Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abun Shafe jiki. Lukam dai ya kasance Shine kadai me izinin shiga wajen salim kai tsaye ba tare da wani shamaki ba.


A Zaune ummu ta samu Lukman yana goge k'ananan kayan salim na shan Iska. Da fara'arshi had'i da ladabi ya gaishe da ummah, tare da k'ara yi mata gaisuwar Rashin da akayi, Dan kusan Lukman ya Dade da marigayi umar faruk, Duk da cewa yana k'asan shi hakan be hana marigayi umar faruk sake wa Lukman jiki ba ta yadda baya b'oye masa Duk wani damuwar shi, har suka zama kamar abokai koda cewa kuwa marigayi ya girma Lukman, Amma shi mutum ne me matuqar Sauk'in kai.


Lukman be hana umma shiga ganin salim ba, saboda ya Santa farin sani, iso yaso ya mata zuwa d'akin da salim ke ciki, Amma umma ta dakatar dashi...


"karka damu yaron Albarka, yimun nuni da d'akin kawai, kanna tsaida maka aiki!"


Lukman be Musa ba kuwa ya nuna mata d'akin dake d'an nisa da wajen da yake guga. Godia umma ta masa, sannan ta nufi d'akin.



Da sallama d'auke a bakin ta, ta tura k'ofar d'akin. Ba k'adan ba yadda taga yanayin da salim a ciki yayi matuqar d'aga mata hankali. Daga kuma ba saboda komai yake ba se dan farin cikin Wannan gidan da kuma wasilcin d'an uwan shi...

Wasu siraren hawaye ta goge, kafin ta samu gu ta zauna a kusa dashi gefen drawer.
Tun da ta shi d'akin gaban salim ke dukan takwas takwas, baran ma ganin kallon da ummah ke bin shi dashi na tuhuma...


Cikin sanyin murya, daga sama Yaji ummah ta wurga masa tambayar

"har zuwa yaushe zaka cigaba da b'oyon kuruwa AHMAD????


Dummmmm! K'irjin salim yayi mummunar bugawa....






Muje zuwa 💃🏻


Taku har kullum

SIDIYA ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 9⃣1⃣➡9⃣2⃣




Zuciyar salim ce ta tushe, ya rasa ta ina ze fara. Ganin yabi k'ofar shigowa da kallo, yasa umma tayi saurin Gano me yake nufi. Cikin tafiyar ta ta manyanta ta nufi k'ofar ta rufe da makulli, sannan ta dawo ta zauna. Wurin ya d'auki shiru nad'an wasu lokutta, ganin Shirun baze k'are ba yasa umma ta sake wurga masa Tambaya

"kayi shiru!".

Kallon da taga ya bita dashi, alamar yana son maimaici yasa umma batayi k'asa a guiwa ba, ta sake maimaita masa, sedai Wannan karon fuskar nan nata ba wasa a ciki.


"Ahmad ina son ka sani cewa, lokacin da Kuna jinya a asibiti, Duk maganar da marigayi yayi dakai Allah ya masa rahma, naji ku sarai!"

Du-dummmm! Gaban salim yayi mummunan bugawa. Ido kawai yake zaro wa kamar wanda yawa sarki k'arya. K'ure ta yayi da ido nason gasgata abunda yaji.

Gyad'a masa kai umma tayi, tare da cewa

"tabbas ma kuma, naji Duk irin wasilcin daya bar maka, Na abunda ya Shafi iyali da"..... Nan umma ta shiga rattafo Mai Duk abunda taji a wancan lokacin, daga karshe ta rufe da

" hatta had'a bakin da kuka yi kan ace ka samu matsala na Rashin lpian k'wak'walwa Duk ba abunda banji ba, Dan haka ka tashi muyi magana."


Wani zufa ne ya shiga tsiyayowa salim ba shiri yayi hanzarin tashi xaune, wanda dak'yar yake k'ok'arin tattaro k'arfin shi.

Cikin yanayi na tausayi da nuna damuwa umma ta dube shi, tare da cewa

"ka gani ko! Kaga irin Abinda ake gudu ko? Yanzu ina amfanin hakan Ahmad? Menene fa'idar Wannan? Shin ka kuwa San hatsarin daka ke k'ok'arin jefa kan ka? Dubi ka ganka, sati d'aya Kenan kana cikin Wannan yanayin, shin ashe me zaka gayawa Allah idan ka mutu a Wannan halin? Ashe ina tunanin kai ne din zaka maye gurbin marigayi?, sedai banga alamar ka shirya karb'an kujerar ba! Shin kai ba namiji bane? Meyasa ba zaka nuna mazantakar kaba? Allah ya tsare ya kauda b'acin rana, ashe da wani Abu wanda yafi Wannan muni ze kuma faruwa ba zaka tab'uka abun Azziki ba? Karka manta umar faruk ya tafi, ba kuma ze taba dawo wa ba, wanda ya bamu ya karb'a kayan sa, shida ya tafi beyi gaggawa ba, haka Muda muke raye bamu yi jinkiri ba. Ahmad da kunne na naji kana amsa wasilcin da yayan ka yabar maka, kuma kayi alqawari kace ka d'auka, Duk ma bashi ba, ashe ba zaka Dubi mahaifiyar kuba, wacce tafi kowa buk'atar ka a yanzu! Ka kuma iyalan sa, shin wani dalili ne yasa umar faruk ya baka wasilcin 'ya' yan sa?, ba dan kar suyi maraici bane? Ashe an gyara goma ne biyar bata gyaru ba!, to tun wuri kaiwa kanka fad'a, Wannan hanyar daka dauko Sam bame b'ullewa bace, ya kamata ka sake tunani! "...



Tunda umma ta fara magana, salim ke aikin zubarda k'wallan bak'in cikin da tausayin kan shi. Da k'yar ya tattaro kuzarin shi, yayi k'arfin halin bud'e bakin shi wajen furta


" nagode sosai mama da tunatarwa Ki a gare ni, kuma insha Allah zan d'auki shawarwarin Ki, sedai dan Allah inaso kimun alqawarin Baza Ki sanar da kowa gaskiyar lamarin nan ba, kamar yadda nake kyautata zaton ba wanda yasan maganan a yanzu daga ke se ni se Allah "...

Wani siririn ajiyar zuciya umma ta sauke, kafin tace

" shikenan na maka alqawarin ba wanda ze sani ta b'angare na, Na maka Wannan alqawarin, Amma fa nima seka mun alqawarin sauyuwar abubuwa! "


Cikin yanayi na Allah gani gare ka kai kasan yadda zakayi dani, salim ya amsa da


" na Miki alqawari. Sedai ina buk'atar lokaci "

Umma tace
" har tsawon wani lokaci Kenan? "

" nan bada jimawa ba insha Allah, Na Miki alqawarin hakan... " salim ya bata amsa


Umma tace
" na Amince. Amma a gaskiya bata Wannan hanyar ba! Idan bazaka damu ba ni inada Wata hanya, kuma nasan zata amfane ka


Cikin zak'uwa salim ya gyad'a mata kai, alamar yana saurare

Nan da nan umma ta fara zayyana masa yadda shirin su ze kasance.

Cikin nuna gamsuwa da kalaman ta salim ya furta "na Amince"



umma ta amsa da
" shikenan, Allah ya mana jagoranchi, Allah kuma ya baka ikon sauke nauyin dake kan ka "


Salim ya amsa da" ameen". Kafin sukayi sallama umma ta koma gidan ta.





*BAYAN SHEKARA D'AYA* ...






Muje zuwa 💃🏻


Taku har kullum

SIDIYA ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SIDIYA ) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 9⃣3⃣➡9⃣4⃣







BAYAN SHEKARA D'AYA!!!

Abubuwa da dama sun sauya daga ko wani b'angarorin biyu, idan muka cire sha'anin ciwon salim da tun a karo na Farko likita ya tabbatar musu baze warke ba a mma ba a zahiri ba, Wannan Duk an k'addamar dashi ne a k'ark'ashin jagoranchin marigayi umar faruk, wanda shi a tunanin shi ta Wannan hanyar ne kadai zasu shawo kan matsalar daza ta kunno kai, koda baya raye...


BINAFA taci gaba da zama a gidan hajiya karime cikin kulawa da son junan su. Bayan ta Gama takaba hajiya karime ta nemi alfarman ko zata ci gaba da zama da ita idan ba damuwa, badan komai ba sedan da d'ebe mata kewar marigayi, gashi idan taga jikokin ta SHA'IB da BA'ISH, se ta dinga ganin kamar umar faruk take gani a raye.

Ba kadan ba hajiya karime ke ba BINAFA da 'ya' yan ta kulawa, Duk abunda suke buk'ata ita ke d'auke da nauyin shi, bata kaunar abunda ze taba su ko nan da can, Duk wani lallurori nasu kuma bata barin BINAFA tayi, dukda cewar umar faruk ya mutu yabar wa iyalan sa tarin dukiyar da har ma ita kan ta bata San me zata yi dasu ba, saboda tun kafin ya rasu ya mallaka mata kaddarori da dama, banda zunzurutun kudi da yake loda mata a asusun bankin ta ba dare ba rana, da wanda tasan ya saka da wanda bata da masaniya sedai taji alert...


Masha Allah BA'ISH da SHA'IB sunyi wayo abun su, suna gudu ko ina, gasu en dub'ul -dub'ul gwanin ban sha 'awa, inde zaka yi Ido hudu dasu, to se kaji sha'awar d' akan su. Gatan duniyar nan ba kalan wanda hajiya bata nuna musu, BINAFA har magana take kan Gatan yayi yawa, Amma hajiya karime se tace, idan bata musu ba suwa zata wa?. Haka Rayuwa yaci gaban su.

A b'angare d'aya kuma BINAFA na matuqar kewar mijin nata, wanda ita kadai takan keb'e kanta taci kukan ta seta godewa Allah. Ta kasa jurewa, da gasgata cewar umar faruk baya raye, Amma kuma tana kokarin yak'ar zuciyar ta.
Sannu a hankali ta fara murmurewa, Dan hajiya tana iya kokarin ta na ganin ta d'ebe mata kewa. Lokaci zuwa lokaci kuma, BINAFA da 'ya' yan ta kan kaiwa umma ziyara, idan ta kama su kwana ma zasu kwana, Duk da hajiya karime bata qaunar abunda ze nisan ta ta dasu, Amma ita kanta tana matuk'ar daraja umma, tana kuma bata girman ta, se ma suka zama yadda kuka San kawaye, Duk wani abun da hajiya karime zata yi takan tambayi umma shawara, Dan Ba kadan ba take Jin dad'in shawarwarin umma dan bata taba d'ora ta a hanyar banza ba, tun umma bata sake wa, BINAFA ce ta kara gyara hajiyar a wurin umma, yanayin kirkin ta da kuma yadda take kula dasu ita da yaran ta. Wannan ne ya kara sa umma ta sake da hajiya karime.


Wajen kula wa da salim ma, daga BINAFA har hajiya ba'a bar su a baya ba, kai hatta umma takan zo lokaci zuwa lokaci, sedai abun ya fara damun ta ganin ciwon na so ya koma masa na gaske...



Wata safiyar asabar, lukman ya gama ayukkan shi na sashen salim, ya had'a masa tea ya kai masa d'aki, shigar sa d'akin keda wahala, yaga abunda yayi masifar d'aga masa hankali.
Salim ne ya fad'o daga kan Gadon da yake kwance, ga wani farin kumfa da yake fitar masa a baki, ba shiri lukman ya k'arasa ciki da gudu, zubewa yayi kan k'afar shi, ya tallabo kafad'un salim, jijjiga shi yake ba girma ba Azziki, yana ihun Kiran sunan shi, iya muryar shi



"me gida salim!!! Me gida salim meya same ka? Dan Allah ka tashi...innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, jama'a Ku taimako!!! Hajiyaaaaaah !"


Hajiya dake harabar gidan tare da 'yan jikokin ta suna shan Iska, bata iya juyo komai ba, Dan yaran dake gaban ta sun d'auke mata hankali.
BINAFA dake waya ne taso taji yo sautin muryar lukman dake fita da k' arfi, d'an janye wayan tayi a kunnen ta dan taji dakyau, aiko Sega sautin muryar lukman yana kwad'awa hajiya kira...


Cikin hanzari BINAFA ta ankarar da hajiya, ba shiri suka rantaya zuwa sashen salim, BINAFA har da d'an gudu take had'a wa, yaran ma da gudu suka bi Bayan kakar tasu, tab'ui-tab'ui...







Muje zuwa💃🏻

Taku har kullum

SIDIYA ✍

[5/31, 19:15] +234 906 445 8468: 💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SIDIYA ) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 9⃣5⃣➡9⃣6⃣







Sharkaf aka kwashi salim inda BINAFA ke tuk'a motar, lukman na gidan gaba, hajiya kuma na gidan baya ita dasu BA'ISH, salim na malale kan k'afar ta, Shafa kan shi take tana tofa masa Duk abunda yazo bakin ta. Yaran kuwa se tab'a shi suke, suna so ya bud'e Ido, kamar sun San me yake faruwa, lokaci d'aya suka fashe da kuka, Dan inda sabo sun haddace fuskar salim, kasancewar Duk lokacin da maman tasu zata je duba shi tana zuwa dasu, idan taga kamar zasu ishe Shine seta kora su.
BINAFA gudu take da mota a tsiyace, bata taka burki ko ina ba se babban asibitin Abuja dake AREA 1. Da isar su keda wuya sega ma'aikatan lpia sun fito kowannen su cikin shigar aiki, da yake tun suna kan hanya BINAFA ta musu waya ta sanar dasu zuwan su.
Gadon Marasa lpia aka gunguro, ba shiri aka tallabi salim aka d'ora shi kan Gadon, wanda dashi da gawa Duk basu da banbanci, kai tsaye emergency aka nufa dashi, a inda su hajiya suka rufa musu baya, suna Isa kofar shiga aka dakatar dasu, su BA'ISH se tsulla - tsulla suke ala Dole se sun shiga, lukman ne yazo ya kama hannun su yana kokarin fita dasu, Amma Tausayin su ya kama shi. Tsakanin BINAFA da hajiya karime kuwa baki ya d'auke, kowannen su guri ya samu ya zube a k'asa, kafin ka an kara se hawaye shahhh!

Su BA'ISH na ganin haka, suka k'wace hannun su, SHA'IB ya nufi wajen hajiya, a inda BA'ISH kuma ya nufi BINAFA, rumour su sukayi, cikin yaren su da baya fita sosai, suka lallashin su. Nuna lukman suka shiva yi wai shi ya buge su "buuuh bamm!" Shine abunda yaran ke maimaitawa idan suka kalli lukman. Murmushin k'arfin Hali hajiya tayi, tare da share hawayen ta, sannan ta janyo SHA'IB jikin ta, tana bubbuga Bayan shi, ganin haka yasa shima BA'ISH ya nufo hajiyan. BINAFA dake rakub'e, tausayin su ya kama ta. Suna cikin Wannan yanayin Sega Kiran umma, a sanyaye ta Dauka tare da yin sallama, umma najin muryar ta haka, hankalin ta ya tashi, ta fara tambayar ta meke faruwa?

"muna asibi umma"!

" ash sha! Waye kuma ba lpia? "

" salim " ta furta a tak'aice. Ai hajiya bata jira komai ba, ta tsinke wayan, cikin minti talatin Sega ta ta iso asibitin. Cikin fuskokin damuwa da jajantawa umma ta gaisa da hajiya, tambayar take ya jikin salim d'in fa? Kafin tace wani Abu Sega likita ya fito, umartan su yayi dasu biyo Bayan shi. Da taimakon umma hajiya karime ta mik'e, hannun yaran umma ta rik'o ta dank'awa lukman tace ya fita dasu, su hajiya ne a gaba, BINAFA na Bayan su a haka har suka isa office d'in likitan. A Zaune suka same shi, ya musu nuni da kujerun dake office din yace su xauna. Jiki a sanyaye suka Zauna. Zare glasses d'in da ke idanuwan shi yayi, ya fara musu magana kamar haka

"hajiya! Gaskiya am sorry to say, lamarin ciwon Ahmad akwai rud'ani a ciki, a yanzu haka iya gwaje gwajen da muka masa mun Gano cewa spinal cord d'in shi na kokarin samun matsala, saboda wani dalili da ban sani ba, a b'angare daya kuma zuciyar shi na Neman bugawa, a inda yake tsakanin mutuwa da Rayuwa, sannan nayi mamakin ganin cewa yana d'auke da ciwon k'oda na tsawon lokaci, wanda a yanzu haka k'odar shi d'aya na buk'atar canji, yunwa kanta kadai ta Isa ta kassara shi".

Wani dogon numfashi likitan ya sauke, sannan ya dubi hajiya cikin kulawa yace

"hajiya Dole akwai abunda ke damun Ahmad na tsawon lokaci, a yanzu mu mun masa abunda zamu iya, sauran mun barwa Allah, sannan kuma Dole muna buk'atar taimakon ku, Duk abunda kuka San yafi so Dole ne ya kasance dashi a Wannan lokacin, samun haka ne kawai ze dawo shi har yaci gaba da Rayuwar shi kamar kowa, Rashin haka kuma kuyi hakuri zan iya cewa zaku iya rasa shi. Hajiya an cutatar da Rayuwar bawan Allah nnan, alamu sun nuna tun Bayan wancan ciwon da yayi, baya samun kulawa yadda ya kamata, hasali ma Duk wani 'ka' idodi da muka bayar ba wanda aka kiyaye. Yanzu dai zaku shiga dashi aiki kan matsalar 'k'oda, muga abunda Allah zeyi, matsalar spinal cord kuma zamu d'ora ku akan magani idan anyi nasara, sannan se ciwon zuciya, shakka babu hajiya kune maganin Wannan matsalar "!!!

Tunda likita ya fara magana wajen yayi tsit kamar ba kowa, Dukkan su sauraron bayanan likitan suke, BINAFA kuka take kamar ranta ze fita, hajiya karime ma hawaye take wani nabin wani, umma da kanta ya k'ulle gaba d'aya, tambayoyi na fal a ranta, Amma bata San inda zata samu amsar suba. Umma ce tayi 'k'arfin halin yiwa likitan godia, sannan ta taimaka musu suka tashi, a sab' ule suka bar office d'in. Wani d'aki umma ta samu ta shiga dasu, kamar suna jira su keb'e, daga hajiya har BINAFA suka k'ara sautin kukan su.


Cikin jarumta umma ta kauda kanta gefe, tare da share hawayen dake 'ko' karin sauko mata, dake wa tayi cikin k'arfin Hali sannan ta fara magana kamar haka



"shakka babu hajiya kune silar faruwar Duk halin da salim ke ciki, wllh Allah baze barku ba matuqar Ahmad ya mutu a Wannan halin, se kace ba musulmai ba, baku San kaddara bane?, Ahmad na kokarin kashe kanshi ne ba saboda kowa ba se saboda ku"...


Cak! Kukan ya tsaya, Daga BINAFA har hajiya


Umma taci gaba da cewa "eh kune sila. Yanzu kuma zaku ji komai"....








Muje zuwa💃🏻

Taku har kullum

SIDIYA ✍
[5/31, 19:15] +234 906 445 8468: 💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SIDIYA ) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 9⃣7⃣➡9⃣8⃣







Nan ummu ta shiga basu labarin Duk abunda ta sani tun daga lokacin da marigayi umar faruk ke barwa salim wasilci, da plan din da sukayi na Rashin lpian salim din, hatta plan d'in da tayi ita kan ta, wancan lokacin da bamu ji me take fada wa salim din ba, seta ta Gaya musu, nace

"na shirya haka ne badan komai ba se dan farin cikin ku, a tunani dan mu kawo karshen kwanciyar da yake a waje d'aya yasa na shirya masa, Duk ranar da ya shirya, y a sanar dani zamu yi basaja, yayi Rashin lpia akai shi asibiti, daga nan se likitan ya tabbatar mana ya warke, Amma ya manta komai daya faru a baya, kar kuma ayi yunk'urin tuna masa dan hakan ze haifar mada kwakwalwan sa matsala gaba d'aya. Inaga Wannan Shine musabbabin daya sakar masa ciwon k'ashin baya, ciwon k'oda kuma ban taba sani ba, se yau da likita ya bayyana a gaban ku a gaba na".

Kuka umma ta fara yi, sannan taci gaba da cewa,

"hajiya kuyi hakuri ku yafe mun, inaga inada lefi a ciki, da ban bada Wannan shawaran ba da tabbas matsalolin Baza suyi yawa ba, ni kuma a bahagon tunani na shawaran ze taimaka, ashe bansani ba sedai ya dad'a tarwatsa abubuwa ba. Hajiya Duk abunda salim yayi yayi ne saboda samun daidaituwar ku, yayi ne saboda ya samu karb'uwa a wajen Ki, yayi domin farin cikin Ki hajiya, yayi dan ya samu matsayi na d'a a wajen Ki, yana so Ki d'auke shi a matsayin da kika d'auki umar faruk, Amma se yake ganin kamar hakan baze samu ba. Hajiya ina amfanin haka? Shin ashe kin manta haqqi na 'ya' ya akan iyayen su? Shin hajiya ko kin manta cewa 'ya' ya Amana ne a wajen mu, kuma Allah yayi alqawarin ze tambaye mu akan amanar daya bamu ranar alqiyama? Hajiya kina da lefi, ina dashi suna dashi, kowa nada lefi a wajen Allah, Amma Allah dakan shi yace, idan munyi masa lefi mu kuma muka nemi yafiyar sa, haqiqa shi din me gafara ne kuma me Jin k'ai, hajiya tun wuri xan so Ki zubadda makaman yak'in Ki, hasali ma Ahmad bashi ya Miki lefi ba, lefin uba kuma baya shafar 'ya' ya, se idan dama kin k'udurta hakan. To ina Miki nasiha dani dake dasu mu tubawa Allah mu kama hanyar gaskiya, mu so 'ya' yan mu, mu kuma ja su a jikin mu, sanadiyyar hakan se kika ga mun samu rabauta. Hajiya halin da kika nuna wa salim na ko in kula shiya janyo har ya shiga Wannan halin, kinsa yana ganin kansa a matsayin me lefi, wanda Wannan tunanin ne yasa ya kasa tunkarar Ki shekara da shekaru Bayan dan uwan shi ya Gano shi acan Wata qasar. Har kinsa shi ya fara tunanin anya ma kece mahaifiyar shi kuwa? To ina amfanin hakan da girman Ki da ilimin Ki? Nasan fushin zuciya ba abunda baya haifar wa, Amma Ki d'auki komai ba komai ba.
Hajiya Ki dubi girman Allah idan ma kina rike dashi ne a ranki , Ki yafe masa, wllh fushin Ki kadai ya Isa ya sanya shi a Wannan hatsarin, Kisa a ranki Allah nason Ki da rahama ne, tunda har ya karbi umar faruk ya dawo Miki da makwafin sa, lallai Allah Shine hakimin masu HIKIMA, kuma shi kadai yasan abunda hakan ke nufi,,, idan kika yi tawakkali se kici ribar abun gaba, kuma Ki samu lada a wajen Allah.... "


Tunda umma ta fara magana, hajiya ta tsinke, ta kasa cewa komai, zuciyar ta na mata wani irin rad'ad'i. Tabbas hajiya tasan tayi kuskure, kuma hakika tane me nadamar abunda ta aikata, dukda cewa laifin mahaifin su shita tara ta tattara ta d'ora shi akan salim da be San hawa ba besan sauka. Cikin muryar kuka hajiya karime tace

"tabbas na tafka babban kuskure, hakika na zalunci Rayuwar SHA'IB, ni ban kasance uwa ta gari a wajen Shiba. Babu karfi babu dabara se a wajen Allah, duniya da lahira na yafe maka SHA'IB, Na yafe maka wllh, Allah ka yafe min nima. Hajiya nagode sosai da tunatarwar Ki a gare ni, shakka babu shed'an yaso yayi tasiri a zuciya ta. Hajiya ke Uwa ce jajirtacciya, Na g... "


Kafin ta k'arasa hajiya ta dakatar da ita da" ya Isa haka hajiya, Alhamdulillah hakan ma ya faran ta min, Allah yayi ma zuri'a Albarka "...


Saboda tsabar farin ciki hajiya karime bata ma San Sanda ta rumgume umma ba, tana zubadda kwallan nadama. Umma ma rumgume ta ba. BINAFA dake gefe tana aikin Abu d'aya, wato kuka, tana ganin kamar ita kanta tana da lefi, ta kasa yafe ma kanta. Umma ce ta janyo ta, ta share mata hawayen ta, sannan tace "ba lokacin kuka bane yanzu, addu'a zamu yi masa Allah ya bashi lpia yasa kuma ayi aikin a sa'a. Wato ke me uwa ko, kuka had'ewa d'ana kai keda hajiyar Ki gata nan ko? Ke me uwa? To kannaji kanna sake Jin makamancin Wannan, Dan idan hakan ta sake faruwa to Bazan yafe muku ba keda hajiyar Ki! "

Murmushi hajiya tayi irin nasu na manya tace tare da hade hannayen ta

" baze kuma faruwa ba insha Allahu rabbi, uwar d'a, a mana afuwa. "


Cikin yanayin farin ciki umma tace" to Allah ya yafe mana baki d'aya! "



Dikkan su suka amsa da" ameeen"! Ko wannen su fuska d'auke da fara'a.




Suna cikin Wannan yanayin ne likita ya fito, yake sheda musu....





Muje zuwa💃🏻

Taku har kullum

SIDIYA ✍

💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SIDIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚



*PAGE* 9⃣9⃣➡1⃣0⃣0⃣





Gaba ki d'aya hankalin su ya karka

Please Login or Register in order to submit comment