Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba a cikin blander a markade, sai a zuba garin ridi a ciki ,a zuba madara da zuma ki zuba wa angoki cikin Kofi kisha ya sha..
Wanna hadin yana kara ni'ima, maniyyi yana hana karnin dake fitowa.

HADIN KANUNFARI

karin ni'ima da matso sha'aw Kiji ka kanunfari shi kadai ki rinka sha ki kuma kama ruwa dashi (TSARKI) shi ma wani nau`in' karin ni'ima ne (kanunfari) .

HADIN ZUMA

Karin ni'ima da motso sha'awa Zaki sami zuma mai kyau ki zuba garin habbatussauda da man zaitun ki juye su guri daya sai a dinga sha babban cokali biyu da safe da kuma yamma.

HADIN ZOGALE

( xaburar da mace wajen sha'awa da karin juriya batare da gajiyawa ba)

danyen zogale
madara peak
zuma
kanunfari
Zaki gyara ganyen zogalenki ki wanke ki markada shi sai kitace ki zuba garin kanunfari ki zuba madara ta ruwa, da zuma ki rinka sha ,safe da yamma.

HADIN FUREN ZOGALE

Wannan hadin anso namiji yarinka amfani dashi domin karin ni'ima da kuzari asannan koda yaushe zai bukaci mace kusa dashi).

Huren zogale
Ya'yan zogale
Dabino
Cukwui
A shanya furen zogale da ya'yan zogale a cikin inuwa, sai a hada da dabino a daka a rinka sha da nono,ko madarar peak.
Wannan hadin yana saurin sauko ni'ima

KARYA GADO

Wannan hadin shi ake cewa karya gado..
Zaki wanke farar shinkafarki,sai ki dan soya ta sama-sama ma'ana kada ta soyu kwarai, zaki tafasa ruwa saiki zuba gyadar daki soya kitace ta sai ki shanya idan kin yi dai-dai zaki ga bawon gyadar yana cirewa da kansa kafin ta bushe

Idan tayi sai ki murmusheta ki dake lukui sai ki daka cukwi da dabino, ki ya'yan zogale ki cire kwafar ki cire fatar ki shanya a cikin inuwa idan sun bushe ki hade su da dakakkiyar soyayya shinkafarki da gyadar daki dabino, sai ki rinka sha da madara peak

HADIN GWANDA

Wannan hadin shi ake cewa sa kishiya tagumi idan kuma ke daya ce tofa sai dai a ki rashi mutu ka taba.

kankana
gwanda
dabino
zuma
Za a samu kankana a gyaranta ajika dabino, sai a hade su GU daya a markade su a zuba zuma a ciki, a rinka sha

HADIN NONO RAKUMI

Wannan kuma shi ake kira da hana mai gida hirar dare domin da zarar ya tuna dake tofa sai gida domin irin ni'ima da Allah yayi maku uwar gida.

nonon rakuma
ridi
Zaki iya hada nonon rakuma da garin ridi guri daya ki rinka sha, shi ma yana saukar da ni'ima.

HADIN BAGARUWA

Wannan kuma hadin shi ake cewa
MAI DA TSOHUWA YARINYA
Domin yana sa gaban mace ya tsuke ya matar

Anan so a koda yaushe idan mijinki zai kusance ki ya kasance yaji ki a matse kike , ba a son lokacin da miji yazo zai shiga matarsa aji ya wuce siririf an fison ya shiga a hankali ,domin hakan anfi so mace ta rinka kula da kanta kada ta bar gabanta ya bude

bagaruwa
alif
kanunfari
Zaki samu bagaruwa danya ki dan kona ta, sai ki matse ruwan dake jikinta, kiyi matsi dashi a gabanki, yasamu kamar tsayin (1h) sai ki sanya alif ya kasance shine a matsayi sabulun ki rinka wanke kowane lungu da sauko a cikin gabanki da ruwan dumi zaki amfani

Bayan kin gama saiki samu garwashi sai ki zuba kanunfari a ciki ki tsuguno akai idankin gama sai ki samu miski mai kyau shi ma kiyi matsi dashi

HADIN LEMON TSAMI

Yana hana maniyyi mace karnin kuma yana karawa mace ni'ima sannan mijinki baya tunanin ko shayin tunkarararki

Lemo tsami Ki samu lemon tsami ki yanka shi zaki tanadi ruwan dumi, sai ki sanya wannan lemon ki rinka wanke kowane lungu da sako na cikin gabanki

Wanna hadin yana hana warin da ke fitowa gaban ya'mace yana matse kofar (farji) mace
Wanna hadin yakan sanya mace ta zama yar fata

HADIN MISKI.
bagaruwa
alif
Miski
Ki hade su wuri guda ki dafa, zaki zuba miski a ciki inda ya sha iska,sai ki rinka kama ruwa dashi

HADI NA MUSAMMAN.

man tafarnuwa
man zaitun
zuma
Ana hada su guri daya, sai ki rinka sawa a gabanki yana matse gaban mace

MAI DA TSOHUWA YARINYA.

HADIN ' Y'A'YAN BAGARUWA

ya'yan bagaruwa ta makka
garin baure
Za'a soya ya'yan a hada garin baure adinga sha

HADIN KANKANA

Wannan hadin yana gigita mai gida
kankana
A matse ruwanta, mace zata yi matsi da shi,idan ya samu kamar 10 m sai a wanke ,yana kara ni'ima sosai

Gyaran nono.

Kunun alkama da madara zaki yi shi sau biyu,a rana zaki yai hakan kafin sati biyu a yi yaye da kuma sati biyu bayan yaye.

Gyaran nono

Hulba za'a samu a tafasa ki rinka gasa nono da shi ,sai kuma a shafa man hulba.



'YAR UWA KIN IYA BARIKI???

Ba'ana nufin kitai yawan bariki ba fa ah to SIDIYA bata ce ba
Barika da mijinki akeson kiyita! Ya akeyinta.
Misali! Wlhy baby gefen qugu na ke qaiqayi Dan sosaman, k Kice dubaman kasan breast Dina zafi nakeji, ko baby Dan sosa man jikina kicire kayan. Wlhy inbaki iyata ba kinbaro mata.

Zaki cire Riga ko braziya, zakice honey Dan taimakaman incire rigarnan cikin murya tattausa. B kamar gardi ba. Baban wance cire man, ya cire maki me? ahakan? Inzaiyi aski kibi kewaye kimasa dakanki, duk sadda yai dakansa harkukan qarya kiyi masa kinuna meyasa zaiyi gaki. Bariki ta fannin Mu amala kenan.


Kin iya bariki? In kin iya ya take? Ya akeyinta? Shin ko kin iya soyaiya? Idan har kin Santa kuma kin iya ta, ya akeyinta?
Anya kin iya cire kunya lokacin da kike tare da mijinki, inkin iya Yaya kikeyinta?
Anya kin iya salo na magana masu daukar hankali, masu susuta Wanda yajisu, inkin iya awane yanayi kikeyinta?


Sai maganar soyaiya! Da anyi magana muce mun iya soyaiya🤨
Kin iya soyaiya Amman bazaki iya rungume mijinki ba kimasa kiss inzai fita, koda acikin daki ne ki koya masa yi maki kiss da hug kafin ya fita! Kin iya soyaiya Amman bazaki iya furta wa mijinki kalmar kinasonsa ba, kina jira saiya fara ce maki sannan, anya ke mace ce?

Idan har tunaninki, ki wanke masa kaya ki goge masa takalma ki rakashi shine soyaiya to kina kashe kanki daga zaune ne! Ki aje kunya kiyi soyaiya da mijinki, wadda tafiki daraja tayi soyaiya da mijinta ba kunya, Wanda yafi mijinki daraja Wanda sanadiyyarsa kike cikin duniya yayi soyaiya da matarsa ba kunya! To ke acikin mutane wacece dabazakiyi ba...

Sai maganar cire kunya! Ashe kinada kunya? harkika yarda sex ya shiga tsakaninki da minjinki. Ashe kina da kunya? Kike hada makwanci dashi, bantinanin kina da ita!
To tunda har Kika iya hakan, Ashe kuwa babu sauran kunya tsakaninki dashi! Wlhy mata musan me mukeyi! Cire kunya na daya daga cikin abunda ke qarawa mijinki kaunarki, kusantarki, sha awarki, mararinki! Idan kau har Kika tsaya kunya zakiga result dinki ahannu wlhy.


Sai maganar salon magana hajiyata kibar bacci yanxu ko yarinya ta iya salon magana balle ke!

Bazaki iya cewa mijinki kina sha awarsa sbda girman, wai saikiji tana yaza ai ince masa haka, kiji wadda tarako mata kamar ba mace ba

Sai aukin shan maganin mata! Aisu zasu qara mata qeemah! Mashiriri ciya ki iya wadannan ko babu maganin zaki tsira da mutuncinki



kada Kiyi sake Kiyi sakaci da mijinki har Wata ta kwance miki shi, saboda haka ki kula sosai, sannan kuma ki rike abin ki da kyau, saboda Galibi sakacin mu na Mata shi yake sa namiji sha'awar Kara aure, ko kuma ya fada Neman matan banza, duk ire-iren wadannan sakaci ke jawosu, don haka kar ki kuskura ki sake da wadannan abubuwa:

abinci mai dadi.
tsaftar gida, jikinki da dakin kwanciyarku.
tarairayar miji kamar karamin yaro.
dauke masa nauyinsa, ( wato ki bashi hadin Kai a duk lokacin daya bukace yin kwanciyar aure dake )

Ki kuma dinga amfani da kayan Kara ni'ima jiki.
rake.
gwanda.
kankana.
kunun aya.
farfesun kaza/kifi.

Ki dinga shan

Zuma
Kanunfari
Sannan kuma ki sangarta shi, yadda duk Inda yaje, zai dinga tunaninki, ya kasa sukuni har sai ya dawo gida tukun sannan zai ji dad'i.



Se zancen
YAR AIKI ...

wato yan'uwa Mata abinda yasa nace a dinga Lura, to ba wani Abu bane za'a Lura dashi ba daya wuce mai aikinki da kawayanki, musamman mai aikinki da zaku zauna gida daya da ita, tunda ita kawa sai lokaci-lokacin take zuwa.

Amma dukansu abin Lura ne sosai, saboda haka a dinga taka tsan-tsan!

Idan ba haka ba kuma, to ko dai a aure miki miji, ko kuma su dinga fasikanci, ke kuma ki na nan kin Saki baki, ki na ta kwashe sirrin ki ga kawa.

Ko mai aikinki, ba ki san abinda yake faruwa ba, don haka a Lura sosai a kuma yi da gaske da su.
Don gudun abinda zai Je ya komo, Wanda bama fata.




SIRRIN GYARAN JIKI

gyara fuska 1

・madara.
・kwai.
・fulawa.
ki samu madarar ki garinki Rabin cokali, kwai kwanduwa daya, fulawa Rabin cokali, sai ki hade ki kwaba da ruwa ki shafawa fuskarki da dare in Zaki kwanta sai ki wanke da safe yana sa kyau fuska.

maginin kurajen fuska 2

▾ kurkur.
▾ Zuma.
▾ kwai.
▾ aloevera (ki bareta ruwan ake so)

Ki kwaba ki shafa da dare da safe, ki wanke ki ga yadda fuskarki zata yi kyau gami da sheki.

・HADIN SABULUN GYARAN FATA ・
❊ sabulu Ghana.
❊ sabulu salo.
❊ dudu osun.
❊ kurkur gari.
❊ Zuma.
❊ madarar turare
❊ lalle gari.
❊ nescafe babba cokali.
・ madara gari

Ki hade su wuri daya, ki dake su,ki rinka dauka kina wanka, kinga yadda jikinki zai yi laushi.

SABULUN GYARAN JIKI

・dudu osun.
・black soap.
・madara gari.
・lalle.
・kurkur.
・man zaitun.
・turaren na jiki.
・kwal.

Ki hade su ki cuccurasu, ki rinka wanke fatar jikinki, zata sauya jikinki ya yi kyau.

. WANKE GASHI

・ganyen ruman.
・ganyen magarya.
・ganyen aloevera.

ki tafassa su ,in sun huce ki tace ruwan ki sa kwai daya sai Zuma cokali uku, ki wanke Kai dasu yana saurin zubo da gashin.


'Yar uwa ko kinsan cewa

GANYEN GAMJI
ki jika shi, ki rinka Kama ruwa da ruwan har tsawon wani lokacin, ke da kanki zakiji kin canza, kin hade,

sirrin na biyu 2

MAN ZAITUN

ki rinka lakatashi a gabanki, kina kuma shan cokali uku.

sirrin na uku 3

MISKI MAI KYAU

bayan jini ya dauke miki ki lakatashi a gabanki Zaki iya lakatashi ko da ba kya cikin jini ba Amma ba kullum ba.

KARIN BAYANI

wani Karin bayani da Zan yi a nan , shine yan'uwa Mata muyi da gaske mu kame mazajen mu Daga shiga gurbatacciyar rayuwa.

kuma duk Wata mai matsala a gidan auranta da ta samu wannan post to insha Allah zata samu hanyar warware matsala ta.

KIRA GARE KI

Kira na gareku yan'uwa don Allah Ku aje makahon tunaninku, mu dauki mai Ido, mu ajiye wuta, mu dauki aljanna, mu aje duhun Kai, mu dau haske don ta bayyana garemu.
Mu yi watsi da aikin jahilci, mu dauki ilimi da aiki dashi.

iyaye a dinga koyawa Yara.
abinci
kwalliya
tarba miji
Kada kice ai yarinya zata sani Inda taje gidan mijinta.
Wanna yasa aure yake yawan mutuwa a cikin al'umma mu a dinga Neman ilimi aure da zamantakewar rayuwa.
[9/16, 12:23 PM] Sadiya Sidi Said: Mallakar miji
1⃣
1. kamar yadda jarumta ke kan gaba a fagen yaki haka zalika gidan aure hakurine kan gaba har yanzu babu macen da take kalubalan miji karshe tayi nasara a rayuwarta mata masu kima da daraja zaka samu hakuri suka yi suka manta da ne man 'yancinsu suka yi bauta a gidan miji karshe Allah ya sawa mazajensu soyayyarsu ya kuma dukkan nasara ta rayuwa

2⃣
Zaman aure baya tasiri idan aka rasa saduwar aure tsakanin miji da mata domin babu wata halaka da yake hada jinin mata da miji sama dashi yayinda shi kuma aka rasa ni'ima tofa komai yanda kike wajen miji a hankali zai qaurace miki bazaki ta6a tabbatar da hakanba sai haka ta faru dake.


3⃣
Haka yasa zan baki wani sirri yar uwata ki dinga amfani da gumbar baure ita dai wannan gumbar dai dai take da tsumin baure domin yadda aka samu tsumin haka aka samu gumbar wanda tuntuni mata ke amfani da ita fiye da sumin duk da cewar sumin ya fi saukin hadawa amma saboda tafi sumin bada ni'ima a sauqaqe dan gaban mace zai ta6a zama a bushe ba.

4⃣
Ki hada lefton dinki karki samai madara ki zuba gumbar baure cokali daya kisa zuma kibarshi ya yi kamar 7 minutes sannan ki sha da zaki daure kina yi akai akai wayyo 'yar uwa har na tausayawa majinki.

5⃣
Ki samu sassaqen bauren da 'ya 'yansa da dan bashanana da gyadar mata ki hada ki dasu ki aje
San nan ki samu gyada danya mai 6argo ki hada da aya soyayya da dabino ki hada kiyi garinsu san nan ki dauko wancan gari ki hada kita dakawa har sai ya hade gu daya saiki kwashe kina amfani da shi..."



Walima kam har walima wannan garaba sa haka anya be muku yawa ba? ... Anyi taro lpia an kare lpia anci ansha masha Allah ranar kowa da farin ciki fal a ranshi ya koma gida...


A Daren ranar laraba latifa tadau hanyan zuwa Niger wajen tsafe-tsafen ta da kuma shirinta naduk yadda zata hana Auren Umar da binafa...

A Daren ranar ne kuma da Binafa tayi kwanta tayi mafarkin latifa ,da duk wani shirin da take akanta itada Umar ,kasancewar tana da iska, matuqar zaka nemeta da sharri to insha Allah allah baze bari ba ,saboda tana da makarai masu rafanai. Sannan matuqar kace zaka shiga gonar ta koka shiga tsananin ta da abunda take so ,tofa ka kirawa kanka ruwa ,Dan iskan kanta bazasu taba kyale ko waye ba.... Wannan kuma wani sirrin boye ne dake k'unshe a rayuwar Binafa....


Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE6⃣1⃣➡6⃣2⃣*




Har kusan asuba tana wannan mafarkin, a gigice ta farka ta had'a wani uban gumi

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wa'ni'imal wakil ,la'ilaha illa anta subhanaka inna kuntu minazhzhalumin"... Shine abunda Binafa ta dinga maimaitawa tare da son gasgasata abunda ta gani a cikin mafarkin ta. Jikin ta duk ya mata nauyi, Dak'yar ta mik'e ta shiga toilet ta d'auro alwallah.
Tana idar da sallah wayarta ta lalubo ,numbern mlm musa me farin allo ta danna ,nan ya shiga ringing ,bugu biyu ukku ya d'auka ,seda suka gaisa sannan take zayyana masa irin mummunan mafarkin data yi ,alamar tana son k'arin bayani...

Numfasawa mlm musa yayi kafin yace

" Aidama ko baki kirani ba zan kiraki ,saboda kusan zan iya ce miki ni kaina mafarkin Dana kwana yi kenan ,sannan gaba d'aya jiya na kasa aiki ,Dan duk Aikin da zanyi sena ganki a ciki ,ni kaina bansan abunda hakan ke nufi ba ,sannan nayi istikhara saboda binciko ma'anar mafarkin amma gaba d'aya na kasa ganin komai"....

Tunda mlm musa ya fara magana Binafa ta natsu ta bashi hankalin ta tana sauraren shi ,zufa ne ya shiga tartso mata kamar wacce aka jika da ruwa... Wani nannauyan ajiyan zuciya ta sauke sannan tace

"To mlm nikam menene abun yi ?"...

" baki ji mena ce ba mamana ? Wllh ni kaina al-amarin ya kulle min ,bansan ta ina zan fara"

Tace
"To amma mlm me kake ganin ya kawo hijabi tsakanin Aikin ka da nawa?"..

Yace
" To abun dai ba wani Abu bane bayan abunda kika sani nasani. Ni inaganin kamar makaran kine suka mun shamaki da Aikin ,ina ganin kamar su suka karb'i Aikin ki shiyasa suka rufe ni daga aikata wani abun"...


Binafa kasa cewa komai tayi ,jin wani Abu daya zo mata kan k'irji ya tokare ta. Dak'yar ta bud'e baki tace

"To shikenan mlm ba damuwa "


Daidai nan anty Hindu ta shigo ta tashe ta sallah ,ganin ta akan dadduma tana waya ya tabbatar mata tayi sallah ,hannu Binafa ta d'aga mata alamar tana zuwa ,sannan anty ta fice

Daga b'angaren mlm kuwa murmushi yayi sannan yace
"Karki damu mamana ,insha Allahu ba abunda ze faru se alkhairi, sannan makaran ki suna da kyau ,ni kaina nayi kwadayin aiki dasu ,saboda alkhairin dake tare dasu, saboda haka tunda kika ji nace miki su zasu aiki akan wannan matar to kisa ido kawai kiyi kallo ,ita d'in banza ,halittar tafa akayi, to Dan haka ki zuba ido kiga yadda zasu yi da ita"...

" to mlm nagode" Binafa ta furta a sanyaye

Mlm yace
"Karki wani tada hankalin ki mamana ,ai Wanda Allah kewa fad'a baya fad'a". Wani dariya mlm yayi Wanda shi yasan ma'anar sa ,cikin ransa yace bazaki gane bane ni nasan mena gani ,na kuma San wahalar Dana sha kafin suka banni na fara miki aiki ,duk kuma wani abunda zan baki su suke bani ,Dan basu yadda kiyi amfani da wani abun daban ba ,wannan dalilin nema yasa suka kafe ki a waje na kika kasa attaka....


Jin shiru yad'an yi yawa yasa Binafa ta katse shirun da cewa
" to nagode sosai mlm ,se munyi waya"

Mlm yace
"To Amarya nima nagode asha hidima lpia"

Dariya maganar mlm ya bama Binafa tace
"Amma dai mlm zaka zo dai ko?"

Shiru yayi ,yana tunani ,tunowa da yayi wacece Binafa yasa ya furta

"Eh insha Allahu zanzo ma'ana , Allah ya bani ikon zuwa kinji"

"Ameen Binafa ta amsa mishi ,sannan sukayi sallama ta aje wayan...


Tana gama wayan ta kama hanyar d'akin umma Dan yi musu ina kwana ,nan ta taradda haddasu anty Hindu anata hira ,tana shiga suka soma zolayarta " Amarya Amarya Amarya kinsha k'amshi ,ita dai se Aikin murmushi take ,nan ta zauna aka dasa hirar da ita. K'arfe 8 na safe me k'unshi tazo daidai lokacin suna karyawa. Bayan sun kammala Binafa aka fara yarfawa wani had'ad'd'en design ,Wanda yayi cas a hannun ta da k'afafunta ,kowa se yaba kyawun k'unshin yake ,ba kadan ba lallen yayi kyau kasancewar binafa nada cikar hannu da naman k'afa ,yadda kuka san da inji aka zana mata shi.
ita kanta Binafa tasan an watsa mata had'ad'd'en design matakin farko ,ba abunda take hakaito wa se Umar faruk ,se Aikin murmushi take kamar tana gaban shi ,ana gama mata akama anty Hindu sannan aka farawa 'yan uwa... Bata wani damu da kitso ba ,gyaran kai taje aka mata ,gashin se walkiya yake shek'i ga Binafa da yalwar sufa...


Daren bikin , misalin karfe tara na dare Binafa na kwance Umar ya kirata ,take wata dad'ad'd'iyar wak'ar aure ya gauraye d'akin,,,,kallo tabi screen d'in wayar dashi a lokaci d'aya murmushi ya kub'uce mata

D'aukar wayar tayi tare da sallama had'i da kirari ga angon nata cikin wata murya da ita kanta batasan tana dashi ba...



"Amincin Allah, Rahma ,falala, gafara ,salama ,ni'ima, wadata, lpia da wanzazzen zaman lpia, kwanciyan hankali mai dorewa, farin ciki na har Abadan da Nisan kwana mai albarka ,su tabbata ga ma'abocin Neman halal, kuma masoyin Mustapha d'aha imamur rusuli. Abban ARYAN kuma ango agun BINAFA ,,,,Da fatar abun qauna ta ya wuni cikin k'oshin lpia???"...


Wani irin sanyin dad'i ne ya kashe Umar faruk daga zaune, yama kasa cewa komai ,har cikin k'wak'walwan shi yake jin kalaman Binafa ta ratsa ko wani jijiya na tsani....


Jin yayi shiru yasa ta hura masa iska fuuuuuuuih,,,, cikin wani irin salo na daban


Haba kawo yanzu kam Umar faruk yayi mutuwar zaune ,ba kad'an yana masifar jin dad'in salon Binafa da yadda take magana ,dakyar ya bud'e baki yace

" Matar Umar!!!"

Cikin shagwab'a tace

"Na'am mijin Binafa!!!"


K'asa k'asa yayi da murya yace
"Yanzu gobe war haka muna tare?"

Cikin zolaya tace

"Wa? Aah ai kozan tare se k'arshen watan nan"


"Tabbbbbbbd'i wllh ban yadda ba"... Umar faruk ya saki wata k'ara daya sa Binafa kauce wayan daga kunnen ta

Kukan shagwaba ya fara mata yana fad'in
" wllh ni mutuwa zanyi ,Dan Allah ki tausayamun idan baki se rijiyar agadaz.."


Dariya Binafa ta kwashe dashi hadda k'yak'yatawa tana fad'in
"A'ah ni ka rufamun asiri karka siyomun takaba da kud'i banjiba ban gani ba"


Dariya Umar keyi shima hadda Dan guntun hawayen shi ,seda ya tsagaita sannan yace
"Bama yanzu ba insha Allahu matata se mun rayu cikin aminci da qaunar juna"


"Insha Allah " shine abunda Binafa ta furta

Tsokanar shi ta shiga yi tana fad'in
"Kaji fa me sunan manya wai yanzu an iya soyayya"

Shima cikin sigar zolaya yace
"Hhhh bari zakiyi yarinya wani abun ma se ranar "...

Dikkan su dariya suka sa. A haka Seda suka raba dare suna waya sannan sukayi sallama shima d'in badan dan sun gundura da junan suba...

To akace ta faru ta k'are wai anyiwa me dami d'aya sata....🤓


Washe gari ranar asabar misalin karfe 12:30 na rana aka d'aura Auren Binafa da Umar ,daurin aure ne daya tara dandazon mutane, bayan an gama daurin Auren aka gudanar da walima da maza...
Dak'yar na iya ganin ango dake cikin taro yana ta faman gaisawa da jama'a...


Seda ya samu taron ya fara ragewa sannan ya turawa

Please Login or Register in order to submit comment