Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


" karka ga na tsaya maka akan Zainab kaji dadin watsewar ka a bariki y'anda kakeso toh bazan dauki tanbad'a ba a zuri'ata, oh haka kakeso inbaka yarinya kaje can ka wulakanta ta a inda batada kowa? to nagano ka. " wai meyayi zafi shiba wuta ba hajjo na? " zai yi zafin dai karka damu, ni zansa ma yayi zafi harya tafasa.
" toh ni afada min me nayi daga shigowa ta anfara min fitina?.
" wacce shegiya ce ta zo mana har cikin gida lokacin walimar iya shegen ka?
Dariya yayi tareda riko hannun ta cikin shakiyanci yace " yanzu na fahimta kishi ne ya janyo wannan rikicin. " karka raina min hankali kaji ba wasa kaga inayi ba, kayimin bayani ko inkira iyayen ka su kafada musu ai. " Hajjo banson rikici fa, wannan yarinyar ba kowa bace kar sanadin ta ki rusamin rayuwa. " ai ni inba rusa makaba kai ka rusa abinka. "Wai ma waya fada miki wannan labarin ne da ya kwana biyu? " zainab ta fadamin don uwa ka. "Mami dai Hajjo? " in Itace ai kasan sauran Hamra dai. Zaro idanu yayi tareda cewa " What? Amrah ? Hajjo why zata fada miki wannan maganar? " da gaske dai yafaru? Toh ai sai kaje kafadawa iyayen ka suje su nema maka Auren yafi tashi ka bani wuri. Mikewa yayi yana nazari a zuciyar shi " Wannan yarinyar ta kuma ballo aiki. Part din Mami ya nufa domin yasan zai iya ganin ta a can, ya samu basa nan gaisawa Kawai yayi da ita tayimai sannu da zuwa ya tafi wurin Ummi, yana shiga suna dawowa, kanta a kasa ta shiga falon batareda tasan akwai mutum ba, kwance daurin kanta tayi tareda warware doughnut din da akayi mata a saloon domin zafin da takeji cikin kan, Farha ce a bayanta tace "Amrah kanki yafi nawa relaxed. Baje shi tayi kan kafadar ta " Wani irin zufa nakeji bari in karba kayan Wurin Ummi muje inyi wanka. Saida suka Kara so tsakiyar falon suka ganshi yana danna wayar shi, Saurin jan burki sukayi Farha baki na rawa tace " Yaya Sannu da zuwa. Gyada kai yayi tareda dagowa yabasu kallo daya, fitowar Ummi yasa suka tsere basu ko jira sun karbi kayan datace suzo su karba ba.

"Kuzo nan. Ya tsaida su, gaba daya cikin su ya duri ruwa musamman ita data mai hadi wurin Hajjo, takuma san halin ta bata boyo don haka sai daga baya tafara data sanin fadar maganar. Mikewa yayi bayan yagama magana da Ummi suna tsaye cak yace su kawo mai Abinci dakin shi yanzu, ya juya ya fita, kowaccen su ta tsaya kallon Y'ar uwar ta. "Bazaku ku zo ku dauka ku kai mai ba kun tsaya a wurin kamar zakaru. Da sauri suka wuce kitchen suka samu yana hade a basket, Farha ta dauka. " shikenan ke zaki kai mai, ni bari intafi in watsa ruwa. "Allah baki isa ba tare zamu je tace " ko ba inda zataje. Yana tsaye a kofar dakin nashi domin yafi kusa da part din Ummi, yana hango y'anda suke jayayya, kamar yasan bazata zoba ya tsaya a wurin. Ta juya zata wuce ya ce Farha ta bata basket din ita ta tafi. Karba tayi Jikin ta na rawa ta wuce da Sauri da niyyar tana Ajiyewa ta gudu. Sai dai kash tana shiga yana bayanta, a tsorace ta matsa gefe tareda cewa " Sannu da zuwa Yaya. Batayi zato ba taji ya fisgi hannun ta bai tsayar da ita ko ina ba sai a kan kujerar dake falon nashi, ya zaunar da ita da karfi kafin ya tsuguna a gaban ta a kasa guiwa biyu. Kallon ta yakeyi cikin ido yana hango tsantsar tsoron shi da takeji a duk lokacin da suka kasance tare.
Itama duk idanun ta suna cikin nashi domin so take taga karshen game din, wai haka yakewa su Nimrah da Farha ne ko ita kadai ya raina? " au raina ki nayi ko? Taji yafada, don haka ta tabbata ba a zuciyar ta tayi zancen ba, dafe bakinta tayi tana jujjuya kai cikin tsoro. "Yi hakuri Yaya don Allah. Wani irin miskilin murmushi yayi kafin yace " hakuri dame? Da kokarin hanani Auren da nake lallaba Hajjo shekara da shekaru kinje kina so ki rusa min plan, look because of your mouth idan na rasa yarinyar da nakeso zakisha mamakin me zanyi miki, saboda soyayyar da nake mata banayiwa kaina ita, ina sonta fiyeda komai na rauwata. Bakin ta na rawa tace " Yaya kayi hakuri don Allah bani na fadaba Momy ce. Ta fada mai komai cikin rawar murya batareda ta shirya ba, " me yasa ke kika fada da bakin ki? Kinsan me kikayi kuwa? Look I can't afford to loose her. Wani irin kallon da bata shirya ba take yimai domin dai ita yanzu ma mamaki yake bata, bata taba tunanin zai iya tsayawa yayi magana da ita haka ba bare har maganar da ta shafi Rayuwar, she can saw everything in his eyes, gaskiyar zuciyar shi yake fada mata, Ashe zai iya tsayawa yayi zancen wadda yakeso agaban ta? . Tayi dogon nazari har saida ya buga hannun kujera tadawo hayyacin ta. " ki shirya karbar hukunci idan na rasa farin ciki na da mafarkin Zuciya ta. Ya mike tareda cewa "Kuma daga yau har in koma ina bukatar ki rika kawomin Abinci safe rana da dare batare da naji wani complain ba, in kika bata lokaci zaki fuskanci hukunci na, now go.
Ai kamar jira take ta deba da uban gudu, tafita dakin. Saida ta D'an gana da part din Mami ta tsaya, tareda maida numfashi tana godiya ga Allah da yasa bai mata komai ba. Tunawa tayi da Umarnin shi ta Gyada kai akan ai ya sassauta mata ma, zata lallabashi su rabu lafiya, ita wallahi yanzu ma Aure takeso kodan tayi nisa da gidan nan ta daina hada hanya dashi, naturally tsoro yake bata, idan zata zauna dashi inuwa daya na tsawon wata zata iya samun damuwa a rayuwar ta. Dariya Farha tayi ta mata bayan Tafada mata abinda yafaru tun farko. " baki ki yaja miki ai waya aike ki kinsan halin Hajjo mai jiran abu bare ta samu dalili.
Nimrah ta shigo jiki a sanyaye domin Al amarin Momy tsoro yake bata, ganin y'anda Fahad yazo gidan batareda ya nuna yasan taba, bayan sunyi ido biyu, taga y'anda yake rawar kafa a gaban Aunty Farida, tuni ta kara sallamawa lamuran Momy dana wata hatsabibiyar kawarta Ladiyo. Tabata sukayi tareda cewa " ke yau lafiyar ki? Murmushin yake tayi tace " bakomai Kawai ina tuna daga gobe shikenan Aunty Farida sai gidan Miji.
Tuni suka cigaba da tattauna wa har suka kwanta.
Da safe tunda wuri ta tashi domin gudun laifi bata ko jira Mami ta dora ba Kawai fitowa tayi ta ganta tayi kaca kaca tana mai girki domin batason taje tace zata karbo mai wurin Ummi zata tuhumeta don haka ta yanke shawarar girkawa da kanta......... 🖊




*Matar Soja*
🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻



*WRITTEN BY FENERH*


https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Join our free page group

Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb.

Free page


Page 9⃣


.................Mami tace "aa yau dadi zamuci ne irin wannan kamshi haka ya cika ko ina?. Juyowa tayi hankali kwance tana yanka Albasar da zata soya kwai, tace " Abincin yaya ne. " kamal hala?. "Yaya Nazir ne. Tafada tareda ci gaba da aikin ta,
Fuskar Mami kuwa kamar gonar Auduga saboda farin ciki tace "ci gaba da aikin ki idan kin gama mayi namu. Ta juya tabar mata kitchen din, cikin natsuwa ta hadamai breakfast din da tasan Ummi nayimai time to time, wato doya da kwai da kuma ruwan bunu mai kayan kamshi kala kala,
Hadawa tayi a basket kamar y'anda taga Ummi nayi ta fito a gurguje kafin ta karawa kanta laifi tayi dakin shi. Yana zaune yana amsa wayar Fauziya har tayi sallama ta shigo bai katse ba ta tsinci kalmar shi ta karshe........ "Karki fara takomin kafarki anan garin again, so kike ki rusamin farin cikin rayuwa ta saboda iskancin ki, I told you don't even think of it,, Auren kanwata ce and you are not invited ok tanks. Ya datse wayar tareda Kallon y'anda ta tsaya tareda zubamai ido, " yana sonta yana sheka mata wulakanci? Wallahi ya NAZ D'an duniya ne, amma yazo sai fadamin yake yadda yake sonta. " idan kin gama yimin laben ki Ajiye kitafi, in yaso daga nan sai dakin Hajjo sai ki fadamata komai kinji. Yafada batareda ya kalleta ba, Kara sowa tayi ta Ajiye ta juya batareda tace mai komai ba, wato munafuka ya dauke ta kenan, " waye zai zuba min da kika wuce? Tsaya wa tayi tareda tura baki ta baya " wallahi ta fara gajiya tun yanzu. Tafada a zuciyar ta tareda juyowa ta tsuguna a inda ta Ajiye abincin, yana kallon duk y'anda ta shirya basket din, har ta ciro kular mai kyau dake dauke da doya tayi mata yankan Irish kana na ga kwai da yaji su Albasa da tarugu, abun ya burgeshi sosai, lokacin da ta bude jug din ruwan zafin saida ya lumshe idanun shi saboda kamshin da ya ratsa zuciyar shi. Wayar shi ta kuma yin kara, ya dauka ganin number Ummi ce, cikin Sauri yace " Ummi ina Kwana? Batajin me take fadamai Kawai toh yace tareda cewa sai zuwa Anjima zai shigo.
Ya Ajiye wayar tareda kallon ta cikin Alamar tuhuma yace " a ina kika dakko min Abinci? Saurin kallon shi tayi cikin tsoro tace " a part din Mami na hada.
" kika what? yafada cikin surprise, a zuciyar shi kuwa ba Abin da yake muradi irin ta kauce yaci Abincin don haka cikin basarwa yace " jagwal gwalonki zanci? Oya out. Ta mike tana cewa " wallahi ba jagwal gwalo bane ko Abba na cin Abinci na. Shidai idanun shi akan abincin har ta fice baiji ma me take cewa ba, hannu yasa ya dauki yankan doyar yakai bakin shi tareda lumshe idanun shi, " Hmmmm, yafada sannan ya dauki cup din ruwan zafin ya kai bakin shi, a duk duniya Abinci biyu yakeci Hankalin shi kwance, daga na Mami sai na Ummi, duk inda yaje Abinci na bashi wahala sai dai ya wuni shan tea ko ya dafa indomie shi ba mutum bane mai cin abin kasuwa, yanada tsantsaini.
Bajewa yayi yaci yayi nak tareda jingina a Jikin kujera yana lumshe idanun shi, ina hango wani kyakkyawan murmushi akan fuskar shi akwance, ranar dai Ummi bata ganshi ba haka ta karaci Ajiya ta baiwa masu sharar gidan. Da rana kuwa zasu tafi lalle da wuri ta shiga ta hada tuwon semovita da miyar kubewa da taji kifi da namomi, harda gandar ta. Ko a ido ka kalli miyar zakayi sha'awar cinta bare ka ji kamshin ta, Mami kuwa harda tsokanar ta " wannan Yayan yana cinye dadi yana barin mu, toh nidai a zubon tuwon zanci bazan yarda ba. Dariya yayi tareda cewa " kai Mami kece fa kika koyamin. Wannan karon data kai tayi sa'a baya gida don haka shiga tayi falon kai tsaye ta Ajiye mai ta fito tareda godewa Allah,
A gurguje suka shirya suka bar gidan Nimrah na mata tsiya " ke yaushe kika zama kuku ne? " bansani ba munafun.
Dariya suka yi farha Tafada mata abinda yafaru, suka ta mata dariya. Gidan lalle suka tafi a can suka wuni sai la'asar suka dawo, lokacin an baza canopy a haraba da wajen gidan, bakine ta ko ina, wanka suka fara yi suka shirya cikin ankon kamun Amarya, wanda za'ayi karfe hudu.
Saida gidan ya cika ya batse kafin Amarya tafito da kawayen ta y'an karya, gefe daya Momy da kawayen ta itama mazaunin su daban su Ummi kuwa suna ciki suna fama da baki da sukazo daga yabo D'an gin miji.
Harda gwaggon su tazo wato me sunan Farha Khadija. Ta kalli Mami tace "Matar yaya don Allah wane irin Auren gaggawa ne wannan su yaya suka tsaida? Aure ko wata biyu ba'ayiba kamar ana neman kai da ya'?. Mami tace " kedai Hadiza kiyi fatan Alkhairi Allah yasa gidan zaman tane, shi Aure ai kamar habo ne. " toh Allah ya kade fitina amma gaskiya tunda naji Hajjo na complain nasan akwai matsala, wai yaushe Saratu zata gyara ne?
Hakuri Suka yita bata, basu fita taron ba, har lokacin da ango ya iso da uban tawagar sa, su Amrah ne masu entertaining mutane da kayan motsa baki sunyi ado cikin dogayen rigunan atamfa tareda murza dauri takalma designers yaran Mami sunyi matukar yin kyau kamar ka sace su ka gudu. Amrah da Farha sunsha mamaki lokacin da sukayi ido hudu da ango, Farha ta taba Nimrah, idanun ta a waje tace " ke kamar gayen da yabiyo Amrah? Daga kai tayi tareda cewa " Anya shine?. " eh wallahi, yaushe suka shirya da Aunty Farida? Amrah ta tabata " ke ina ruwanki da yaushe suka shirya? Ai karshen shiri yanzu zasuyi Aure, don haka muci gaba da aikin mu Kawai.
Dole suka basar tareda cigaba da hidimar su, sai dai ta bangaren ango yana hango Amrah kanshi yafara kwancewa Kallon ta yake yi yanaso ya tuna wani abu amma ina abun ya gagara, kanshi yaji yana mai ciwo, aduk lokacin da ya daga kai ya kalli Amrah sai wani Abu ya soki zuciya da gangar Jikin shi. Daga karshe ko fara gudanar da bidi'ar ba ayiba ya Mike, FARIDA ta rike hannun shi tareda yimai wani abu Murmushi, " ina zakaje dear? Fisgewa yayi tareda bata wani irin kallo wanda saida hanjin ta ya kada. Babban abokin shi ya taso ganin har yabar kujerar da aka shirya domin su. Rage murya yayi " Aboki na yane ina zakaje? Idanun shi sunyi ja yace " let go home please I can't stay here. " why now is your kamu, ya zakace zaka tafi please ka tsaya bazamu wuce hour daya ba. Ya koma ya zauna badon yaso ba Amma fuskar shi kamar gobara, tuni hanjin cikin FARIDA sun gama juyawa ta hada ido da Momy, ta nuna mata ta share da hannu, dukan su dakyar sukaga karshen wannan kamun, ita a mugun takure take saboda gani take ya gama dawowa hayyacin shi.

Sudai su Amrah sunji dadin sha'anin domin duk da bata rawa ta taka a bayan fage, wanda Aramma yana hango ta gefe shida Kb, ido Kawai yake binta dashi ko murmushi yakiyi, wani ma babbata rai yakeyi Kawai Yaki sakewa. Dafashi kb yayi yace kai nawan kayi fara'a mana baka ganin y'anda babe din tasha wanka, gaskiya kayi mamaya anan. Tsaki yaja Kawai shi yasan meke damun shi.
Bata masan yanayi ba, itadai tray ta dakko batama san suna Jikin motocin dake gefen gidan ba saboda yawan jama'ar dake wurin, wani gaye ne yasha gabanta a cikin abokan ango yaci ado kana ganin shi kaga D'an hutu domin kalar shaddar da yasa Kawai zata fada maka anjiku da Naira, zare ido tayi domin ya mamaye ta, taja baya kadan, " Am sorry beauty na tsayar dake kina tsakiyar aikin ki, don Allah inba zaki damu ba ina son kibani digit dinki zamuyi magana letter if you don't mind??. Ajiyar zuciya tayi tareda jan mayafinta da kyau tace " banda number.
Dariya yasa kadan hakoran shi suka bayyana yace, " wasa ne wannan ya budurwa zankadediya kamar ki kice bakida waya? "Yes saboda ba wanda zankira, duk wanda zankira yana tareda ni so bana bukatar wayba.

Tsawar da Nazir ya mata yasa saida ta saki tray din hannun ta, domin ita yau tunda take kai mai Abinci bata hadu dashi ba, "Uwar me kikeyi anan wuce ko in tattaka ki. Ba arziki ta bar wurin da Sauri Jikin ta na rawa, shi kuwa gayen ya kalli Nazir cikin girmamawa yace " kayi hakuri don Allah ni na tsayar da ita, and Kawai number ta na tanbaya kuma batada shi so..... Kawai wucewa yayi fuuuu kamar walkiya yabi bayanta domin yana hango inda tabi. Kb dake gefe yana kunshe dariya ya matso tareda dafa gayen yace " am sorry abokina ka shiga fadamar da batadace bane, that's his wife to be, so don't be offended, yana mugun kishin tane ko kai zaka iya yin haka akan wadda kakeso is normal. "Yeah I understand my friend tank you, baida laifi ai ko ni zan iya yin fiyema da haka akan abinda nakeso, banga laifin shi ba. Suka kashe ya wuce, ango dai abu yaci tura tuni ya bazawa rigar shi iska ya tafi batareda abokan shi sun ankare ba, sai daga baya, ita kuwa FARIDA kai ta dukar tafara fitar da hawaye har Momy ta hango ta, don haka cikin hikima suka tashi taron.

Tunda Fahad ya tashi motar ya fisgeta, ya nufi gida, bai kai ga isa gidaba kwakwal war shi tafara war warewa a hankali ya kara tuno fuskar Amrah, tuni ya tuna komai tundaga haduwar su zuwa yau da yaganta cikin ado mai daukar hankali, tayi matukar haduwa cikin ankon nasu, don haka yana fakawa ya shige cikin gida sai gumi yakeyi, ko ina mutane ne a gidan nasu don haka kuryar dakin Momyn shi ya wuce tareda zubewa kan gadon ta,
Shigowa tayi cikin Sauri, tana cikin ado mai daukar hankali da tsada wanda kana ganin ta kasan wankan kudi ne a wurin.

"Ya akayine Angon FARIDA yaya da dawomin haka tun taro bai watse ba kaida zaka Auri wadda kakeso". " Momy wacece kuke Auramin? " bangane wacece ba?? Wace irin tanbaya ce wannan. Farin cikin ka zaka Aura wadda kuka hadu. " no no no momy she is not the one I saw her today I remember everything wallahi naga yarinyar da nakeso momy what did you do? Tuni ya rud'ata saboda shidin D'an gatan tane. "Tsaya kamin bayani y'anda zangane, me kake nufi da ba ita bace kaga wadda kakeso? " Momy the girl I saw close to me is not the girl I love, I saw my love there, what is happening to me momy.
"Fahad", don ina sonka bashi zaisa inbiye maka injawa kaina matsala ba, kasan halin babanka so ka rufamin Asiri kabar wannan maganar na rokeka kaga muntara mutane karkaja min magana. "Wace magana Momy? Ina magana ne akan rayuwata ya za'ayi in Auri wadda bana so?
Mikewa tayi, "kaga banda lokacin wannan maganar yanzu ina fama da jama'a idan kanada magana babanka yana nan kaje ka sameshi Banson shirme. Ta fice tabarmai dakin.


Amrah
Tunda ya buga mata tsawa tayi cikin gida, gefen Hajjo don tasan ba wasu mutane a wurin, tana shiga yana biyo bayanta, don haka da gudu ta shige falon, ba kowa tayi cikin uwar dakan, kirjin ta na mugun duka, hajjo ta tareta tace " ke waya koroki haka? "Wanda ya isa, wallahi zanjiwa wannan yarinyar wata rana, Hajjo Kifada mata ta kiyaye zan karyata baras idan tayi wasa, ya zata maida ni D'an iska. Idanun ta a waje domin ita dai tasan batayi mai komai ba, tsaida ita gayen yayi bayan haka ba wani laifi to me zaisa shi yin wannan babatun? " kai kai, dakata meye na biyota kana sababi haka? Boyewa tayi bayan Hajjo saboda tsorata, bai tsaya wani bayani ba ya juya yabar dakin. "Eh zaka tarar dani yaro ni zakawa rainin wayau ka koro yarinya ina magana ka juya katafi, ke me kikayi mai haka da zafi ne?. "Hajjo fa ba Abinda nayi mai, ni Kawai wani ya tareni wai inbashi number wayata Kawai ya dakamin tsawa. "Ah toh yanzu naji batu ai sai ki wuce kibani wuri can ku karata keda shi. "Haba Hajjo inya dakeni fa? " ke kika sani tsakanin kune wannan. Ta kauce tana d'ingisa kafarta ta girma. Kinfita tayi saida su Farha sukazo suka jata, lokacin kowa ya shige cikin gida, FARIDA ba Abin da takeyi sai kuka, Momy tajata kuryar daki tafara yimata fada, " kiyi kokari ki tona min asiri kinji, nayi Abu saboda jindadin ki kina so ki watsamin kasa a ido kiyi kokari ki janyo Hankalin kowa ya gano abinda yake faruwa. "Momy kinga irin mugun kallon da yakemin ne kamar zai cinyeni. "Momy gaskiya akwai kura meye mafita? "Sadiya mafita daya ce dole sai ta shiga gidan komai zai daidaita. Su uku sukayita kuskus dinsu ba wanda yasani. Nimrah Jikinta ya mugun sanyi domin ji takeyi ta munafunci y'an uwanta taki fada musu gaskiya saboda gudun tsinuwar Momy.

Fahad
Abokanshi ne zagaye dashi duk ya burkice musu, " wallahi idan ba itaba bazanyi Auren nan ba yazasuje su nema min Auren wadda ba ita nace ba. " Relax abokina kabi a hankali may be ansamu misunderstanding ne, kasamu Dady kaji. Wani yafada mai. Mikewa yayi kawai ya nufi inda yasan zaiga Dadyn. Falon shi na cikeda jama'a haka ya hakura ya dawo fuskar shi kamar gobara. Abokin shi da ya tsayar da Amrah yace " abokina nima naga babe a gidan nan Amma fa wani zaki ya wafce ta Already, gaskiya yarinyar matar manyace wallahi. Yafada tareda fitoda wayar shi ya kalli hoton ta daya dauka ya nuna musu tareda fada musu abinda yafaru tsakanin su. Tasowa Fahad yayi cikin zafin rai ya fisge wayar " she is the one. Kallon shi sukayi duka, yace " itace wallahi, ita Nagani Nace inaso bankoma ba saboda Wannan Yayan nasu D'an rainin hankali, now see what happened because of him zan rasa farin ciki na. "Amrah that's her name, I remember one of her sister call her. Abokin shi yafada, "am sorry Fahad bansan itace babe din da kakeso ba, yanzu dai before a daura kafadawa Dady. "Hmmmm. Ya sauke doguwar Ajiyar zuciya tareda cewa " were did that FARIDA came from?.............. 🖊


"I will surely ask Hussy Ali???????
"So Hussy who the hell is FARIDA? 🤔



*Matar Soja*


🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻



*WRITTEN BY FENERH*


https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Join our free page group

Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb, ko ku tuntube ni ta wannan number domin Karin bayani 09011251444 or 09069200154.

Last free page

Page 🔟



............... Sai da dare Momyn shi tasamu his Excellency, tafada mai abinda Fahad yace, Kallon ta yayi cikin zafin rai yace " toh ki kiramin shi yanzu yanzu. Minti biyar yayi yawa ya iso ya gaida Dady sannan ya zauna kanshi a kasa, uban yace " Fahad wane labari nakeji a wurin mahaifiyar ka?. D'an shiru yayi kafin yace gaskiya ne Dady that's not the girl. " Uhm Amma kaje bayan munje mun tanbaya ai da wace yarinyar ka gana FARIDA ko Y'ar uwar ta? Shiru yayi kawai domin he can't recall anything. "Ok yanzu na fahimta so kake in zama mutumin banza a fuskar wainnan dattijan mutanen sunyi mutunci sun bamu Y'ar su ba wani jayayya, yanzu kai kana so ka tarwatsa musu gida da haukar ka, toh bazan yarda ba, FARIDA ce kaddarar Rayuwar ka so kaje kaci gaba da shirin Aure gobe ba fashi. Daga kai yayi fuskar shi kamar zai kurma ihu yace Dady bana sonta. "Zaka sota tunda kaga waccen rana daya kace kana so itama kasa soyayyar ta a zuciyar ka, now get up and leave. Momy ta kalle shi cikin lallashi tace " Ranka ya dade da

Please Login or Register in order to submit comment