Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dodone ni da zaki ganni ki gudu? Banason raini, and. Ya matso tareda kallon cikin idanun ta dayake hango tsantsar tsoron shi, " just saboda na kusance ki shine zaki taramin mutane kamar wata premature girl? "Kin girma ko ince kin kosa banga dalilin pretending kamar wata Y'ar Karamar yarinya , me kikeso in tsaya inyi miki, kinsa Momy tayi ta yimin fada saboda shegen raki, bazan iya lallashin mace ba, da ace zee baby nake Aure I can do more than that, because I love her with all my heart, kinyiwa rayuwata shishshigi dayawa, I hate you, please do me a favor ki tafi gidanku. Wani irin kallon damuwa take mai domin tasan itadai batada sauran amfani, tanajin kawayen su na fada koda namiji baya sonka idan yayi making love dakai zai fara sonka, Ashe marubuta karya suke mana ba ya faruwa a zahiri? Domin ita tasan budurcinta ya cinye yanzu yadawo yana gasa mata magana kamar wadda ta watse a waje. Kuka tasa tareda durkushewa tayi, kanajin sautin kukan kasan zuciyar ta na mata zafi, haka ya gama kwaba mata zance ya fice.
The next ganin da zatayi mai kuwa ya shigo ne shida wata babe Y'ar gayu tana tafe kamar bata kashi suka wuce cikin falon shi, tanaji tana gani yarinyar ta fito tareda shiga kitchen ta hado mai coffee ta koma dakin. Meyafi wannan ciwo a rayuwar ya' mace?. Duk ta fita hayyacin ta ga wani ciwon kai dayake yawan damunta a cikin kwanakin tayi fiyat tayi fau kamar batada jini. Ta zama wata irin silent, tanason ko y'an uwan ta su zo yace karta sake yaga bakin ta a cikin gidanshi bayason kwadayi don haka ta hana ko Aunty Sadiya zuwa dasu Farha da sunce zasu zo zata basu excuse. Gashi yanzu Momy ta tafi umara itada Dady gidan ita kadai shiyasa damuwar tayi mata yawa masu aiki ma ya hanasu shigowa yace bayason ganin su a part din shi.
Dayake ma ba wani aiki takeyi ba, abinci ma ba wani abu take dafawa ba bata wuce indomie ko tea shine Abincin ta, wata rana ma zataji bata son cin komai haka take zama. Rayuwar ta abin tausayi gashi ko Momyn ta takira ta tanbaye ta bata ce mata komai sai dai tace lafiya kalau.

Amrah

Da wuri suka shigo Sokoto saboda shiya tuko jirgin da kanshi yasa akazo aka dauke su da mota, kafin yagama clearance yabarwa dayan pilots din da zai juya da jirgin tareda wainda zasu koma.
Amrah kamar an sakata a Aljanna saboda farin ciki, Hajjo dai mita takeyi " kin dage mu dawo cikin wannan D'an banzan zahin. Dariya yayi domin ya tuna y'an da take tada balli zata dawo, wai yau ita ke fada da Amrah. Mutanen gidan sunyi matukar farin cikin ganin dawowar Hajjo domin ita din hasken gidan ce, su Nimrah sai murna sukeyi suka jata part din Mami domin suji tsegumi, hajjo kuwa labari ya tashi kamar wadda taje yawo garin kaduna, surukanta sun zagaye ta da cima kala kala, tace " ijin kun kaiwa Naziru bawan Allah shiya tukomu ko hutawa bayayi Ai dai Allah yayi Albarka wannan yaro. Murmushi Mami tayi ta mike tabar wurin tareda nufar gefen ta cikeda farin ciki. Saida ta hado mata nata abincin ta isa cikin dakin tana jiyo hayaniyar su, "oya ku bata wuri zataci abinci kunzo kun cikata da magana. " kai Mami muna hirar yaushe gamo ne don Allah. Har zatayi magana yayi Sallama ya shigo, tuni suka tashi suka fita bayan sun gaishe shi. Zama yayi gefen gadon tareda kallon ta ya gaida Mami, tace " me zakici? Kifi ko awara ga Kuma D'an wake. Murmushi yayi cikeda farin ciki domin yasan soyayyar da Mami ke yi mata ta dabance, bare yanzu tana dauke da jikan ta, "ai Mami yanzu kwai ne kawai dataci Sai Amai Kuma. Tura baki Tayi " zanci awara Mami da D'an wake babu a can. " waya fada miki? Kece baki ce zakici ba da zan siyo miki. Bajewa tayi ta kwashi awarar ta sannan ta ci D'an waken Kuma cikin ikon Allah batayi amai ba. Yaji dadi sosai, shima ya taya ta ci bayan ta koshi, ba ruwan shi da idanun Mami Sai faman shige mata yakeyi,
Suna cikin rahar su Momy tayi Sallama kamar anjeho ta cikin dakin.......... 🖊

Very soon zanfara baku two page saboda muyi sauri mu gama da izinin Ubangiji Allah ya taimakemu.

*Matar Soja*

🌻🌻🌻🌻🌻


Page 2⃣8⃣


........... Amsa mata sallamar ta Mami tayi tace "Saratu kece?. Tana zare ido ta kalli Amrah kafin ta maida kallon ta ga Nazir, cikin in ina tace " eh yaya ni ni ce nazo ganin baki da yi musu sannu da zuwa. Ko daga kai Nazir baiyi ba bare ya kalleta, yaci gaba da tura D'an waken shi, da farko mugun jin dadin shi yakeyi amma yanzu gaba daya yayi lusting apatite dinshi saboda ganin ta. Taunawa kawai yakeyi yakasa hadiye wa, she is the villain, itace sanadin komai dake faruwa a yanzu a rayuwar shi tazamo mai karan tsaye a cikin farin cikin shi, don haka ko shirin gaishe ta baya yi. Amrah ce tace " ina wuni Momy. Ta amsa da sauri harda washe baki cikeda fargaba tace " Sannu Amrah Maman biyu Allah ya ingata kinji, bari inje inkawo miki Abinda zakici irin na masu ciki. "Aa nakoshi. "Takan koshi yanzu sai dai Anjima. Mami ta fada. Shidai yayi biris itace ta kalle shi tace " Aa Soja ba gaisuwa ko duk cikin dadin D'an waken yaya ne?
Kara gimtse fuskar shi yayi kafin yace " ya muka sameku? Saboda idon Mami domin bai shirya magana ba har yanzu yana jiran right time. Tashi yayi ganin tana shirin zama yace " Mami zanje indawo Anjima.
"Aa ka ko shine? " no yanzu ko naci bazai wuce min ba a Ajiye min letter. Yayi gaba batare da ya tsaya jin wata magana ba. Tsegumi ne ya kawo ta Kuma he want let her see anything. Ganin ya fita tace " toh bari inje na gaishe ku. Saida ta fita Mami tayi shiru tana nazarin Nazir, duk da tasan tun Asali ba wani jituwa a tsakanin su, wannan karon abun ya wuce tunanin ta.
Shidai yana fita part din Ummi ya wuce, Wanda saboda kunya ya manta randa ya shiga. Tana zaune fuskar ta a sake bata nuna mai komai ba ta tarbe shi tareda cewa " naji wannan yarinyar ce ta saku tahowa baku shirya ba, ku Kuma kuka biyeta ko? Murmushi kawai yayi domin harga Allah kunyar ta yakeji musamman yanzu da yasan tasan da zancen cikin. Bai taba jin kunyar kowa kamar yanda yakejin kunyar Ummi don haka bai wani sake ba ya bar wurin, yana fitowa ya kalli part din Momy, a karon farko ya daure fuska ya nufi hanyar cikin shirin rashin mutunci.

Waya takeyi cikin fada, " nafada miki banson shegen cikin nan inga karyar daukar kai da yakeyi da ginshira shiba D'an sarki ba ba jinin sarauta ba, ga shegiyar yarinya tayi bulbul daga gani ba Abinda yake damun su, nidai bana son ingan su tare y'an da yaki Auren Ya'yana bazai zauna da kowa ba, kije kiyi....... Kalmar ta ma kale lokacin da tayi ido biyu dashi yana tsaye jikin kofar shigowa ya harde kafa hannayen shi cikin pocket.
Yaji duk hirar ta saboda ta bada baya. Sakin wayar tayi tafara in ina domin shi mara gaskiya.... Fuskar shi sam ba Annuri ya karaso cikin falon yana kallon ko ina a karon farko, saida ya kawo kusa da ita ya daga kai ya kalleta, " am sorry na shigo kai tsaye, but ba matsala ta bace tunda nayi Sallama kina can kina kokarin gina sharri , look I can't call you Momy because you didn't deserve the name, ban san meyasa kika tsani ganin farin cikin bayin Allah ba, me muka tsare miki nida Amrah? Meye matsalar ki da Rayuwar Aure Na? " kin shiga hurumin da banaki ba why, yakama ta ki gode min saboda ban fadawa kowa Abinda kika aikata ba amma kisani wallahi kiyi Addu'a matata ta haihu lafiya batareda wata matsala ba, inba haka ba zan manta ke babbace a cikin gidan nan, Kuma ki sani kina cin darajar mutane biyu na farko Abba na biyu Nimrah domin ita din zuciyar ta a tsarkake take. Cikin karfin hali tace " toh na gode mara kunya, tunda kazo har nan ka zageni zaka iya zuwa ka zafi zai..... "Ke".! Ya buga mata tsawa har saida taja baya " ki godewa Allah da ban daga hannu na zabga miki mariba, am ashamed wallahi ace ke din mun hada jini dake saboda sisters dina just tank God Mami ta koyamin girmama nagaba if not... Ya girgiza kai yayi gaba. "Kaje kayi duk tsiyar da zakayi Bazaku taba samun farin ciki ba muddin ina raye. Tsayawa yayi har yakai kofa ya juyo " lallai zakuwa kisha mamaki soon. Yafita.

Sai dare yadawo gidan yasamu su Abba a falo ya shige cikin su kamar yanda yasaba suka tanbaye shi aikin shi da Kuma yanayin zaman su yace baida matsala, Abba Mustafa yace " yanzu zaku koma kaida ita ne ko anan zaku zauna saboda lalurar ciki? Kanshi a kasa yace " nan takeso Abba so zata koma gida na itada Hajjo. "Abba babba yace "meyasa bazaka barsu a nan ba harta haihu ta koma can?. "Aa yaya kabarshi ya tsara Rayuwar gidan shi y'an da yakeso shima yanzu magidanci ne. " toh Mustafa na kyale dama wai shawarace. " toh bata karbu ba. Sukayi dariya, shidai yanzu tausayin Abba Mustafa yakeyi saboda irin matar da yake Aure idan yasan mugayen halayen ta zai shiga damuwa duk da yasan batada kirki dama. Abban Amrah yace " Yaya nace yakamata a duba mana lafiyar Farida tunda ta tare bamuji wani bayani ba gashi bata ko kiran waya. "Ai ina ganin lafiya ce ta boyeta don da ace akwai matsala uwarta zata sani Kuma bazata yi shiru ba don Kunsan halin ta. Abba Mustafa Yafada.
Abba babba ne yace " aa koma dai mene ne Naziru gobe ku je kaida Amrah taga Y'ar uwarta haka zaifi. "Toh Abba Yafada badan yaso ba domin baya kaunar D'an ganta kanshi da duk Abinda ya shafi momy, sannan Fahad yana kishin yaga mai Mata. Haka sukayita hira har zuwa karfe tara kowa ta watse,

Kwance yake a dakin shi na gauraye yana kallon saman silin, "yayi Aure amma baida banbanci da gauro saboda sharrin Momy. Allah ne yaso shi yagano gaskiya da Yanzu yafara tsanar ta, don haka yake binta a hankali karya takuri Rayuwar ta dayawa.
Yana matukar cutuwa, amma yazaiyi.
Tana can tana juyi itama haka kawai take tunanin y'an da take bacci akan kirjin shi kwana biyu kafin su tawo, bacci ne mai cikeda nishadi da farin ciki, tana son shakar kamshin turaren shi idan ta shaka jinta takeyi kamar tana cikin lambun turare. Zabura tayi ta zauna tareda tuna wani littafi da Nimrah ta tura mata ta karanta fuska biyu na Halima k mashi, jarumar data samu ciki haka tayi ta nacin turaren mijin ta, girgiza kai tayi, " bazai yuwuba bazan yi hakan ba ta koma tareda dunkule wa tayi baccin wahala rabi da rabi, jinta takeyi kamar ta kurma ihu bataso ta Amince da muradin zuciyar ta, so take tsanar nan da take mashi karta bar zuciyar ta. Saida tunda ta tashi da safe take kallon kofa ko zai shigo, tasan at least idan yazo zai rungume ta tasamu salama, amma har karfe goma takasa cin komai, tashi tayi ta nufi part din Hajjo ko zataci karo dashi, Hajjo ta gama surutun ta tabar mata wurin ta fita tayi na Ummi, kamar kuwa tasan jiranta taki zuwa tun jiya.
Tana zama ko amsa mata batayi ba tafara " ke banason shashanci meye matsalar ki da bazaki tsuguna dakin mijin kiba, kin taso bawan Allah kinsa yabaro aikin shi ya kawo ku, uwar me zaki tsinta anan? Ki kula banson shirme. Dama jiran take atabata tafara kuka, domin bakin cikin rashin ganin shi , tafara cewa " Ummi ni Auren shi ne banaso wallahi narasa dalilin da na tsani ko ganin shi kusa dani gashi yanzu neman shi nakeyi tundazu bangan shiba. Kallon ta Ummi tayi tareda yin nazarin maganar ta. Tuni taji wani irin tausayin ta abinka da uwa Kuma mai ilimi tanada sani akan wasu matsaloli tace "ya isa kidaina kukan ina zuwa. Tashi tayi ta shiga dakin ta ta fito da wata roba daukeda goruna ta dauki wani D'an mitisilin kofi, ta fara zuba mata Zuma kadan ta zuba ma'ul kal da man zaitun habbatus sauda da ganyen magarya kafin ta zuba busashshen ganyen magarya Guda bakwai tareda cika kofin da ruwan zam zam, ta daga ta karanta Ayatush shifa ta tofa tace " shanye banda ganyen yanzu ki rufe ido nasan badadi. Shanyewa tayi ba musu ta ce Anjima kidawo ki kuma shan wani, Kuma ki yawaita al wala da azkar sakaci ne yake janyo irin haka, kin saki Addu'a dole kuga jarabawa.
Tashi tayi ta fita ta na kallon kofar dakin shi a rufe kamar ta zuba ihu, har wasu sabbin kwalla ke zubo mata, komawa tayi Mami tace " inata cigiyar ki Ashe kin fita. " eh Mami naje na gaida su Ummi.
Dakin ta shiga tasamu Mutanen ta, cikin sauri tace " Farha please ko kinga Yaya?. Kallon ta sukayi tareda shekewa da dariya " oh love tin tin, yanzu aike zaki fada mana inda yake. "Serious ina neman shi. " ni tunsafe nakejin yafita ya leko ai amma iyakar shi falo. Shiru tayi batareda ta na sauraren suba, ko dai fushi yayi? Ko ya gaji da halin ta ne? Ya hakura ne da ita kamar yanda take ta rokon ya saketa?
What of inya saketa a halin yanzu? Wani irin faduwa gabanta yayi, zabura tayi tafara neman wayarta Tsabar rudewa ta kasa ganin ta saida Nimrah ta bata, karba tayi harda godiya, sai dai ta kirashi kusan sau hudu bai dauka ba, Ajiyewa tayi ta nufi toilet, kuka takeso tayi amma ba hali bataso sugano ta, don haka saida ta matse baki Tayi kadan ta watsa ruwa ta fito tayi matukar tsorata da sharewar shi a yau.
Ya yakasance all this long yanda tayi ta wahalar dashi?.....🖊

I try my best saboda bana son bada excuse wallahi tunjiya bamuda wuta Ina posting na sauka throughout wayata na kashe, Insha Allahu idan nasamu y'an da nakeso daga gobe zuwa Friday zanfara 2 page I nsha Allahu.


*Matar Soja*


🌻🌻🌻🌻🌻


Page2⃣9⃣


............. Suku ku haka tayita Rayuwa har zuwa wani daren bashi ba labarin shi, lokacin da ta koma wurin Ummi shan magani harda tanbayar Imran kanin ta tayi ko ya shigo ko yagan shi?. Yace bai ganshi ba, haka takasa cin komai, ta koma wurin Hajjo, tana zaune tana shan furar ta, zama tayi kusa da ita tareda leka kwanon ta ce "Hajjo karki shanye ki ragemin. " aa bazan bayarba don ba isa ta zatayi ba, ki Kira mijinki ya kawo miki kema. Cikin sauri tace " Hajjo shiya kawo miki wannan? Ina Yayan yake? " kibishi wurin aiki yatafi ana neman shi da gaggawa kinsan aikin nasu a kullum ba hutu. Wani irin faduwa gabanta yayi ta kalli Hajjo kamar yayi kuka tace " don Allah da gaske ya tafi hajjo ban ganshi ba.
Kallon ta yayi tareda Ajiye ludayin ta tace " toh sabon salo kiran sallah da usur, mijin naki Kuma kike tanbayar ya tafi bai fada miki ba? Saboda me? Ai kin manta da irin cin kashin da kikayi ta yimai bawan Allah yana shanye wa, Naziru D'an halak ne, yaron nan namijin duniya ne, ya sauke duk hakkin da Allah ya dora mai yabarki da kaya aka, wulakanci iya wulakanci kinyiwa yaron nan ya shanye batareda nuna damuwa ba, kai ai dole in nemo mai matar da zata san darajar shi ta kula dashi, yaro na rayuwa kamar mara galihu.
Wasu irin hawaye ne na kishi suka zubo mata a fuskar ta, karon farko datasan wata kalma wai kishi, jitayi wani irin mashi mai D'an banzan tsini ya ca keta tundaga kahon zuciyar ta har zuwa makoshin ta, kwatanta shi da wata yasa tuni taji amai ya taso mata, da gudu ta fita tsakar gidan ta kelaya ta zauna dabas ta kunna wayar ta tana girgiza kai, " na mutu ni Amra ina zansa zuciya ta, Yaya don Allah kadawo, ba wanda nakeson gani sai kai please don't leave me. Saida ta hango zuwan su Nimrah ta share hawaye tareda mikewa, kallon ta sukayi tareda cewa " ke Kuma lafiya? Ko abin masu ciki ne yafara.
Banza tayi musu ta kalli Farha, " don Allah ki kiramin Yaya. " aa wallahi ki Kira shi da taki wayar haka kawai Insha fitina ina zama na. " dialing tayi, tajita a busy, ta gwada yakai sau goma a busy, ta mike tayi part din Mami tana hawaye, wato har ya hakura da ita yana hira da wata a waya? Yanzu duk expenses kalaman shi wata yake fadawa, tasan yana daraja Hajjo yana jin maganar ta, don haka duk ta gigice tuni desire din son kwanciya a jikin shi ta kau sai bakin kishi, karo sukayi da Mami ta riketa ganin bata ganin gaban ta, "kibi a hankali karki fadi kinga bake kadai bace karki jiwa kanki, ina kika fito? Ganin tana kuka tace " aa waye kuma ya tabo ki? Rungume Mami tayi tace " Mami wai yaya zai kuma yin Aure?. "A, a inji wa? " Hajjo ce tace zatasa yayi Aure. "Wani irin murmushi Mami tayi, " aa ina ya isa ai ba maiyiwa ya'ta kishiya, muje kici abinci zancen hajjo ne. "Hmmm Mami toh ina yake?. " aa bai fada miki ba? Ai yana kaduna tundazu ankira su ko zasuje wane gari? saboda y'an bandit gomna yace ana bukatar pilot suyi clearing garin ta sama shiyasa ya tafi. "Cikin damuwa tace birnin gwari naji suna cewa shida yaya Kb, Mami garin suna kashe mutane. "Kedai kiyi mai Addu'a Allah ya tsare shi yadawo dashi lafiya Addu'ar mata ga miji Allah yana karbarta. "Toh Mami Allah ya dawo dashi lafiya. "Amen Y'ar Albarka je Abincin na ciki. Tafiya tayi zuciyar ta a matukar dame, abincin tsakura tayi, duk bayan minti daya saita gwada wayar shi busy, tagano bazai dauki Kira ba kenan, don haka kwanciya tayi tareda fara kokarin tura mai sako ta inbox. Kawai tama rasa mai zata fara rubutawa duk tafara saita goge daga karshe ta tura mai " please Yaya call me. Ji tayi duk duniya ba abinda takeson ji da gani sama da shi da muryar shi. One by one take tuna moment dinsu dashi tundaga farko har zuwa Kaduna, kawai sai taji ba Abinda yake sata nishadi sama da tunanin shi, cikin kwana biyu kowa yasan takara natsuwa idan bata tura mai sako tana sallaya tana azkar.
Zaune take jingine da gadon dakin Mami tana shafa marar ta datakejin wani irin dil dil Alamar harbawar jini, wani irin farin ciki taji domin hakan na nuna mata kobaya nan zuciyar shi tana tareda ita wato gudan jinin shi dake tareda ita a yanzu. Karon farko taji bayan shi ba wani abu datake so sai cikin nan na jikin ta,
Cikin rawar murya tace " my baby, ina son ka ina son Abban ka kaji, I love you and your dad. Wasu irin hawaye ke bin kuncin ta tana sharewa. Yanda yayi farin cikin samun wannan cikin kawai idan ta tuna hawaye takeyi, rashin kulawar data nuna mai a kaduna yafi komai damun zuciyar ta, wane irin miji Allah yabata tayi wasa da damar ta? Kanta take blaming domin gani take koma meye laifinta ne duk ta tsangwami zuciyar ta.
Wasa wasa haka aka kwashe sati hudu batareda taji muryar shi ba, kulawa tana samu bakadan ba a wurin Mami, Hajjo ma Takan yi mata abun arziki intaso, su Abba duk kulawar su ta koma gareta, ganin yanda cikin kedan bata wahala, koda yaushe kwanciya, su a tunanin su duk cikine ita kuma kewar mijin ta ke damun ta. Duk da baza a rasa me ciki da y'an matsaloli ba, amma damuwar mijin ta ce a ranta.

Kaduna

Tunda yatafi baisamu natsuwa ba, they are always busy, basa samun damar yin waya, gaba daya zuciyar shi tana cikin damuwa, he is worried amma dole ya danne zuciyar shi domin yayi aikin dayayi rantsuwa da rayuwar shi, dole ya bautawa kasar shi, yakan tunata da cikin ta a duk bayan dak'ik'a. Ga garin ma ba network duk an katse saboda irin barnar da y'an bindiga keyi a garin, saida suka kwashe sati biyu ya samu ya shiga kaduna a gurguje, yana zuwa ya kunna wayar shi. Messages dinta ne yafara cin karo dasu, tuni ya nasu yabisu a natse wasu ma sai ya biya sau biyu ko sau Uku, itace take rokon yadawo tana son ganin shi ko gizo wayar shi ke yi mai. Harya danna zai kirata zuciyar shi ta karanto mai ya bari suyi ido biyu da ita, don haka ya koma cikin farin ciki da nishadi tareda kwanciyar hankali, yasan yanzu cikin shi is save. Tunda tadawo hayyacin ta.
Su Abba ya Kira tareda Mami tafada mai matar shi na kewar shi, yayi dariya yace kyaleta Mami sai nadawo karki fada mata na Kira. Ko Hajjo labarin kenan yayi dariya sukayi Sallama, bayan tayi mai Addu'a.

FARIDA

Da safiyar litinin ta shigo gidan nasu jikinta a farfashe fuskar ta a kunbure idanun ta kamar zasu rufe saboda kunbura, duk su Abba na gida basu fita ba, tsayawa tayi tana tunanin ina zata nufa? Zuciyar ta ta karkata gefen Hajjo, can ta nufa lokacin su Abba na zaune suna hirar safe kafin su fita. Da Sallama ta shiga tareda Kara jan gyalen data saka tana rufe fuskar ta tsuguna. Hajjo tace musu " kamar FARIDA? Ko ba ita bace ke dago fuskar ki da kyau ingani ko gizo nake gani.
Janye mayafin tayi tareda share hawayen datake kokarin tarewa, salati Hajjo tasa tareda cewa " ke Y'ar nan barnar mota kikayi bamuji labari ba? Ina mijinki? Abba karami cikin bacin rai yace " Hajjo ba mota bace wannan duka ne kalli idanun ta da kumatun ta, Abba babba yace " wane irin duka meya faru da har wani zai bugeta haka? "Ke fada mana meke faruwa? Waya da ke ki? " Abba Fahad..... Ta fashe da kuka wani irin zafi da turnuki yasa ta sulale a sume domin ta tara damuwa da wahala da yawa. Nan take suka rude Hajjo tafara kunfar baki, "ai ku sani in dai har bugun nan mijinta ne yayi mata shi toh ba shakka kotu zata shiga tsakanin mu, don ban yadda ya Kama min jika ya mata bugun masu wanki da guga, ku dauketa ku samin ita kan kujera, kai samaila kiramin Zainabu yanzu. Abba Mustafa na zaune yakasa motsawa harga Allah zuciyar shi tayi mugun sosuwa Y'ar shi za ayiwa haka? Cikin minti kadan sun cika part din hajjo dukan su, Momy ce karshe ta shigo tana daura zani, kowa ranshi ya baci ganin yanda ta rame sai haske ga kamnin ta duk sun sauya, saboda wahala. "Wallahi bazan yarda ba sai anbimin hakkina, Uban me tayimai zai Dakar min ya' kamar jaka. "Imin shiru inga farfadowar ta kinji Saratu. Hajjo tafada cikin bacin rai, ruwa ta yayyafa mata tareda shafawa kan fuskar ta saida tayi kusan sau Uku kafin ta farfado, a zabure tana cewa "don Allah kadaina wallahi banfita yawon banza ba.
Riketa Hajjo tayi tareda cewa" ke

Please Login or Register in order to submit comment