Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin Abu ni hajara. Tafada tana zama gefen gadon ta tareda kwace hannun ta, zubewa yayi gaban ta yana magi ya, " wallahi hajjo nakai makura bakisan irin kalubalen da nake fuskanta ba a rayuwar aiki na ina samun attack ta ko ina kar tun ina kaucewa akaini limit din da zan kasa jurewa don Allah Hajjo......... 🖊




*Matar Soja*

🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻



*WRITTEN BY FENERH*


https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Join our free page group

Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb.

Free page

Page 4⃣

............. Subuhanallahi ni Hajara kawai ka fito Ka fadamin abinda ke zuciyar ka gaba daya ba kwana kwana ba, kai ni na haihi ubanka nasan duk abinda kake nuhi, don haka barmin daki tun ranka bai baci ba,mu zuba mata sai dai ka Hangota gidan Wani ba naka ba. Harya juya da farko zai tafi saboda yaji ta fara zagi amma kalmar ta ta karshe tasa ya tsaya cak tareda juyowa cikin fusata, " ko a mafarkin ki hajjo kika gani hakan ya faru ki ce Astagfirullah bare a gaske, ya juya ya fice cikin fushi ya barta rikeda baki tana salallami, " kaji d'an cin durun uwar yaro zaka hadu dani mu zuba.
Amrah kuwa tuni tabar wurin gaba daya karma su kuma haduwa, ta tafi da kalmar d'an iska a bakinta, ya manta cewar ita din kanwace agareshi? Kenan zai iya fadawa Farha hakan? Karon farko ta koma part din Ummi suna zaune itada Abban ta afalon yana shan black tea gefe guda kanin tane ke home work a kasa, zubewa tayi tagaida su, cikin fara'a Abba yace Uwar gidan Yaya ya akayi ne yau kika shigo mana hope bakomai? Diririce wa tayi tareda da fara in ina domin batasan dalilin zuwan nata nan ba. "Ai saiki tashi ki bamu wuri ko. Ummi tafada. Harta mike Abban ta yace"Aa zo nan Zainab Akwai magana ne?. "Aa Abba nazo ne muyi sallama gobe zamu koma school da safe. " to Allah ya kaimu, kunada komai ai domin nasan yayan ku ya sallame ku? " eh Abba. " masha Allah, ko Akwai magana ne? "Abban Su kadaina tanbayar ta, indai ba rashin godiyar Allah ba meta rasa da zata ce tanada magana, bayan Yaya na iya kokarin ta akansu. Mikewa kawai tayi, tace sai da safen ku. Domin itadai tanada muradin kulawar Ummi agareta itace Uwar ta tana matukar son taganta suna koda hira ne, zataso yau ace tana iya fada mata duk abinda yake damun ta Amma ina kawaici ne ko Kara ko kawai sonta ne batayi da bata kulata?
Ranta yayi mugun sosuwa Amma batada y'an da zatayi, bayan fitar ta Abba ya kalli Ummin yace " yakamata ki canza mu'amalar ki da zainab ki janyota ajiki karar zata zamo kwaruwa agareta tana bukatar kulawar uwa. "Hmm Abban su kenan, wato duk kulawar dasu Hajjo da yaya kebata bai isaba? Ai sai in zamo daya daga cikin mutane marasa godiyar Allah. "Hhh kedai kinci sunan naku na fulatanci. Haka sukaci gaba da tattauna war data shafesu. Wannan kenan.

********************

Sun koma makaranta lafiya sunci gaba da karatu cikin nasara da maida hankalin su domin sam basa wasa, tunda ta koma school kusan kullum sai ta tuna abinda Yaya NAZ ya mata akan hoton banzan nan don haka take kara tsanar shi Addu'a takeyi kada Allah ya kara hadasu ko a hanya ne, haka suka cinye wannan term din suka dawo gida wannan zuwan ya musu dadi saboda ba dodon don haka sun wataya son ransu, haka sukaci karensu ba babbaka har suka koma wanda daga wannan Tafiyar insun koma shine zangon karshe da zasuyi candy, wanda suka kara dagewa tareda bada Himma. Cikin nasara suka kammala suka tarkato nasu ya nasu suka dawo birnin shehu. Rayuwar makaranta ta kare saura jiran result suma suje gaba kamar y'an uwan su su Sadiya,
Sukan zauna wurin hajjo susha shaftar su suci ganye sushanye mata fura, kasan cewar sun kammala basa zuwa ko ina Abba babba yasa mo musu Wani ustaz yana kara musu karatu domin tun Asali sunyi nisa sosai kasancewar suna boarding yasa basu sauke ba yanzu ya musu Alkawari duk wacce tafara saukewa cikin su tanada babbar kyauta, don haka sun dage kullum suna maida hankali,

Sun kwashe akalla wata Biyu har sunyi mugun saboda da malamin nasu, har Amrah da bata sakewa da maza tana kula uztaz Salim saboda mutum ne mai ilimi gashi very cool and calmed, yana matukar kama mutuncin shi, yau ma suna kammala karatu ya kalleta, " Mu'allima zan iya samun number ki. Saboda haka yake kiranta har su Nimrah suna tsokanar ta dashi " Yah mu'allima, sai dai tayi dariya saboda y'anda yake kiran sunan ita kanta yana burgeta, ba wani musu ta bashi number Farha tace zai iya kiranta da wannan saboda batada waya don tun lokacin da ya Naz ya karbe bai bata ba, suka kwashe littafan su suka yi cikin gida, Farha tace " tab lallai uztaz Salim ya taka leda, Yaya kb yayi maita har yagaji kinki kibashi number yakira layi na kinki karba yanzu da hannun ki kin baiwa Uztaz, anya dai Amrah???. "Anya me? Ta kalleta tareda d'an yin murmushi tace zakiji dashi ai. "Intayi wari zata fito muji. Nimrah tafada, itadai bata kuma cewa komai ba Addu'a take Allah yasa Abinda take tunanin ne a zuciyar shi,yayi matukar kwanta mata a zuciya.

Ranar a gefen Mami ta kwanta saboda tasamu tayi wayar batareda sa idon hajjo ba, ta jira call dinshi har zuwa karfe goma ta hana Farha wayarta, sai misalin karfe goma da rabi ya fara turo mata sako da sallama ta inbox, cikin Sauri ta Amsa saboda yasan tana farke, "zan iya kiranki baki kwanta ba? Ko sai da safe kin gaji?
"Ka Kira banfara bacci ba. Ta mayar mai, second biyu kiran shi ya shigo ba wani jan aji ta dauka, " sallama tayi cikin kwantar da murya, ya Amsa tareda cewa "Afuwan mu'allima kinsan nima dalibine ina daukar karatu don haka sai karfe goma na tashi a masallaci. "Bakomai ya karatun? " Alhamdulillah kuna kan muraji'a ko? " eh. "Masha Allah, "Hmmmm nasan zakiyi tunanin abinda yasa na karbi number ki da farko ko?, toh ba komai bane face sirrin zuciyata nake so in bayyana miki ban iya hakura a gaskiya, naso in matse zuwa lokacin da zaku sauka Amma na gaza hakuri, don haka ga Almajiri da kokon bara ataimake shi, ni din nasan nayi tsaurin ido ta kawo kaina a wurin ki bayan nidin ina Almajiri mai neman rufin Asirin yau da gobe, nasan baki san komai akaina ba a hankali zan bayyana miki koni waye, amma zancen gaskiya banida karfin Aljihu talaka ne ni sai dai wayasan gobe tunda muna kan nema Allah muke roko yabamu dacewa. "Amen. Ta furta tana jan numfashi mai dauke da kwanciyar hankali, Allah yagani tana son Salim yayi mata, saboda kamewar shi ga ilimin Addini ita din tana son Auren mai ilimin Addini bai kula da Addini ba namiji irin su sarkin rawa da iskanci ba ya Naz.

"Zan baki lokaci Idan kin gama tunani inajiran amsata ma'assalam. ya kashe wayar, tayi Saurin dawowa dai dai tareda dafe goshi, garin tunanin banza har ya kashe wayar tana sauraren kalaman shi masu bata natsuwa, lallai yaya NAZ shaidan ne tunda tunashi kawai yazamo mata katsewar farin ciki. Haka ta kwana cikin farin ciki ta tashi cikin walwala tayi matukar matsuwa lokacin karatun su yayi yazo gidan taga idanun da suka gama fada mata wainnan kalaman masu kwantar da zuciya, saida hajjo ta ganota tace ke kuwa yau wayayi miki wahayi da sakon Alkhairi irin wannan Annuri? "Uztaz Salim ne hajjo. Su Nimrah suka fada domin suna cikin falon nata tare suka shigo, harara ta watsa musu " to sa'idawa. " ku dakata wanene salmin?. "Kai hajjo Salim akace kin bata mai suna. "Oh toh ai sai kumin bayani yanzu ingano inda aka dosa. Farha ta fada mata waye shi, taja numfashi tareda cewa " tabdijam akwai hauka kenan agidan nan Idan shugaban masu hankali ya diro. " waye hajjo ya Khalid? Farha ta tanbaya? Cikin gatse tace "Haladu dai, kutashi kutafi ciki ke hadiza kiromin Zainabu yanzu. Duk ta rude tarasa meye hajjo ke nufi da wannan kalmar don haka ta tashi a sanyeye, tabar gefen nata ta nufi na Mami wanda atake ita kuma tabiyo umarnin hajjo ta tafi,


Kamar da wasa yau ba Salim ba labarin shi har lokacin daukar karatun su, tayi matukar shiga damuwa ga Farha ta karbi wayar ta ba y'anda zatayi taji ko daga gareshi, don haka ta zubawa sarautar ido,
Tun tanasa ran jin wata magana agidan d'an gane dashi har ta fawwalawa Allah, kamar da wasa kawai sai sabon Malami aka kawo musu, anan ta tabbatar da Salim bazai taba dawowa ba, haka taci gaba da daukar karatu bata kuma cewa komai ba ko su Farha bata yiwa complain ba y'anda taji ba wanda yace wani abu acikin su, haka lokacin yake tafiya har suka kwashe wajen wata shida agida,
Tun tana tunashi harta manta dashi domin tasan da yana kaunarta Tsakani da Allah zai nemeta tunda yasan gidan su,
A tsakanin ne Abba yasamo musu computer school kafin result dinsu ya fito suna zuwa da safe zuwa karfe hudu sundawo suna jin dadin karatun sosai.

Yau ta kasance lahadi ne suna gida suna hutawa a harabar tsakar gidan Hajjo, kasancewar garin na sokoto mai tsananin zafine yasa kowaccen su tasaka kaya na shan iska saboda ba wani namiji dake shigowa gefen na hajjo bayaga jikoki kuma duk basa gari sun baje suna cin koson rogo da yaji da Nimrah ta soya hajjo na ci tana mitar ta cika tanka, na kallesu dakyau dukansu masha Allah kowacce taji kayan alatu musamman jarumar taku tana sanye da bakar shimi mai roba a tsakiyar kirjinta wanda ya raba tsakanin mamanta kamar bra sun baje sunyi mugun kyau tareda cikowa Alamar a zaune suke kyam masu gindin tasa, Allah ya mata wata irin k'ira mai tada fitinar da namiji, don haka take jin kunyar sakin jikinta a KO ina, ko yanzu da karamin hijabi a gefen ta saboda tsaro, cin kosan su suke suna raha tareda tsoka nar Hajjo tana ramawa, basu ankara ba kawai sukaga mutum kamar ankoro shi tsakiyar kansu batareda tsammani ba, sanye cikin wandon kaki da T-shirt na camouflage,
Tuni suka yi Suman zaune musamman Amrah, tayi wani irin freeze saboda tsorata ko motsi ta kasa yi bare ta dauki hijabin ta lulluba a jikinta, muryar Hajjo ce tasa ta dawo wa hayyacin ta kadan, " kai meye na fadowa ba sallama cikin gidan mutane sai kace korarre.

Wani murmushi yayi mai matukar kayatarwa tareda bata amsa idanun shi na yawo a kasa bazaka taba sanin ina suke kallo ba, " Sallama sai dai in speaker zan dakko, nayi sallama kamar zan rasa muryata kun cika gida keda wainnan kanarin ya zakuji sallama ta?. Tuni Nimrah ta tattara plate da robar yaji ta mike Farha ma tamike suka fara gaida shi tareda shigewa ciki da Sauri, Amrah kuwa takasa koda motsi domin tasan bata isa ta mike ta wuce a y'anda take ba saboda tight tree quarter ne ajikinta bayan shimin, da Sauri ta tuna da hijabinta ta janyo ta zura kanta a kasa, kujerar dake gefen hajjo ya zauna wanda tanajin duk wani motsi da fitar numfashin shi tareda tashin fitinannen kamshin Jikin shi, jin numfashin ta na sarkewa dole ta mike batareda tace uffan ba ta juya tareda daga mulmulallun kafafun ta farare gwanin sha'awa ta fara tafiya cikin natsuwa, wani arnen numfashi yaja tareda Kallon Hajjo cikin fuskar Marai raita kamar zaiyi kuka, " haba Hajjo kina kallon ta zata wuce ko kallo ban isheta ba, Hajjo kodai tanada saurayi ne? "Kai karka karanta min hauka anan Idan zaka samu yarinya ku dai daita kaje kasame ta ina nan kan bakana sai ta Amince zansa baki ba Auren dole a zuri'ata, "wallahi bazan je ina lallaba yarinya ba kawai don ina son Auren ta bayan inada iko da ita ma, nifa nakai bango yanzu bazan bar garin nan ba sai nasan matsaya ta. "Mu zuba nida kai shege ka fasa. Ta mike tabashi wuri, ya zame kasan tabar ma tareda dora kanshi a kujerar yana jan Wani irin numfashi mai zafin gaske,........ 🖊

"Wai ya za ayi wannan Al amarin ne??

*Matar Soja*

🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻



*WRITTEN BY FENERH*


https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Join our free page group

Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb.

Free page

Page 5⃣

............ Tunda tashiga bata tsaya wani abuba ta nemi kaya masu mutunci ta saka kafin tadawo falon suka fara hirar su, Nimrah tace " guys ko kunga yaya NAZ ya kara eh. Kamar jiranta take yi tace " ina ruwan mu da Abin da yakara inyaso ya fi duk samarin duniyar nan kyau who care???. " he he he relax, ya haka daga fara magana kamar kina jira? Oh Ashe kingane yanada kyau yanzu?. "Don Allah yiwa mutane shiru haka Nimrah, ko zakije ne ki rika mai zaman fada saboda yabo?
Farha tace " kai kun isheni kubarmu haka ina ruwan mu da Yaya NAZ shi yana can yana ta kanshi ku kunzo nan kuna son tada hayaniya akan shi mtswww. "Waye zaiyi hayaniya akan shi anan? We are just talking, hayaniya sai su Aunty Farida da Aunty Sadiya sune masoyan shi, mu ai bamai jin kanmu we are triplets Nimrah ta kuma fada, nan sukaci gaba da sha'anin su har zuwa dare.


Nazir kuwa tunda yabar part din na Ummi yaje ya gaida ita yaci Abinci kafin yaje na Mami tayi mai maraba tareda farin cikin ganin nashi domin ya kwana biyu baizo ba, ta d'an tarairaye shi da abubuwan motsa baki ya d'an taba yace Ummi ta cika min ciki Mami. Murmushin farin ciki tayi domin ance mai da' wawa don haka take matukar kaunar Ummi y'anda take son jinin ta tareda tarai rayar shi aduk lokacin da yake gari itake da wainiya da cikin shi har yakoma, "kace Maman ka ta cika ma ciki to barmin nawa ya'ya na zasuci dama saboda Amrah nake Ajiye shi tafi son cin kayan fulawa akan Abinci wannan ma da kanta ta yi shi jiya. Plate din ya kuma kallo tareda nazarin when tafara shiga kitchen and who teach her. Abinka da uwa tuni ta harbo shi tace " ai duk tafisu iya sanwa domin indai ina girki tana gefe na don haka ta iya sarrafa tukunya fiye da tunani. Gyada kai yayi tareda jan numfashi ya mike, plate din yakeso ya dauka no way don haka yace " Mami zanje in d'an watsa ruwa in huta. "Toh Idan kana son snacks din Anjima zansa yaran nan sukawo ma. "Ok Idan zanci zankira akawo am full now. Ya tafi cikin takun shi na kosashshen namiji. Tabishi da kallon so irin na d'an da ya shiga zuciyar Uwa, duk y'an da takai ga kara kana gane soyayyar da takewa d'an nata,

*******************************

Juyi yakeyi akan gadon kamar zai fado tun zuwan shi garin jiya bai kuma fita ba, zan iya cewa tunda ya ganta jiya Jikin shi bai kuma samun kuzari ba bacci kuwa shiyasan kalar wahalallen da yayi mai cikeda mafarkai masu Alamar error, tsaki yaketa faman yi, tashi yayi tareda dukan matrass kamar zai fasa yace " Hajjo Hajjo me yasa bazaki rufamin Asiri ba?.
Har karfe tara yana kuryar part din shi bai fita ba gashi yafara jin yunwa ya dauki waya ya riketa gam kafin ya d'an na wa Momy Kira. Dagawa tayi cikin Sauri domin tana kusa da ita, " Mami ina Kwana. " lafiya kalau, ince ko lafiya? Lafiya kalau Farha za aturomin don Allah. Kallon gefe ta yi Amrah ce ke gyara wa Mami farce, " Farha bata gidan nan ban masan ina suke ba itada Nimrah Amrah ce kawai a kusa dani. Tashi yayi da Sauri yafara zarya bai iya cewa komai ba na d'an second kafin yace " tazo. Murya can ciki kamar mai ciwon makoshi shikadai yasan halin matsi da takurar da yafara shiga just because of her, things a getting out of hand slowly,
Ita kuwa tuni gaban ta ke bugawa tunda taga kiranshi domin taga y'anda mami tayi saving sunan shi da yayan su, lokacin da mami tace sai ita kuwa kamar ta kurma ihu tasan halin shi zai iya sawa tazo ya wahalar da ita domin tasaba tun tuni da irin halayen shi, haka kuwa Momy tace mata ta tashi ta tafi, ba zabi dole ta mike bata tsaya yin komai ba domin abayace mai kyau da d'an karamin breziya hijab baki wanda ya kayata fuskar ta tana kamshi mai kwantar da zuciya, domin Momy bata barin su ba turaruka har su humrah culacca duk tana siya musu,
Zuciyar ta na harbawa haka ta wuce ta tafi,
Ta dade akofar part din nashi kafin ta buga, yana zaune akan wata kujerar hutawa guda daya mai kamar jirgi ya ware kafa dagashi sai short iya rabin cinyar shi, duk wani gashi na jikinshi a bayyane ga kirjin shi cike fal da suma mai kyau dole mace ta ganshi ta rikice ta haukace, don haka ya fito a haka he want to test her, yanaso ya dasa mata soyayyar shi so yake ya yaki zuciyar ta, in har mata zasu ganshi surude why not ita? " you most love me. Yafada cikin ranshi, bugun kofarta yasa ya mike tareda nufar kofar ya bude,
Kanta akasa tana wasa da yatsunta da sukaji jan lallen gargajiya hannun gwanin sha'awa kamar ka lashe, taji tsayuwar shi domin wannan kamshin nashi ya Sanar mata don haka takasa daga idanun ta shikuwa kamar yasamu television haka ya zama tundaga kasa har sama yake kare mata kallo dakyar ya saita zuciyar shi ya kauce tareda d'an daure rai " get in malama kinzo kin tsaya min kamar gunki a kofar daki. Dago kai tayi tareda kallon shi sau daya ta mayar da kanta Jikin ta yafara rawa, zata iya cewa yau ne karon farko da taga wani garsamemen kato ba kaya dagashi sai wandon da ba abinda ya rufe a ganin ta, kafafun ta takasa jansu bare ta shiga don haka ji tayi kamar ta koma, kasan zuciyar ta kuwa cewa take "tab su Aunty farida basuda hankali da za suso wannan mutumin ai wannan sai ya kashe mace mutus. Har yakai kan kujera bai ganta ba, cikin tsawa yace "Were are you? Kamar an hankadota haka ta shigo kafarta kamar bazata dauketa ba, bata kuma Y'ar da ta dago kai ba. Muryar shi ta jiyo cikin fada " look here my friend, ko baki taba ganin namiji bane da kike wannan dukar da kai, ki daga kai ki kalleni kafin in fasa manyan idanun nan yanzu tunda ni ba dodo bane kuma ba kuturu ba. Girgiza kai tayi domin Allah ya gani kirar shi ta firgita ta don haka batajin zata iya hada ido dashi,
"Ke I said look at me. Tuni ba shiri ta daga kai tareda sauke idanun ta cikin kwayar nashi tana juya kai saboda tsoro, " Am sorry ya NAZIR please zan tafi wurin Mami. Tafada cikin tsabar kidimar da tuni ya sassauta kanshi tareda jin zuciyar shi na narkewa tana kara bajewa, saboda kalmar cikin shagwaba tayita wadda ita sam batasan tayi haka ba, tuni ta cinnawa zuciyar shi wutar dake ta ruruwa tun tuni bata gama kamawa ba, my goodness am dead. Yafada cikin zuciyar shi, sam baiyi gigin tashi ba gyara zama yayi cikin wata irin murya yace go please. Domin yana ganin one more minute ta kara akwai babbar damuwa don haka tana fita ya juya ya kife a kujerar yana numfar fashi ya dauki dogon lokaci kamar zai shige cikin kujerar ya binne kanshi, "Hajjo Hajjo Hajjo please help your grand child. Yaketa furtawa, how can I talk to her? Yanzu yake sanin shi din ragone Idan akan zancen Amrah ne he don't have strength agaban ta duk y'anda yake ganin he is man enough if she is around yakan rasa kuzarin shi, akanta yanada rauni ya Y'ar da a yau, he no he loves her tun zuwan ta duniya, but bai taba sanin zuciyar shi tayi rauni akan sonta ba sai yanzu .
Bai fita ba sai karfe daya saboda zuwa masallaci, ya sanya wata designer jallabiya ta maza mai kalar ruwan kasa yana sheki , sai da ya idar da sallar ya shigo cikin gida, gefen Ummi ya nufa tana shirya table din ta domin Abba karami ne agidan kawai, taci ado tana zabga kamshi, she is just a great woman ga manners ga addini ga iya zaman Rayuwa he loves that woman for so many reasons, "Yayan su dama kana gida bakazo kayi breakfast ba na dauka ka fitane? " aa Ummi ina nan gajiya nayi shiyasa na huta yanzu zanyi lunch. "Ok sit down bari in hado maka.
Bajewa yayi yaci ya koshi da girkin Ummi mai shegen dadi, kafin ya tafi, a hanya yaci karo da Momy ita dasu Sadiya anci ado za afita kamar kawaye sunatafe ana shewa, ya hangosu sarai ya basar kamar ma yakoma inda yafito su wuce, su Sadiya suka fara gaida shi cikin rawar jiki, itama Momy tace " aa Nazir yaushe agari? Gaida ita yayi ba yabo ba fallasa yace "jiya da rana. A takaice, " oh shine baka lekomu ba ai bakomai nasan kaje wurin su Zainab. Wani irin kallo ya watsa mata, that's why he hate her yazata hada kanta da uwar shi mtswww. Yaja tsaki ya wuce a ranshi tana mita. " Nagano wanda ke min farraku da yaron nan duk tsugudidin Aisha ne kuma nakusa maganin ta ca takeyi bansan munafurcin da take shiryawa ba, nasan sarai so take ta cusa mai Y'ar ta shiyasa take kan kankan ba tareda asire Asire domin ta siye zuciyar shi. "Momy please muje kar kayan su kare. Sadiya Tafada domin ita tama cire rai da zancen wani Yaya NAZ saboda tasan Y'ar banzar wahala zatasha, FARIDA kuwa tunda sukayi two eyes zuciyar ta ta kara narkewa, da bata wani damu dashi ba yanzu kuwa ta kwallafawa ranta Auren shi domin maza irin ya NAZ ba karamin iya Soyayya sukayi ba irin su ke ririta mace tareda shagwaba ta, suna tafe tana imagine ganinta cikin faffadan kirjin nan nashi Idan sunyi Aure.

Sati daya ya kwashe a sokoto yayi iya yinshi domin ganin ya bawa zuciyar shi natsuwa ya tunkareta abun ya gagara gashi duk haduwar da zasuyi kara wahalar da zuciya da Ruhin shi takeyi batareda ita tata zuciyar tayi laushi ko ta karkata agareshi ba impact ya lura she is running away from him,yarasa dalilin tsoron da yake hangowa a zuciyar ta gashi kwata kwata sau biyu suka hadu tun zuwan shi garin har zai koma he try his best abu ya gagara haushin Hajjo yakeji don haka ko zuwa wurin ta bayayi. , " no no no Amri zaki wahalar dani da yawa. Yafada batareda ya shirya fitowar zancen ba, yana zaune a falon Ummi bayan yagama dinner, kuma tana gefen shi, ta lura da y'anda duk kuzarin shi ke raguwa a kullum, yarasa ta ina zai bullowa lamarin. Kasancewar Ummi macece mai Kauda kai, yi tayi kamar bata fahimci kalmar data fito bakin shi ba, amma ta tsorata

Please Login or Register in order to submit comment