Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" ke fito kici abinci ba ruwan ciki da fushin da kike da ubanshi maza kafin kisha carbi. Tasowa tayi ba shiri ta fito tareda cewa "hajjo banajin yunwa ne ki barni zuwa Anjima. "Ban yarda ba maza sakko gashi tuwon masarar da kikace ne miyar kuka harda manshanu Aisha tayi miki. Wasu irin hawayen damuwa ta mayar, Ummi Mami dukan su mutanen kirki ne amma Momy ta tsane su tana musu kallon makiya basa kaunar ta.
Zama tayi ta kwashi tuwon nan fiye da tunanin ta, ya mata mugun dadi, har Aunty Sadiya ta tayata itama.

****************
Ina labarin Uban gayyar? Tunda yabar Sokoto bai samu kanshi ba ga barazanar y'an bindiga ta harba jiragen su da sukeyi shidai Allah ya tsare shi, amma zuciyar shi na wurin Amrah yayi matukar kewar ta gashi dajin ba network wannan karon basu samu damar shiga gari ba saboda matsawar y'an tawayen, duk ya shiga damuwa sai yanzu yake daya sanin tafiya baiyi mata sallama ba gashi abun ya dame shi bayan dafin data watsa mai na zallar ruwan kaunar data rika wanke shi dasu gashi yana tukin jirgi yana tunawa.
Jiyake kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a gaban ta.
Ita kuwa tana lafe a gefen Mami tana mata rigima, " Mami kinga yaki Kira kuma wayar shi bata shiga gashi gabana nafaduwa don Allah nidai zanje kaduna kifadawa Abba kinji. "Aa Amrah koni bazan barki ba kinga bake kadai bace sannan gashi ko kinje baya wurin yana daji, kedai kici gaba da yimai Addu'a Allah yadawo dashi lafiya kinji, sannan kidaina sa damuwa kinga y'an da yadamu da cikin nan in kika sa tunani zaki cutar da kanki ki cutar da cikin, kuma kinsan mijin ki ai, kiyi hakuri kinji zai dawo lafiya ya ganki.
Gyada kai tayi har cikin zuciyar ta tasan ba zata iya cire damuwar ba saidai tayita Addu'a Allah ya tsare mata shi, duk bayan second gaban ta ke faduwa abun duk ya dameta bata kuma cewa komai ba ta dukufa Addu'a tareda dakko Jakarta data zuba kudin da Yaya kamal yakawo mata wai inji yaya, batada Abinyi dasu takai ta Ajiye, yanzu ta ciro tareda kiran daya daga cikin masu aikin gidan su ta bata Dubu Ashirin tace ta je ta bawa masu bukata sadaka tadawo don Allah. Domin ta yarda da tsoron Allah n matar ta dade tana aiki idan za ayi girki mai yawa a gidan tana tayasu ana biyanta, nan da nan kuwa taje ta raba tadawo tace mata ta basu sunata Addu'a. "Dubu biyar ta ciro ta mika mata tace" ga naki baba nagode. Ta amsa tayi ta godiya tareda cewa "Allah ya dawo da megida lafiya. "Amen tace ta kwanta tana kallon gallery din wayar ta, haka kawai take son kallon hotunan shi wasu da kaki wasu da manyan kaya ba wanda zata bude bata bata lokaci wajen kallon shi ba,
Ashe ba Karamar Asara taso tabkawa ba, gaskiya ita din me sa'ace, domin soyayyar da kawai ya nuna mata ta isheta Alfahari, ita tasan wannan shine mijin wuce sa'a jarumi haziki kyakkyawa kuma mai mutunci a idon duniya baida rawar kai irin na samarin zamani, lallai ita tasamu NAMIJIN DUNIYA. "My soul kadawo nayi kewar koman ka. Ranar haka ta kwana rungume da hoton shi.

Fahad kuwa yazo gidan ya ci karo dasu kamal tuni suka hanashi shiga gidan yayi iya yin shi sunki haka ya koma gida tareda niyyar dawowa gobe yafara kenan har sai sunbashi kayar shi. Haka kuwa da safe karfe takwas a kofar gidan tayi mai, yaci sa'a Abban Amrah yafito zai fita a motar shi, kallon shi yayi ya fito cikin natsuwa ganin shi a rabe. Hannu ya bashi ya duka tareda gaida shi. " ya akayi Fahad takardar ka kawo da kanka? Shiru yayi kafin yace "Aa Abba kuyi hakuri nazo inbaku hakuri ne. Shiru yayi kafin yace " Aa ai bamu kayiwa laifi ba Y'ar mu kayiwa toh idan hakurine ita zaka bawa mudai takardar ta mukeso domin ko akuya bazamu kai wani wuri amata irin wannan duka muyi shiru ba bare Y'ar mu. "Nayi kuskure babba Abba ni mai dumbin laifine don girman Allah zan shiga inbata hakuri, don Allah Abba. "Aa gaskiya sai kafara ganin mahaifiyar mu inta Amince toh don ni har yanzu ina bin magabata ban isa na zartar da hukunci ba, don haka inka shirya muje wajen Hajjo. Hadiye yawu yayi domin yasan fitinar tsohuwar nan, amma saboda farida zai je kuma zai dauka.

Suna zaune a falon hajjo itada su Nimrah suna cin kosai harda Amrah da yajin su a gefe Farha tace "muna tsakiyar masu ciki zamuga tsurfa wai kosai harda yaji da salad. Dariya Nimrah tayi. sallama Abba yayi Fahad na bayan shi, basu shiga ba kai tsaye domin yasan suna ciki kuma bashi kadai bane, yana jiyo muryar FARIDA tana bawa Farha amsa, "eh ai ciki zai zo kanku lokacine muma zamuyi dariyar hardai ke Nimrah bari Yaya kb ya motso musha biki.
Kodai mafarki yakeyi, ko waye mai cikin? Toh ai itada Amrah ne sukeda Aure, dafe kirjin shi yayi tareda runtse idanun shi yana Addu'ar dacewa. Saida Abba yace bismillah hajjon na ciki. Ya dawo hayyacin shi domin bai koji babatun hajjon ba.

"Samaila kaine kadawo kuma? "Eh Hajjo. Dukan su tsayawa sukayi kasake suna kallon Fahad dake bayan Abba, sunkasa motsawa Amrah ce ta zabura domin batason ganin shi ko kadan, aunty Sadiya da Nimrah ma suka bita ciki itace karshe domin shocked din ganin shi, dakyar ta tashi, yabita da kallon kurulla, she changed so much tayi fresh tayi kiba tayi bulbul ga wani irin haske da kyalli wanda zai fada maka tanada yaron ciki, koda baisan Alamun ciki ba nata na bayyane,
Maganar hajjo tadawo dashi " ina kasamo saurayi kuma bako mukayi?. " aa hajjo Fahad ne mijin FARIDA. "Toh kace D'an gidan gwamnati, Allah ya kawoka? Toh zakaci kwal ubanka yau dama inada cikin ka. Dama sunfi kusa tuni yafara amsar carbi ta shauda mai yakai goma. Yana sosawa domin zafi.... Abba ya kauda kai domin koshi a cike yake dashi. Saida ta gaji tace 'ka kuma. Ka cutar min da jika ka duketa kazo ka zazzaga mata ciki ka antayo mana......... 🖊




*Matar Soja*

NAMIJIN DUNIYA


🌻🌻🌻🌻🌻


Page 3⃣4⃣



...... Duk jikin shi zugi yake domin carbin Hajjo Amma kalmar cikin yasa yaji bayajin zafin, "so is true my wife is pregnant? Yafada a bayyane, wanda ya tunzuro Hajjo domin duniya ta tsani amata yaren nasara. Tsula mai wani carbin tayi da karfi, " toh ka zagemu kaji, toh tun babu gidan gwamnati mukasan boko mukasan turanci, ni har ka fadamin turanci nida keda Naziru don ubanai shima ya bari daya sha bugu bare kai D'an tayi, matsa ko in katse ta a jikin ka don in huce takaicin daka kunsawa jikata, kuma mikon takardar yanzu. Matsawa yayi da sauri don ya zanu gaskiya, ya koma gefe, Abba baice komai ba amma dariya yakeyi a boye don rigimar tsufa na Hajjo. Suna jiyo Abinda yake faruwa a falon hajjo, dariya suma sukeyi banda FARIDA domin bataji dadin ganin shi ba, kuma ga Hajjo ta Kara sakin layi wai ciki, saidai kalmar shi ta bawa dukan su mamaki "kalmar wai farida matar shi keda ciki? Yaushe ya Amince ita din matar shi ce? Surutu sukayita yi tsakanin su saboda takaicin Fahad, sai dai yanda sukaji yafara rokon Hajjo ya mugun basu mamaki hardai FARIDA.

"Don Allah ku gafarce ni nayi kuskure Hajjo, bakuma zan kuma mai maita kamar shiba ko a mafarki da yardar Allah, yanzu ina farin cikin jin labarin cikin jikinta kuyi hakuri ku mayarda ita zanbata kulawa da yarona Bazaku kuma kuka dani ba ina son matata duk na fita hayyacina saboda rashin ta, bansan na shaku da ita saida tabar gidana naga jarabawa, na Amince idan kukaga kuskure kudauki mataki akaina wallahi. Kallon shi hajjo keyi kafin ta tsuke baki tace " toh tashi katafi sai munyi shawara in kuma ita yarinyar zata Amince.
Jin haka ta zaburo tafito cikin jin takaici bata tsaya wata jin kunyar Abba ba " Hajjo ni bazan koma ba basai yadawo ba kufada mai ni bazan zauna dashi ba, baya sona baya kaunata kaddara ta hadamu, kuma ta rabamu don haka ya barni a cikin gatana so kawai yake in koma ya karasa ni, domin duk wanda yace baya kaunar ka toh har abada bazai taba sonka ba.
mikewa yayi cikin tausayawa kanshi ya ce " please kibi a hankali kinga bake kadai bace please ki daina motsawa dayawa. Yafada yana kokarin tare cikin kamar wanda ya fito, jinta yake kamar kwai, baiko damu da zancen taba, matsawa tayi baya karya taba ta kamar zata fadi ya rikota da sauri yana cewa " Hajjo please kice tayi a hankali kinga bata lallaba kanta, don Allah please kiyi hakuri kibi a hankali idan kin haihu sai kimun hukuncin da duk zai huce zuciyar ki amma ni yanzu ko magana mai karfi wallahi jin ta nake kamar zuciya ta zata fashe. Ya manta da Abba ita Hajjo ba a ta ita, sukuwa y'an tsegumin tuni haushi ya koma shauki sun fara "awww, Awww. Daga ciki accept Amrah da yake bata haushi domin ya nuna musu shidin bai san kaddara ba da yakasa hakura har da dukar mata Y'ar Uwa. Abba tuni ya mike ya tafi don bazai iya shiririta ba, Hajjo dai ta saki baki da hanci saida ta gaji tace " kai karamin mara kunya zoka wuce bamu maraba dakai kadaiji Amsar ta, toh maza zoka barmin gida kafin insa jikokina sufitar min dakai yanzu. Kamar yayi kuka haka ya fara matsawa da baya yana kallon ta, " please your number my FARIDA the old one is not going. Harara ta maka mai ta shige cikin dakin tabarshi da babatun hajjon, haka ya hakura ya tafi, saidai ya tafi da abu biyu farin ciki da tsoro yasan ko su fada sukeyi bazata saku ba tanada ciki, kuma fatan shi yasamu ta koma yareni Abun shi, tuki ya keyi yana dukan sitiyarin motar shi saboda jin dadi, " am going to be a father soon, Alhamdulillah, tank you lord for All your blessings.
Yana isa gidan Momy yafara fadawa good news itama tuni ta manta da fushi ta rungume D'an ta, " aa dole inje inganta zan samu jika nima Allah nagode maka. Haka ko Dadyn shi yayi farin ciki duk da yace bazai je ba saboda kunya saida ya ce zaije shima gidan ya nemi sulhu kodon jikan shi bazaiso ya taso ba gatan su ba.

FARIDA
Tun tafiyar Fahad tafara kuka ganin y'an uwan har sun manta suna yimata dariya, Aunty Sadiya saida taga sun rage sukadai ta fara bata baki " FARIDA kukan me kike yi? Idan ba a hakuri da Abba bai kalli Momy a cikin gidan nan ba da bamuyi mutunci a idon su Ummi ba da Amrah ba zata kuma kallon mu ba, bakin cikin me kikeyi wace irin azabtuwa kikayi da kike ganin bazaki iya yafewa Fahad ba, karki manta yanada right domin ba haka yaso ba, ki sa kanki a matsayin shi keda kike mace zaki iya yin hakuri ki zauna da wanda bashi kika zaba ba? Think."now listen Allah ya nuna mai har yadawo badon cikin ba sai don Allah ya dubeki yasa mai soyayyar ki a zuciyar shi, wannan wata baiwa ce, ki duba baiji kunyar kiba baiji kunyar Abba KO Hajjo ba what matter is you. "No Aunty ya damu da cikin shine kawai. " and sai kiyi farin ciki ko a hakan wata baiwa ce, yanzu bakya ganin gani ba wani mashin shini, duk gayun sun watse dakayi zancen Aure sai su gudu, ke kinsan as he is Idan mata hudu yakeso yau zai Aura, but he came back to you, na gama fada miki is left for you to think. Shiru tayi bayan tafiyar Aunty Sadiya, tana tunani, she is right amma mugun tsoron Fahad takeyi har gobe because he torture her.
Hajjo ma ta zage ta fada mata gaskiya kai har Aunty Zuwaira sun mata magana, su Abba dai basu ce komai ba. Har Momy a daren ranar tazo cikeda tsarabar ta na masu ciki sai famar tarai rayar ta takeyi kamar tagudu da ita, Hajjo harda magana ta gwaba mata " waike hala a zuri'ar ku an shekara dari bakuga ciki bane irin wannan zumudi kamar kanku farau? Saida FARIDA taji kunya, amma Momy tayi dariya tace "wallahi tunkan Fahad Allah bai kuma bani haihuwa ba shiyasa
kikaga ina yin haka. "Toh Allah ya inganta.

*********************************
Amrah yau faduwar gaban ta yafi na kullum duk ta kasa sukuni saboda yanayin datake jin kanta, yau part din Ummi taje ta kwanta tayi shiru, saida ta tanbaye ta " tace "wallahi Ummi tsoro nakeji da faduwar gaba ka mafarkai akan Yaya kullum. " toh ina kika bar Addu'a? Ki yawaita istigifari da Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, zakiji saukin faduwar gaban. "Toh tace taci gaba dayi a zuciyar ta har bacci ya kwashe ta a gadon Imran,
Tana part din har yamma Mami tazo taja Abarta, Ummi tace "yaya keda Y'ar ki dama takurani takeyi kuje can gidanku yafi mun. " toh ai dai na dau abata ko mun baki wuri. Tana zuwa wanka tayi tareda cin Abincin da Mami ta Ajiye mata bawani ci tayi ba, Abba ya shigo, wanda tasan Abu mawuyaci ne agan shi cikin gidan idan ba babban dalili musamman irin wannan lokacin. Saida ta Ajiye spoon dinda take shan faten waken da yaji hanta da ogu.
Tana jiyo Mami nacewa "Abban Farha lafiya kadawo yanzu? Juyawa yayi " yace " zo Zainab. Tabi bayan shi bata dade sosai ba ta shigo falon ta zauna ta kuma mikewa ta koma dakin ta ta zauna bakin gado taja numfashi, " Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.
Shine kalmar data fara fitowa daga bakin ta kafin ta D'an samu natsuwa ta kuma fitowa falon batason shiga wurin Amrah, ita kuwa duk ta matsu Mami tadawo, jin shiru yasa tafito batareda ta Kara koda cokali daya ba. Ganin Momy zaune a wani irin rudu yasa ta matso da sauri tareda zama gefen ta " Mami lafiya dai ko Abba ya shigo?. Dagowa tayi tana kakaro murmushi na yake da bai kai koda wuyan taba bare zuciya ta ce " laifi nayi ya kirani karki damu haka Rayuwar Aure take.
Bata gamsu ba don haka ta tashi tafita waje, part din Hajjo ta nufa,takalman su Abba jere Amma batajin me suke cewa, Sallama tayi suka Amsa Hajjo tace " ku kyale zancen wannan Fahad din ni kaduna ma nakeson zuwa yau inga jikana nida Zainab don haka ina bukatar D'an rakiyq cikin ku yau. Ajiyar zuciya ta saki tagaida iyayen nata ta kalli hajjo jikina rawa tace " Hajjo inje in shirya yanzu??. "Eh jeki maza ina jiran ki. Fita tayi da sauri domin harga Allah tanaso taji mijin ta kota ganshi tayi matukar gajiya da karar da takeyi, don haka ta wuce domin shiryawa, Mami na ganin ta tace "yadai? Fada mata tayi zasuje kaduna da Hajjo yanzu. Mikewa tayi ba tanbaya ta rakata tareda cewa " karki deba kaya da yawa. Juyowa tayi tareda tanbaya " saboda me Mami? " bakinada wasu a canba?. " eh hakane ma kadan zan deba a trolley.

Can dakin Hajjo tana fita tace " karkuyi maganar nan yara suji kubari mutafi tukuna kai Mustafa zaka bimu, ku kuma kwazo da safe. "Hajjo toh tafiyar da kun bari sai da safe mu mutafi yanzu saboda dare. Abban Amrah yafada. Tace " baka ganin yarinyar nan bata cikin natsuwar ta? Ku bari muje ta ganshi ko yafi taji labari. "Toh bari inkira kabir ko sunada jirgi mai tafiya yanzu........ 🖊.


*Matar Soja*

NAMIJIN DUNIYA


🌻🌻🌻🌻🌻


Page 3⃣5⃣




.......... Sunyi sa'a sun dace misalin karfe biyar suka fita, da taimakon kb sun samu available plight nasu, harda Abba Mustafa bai tsaya ba, don haka tuni tafarajin wani irin yanayi mai ban tsoro a tattare da ita, ga hajjo banda jan carbi bata cewa komai wanda kowa yasan Hajjo bata rasa complain, hakuri kawai takeyi da wannan tafiyar har taga karshen Al amarin, tun agida hankalin ta ya tashi ganin kowa fuskar shi bawata walwala. Bata Kara rudewa ba saida Allah ya saukesu lafiya taga suna isa kb yazo daukar su, duk pretending dinshi ta fahimci yanayin shi ya sauya domin mutum ne shi mai barkwanci da wuya su hadu bai tsokane taba, sai gashi yau tunda suka gaisa ya kwashe su motar tsit, saida ya sauke su kofar gidan NAZ yace Hajjo da ita su shiga bari suje wani wuri da Abba. Bata tsaya wata wata ba ta shige, tareda kallon ko ina a falon, ya nuna Alamar bakowa kuma andade ba'a ciki, Hajjo na shigowa tace " zanyi sallah ankira magariba. Tarar ta tayi " Hajjo wai ina yaya? Meke faruwa ne kowa shiru ba wanda yake cemin komai hajjo in wani abu ne ya faru kufada min insamu sauki kafin zuciya ta tabuga mana wallahi nagaji da irin wannan aikin na yaya yau kusan wata daya banji shiba sannan yanzu munzo ba Alamar shi agida haba Hajjo. Ta durkusa tareda sa kukan tausayi, "ke ki rufamin Asiri kar makota su shigo mana don girman Allah meye na kuka koma meye zakiji zaki gani bagamu munzo kadunar ba?. " Hajjo wani abu yafaru da Yaya? " aa bance ba yazan sani baya Kira Kidai bari kabiru yadawo mu tanbaye shi. Zaman jira ta zauna yi bayan sunyi sallar su, bata runtsa ba tana jiran dawowar kb gashi batada number shi, su Nimrah sun kirata yafi sau goma suna tanbayar ta ko lafiya irin wannan tafiyar? Saidai kuka take saka musu, don haka suketa Kira suji koda wani update.
Duk jikinta yayi sanyi. Ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, dakin ta ta shiga tareda zubawa ko ina ido, tagan shi fess sai Kamshin shi ke tashi a gadon ta kwanta tareda rungume filon shi, wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata, "please Yaya kana ina ne? Kazo ina matukar bukatar ganin ka don Allah.
Wasa wasa har Asuba tayi juyi har ta gaji ta mike tafara nafiloli, tana kan dadduma har karfe bakwai taji motsin Hajjo da maganar ta, tafito falon da sauri. " Y'ar nan kin koyi bacci? Girgiza kai tayi, "toh maza bude kofar na rufe nakasa budeta naji maganar Mustafa a waje. Da sauri ta nufi kofar ta bude, shikadai ne ba kb, " Abba ina kwana, ina kaje tun jiya?. " muje ciki Zainab,Hajjo ku shirya mu fita yanzu.
Bata tsaya tanbayar komai ba Hajjo ta koma cikin dakin data sauka ta canjo hijabi, itama komawa tayi kawai wayarta ta dauka don tagaji da kalar game din da take gani tun jiya sunki ce mata komai. Fitowa sukayi tareda kulle kofar, kb na jiran su a mota, gaisawa sukayi Hajjo ma ta ce " ya gajiya kabiru ya kokari? Mun gode Allah yayi maka Albarka. "Amen. Kawai yace, ko kallon shi batayi ba saboda haushi yake bata. Don me zai zuba mata ido bazai fada mata ina mijinta yake ba.

Kallon hanya takeyi saida suka iso bakin tangamemen Asibitin na Soja wato 44 ta kalli sabon sign board din gaban ta yayi wani irin lugude, ji tayi tafara jikewa da gumi. Musamman yanda take ganin fuskar Abba ba walwala sam. Tuni ta saki kuka da sauti wanda bata shirya ma zuwan shi ba, "Innalillahi, Hajjo Yaya baida lafiya shiyasa kuke boyemin ko shiyasa bai kiraba ko, me ya same shi don Allah Yaya kb???. " Ashasha meye na kuka kuma keda zaki godewa Allah yana raye kiyi shiru karkija su hanamu shiga ciki kinsan su da dokokin su. Sharewa tayi har ya shiga bakin emergency room din da ake Kira operation lafiya dole, Asalin wurin domin sojojin da suka hadu da tsautsayi daga mai duguri zaki gani wasu anyanke kafa wasu ba hannu wasu sun kurumce kai gaskiya ko kurman zuciya gareki kikaje wurin sai kin koka. Ita tafara fitowa Abba ya ce "natsu Zainab kinji.
Sojoji ne birjik a wurin da masu gadi da masu jinya, irin y'an da take ganin wasu da sanduna kawai yakara daga mata hankali. Ganin kb yayi gaba tabishi da Sauri batareda ta jira Umarnin kowa ba domin tasan dai yanzu yaya NAZ dinta ne anan kwance. Runtse idanun ta Tayi domin wasu inta kalla zata iya suma saboda tausayi, har ya isa gadon da Nazir ke kwance, a hankali take karasowa jikinta na rawa har ta iso, kallon kb tayi "ina mijina yaya kb? Nuna mata yayi tareda maida hawayen da suke kokarin zubo mai, Kara kallon shi tayi yana nade da bandages tundaga sama har kasa idanun shi kawai take iya gani suma sun kuje sunyi ja, yana kwance ba Abinda zai nuna mata yanada rai sai numfashin shi dake fita, tana hango motsin fitar ta bandage. Hannu ta nuna bakinta na rawa takasa magana tayi baya baya zata fadi Abba daya shigo ya tareta tareda riketa yayo waje da ita tuni numfashin ta yayi kaura, kb ya fito tareda kawo ruwa suka watsa mata, nurse tafito da Sauri tana fada tareda dubata, " kudaina bari mata na shiga irin nan especially ita ga ciki.
"Toh ai mijinta ne dole ta ganshi. " ku kiyaye dai karku kuma barinta this is emergency kb you know is not allowed.
Dakyar suka samu numfashin ta yadawo, da kuka ta bude idanun ta " Wayyo Hajjo Yaya na mijina ku taimake ni kar in rasa shi Hajjo yaya me yasa meshi suka nade shi da bandage kice su cire ingan shi. Hawayen da Hajjo ke kokarin rikewa ta kasa ta rungume ta a jikin ta , Abba ya fara basu baki, " kuyi hakuri Hajjo haka Allah ya nufa da Naziru. Kb ya tsuguna " kuyi hakuri Hajjo mun godewa Allah ma da muka sameshi da Rayuwar shi, domin irin harbin da sukayiwa jirgin Allah ne yasa ya diro ta parachute da tarwatsewa zaiyi domin jirgin duk yayi pieces, bai fado a wuri mai kyau bane yajijji ciwo ko ina nashi ya kuje Amma ba karaya ko daya gaskiya sai buguwar da yayi akai, kuma Insha Allahu baza asamu matsala ba.
Sunji sanyi kadan Amma har cikin zuciyar ta bataji wani raguwar tashin hankalin taba. Kallon yaya kb yayi tace " Yaya don Allah inaso inkoma wurin shi. "Bazasu bari ba Amrah kiyi hakuri zuwa gobe zasu iya canja mai daki. Abba ma yace yayi hakuri, yanzu su koma gida domin tsayuwar banza sukeyi baza abarsu su kuma shiga ba, dama Hajjo dai takasa ko lekawa, kukan Amrah yaki tsayawa musamman da taga bazata kuma wai ganin shi yau ba, duk ta sukurkuce, Abba sai baki yake bata. Amma ina batajin akwai wanda yanzu take bukatar lallashin shi sama da yayan ta kuma mijinta, don haka suna zuwa gida ta dauki waya takira Ummi. Kuka takeyi kamar wadda taga gawar shi, Koda Ummi ta dauka batayi shiru ba saida tace " Zainab. Akaron farko taji sunan ta abakin Ummi, tuni tasamu natsuwa, " ina fatan baki Kira Mamin ki kina mata irin wannan kukan ba? " aa Ummi, wallahi yaya na cikin wani hali, Ummi baisan ma ina wurin ba, duk sun saka mai bandage. Takara sa wani sabon kuka she can't imagine wai NAZ dinta ne D'an gayu jarumi akwance agado baisan tana ma kusa dashi ba. "Ya isa haka kukan kici gaba da Addu'a tunda ya dawo da ranshi mungode wa Allah. Ta lallashe ta sosai tareda bata Addu'oi tace ta rikesu idan taje gareshi ta rika yimai. Taji D'an sanyi maganar da tayi da Ummi, ta Kira Mami bata yi mata kuka ba domin idan

Please Login or Register in order to submit comment