Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guda biyu sai kuma kannin su da suka kammala secondary shekarar nan sun sauke kuma suna computer academy kafin sakamakon su ya fito suci gaba. "Masha Allah hakan yayi kyau kuma ya tabbatar min da kudin dattijai ne don haka zanyi matukar farin ciki da'na yasamu Auren daya daga cikin Zuriar ku, sai dai wani hanzari ba gudu ba Yafada min bata fadamai sunan taba yanaso yasamu izini su dai dai kansu. Abba ya kara gyara murya yace " akwai sarkakiya kenan domin da nasan wacece sai mu tsaida maganar a yau ba sai gobe ba. "Ai ko yanzu inaso inje da labari mai Dadi don haka ku bamu dama zuwa gobe inturo y'an uwa na da goron angani anaso.
"Bakomai Yaya koma wacece mun basu sai yaron yazo Yafada mana wacce yakeso kawai.Baban su Nimrah yafada. Ba y'anda Abba ya iya dole ya Amince suka yi sallama tareda rakashi har waje yatafi.......... 🖊



"Akwai ta kenan.


*Matar Soja*
🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻



*WRITTEN BY FENERH*


https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Join our free page group

Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb.

Free page

Page 7⃣

........... Saida ya wuce suka tsaya kamar zakaru domin basu san ta ina zasu bullowa Hajjo ba, "Mustafa yanzu Sai muje mu tunkari tsohuwa muji ta bakinta tunda ka ce musu mun basu kai tsaye. "Toh ai Yaya dolen mu mubashi ace kamar shi yataso yazo bawai D'an aike ba ace mun jamai rai ai abun baiyi ba, ko ya kagani kabiru? Ya kalli Autan su Baban Amrah. "Hmm yaya ai ba nan rigimar takeba tana wurin Hajjo don kasan bata bamu damar tsayar musu ba kaga ko Naziru tace ita keda zabi don haka muje kafin lokacin masallaci yayi. Haka suka dunguma zuwa gefen Hajjo, domin tun fitar su ta dingisa tadawo nata gefen, goron ta take balla a hankali tana jiran zuwan su domin tasan koma meye dole a Neme ta,
Zama sukayi kasan kilishin dakin nata tace " ya akayi ince ko lafiya? "Uhm Mustafa kafada ma hajjo kawai. "Aa inace kaine babba? " eh Hajjo. "Toh ina jiran bayani yanzu. "Um dama akan zancen Auren D'an shine yace yana nemawa D'an shi Auren daya daga cikin wainnan yaran shine ya taso yazo. Yayi shiru, saida ta taune goron ta tas tace "toh ku meye Amsar ku a gareshi? "Nafada musu mun bashi Hajjo. Kallon su yayi dakyau kafin tace " lallai samaila wato da raina tun bankwanta dama ba ka nuna min bazaka iya wakilci akan abinda na doraka akai ba, kana kallo kuma kanaji kanin ka ya zartas da hukunci, wato kai kuma Mustafa wuyanka yayi k'auri har zaka yanke hukunci ga yayan ka a wurin ko? Toh yadda kabashi ka koma kace ni hajara mahaifiyar ka nace kaje ka amso ban bada ba.
Kamar walkiya haka Momy ta fado dakin "haba hajjo wannan ai sai ince bakin ciki kike yimin haba, yaza ace yaro D'an gidan girma ya fito neman Auren yarinya kice kar a bayar gaskiya nidai ana nunamin bakin hali da ban ban...... "Ke mahaukaciya, waya baki izinin zuwa nan?"Mustafa ya isa, ke Saratu Zauna anan. Abba ya bata Umarni " wacece acikin su Fahad ke nema? " FARIDA ce yaya sun dade tare ka tanbaye ta ma, ke FARIDA shigo ciki kiyi bayani. Kwatsam ya fito daga cikin dakin hajjo domin duk abinda suke fada yanajin su so yake yaji karshen danbarwar kuma yanada masaniyar hajjo bazata taba yarda ya rasa taba sai dai bazata bashi ita cikin dadin rai ba may be sai tagan shi kwance a Asibiti, gashi tun ranar Mami ta warner shi tace kar taji ya musu fada akan hakan, don haka yayi shiru yana jiran dawowar Fahad don haka ko hajjo bai kuma ce mata komai ba, yanzu haka tun safe take korar shi yabar mata gida yama shige ya kwanta agadon ta duk don yanaso ya yi ido biyu da Amrah , ita kuwa kamar ta sani taki ko lekawa sasan hajjo. Yama gaji da wannan yanayi zuwa zaiyi yabar musu garin enough of the hutun, don haka he decide tomorrow morning zai koma kaduna yakarasa pass dinshi a can.


Duk su Abba kallon shi sukayi kafin Abba yace " kai kana ciki kamar mace.
Bai amsa ba sai mugun kallon da yafara watsawa FARIDA kafin yace " bace min da gani kafin in sumar dake yanzu. Tuni ta gudu sai Momy tafara kunfar baki " aa kaga banson bakin halinka na gado yazaka kawo min bakin ciki bayan kaki Auren su yara sun samu miji wanda yafika zaka hana, wallahi ban yarda ba indai kaga Farida bata Auri Fahad ba toh ban numfashi. Bai tanka mata ba, ba Kuma wanda yace mata tak harta kai karshe tayi waje Abba ya mike bayan ya duba Agogo yace suje Masallaci sudawo tukuna sai suci gaba da maganar. Amma duk inda ran Alhaji Mustafa yake ya baci saboda shidai yasan baida Matar Arziki duk y'an uwan shi sunfi shi sa'ar abokan Zama.
Haka sukaje masallaci harda Nazir suka dawo, Lokacin Hajjo ta hada duk matan gidan a falon ta, Momy na zaune tana girgiza Alamar kiris take jira tahau tofin Ala tsine, suka shigo da sallama shikadai ne a cikin yaran ya shigo wannan taron,
Hajjo ta gyara zama tace " bismillahir rahmanir raheem, a uzubillahi minash shaidanirrajeem, ke Saratu ki hita Idona dazu Kinyi ganin damar ki Toh inada rai da sauran karhi zan dauki mataki akanki Idan baki shiga hankalinki ba kinji ni ko yauwa sannan ku kuma zancen Auren da kuka bayar tunda sunce FARIDA ce na Amince su kawo kayan sa ranar su sati mai zuwa, sannan abu na biyu itama Sadiya ta turo nata a hade su tun ba'a fara zancen kannin bayansu ba, kuma ku sani Umarni nane ba canzawa don haka kuje ku fara shirin biki don haka kutashi kubani wuri nagama magana, ke kuma Zainab kijirani inada magana dake.
Tunda ya zauna wurin bai motsa ba sai sauraren su Hajjo yakeyi sarkin mulki da tsari, kuma shi abun bai mai ba domin yasan akwai sauran rina a kaba, yaso tasa nashi zancen Amma Hajjo sam taki furtawa don haka zuciyar shi mugun tafasa takeyi har iyayen su suka watse bai saniba yarage dakin daga Hajjo sai Mami sai shi, "tashi kabarmin daki inada magana da Uwarka kaji ko malam miskili. Dagowa yayi fuskar shi murtuk yace wai Hajjo me kike nufi dani ne? Mami tace "kai kabamu wuri zamuyi magana kaji Idan ka shirya Auren kasan me zakayi ai. "Nagode Zainabu. Hajjo tafada, tashi yayi saboda Mami yabar falon, shi yasan waye Fahad keso kuma koma meye dole liki ya balle don haka yaso ayi nashi zancen a wuce wurin.

Tsabar takaici da zuciya yasa tun Asuba yabar garin sokoto kuma ko Sallama baiyiwa kowa ba sai Farha daya Kira yace ta bashi Number ta, wanda abun ya matukar bata mamaki sai dai bata iya fadawa kowa ba, Hajiya Momy Saratu kuwa ta dage sai shopping takeyi ana siyi wannan siyi wancan, ko yanzu tana zaune ya'yan ta na zagaye ga wata mai kayan mata ta baje musu sai zabe sukeyi tana tayasu, " ku zabi kaya dole ubanku yabiya duk makon shi. Tafada tana kara debar musu, a ranar ta sameshi akan yakawo kudin kayan gyaran yara dubu dari biyar su biyu, Kallon mahaukaciya yayi mata kafin ya ja tsaki yace " gaskiya Saratu kina bukatar Asibitin mahaukata su duba kwakwal war ki, yanzu ko tsaida maganar Auren bamu gama yiba kinfara shirme toh sai kizo ki kwaci kudin. Ya baza malum malum ya fice kafin tasamai hawan jini.

Hira suke tsakanin su ukun suna dariyar Abinda yafaru ranar tsakanin su da Fahad, duk wainar da ake toyawa basuda labari agidan sun san dai za'ayi Auren su FARIDA, waye zasu Aura oho basu sani ba, bakuma ruwan su, har Nimrah bata shiga sabgar ta domin Momy cewa take ji take ba jinin ta bace ita kila an mata canje a Asibiti shiyasa zuciyar ta tafita daban a cikin ya'yan ta. Ita kuwa saboda zama da su Ummi tasan Momyn tata akwai gyara kuma ta godewa Allah da yasa bata cikin shirmen su, wayar Farha tayi Ringing tayi Saurin picking domin tunda ya karba bai kiraba sai yanzu. Shiru yayi yanajin dariyar su Amrah da Nimrah akan y'anda suka rika boyewa ganin shi, mikewa Farha tayi zatayi waje yayi Ajiyar zuciya yace " go back, and don't cut the call. Jikinta na rawa ta koma ta zauna tareda Ajiye wayar a gefe tayi tsit kamar ruwa ya cinyeta Idan sunyi magana sai dai tayi yake taki Y'ar da ko tari ta Kuma yi yajiyo ta. Amrah kuwa kamar ranar an saka mata remote " Amrah wannan gayen mahaukaci ne kina ganin y'anda ya rika biyo mu muna Y'ar fashi da yake banza ne har da biyomu kofar gida, kunsan me? wallahi naji dadin da Ya NAZ ke gida ya kore shi don natsani namiji mara Zuciya kuma banason ragon namiji daga ganin shi kin san baida wani karfi don wallahi duka yaya NAZ zai mai yabar shi a kwance a wurin don kina kallon shi kinsan biscuit bone yakeda. Dariya suka saka harda Farha domin hirar tasu ta man tar da ita da wata waya Amrah ta kai mata duka tana dariya " kedai anyi banza wallahi, yaushe kika taba ganin namiji rago a kul, Tafada tana kashe mata ido Alamar ta mata fassara. Harara ta watsa mata " ke kika sani banza kinsa hirar ma ta fita kaina mtswww. Ta tashi tareda rage kayan Jikin ta " to kwaduwa wankan ya tashi? Toh don Allah karki dade kiyi kifito nima zan watsa sai mutum ya kwashe kusan hour a bathroom kome yake wankewa oho. Hasken wayar Farha yasa ta tuna da kiran shi, tuni ta dafe baki that means yagama jin tabar gazar su? Innalillahi. Wani irin k'ugi cikin ta ya dauka ta janyo wayar tareda tuna ita mema tace a hirar?.
Amrah tace " ke wai Kinyi secret admirer ne kike daukar waya a sirri? "Aa secret lover mtsss.

Dai dai yake kwance akan katon gadon dake cikin dakin nashi dagashi sai boxer yayi dai dai, Tsabar kewa da wani irin muradi' ko ince marmari da shauki ke dibar shi, a duk lokacin da yayi nisa da ita kewar ta tabi addabar shi, shiyasa ya karbi number Farha domin ya daure ya mata magana ko a phone ne yasamu saukin zuciyar shi, hirar su ta motsa wani bangare na zuciya da gangar Jikin shi nishi yaja mai karfi ya juya rub da ciki he is imagining her a bathroom, wanda yayi iyakar yaki da zuciyar shi abun ya gagara he don't want to think about it amma ina abinka da mai lafiya tuni duk wata gaba da gangar Jikin shi ta amsa har wani shaking yakeyi a kife, filon shi ya daga tareda cire wata kyakkyawar brah ya matse ta gam tareda dorawa akan kirjin shi, kamar Wanda ya rungume mace akirjin shi haka ya koma cusa fuskar shi aciki, ya dauki lokaci kadan kafin yasamun saituwar Al amura, numfashi ya fesar tareda goge gumin goshin shi, ya daga bra din ya kalla tareda yin murmushi, tanks wife. Jikin shi ya kalla ganin y'anda yayi kaca kaca yasa ya mike yana cewa " she is the course. Wato wannan bra din tun ranar da yaga Mami ta siya musu yaje store ya nemi same size ya siya sunkai dozen goma ya Ajiye a waldrp din shi guda daya kuwa abokiyar Rayuwar shi ce kullum tana tareda shi the more ya kalle ta the more yaji wani irin urge na son kasan cewa da ita, wanka yakeyi yana ayyana abubuwa da dama Idan Allah ya mallaka mai ita,
Dariya yayi tareda cewa " Wannan yarinyar miskila ce taji nayi confessing how much I love her amma ta nuna min kamar batasan komai ba, " ok I will show you practically. Kamar irin wanda yasameta ya fada mata din nan. Koda yayi wankan tsarki ya dauro towel Jikin shi na zubarda ruwa Idan ka kalleshi dole ka kuma Kallon shi, Nazir Namiji ne mai suna namiji wanda ya Amma suna namiji, basuda jibi da fulani Amma Idan kaga zuri'ar su zaka dauka sudin fulani ne musamman ma shi ga fuskar shi dake yawan tara kasunba don dai yana askewa, kirar Jikin shi kuwa masha Allah don haka yake ruda y'an mata a duk inda ya shiga tundaga gida har wajen aiki yana samun farmaki.

Kai tsaye ya nufi mirror tareda daukar turare yafara fesawa a armpit dinshi kafin ya zare towel din kai tsaye ya fara goge Y'ar sumar dake kanshi dake nan kamar ta y'an China tana sheki baka wuluk.
"Oh my god baby you are more than sexy I swear. Saurin juyowa yayi batareda ya shirya ba towel din hannun shi ya fadi kasa, because ta mugun shammatar shi, kafin ma yayi wani abu harta iso gaban shi tareda fadawa kirjin shi ta saka mai kuka. "Oh oh oh my god NAZ please loves me I beg of you. Cikin zafin nama ya fincike ta a Jikin shi tareda dukawa ya dauki towel dinshi daya fadi yana dagowa hannun ta na kan machine gun dinshi dake nan kyam tun dazu bawai ta rusuna ba, wata irin cafka takai mata dayasa bai san lokacin da ya zabga mata mariba saida ta kife, tuni jijiyoyin Jikin shi sun mike saboda fitina. " how dare you? , uban waye yace ki shigomin apartment? Look zan iya kashe ki inkashe banza Idan kina kawomin haukar ki anan banza karya, am not that cheap da zan nitsa my precious body a Jikin ki kina shaddar kasuwa, look at you the way you pix atarch in your head and all this nasty and disgusting things, wa zaice ke Y'ar musulmai ce a haka look you no what? You are smelling like garbage please out. Hawaye ne a fuskar ta kamar famfo " don Allah kadaina yimin irin wannan wulakancin Naz I really love you karkace ina sha'awar Kane I can change for you I promise am willing to change only because of you please.
" oh bazaki canja ba saboda Allah sai saboda ni? Aikin banza zakiyi kenan domin nafada miki not today kullum ina kara gaya miki ni ba akasuwa nake ba am already sold out,kije ki nemi dai dai dake. "Haba NAZ karkayi min haka mana don girman Allah ka ceci Rayuwata kasoni, niko bazaka Aure ni ba don Allah ka yarda muyi Rayuwa tare na kwadai ta dakai wallahi zan iya yin komai saboda kai, look meye banda shi a Jikin mace na hada komai da namiji keso diri wallahi ka yarda yau inbaka kulawa zakaji dadi sosai. Tafara kwabe kayan Jikin ta yana tsaye kamar gunki saida ta gama tsab ya tsuguna ya kwashe kayan nata da ita ya watsa waje ya rufe gidan shi yana tsaki, kallon kanshi yayi dakyau yaga duk wani feeling nashi ma ya kwanta saboda ita, shi mutum ne mai tsananin kishi don haka bazai taba iya hada jiki da karuwa ba, yagode wa Allah da irin rayuwar shi badon haka ba halin da yake ciki zai iya bin matan banza.

Ina labarin Fahad?
Ai tunda mahaifin shi yaje mai da labarin ya bar kasar yayi Dubai domin can cadowa Amaryar shi kaya na kece raini bazai dawo ba sai yaji ansa rana yazo ya gayawa wannan D'an rainin Hankalin yayan ta magana yana nan yana jiran karon su Sai ya narka mai rashin mutunci.

Ita kuwa Amarya Farida andage sai shiri ake da rawar kai yanzu ma zaune take tana duba posting nashi akan zancen Auren shi soon,taga y'anda ake mai likes da Addu'oi tuni taji kanta kamar yayi bindiga saboda jin dadi sai dai matsalar ta guda daya ce Idan tayi mai magana baya amsata har yanzu, kallon Momy tayi dake zaban furniture's online tace " Momy har yanzu Yaki ya kulani kinga msges nayi har nagaji. Ajiye wayar tayi tareda cewa " ke bansan wutar ciki tunda manya sunsa baki meye naki na damuwa ki jira adaura lokacin zaki kwashi romon Soyayya har ki samu ciki ki haifo mana jikokin gidan gwamnati. Suka tafa kamar kawaye Sadiya na gefe ta zabga tagumi kamar tayi kuka tace " ni kuma fa Momy? Kina kallo kinki ki taimake ni kisa baki Abdul Yaki zuwa tunda nayi mai zancen turowa gashi ko dazu su Abba sun kuma yimin magana, gashi Momy kin zagi yaya NAZ da mun dai dai ta nima in shige daga ciki wallahi Farida tayi Aure tabar ni zansha surutun jama'a dana kawaye zasuyi min dariya don nice babba. "Haba sister kiyi hakuri koda bai turo ba Momy zatasa baki ku dai dai ta da yaya Nazir. Nimrah ta shigo tasame su zaune suna tattaunawa ta zauna tareda cewa " Aunty farida banga mijin nakiba haryanzu inganshi a hoto mana.
Momy ce ta rufeta da fada " yazaki sanshi kina can cikin makiyana kintare banza mai halin Y'ar kishiya. "Kai Momy kyaleta can, barta Tagani taje ta gaya musu ai ba abun dariya bane mijin nawa na nunawa sa'a dole ma suji bakin ciki. Hoton shi ta haska mata tareda wani yatsina " idanun Nimrah a waje ta nuna hoton tareda cewa dama Fahad ne da gaske D'an gidan deputy govnor ya biyomu?...... 🖊


😂😂😂😂



*Matar Soja*

🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻



*WRITTEN BY FENERH*




Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb.



Free page


Page 8⃣


.........."Ke me kikace? " Eh wallahi shine Momy ranar ya biyomu yana son Amrah Yaya NAZ ya koreshi". Tuni cikin su ya duri ruwa Momy ita kuwa imagining yaushe har suka hadu da Aunty Farida suka dai dai ta?. "Wai yaushe kuka hadu kuka dai dai ta ne Aunty? Janyo kunnen ta Momy tayi cikin bacin rai, " jinan, wallahi wannan maganar ta mutu daga nan, Idan naji kin baiwa wani labari ban yafe miki ba. Duk sun shiga gashi saboda tashin hankali, FARIDA ta kalli momy kamar zatayi kuka, Tace " Momy yanzu yazanyi da wannan Abin kunyar don Allah? "Ai abun kunya nike cikin shi ba keba Y'ar nan, ai banga ta zama ba yanzu zan bazama, ai Auren nan Idan ba a daurashi ba basuna na Saratu ba. Kallon ta Nimrah tayi cike da tsoro Tace " Momy don girman Allah ki fadawa Abba a gyara Al amarin nan kafin komai ya kwabe kinga dai Aure ne ba wasan kwai kwayo.... " fita don tsohuwar ubanki kafin in karyaki in karya banza, shegiyar yarinya mai halin Y'ar kishiya, kuma inji zancen nan wallahi sai na tsine miki, banza wadda bata kishin y'an uwan ta. Tashi tayi sum sum kafin tasha Mari na Uku domin yanzu tasha na biyu, tana share hawaye ta fita batada yanda zatayi haka ta ja bakinta tayi shiru.

Haka sukaci gaba da shirye shiryen su, ba ango ba labarin shi, domin tuni su Momy sun shiga sun fita wurin boka, yakuma yi musu Alkawarin aure zai dauru Amma zaman akwai matsala don haka ana gama daura Aure su dawo akuma hada musu sihirin da zasu bawa ango yaci ya manta da zancen Amrah. Nimrah nata ido domin bata isa ba tayi magana, sun dage sai shiri suma sukeyi Har Amrah da bata san wainar da ake toyawa ba. Momy kuwa sai habaici take sake intaga su Ummi da Mami " Ayyiriri ya'ya na masu farin jini Alhamdulillah. Sukuwa ko ajikin su basuda lokacin shirmen ta.
Sadiya dai tana cikin damuwa domin Angon da take sa rai ya fasa tunda yazo yace zai turo manya ba Wani bayani har an tsaida ranar na FARIDA,
Haka Momy ta kuma bazama kudi harda zinarin ta ta kad'ar saboda biyan bukatar ta tace zata maida ukunsu in Y'ar ta ta Auri Fahad. Har bikin Farida ya matso ba labarin na Sadiya sai kuka takeyi Momy na tausar ta, Hajjo ta fara fada tareda baiwa su Abba Umarni Idan bata fito da miji ba har ranar Auren Y'ar Uwar ta ku hadata koda da yaran shagon kune, don wannan Iya shegen Saratu ya isheni ku hadasu duk ku tura dakin miji, muji da y'an baya kuma. Ganin Hajjo da gaske take yasa dole ta sauke kai, Haka ta samu Hajjo hardaki cikin kwantar da kai tace "Hajjo nazo wajen ki kan zancen Sadiya naga duk kin isa damu da ya'yan mu, don haka me zai hana a hada Sadiya da Naziru a wuce wurin tunda har yanzu bai tsayar da mataba. Hajjo ta kare mata. Kallo kafin tace " toh Shine dalilin zuwan min kamar kazar munafukai? Toh tashi kitafi shawarar ki bata karbu ba, da kikace wai na isa daku a gidan Ubanwa na isa dake Saratu? Nadai isa da matan da sukasan mutunci na a gidan nan wainda inna fada ta zauna bake ba, kidai je ki ji da wanda zakiyi dana sani yanzu, ace yaro daga turowa bai zoba bare mu yaganmu mu ganshi, kin dage kin cije ke za ayi miki bakin ciki, toh Ayi mugani in tusa na hura wuta, kwadayi ko? Toh muje zuwa, sannan sunan Naziru ya fita a bakinki wallahi don banson ji, tashi kibarmin gida, inba neman magana ba inake ina Naziru kina surukar D'an gidan gwamna ai kijira itama zata samu D'an gidan shugaban kasa. Tura baki tayi tareda mikewa tace " ai ni nasan an tsane ni an tsani ya'ya na don haka sau biyu ina zancen hada Auren kina ki, bayan ma shi nazirun taimaka mai Zanyi inbashi budurwar yarinya, yaro shekara talatin da takwas ya tasarwa Arba'in ba mace Hankalin shi kwance, Hmm kudai bincika wallahi yana nan tareda matan bariki don ko walimar da yayi wata k'an ka'rarriya ta biyoshi har cikin gidan nan. Tana gama fada tayi waje, Hajjo tayi shiru kadan tana nazarin kalmar ta ta karshe, fitowa Amrah tayi daga kuryar daki domin tanajin Momy, abinka da mai jira ta zauna tareda cewa " gaskiya Hajjo da kin yarda wallahi da gaske Momy keyi wata Y'ar duniya ta biyoshi har nan tare ma mukaje da ita a mota.hajjo tace " toh da gaske ne? " eh mana Hajjo wallahi Yaya NAZ D'an iska ne harda hotunan banza y'an mata ke turomai a waya. Kallon ta takeyi kamar tana tuhumar ta kafin ta kada kai " yanzu me yasa kike fadamin haka? " Wallahi Hajjo ba sharri, nikam na tsani Yaya NAZ saboda baida hali ko kadan. Ajiyar zuciya ta sauke tace jeki abunki.
Ta tafi tana dariya a dole yau itama tayi bajinta tafadawa hajjo halayen shi marasa kyau ko banza tasan zata fadawa Abba ya tsawata mai.

***************
Bayan kwana biyu ya shigo garin Sokoto, domin shirin biki, lokacin sunfita saloon dukan su, da sashen Hajjo yafara kamar yasan tana jiran shi, da sallama ya shiga yana buga kamshi cikin wata narkakkiyar shadda sky blue kamar wani sabon ango, idan ka kalle shi dole ka kara kallon shi,
Zama yayi gab da ita tareda cewa " aa uwar gida ya da hade min fuska daga gani na? Juyowa tayi tareda zabga mai mugun kallo tace " matsa min kafin in mareka. " tofa me kuma nayi daga zuwa na?
Kallon shi tayi cikin bacin rai tafara fada.

Please Login or Register in order to submit comment