Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abun se Wanda ya gani.

A haka ta k'arasa bakin motar tana wani karairaya tana k'arawa ,se wani lankwashewa take kamar ta na. Mota ta bud'e ta shiga ,cikin karya murya tace


"Amincin Allah yatabbata ga zuciyar da bata fushi balle tai yaudara.Sallama irinta addinin musulunci wadda farkonta rahama,tsakiyarta aminci, karshenta albarka. akoda yaushe sadaka na maganin masifa,gaisuwa nakara zumunci,Sannan kuma zumunci nakaiwa ga hanyar aljannah. Da fatar na samu Rabin raina cikin koshin lpia kamar yadda nabar shi?"


Ai Alh Aliyu besan lokacin daya saki wani murmushin jin dadin kalaman Binafa ba. Ba tareda bata lokaci ba ya fizgi motar cikin shauki ,suka bar wajen...





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE7⃣➡8⃣*




Washe gari da safe Alh Aliyu ya dawo da Binafa gidan Aysha bayan ya cika ta da alkhairai. Banda tsabar kud'i daya bata. Seda ta kwana biyu a gidan Aysha sannan ta koma makaranta. Sati d'aya da komawarta ta samu har ankusa fara jarabawa, ga C.A da akayi duk bata nan ,banda assignment da presentation datayi missing. Ko kad'an banga alamun damuwa a tattare da itaba. Wani guntun tsaki kawai taja

"Mtssss, nasan wannan jarababben lecturer nne kawai ze bani matsala, Dan ba kirki ya ishe shiba". Can kuma se ganin nayi ta saki wani shu'umin murmushi alamar tasan yadda zatayi dashi. Binafa mace ce wacce ta amsa sunan ta ,akwaita da wayo ga dabara ,ta iya kirfa ,salo da kissa iri daban daban ,cikin kankanin lokaci idan ta zauna da mutum se yaji ta burge shi. Gashi tana da shiga rai da saurin sabo.


Ba tada matsala da kowani malami a school din ,dikkan malaman tanada kyaky-kyawar fahimta dasu. Inbanda H.O.D din X-RAY( Radiation), shima akwai chakwakiya ne a kasa tsakanin ta dashi ,amma ga dikkan alamu ta gano hanyar dazata yi dealing dinshi. Ba bata lokaci ta fara kiran Malam daya bayan daya tana kashe su da dad'in baki ,Dan dama makaranta tasan da tafiyar ta kamar yadda ta gaya musu zata je ganin mahaifiyarta ne batada lafiya. Kuma bata wani sha wahala ba suka yarje mata.
Tayi sa'a kuwa cikin sati daya ta had'a dikkan wani C.A da tayi missing banda na malam ja'afar ,da alama akwai shirin data ke masa.


Sauri sati daya su fara exam din first semester 200L a karkashin course dinda take karanta wato DENTAL SURGERY TECHNICIAN a school of Hygiene dake garin Kano ta dabo. Gaba d'aya ta kashe wayoyinta ,Dan ta samu maida hankalin ta kan jarabawa. Tana son nishadi amma hakan be hanata karatu ,bata taba Carry over ba dukda shaashancin data sa a gaba ,Wanda take da manufa da aikata hakan ,kuma koda yaushe fadin take bata NADAMAN abunda take aikatawa ko daida kwarazzarra.

Cikin sati biyu suka kammala exam din su ,a ranar data yi last paper a ranar tabar garin. Legos ta wuce ya saro kaya ,kama daga lace ,atamfa ,materials, takalma ,Dan kunnaye da dai sauran su. Satin ta daya a lagos tana siyayya ,kafin ta wuce Abuja can wajen ummanta.

Koda ta isa da murna ummanta ta tarbe ta ,musaddiq baya nan se su twins ne ta samu suhail da sultan wa'yanda sune little brothers dinta da basu wuce 2yrs ba. Da murya suka fata jikinta suna mata oyoyo da muryarsu da wani fita yake sosai ba

"Oyoyo anty... Oyoyo anty..."rumgume su tayi ,tana dariya tace

" wai Umma me kike bama yaran nanne naji sunyi nauyi haka ,jifa kamar zasu karya ni" . dariya ummanta tayi tare da cewa

"Aah fa bana son sharri, ina suka ga girman da zasu wani karya ki?"

Tace

"Umma wai kinji nauyin su kuwa?" Ta karashe maganan tana dariya. A haka suka k'arasa ciki ,nan yara suka shigo mata da kayan ta. Hand bang dinta ta bud'e ta ciro chocolate dinda ta siyowa su suhail ta basu, da murna suka karba

"Thank u aunt".. Suka ruga waje da gudu. Dariya tayi ta maida dubanta ga Umma tace

" Umma bari indan watsa ruwa se in fito mu bud'e kayan ki gani!" Tace

"To shikenan ".. Tashi tayi ta ida shiga da kayan ciki, ita kuma Binafa toilet ta fada tayi wanka ,ta fito tayi sallah ,tasa kaya. Abincin da Umma da aje mata tadan bud'e taci ba lefi ,saboda favourite dinta kenan ,tuwan shinkafa vegetable soup. Seda ta gama sannan suka shiga bud'e kayan.

Umma se yaba kayan take ,musamman da taji farashin su ,tace

" gaskiya kaya sunyi kyau ,gashi ma naga kayan sun sauko?" Ta karashe maganan tana d'auko wani pink material. Binafa tace

"Aikam kaya an samu rahusa,takalman daine suka Dan daga suma ba wani sosai ba".

Nan ta shiga zayyanawa Umma farashin kayan, Umma na rubutawa Dan karta manta ,seda suka gama sannan ta maida duban ta ga Binafa tace

" Yauwa kinga ma na manta ban gaya miki ba ,an had'a sauran kudaden na wancan kayan ,idan kin tashi tafiya seki karb'a ".

Binafa tace

" OK to hakan Nada kyau amma kibar su kawai a hannun ki ,ni bana buk'atar komai".

Hira suka Dan taba da Umma har take cemata

"Kinga kuwa na manta ban gaya miki ba ,malam ya aiko mun zancen kud'inda Abban su suhail ke badawa, wai har yasa k'ara kotu cewa a bashi 'ya'yan shi danya gaji da bata kudin ciyar dasu"

Cikin mamaki Binafa ke kallon Umma. Se kuma ta fashe da kuka tana fadin

"Wai Umma me bawan Allah nnan ke nufi damu ne ,meyasa baze kyalemu muci gaba da rayuwar cikin jin dad'i ba ,meyasa yake bibiyar mu da mugun nufi ne haka ,ya barmu ,ya fita a rayuwar mu kamar yadda ya nema"... Ta k'arasa maganan tana kuka me ban tausayi.

Umma bata iya cewa komai ba ,se wani ajiyan zuciya data sauke..









Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE9⃣➡🔟*




Umma bata hana Binafa kuka ba ,Dan tasan ba k'aramin kunci da barazana suka fuskanta ba a rayuwar su na baya. Binafa seda tayi kukan me isanta. Kanta taji ya fara sarawa ,yasa ta tashi taje ta wanko fusktarta tareda dauro alwallah. Nafila tayi ,ta janyo wayarta Qur'an app ta bud'e ta fara rera karatun alqur-ani cikin muryarta me sanyin dad'i. A hankali taji ta fara samun natsuwa ,Ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita.

"Washe gari da safe ita ta shiga kitchen ta had'a musu break fast. Ta shirya musaddiq da twins cikin school uniform ,ta had'a musu lunch box dinsu. 7:30am uncle idris ya shigo(kanin umma kenan) , lokacin Umma na toilet ,nan ta gaishe shi ,tareda sheda mai sun shirya ,dake shike kaisu makaranta. Suma yaran gaishe shi sukayi. Yace

" to Ku taso mu tafi ko? Lokaci na tafiya kar kuyi latti". Ya k'arasa maganan yana duba agogon hannun shi. Kallon shi Binafa tayi tace

"Uncle break fast din fa?" Cikin sakin fuska yace

"Bari sena dawo bana so muyi latti ne. Kai Ku taso muje" ya k'arasa maganan yana mikawa su twins hannu. Rakiya binafa ta musu har gate sannan da dawo ciki ta fara gyaran inda suka bata. Umma na fitowa jin bata jin motsin kowa ba yasa ta fitowa parlour, taga Binafa nata aikace aikace ,gaisawa sukayi kafin tace

"Badai har sun wuce ba?"

"Sun wuce uncle ya shigo ya tafi dasu".

" aikam kin kyauta ,Dan danice dasuka raina ,da har yanzu muna nan muna drama dasu, se nayi da gaske suke tafiya ,, Dan ma Idris baya musu wasa Aida nasan wataran ma makarantan bazasu je ba". Binafa murmushi tayi Wanda ke k'ara fito da kyawun fuskarta tace

"Aiko gara a dage musu. Ba wani gata da za'a basu daya wuce karatun nan. " magana take tana aikace aikacen ta ,maida duban ta tayi ga Umma tace

"Yauwa Ummu ya kamata muje kasuwa ,Dan naga kamar wasu abubuwan na kitchen sun kare (kayan abinci take magana). Kinga idan uncle ya dawo seya kaimu ,Dan ba jimawa zeyi ba ,kinga ko break fast beyi ba yace mun seya dawo baze jima ba".

Tabe baki Umma tayi tace

" wa badai idris din ba ,ai sedai muje zuwa anjima idan garin ya kara wayewa. Dan in kuwa idris zamu jira bazamu ba Ashe" dariya maganar yaba Binafa tace

"Haba dai Umma aize dawo kinsan baya wasa da cikin shifa" Umma tace

"Sedai kace kin manta waye uncle din naku, ai idan ya fice to kuma se an ganshi".

" lallai uncle" shine abunda binafa tace ,ta kara gaban Umma ta janyo stool dinda ke kusa da wajen ta Dora mata tea dinda ta had'a mata ,tare da toasted bread a plate ,tace

"Umma ga break fast dinki". Umma tace

"To sannu Allah yayi albarka". Binafa ta amsa da

" ameen".


Misalin karfe goma suka shirya zuwa kasuwa ,siyayya sukayi na kayan abinci sosai, Wanda duk a jakan Binafa kudin cefanen ya fito ,da Umma ta fito da kudi zata biya ,se tace aa ta bash-shi ita ta biya dikkan siyayyan da sukayi ,se wajejen azuhur suka dawo ,mota suka samu drop ta kawo su har kofan gida. Nan suka samu yara suka shigar musu da kayan cikin gida.



Satin Binafa 2 da zuwa Abuja ,amma bata nemi
ba gudun kar ummanta ta zargi wani abun. Ana haka aka kira su a school Dan su karb'i posting letter na practical dinsu. Seda ta k'ara sati sannan ta wuce Kano. A gidan Aysha ta sauka ,kasancewa mijin Aisha bame zama bane. Satin ta d'aya a Kano ,a ranar da zata bar Kano zuwa Legos Dan babban asibitin jahar ta cika wato LUTH. A ranar tayi wani new catch a jirgi. Tana zaune ta zura earpiece a kunnenta tana sauraren kira'ar mai shawiy. Idanuwanta a lumshe kamar me bacci ,knocking ya mata tare da sallama ,kamar bazata tanka ba se kuma ta bud'e ido tare da cewa

" yadai?" Da mamakin ta se cewa yayi

"Kamar seat dina ne kika zauna fa ko?" ,wani kallon rainin hankali ta wurga masa ,ganin alamun zata mai tijara yasa ya nuna mata seat number dinshi. Murmushi tayi tare da cewa

"Sorry". Ta matsa kusa da wannan seat din Ashe shine nata ,shi kuma ya zauna. Bata k'ara bi ta kanshi ba ,sedai taji a jikinta ana kallon ta ,kuma duk lokacin da zata dago se sun had'a ido, duk seta ji ta tsargu. A hankali yayi ta janta da fari harta Dan sake mai ,kafin jirgin su ya sauka a babban birnin Lagos. Da zasu tafi exchanging number sukayi. Kafin ta kira honourable ta sheda masa ta iso. Kasancewar baya kasar yasa ya aika mata da driver. Cikin mintuna kad'an driver yazo ya dauke ta. Ba taka burki a ko inaba se a wani Dan madaidaicin gida Wanda ya tsaru ,ginin zamani. Horn yayi me gadi ya wangale musu gate, ya shiga da motan.

Juyawa yayi ya bata makullin motar daya kawota ,tare da wasu makullan ya nuna mata tare da cewa

" Hajiya ga makullin motar ,Alhaji yace inbar miki ita a nan. Sauran makullan Kuma na gidan ne". Ta ansa shi kuma ya fice daga motan...







Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE1⃣1⃣➡1⃣2⃣*

Parlour-n ta bud'e, wanda yaji kushin's ,ga plasma Tv a bango, komai na parlourn ash colour ne ,taga komai neat ,tsarin ya mata kyau, ciki ta k'arasa ta bud'e wani daki ,taga shine bedroom din ,daki ne da yaji furnitures masu kyau, komai na cikin shi me kyau ne. Jakarta ta ajiye ,ta leka toilet shima a gyare tagan shi. Fitowa tayi ta shiga dakin dake kusa da Wanda ta fito ,se anan ta gane Ashe gidan 2bedroom flat ne. Se kitchen dake daga baya hadida store a ciki. Babu abunda babu a gida ,sosai tsarin gidan ya mata. Parlour ta koma ta shigar da kayanta dakinda ta ajiye hand bang dinta. Har cikin ranta taji dad'in yadda honourable ya karrama ta haka. Toilet ta shiga ta watsa ruwa ,koda ta fito ta samu missed call a wayanta ,Dan guntun murmushi tayi ganin honourable ne ya kirata ,saman gado ta fad'a tare da janyo pillow ta rumgume tam.
Dialing numbern honourable tayi ,bugu biyu ya dauka ,tare da fadin

"Ya dai sweety ? Gidan ya miki kuwa?

Murmushi ta sakar masa kamar yana ganin ta ,tace cikin kasalalliyar murya

" Komai yayi chocolaty na, ka gama mun komai, nayi matuqar farin ciki.". Ta karashe maganan tare da sakar mai Wani hot kiss

"Wayyo Allah na baby na banni haka... Haka aise kisa inkasa Aikin Dana je yi a Istanbul. Karfa kisa in dawo cikin satin nan. "


Cikin sigar shagwaba tace

"Haba dai chocolaty na ,ni bana son kabar Aikin ka. Ai muna tare ,kuma baka ce 2mnths zakayi ba? Ni kuma ina nan har 4mnth ..."

"Wow babyna harkinsa hankali na ya kwanta. Dan Allah ki kulamun da kanki ,ko magana ban yadda kiyi da maza ba koda drs din LUTH ne indai ba'a fannin aiki ba, kinji babyna?"...

Cikin kashe murya tace

" angama nawan. Kaima kasan ba wani idan ba kaiba. Ni se nake jin ma kamar saboda kai akayi ni. Wai kuwa kanajin abunda nake ji idan muna tare?"

"Aah baby na sekin gayamun?"

Ta kara narkewa tace

"Ji nake ba Wanda ya kaini sa'a a duniyar nan. A duk lokacin da muke tare wani dad'i da nishadi ne ke ratsowa tun daga cikin k'wak'walwa ta har tafin k'afa ta"

"Allah baby na?" Honourable ya bata amsa cikin jin dad'in kalaman ta

Tace

"Kwarai ma kuwa. Kaide ka bari kawai wani abun seka dawo. Amma yanzu bazaka gane ba".

Dariya honourable yayi na farin ciki har yana wani lashe baki yace

" an gama autar mata." Shiru ne ya biyo baya nadan wasu lokuttan kafin yaci gaba da cewa

"Wai kinsan ma menene?"

Cikin sanyin murya tace
"Aah chocolaty na Seka fad'a!"

Yace

"Ina me miki albishirin ,wannan gidan da kike ciki na mallaka miki shi halak malak ya zama naki ,ga kuma mota nan idan bata miki ba se kiyi magana in canza miki wata ,zan aiko wasu lawyers su biyu ,zasu kawo miki takkadun gidan ,dana motan se kisa hannu ,Danni na Riga nayi signing tun kafin in tafi".


Binafa jin abun tayi kamar a mafarki ,ta rasa me take ji farin ciki ko akasin haka. Kasa cewa komai tayi ,dakyar ta iya bud'e baki tace

" chocolat..." Bata k'arasa ba ya katse ta da cewa

"Karki ce komai babyna ,bana son godiyar ki. Kinfi karfin hakan a waje na idan da kari ma kin cancance shi. Wai kuwa kinsan yadda kike faranta mun? To ni wannan ba komai bane a waje na ,saboda hk bana son jin komai kinji tawan?"

Kai ta gyada kamar yana ganinta tare da furta

"Bansan wani kalamai zanyi amfani dashi ba wajen yima godiya. Ina sonka chocolaty na, ina matuqar matuqar qaunar ka ,kewarka na nema ya tagayyara ni".

" nima inason ki babyna ,yanzu dai bari inbarki haka ,ki huta nima zan shirya inje meeting ne ,se munyi waya zuwa anjima".

" okay take care dear "

"Bye" ya bata amsa tare da yanke wayan


Wani tsallen dad'i Binafa ta daka tare da mikewa tsaye kan gadon tana rawa tana juyi, fad'a wa tayi kan gadon tana shewa tare da furta


"Yesss I make it. Seni 'Yar ummana. Tulu me santsin baya, dutse kakan rauni, daka fada gara a fad'a ma. Dakalin majina a hauni a zame , na hau mutum na zauna daidai. Wai akace da budurwan qauye ga kyautar fatanya tace dama baba na nema" ta k'ara she maganan tana wani arnen dariya...


Tana cikin wannan yanayin kiran waya ya shigo ,kamar bazata dauka ba ,ganin me kiran yasa tadan saki murmushi ta dauka ,gayen nanne da suka had'u a jirgi
Gaisawa sukayi ,yace dama ya kira ne ya tambaye ta yata ita gida? Tace ta isa lpia. Hira suka Dan taba kad'an kafin sukayi sallama.


Kitchen ta shiga ,ta fara duba ko zata samu wani abun me Dan sauki tasawa cikin ta. Bude bud'e ta fara amma bata ga komai ba. Har zata fita ,se kuma tace bari ta leqa store, a mamakin ta se taga kayan abinci komai da komai babu abunda babu.


"Oh my God chocolaty ur style is killing me" kwalin indomie ta janyo ta farka ,guda biyu ta dauka dake kanana ne ,ta fito kitchen din ta samu tukunya Dan madaidaici ta dafa ,Dana gamawa ta soya kwai ,ta koma parlour taci.


A ranar rasa tayi inda zata tsoma kanta Dan tsabar farin ciki. Kwana waya sukayi da honourable ,seda ta tabbatar ta gamsar dashi sannan sukayi seda safe.

Monday Binafa ta fara shiga asibiti. Sosai taji dadin wajen. Hankalin ta kwance take zuwa Aikin ta ta dawo.


Bayan wata d'aya kawo yanzu Binafa sun shaku da salim (salim shine guy dinda suka had'u a jirgi), suna yawan fita shan iska ,sosai yake kula da ita.
Yau laraba ,Binafa bata je asibiti ba ,Kasancewar tayi night a asibiti na sati daya ,yanzu tana off. Dan haka tsarin yake ,duk lokacin da kayi night duty zaka samu hutun kwanan biyu. Misalin bayan isha salim yazo ya dauke ta. Suka dinga zaga gari ,ba su suka dawo ba se goma yazo ya aje ta. Ai fa Binafa tunda taji salim Dan Dan majalisar dattako ne na kasa, dad dinshi ne ya turo shi wani aiki na tsawon wata biyu.



Tana shiga kai tsaye bedroom dinta ta wuce, Jakarta kawai ta aje ta janyo wayanta. Contacts dinta ta shiga lalubowa ,can wajen M taga malam musa me farin allo ,batayi wata wata ba tayi dialing numbern.



Seda kiran ya kusa yankewa sannan malam musa ya dauka. Gaisawa sukayi ,sannan taba malam musa labarin salim da yadda take so amata aiki a kanshi. Kwana ukku malam musa ya bata. Dan ba kad'an ba yanajin dadin yiwa Binafa aiki ,Dan bata tauye hannu wajen ihsani... Sunkai kusan awa daya suna waya kafin ta mishi sallama ta aje wayan...






Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)


*NOTE*
*Assalamu Alaikum warah matullah. Gare Ku readers. Zanyi wannan korafin ne ganin Abu ne dayake ciwa writers tuwo a kwarya ,wato rashin comments. Zamu turo kuma zaku karanta ,amma common sharhin layi biyu ukku ya gagare Ku fisabilillahi. Se randa bamuyi posting ba ace anji shiru. Ga rashin uzuri. Ku duba fa kuwa kanku adalci ,muda muke bata lokacin mu mu aje abubuwan mu masu muhimmanci Dan kawai mu faranta muku rai. Amma Ku mu gagara samun samun farin ciki a wajen ku? Anya Kunawa kanku adalci kenan? A Gaskiya ya kamata Ku gyara* .

*SAK'O*
~Daga kungiyar marubuta ta duniyar yanar gizo~📚✍



*PAGE1⃣3⃣➡1⃣4⃣*




Bayan kwana ukku kamar yadda Malam musa me farin allo yawa Binafa alqawarin yi mata aiki akan salim Dan Dan majalisar dattawa ta k'asa. Haka akayi kuwa bayan kwana ukku ,kawo yanzu salim duk ya gama fita a hayyacin shi akan binafa ,gaba daya sonta na nema ya zauta shi, kud'i kuwa bani da kud'i ba yadda yake sakar mata Naira kamar yana tsinkowa a bishiya.



Yau ranar weekend ne ,Binafa na zaune a parlour tana chat ,Sega kira ya shigo wayanta. Tsayawa tayi tana kallon me kiran ,wani killer smile ta saki tare da furta

"Smatcher".. Seda kiran ya yanke ,aka sake kira sannan tayi picking.

" kin kyauta Mara mutunci. Yanzu Ashe bakya ma gari amma ki gagara sanar dani. Alqawari bece haka ba".. Ita dai Binafa jinta kawai take seda takai aya sannan tace


"Nayi lefi amun rai uwar daki na. Tafiyar ne yazo mun bakatatan kuma bana samun isash-shen lokaci ne shiyasa ,amma wllh kina raina".


" wato Binafa yanzu kikace liyafa yaci uban Nada, harkan nan ba k'aramin karban ki yayi ba naga alama, Ashe yanzu har barin gari kike wajen babban harka?"

Wani dogon tsuki Binafa taja jin inda smatcher ta nufa. Tace

"Ke dalla Malama niba abunda ya kawo ni ba kenan ,practical nazo yi na wata hud'u gashi yanzu ma haka ina cikin wata na biyu."

Jin yadda Binafa tayi magana yasa smatcher saukowa, Dan sarai tasan halin kawarta ta yanzu seta kwabe musu. Sassautar da murya tayi tace

"To yanzu dai ya Aikin ,fatar komai normal?"

"Alhamdulillah" Binafa ta bata amsa a takaice

Smatcher taci gaba

"Gaskiya fa yarinyar nan kin samu Hutu. Nasan ana nan ana gara mazan iko" da k'arasa maganan tare da fashewa da dariya"

"Aikuwa dai kam" binafa ta amsata

"To wai yanzu a ina kike zaune? ,ko kina can wajen family din mummy?" Smatcher ta tambaya

"Wa ni? Cabdi aini na wuce nan en mata, ina nan a gidan kaina". Binafa ta bata amsa ,kuma da biyu ta gayama Smatcher cewa tayi gidan kanta ,dukda tasan ba lallai ta yadda ba.


Wani shewa smatcher tayi tare da cewa

"Shegiya ,boka alqalinki Allah. Kina dai gidan mutane ,ni kinga ba wannan naja kiba"

Binafa ta kule tare da cewa

"Me kike nufi karya na miki kenan? Na wuce nan wllh kema kin sani ,yau ko jirgi nace miki inada shi aibe kamata kiyi mamaki ba ,Dan kinfi kowa sanin wacece BINAFA, amma ki bari duk randa kika shigo kyazo ki kashe kwarkwatan idon ki"...


Mamaki ne da tsoro karara ya bayyana a fuskan Smatcher tayi saurin taron numfashin Binafa da cewa


" Aikuwa cikin satin nan zan shigo ,zanzo saran kaya ne, shiyasa ma na kiraki inji kozan samu masauki"

"Masauki kamar kin samu" binafa ta bata amsa ,dukda cewa tasan gulma ne ze kawo Smatcher ba wani siyayya tace cikin ranta "zaki

Please Login or Register in order to submit comment