Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata ba.


Satin su Umma biyu suka koma tare da Binafa. Inda Binafa ta sake bud'e sabon shafin shanawa. Ga honourable Adamu daga dama se comrade daga hagu. Dikkan su sun rike mata kan maciji tana wasa da wutsiya.


Binafa tayi amfani da wannan daman ,ta gayawa Umma cewa ai honourable Adamu ya bata kyautan gida da mota a legos. Wanda kuma bashi ne ya bata ba, wannan gidan ne da honourable ya bata lokacin da tayi practical a legos.


Takaddun ta d'auko ta dankawa Umma. Sosai Umma ta girgiza ido ta kara gogewa Dan ta gasgata abunda take gani. Sosai Umma tayi farin ciki harta ce akira mata shi tamai godia. Ba musu Binafa ta kira shi tare da mika mata wayan. Godia Umma ta masa bayan sun gaisa, akan sun gode da dawainiya allah ya kara daukaka. Honourable Adamu kuwa be kawo komai a ransa ba. Tunda iya alkhairi yanawa Binafa. Se yayi tunanin ko akan karatun tane daya ce ya dau nayi.



*BAYAN WATA BIYAR*


Da gama makarantan Binafa. Yanzu ta dena zuwa lagos ,sedai ta tura kudi a turo mata kaya. Kasuwancin se Dada hauhawa yake. Dan yanzu har kwatano da onicha Umma ke zuwa wajen saro kaya. Inda uncle idris kanin Umma ke tafiyar da business din, Dan Kuwait babban kati Binafa ta bud'e a cikin garin abuja, Wanda ta bama uncle idris manager a wajen , duba da ya gama poly amma har Yanzu ba zancen aiki kuma be ci gaba ba. Ba kad'an ba Binafa ke jin dadin business da uncle ba.

Yanzu ba kano ,Abuja da bauchi kad'ai take tura kaya ba. Kasuwancin ya zaga jaha jaha.


Ganin yanzu ba ita ke tafiyar da kasuwancin ba yasa tace bari ta kawo k'arshen zaman kadaici. Dan jin tayi duk ta gaji da zaman bata komai. Inbanda Aikin receiving waya koda yaushe akan waya kamar 'Yar siyasa.


Me aiki ta sama wa Umma ta kula dasu musaddiq da twins ganin umman ba zama take ba ,uncle kuma yana shago wataran ma idan aiki yayi yawa a can yake kwana.

Yanzu ba kasafai take bin flight ba ,se idan tafiyar me nisa ne sosai. Tafiso taja mota. Sati d'aya ta shirya ta wuce Kano ....





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE2⃣1⃣➡2⃣2⃣*



Makaranta taje ta nemi a bata posting letter zuwa asibitin LUTH. Kafin result din su ya fito.
Bata wani sha wahala ba Dan kuwa a ranar data je a ranar ta kammala komai. Suka hada mata hadda statement of result. Dan dama ta Riga ta sanar dasu kafin tazo da abunda ze kawo ta.

Washe gari taje gidan su Smatcher. Taji dad'i sosai yadda ya taradda kasuwancin Smatcher na tafiya. Ita ma Smatcher taji dadin zuwan ta, bata so kwana a gidan ba amma umman Smatcher ta matsa mata dole seda ta kwana.


Washe gari da zata tafi ,bata bar gidan ba seda ta cika umman Smatcher da alkhairi. Haka tayita mata addu'a dasa mata albarka. Itama Smatcher da godia ta rakata. Satin ta d'aya a Kano ,ta wuce legos. A Kano ta yanke shawaran barin motanta ,tunda tanada wani a lagos. tickety ta yanka na jirgi tabi flight din safe ranar jummu'a.


Koda ta isa ,ba wani aiki tayi ba ,Dan ta riga ta sanar dame gadin zuwan ta ,kasancewar akwai extra makulli a hannun shi yasa duk ya gyara mata ko ina tas


Monday ta fara fita asibiti, sosai likitocin da sauran majinyatan lafiyan sukayi murna da ganin ta. A haka taci gaba da aiki dasu cikin kwarewa. Ganin yadda take jajircewa wajen yi musu aiki tukuru yasa har allowances suka fara biyan ta duk wata. Hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba.


Watan ta biyu da fara aiki a LUTH. Aka shirya wata seminar a jahar gombe na ma'aikata. Seminar na daya kunshi bangare da dama a fannin aiki. Kama daga manajoji, likitoci ,da dai sauran su. Wanda a LUTH suke shirrin tura BINAFA ta wakilce asibitin su.

Wanda kwatakwata ba tada masaniya akan hakan. Yau ma kamar kullum ta gama Aikin ta lokacin tashin ta yayi. Tana ta shirye shiryen fita, Sega sister rahama ta shigo ta sheda mata MD nason ganin ta. Ta tambaye ta

"Lpia kuwa?"

Sister rahama tace

"Gaskiya wannan karan ban sani ba ,amma dai kije koma menene aikya ji".

Tace " toh Allah yasa muji alkhairi ".

Bata wani bata lokaci ba ta kama hanyan office din shi. Knocking tayi ya bata izinin ta shigo. Ta murda kofan ta shiga. Gaishe shi tayincikin girmamawa kamar yadda ta saba. Ya amsa mata fuskar shi dauke da fara'a tare da nuna mata waje alamar ta zauna. Haka ta zauna tana jiran taji kiran me ya mata.

Hankalin shi ya maida kan computer din da ke kan desk dinshi yaci gaba da Aikin da yake. Yafi 30mins sannan ya kalli BINAFA data gama kulewa ,wani envelope ya d'auko akan table din shi ya mika mata. Hannu biyu tasa ta karb'a tare da kallon shi, ganin bata bud'e ba yasa ya kalleta tare da cewa


" zaki iya bud'e wa"...

Ba musu ta bud'e tana dubawa. Seda ta gama ta kalle shi dauke da mamaki a fuskanta. Ta furta a sanyaya

"Dr wannan fa?"

Yace

"Me kika gani?" Ya furta kamar bashi ya shirya komai ba.

Tace

"Naga kamar seminar, kuma sunana ne akai?" Ta karashe maganan alamun tana Neman Karin bayani

Kallon shi ya maida kanta ,ya zare glasses dinda ke manne a idon shi ya aje a gefe. Ya fara mata magana cikin natsuwa.

"Binafa!!!" Ya kira sunan ta in a low voice

"Na'am Sir"
Ta amsa shi a sanyaya ,yaci gaba da cewa

"Abunda idon ki ya gane miki no doubt, is a seminar, Wanda za'a gabatar a gombe 2wks coming insha Allah. Sannan za'a yi shine har tsawon wata d'aya.
Na zab'e in tura kine sanin ke din me kwazo ce ,nasan ki sarai ba kida wasa sannan kinada maida hankali da daukan Abu da muhimmanci. Sanin kanki ne muna da professional Doctors da zamu iya turawa. Amma na zabi in tura ki. Da fatar bazaki bani kunya ba?"


Ba yadda binafa ta iya, dukda cewa bata so tafiyan ba. Cikin ranta take cewa. "Lallaima wannan likitan dan rainin sense ne ,wato be sanar dani ba seda ya gama shirya komai, sannan ze wani kashe ni da dadin baki, ba yadda na iya tunda ka Dora mun kamaya-maya Dan banzaru". A fili kuma murmushi tayi tare da cewa


" Bakomai sir. Insha Allah zanyi iya bakin kokari na. Sedai kuma naga kamar matakin karatu ne bekai ba aiko?"

Yace

"No dear. Is not about da qualification, is all about experience, hope u got me right?"

Kai ta daga mishi alamun ta fahimta. Sannan yace

"Good gurl" . wani kallon raini tamai ta gefen ido jin ya ce mata gurl. Ni kuwa nace kaji binafa da son girma kamar *Aufana* ,kila woman take so yace lolz😂


Wani envelope din ya sake mika mata ta karba yace

"Wannan kuma duk wani bayanai da zaki nema akan seminar yana ciki. Akwai kuwa check na two hundred thousand #200.000.0000 a ciki da suka turo a baki, na kudin hotel, transport da kuma abinci. Idan kina buk'atar wani abun zaki iya sanar dani!"

Tace

"Ohk sir" a takaice.

"Wish u d best of luck my dear."

Kanta a kasa ta amsa da

"Thank u sir"


Sannan yace
"U can take ur leave"


Dama ta kagara tabar office din. "A tashi lpia" shine abunda tace tare da barin office din.

A bakin kofar office din ta tsaya ,tana kara duba envelope din ,haushi duk ya gama kashe ta. Kwaikwayon maganan shi ta fara yi.

"Naga kina da nutsuwa ne ga jajirce akan aiki sannan kinada maida hankali kan Abu....yeeen...yeen....green. Baho duk yabi ya cika ni da surutu". Wani guntun tsaki taja sannan tabar wajen....




Share
&comments





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*Wannan page din naku ne masoya na na Facebook, ba kad'an ba nake jin dadin comments dinku. Har kullum karku manta kuna ran SIDIYA, kazalika tafiyar bazata taba yuwa ba idan ba ku. Ga masu bakuwar number na Dan nema na ta WhatsApp kofa a bud'e take 09064458468. SIDIYA na muku lale maraba. Kuci gaba da nuna mun kauna ta hanyar ci gaba da suburbude comments tare da addu'o'i. Allah yabar qauna...👌💋*




*PAGE2⃣3⃣➡2⃣4⃣*




Sannu a hankali soyayya me karfi ya soma shiga tsakanin BINAFA da SALIM ,ba kad'an ba yake nuna mata kulawa tare da yin duk wani Abu daya San zeyi winning Hrt dinta. Binafa ta kasa gane shin son salim take ko damuwa tayi dashi ,Dan wasu lokuttan ko ranta a bace yake idan ya kirata takan ji komai ya wuce.


Salim yasan kan shi ,haka gwani ne a iya rikita zuciyan 'yan mata ,ba kad'an ba salon shi ke burge BINAFA. Dukda seda yayi da gaske ganin ba wani damuwa tayj dashi ba. Ko kiranta yayi a waya shi kad'ai zeta surutun shi, wani lokaci tace mai tana aiki, Wani lokacin ma bata dauka. Kiran asuba daban, danshi ne ya koma mata kaman alarm ko bata dauka ba ze matsa mata da kira har ta tashi tayi sallah. Tana kaiwa wajen aiki to 8 text dinshi me dadi ze shigo da addu'an adawo lpia, tare da yi mata fatar yini cikin aminci. Wuyar shi karfe 10 tayi ze sake kira yaji yata isa ,yaji kuma ya aikin. Idan day tayi to 2 ze kirata yace lokacin tashi yayi, in kuma afternoon tayi 6pm ze kira suta waya harta karasa gida. Ranar kuma da take night to idan ta gama ji da patient kwana waya zasuyi har se ya tabbata ta fara jin bacci sannan ya kyaleta ta kwanta. Wasu lokuttan har mamakin irin kiran da salim ke mata take, se kace wanda beda abunyi.


Dan kanta ta fara gane cewa yanada kulawa. Kuma koba komai Wanda ya nuna ya damu dakai kaima ya kamata ka damu dashi. Wani lokacin haka take jin tana kewar shi musamman ma randa yake busy a wajen aiki, dukda duk yadda yake busy baya kin kiranta ko yaya ,amma jin ba'ai mata yadda aka saba ba ,duk seta damu, aifa ranar wuni tura ma juna text suke. Ga salim idan ya bugo wani shirmen yadda kasan Dan fari ,haka zata ta biye shi ,har ta gaji Dan shi baya gajiya...


Yau alhamis Wanda idan lissafi be bace mun ba tafiyar BINAFA ya rage saura kwana takwas


Da daddare bayan ta gama shirin ta na bacci tana kan system dinta tana research akan seminar da zata halarta a gombe. Kiran salim ya shigo wayarta daidai lokacin hannun ta ya kai daidai receiving call ,dariya ya kwashe dashi tare da cewa

"Woww yau wace rana? Ashe jiraye ake dani ?, aiko naji dadi an dena mun Jan ajin nan ,Dan idan na kira naji baki dauka ba ji nake kamar zan kama da wuta"...

Wani murmushi mugunta tayi sannan tayi rejecting kiran. Jin shiru yasa ya gane ta yanke kiran ,seda ya kira kusan so ukku bata dauka ba se ana Hudu ta dauka shima seda ya kusa katsewa. Dauka tayi tasa a kunne tare da sakar masa murmushi, a bangaren shi shima murmushin yake.

" shine zaki kashe mun waya ko ,kuma kinsan bana so"?

Taci cikin muryarta me daukan hankali

"Amma ULFAT so nawa nake gayama ka saba da sallama Dan Allah".


" kash " ya furta tare da dokan goshin shi ,ya shagwabe !murya kamar zeyi kuka yace

"Amun afuwa my baby doll. Wllh mantawa nake ,Dan Allah kiyi hak'uri. Zan dingayi insha Allah, fatar bakiyi fushi ba?"

"Nayi " ta bashi amsa a takaice.

Kukan shagwaba ya fara mata ,yana magiya haddasu cewa idan bata hak'ura ba ya dena cin abinci.

Yanayin yadda yake magana ba k'aramin dariya ya bata ba. Cikin ranta take cewa

"Ji wannan katon banzan don Allah yadda yake wani narkemun kamar wani Yaro. Yo idan ma bakaci abincin ba cikina ko cikin ka. Dan bantan uba ulcer tasan yadda tayi dakai".

A fili kuma tace

" wa ni na isa. Aiba a fushi da me gida takobin daga. Yo kai idan ba a rashin sani ba taya karen gwauro ze kori bazawara!"

Dariyan shima yake Dan BINAFA badai Karin magana ba. Yace

"Baby na nayi missing dinki fa"

Tace

"Nima haka"

Yace

"Amma ba kamar niba. Dan Allah ki daure ki soni ,koda rabin sonda nake miki ne ,bazan iya ba idan bake, rayuwata is useless wit out u, baby na pls..."

Murmushi tayi tare da ajiye system dinda ke kan kafanta ,ta kwanta kan gadon tana sauraren yadda muryar shi me dad'i ke ratsa kunnuwanta. Tace cikin sigar zolaya

"Na tsane ka "


"Wash... Wai so nawa zan gaya mk hakan k'aramin sonki yake? I love u my Hayat".

Dikkan su dariya suka sa ,seda suka raba dare suna shan love sannan sukayi sallama...


Washegari ranar jumma'a ya kama saura sati daya BINAFA taje gombe kuma a ranar ya kamata ta dena zuwa aiki Dan maida hankali akan seminar da kuma yin shirye shirye. Misalin karfe 8 na safe ta shirya taje asibitin Dan karban takaddan izini. Lokacin data aje mota daidai lokacin MD ke fitowa daga tashi hadaddiyar motan kiran Bugatti.


Murmushi ya sakar mata ta maida mishi ,cikin girmamawa ta gaishe shi ,fuskar shi a sake ya amsa mata. A tare suka jera suka k'arasa cikin asibitin. Kai tsaye office dinshi suka nufa. MD kamar ya nutse k'asa Dan murna.

Seda suka kammala dikkan wani tsare tsare akan tafiyan ta ,sannan ya dauki wani hadadden envelope ya bata. Kallon shi tayi tare da cewa

" wannan fa? shima dik akan tafiyar ne?"

Yace
" aah wannan ma zan iya cewa kusan yafi tafiyar muhimmanci ,amma ki bari ba'anan ba idan kin isa gida zaki iya dubawa ".

Da mamaki take kallon shi ,kai ya daga mata alamar " eh". Bata wani jima ba tamai sallama. K'arasa wa tayi cikin asibitin tawa abokan Aikin ta sallama su sister rahama. Se wajejen 12pm ta baro asibitin. Kai tsaye restaurant ta wuce Dan jin tayi kota koma bazata iya girki ba.

Koda ta isa gida ,bata bi takan envelope dinda MD ya bata ba ,sallah kawai tayi tai wanka tabi lafiyan gado.... Se wuraren la'asar ta farka....





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE2⃣5⃣➡2⃣6⃣*



Yau ya kama Saura kwana biyu BINAFA ta wuce gombe. Shiri ta fara yi Dan tana so ta biya taga umman ta kafin ta wuce. Ta kammala shirin ta tsaf tana zaune ta tuna da envelope din da MD ya bata ,tashi tayi ta janyo bedside drawer ta d'auko envelope din. Se kuma taji ta kasa bud'e envelope din. Tafi minti 30 a haka se jujjuya envelop din take a hannun ta. Kafin ta warware zaren dake zagaye da envelope din, ta bude takaddan a hankali ,ta fara karanta sakon dake ciki kamar haka...


_"Assalamu Alaikum warah matullah wa baraka tuhu. Bayan gaisuwa irinta addinin musulunci ,godia ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad S.A.W_ .

_Kin cancanci a soki Binafa saboda kin cika dikkan wani nau'in dabi'u na mace ta gari Wanda ko wani namiji ke kwadayin samun ta a wannan duniyar. Na kasa jurewa ,bazan iya hak'uri da juriyar rasa kiba, bazan bi kagaggen karatun karyan da zuciyata ke karanto mun ba na katange ni daga soyayyar ki. Ki daure ki sama min matsuguni a zuciyar ki_ ...


_Ki sani ,Hakika zuciya bazata daina tunanin kiba, kasantuwarki ma'aboci addini da dukkan wani nau'in dabi'u na gari_ ...

_Mantawa dake wani abu ne mai matukar wuyar fassara, rashin ki Kuma babban barazana ne agare ni._

_Zuciya ta bazata daina fatan alkhairi agare kabi ,da fatan kasancewa da Wacce zata kasance dalilin wanzuwar farin cikin taba, Kuma dalilin shigarta aljanna insha Allah_ .

_Ina matukar matukar qaunar ki farin ciki na. Da fatar ,zan samu karb'uwa a wajen ki da addu'an Allah yasa wani be Riga niba_ ...

_Daga me qaunar ki a koda yaushe... Muhammad sani MD. Ki zama cikin aminci a duk inda kike_ ..

_Ma'assalam..."_


Tunda Binafa ta fara karanta sakon MD gaba d'aya jikinta yayi sanyi. Se ta samu kanta cikin nazarto MD da kyawawan halayen shi.

"Tabbas kanada kirki ,kuma ka cancanci a soka MD" ... Ta furta a sanyaye tare da maida kanta ta kwanta tana kallon sama. Wayanta ta janyo da niyyan kiran shi ,se Kuma ta tuno da salim, jifa tayi da wayan nan take hawaye suka fara bin fuskanta tana fadin


"No...no.. I can't"... Se kuma ta fashe da kuka, Wanda ita kanta bazata ce ga dalili ba. Daga gefe ta hango wani hadadden zoben azurfa , da alama daga cikin envelope din ya fad'o. Tashi tayi ta d'auko zoben tana kare mai kallo. Ta furta a sanyaye

" wat a beautiful ring",,, Saka zoben tayi a Dan k'aramin yatsanta na hagu, tare da sunbatar zoben... A haka bacci yayi awon gaba da ita...


Washe garin asabar da asuba ta wuce abuja. Sosai taji dadin yadda taga umman ta da kannen ta cikin walwala ,ba wata damuwa a tare dasu. A bangare d'aya kuma kasuwancin su se dada bunkasa yake.

Kwana daya tayi ta wuce gombe. Tana isa wani hotel ta samu me kyau tayi parking motan ta a inda aka tanada Dan aje motoci, daidai lokacin da wata hadaddiyar motar k'irar EOD ke pakawa daga gefen ta...


A tare suka fito. Wani nutsats-tsen magidanci magidanci matashi matashi ne ya fito a motan ,saboda shidai ba yaro bane ,ba kuma za'a kirashi da babba cancan ba.
Tsayawa yayi yana k'arewa Binafa kallo, ita ma kallon sa take. Murmushi ya sakar mata ta maida mishi. Sannan ya mata sallama ,amsa mishi tayi tare da gaishe shi. Sannan suka kama hanyan reception din hotel din Dan karban d'aki... Key din room 3 aka bata shi kuma aka bashi na room 4... Sannan aka had'a su da Wanda ze musu jagora.


Ita ta fara wuce wa ,suna isa ta kalli dakunan dake wajen sannan ta dubi makullin hannun ta. Kai tsaye room 3 ta nufa ta bud'e. Dakin kal dashi, wanka ta fara yi tai sallah sannan ta bud'e system dinta ta fara aiki akan seminar...




Comments
&
Share




Taku har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE2⃣7⃣➡2⃣8⃣*




Washe gari Binafa tayi shirin ta tsaf ta halarci abunda ya kawo ta. Sosai taji dadin wajen ,Dan koba komai ta kara samun experience akan abubuwa da dama, sannan ta had'u da mutane iri daban daban. Ba kad'an ba abun ya kayatar da ita ,dukda cewa wannan shine karo na farko a rayuwar ta data halarci irin wannan seminar din ,sedai kuma bata wani damu ba saboda ta saba da irin hakan, dukda wannan taron ya banbanta da Wanda aka saba tura ta a makaranta...


Ba ita ta dawo ba se karfe shida na yamma, seda ta biya restaurant taci abinci sannan ta koma masaukin ta.
Gajiya ne sosai a tare da ita ,hakan yasa tana shiga kai tsaye toilet ta fad'a tayi wanka sannan ta gabatar da sallan magrib.
Karatun alqur'ani tayi har aka kira isha sannan tayi sallah ta kwanta.


Haka tayita fama da seminar kullum bata dawo wa se shida na yamma.
Duk lokacin da tazo fita idon Alh Umar faruk na kanta. Ba kad'an ba Binafa ke burge shi, musamman daya karanci yarinya ce me natsuwa.
Duk lokacin da ya dawo daga masallaci sallan asuba da sallan magrib yana yawan jin karatun ta, wasu lokuttan ma har yakan tsaya ya saurare ta, har cikin ranshi yake jin dadin karatun ta.
Sosai ya karanci Binafa Nada addini daidai gwargwado, hakan yasa ta kara shiga ranshi ...


Koda yaushe yana so yadan samu zama da ita amma ganin bata cika zama ba yasa yadan daga mata k'afa, dukda wasu lokuttan idan tazo fita akayi sa'a shima se fita sukan gaisa. Haka yayita kokarin ganin ya samu kusanci da ita.


A hankali kuwa har suka fara sabo dashi ,tun bata sakewa dashi ,har ta fara bashi fuska. Sautari sunfi haduwa a garden din hotel din su sha hira abun su. Wani lokacin kuma idan akayi sa'a sun dawo a tare. Sosai Binafa ta yaba da kirkin Umar faruq. Ba shida girman kai ko kad'an ,gashi da nuna kula da mutum. Saboda wasu lokuttan idan yaga sun kwana2 basu had'u ba ,har leqata yake yaga ko lafiya har yadan zauna suyi hira...


Sedai wani Abu d'aya dake bashi mamaki da daure mishi kai shine ,yadda koda yaushe ake zuwa wajen ta ,tun yana tunanin samarin tane ,har ya fara zargin ta. Saboda wani sa'in ma kamar bazata dawo hotel din ba ,yana jin shigowan ta 10 ko 11 na dare. Ba kad'an ba sha'anin ta ke damun shi. Haka kawai yaji yana so yasan ko ita wacece.


Kusan watan Binafa d'aya a gombe tana tafiyar da Aikin da ya kaita yadda ya dace. MD na yawan kiranta a waya suyi hira. Kuma sosai take jin dadin yadda yake nuna mata kula da yadda yake jinjinawa namijin kokarinta. A bangaren salim ma haka yake tarainiya da ita kamar ze had'e ta Dan tsabar kauna...


Yanzu ta rage waya da honourable, saboda har yanzu be dawo kasar ba ,kuma koda yaushe busy yake a can ,se idan yadan samu sarari ne yake kiranta su Dan taba hira ,shima ba wani jimawa

Please Login or Register in order to submit comment