Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dasa karas, tace


"Kinji labarin mu, Kin kuma ji tarin bakin ciki da kazantar dake ciki wanda yasa muka Kasa sanar dake... "



BINAFA ta tsabar tsoron Allah ya cika mata zuciya yasa ta rasa wai shin me zakayi Kuka kome, a ranta take ayyana cewa "lallai Duk yadda kake kafi wani, kuma komai damuwarka da shiga kunci idan kaji wani xakace a aljanna kake, tabbas Dole umar faruk ya Kasa sanar dani Wannan labarin, Dan babu dad'i a sauraren shi, wato dai kowa dana shi kaddarar rayuwar???" "




Wani nannauyan ajiyan zuciya ta sauke, sannan ta same ta da sakar wa hajiya tambaya


" hajiya kina nufin baki San salim na raye ba? Kuma baki San inda yake ba??? "


Murmushi hajiya karime tayi wanda yafi mari ciwo, tace


" haba fatima! SHA'IB kam ai ya Dade da barin Wannan duniyar "

Bude bakin BINAFA keda wuya zatayi magan, karar wayan hajiya karime ya dakatar da ita. Numbern ba suna, cikin sanyin jiki ta daga wayan tare da sallama...







" innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil"... Shine abunda hajiya karime ta maimaita har so ukku....



A zabure BINAFA ta Mike tsaye tana tambayar hajiya lafiya???...











Taku har kullum

SIDIYA ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 8⃣5⃣➡8⃣6⃣











Cikin tsananin tashin hankali hajiya ta janyo hannun BINAFA... Janta take har suka kai bakin mota, tace mata ta shiga, hajiya da kanta ta shiga gidan driver ta ja motar a 36...

Basu taka burki ko ina ba, se general Hospital area 1, tun kafin hajiya karime ta taka burki BINAFA ta Bude murfin mota ta fito. Dan ganin mutane data yi birjik a wajen ya tabbatar mata lallai akwai matsala.


Daga ita har hajiya karime rige-rigen shiga ciki suka farayi, wani doctor ne ya fito ta daidai kofar A&E, kasancewar yasan hajiya yasa yayi saurin taron hajiya, yana mata nuni alamar ta biyo shi.



BINAFA ne tasha gaban shi,,, wani kallon tuhuma take binshi dashi Nason Jin hakikanin abunda ke faruwa...

"doctor waye ba lpia ne wai?"

Cikin yanayin mamaki ya kalle ta, tare da cewa

"madam me gida umar ne aka kawo sunyi mummunan hatsari shida abokin shi. Ashe ba kida labari?"...

Wani kallon tuhuma take bin shi dashi, maida duban ta tayi gun hajiya tana so ta gasgata abunda kunnan ta ke jiye mata...

Cikin rawar murya da sassarka take tambayar hajiya karime


"ha.. Haj.. Hajiya wai da gaske ne mijina ne yayi hatsari? Hajiya kice mun Wannan labarin kwanzon kurege ne... Hajiya dan Allah kice wani Abu!"...
Kuma BINAFA ta fashe dashi me tsuma zuciya da karya zuciyar me saurare... Kan hajiya tace wani Abu, likita ya kalle ta cikin sigar lallashi yace

"kuyi hakuri, Wannan ba lokacin Kuka bane, insha Allah koma menene ze zo da sauki"

Rufe bakin shi keda wuya BINAFA ta fara salati tare da dafe gefen cikin ta. Cikin sec 30 Sega jini ya goce mata... Nan fa hajiya ta fara kidimewa tana Neman taimakon doctor...


Likita yace

"bari in kira azo a dauke ta, ina ganin labour ne"...


Jin an ambaci labour yasa hajiya ta kara fashewa da wani marayan Kuka...


Cikin minti 3 doctor yayi waya Sega wasu ma'aikatan asibiti sun zo da gadon daukar marasa lpia, da taimakon hajiya karime aka d'ora BINAFA da kawo yanzu Duk ta Gama ficewa a hayyacin ta...



Haka Suka d'unguma. Ana kaiwa daidai labour room a bakin kofa aka dakatar da hajiya, su Kuma suka shige aka duku fa kanta...



Hajiya karime Ganin abun ya mata yawa ita kadai, yasa ta dauki waya ta kira umman BINAFA ta sheda mata halin da ake ciki. Cikin tsananin tashin hankali umman BINAFA ta iso asibitin , ita da k'annan BINAFA Wato Abdallah da imran, wanda a daren jiya suka iso garin Abuja...


Isowar su yayi daidai da fitowan likita, a tsaitsaya umma da hajiya suka gaisa tare da jajantawa juna. Su Abdallah ma haka, gaishe ta sukayi sannan suka mata jajen halin da ake ciki.


Likitan ne ya k'araso inda suke, ya amurci hajiya da umma dasu same Shi a office... Haka suka d'unguma yana gaba suna biye dashi har office.


Kasancewar baya buk'atar wani tsaiko yasa ya fara da cewa


"A gaskiya fatima ta zubarda jini sosai. Dukda lokacin nak'udar ta beyi ba, Amma rud'ani da tashin hankalin data shiga ya janyo mata nak'uda. Munyi iya bakin kokarin mu Amma abun na nema ya faskara, Dan haka na Yanke cewa za'ayi mata C. S. Dan haka ku kwantar da hankalin ka insha Allah zamuyi iya wayin mu, sedai Ku taya mu da addu 'a. "



Hajiya karime fashewa tayi da wani marayan Kuka, tana girgiza kai

" a' ah likita, bana so akai ga operation, Dan Allah Ku taimaka kudai sake wani dabaran! "

Dr" gaskiya hajiya Dole ne se anyi operation dinnan inba haka ba za'a iya rasa su duka. Ta hanyar operation dinne kadai ma zamu iya ceton daya daga ciki, ko uwar ko babyn"...



Kuka hajiya keyi, umma ce ma ke karfin halin lallashin ta, tana bata kalamai Masu dad'i...


Imran umma takira yazo yayi signing sannan aka shirya shiga da BINAFA operation. Kusan ranar a tsaye suka kwana. Kowa da addu'ar da yake karantowa...



Daga b'angaren umar kuma an hana kowa ya gansu, kasancewar ba k'aramin rauni suka ji ba.


Misalin karfe ukku na dare aka gama shirin shiga dasu umar tiyata, sedai ya buk'aci yaga hajiya. Ba bata lokaci likita ya umarci daya daga cikin nurses din data kirawo masa hajiya.



Nan aka zo aka kira hajiya karime da duk ta gama fita hayyacin ta, tsabar Kuka da tashin hankali. Tafe nurse din take hajiya nabin Bayan ta har suka isa A&E...



A bakin kofa suka ci Karo da Likitan ze shiga ciki. Iso yawa hajiya karime har ciki.


Sallallami da kalima hajiya ta shiga jero wa lokacin da tayi Ido biyu da umar faruk sharkafff akwance kamar gawa, ga raunuka birjik a jikin shi...


Da sauri hajiya tayo kanshi, tana zubda kwalla, cikin sassarkan Kuka ta fara mishi magana


"Ba'ish!!! Ba'ish meya same ka haka? Me nake shirin gani? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"...


Magana umar faruk ke son yi mata Amma ya Kasa, nuni ya mata da yatsa, bin inda yake nuna mata da hannu tayi. Da sauri ta karasa wajen daya gadon da yake nuna mata...

Juyowa tayi tana tambayar shi


"Ba'ish waye Wannan? Ko Shine abokin Naka da aka cemun kunyi hatsari tare?"...


Umar faruk Magana yake mata Amma bata Jin me yake cewa, Dan haka ta k'araso har daidai setin kunnen shi dan taji me yake cewa.


Murya can k'asa-k'asa ya furta


" SA....SALIM!"...

Da sauri hajiya ta janye jikin ta , tana masa kallon ban gane me kake nufi ba. Cikin shak'ak'k'iyar muryar ta da baya fita sosai ta ce


" Ba'ish ban gane wani salim kake cewa ba, ko kanada aboki me suna salim wanda ban San shi bane? "... Umar faruk dai ba baki .

San kasan makoshin shi ya furta


" SHA'IB! "...


A razane hajiya tayi kan salim tana kara duba shi dan ta gasgata abunda kunnen ta ke jiye mata...

Takai kamar mintuna 3 tana kallon salim da bema San da ita a wajen ba kafin ta furta


" tabbas SHA'IB d'ina ne, wallahi Shine. Dama kana raye Shine baka taba nema na ba? A ina aka Gano mun kai SHA'IB?. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"...


Wani sabon Kuka hajiya karime ta sake fashewa dashi me ban tausayi. Tana cikin Wannan yanayin ne likita da mak'araban aikin shi suka shigo cikin shirin su na shiga tiyata.



Dak'yar suka lallashi hajiya karime suka janye ta, kafin aka gungura umar faruk da salim zuwa d'akin tiyata...



Ni kau nace "Allah dai ya fidda rai"...






Taku har kullum

SIDIYA ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)




INA TAYA D'AUKACIN AL-UMMAN MUSULMAI NA DUNIYA BAKI DAYA MURNAN SHIGOWAR WANNAN WATA ME GIRMA DA DARAJA NA RAMADAN. MUNA ROKON ALLAH DAYA SADAMU DA ALKHAIRAN DAKE CIKIN SHI, YA KUMA KARE MU DAGA FITINTINU DA MUSIBU. ALLAH YA MANA MAGANIN ABUNDA BAMU IYAWA KAN MU ALFARMAN ANNABI DA ALQUR'ANI. AMEEN...





*PAGE* 8⃣7⃣➡8⃣8⃣










Ranar umman BINAFA kwana tayi akan hajiya tana bata baki da addu'an Allah ya tashi kafad'un su gaba d'aya...

Misalin k'arfe 5:30 na asuba Allah ya hukunci aka yi nasaran fitar wada BINAFA 'yan biyu Duk maza. Yaran masha Allah gwanin sha' awa dasu gasu tubarkallah kamar ba 'yan biyu ba. Sedai kamar yadda Mahaifin su umar faruk yad' an fi d'an uwan shi jiki, haka Yaran suke, dukda cewa umar da Salem na matuqar kama da juna, hakan be hana a gane Wannan umar ne Wannan salim a Yaran... Murna wajen su umma ba'a cewa komai, barin ma hajiya karime data Kasa gane shin wani ya nayi take ciki, farin cikin samun k'are wai an haifa mata jikoki 'yan biyu ko kuwa bak'in cikin halin da Yaran nata ke ciki...


Ba yadda hajiya karime bata yi ba akan abar su suga BINAFA Amma likitan ya hana akan se nanda awa ashirin hudu, lokacin sun gama bata Duk wani taimakon daza su bata. Hajiya fafur tak'i yadda, seda likitan ya tabbatar mata har yanzu BINAFA na unconscious sannan ta hakura...

Misalin k'arfe 7:00 na safe aka fito dasu umar daga tiyata, Alhamdulillahi anyi a sa'a, likita ya kuma tabbatar musu da zasu farfad'o nan da awa 24 kamar dai yadda aka bada lokuttan farfad'owar BINAFA...


Basu iya Kiran kowa sun sanar dashi haihuwan ba, kasancewar halin da ake ciki. Dak'yar umma ta shawo kan hajiya akan ya kamata taje gida ko Wanka tasamu tayi. Badan taso ba haka Abdallah yakai ta sedai bata bari ya barta ba, tare suka dawo. Kota kan abinci bata bi ba, kaya kawai ta iya d'aukowa na jarirai data jima tana musu tariya...




K'arfe 7 da mint 45 na dare Bayan su Abdallah sun dawo masallaci, likita ke shedawa su umma BINAFA ta Farka, kaida ka gansu ba angaya maka sunyi murnan Jin hakan ba. Gaba d'aya suka d'unguma zuwa ganin ta.


Ba kad'an ba sun tausaya mata, hajiya hadda k' wallan ta, ganin BINAFAR kamar wacce ta Shekara tana jinya, ta jeme ta kod'e, ga Rama da tayi da bak'i ba'a magana.


Sannu suka shiga jero mata, ita dai BINAFA kai kawai take gyad'a musu... 8:30 daidai aka sake zuwa musu da wani albishir na farfad'owar su umar faruk, Abu d'aya ne ya girgiza su najin cewa salim yayi loosing memory - nshi, Ana tunanin ma sakamakon buguwar da kanshi yayi kamar Wata jijiya ta tsinke a cikin k'wak'walwar shi, wanda likitan ya tabbatar musu da Dole se an ziyar ci psychiatric hospital dashi (wato asibitin mahaukata).


Wannan labarin Sam beyi wa kowa dadi ba. Sedai sun dauke shi a Matsayin kaddara. Ganin kamar zirga-zirgan ze musu yawa, yasa umma ta bukaci da a had'e musu majinyatan su waje d'aya. Haka kuma akayi , daki d'aya aka hade su me tsabta.


Ranar su umma kwana nafiloli da addu'o'i sukayi na nema wa 'ya' yan su lpia. Bayan kwana biyu BINAFA da umar faruk lpia ta fara samuwa, Dan har magana suna d'an maidawa jefi jefi, salim kuma bacci yake ta fama ba dare ba safe.

Rana ta uku jiki ya kara sauki, Dan har an fara Bama babies din mamma, umar kuma ya yiwa yara had'uba daga nan kwancen dayake. Yara sunci sunan mahaifin su da d'an uwan shi, wato umar faruk da Ahmad salim, ya kuma yi musu laqani da laqanin su wato BA'ISH da SHA'IB, kamar yadda hajiya karime tayi musu laqani tun suna jarirai...



Kowa yayi murnan hakan sosai, banda BINAFA data Kasa gane manufar mijin ta na aikata hakan. Musamman data San halin mijin ta sarai, tasan tabbas Duk abunda zeyi akwai dalili a tattare da abun, ta kuma k'ware wajen hakaito dalilan sa, sedai Wannan karon yasha bambam dana ko yaushe, Dan ta Kasa Gano komai game da hakan...



Kwanan su hudu a asibiti, ranar kam umar faruk gara wasai sauki ya samu, ansha hira dashi kamar ba mara lpia ba. A cikin hiran ne umar faruk ke fad'in kyaututtukan da yawa yaran shi na kamfanoni, gidaje, motaci da kuma zunzurutun kudi, Abdallah da imran kannen BINAFA Ma be barsu a baya ba seda ya musu kyautar gida kowannen su guda d'aya flat house me kyau, hajiya karime uwa uba, umma ma be barta a baya ba, haka ya ware adadin abunda yake so ayi masa sadaka dashi,sannan ya ware wanda za'a nemar wa dan uwan shi salim lpia dashi.

A takaice dai garin Allah be waye ba seda umar faruk yayi kyauta da duk wani Abu daya mallaka a fad'in duniya. Wanda ba karamin daure wa mutane kai Al-amarin yayi ba. Tabbas sun San umar da kyauta, Amma Wannan karon kyautar nashi ya gigita kowa, barin ma BINAFA data fara Kuka tana ganin kamar umar faruk mutuwa zeyi ya barta. Ganin hankalin ta yayi matuk'ar tashi yasa umar faruk ya shiga bada labarin barkwanci, a haka har seda ya tabbatar ya saka kowa dake wajen dariya.


Ranar dikkan su a asibitin suka kwana. Umma, hajiya karime, abdallah da kuma imran.



Misalin karfe 4 na asuba, bacci b'arawa ya saci kowa Amma banda umma da tayi kwanton b'auna, bata San dalilin dayasa bacci ya gagari idanuwan ta ba...

Iko se lillahi Allah , salim da tunda abun ya faru ko motsi be taba yi ba, wanda har kowa ya cire masa rai seda likita ya tabbatar musu cewar da izinin Allah ze farka sannan suka samu natsuwa. Se gashi asuban yau ya farka.
A hankali ya bud'e idanuwan shi, se akan umar faruk. Hakan yayi daidai da farkawan umar da dama shima ba baccin yake ba, tun daren jiya bacci ya k'aura daga idanuwan shi... Kasancewar Gadon umar faruk da salim a had'e suke Wannan ne yabama umar faruk daman rik'o hannun d' an uwan shi salim.


Da murmushi d'auke akan fuskar shi yace

"welcome back d'an uwa na. Nasan dama bazaka taba tafiya kabar niba, sedai ni in tafi in barka. Ka dawo a lokacin dana fi buk'atar ka dan uwa na. Inaso kahau kujera ta, ka kuma wakilce ni. Ga mahaifiyar mu nan da tun tashin ta bada wanda ta saba inba NI ba, tabbas seka daure ka kuma jure, sannan Kasa hakuri a zamantakewa, a sannu zaka ga ribar hakan. Ga kuma matata nan" wani siririn murmushi umar faruk yayi daya ambaci ga matar shinan, yaci gaba da cewa


"nasan zaka sha fama da ita, although ka Santa ka kuma saba da ita, Wannan ze taimaka maka wajen kara fahimtar ta. Ga kuma 'ya' yan ka. AHMAD ko Bayan raina ban yarje maka 'ya' yanka su San ba kaine ka haife suba. Toma dama wayace bakai ka haife suba, ai naka ne halak malak Allah ne ya baka, Dan haka seka rike Amana ka kuma gode masa"...



Wasu siraren hawaye ne suka sauko daga idanuwan salim, Murmushi umar faruk yayi wanda ya assasa bayyanar kyawun shi, sedai ramar dayayi.
Kumatun shi yaja tare da cewa

"lallai kuwa akwai aiki, baban yara na Kuka, to idan ya ranka na kukan da wani kalma zaka yi Amfani dashi dan lallashi? Oh nasan cewa zakayi, muyita Kuka se mun gaji mun bari"... Umar faruk ya k'arasa maganan kamar wani yaro, ala Dole wai shi yana kwaikwayon maganan yara. Wanda hakan seda ya Bama salim dariya, sedai ba halin dariyan, murmushin shi me ban sha'awa ne shimfid'e akan kyaky-kyawar fuskar shi...



D'an lakuto hancin salim umar faruk yayi tare da cewa

"ko kaifa carrying jerry. Murmushi na maka kyau, keep on smiling kaji kanina?"

Ido salim ya lumshe alamar Yaji komai ya dauki dikkan nasiha da amanar da d' an uwan nashi ya bashi.



Hannun salim umar faruk ya sake damk'owa, ya manna a kirjin shi dake dukan tara-tara. Yace


"baban yaran shi idan xan iya tsaida Wannan bugun zuciyar nawa, to xan iya yafe maka idan har kayi kokarin fallasa sirrin dake tsakanin mu." shiru ne ya biyo baya kafin umar faruk yace


"Allah ya tayaka rik'o"... Da murmushi dauke a fuskar shi a haka har bacci ya kwashe shi.

Duk abun nan da umar faruk ke zayyanawa dan uwan shi basu San cewa idon umman BINAFA biyu ba, ta kuma ji komai.



Misalin K'arfe 6 na safiyar jummu'a, akaji umar faruk na kalman shahada. Kafin kowa ya sani rai yayi halin sa.


Umar faruk ya karba Kiran ubangiji... Sedai fatar Allah ya yafe masa...











Taku har kullum

SIDIYA ✍



💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



INA TAYA D'AUKACIN AL'UMMAR MUSULMAI MURNAR BIKIN SALLAH, FATAR DUK MUN YI SALLAH LAFIYA? TA'ALA YA KARB'I IBADUNMU MU YASA MUN DACE DUNIYA DA LAHIRA, AMEEN👏...



*PAGE* 8⃣9⃣➡9⃣0⃣







Ba kad'an ba mutuwar umar faruk da girgiza mutane, Dan kuwa ba wanda be zubarda k' wallan Rashin shi ba. Duk kuma wanda yazo ta'aziyya da irin nashi yabo, karamci da kuma taimakon da umar faruk ya masa yake fad'i. Su kansu iyalan shi basu k'ara tantance waye umar faruk ba se Bayan babu shi. Yabo kam yasha ba'a magana, daga masu fad'in "sun shiga ukku hannun dake basu ya tafi, se masu koken" ina zasu saka Rayuwar su. To jama'a mutanen waje Kenan, ina ka ga matar shi da mahaifiyar shi.

BINAFA ganin mutuwar umar faruk take kamar wasa, bata da aiki sena zubadda k'wallah, tun tana ganin abun wasa, har ta jingina tabar wa Allah, ta kuma karb'i kaddarar da Allah ya aiko mata dashi, tasa a ranta mutuwar umar faruk Duk yana cikin muqaddari na Rayuwar ta da bata Isa ta kauce wa hakan ba. Haqiqa BINAFA jarumar mace ce, kowa yasan mutuwar miji yadda yake da d'aci musamman ga wa'yanda basu da mazajen, tun tana kukan har ta dawo yin na zuci, ta kuma wakkalama Allah al'amurran ta, tare da nema wa mijin nata gafara da rahmar Ubangiji, koda yaushe ka shigo gidan akan dadduma zaka taradda ita da calbin ta a hannu tana kuka tana gayawa Allah daya lamunce ya kuma karb'i bak'uncin mijin ta...


Cikin satin mutuwar umar faruk Duk BINAFA ta kod'e tayi bak'i, da dawo gwanin ban tausayi, Duk Wanda ya kalle ta Dole ne ya tausaya mata. Sauk'i d'aya take ji, da hajiya karime mahaifiyar umar faruk keta k'ok'arin luradda ita k'addarar data same ta, tabbas hajiya karime tasan Itace ta haifi umar faruk, ta kuma yi jimami da kuka na Rashin d'an ta d'aya tilo Mai matuqar son ta da tausayin ta, tabbas hajiya karime ta shak'u da umar faruk, shak'uwa mara misaltuwa, wanda Wannan Shine karo na Farko da zata fara Rayuwa babu shi a kusa da ita, Bama a kusa da ita ba, baya duniyar, koya Rayuwa zata kasance musu? Allahu a'alamu.
Dukda cewar ita macece me tawakkali, kuma wacce ta had'u da jarabawowi na Rayuwa Iri daban daban, kusan ma se ince ita da umma mahaifiyar BINAFA bamu San wanda yafi wani shiga taskon Rayuwa ta, kai koda yake anya ma zamu had'a?, to masu karatu Wannan amsar na wajen ku...




Hajiya karime da kanta tasan shakka babu, hak'ik'a BINAFA ta fita Jin mutuwar umar faruk. (ni kam nace anya hajiya kuwa? Ita da tun tashin umar da ita yake Rayuwa ba wanda ya sani idan ba ita ba. BINAFA kuma umar faruk ya shigo Rayuwar ta ne a lokacin da tafi buk'atar shi, wanda hakan ba k'aramin sauyi ya kawo wa Rayuwar ta ba)...


Kwanan umar bakwai da rasuwa, mutane suka fara watsewa, cikin masu shirin tafiya kuma akwai umma mahaifiyar BINAFA. Dan Duk nan gidan mahaifiyar shi akayi komai, har ansan gaisuwa.



Bayan umma ta Gama shirin ta tsab na komawa gidan ta, nan ta buk'aci son ta zauna da duk ahalin umar faruk, sedai banda salim dake keb'e a sashen da aka ware masa dake ta Bayan sashen hajiya karime. Sosai umma tayi musu nasiha me shiga jiki, ta kuma k'ara tuna musu waye umar faruk da irin tarin yabon da ya samu a bakunan Al'umma, ciki hadda alkhairan da yake mata wanda ko BINAFA bata San dashi ba, ta k'ara tabbatar musu Rashin umar ba nasu bane su kad'ai na kowa da kowa ne. Ta basu shawarwari masu yawa ta yadda komai ze zo musu da Sauk'i, sannan ta seda mata BINAFA zata Zauna anan har ta Gama takaba, tana kuma fatar kafin lokacin Allah ya kawo wa zukatan su d'auki da sassaucin abunda ya faru.

Daga k'arshe hajiya karime ce kawai tayi k'arfin halin bud'e baki na yiwa umma godia da nuna Jin dad'in ta, Dan kamar umma tasan abunda ke ran hajiya karime Kenan, Na son abar BINAFA a wajen ta na d'an wani lokaci.


Ummah ta dakatar da ita, ta yadda ta nuna mata ai BINAFA ta zama 'yar ta, tunda har matar umar faruk ce, koda ba rabo a tsakanin su bare ga rabo harna' ya'ya biyu a lokaci d'aya, sannan tana hango zaman BINAFA a tare dasu Bama na yanzu ba, har abada.


Ita dai BINAFA uffan ta kasa cewa, se ma aikin kuka da tun Bayan rasuwar umar ya zame mata Abinci.

Taron ya watse da addu'a, kafin umma ta fito ta shiga sashen salim.



Salim dake kwance kamar wani makararren tsoho, duk ya gama fita a hayyacin shi, yake kuma cikin rud'ani da taraddadin yadda Rayuwa zata kasance mishi, babu abunda ke koranya a idanuwan shi safe da marece se hawaye...


Hadimi d'aya ne a sashen nashi me kula dashi me suna lukman. Shine kad'ai ke ma'aikacin shi na din-din-dim. Duk kuma wani d'awainiya kama daga kula da sashen harkar shara da goge-goge, Wanki da gugan kayan shi, bashi Abinci, Wanka da sauran su.

The worse part a wajen salim be wuce Wanka da ake masa ba, Duk da cewa dan goge masa jiki ne kawai a dan karamin

Please Login or Register in order to submit comment