Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke ba, Abu d'aya ya damu dashi Wanda duk lokacin da zasuyi waya seya maimaita mata shine ,ya matsu ya dawo ayi Auren su. Har yake ce mata yana ganin kamar zasu maida shi can Istanbul din da aiki gaba daya ,wai se su tafi tare.

Ita dai Binafa amsa shi kawai take.


Amma wani abunda mazajen suka kasa ganewa shine ba aure a zuciyar Binafa ,ko kad'an bata shirya aure ba. Hasalima ta tsani maza to the extend...




Comments
&
Share





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*Wannan page d'in naku ne BINAFA FANS GRP ,sosai nake jin dadin comments dinku ,kuna sanya ni nishadi. Wato a rayuwar nan ba abunda yakai samun masoyi dad'i. Kuci gaba da nunan qauna, nima ba kad'an ba nake son Ku har cikin raina,,, sidiya na qaunar me qaunar ta a duk inda yake...💋*




*PAGE2⃣9⃣➡3⃣0⃣*



Washe gari da safe Binafa ta tashi tayi shirin ta tsaf na fita. Se jin tayi kuma kamar bazata iya zuwa ba ,saboda wani irin zazzabi dake saukar mata. Abincin ma da aka aiko mata dashi na hotel d'in kasa ci tayi. Tafi minti 30 a zaune kafin ta mike dakyar ta fita.


Ranar duk Wanda ya ganta yasan batada lpia ,daure wa kawai take tana harkokin ta. Dukda Binafa batada raggonta, amma sosai take jin zazzabi a jikinta ,kuma ita kanta tasan bakomai bane hadda gajiya ,Dan tunda taje gombe bata huta ba koda yaushe tana cikin taro...


Ranar ba'a tashi da ita ba. Dan kuwa wuraren karfe 4 na yamma ta dawo.
Duk shiga da ficenta akan idon Umar faruk yake.
Ya lura da yadda take yau din se a hankali.
Yana daga farfajiyar hotel din ya hangi shigowar ta. Tashi yayi ya k'araso suka gaisa, sannan yake tambayar ta

" me sunan larabawa meke damun kine yau ?,(haka yake kiran ta). naganki kamar se a hankali"

Murmushi ta masa ,tare da cewa

"Wllh zazzabi ne me sunan manya. Tunda na tashi da safe yau bana jin dad'i, ko abinci ma na kasa ci ,dakyar na samu ma na fita ,jin zazzabin ze iya kwantar dani yasa na nemi izini na dawo ,indan samu Hutu"... Ta k'arasa maganan tana jinginawa a jikin mota, saboda wani jiri dataji yana ibarta...


Cikin yanayin damuwa yace

" to amma shine baki kirani na kaiki asibiti ba?"

Murmushin ta me kayatarwa ta sake mai tare da cewa

"Karka damu ,Dana samu bacci zan warware da yaddan Allah!"

"Kin tabbata?"

Kai ta daga mai alamar eh. Jakarta ya karba ya taka mata har bakin dakin ta ,sannan ya tambaye ta makullin fa ,tace yana Jaka. Ya dauke ya bud'e mata suka shiga ,seda ya aje mata jakan sannan yace

"Pls idan kina buk'atar wani abun ki sanar dani"

Ta daga mai kai ,alamar toh ,sannan tamai godia ya fice.

Binafa kamar jira take Umar faruk ya fita ,nan ta fad'a kan gado ta fara rawar sanyi, dakyar ta janyo bargo ta rufe. Wani irin amai taji yana taso mata, da gudu ta figa tayi bayi.

Wani koren amai take me wahalar wa ,gashi ba abunda ke fita yunkurin kawai take


Umar faruk na dakin shi amma gaba daya tunanin shi na gun binafa, ji yayi yana so yasan halinda take ciki. Tashi yayi ya fito daidai kofar dakin ta ya fara knocking, yafi minti biyar amma ba response. Da haryp yayi tunanin ko ta samu bacci ne ,har ze juya ,se kuma wani bangare na zuciyar shi ya bashi ya shiga dai ya duba.


Ganin ta da yayi darshe a bakin bayi ,hankalin shi in yayi dubu ya tashi. Da sauri ya k'arasa wajen ta ,yana tambayar ta jikin ne? Ko magana ta kasa yi ,taimaka mata yayi ta tashi ,ta zauna kan kado sannan yace mata yana zuwa.

Fita yayi daga d'akin, jim kad'an ya dawo hannun shi rike da makullin mota, yace ta tashi suje asibiti, ganin ba wani abunda zata iya yi yasa ya d'auko mata hijabinta ta ya taimaka mata ta saka. Taimaka mata yayi ta mike.
Rike yake da ita har bakin mota ,yasa makulli ya bud'e sannan ya bud'e mata k'ofar baya ta shiga ta kwanta...


Tada motar yayi suka kama hanyan asibiti ,ba bata lokaci suka isa wani private hospital. Fitowa yayi ya bud'e mata tare da dago to. Kati ya fara yankar mata .Tana jikin shi har suka isa dakin likita.


'Yan Tambayoyi likitan ya mata ta bashi amsa game da yadda take ji. Nan ya basu test kala biyu ,suka je sukayi. Ba'a wani jima ba aka kawo ma likitan sakamakon gwajinda aka mata. Nan likitan ya tabbatar masa typhoid ne ya mata yawa a jiki, sannan yace za'a sa mata drip saboda ta samu karfin jikinta.

Ruwa aka sa mata tare da yi mata allurori, ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita. Bacci take tana sauke numfashi a hankali. Duk wani motsi da zata yi idon Umar faruk na Kai. Ba ita ta farka ba se wuraren isha.

Koda ta tashi jin tayi kamar an tsare mata ciwon. Tashi tayi zaune amma a mamakin ta bata ga Umar faruk ba. Tunani ta fara wai ina yake? Aiko se gashi kamar an jefo shi ,da sallama ya shigo hannun shi dauke da ledoji. Ganin ta farka yasa ya k'araso wajen ta da sauri yana yi mata sannu da jiki...


Ta Fad'ad'a murmushin dake shimfid'e a fuskanta sannan ta amsa shi. Ledojin ya aje akan kujera ,sannan ya ciro take away daya ya aje a gaban ta tare da bud'e wa. Yace

"Bismillah " chips ne da soyayyen k'wai

Kamar bazata ci ba ,se kuma taga baze ji dad'i ba. Haka da daure ta dinga turawa. Bata wani ci sosai ba tace

" na k'oshi". Kallon yayi se kuma ya bata rai tare da cewa

"Cinye shi zakiyi tas"

Kamar bata jiba ,seda ya maimaita mata

"Sefa kin cinye shi"

Haka ta fara ci kamar zata fasa ihu. Yadda take tura abincin ba kad'an ba yaso ya bashi dariya ,se kuma ya dake. Seda ya tabbatar taco sosai sannan ya janye take away din ya bata drink ta karb'a. Ya janyo ledan magani ya b'alla mata ya bata tasha...


Seda yayi sallan isha sannan yazo suka karbi sallama suka koma masaukin su. Dakin shi ya wuce da ita, bata musa ba ta bishi ,har cikin ranta taji dadin yadda ya nuna mata kulawa. Bayi ta shiga ta dauro alwallah ,ta fito ta fara rankon sallah. Seda ta idar ,tana so tayi karatu amma ganin bataga wayanta ba yasa tayi tunanin ko basu fita dashi ba.

Kallon shi tayi da hankalin shi gaba daya yana kan system yana wani Aikin. Tace

"Pls kad'an aramun wayanka"

Ba musu ya mik'a mata, Ta karb'a. Qur'an app ta bud'e ta fara rera karatun alqur'ani cikin muryatta me dad'i. Kusan minti20 tanayi sannan ta kashe ta bashi. Kan dadduma take ta dan kishingid'a da gado. Hira yake ta janta dashi tana bashi amsa jefi-jefi. Bata San ma tayi bacci ba...


Ya jima yana aiki akan system dinshi ,ganin dare yayi sosai yasa ya rufe ,yayi addu'a ya kwanta kan kujera.


Misalin karfe biyu na dare harbe harben da ake na bindiga ya tashe shi. Jin harbin kamar a cikin hotel din yasa ya furta

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"... Daidai nan binafa ta farka. Itama karar harbin ne ya tashe ta.

Tsantsar tsoro ne da firgici shimfid'e a fuskanta. Kallon Umar faruk tayi dake kan kujera tace

" k'arar me nake ji?"

Yace

"Ina tunanin kamar 'yan fashi ne suka shigo hotel din"...

" innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati"... Ta furta a sanyaye.






Comments
&
Share




Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*Sis Nerja'at na tayaki murnan kammala littafin ki me suna ZAB'IN RAINA ,hakika kin baje ruwan basirar ki acikin wannan littafi. Ba kad'an ba kin kayatar damu ,littafi ne daya fadakar, ya ilimantar* *ya kuma nishadantar. Zan iya ce miki zabin raina is 1 of my favourite novel dana taba karantawa .Ba muda abunda zamu ce miki sedai muyi miki fatar alkhairi da addu'an Allah ya biyaki da gidan aljanna, kura-kuren dake ciki kuma Allah ya yafe miki ,Allah kuma ya bada ladan fadakarwa. Se mun jiki a sabon littafin ki me zuwa.*
*Up...Up sisi na. SIDIYA na yinki har cikin ranta* ...💖




*PAGE3⃣1⃣➡3⃣2⃣*



Tashi tayi zata fita ,ya rike to tare da cewa

"Ina kuma zaki cikin wannan yanayin?"

Cikin tsoro tace

"Zan koma d'aki na ne!"...

Janyo ta yayi ta dawo ,yace

" a'ah bazan iya barin ki ki fita ba a halin da ake ciki, dukma abunda ze faru muna tare ,kuma Allah ze kawo mana shi da sauki "...


Binafa durk'ushewa tayi kan kafarta ta fara rera kuka me ban tausayi. Suna cikin wannan yanayin aka banko kofar d'akin da suke ciki da karfi.
Wasu manya manyan gardawa ne, su hud'u fuskokin su a rufe ,dikkan su d'auke da bindiga.


Bindiga suka Dora musu tare da cewa su kwanta... Ba musu suka kwakw-kwanta. Omar faruk ne ya dake tare da cewa

" Dan Allah karku taba ta duk abunda kuke so Ku fad'a ,amma Ku kyale mu"...

Ogan cikin su ya daka mishi bindiga akai tare da daka mai tsawa

"Kai din uban waye dahar zaka dinga fad'a mana abunda zamuyi?"

Koma wa yayi kan Binafa dake rigingine a k'asa tana sharb'an kuka ,yace ta taso. Zagaye ta ya farayi yana fad'in

"Kyaky-kyawan yarinya dake",,, hannu yakai ze taba mata fuska ,Umar ya rik'e shi tare da cewa

" karka yadda kazamin hannun ka yakai ga jikin ta"..

Duban shi ogan yayi tare da juyowa kan shi yana fadin

"Wowww, amma fa zafin naman ka na burge ni"


Wani daga cikin barayin yace

"Oga kawai kabar mana wannan mu bud'e masa wuta" . ya k'arasa maganan yana Dora wa omar faruk bindiga a kai .


Hannu ogan ya daga mai alamar ya koma baya. Sannan yazo kusada kunnen Umar yace

"To naji ,kuma na dauke kazamin hannuna akanta ,amma Ku me kuke aikatawa idan ba kazantar ba?"... Runtse ido Umar faruk yayi yana jin wani daci na ratsa zuciyar shi. Binafa kamar ya fad'a a kunnen ta ,cikin rawar murya tace


" abunda ka...kake tunani bashi bane. Wllh ba haka bane" taci gaba da cewa

"Kuji tsoron Allah Ku kyale mu ,karku mana komai, Ku sani Allah baze taba bari Ku cutar damu ba"...

"I see" shine abunda ogan ya fad'a, sannan ya dawo setin ta tare da cewa

"Ku mata da miji ne amman ko?" Yace in a whispered voice.

Dagowa tayi ta masa wani kallon tsana tare da cewa

"Aah yaya nane ,wani aiki muka zo yi anan".

Umar faruk be so tace hakan ba ,Dan yasan kaidin b'arayi da girma yake ,ba abunda baza su iya aikata musu ba. Yana cikin wannan tunanin se kuwa daya daga cikin b'arayin ya fara kwance belt yana fad'in


"Oga wannan kawai ka bari a keta ta tunda bakinta baze mutu ba". Ya karashe maganan yana matsowa.

Dakatar dashi ogan yayi tare da cewa

" stupid of u... Wannan ta maka kama da kalan ka ne?, wannan ai ta manya ce sedai ogan ka, baka ganta kyaky-kyawa ba sona kin Wanda be samu ba "... Ya k'arasa maganan yana wani lashe baki kamar tsohon maye, se zagaye ta yake.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Binafa ta furta a sanyaye tare da maida komai ga Allah. Ba abunda take inbanda kuka

Kukan da Binafa keyi kaida ka gani bana Abu d'aya bane...

Matsota ogan ya farayi tana ja da baya. Kukan kura Umar faruk yayi ze cafko shi ,wasu daga cikin barayin su biyu suka rike shi. Se kucce-kucce yake yana fad'in

"Karkayi ....karka kuskura ka taba ta... Bazan yafe maka ba idan ka aikata mata wani abun"...

Shafata ogan ya farayi tana ture shi, wani gigitaccen mari ya dauke ta dashi ,daya sa ta fara hango taurari


Ido Umar faruk ya rumtse yana girgiza kai , har cikin ranshi yaji marin ,nan take hawaye suka fara saukar masa a fuska....


D'aya daga cikin barayin dake gefe ,ya je daidai kunnen ogan ya masa rad'a, se ganin su kayi ogan ya tsaya daga abunda yake shirin aikatawa. Sannan ya juyo ya kalli Umar faruk yace

"Na lura fa kana ji da kanwar nan taka, sedai zan baka option"... Umar faruk be jira ya k'arasa ba ya fara fad'in


" eh wllh koma menene zan maka ,ko rayuwa ta kake so zan bada indai zaku kyaleta".

Wani arnen dariya ogan ya saki seda ya tsagaita sannan yace

"A'ah ustaz. ai baka cancanci wannan ba, bama taba masu gemu ,koba komai kuna mana addu'a. Zabin da zan baka shine ,kodai ka barni in angonce da kyaky-kyawan kanwar nan taka ,ko kuma kai ka wakilce ni...."


"Ina baze taba yuwa ba, baze yu ba".. Umar faruk ya fad'a cikin daga murya da tashin hankali. Wani dariyan mugunta ogan ya sake ,sannan yace

" to idan kai baze yu a wajen kaba, ni wannan shine mafi sauki a waje na"... Be jira amsan Umar faruk ba ,ya nufi Binafa gadan-gadan ,yana zage belt din wandon shi. Janta ya farayi zuwa kan gado yana kaiwa yaje fata. Kuka binafa keyi kamar ranta ze fita tana rokon shi akan ya kyaleta amma ina ko sauraren ta bayayi.



Har ya nufe ta kamar ze hau kanta, Umar faruk yace

"Tsaya... Dan Allah karka yi. Ka tsaya".

Wani shu'umin murmushi ogan yayi tare da cewa

" zaka yi kenan?"

Rufe ido Umar faruk yayi sannan ya furta a sanyaye

"Eh zanyi..."

Hannu ogan ya daga musu alamar su sake shi ,ba bata lokaci suka sake shi. K'araso wa yayi har kusa da ogan ya durkusa ze yi magana ogan ya dakatar dashi ,fuskar nan tashi ba alamun rahama yace

"Bana magana biyu ,matuqar ka mana taurin kai kuwa fiu"... Ya daga yatsun sa biyu sama alamar kashe shi zeyi.

Binafa take daga gefe ta sandare kamar an dasa karas ,k'arasowa tayi daidai wajen Umar faruk tana jijjiga. Cikin muryan ta na kuka da baya ma fita sosai tace


" A'ah me sunan manya, bazan juri ganin mutuwar ka a gaban ido na ba, ka dubi girman Allah ka aikata abunda suke so ka aikata ,indai shi zesa su kyale ka..." Ta karashe maganan tana kara fashewa da wani sabon kuka


Umar faruk dagowa yayi ya kalleta da raunannun idanuwan shi da suka kad'e sukayi jajir ,bata jira yayi magana ba ta sake cewa

"Plss. I beg u..." A hankali ya taka ya k'arasa har inda take, se kuma ya tsaya. Hannun shi ta riko ta sake ce masa

"Na rok"e ka me sunan manya"... Hawaye se kai kawo suke a idanun Umar. Haka ya daure ya fara kokarin rapping dinta. Binafa kuka take kamar zata shek'e jin wani al-amari na shirin faruwa da ita karo na farko a rayuwar ta.

Lokacin da Umar faruk yazo shigan ta, rumtse idon ta tayi ta had'iye sabon kukan dake shirin fito mata Dan azaba. Jinta a kulle gam yasa ya kasa k'arasa shiganta. Mamaki ne shimfide a fuskan shi ,yace cikin muryan da daga shi se ita kejin abunda yake cewa

" Binafa bdurwa ce ke ?" Ya tambaye ta

Kasa magana tayi ,kai kawai ta iya daga masa alamar "eh"... Wani irin sonta yaji yana fizgar shi.

" ina bazan iya ba". Ya furta cikin daga murya lokaci daya matsawa gefe.

Binafa ta kalle shi tace

"Me kake shirin aikatawa ne haka me sunan manya? Me yasa zakayi wasa da rayuwar ka?" Katse ya yayi da cewa

"Bazan iya ba Binafa, bazan taba iya lalata miki rayuwa ba, bazan so in kusance ki ta haramtacciyar hanya ba."

Tace

"Saboda me?"

Yace

"Saboda ina sonki".

Cikin kuka tace

" Rayuwar ka fa?"

Yace

"A shirye nake da in bada ita saboda ke"


Kallon su ogan yayi sannan ya kalli yaran shi yace

"Ku fige shi!" Yana kaiwa nan yayi waje.


Nan take sukayo kan Umar faruk suka fara jibgar shi kamar me.
Kuka binafa take kamar ranta ze fita ,ture su ta farayi tana rokon su kyale shi ,amma basu saurara masa ba seda suka ga baya motsi.
Bindiga wani daga cikin barayin ya Dora ma Umar faruk ze halbe shi ,da gudu Binafa tazo ta kai masa cizo a hannu, k'ara yayi tare da buga mata bindiga akai, nan ta fad'i kasa ba numfashi... Sannan suka fice da gudu suka bar dakin...






Comments
&
Share





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE3⃣3⃣➡3⃣4⃣*



Ba bata lokaci jami'an tsaro suka kawo wa hotel din d'auki Dan an musu waya. Sunyi sa'an cafke wasu yayin da wasu kuma sun yanki na kare. Duk wanda ke cikin hotel din Hankalin shi a tashe ,Dan sun harbi mutane da dama sun kuma daddaki wasu.... Lokaci d'aya kuma se ga motar asibiti ta iso.


Manager-n hotel din kamar ze had'e sojojin da aka turo da masifa ,ganin tun farkon faruwan al-amarin ya musu waya amma basu suka zo ba se yanzu da aka gama ta'addanci. Hak'uri suka yita bashi da dalilan su na banza...


Nan aka fara zaga daki daki ana kwaso mutane ana zuba so a motar ana wuce wa dasu asibiti Dan basu agajin gaggawa ,ciki hadda Umar faruk da Binafa da ba alamun akwai rai a tare dasu.


Washe gari misalin karfe 12 na rana Binafa ta farka. Dafe kanta tayi Dan tsabar ciwon da yake mata, ji take kamar ba k'wak'walwa a cikin kanta Dan azaba. Wata nurse ta k'araso kusa da ita da sauri ta rik'e ta ,sannan ta fara ihun kiran

"Doctor!!! Doctor!!!"

Ba bata lokaci likitan ya shigo ,kara duba ta yayi sannan ya banka mata wasu allurori masu karfi ,ba bata lokaci bacci yayi awon gaba da ita...


Ba ita ta farka ba se wajajen la'asar. Alhmdllh ciwon kan ya mata sauki sedai duk se a hankali take jinta bata da wani kuzari... Wata nurse ce ta shigo inda take take k'ara tambayar ta karfin jiki ,tace da sauki. Har zata fita ta tambaye ta Dan Allah ina Umar faruk? Bata San wa keda wannan sunan ba ,Dan haka tace mata


"Gaskiya bansan me sunan ba ,saboda patients din nada yawa"

Nan Binafa ta siffan ta mata shi ,ta kuwa yi sa'a ta gane shi ,nan take sheda mata yana emergency ,rai hannun allah ,saboda akwai raunuka sosai a jikin shi ,yana buk'atar proper treatment, kuma har yanzu be farfado ba.


Nan take wasu zafafan hawaye suka fara saukar wa Binafa. Tace cikin muryarta da baya fita sosai

"Dan Allah ko zan iya ganin shi?"

"A'ah a yanzu dai baze yu ba gaskiya, sedai munga abunda Allah yayi". Nurse din ta bata amsa

Nan Binafa ta had'e Kai da guiwa ta bud'e wani sabon shafin kukan me ban tausayi da ratsa zuciyar me saurare. Hak'uri nurse ta shiga bata ,sannan ta fice daga dakin ,bata wani jima ba ta dawo hannun ta rike da take away ,abinci ne ta kawo wa Binafa, ba yadda batayi da itaba amma tak'i ci se kuka take ,haka ta hak'ura ta k'yale ta...


Nurse din na fita ,Binafa tayi kokarin mik'ewa ,dak'yar take tafiya ,Dan wani jiri da ciwon kai da take ji ,amma haka ta daure ta dinga bin bango...


Haka ta dinga zagaye asibitin ,kafin Dan nisa da ita ta hango emergency. Haka ta k'arasa daidai kofar shiga ,a nan ta hangi Umar faruk a kwance duk jikin shi yasha bandages ya sauya kamanni kamar bashi ba. Wasu zafafan hawaye suka fara sauko mata ,da sauri ta k'arasa ciki...


Kan kujera ta zauna ,ta fara rera wani sabon kuka me ban tausayi. Gaba d'aya ji take ta tsani kanta, musamman ma idan ta tuno da akanta akayiwa Umar faruk haka. Haka hawaye yaci gaba da saukar mata wani na bin wani...


Hannun shi ta rik'o tasa a nata cikin kuka take fad'in

" Dan Allah karka tafi ka barni ,rayuwa ta bata da amfani idan babu kai Umar ,ka rufamun asiri ka tausaya mun ka bud'e ido." kuka take kamar zata shek'e ,idanuwan ta sun kad'e sun koma jawur. Gab'a d'aya ta gama fita a hayyacin ta. Taci gaba da cewa


"Yanzu saboda ni aka maka haka? ,,,Ka zab'i ka bada rayuwar ka akan nawa rayuwar?,,, Saboda ni kake cikin wannan halin?,,, akaina kake barazanar rasa rayuwar ka?,,, ka gayamun menene amfanin rayuwa ta idan ka tafi ka barni ?,,, na tabbata kana mutuwa nima bazan jima ba a wannan wahalalliyar duniya daba komai a cikin ta inba k'unci ba. Kace kana sona Umar? ,,,Umar ka tashi na maka alkawarin soyayya ta ,dakai zan k'are sauran rayuwa ta, Umar Dan Allah ka tashi... Ina son ka..." Ta karashe maganan tare da fad'awa jikin shi ta fashe da wani sabon kuka...


Nishi ya fara sama-sama, nan take Na'urorin dake jikin shi suka fara kawo danger, Layin dake jikin na'urar ya d'auke alamar baya numshi. Cikin tsananin firgici binafa ta fara jijjiga shi, tana fad'in


"Karka tafi ka barni Umar ,ka tashi" ganin kamar tana yi da gawa yasa ta furta


"Nooooo!!! Pls help... Help " ,cikin daga murna .


Nan take likitoci har uku suka shigo ,sukayo kanshi, wasu nurses su biyu suka rik'eta sukayi waje da ita ,tana turjewa tare da fad'in

"Don't dare leave me alone pls , u're my everything, i can't do with out u, with out u my life is useless . I love u to the extend Umar ,,,,"

Haka ta dinga maimaitawa ,dak'yar sukayi waje da ita.





Comments
&
Share





Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*



Please Login or Register in order to submit comment