Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE3⃣5⃣➡3⃣6⃣*



Kusan likitoci kwana sukayi akan Umar faruk suna bashi agajin gaggawa. Yayin da Binafa ke can kawo yanzu duk ta gama fita a hayyacin ta ,ta wani zare kamar zautacciya. Ba aikinda take sena kuka ,ganin baze fish-sheta ba yasa ta tashi ta d'auro alwallah ,wata nurse ce ta bata hijibinta tare da d'auko mata sallaya. Nan ta fara rankon sallan dake kanta ,tare da jero nafil-fili, tana rok'awa Umar faruk samun Lpia. Ranar kusan kwana sallah tayi tana me k'ask'antar da kanta ,tare da zubadda hawaye ga Allah tana gaya masa buk'atocin ta... Kusan kasa bacci tayi tana jira taji daga likitocin ,amma shiru har kusan asuba...



Su Kansu likitocin sun fidda rai da Umar ,Dan sunyi iya bakin kokarin su amma ba alamun Umar ze farka. Da har sun yanke shawaran su fad'a wa Binafa ya mutu ,se wani daga cikin likitocin yace karsu yi hantsari ,su jira su gani ,shi yana tunanin doguwar suma Umar yayi ,Dan haka yace abari aga zuwa da safe idan be farka ba shiya nuna rai yayi halin sa...



K'arfe 6 na safe Umar faruk ya motsa sedai be bud'e idon shiba, alokaci d'aya layuyyukan dake jikin na'uran suka dawo ,alamun numfashin shi ya dawo. Da sauri likitocin dake wajen suka k'araso wajen sa ,suna masu godia ga Allah.
Nan take suka shiga bashi agajin gaggawa ,a hankali ya fara sauke numfashi. Aiki suke cikin k'warewa, Wanda har suka gama bashi taimakon da zasu iya bashi Umar be bud'e ido ba. Doctor haris ne yace su bashi lokaci su gani ,ai tunda dai yana da rai komai me sauki ne Insha. Nan yace aje a sanarwa matar Umar ,duk a Cewar su Binafa matar Umar ce ganin yadda ta kid'ime ta sauya kala ,ta kuma damu da rashin lpia-n Umar...


Wata nurse aka tura ta sanar wa Binafa. Koda taje kishingid'e ta same ta ,tana lazimi ,hawaye wani nabin wani. Tayi zurfi ainun a tunanin halinda umar ke ciki, hakan yasa Bata ji shigowar mutum ba. Sunanta nurse din ta kira


"Mrs faruk!"... Shiru bata ko San da ita ba ,ganin hankalinta ma kwata-kwata baya tare da ita yasa ta k'arasa tare da dafa ta lokaci d'aya tana sake kiran sunan ta

" Mrs faruk tunanin me kike haka?".. A dan tsorace Binafa ta dawo cikin hankalin ta tare da dora rikid'ad'd'un idanuwanta akan nurse d'in. Murmushin k'arfin hali ta sakar mata. Sannan suka gaisa. Nan take mata albishir da Umar faruk ya farfad'o, amma har yanzu be...


Ai binafa bata ma jira taji k'arshen zancen ba ,a zabure ta mik'e tana sake cewa

"Me naji kince sista Fatima? ,Umar ya...ya farka fa kikace?". Ta k'arasa maganan cikin rawar murya.

" ko shakka babu!" ... Nurse din ta bata amsa


Binafa bata jira me nurse zata ce mata ba ,da gudu tayi hanyar fita. Cikin sauri take tafiya ,har tana d'an had'awa da gudu-gudu. Ai tana kaiwa kofar emergency d'in iya k'arfin ta tasa ta banka kof'ar... Tsayawa tayi cak ,ganin Umar din na nan kamar yadda ta barshi ,da k'yar ta iya tattaro natsuwarta ta fara tafiya kamar wacce batada lakka. A haka ta k'arasa har bakin gadon da Umar ke kwance... Nan take ta fashe da kuka ,kuka take kamar ranta ze fita, magana take so tai masa amma ina kuka yaci k'arfin ta...


Ta kusa mintuna 15 a tsaye a wajen tana Aikin Abu d'aya. Kamar a mafarki taga k'afar Umar na motsawa ,lokaci d'aya kuma hannun shi ya motsa. Ba shiri ta isa gare shi ,goge hawayen ta ta farayi cikin farin ciki tana cewa


"Tabbas baka mutu ba Umar ,wllh naga kayi motsi, ni nasan bazaka tab'a tafiya ka banni ba Umar, Umar ka taimake ni ka bud'e idon ka, Umar ka bada rayuwar kane saboda ni ,wllh Umar idan baka bud'e ido ba mutuwa zanyi ,mutuwa zanyi wllh..." Ta k'arashe maganan tana k'ara fashewa da wani kukan me ban tausayi...


Duk lokacin da Binafa zatayi magana se Umar yayi motsi ,maganar ta ya daki dodon kunnen shi ,se jin abun yake yana masa yawo... Zan mutu Umar ....zan mutu...


A hankali Umar ya fara k'ok'arin bud'e idanuwan shi. Yayin da Binafa ta kifa kai da gado tana ci gaba da kuka. Jin motsin yayi yawa yasa ta d'ago kanta ,aikuwa kamar ance ta d'ago. Sukayi ido biyu da Umar faruk daya kafe ta da ido. Ba shiri Binafa ta fad'a jikin shi ,Dan tsabar murna harta manta da ciwon dake jikin shi...


Hannunta ta d'ora akan fuskar shi tana mai yawo dashi tare da cewa


"Ka farka Umar? Wllh ka farka. Dan Allah ka kira suna na ko so d'aya ne me sunan manya ,ko zanji saukin rad'ad'in da zugin da zuciya ta keyi. Dan Allah na rok'e ka kayi magana..."


Cikin muryassa ta bata fita sosai ya furta a dasashe

"Binafa...

Wani irin dad'i ne ya ratsa tun daga k'wak'walwan Binafa har cikin k'afa. Bata an kara ba ya sake kiran sunan ta, yanzu kam ya d'an d'aga murya ba kamar farko ba... A lokaci daya yana me sakar mata murmushin sa me k'ayatarwa. Wanda duk da halin rashin lpia da Umar faruk ke ciki ,ba k'aramin kwarjini murmushin da ya masa ba.


Binafa bata San lokacin da ta sake mak'alk'ale shiba Dan tsabar farin ciki. Wannan karon Umar hadda Dan k'ara ya saki jin irin damk'ar da Binafa ta masa tare da cewa


" wash ...Allah na zaki k'arasa ni" ya fad'a cikin muryar shi da baya fita sosai

D'agowa tayi ,a lokaci d'aya suna sakarwa junan su murmushi...








Comments
&
Share






Taku har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE3⃣7⃣➡3⃣8⃣*



Kwanan Umar faruk 3 da farfad'owa ,alhamdulillah ya fara samun sauki ,idan ma kaji yana magana rambad'ad'au bazaka ce yana cikin jinya ba. Sosai Binafa ke bashi kulawa, dak'yar ya samu ya lallab'ata ta koma masaukin su tayi wanka. Seda ta gama shirin ta tsaf har tazo fita taji k'arar wayanta, se a lokacin ta tuno da rabonta da waya kusan sati kenan. Wani guntun tsaki taja sannan ta koma ta lalubo wayar , a mamakin ta missed calls ta gani sama da 200 ,baki ta rufe tare da furta


"Kutt"... Batayi mamaki ba Dan tasan dama dole za'ayita nemanta


Harta bud'e zaka zata jefa wayan kiran MD ya shigo wayanta. D'auka tayi tare da sallama.

Wani nannauyan ajiyan zuciya MD ya sauke ,kafin ya amsa mata sallama cikin kasalalliyar murya. Sannan ya fara tambayan ta lpia?

" Binafa meya same ki haka ,Dan Allah ki gayamun? Wllh hankali na ba k'aramin tashi yayi ba jin ina kiran ki bakya d'auka! Ko bakida lpia ne?"

Seda ta sauke numfashi sannan ta fara magana jiki ba k'wari

"Eh wllh doctor nayi rashin lpia ne ,harma seda na kwanta asibiti, amma yanzu alhamdulillah na samu sauk'i"...


" ya salam! Meya same ki Binafa kuma ya kike jin jikin yanzu?, kodai in zo in taho dake ne? ". MD ya tambaye ta wit full of concern


Murmushi Binafa tayi tare da cewa

" karka damu Dr I'm feeling much more better "..

Wani ajiyan zuciya MD ya sake saukewa tareda cewa

" To alhamdulillah. Wllh duk naji ba dad'i ,Ashe shiyasa baki halacci walimar seminar d'in ba ,Dan sun kira ni sunce sunata kiran ki baki d'auka ba, har suke sheda mun asibitin muce tayi na d'aya "


Cikin farin cikin jin kalaman MD Binafa tace

"Congratulation sir!"... Murmushi MD yayi sannan yace

" kinji ki ,aike za'a yi congratulating ba kowa ba. Yanzu dai yaushe zaki dawo? Kinsan dole za'a had'a mk walima ta jinjina da ban girma ,kan namijin kokarin da kika yi!"


"Insha Allah zuwa next week zan gama ganin likita na ,Dana kammala zan dawo!" Ta bashi amsa a tak'aice


Yace

"OK to ba damuwa. Wish u speedy recovery".

" thanks ". Ta bashi amsa a tak'aice sannan ta masa sallama cike da matsuwa ta yanke kiran.

Wani dogon tsaki taja


" mtsss... Wato kai ta ma celebrating kake ,bata lpia na ba, bayan duk abunda ya faru dani wannan ahegen seminar d'in ne sila. Abu d'aya nasani shine da wani Abu ya sami Umar faruk bazan taba yafe maka ba MD ,saboda shine komai nawa a yanzu. A gefe d'aya kuma ina gode maka Dan Kaine silar Dana had'u da *ZAB'IN RAINA* ..." Haka tayi ta sambatu ita kad'ai, ganin lokaci na tafiya yasa tayi harman komawa asibiti Dan ta sake duba jikin Umar faruk


Isar ta bakin asibitin keda wuya kiran salim ya shigo wayan ta. Kaman bazata d'auka ba ,Dan ta tsani duk wani Abu dazai mata shamaki da ganin Umar. Seda kiran ya tsinke ya sake kira sannan ta d'auka...


Tana d'auka me zata ji idan ba salim daya fashe mata da kuka ba. Wani sororo tayi Dan tasan kad'an kenan daga halin salim. Ganin baze yi magana ba yasa ta fara magana


"Lpia kuwa? Meya same ka?" Ta tambaye shi

Kamar baze yi magana ba ,se kuma ya share hawayen dake gangaro masa ,yace

"Ina kika shige haka swthrt? Meyasa zaki azabtar da zuciyata ta wannan hanyar? Wani irin lefi namiki da zaki zartar mun da wannan d'anyen hukuncin? Pls swthrt me namiki ki gayamun?"...


Jikin Binafa ne yayi sanyi ,Se duk tausayin salim ya kamata. Dak'yar ta iya bud'e baki tace


" kayi hak'uri s... " swthrt zata ce masa se kuma taji ta kasa data tuno da Umar faruk. Ganin karya zarji wani Abu yasa taci gaba da magana


"Banda lpia ne dear, har admitting d'ina akayi sati d'aya kenan amma yanzu na samu sauki alhamdulillah."


Jin ze sake fashe mata da wani kukan yasa ta katse shi da cewa

"Sorry dear ,yanzu haka nazo asibiti check up ,idan na koma gida zamuyi waya". Bata jira taji me zece mata ba ta yanke kiran... Sannan ta k'arasa cikin asibitin


Mamaki ne kwance a fuskan salim ,ya rasa meke masa dad'i, yana so ya gasgata abunda yaji agun Binafa amma zuciyar sa ta kasa tantance masa. Jikin shi ya mace Wunin ranar gaba d'aya haka ya wuni kamar Mara lpia...


Satin salim 2 aka sallame shi ,suka koma masaukin su. Sosai Binafa ke kula dashi ,Dan indai har kaga tabar d'akin salim to d'ayan biyu ne ,wanka ko idan zata d'auko wani Abu.


Bayan sallah isha ,Binafa da Umar ne zaune suna hira. Umar yace

" Niko me sunan larabawa inaso in tambaye ki wani abu Dan Allah! "

Wit full concern ta maida hankalin ta kanshi tace

"Inajin ka me sunan manya. U're free to go"


Dan numfasawa yayi sannan yace

"Dan Allah menene tarihin ki nikam?"

Nan take Binafa ya nemi farar dake fuskar ta ya rasa, a lokaci d'aya wasu zafaffun hawaye suka fara sauk'o mata, kan kace me kuka ya k'wace mata...





Comments
&
Share





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)

*PAGE3⃣9⃣➡4⃣0⃣*

Kuka Binafa keyi me ratsa zuciyan me saurare. Se Umar faruk duk yaji beji dad'i ba ,ya kuma yi Dana sanin yi mata wannan tambayar, Dan dama ya dad'e da karantar akwai k'unci a tattare da rayuwar ta Wanda bata so ta tuna shi... Yaso ya lallashe ta amma ganin yadda Binafa ke kuka bata ji bata gani yasa ya kasa tab'uka komai... Ido ya zuba mata yana jin wani so da qaunar Binafa na k'ara ratsa ko wani jijiya da sassa na jikin shi.
A ranshi yake raya cewa ,koma menene tarihin ta yayi alqawarin auren ta ,yayi alqawarin kasancewa da ita har abada ,ze zame mata shamaki kuma tudun dafawa sannan abun godogo...

"Insha Allah"... Shine abunda Umar faruk ya furta can k'asan mak'oshin shi...

Seda Binafa tayi kuka me isar ta, jin kanta ya fara sarawa yasa ta dan fara tsagaita kukan... Kan ta a k'asa tana sauke ajiyan zuciya kamar wacce akawa dukan tsiya.

Ankishif ya mik'a mata ,tasa hannu ta karb'a tana goge fuskanta jiki babu k'wari. D'akin ya kasance shiru nad'an wani lokaci. Kafin Binafa ta fara magana cikin sanyin murya ...

" *BAN YI NADAMAN* abunda nake aikatawa ba ,hasalima ban tab'a *NADAMA* ba ,ba kuma zanyi Nadama ba har abada"... Girgiza kai ta shiga yi tana ci gaba da cewa

"Wllh Allah ma naso na daya banni iya haka, ina tare da Allah sa kariyar shi a duk inda na shiga ,badan haka ba ni nasan da k'ilama bana rayuwa a wannan duniyar. Nasan Dana dad'e da barin wannan wahalalliyar duniyar me tattare da k'unci da kuma k'alubale.

" A da nayi tunanin nida farin ciki munyi hannun riga !...,nayi tunanin nayi bankwana da salama !...nayi tunanin kwanciyan hankali ya k''aura mun!... Nayi tunanin bani ba jin dad'in zaman duniya!... Nayi tunanin bazan sake rayuwa me dad'i ba!...

Murmushi binafa tayi wanda yafi mari ciwo sannan taci gaba da cewa


" tun bayan fitowa na daga gidan kurkuku ,bana ganin akwai wata Sana'a wacce ta dace dani sama da sana'ar karuwanci "...


Zaro ido Umar faruk yayi a lokaci daya kirjin shi ya tsananta bugawa, kalaman Binafa se yawo suke mai a k'wak'walwa ,haka yake jinsu kamar saukar aradu...


Binafa kasa ci gaba tayi da magana saboda wani sabon kuka daya zo mata. A cikin kukan taci gaba sa cewa


" mu 'yan asalin k'aramar hukumar kubau ne dake jahar kaduna. Mu 8 agun mahaifiya ta ,yayin da agun mahaifi na mu goma ne. Nice ta had'u a haihuwa.


Mahaifi na sannan mutum ne me yalwar dukiya sannan kuma mutum ne me dattago ,sedai Sam wani b'angare na rayuwar shi abun k'yama ne. Mutum ne Wanda Allah ya wadata, se kuma yake ganin kamar dabarar shi tasa Allah ya bashi ,ya manta Allah "kun faya kun ne" shi yake yi yadda yaso kuma a lokacin daya ga dama...


Mutum ne shi be son kanshi da biye k'agaggen karatun zuciyar shi. Da mahaifi na aka d'ana mun tarkon daya kusa zama sanadiyyar raba ni da rayuwar danake a yanzu!!!!....


Cikin mamaki da firgici Umar faruk ya tambaye ta

"Me sunan larabawa kinsan me kike cewa kuwa ?... Anya haka ze tab'a yuwa??!... Kina tunanin uba ze haifi 'ya ta cikin shi kuma ya zama sanadin raba ta da duniya...???"


"Shakka babu " Binafa ta bashi amsa ,sannan taci gaba da cewa

"" k'warai kuwa me sunan manya ,saboda ya faru akaina. Da mahaifi na aka had'a baki wajen kashe ni!!!"


Dumm!!!dumm!!!! Umar faruk yaji gaban shi ya fad'i. Ya furta can kasan mak'oshin shi


"Kisa!!!kisa!!!


" why and how ?" Ya tambayi kanshi...







Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE4⃣1⃣➡4⃣2⃣*



Haka Binafa taci gaba da bama Umar faruk tarihinta kamar haka

"Kamar dai yadda na fad'a ma mu 'yan asalin k'aramar hukumar kubau ne dake cikin jahar Kaduna.

Mahaifi na me suna ALH. IBRAHIM ARILLE yayi aure da mahaifiya ta me suna HAJ. BINTA shekaru talatin da d'ori baya. Alhamdulillah na tashi cikin peaceful family sedai abunda ba'a rasa ba...
Sosai suke zaman su lpia da kaunar juna. Dukda hali na rashi da suke ciki hakan be Shafi zaman su ba.
Mahaifiyar mu macece me zafin nama da k'ok'ari wajen neman ,koda yaushe bata rabo da saida k'walama-k'walama na yara ,hakanne ma yasa har ake kiran ta da *MAMAN NAIRA* ...


A haka har suka haifi babbar yayar mu anty Hindu ,bayan ita umman mu ta sake haihuwan wani yaro sedai bezo darai ba ,sannan ta haifi yaya imran se ni saudat. Nice ta had'u a haihuwan gidan mu...
Koda yaushe addu'an iyayen mu shine Allah ya yassare musu ya hore musu abunda zasu d'au nauyin mu dashi, saboda wani irin rashi daya same su a wancan lokacin. Babu ta d'aura aure dasu. Randa aka samu aci randa kuma ba'a samu ba ayi salatin annabi akora da ruwa akwanta...


Abinci ma ba koda yaushe muke samu ba ,se ayi kwana da kwanaki ba'aci ba. Duk kuma randa za'a yi girkin to badai aci so ukku a rana ba a'ah, basa cin na safe sedai ayi kona rana kona dare.

Randa ko akace an dafa taliya tofa ranar su 'yan gayu ne ,baki har kunne. Idan anty hindu taga yaya imran na handama zakaji tana ce masa "wawa karka cinye duka ka rage mu b'oye koda gobe ba'a dafa mana wani ba se muci". Idan akayi sa'a Umma taji su haka zata shige d'aki taci kukan ta kamar ba gobe a ranta take k'ara tausayin halin da muke ciki...


Ni kaina ba wani isash-shen ruwan nono nake samu ba ,saboda Umma na bataci wani abun kirkin dahar ze isheta ba balle ni in samu, toma ba abinci ta ina ruwan nono ze samu?... Haka zanta kuka tana lallashi na ,wataran idan tana da ishirin ko goma sedai ta aika asiyo mun koko ,shima ba suga haka zata bani shi...

Sannan kasan Yaro be San babu ba ,shi kawai abashi yaci yasani. Haka watarana anty Hindu da yaya imran zasu ta kukan sun yunwa suke ji, idan Umma taci suna shirin Tara mata mak'ota haka zata tashi taje daji tayo yaye-yaye na kara tazo takunna ,kar kuma kace wani abun zata dafa ,kawai ruwa zata d'ora suyita dahuwa ,Dan kawai ta b'atar musu da hankali se kaji tana ce musu " to kuyi hak'uri gashi nan na d'ora yanzu ze dahu. Nan fa zasuyi ta murna suna jin dad'i. Bini-bini zasu ce su dafa ta suna tambayan ta abincin ya dahu ? Tace ya kusa,,,,, a haka har bacci ya kwashe su...
Tun tana musu haka har suka fara gano takunta. Ranar ta d'ora ruwan ta shiga ban d'aki ta kama ruwa, yaya imran yaje ya bud'e tukunya a zaton shi yaga abincin yana dahuwa kamar yadda Umma tace musu amma se yaga ruwa kawai ,nan fa ya fad'i kasa yanata murje murje yana kuka aifa ba'a Ankara ba nan tukunyar ruwan zafin ta biyo shi, se gashi tsamo-tsamo cikin tafasash-shen ruwan zafi ,aifa ihun shi da Umma taji yasa ya fito ba shiri ,ganin shi kwance a k'asa ga tukunya akanshi yasa Umma yadda butan hannunta ,ba shiri tayo kanshi da gudu itama ihun take ,nan ta shiga Neman taimakon mutane ,cikin k'ank'anin lokaci fatar shi ta kwaye ,duk Wanda yagan shi seya zubar masa da hawaye. Gashi basu da kud'i balle akai shi asibiti ,zumar ma da ake shafa masa wata mak'wabciyar suce ta bada ,to shima tunda ya k'are shiru ba wani labari.
Da daddare baya iya wani baccin kirki, haka ze d'ora hannun k'onanne akai yayita kurma ihu "wayyo hannu na!!!wayyo hannuna!!!" Kusan kullum ahaka suke kwana ido biyu. Wani babban tashin hankalin ma be wuce da Umma taga yatsun yaya imran a had'e ba ,gaba d'aya sun had'e da juna yadda kasan kuturu.
Ranar wani abokin mahaifin mu yazo duba shi, nan yake gaya musu ,idan basu tashi tsaye akan hannun yaya imran ba hannun ze iya rub'ewa. Hankalin kowa inyayi dubu ya tashi, nan suka tambaye shi menene mafita? Yace akwai wani me bada maganin wuta ana ce masa shegen gaye ,sosai maganin shi ke aiki ,Ku jaraba ko za'a dace. Nan Abban mu ke tambayan shi ya za'a yi su same shi ? Yace ba wani Abu bane me wahala sudai aje kud'i insha Allah zesa a nemo musu shi nanda sati daya zasu dawo tare. Umma ce ta tambaye shi kamar nawa? Yace naira dubu hud'u ne ba tsada!


Nan fa hankalin su ya tashi ,jin kudin da Malam bala ya kira musu ,Umma tace "mun shiga ukku ,yanzu a ina zamu samo wannan zunzurutun kudin malam? Ta tambayi Abban mu ,nan yace mata " insha Allah baza'a rasa yadda za'a yi ba ,ai Allah na nan kuma be manta dasu ba." Sallama malam bala ya musu ya tafi abunsa akan nanda sati ze dawo tare da me maganin.



Yau kwana shida saura kwana d'aya kamar yadda sukayi da malam bala. Amma sun buga sun buga kota ina shiru kake ji. Ana cikin wannan yanayin ne k'anin Umma dake kudu acan yake kasuwancin shi, ya kira a wayar mak'wab'ciyar ta Dan dama tanan suke waya ita bata da waya ,ta siyar tun lokacin da anty Hindu tayi wani ciwo gashi basuda kud'i to lokacin ta saida wayarta...


Bayan sun gaisa yake tambayan ta ko akwai wata matsala ,shiru Umma taki ce masa komai Dan bata so ta takura shi


Jin tayi shiru yasa ya gane akwai matsala, nan ya sake tambayan ta" Anty menene? Gayamun Dan Allah ". Umma na kuka dukta rattafa masa halinda ake ciki, sosai yaji tausayin er uwar tasa yace insha Allah zeyo mata aike gobe taje tasha ta karb'a da yamma... Nan tayi masa godia sannan sukayi sallama.


Washe gari kuwa akayi sa'a malam bala basu zo ba seda yammaci bayan Umma taje ta karb'o sak'onda baba tukur ya aiko mata. Da farin ciki ta shigo gida wani almajiri na biye da ita da kaya a baro, lokacin Abban mu na zaune rik'e da yaya imran ,nan ta shiga nuna masa irin abun azzikin da baba tukur ya aiko ,taliya ce kwali d'aya, masara tiya biyar ,gero tiya biyar ,shinkafa jiya ukku ,se kud'in cefane naira dubu biyu ,banda kud'in maganin yaya imran dubu hud'u, ga kuma waya k'irar Nokia ya sanyo mata layi a ciki . Nan fa suka shiga murna Umma hadda hawayen ta, tana fad'in Dan uwa me dad'i... Yara kowa se murna yake hadda yaya imran dake cikin jinya ,anty Hindu se faman washe baki take tana fad'in" yeh muma mun zama 'yan gayu"...


Farin ciki ne kwance a fuskan Umma ganin yadda yaranta kowa ke cikin farin ciki. Ana gabda magriba mlm bala yayo sallama, nan ya sheda musu tare yake dame maganin, nan Abba yace masa su shigo ,bayan sun gaisa aka kawo masa ruwa yasha sannan yace a mik'o masa yaya imran, Abba ya mik'a sa. Kallon hannun yayi nadan wani lokaci sannan ya fara Aikin shi, seda ya kwashe fatar hannun tsaf ,yaya imran se kuka yake kamar ze shek'e Dan azaba hadda suman shi ,tausayin shi yasa kowa se kuka yake musamman umman

Please Login or Register in order to submit comment