Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake jin kamar fatar jikinta ce ake kwashe wa. Yad'au kusan minti 40 yana Aikin hannun ,duk ya shafe hannun da wani magani bak'i na gari, ya tofa masa addu'o'i sannan ya mik'a ma Umma shi ,ya bata wani magani da za'a dinga bashi yana sha da daddare, na kwana ukku. Godia Umma ta masa ,nan Abba ya bashi dubu hud'u kamar yadda malam bala yace. Shegen gaye dubu ukku ya d'auka duba da yadda yaga gidan da halin da suke ciki , ya maidawa Abba dubu d'aya yace su rik'e ,nan sukayi ta masa godia...


Bayan sati biyu alhamdulillah yaya imran hannu ya fara warkewa, Dan kusan kukan dayake na dare ya dena ,ga k'onuwar ma ya fara k'amewa... Umma da Abba se hamdala suke wa ubangiji.




*BAYAN SHEKARA D'AYA*


Muka murmure kamar bamu ba, yanzu ba muda matsalan abinci Dan kusan lokaci zuwa lokaci baba tukur (k'anin umma) na yo mana aike. Har 'Yar kuba-kuba muka d'anyi. Muka fara rayuwa cikin jin dad'i... Amma ina Ashe jin dad'in nad'an lokaci ne...


Bayan wani lokaci akayi fad'a tsakanin musulmai da kafirai na kudancin Nigeria. Inda aka kashe musulman mu kamar ba gobe ,cikin wa'yanda suka mutu hadda baba tukur (k'anin Umma) ,Wanda shine dalilin farin cikin mu nad'an wani lokaci....


Lokacin da umma tasamu lbr innalillahi firgici agun Umma ba'a magana dan haddasu sume-sume. Ciwo tayi kamar bazata tashi ba na rashin Dan uwa datayi me tausayin ta, tasan dole zamu shiga wani hali na rashin baba tukur dake taimaka mana... Kusan kullum se tayi kuka ,Abba ma hadda kukan shi...


Aiko tun lokacin da abincin mu ya kare Wanda shine aike na k'arshe da baba tukur yayo mana ,nan fa rayuwa me dad'i ya mana kamshin d'an goro...








Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE4⃣3⃣➡4⃣4⃣*



Muka shiga k'angi da k'unci me wuyar fassara. Muka k'wammace ma gara da, ko yaya ne mukan samu mu sama cikin mu ,amma yanzu kam se abunda Allah yayi...

Ana cikin wannan yanayin ne Umma ta yanke shawaran da zaman wahalar nan da muke gara ko wankakau ta fara ,ta samu koda surfe(daka) haka ta dinga yi ko zamu samu abunda zamu dinga sawa cikin mu... Batayi k'asa a guiwa ba wajen Neman izinin Abban mu ,be musa mata ba ya amince... Tsawon lokaci Umma na wankakau da surfe ,amma ba wani samu ake ba ,Dan a wancan lokacin be wuce idan kayi surfe a baka sule 10 ba ko pan biyar. Wankin ne ma idan tayi me yawa za'a samu 20 ko 15...


Koda yaushe anty Hindu da yaya imran idan suka ga yara zasu boko da kuka suke shigowa gida, Umma data ga haka tasan Menene base ta tambaya ba ,Dan koda yaushe suka zauna basu da magana sedai su akaisu makarantar boko. Abban mu yace suyi hak'uri idan ya samu kud'i ze saka su...


Bayan wani lokaci me tsawo, yaya imran yayi bak'on dauro ,sedai ba'a gane shi bane seda ya gama cin jikin shi ,sosai yake wahala, koda yaushe Umma cikin 'yan jik'e jik'e take mai na itatuwa amma ina ba wani lbr ,kamar ma tana sake kiran ciwon ne, hankalin ta ya tashi gashi bata aje ba bata ba wani ajiya ba. Se a lokacin ta k'ara tabbatar da lallai tayi rashin baba tukur ,haka zata tasa yaya imran a gabanta tayita kuka...

Ranar wata jummu'a Abban mu ya dawo ,ta taso ta tare shi kamar yadda ta saba. Bayan ya huta take tambayan shi ko an samo wani Abu? Yace ba inda be buga ba amma ba wani bayani. Shiru Umma tayi nad'an wani lokaci kamar me nazari sannan tace "ni kuwa Malam ince wani Abu mana?" Ya kalle ta sannan yace" inajin ki ,tace "kaga dai halinda muke ciki ,yau dad'i gobe wahala ,abincin ma da zamu ci wahala yake. Meze hana ka fara zuwa Niger wajen Neman kud'i, kaga seka tuntub'i malam bala da zancen idan ze koma seku tafi tare!!!" Shiru yayi kamar bazeyi magana ba se kuma ya sauke ajiyan zuciya sannan yace " ni kaina nayi wannan tunanin amma bana so intafi inbarku ne ,sanin kanki ne ban tab'a tafiya me nisa ba irin haka ,sannan kinsan Aikin hak'o zinari akwai hatsari a cikin shi" " eh tabbas akwai hatsari amma ka sawa Zuciyar ka zaka iya insha Allah ba abunda ze faru se alkhairi "...
Washe gari ya samu mlm bala da zancen zuwa ARILLE, sosai yayi murna Dan dama ya tab'a yi masa maganar amma dayaga kamar bayada ra'ayi shiyasa be takura saba. Bayan sati d'aya suka shirya suka wuce ARILLE mlm bala shiya masa kud'in mota da guzuri. Randa ze tafi Umma hadda kukan ta a haka sukayi sallama ya kama hanya...

Watan shi biyu da tafiya yaya imran Allah ya karb'i abunshi, Umma taci kuka, 'yan uwa duk anzo mata ,masu bata hak'uri na bata ,masu mata alkhairi na mata... A wasa wasa seda Abban mu yayi wata 6 a ARILLE sannan ya dawo. Ba lefi ya samo kud'i ,sedai yaji ba dad'i lokacin da Umma ke sanar dashi mutuwar yaya imran... Kayan binci ya siyo musu ya aje,sannan ya bata wasu kud'i yace ta fara wata 'Yar Sana'a. Yanzu kam ba muda wata matsala ,muka fara rayuwa cikin jin dad'i. Watan shi biyu ya sake komawa ,sedai wannan karon ba sa'a Dan kuma suna cikin hak'o Katanga ta zubo mai a k'afa ,haka aka dawo dashi gida ,wasa wasa seda komai nasu ya k'are wajen Neman maganin k'afar. Anje asibiti akace za'a mai aiki naira dubu 25 ,inba haka ba kuma a yanke k'afar ,ana cikin haka ne aka kira umma taje gida ,Ashe rabon gadon sune ya tashi kusan shekara 10 da mutuwar baban su amma kud'ad'en shi basu gama fitowa ba se a lokacin. Haka ta tattaro duk wani Abu da aka bata tayi masa magani kafin ya warke... Bayan ya warke yace yana so ya koma ARILLE umma taki yadda dak'yar ta amince ,daze tafi ta bashi ragowar kudin dake hannun ta tace yayi na mota...

Wannan karon watan shi 4 ya dawo ,kuma alhmdllh ya samo kud'i... Haka yaci gaba da zuwa ARILLE duk bayan wata hud'u yake dawowa. Alhamdulillah rayuwa ta fara mana kyau ,Dan har ansamu boko nida anty Hindu ,shi kanshi Abban mu ya koma yak'i da jahilci...


Bayan shekara 10 mun fara sabuwar rayuwa ,Dan ko mun baro cikin kubau mun dawo wani babban gida da Abba ya gina mana nan cikin Kaduna.
Umma ta sake haihuwa ta samu namiji aka maida sunan yaya imran, a lokacin anty Hindu na aji biyar (SS2) a makarantar secondary ni kuma ina aji ukku (jss3). Abban mu kuma ya gama Dan harya jona jami'a, a bangare d'aya Kuma yana ci gaba da harkokin kasuwancin shi na zinari...


Bayan wasu shekaru goma lokacin mu 5 ne danko bayan anty hindu ,ni ,imran ,an haifi Abdallah da fatima, lokacin Abba ya nemi umma data tsaida haihuwa haka, bata musa masa ba ta fara tsarin iyali. A lokacin ya k'ara aure ya auri wata maryam muna kiranta da Ummi.


Ba lefi suna zaune lpia, kafin daga baya suka fara samun matsaloli da umma ,haka Amaryan ta dinga had'a mak'ark'ashi bala'in yau daban na gobe daban. Ana cikin wannan yanayin ne umma ta samu cikin musaddiq, nan fa Abba yace wayake so inba itaba, wai akan me zatayi ciki bayan yace baya son haihuwa, haka aka dinga wannan tashin hankalin a haka harta haifi su musaddiq. 'Yan biyu ne sedai d'ayan bezo darai ba.

Watan musaddiq biyu ,yace Umma ta shirya taje gida. Ba musu ta shirya ta tafi ,Ashe yanada kudurin rabuwa da ita bata sani ba, se bayan tafiyan ta da wata d'aya sannan ya aika mata da takadda. Munyi kuka kamar ba gobe. Kowa se tofin Allah tsine yake masa...

Cikin shekara ukku anty Hindu tayi aure a bauchi ,ita ma umma lokacin ta Dade da yaye musaddiq tayi Auren ta acan garin su minna, da zatayi aure anan wajen mahaifiyarta tabar musaddiq...

Lokacin Abba ya rabu da Ummi ,Dan tafiyan umma da shekara d'aya ita ma sukayi rabuwar wulaqanci , Ashe 'Yar duniya ce Dan ko da abokin shi aka kamata, nan fa kowa ya dinga cewa hakkin umma ne ya fita.
To bayan ita ya sake Auren wata habi dukda cewa Auren zumunci ne. Watan habi hud'u suka rabu, ya sake Auren wata ,itama basu jima ba suka rabu ,sannan ya dawo da habi, a lokacin ya samu labarin mijinda umma ta aura ya rasu, nan fa ya koma wai yana son ya maida ita, amma Sam mahaifiyarta ta hana...






Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE4⃣5⃣➡4⃣6⃣*




Ba yadda Abba beyi ba akan yana so ya dawo da Umma amma mahaifiyar Umma Sam tak'i amincewa. Magiyar duniya yayi amma ko sauraren shi batayi ,koda yaushe baya minna baya abuja. Da yake asalin su 'yan minna ne amma a Abuja suke zauna. Duk sati Abba na hanyan abuja amma Hajiya tana kan bakanta. Ganin yadda yake sassarfa koda yaushe yana kan hanyan zuwa bada hak'uri, yasa har wasu daga cikin 'yan uwa suka fara saka baki ana lallashin Hajiya amma dukda haka Hajiya tak'i sauraren su...
Kusan shekara d'aya ana Abu d'aya. K'arshe dai seda malam zubairu yasa baki, dayake Abba yaje ya same shi.
Malam zubairu shine mad'aurin Auren su Umma Wanda tun baban su Nada rai shike d"aura wa 'ya'yan gidan aure.. Malam zubairu be duba tsufan shiba ,da kanshi ya taso yazo gun hajiya. Tunda Hajiya taga mlm zubairu tasan akwai magana Dan ba k'aramin Abu bane zesa Malam yazo da kanshi ,saboda so dayawa idan yanason magana da ita sedai ya aiko kiranta ,amma se gashi yazo da kanshi...


Nan Hajiya ta tarbe shi fuskanta dauke da fara'a ,bayan sun gaisa ,ta kawo masa ruwa yasha ,nan take ce masa meyasa be aiko kiran taba tace" mlm da kanka ,wllh inda ma ka aiko aida base kazo ba". Yace " aah wannan sak'on niya kamata inzo Dan kuwa alfarma nazo nema!" ,jiki a sanyaye Hajiya tace " mlm alfarma kuma? To akan menene?" Yace " akan komawan Binta gidan uban 'ya'yanta ne!!!" Nan take fara'ar dake fuskan Hajiya ya gushe ,yaci gaba da cewa " ba shawaran ki nazo nema ba ,nazo ne inji dalilin dayasa zaki ki abunda Allah ya tsara, Ashe baki yadda da qaddara ba?"... Nan take hawaye ya fara saukowa Hajiya tace " ni Malam ba wai nak'i ta koma bane ,wllh ni kaina inason ta koma kodan albarkacin 'ya'yan dake tsakanin su, amma ina gudun ta koma ya sake wulaqanta ta kamar yadda yayi a farko. Mlm wllh lamarin nan ya soma bani tsoro, idan na tuno da yadda ya wulaqanta yarinyar nan wllh duk se inji na tsane shi ,ka duba fa daya koro mana ita da d'anyen jegon ta ,kuma ya mata sakin wulaqanci ,tunda kai ne sheda mlm ba yadda bakayi ba akan yazo azauna muji idan wani abun tayi masa ,amma kiri kiri yak'i zuwa. Haka ya barmu da yaron nan saddiqu (musaddiq kenan take cewa) ,besan cin shi ba besan shan shiba balle ai maganar surutu. Wllh ni kaji dalili na ,saboda kome koma ma hali ne ,tunda halin shine ba fasawa zeyi ba...


Nan dai mlm zubairu yayi ta bama Hajiya hak'uri had'e da yimata nasihohi da kuma nuna mata tai imani da kaddara. Mlm zubairu bashi yabar gidan su Umma ba seda ya samu amincewar Hajiya ,dukda Hajiya bataso ba kawai dai ba yadda ta iya ne ,kuma malam zubairu tamkar uba yake agun su Umma...


Ita kanta Umma badan albarkacin 'ya'ya ba bazata koma gidan Abba ba Dan bata manta wulaqancin daya mata ba ,kuma har zuwa lokacin bata dena mamakin shi ba da mamakin sauyawar shi lokaci d'aya... Cikin sati biyu akayi komai Umma ta koma ,yara da en uwa kowa se murna yake batta habi tayi murnan dawowan Umma saboda kullum cikin fad'a take da Abba ,ko kad'an baya ganin k'ok'arin ta akan yara ,shiyasa tafi koma murnan dawowan Umma. Koda Umma ta dawo lokacin habi ta haifi 'yarta ta farko ummul-khairi...


Ko kad'an Umma batajin dad'in zaman gidan Abba saboda kwata kwata halayen sa Nada Dana yanzu ba d'aya ba ,ya k'aro wulaqanci ,batayi mamaki ba ,illa dai tasawa kanta hak'uri ,a haka akaci gaba da zaman yau dad'i gobe ba dad'i... Shekaran Umma ukku da dawowa Abba ya sake yin aure ,su Umma suka koma su ukku kenan agun Abba, a lokacin ne aka masa transfer gurin aiki muka koma Kano da zama...


Watan bela'u 3 (sunan amaryar kenan) ,gidan mu ya koma kamar sanbisa, kwata kwata ba zaman lpia ,duk abunda bela ta gayawa Abba dashi yake aiki, kuma ko tusa akayi a gidan mu seta kwashe ta gaya masa wani lokaci ma tun kan ya dawo daga wajen aiki take kiransa a waya ta rattafa masa karya da Gaskiya. Kowa ya koma tsoronta yake a gidan ,yara kullum cikin shan dukan Abba suke ,Dan koda yaushe cikin kai k'arar su take. Zaman gidan ya fara isan kowa...


Bazan manta ba lokacin da aka auri bela shine shekara ta ta farko a school of hygiene, ita ma koda ya aure ta karatu take. Haka inaji ina gani bela tayi duk yadda zatayi ta shiga tsakani na da Abba, kai hatta makaranta ya dena mun komai na makaranta na ,amma ita ina kallo shine komai nata ,duk abunda ya taso na karatun ta shine. Wani lokacin zan ari kud'i inyi lalurar makaranta na dashi ,idan naje nace ya bani ,se kaji yace shibe aike ni cin bashi ba kuma baze biya ba ,inje duk yadda nasan zanyi inbiya kudin mutane inje inyi in biya... Haka bashi ya taru akaina.



Ana cikin wannan yanayin Umma ta samu cikin su twins ,nan fa bala'i ya dawo sabo ,fitinar yau daban na gobe daban a gaban mu muna zaune Abba ke zuwa yawa Umma cin mutunci ,zagi na uwa na uba se Wanda ya manta ,haka zatayi ta kuka muna bata hak'uri ,kullum cikin kyaranta yake akan cikin su twins yadda kasan cikin shige...
Abun ba k'aramin ci mana tuwo yake a kwarya ba musamman ma idan muka ga umman mu na zubadda hawaye... Tun bama magana har ya kawo mun fara sa'insa da bela. Duk yadda bela zata zuge shi ya fito ya mana rashin azziki baze hana idan ya fita ba mu maida mata martani... Ya hana Umma shiga kitchen sedai abunda bela taga dama ta dafa ta kawo mana. Gana d'aya ma ya hanata tab'a komai na gidan ...




A wannan shekarar Allah yayiwa Hajiya mahaifiyar su Umma rasuwa...


Daga k'arshe dai Abba ya saki Umma ,lamarin har kotu ,wai akan ya sake ta tak'i tabar masa gida ,kuma randa akayi case din har yace ya sake ta ,ranar ne yake cewa ,ya tsaneta kuma ya tsani abunda zata Haifa, wai shiyasa taki haihuwa gidan datayi aure saboda wancan mutumin bayada azziki ,shiyasa shi kuma taketa Tara mai 'ya'ya Dan ya mutu taci gado. Kud'i ya jefa mata a fuska yace ta fita tabar masa gidan sa, kuka Umma keyi kamar zata shek'e ,ba abunda take tunowa se maganar Hajiya data ce kome koma wa hali...


Musaddiq shine autan mu a lokacin ,yana kuka yazo kusada Umma yasa hannu yanata share mata hawaye, yace Umma kiyi hak'uri ki k'yale Abba kinji idan na girma nayi kud'i zan siya mk gida da moja in kaiki Makkah... Wanda wannan shine maganar musaddiq aduk lokacin da Abba yawa Umma wulaqanci...



Umma taso tabar gidan amma en uwa sukace ba inda zata ,akace ta bari seta haihu saboda kota tafi ba wani abun ze dinga kai mata ba na ciyar da cikin ,gashi Hajiya bata Raye... Wannan dalilin ne yasa Umma ta zauna. Ranar ina kwance ya kirani a waya be jira na gaishe shiba ya fara magana "dama na kira ne inbaki zab'i, ki zab'a koni ko uwar ki ,Dan naga kamar kina bayan ta ,to bari kiji ingaya mk ,matuqar kika zab'e ta to kimanta dani a rayuwar ki ,kima manta dakin tab'a sani ba ,idan kuma kika zab'e ni ki zauna in mk abunda Allah yace na tsakanin uba da 'ya...Dan haka na baki kwana3 kiyi shawara!"""... Yana kaiwa nan ya kashe wayan...






Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE4⃣7⃣➡4⃣8⃣*




Tun lokacin da Abba ya kirani ya bani zab'i akan in zab'a koshi ko Umma ,nayi bankwana da farin ciki ,tsantsar firgici ,damuwa da tsoron kalamansa yasa na tsinci kaina cikin yanayi na rashin lpia ,haka rayuwa ta taci gaba yau ciwo gobe lpia, ciwo nayi na gaske kamar bazan yi rai ba, ammma Abba ko a jikin shi, Umma ce kad'ai ke d'awainiya dani gashi ba wani k'arfi gare taba, sedai 'yan uwanta dake iya bakin k'ok'arin su wajen taimaka mana.
Bazan manta ba wata rana misalin k'arfe 12 saura na dare ciwo na ya sake tashi, akayi daidai Abba na gida, habi taje ta sanar dashi halin da ake ciki ,amma bud'ar bakin shi se cewa yayi aje a taro a daidai ta sahu akaini asibiti Dan shi ya riga ya kwanta ,ran kowa ba kad'an ba ya baci jin irin son kai na Abba, haka cikin Daren nan Umma da tsawon cikinta suka fita har titi itada su Abdallah wajen taro mai adaidaita ,dak'yar aka samu Wanda yace zeje ,aka so aka kwashe ni ragajab-ragajab akayi asibiti dani... Bayan 'yan gwaje gwajen da likitocin suka mun sakamako ya tabbatar da ina dauke da ASTHMA...

Kusan wata na biyu a asibiti amma Abba be lek'a ni ba ,abunda ma yake cewa shine wllh ya yafe wa Umma ni ,ya cire ni a cikin 'ya'yan shi ,bashi bani ,ya Riga ya sallamani inje duk yadda nake so inyi inje inyi rayuwa ta rayuwa tace be damu ba Dan haka ya cire hannu akaina,,,Saboda shi abba mutum ne da idan ya tsani mutum yafi son kowa ya tsane shi ,kuma yasan duk wata hanya daze bi ya b'ata maka suna dan kawai kowa ya baka baya. Kai akwai fa wataran bazan manta ba wani malamin islamiyyar mu yazo saboda yaga su Abdallah basu je makaranta ba yazo yaji ko lpia, aikuwa se yayi kicib'us da Abba ,nan suka gaisa ,sannan yake gayamasa dalilin zuwan shi, aifa Abba abun nema ya samu ,nan yama malamin iso zuwa babban parlour-n gidan a take ya kira kowa da kowa banda umma da bata qaunar ganin shi... Bala'i yake inda yake shiga bata nan yake fita ba ,har yana cewa malamin wllh ka gansu nan duk basuda tarbiyya shiyasa ma na tsani haihuwa da uwar su"... Kalmar nan ta k'ona mun rai ba'a gama zaman dani ba naji alamun ciwo na nason tashi da gudu na tashi na koma part d'in mu na d'auko inhela ta na shak'a sannan na had'iyi wasu k'wayu.

Umma na ganin haka tasan anyi wani Abu da banji dadin shiba ,tanada yak'inin akwai abunda Abba ya fad'a na suka akan su, Dan dama Abu ne me matuqar wahala tunda aka fara case d'in nan ya zauna ba tare da ya zage muba...


Dukda haka ban fasa gaisa Abba ba ,kullum ina zuwa yi masa ina kwana da sannu da zuwa amma ko kallon inda nake bayayi ,inbanda darajar mahaifiya ta ma da tuni nabar gidan ,ko nace zan bar gidan umma ke hanani kuma ta matsa sena je na gaishe shi...



Akwai watarana na shiga toilet zanyi alwallah, har na gama alwallan zan fito Ashe an zubadda ruwa a tsakiyan tiles d'in bayin ,nan silifas yaja ni suuuuuu!!!! Se jin kake shab'as... K'arar fad'uwa na da ihun danayi a lokaci d'aya yasa kowa yayo kaina, dak'yar aka fito dani ,asibiti aka kaini aka mun hoton k'afan ,Ashe k'ashi nane ya tsage, umma taso amin Aikin asibiti amma rashin Kudin da batada shi yasa tace a dawo dani gida ayi na gida. Kusan gyara ukku akayiwa k'afata amma kamar ba'a yiba danse k'ara kumbura yake kamar fulawa ansa masa yis...

Babu yadda habi batayi da Abba ba akan yayi wani Abu akan ciwon k'afa na amma ko kallonta beyi ba balle ya saurare ta. Son zuwa irin na mahaifi na yasa da yanzu na rasa k'afa ta d'aya... Daga k'arshe dai wani Me magani yake shaidawa umma ciwon k'afa na hadda shafar jinnu... Umma tayi ta kuka, koda yaushe goshinta na k'asa tana kai koken ta wajen Allah...
Haka aka had'a biyu ana Neman min maganin iska ,a b'angare d'aya kuma ana nema min na ciwon k'afa... Kusan wata shida kafin aka fara samu na dawo hayyaci na. Bayan na warke umma tace inshirya inje can kubau garin su mahaifi na in huta ,Dan tasan idan na zauna ba wani dad'i zanji ba anan d'in, haka na shirya na tafi.

Wani babban tashin hankali naje na taras a kubau d'in a gidan babban yayan su Abba baba Alhaji, Dan kusan abunda ke faruwa agidan su shine ke faruwa a gidan shi ,na gidan shin ma har ya soma zarce namu. Shima d'in dai mace ya auro wacce ta tarwatsa masa gida ,har ya ibi 'ya'yan shi su goma sha Tara yakai kotu wai ayi masa farar takadda dasu ba 'yayan shi bane... Wata na biyu a kubau, muna kwance muka samu labarin amaryar baba Alhaji ta kashe shi cikin dare kafin safe ta tattara duk dukiyar shi ta gudu da ita. Hankalin'yan uwa kowa ya tashi ,ana gama ansan gaisuwa na tattara na koma Kano, Dan kwata kwata tsoro ya hanani ci gaba da zama a kubau...


Wata rana na ina wanki ,na wanke ma Umma bargon ta nace bari in fara shanya shi yad'an tsane, naje na shanye acan bayan gida kan k'arfen tanki, bari na wajen keda wuya bela tayi wanki taje ta kwashe mun nawa gefe ta shanya nata ,ban jira tabar wajen ba Dan nasan tunda na ganta da bokiti dama zata nemi fitina ne. Tana tsaye ina zuwa na kwashe nata na yasar a k'asa ,nan ta fara zage-zage ,,,," uban wa yace ki zubda mun kaya k'asa ,nace "ubanki ne " hannu ta ta d'auka ta wanka mun mari ,daidai lokacin da abdallah ke dawowa daga masallaci ,ai kafin ta d'ago ya kaimata wani wawan mari ,nima ina tasowa na k'ara mata ,nan take bela ta fara ganin wasu taurari, batasan dama muna da haushin taba, kokuwa ta fara k'ok'arin yi damu aifa nan muka jebge ta iya son ran mu seda muka mata likis , ranar kowa yaji dad'in dukan da muka yiwa bela saboda dama ta ishi kowa, hatta mak'ota kowa ya tsane ta...


Abba na dawo wa bela taje

Please Login or Register in order to submit comment