƙauyuka har da birni,labari ne mai cike da fa'idodi wanda sai kun bi za ku fahimci mene ne a cikinsa..

Page 1⃣1⃣


........... Da gudu su Nimrah suka koma cikin gida, tareda matukar jin tsoron laifin da Amrah tayiwa Yaya NAZ haka? Jugum jugum sukayi suna faman tunani, ga Aunty Farida da sai ta baka tausayi saboda y'anda ta koma shiru shiru Sai Sadiya ke lallashi da tarairayar ta tana bata baki.
Cikin kuka ta rungume Y'ar uwar ta " Aunty yanzu na zama bazawara, bayan haka duk Wanda yazo neman Aure na sai anfada mai nayi Aure ban tareba, dama ace ko tarewa nayi kafin hakan ta faru da da sauki. "Kidaina fadar hakan, idan kika tarene ma zaki zama bazawarar amma yanzu da sauki, dama ni nasan wannan shirin na Momy bai shiryu ba. Da masifa ta fito daga cikin dakin domin tana can ta kule saboda takaici, "sai kizo ke ki shirya naki kinji don ubanki duk wahalar da nayi don uban waye nakeyin ta badon kuba, idan kukayi Auren nice zanji dadi ko ku? Kunsan dubban kudin da nakashe a wannan harkar? Gashi bazan mayarda asarata ba ga makiya sunyi nasara akaina inaji ina gani yanzu Y'ar nan zata Aure Naziru, don nasan duk munafunci ne shigewa zatayi, wallahi bakusan me nake hango muku ba a Auren yaron nan, ku duba duk hidimar gidan nan a Aljihun shi take yanzu inaga matar da ya Aura me zaiyi mata? " wawayen banza kun kasa saye zuciyar shi kuna nan gind'in gindi'n daku tatsitsiyar yarinya ta siye, ku zauna kune da jin kunya bani ba wawayen banza. Tafada tareda juyawa ta koma kamar mahaukaciya. Sudai nasu ido domin sun saba.

****************
Amrah da tafiya tayi tafiya bacci daukarta yayi domin tafara gajiya, domin duk Wanda yasan hanyar Sokoto yasan irin Nisan da takeda, tsakanin Zanfara da sokoto tafiyace mai zaman kanta bare kuma shi Aramman kaduna zai nufa direct. Saida ya kawo zamfara misalin karfe hudu domin basu fito da wuri ba, baima shirya Tafiyar ba Hajjo taja wannan D'an yen aikin. Dai dai wani tafkeken hotel ya tsaya tareda juyowa ya zuba mata ido tana baccin ta peacefully, yayi D'an murmushi, saidai tunawa da Wai tanason wani yasa ya bugi gefen kafadar ta, ba shiri ta zabura ta mike a tsorace tana cewa " don Allah Yaya kamayar dani gida. Hadiyewa tayi ganin ta bakin Hamdala hotel Zamfara, ta kara waigawa tagani ko da gaskene a zamfara suke. Taga sign board, tuni cikin ta ya duri ruwa, ta juya domin tayi mai magana, tuni ya bude motar ya fita har ya zagayo gefen ta, " kifito kici Abinci I know you are hungry. Fuskar shi ba wurin wasa, haka ta bude ta biyoshi, ta kalli Jikinta tunawa da bayan katon hijabin dake Jikin jalbab sai dogon wando mai fadi da kuma wata Y'ar rigar shan iska, kafarta silipas ne na roba mai kyau, takure Jikinta tayi domin jinta takeyi daban don bata iya fita a haka waje
Jinta takeyi kamar bakomai a Jikin nata, duk da jalbab din.
Oder yayi musu shi coke kawai yace akawo mai, ita kuma pry rice da pepper chicken, kallon plate din kawai takeyi batareda taciba, shikuwa yana sipping lemon shi yana danna waya, kiran mutane nata shigowa Yaki dagawa sai kiran Kb ya daga " yeah? Yace mai, kb yace "Abokina yadai? Abba yakirani yanzu wai ko nasan inda kake zuwa a Sokoto? Wai suna neman ka sunkira baka daga ba, what is going on? " me kace musu? " bansani ba Nace kawai, now tell me were are you? And what is happening? " am coming, inna shigo zamuyi magana let them arrange my house. "Alright Allah ya kawoka lafiya.
Yana gama wayar ya kalleta " look idan zamu kwana anan bakici ba zamuci gaba da zama har sai kin cinye wannan abincin.
Kwabe fuskar ta tayi kamar zatayi ihu tace " Yaya NAZ don Allah ka mayarda ni gida, ina zaka kaini?. " eat your food first ok, and ko ina zan kai ki zaki gani now start eating. Cikin Sauri ta dauki spoon, cin Abincin takeyi amma bazatace ga test dinshi ba, haka ta cusa da yawa, naman kuwa ko D'an d'ane batayi ba, ta sha ruwa tace "Yaya na koshi. Kallon plate din yayi ya mike yaje ya biyasu yace ta taso.
Haka take binshi kamar jela har motar tashi, ya tayar sukaci gaba da tafiya, abu daya ne matsalar ta shine da amfara tafiya zata fara bacci. Tafiya yake hankali kwance yanayi yana kallon ta, wani irin yanayi yakeji a zuciyar shi, ya so ace andaura musu Aure a yau ya nuna mata rayuwar da yake mafarkin nuna mata, da daga yau bazata kuma kallon shi as Yaya ba sai dai miji mai matukar tarairayar matar shi. Gefe daya kuwa zafi kirjin shi keyi mai, saboda yasan Ummi zataji ba dadi domin duk y'anda takai ga kara yasan tana matukar son Y'ar ta, a

Please Login or Register in order to submit comment