Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya tareda rike rigar dake d'an jan kasa gudun karta fadi, takalmin ta mai tudun dunduniya ne sosai, tayi matukar yin kyau kamar ka sace ta, Jakarta a gefen kafadar ta too mach da takalmin ta, Farha tace " toh mu yanzu ya zamu tafi ba mota? Kafin ta rufe baki wata motar taja ta tsaya dalleliya baka wuluk kirar Mercedes, baka ganin Wanda ke ciki saida aka dauki lokaci kadan gefen mai zaman banza aka fara budewa wata tsaleliyar kafa mai dauke da chain na gwal mai masifar kyau ta fara sauka kasa, gata sanye da bakin takalmi mai tsinin gaske, daga Farha har Nimrah zuwa Amrah uwar gayyar sun zuba ido domin ganin wacece wannan... Numfashin su kusan tsinkewa yayi lokacin da aka bude gefen driver Ya NAZIR ya fito sanye cikin ceremonial dress nasu na Air force, yayi masifar haduwa kanshi yaji askin gayu yana sheki, saurin dauke kanta tayi akan Kallon su ta d'an kauce kadan daga wajen, tabar su Nimrah, yi yayi kamar bai gansu ba, ya kalli gefen budurwar " wait for me here. Marai raicewa tayi tareda zagayo wa wurin shi kamar zata rungume shi " please NAZ let me great your family once tunda nazo har ciki please. " who are you by the way Da zaki shiga ki gaida family na? Uban waye yace ma kizo nan garin? Wait here or you leave ok. Yayi gaba cikin sauri, wani irin murmushin keta su Farha suka kunshe tareda cewa cikin rad'a, "mayya ai sai kijira. "Ku zo mu fita mana me muke jira a nan? Amrah tafada cikin haushi, Saurin juyowa tayi ta
Kalle su cikin jin haushin yayan su ta daka musu tsawa " ku bakuda manners ne kuna kallon mutum baku iya gaisuwa ba?.
Kamar jiran ta Amrah keyi tayi carab, " Manners din ne yasa kika ganmu tsaye a cikin gidan Uban mu ba gidan wani Saurayi ba. "Hhhhhhh. Su Nimrah suka sanya mata dariya, har zata bude baki tayi magana taji muryar shi cikin fada, " kun haukace ne kuke wa mutane dariya kamar wasu zararru?. "Badole ba tunda basuda tarbiya suna kallon cikin idanu na suna min rashin kunya sai na koyawa kana nan kwa... " eh hey shut up. Ya daga mata hannu, " listing this is my house and wainnan yaran da zaki Kira da kwa'ri are my blood sisters, so mind your tongue ok.
Kanta ta dukar tareda Kallon shi cikin rage murya, "am sorry NAZ bansan kannin ka bane wallahi. "Now you no, Farha come and sit here ku kuma ku shiga baya, and you if you are going ki shiga bayan tareda su. Yafada yana mai bude gaban ya shige yabar ta cikin bakin ciki,
Da sauri Farha ta shige gaba ta kame, Amrah da Nimrah suma suka shige bayan kodon su cusa mata haushi yasa Amrah ta shige. , a tuna nin su bazata shiga ba, amma ta shige gefe tana famar mannewa da Jikin kofar mota karsu tabata, da gangan Nimrah ta rike bude kafafu tana tabota, tunda suka dauki hanya Amrah batace Uffan ba, wayar ta take dannawa tareda yin murmushi ganin y'anda Nimrah ta takuri rayuwar wannan budurwar a cikin mota saboda iskanci,
Don haka fuskar ta shar har murmushin ta na bayyana zaka dauka wani Abu ne ya dauke mata hankali a wayar. Wata uwar birki yaci saida wayar ta fadi a hannun ta, tayi saurin dagowa saboda ganin dalilin cin wannan burkin, taga ya bude motar ya fita, Ashe an iso ne, fitowa sukayi dukan su suka hade suna dariya ciki ciki, ita kuwa mayyar tuni ta matsa kusa dashi, inda tuni abokan shi suka rufe shi rub, ko kunya bataji tanata famar kad'ifiri suna Y'ar fata saboda uban gayyar ma ko Kallon bata isheshi ba, babban abokin shi ne Kb yace " Fauxi tanks for coming. Cikin wani iyayi wai ita wayayya tace " no problem, bayan ma abokin ka yana y'an kwana ni.
Saurin juyowa yayi tareda watsa mata banzan kallo " go inside if you want please allow me am busy. Wucewa tayi sum sum ba kunya, kb da sauran suka fara yimai tsiya " wai kai me kake jira da bazakayi wuf da Fauxi ba beb din tayi kabada kai gata tana matukar kaunar ka gashi ta biyoka duk da irin wulakancin da kake mata. "Karkaja inzage ka anan fa waye yace kuzo da ita Idan bakwaso inyi mata wulakanci? , now am busy muje natara jama'a let start the program. Tuni su Amrah sun kama kansu sun shige cikin dakin taron inda suka samu iyayen kanzagi su Aunty FARIDA suna ta rawar kafa da kai da komo anci uwar kwalliya, y'an mata ne gabas da yamma kudu da Arewa sai abokan shi sojojo ba manya a wurin saboda walima ce ya hada domin farin cikin zaman shi cikakken matukin jirgin sama.

Tunda ta shiga wurin take zabga tsaki domin karar sautin da ke tashi a ciki kamar ya kashe kunnen mutum, don haka duk ta takura, sukuwa su Farha rawar su sukeyi daga zaune Idan sukaji abun ya musu sugar su mike su taba su zauna, ga Abinci serve your self sai abinda kakeso tundaga namu na gida har na kasar waje, Nimrah saboda iskanci ta anso yakai kala biyar Idan ta D'an dana bai mata ba ta koma ta anso wani,
Kb ne ya matso wurin su sanye shima cikin ceremonial dress dinshi,

"Y'an mata adon gari sannun ku fa. Cikin fara'a Nimrah tace yauwa kaima sannu. Farha ta gaishe shi, Kafin Amrah cikin sanyin jiki tace Sannu. "Nayi mamakin ban san kannin nawa ba duk da am your brothers best friend, any way myself Kabir Al hassan, and you? Yafada yana kallon Amrah dake kallon gefen su Aunty Sadiya masu kwasar rawa harda bada step suda kawayen su, Farha ta fada mai sunayen su, na gaskiya, ta nuna mai Nimrah she is Hajara and that's our grandmother name (Nimrah) and me Khadija (Farha) and Amrah Zainab (Amrah) because taci sunan mahaifiyar mu ne. Cikin sauri yace " Wow Zainab I love your name, can I have your number please?.daga idanun ta tayi a karon farko ta kalle shi, he is young and handsome like Yaya Nazir but yafi yaya NAZIR fara'a da kirki, "No you can't. Ya bashi amsa cikin jin haushi, gaba dayan su suka zuba mai ido yana tsaye hannun shi cikin Aljuhun wandon shi duk ya cika wurin saboda kwarjini, " oh my goodness NAZ allow me to enjoy my damned life, why are you interfering?. "Don't cross your line too if you don't want me to interfere, "let's go friends are waiting. Mugun kallo ya watsa mai, "ka jira in karbi number first. Ya juya " tell me please. Yafada cikin wani irin sanyi. Duk ta k'agara subar wurin don haka ta dago wayar da niyyar bashi Yasaka nashi domin ya basu wuri. Yaya Nazir ya fisge wayar har yana hadawa da hannun ta. " muje zanbaka Number. Yayi gaba tareda tura wayar cikin pocket din wandon shi. "Like really? Yafada yana bin bayan shi tareda mita. Saida suka bar wurin taja numfashi domin kasance warshi a wurin ba karamin bugun zuciya ya janyo mata ba dauriya kawai takeyi, wani uban numfashi Nimrah ta fesar tareda cewa " my god Yaya Nazir karshe ne wallahi kunji wani irin cents mai raba numfashi da gangar jiki kai duk macen da ta sameshi ta more a rayuwar ta wallahi. Wani irin kallo Amrah take binta dashi, Harara Farha ta watsa mata, " oh inace Auren shi kikeson yi me yafaru kika canja? " ke aiko su Aunty Sadiya hauka sukeyi bareni, kina kallon wayewa da haduwa na Fauxin can yana wulakanta ta bare mu Hmm duk suyi sugama. "Ni ya tafimin da waya haka kawai ko me zaiyi da ita?. "Zaki ansa query Idan kuka hadu kinsan kosu Aunty FARIDA basa samari bare mu y'an secondary. "Ni saurayi nayi? Abokin shi ne kuma number kawai ya tanbaya zanbashi. " you are mad Amrah, duk namijin da zai nemi number ki Akwai magana kenan ba haka kawai bane. Rungume ta Nimrah tayi " yeeh baby Kinyi kasuwa kinga y'anda yake wani kallon ki kamar zai cinyeki. Farha tace " wallahi Kinyi sa'a Idan kika samu namiji like yaya kabir inajin labarin shi tun tasowar mu wurin Mami Aminin yaya ne sosai, ke kin zama kifin rijiya shiyasa bakisan komai ba
"Meye gami na dashi da zandamu insan komai nashi?. Daure fuska Farha tayi tareda cewa " Mami ce ta haifeshi karki manta Uwar mu daya uban mu daya dashi, naga kamar kina mantawa saikiyi ta fadar maganar banza akanshi agabana. Shiru tayi batareda ta kuma cewa komai ba saboda batada abin cewa, jawabin da ake na bude taron tareda gabatarwa ya ja hankalin su, Wanda kb ne akan gaba, kab abokanshi sunci ceremonial dress su kawai kake hangowa sai wakar su ta sojoji dake tashi a hankali saboda an rage sauti,

"Alhamdulillah da Allah ya kawomu wannan lokacin na farin ciki, domin wannan abun farin cikine da yazama dole mu nuna murnar mu da godiya ga Allah S.W.A da kai Amini na d'an uwana wannan matsayi tareda cikawar burin shi, Alhamdulillah, muna rokon Allah ya tsare mana shi tareda daukaka shi ya kuma kaimu ranar Auren shi Amen. Ya bada takaitaccen tarihin shi Wanda bana ra'ayin ji don haka sai da naji sautin muryar da ko bakaso sai ka kalli mai ita,
Hole din yayi tsit, "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah, ina godiya sosai ga iyayena y'an uwana dama abokai na masu yimana Addu'a dare da rana akan cigaban mu, nagode wa Allah da ya cikamin burina har nakawo wannan matsayi, Saura babban matsayin Insha Allahu Wanda abokina Yafada Wanda yakusa nan bada jimawa ba. Tafi suka dauka da sowa domin wannan ne karon farko dayayi responding akan maganar Auren, tunda yafara magana kowa hankalin shi yakoma kanshi, bai tsawaita maganar ba Amma y'anda yake maganar cikin jan kalmomin dole ya dauki hankalin jama'a, harda Amrah kuri tayi tana Kallon labban shi pink kamar mai shafa janbaki, zata iya cewa yafi duk y'an dakinsu kyau ko tace duk ma familyn su, yau ne karo na farko data kare mai kallo, tun tasowar su tsoron bin hanyar shi take bare kuma harta tsaya kallon shi saboda kwarjinin shi da rashin sakewa yara, batasan lokacin da ya gama jawabin shiba sai tsintar shi tayi tsakiyar abokai suna chashewa kamar wainda rawar ce sana'ar su ba aikin soja ba, ba namijin da ya iya bada step irin nashi rawar ta mugun burgeta cikin wakar buga dake trending. Saida ta more idonta sannan tayi tsaki tareda cewa "bidi'a dai ba walima ba, su Nimrah tuni suna gaba suna daukar hotuna a wayoyin su, Kb ne ya matso wurin ta, " Hey ke kadai anan? Kanta ta dukar tareda Gyada wa Alamar eh, " you are too cool Amrah right? " Uhm ko kace Zainab my real name. "Good please ina so muyi serious magana, when zamu hadu a gida? " ba a barin mu magana da maza. "Hhhhh how old are you Amrah? Dago manyan idanun ta tayi, " Am eighteen. "Or no wonder, but kin isa Aure a kauyuka even anan ma tsakiyar sokoto why not giving me a chance my sister, zan gabatar da kaina a gaban hajjo or Abba, ba wasa nakeyi ba koda yayanku ya hanani amma gaskiya ban hakura ba...... "You are going to get it from me Kabir, I told you to respect yourself kaki kagane please stop this nonsense ok. Buga table yayi cikin jin haushi har saida ta tsorata tareda mikewa tabar wurin cikin Sauri, " meye nufinka ne Nazir don't you trust me? Am serious wallahi sonta nake da Aure bazan taba kauce hanya ba, she is like a sister to me don't forget Akwai Amana da Y'ar da a tsakanin mu abokina. " oh come on, meyasa bazaka fahimta bane, ok let keep it this way, bazan baka kanwata ba you are not allowed to talk to her again that's my last warning.
"Thank god she is your sister not your daughter and you have elders so bazaka hanani son zuciya taba, "kabir ka daina kafin mu samu matsala dakai akan wannan zancen. Tuni ran kabir ya baci hakama Nazir din don haka kamal kanin shi ya Kira yana matsowa yace "Gani Yaya. " ka mayarda yaran nan gida dukansu right now.Umarni yabi ya tankadasu duka harsu Sadiya suna kunbura suna karawa haka ya lodasu a mota zuwa gida......... 🖊

"masu bukatar karanta NAMIJIN ZUMA da NAMIJIN DUNIYA zai biya 1500 duka biyun.


*Matar Soja*
🌻🌻NAMIJIN DUNIYA🌻🌻


*WRITTEN BY FENERH*


https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Join our free page group

Ga masu bukatar biyan wannan littafi zasu turo kudin su ta account number na 3201188487 Nafisa hassan sani first bank or 7304736012 fcmb.

Free page


Page 3⃣

......... Ita ke gaba tayi shiru tana tunanin me zai biyo baya don tasan bazai kyaleta ba yau, don haka motar na tsayawa tayi part din Mami don tasan can ne kawai zata tsira. Amma ta sha zagi wajen su Aunty FARIDA, saboda ita aka korosu Sai mita suke suna masifa, kunjawa mutum yana cikin holewar shi banza kawai tun baki tafasa ba zaki kone gari, uban wa yace ki saurare shi ma gashi yanzu ankoro mu, mtsssw. Tun daga hotel har suka tsaya surutun sukeyi har saida ya kamal yace " ya isa haka kar inkuma jin wani zancen ita taja, Idan wata ta kuma magana akai wallahi zanci ubanta.
Dole suka hadiye har saida suka shiga cikin gida part dinsu suka fara gunguni gaban Momy, tace " ai dama ta gaji mugun hali wannan yarinyar haka nan uwarta take sum sum kamar ita tafi kowa bautar Allah da jin tsoron shi. " Momy bafa laifinta bane wannan Yaya kabir din ne.Nimrah Tafada mata y'anda abun yafaru. "Shi din da nakewa dayarku hari, kunsan d'an gidan waye? Toh ku tsaya shiririta ta samu sakarkaru kawai.
"Momy FARIDA tayi maneji dashi ni abarmin Yaya Nazir kawai. "Kut wallahi saidai ke ki dauki Kb kibarmin Yaya NAZ. "Kai banason shirme ko wacce ta samu NAZIR din duk daya Idan bazaku natsuba kuma inbawa Nimrah kuje can ku karata.
Kallon mahaifiyar tasu Nimrah tayi cikeda mamaki domin ta hango son zuciya tsantsa ba kuma zata furta ba kartaci duka dole ta tashi ta tabar musu gidan,

Amrah nacan tana taya Mami aiki tunda suka iso bata tsaya ba domin su Abba nagari, kasancewar su y'an kasuwa basa zama, so duk lokacin da suke gari zaka samu jama'ar gidan sunyi busy, don haka itada Farha sundage suna hada lafiyayyan zobo da yaji Abarba dasu citta yana tashin kamshin cucumber, ko ina kitchen din ya gauraye da kamshin dishes, Mami tace " ku je ku duba kayan da aka siyo muku na school Abunda babu kuyi magana kafin gobe tunda kungama aikin. Toh suka amsa tareda wanke hannu suka nufi dakinta, kayane birjik na y'an makaranta, dai dai da pad audugar mata Sai an hada musu agida komai basa nema a makaranta, suna cikin dubawa Nimrah tazo suka raba komai dai dai kowa ya kwashe nashi ya zuba a katuwar troly dinshi.

Ya wannan family yakene??

Bari mu leka muji kafin mucigaba,
Dafarko dai Hajjo wadda take uwa agaresu su , Asalin su y'an yabo ne cikin local government din sokoto daga can suka taso itada margayi mijinta uban ya'yan ta Malam Alu, sunsha gwagwar mayar Rayuwa da ya'yan su harsuka girma, Y'ar Autar ta Khadija wadda Farha taci sunanta, babban su shine Alhaji Isma'il mahaifi ga su NAZIR kamal Sai Ammar Sai Auta Farha, Sai na biyun su Alhaji Mustafa, shine mahaifi ga su Nimrah wadda Sadiya ce babba Sai FARIDA sannan Nimrah mai sunan hajjo, sau Autan mazan mahaifi ga Amrah, Alhaji kabiru, Akwai zumunci sosai a tsakanin wainnan y'an uwan harma da kanwar su mace dake gidan ta, hajjo tayi iya bakin kokarin ta na ganin ba wata baraka, shiyasa bata Y'ar da suka ware ba suna gida daya Wanda kowa, nafarin ciki da hakan, Alhaji Isma'il Abba babba kenan y'anda suke kiran shi, shine mai zartar da duk wani hukunci a cikin wannan zuri'ar ya rike girman shi sosai baya taba banbanta ya'yan shi da sauran, don haka sauran kannin shi ma basu san wahalar komai ba ya dauke musu, hatta da shagon da suke kasuwanci shine ya assasa shi tun yana karami har yazama tanga meme, yanzu dai atakaice shagunan su sunkai goma a cikin garin sokoto, Wanda suka sakawa ALU YABO & SONS wanda sunkai shaharar da basa ko zama saidai yawon kasashe shigo da kayayayyaki, matayen su kuwa, Mami wadda itace mahaifiyar su NAZIR kuma babba, ita ma Sai son barka dattijuwa ce mai karamci da sanin yakama ta, ta gefen ta tsakiyar ce dai sai a hankali Akwai selfishness da greed ness tanada matukar son kanta, don haka sukan kiyaye mata sosai gudun matsala, bangaren Ummi kuwa mahaifiya ga Amrah da Imran Auta dagasu ba kari a gidan wainda dakyar ma ta samesu, saida ta kwashe shekara goma harta fitarda rai, don haka itace ta raini Su NAZIR shiyasa sukayi matukar jituwa dashi zai iya shiga part dinta sau goma bai shiga na Mami ba domin yakan gaya mata komai na rayuwar shi Idan ta kama, Momy abun na mugun bata mata rai musamman yanzu data keda manufa, kunji takaitaccen tarihin wannan zuri'ar,

Cigaba....

Karfe takwas bayan an idar da sallar magrib, kowa na hallare a katon falon harda Oga NAZIR yana gefen iyayen nasu kamar abokin su Sai hira sukeyi dasu, su Ummi ma na nasu barayin su uku sauran yaran kuwa suna kan dining dake falon suna cin nasu abincin domin su Abba basa hawa dining, cikin natsuwa Abba yace "Maman yara kuzo nan yaran ma in sun kammala su matso, duk taruwa sukayi a katon kilishin, yayi gyaran murya tareda Kallon Ummi yace "Ummin Soja toh ki shirya d'an ki yakusa mallakar iyali ya nuna mana yanzu yana bukatar iyali tunda ya samu natsuwa. Murmushi Mami tayi tareda kawarda kai batace uffan ba saboda kara sai dai Ance labarin zuciya a tanbayi fuska, farin cikin dake bayyana kawai ya isa ya Sanar dakai tayi farin cikin jin maganar, tsulum MOMY tace cikin fara'a "masha Allah toh yaya ai sai a zaba mai tunda ga y'an mata nan a cikin gida...... "Munsani Saratu kuma shima kuma ai ba makaho bane Idan yana ra'ayi ko ina ne zai iya zabo mata. Muryar Hajjo ta dawo dasu bakin falon tana shigowa cikin dingisawa saboda kafafun girma, hannun ta rikeda carbinta da take ja. Zabura Abba yayi tareda cewa "Hajjo kika taso ai da kinkirani. "Kamawa tayi. Tafada tana zama a kujerar su kuma duk suka zube kasa har Su NAZIR, nazo a dai dai, karka damu da zancen Matar Naziru nayi mai mata tuni kuma Insha Allahu zan Sanar daku lokacin da nayi niyyar ya mallaki iyalin. Wani irin kallo yake bin hajjo dashi cikin Alamar karkiyi min haka. Ita kuwa ko Kallon gefen shi batayi ba, fuskar Momy kamar wuta saboda takaici "haba hajjo ai yaci ayi abun nan kawai tunda gamu ga iyayen shi, ga yara tsala tsala kun isa dasu ai daurawa kawai za'ayi. "Saratu. . Abba karami ya buga mata tsawa tareda cewa " karki sake kiyi jayayya da maganar mahaifiya ta,ba ya'yan mu ba ko mu ta isa ta fada magana mubi, a karkashi na kike don haka banson jin bakin ki, bake zaki fada mata Abunda ya dace ba. "Mustafa, ya isa itama tanada right tafada ra'ayin ta akai. "Wallahi yaya batada right koni umarnin ka nake bi itama dole tabi. Tuni taja bakin ta tayi tsit zuciyar ta na k'una,. "Hajjo magana ta kare duk lokacin da kika ga yadace haka za'ayi, kai kuma Naziru ka kara hakuri kaji. Fuskar shi kamar gobara sai harara yake watsawa hajjo, daga nan suka fara wata hirar tashi yayi ya kalli Abba yace "Abba zanje in huta gobe zanje kaduna ana nema na a unit din mu. Bai tsaya jin amsar suba yayi gaba, hajjo tayi murmushi taci gaba da hira da ya'yan ta har kowa ya watse yabar su, su Nimrah kuwa part din Hajjo suka suka wuce tareda zubewa suna jiran dawowar ta tabasu garin kulin da take daka musu in zasu koma, tashi tayi tareda shiga uwar dakin hajjo domin ta kwanta saboda dama nan ne makwancin ta, wannan karon saboda ya NAZ taki zuwa part din kwata kwata, yanzu ma saboda taji yace zai kwanta tashiga sasan, dakin fes fes kamar dakin Amarya saboda tsabta gadon dai da Alamar ankwanta akai saboda duk ya yamutse sai katuwar wayar Android dake fitarda haske Alamar sakonni suna shigowa, batare da tunanin komai ba takwanta tareda daukar wayar taganta bude, a zuciyar ta tana tunanin kotasu Aunty Sadiya ce? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, tayi Saurin furtawa tareda Kallon screen din da kyau ganin irin hotunan dake kai nonuwan mace ne rukutum rukutum abun ba kyan gani, , har zata Ajiye taji zuciyar ta na zugata, tuni tayi scrolling down domin ganin meke faruwa waye keda wannan wayar? fara Kallon chart din " ba reply sai chart din me hotunan data turo, " please me na rasa kake yimin wulakanci look at my boobs zaka huta my NAZ please accept my offer once. Tuni tayi fatali da wayar saboda yanzu ta gane wayar waye, sai dai tana jefawa sai agaban shi yana fitowa daga bathroom din Hajjo dake uwar dakin, wata uwar razana tayi har zata wuntsila,
Wani irin kallo yafara binta dashi up and down, tuni ta gigice ta kidime, dukawa yayi yafara daga wayar ya kalli fuskar yaja Wani wawan tsaki kafin ya ce" who give you permission to touch my things? Cikin kwantar da murya, bata ko gane me yake fada cikin rawar jiki tace "am sorry yaya NAZ bansan wayar ka bace wallahi. Matsawa yayi gab da ita tareda haska mata fuskar wayar cikin d'an daure fuska yace " did you saw this. Dakyar tayi kallo daya tareda kawar da kai tace " ba da gangan bane wa...... " shhhhhh quit kina kallon abinda yafi karfin idanun ki ko tun baki kai ko inaba, who tell you to open it. Shiru kawai tayi domin batada abin cewa nafarko bakin cikin ganin irin wainnan munanan hotunan na biyu Yaya NAZ daya tsare hanya, gaba daya duk girman dakin hajjo yau taga ya matse mata, burin ta kawai ya kauce ta wuce. Maganar Hajjo ta dawo dasu, taja Uwar Ajiyar zuciya tayi waje batareda tagano me hajjon tace ba,

"Kai meye ka tsare yarinya a kuryar daki banson rashin da'a da rashin ta ido.
"Toh ni me nayi Hajjo ina cikin nan tun dazu ina jiranki ke kuma kin ki zuwa. "Ka rainawa hadiza don ubanka, kasan me nake magana akai ai zaka basar to tun ba.... "Hajjo please ya isa haka fadan da zage min iyaye baya sai abinda kikace sukeyi, but Hajjo me kike nufi dani ne wai nafito nafada miki damuwa ta kin share, wallahi Aure na nakeso yanzu bazan iya hakuri ba. Kallon rashin kunyar shi kawai takeyi batasan lokacin da ya zama haka ba, " toh rasai, Idan har bakabi y'anda nakeso ba wallahi sai na shuka maka tsiya a gidan nan don haka bini a hankali.
Saurin matsawa yayi tareda riko hannun ta, "Sorry Hajjo na haba Uwar gidana kinsan ke ta daban ce, ki rage Kishi kawai ki bani Amarya ta please Hajjo. "Innalillahi oh ni zamani yau ina

Please Login or Register in order to submit comment