Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha mamaki kuwa yarinya"

A fili kuma ta furta

"Mota zaki shigo ko jirgi?"

Wangale baki smatcher tayi tana me kara kallon screem din wayan ,tace

"Wa ? Ni? Aah kema kinsan mota zan biyo ,inani Ina jirgi? Wannan kam aise Ku shegun gari, nikam banda kudin shiga jirgi"

Tabe baki Binafa tayi tace

"Matsiyaciya kawai. Toki je kiyi booking flight zan turo miki da kudin"

Smatcher tace
" da gaske? "

Wani guntun tsaki binafa taja ,sannan ta yanke kiran. Ba'afi minti goma ba tayiwa Smatcher transferred 50k. Ba kad'an ba Smatcher ta girgiza ,ba bata lokaci ta kira Binafa. Godia ta mata tare da sheda mata jibi zata shigo. Sannan sukayi sallama


Wani shu'umin murmushi Binafa tayi tare da furta

"Lallai Smatcher dani kike zancen, wasar kuma yanzu aka fara bugawa. Zan nuna miki ruwa ba sa'ar kwando bane ,kuma ni na wuce inyi takara dake, binafan da kika sani bata yanzu ba. Da sannu zaki gane da rarrafe Yaro kanyi tafiya ,kuma komai Nisan dare gari ze waye. Haka lokaci ne wannan da kuyanga ke haihuwar uwar gijiyarta. Tabbas kece uwar daki na amma a yanzu kam ,Binafa ta miki Nisan kiwo". Ta k'arasa maganan tare da fashewa da wani kafirin dariya.


Tana cikin wannan yanayin honourable ya kirata ,waya sukayi sosai ,har yake ce mata an k'ara mai wata d'aya. Ba kad'an ba ta nuna damuwar ta, ganin yadda abun beyiwa honourable dad'i ba yasa tayita kwantar mishi da hankali harta samu kanshi. Sunfi awa suna waya kafin sukayi sallama.

Tana aje wayan. Murmushin mugunta tayi tace

" ni wllh hakan yamun dad'i ,wannan ze kara bani daman shakatawa, Dan rainin sense kawai".

Wani dogon tsuki taja tare da wurgi da wayan.


Bayan kwana biyu misalin karfe 2 na rana Smatcher ta kira Binafa ta sheda mata zuwan ta. Tana asibiti amma ta nemi excuse ,ta kumayi sa'a aka bata. Motarta ta murza bata taka burki ko inaba se airport. Ba k'aramin gigita Smatcher tayi ba ganin binafa cikin wannan arniyan motan. Mamaki be kara kashe taba seda suka shigo gidan Binafa me gadi ya wangale musu gate. Kawo yanzu kam Smatcher tayi mutuwar zaune ,daka ganta kasan a firgice take, tana so ta gane shin mafarki
Take ko gaske ne...
Kamar wata zautacciya haka ta dinga bin gidan da kallo har suka k'arasa ciki...






Taku har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)






*PAGE1⃣5⃣➡1⃣6⃣*



Ciki suka k'arasa, Binafa na gaba janye da akwati, Smatcher na biye da ita a baya. Suna shiga parlour-n Smatcher itadai se kallon ikon Allah take. Har suka isa bedroom. Binafa aje mata akwatin ta a gefe. Ta juyi ta kalli Smatcher tare da cewa

"To Hajiya ta inafata kinga masauki na"? Ta k'arasa maganar lokacin da take zama daga gefen gadon

Baki Smatcher ta wangale ta kasa cewa komai, jin bakinta take kamar an Dora mata dutsen dala. Dakyar ta iya bud'e baki tana cewa

" um... Lallai fa naga wuri yayi kyau "...itama samun wuri tayi daga gefen gadon ta zauna tana me kare wa dakin kallo.
Murmushi Binafa tayi tare da matsowa kusa da Smatcher ta dafa ta tace

" Malama wannan kallon fa sedai kace wata dakkon jadad" dukan wasa Smatcher ta kai mata tana cewa

"Aah wllh banni inga abun azziki. Irin wannan kayan alatu haka. Wai kawata miye sirrin ne ,nifa gaba daya kin rikita mun lissafi. Amma dai gidan nan haya kika kama dai ko?" Binafa bata ce mata komai ba ,tashi tayi tabar dakin ,mintuna kad'an ta dawo da wani briefcase a hannunta zama tayi a kan gadon ta bud'e ,takaddun gidan ta d'auko ta bata. Smatcher ta karba tare da cewa

"Wannan fa?" Tace

"Zaki iya dubawa ,kinsan hausawa nace wa gani ya kori ji"... Sosai Smatcher ta firgita ganin abunda idonta ke gane mata ,wai wannan takaddun mallakin gidan Binafa ne. Mika mata tayi tana fad'in

" eh lallai fa nagani. Amma taya kika samu wannan gidan me kyau haka?" Kallon ta Binafa tayi tace

"Kawata wannan ba lokacin wannan maganar bane. Excuse na d'auko a asibiti naje na d'auko ki. Yanzu bari indan sama miki abunda zaki ci ,kafin in dawo se musha hira ,karki damu tawan feel free" . ta k'ara she maganan tana dafa kafadan Smatcher. Itadai ta kasa cewa komai ,tana zaune yadda kuka San andasa karas.


Kai kawai ta gyada mata. Binafa ta tashi ta nufi kitchen. Tunanin me zata dafa mata ta tsaya yi gashi bata so ta bata lokaci. Tunowa tayi da akwai kazar da salim ya kawo mata jiya gasash-she da bata ciba ,tasa a fridge. Fridge din taje ta bud'e ta d'auko kazar. Warmer ta kunna tayi warming kazar sannan ta juye a kula. Fridge din ta sake budewa ta d'auko mata drink 5alive ta Dora cup akan plate takai mata. Tace

"Yauwa toga wannan ki fara dashi, kafin in dawo. Amma zefi kyau ki Dan fara watsa ruwa ko?"

Tace

"Eh hakan zefi kam. Sannu fa da hidima"

Binafa tace

"Haba Hajiya ta Aikin fi karfin hakan. Bari inje kar inbata lokaci. Zuwa 6 zan dawo". Ta kai k'arshen maganan tana janyo wayarta dake kan mirror.

Smatcher masa

" to sekin dawo, adawo lpia".

Ta amsa da

"Allah yasa " sannan ta fice

Smatcher kam tafi minti talatin tana zaune tana ta nazari kafin ta tashi taje ta watsa ruwa. Koda ta fito kaya kawai ta canza tadan fesa Turare ,jin an fara kiraye-kirayen sallan la'asar yasa ta mike ta tada sallah ,seda ta gama sannan ta janyo kulan da Binafa ta aje mata. Gyara zama tayi ta narki kaza abunta sannan ta taushe dame sanyi. Hamdala tawa ubangiji sannan tabi lafiyan kado.


6 na yamma Binafa ta dawo ,jin bataji motsin Smatcher ba yasa ya k'arasa ciki. Dashe dashe ta samu Smatcher akan gado tana sharban baccin ta. Dariya tayi tare da sakar mata duka a k'afa. A gigice ta farka ,binafa ta kwashe da dariya tana fad'in

"To sarkin tsoro nice" hand bag dinta ta aje akan mirror tareda zare after dress din dake saman fararen kayanta. Murmushi Smatcher tayi tare da cewa

"Wllh kin tsora tani" mikewa tayi zaune ta Dora da cewa

"Har kin dawo kenan"?

Binafa ta amsa da

" aikuwa Allah yayi. Aikin ne akwai gajiya ,seka kai zuciya nisa. Bari indan watsa ruwa ko sallah la'asar ban samu nayi ba". Tana magana tana rage kayan jikinta. Towel taja ta fada toilet ,tayi wanka tareda dauro alwallah. Tana fitowa doguwar Riga kawai ta zura ta tada sallah. Seda ta idar tayi addu'o'i sannan ta janyo wayarta tayi dialing my blood. Dan tana aiki dazu daga missed call dinta.

Bugu daya ta dauka. Sallama ta mata sannan suka gaisa. Umma tace

"Dama inaso ingaya miki kaya sun kare ,duk an had'a kudin se neman su ma ake. Kiyi kokari a turo wasu!"

Binafa tace

"Wai har sun kare? Aikuwa sunyi saurin karewa wannan karan ,sati ukku fa kenan?"

Umma tace

"Kedai bari Allah ya sawa abun albarka ai ,semu kara gode masa".

" hakane kam Umma. Insha Allah zanyi kokari gobe inshiga Kasuwan a sissiyo."

Umma tace

"To Allah ya dafa mana".

Binafa ta amsa da

" ameen". Ta Dora da cewa

"Yauwa Umma kinga nayi waya da uncle idris jiya ,yace next week su musaddiq zasu koma school?"

Umma tace

"Aikuwa anyi haka"

Binafa tace

"To ba damuwa zan turo mai da kudin school fees dinsu seya je ya biya"

Umma tace

"Aah kibar shi akwai kud'i a hannuna ,bana son kasuwancinki ya tabarbare".

Binafa tace

" aah Umma ai akwai kudi a hannuna ,saboda yanzu kayan har bauchi nake turo wa wajen maman husnat ,kusan wata biyu kenan ,ina tura mata tana Dora nata riban akai, kuma alhmdllh ana samun ci gaba"

"To masha Allah ,hakan Nada kyau naji dad'i sosai ,Allah yayi albarka." Umma ta bata masa. Kafin ta mata sallama ta yanke kiran.


Binafa na aje wayan tawa uncle idris transfer din 30k ,sannan ta kira shi ta sheda mai ta turo kud'i.
Tunda ta fara waya ,baki a sake Smatcher ke kallonta jin har kasuwanci take. Da mamaki take kallon Binafa tace

"Business kike ne?"

Murmushi Binafa tayi sannan ta bata labarin yanayin yadda kasuwancin nata ke tafiya. Mamaki ne shimfide a fuskan Smatcher. Ganin haka yasa binafa ta kauda zancen tace

"Kinga tashi muje in xaga dake kiga tsarin gidan". Ba musu Smatcher ta mike ,nan binafa ta dinga zagawa da ita har akayi sallan magrib sannan suka koma ciki.
Misalin bayan isha kiran salim ya shigo wayan ta. Dauka tayi suka gaisa. Har take CE masa yazo ya kaisu yawo sistern ta tazo, yace ta bashi 30mins


Sanin da tawa salim na baya wasa da lokaci yasa tace Smatcher ta shirya su fita. Nan suka tashi suka kimtsa. Yazo ya dauke su. Wajen cin abinci ya fara kaisu ,sannan ya dinga zazzagawa dasu cikin gari. Ya biya ya musu shopping ba nida shopping ba. Se 11 na dare ya dawo su. Kyautar kudi ya bama Smatcher na 50k ,yace

" sister ga wannan ayi hak'uri dashi. Zaro ido Smatcher ta shiga yi tana fad'in

"Aah wllh ka bash-shi hakan ma mun gode" aikuwa salim ya dage akan seta karb'a. Haka Smatcher ta karba tanata mai godia ,nan ta fita yabar su tare da Binafa.

Minti 20 da shigan Smatcher Binafa ta shigo. Nan suka baje parlour sunata duba siyayyen da salim ya musu. Smatcher se santin kayan take. Nan take tambayar ta

" wai nikam binafa ina kike samun kudi ne haka ,da masu kud'i ,abun fa yaso ma bani tsoro?"

Dariya Binafa tayi nan ta fara bata labarin Wanda ya bata gida da mota da yadda ta had'u dashi. Da mamaki Smatcher ke kallonta tace

"Amma dai baki barsu haka ba dai ko?"

Binafa tace

"Tace kema kin sani ,ai sawa nake a rike mun su"..

Smatcher tace

Amma dai kina Dan basu abunnan ko?"

Binafa bata amsa taba ,Dan wannan sirrin tane se kawai ta share. Ganin bazata amsata taba ,yasa itama ta share seta kara wurga mata wani tambayar tace


" ni kuwa a ina kika samu wannan shahararren malam daya iya aiki haka?"

Binafa tace

"Wanda dai kika sani ne ba wani ba!"

Tace

"Badai malam musa me farin allo ba?"

Binafa tace

"Shi kuwa"

Da mamaki Smatcher tace

"Aini na yadda shi danko yamun aiki baya ci."

Se a lokacin Binafa ta tuno da maganan da Malam musa ya mata na cewa bayawa mazinata aiki.






Taku har kullum
*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE1⃣7⃣➡1⃣8⃣*



Smatcher ta katse mata tunanin da take da cewa

"Anya dai malam musan ne ? Kodai kin samu Wanda ya fishi iya aiki ne? ,amma da mamaki ace malam musan da nasani shike miki aiki"...

Binafa tace

" kindai San shige shigen malamai ba Sana'a ta bace ko? Wannan din ma tare na ganku danke kika had'a ni dash. Sannan abunda yasa kikaga harmun jima tare na fuskanta cewa bawai malamin tsubbo bane ,da ayar Qur'ani yake aiki ,kuma inajin dadin Aikin shi."

"Eh sosai na fiki sanin ba malamin tsubbo bane. Amma abunda nake mamaki shine meyasa idan yamun aiki baya kamawa?"

Wani guntun tsaki Binafa taja tare da cewa

"Wannan kuma seki tambayi kanki. Saboda karki manta malam musa Nada dokoki da shuradai Wanda idan ka bisu ba zaka taba samun matsala da Aikin shiba. Ke kuma bakya bin wa'yannan dokokin"..


Cike da mamaki take kallon Binafa tace

" ke nifa ban fahimce kiba!"

Tace

"Smatcher amsar tambayar ki a fili take. Keda kanki kinsan kina huldayya da maza ,ma'ana kina ba maza kanki, kuma doka ce ta malam matuqar kana zinace zinace koya maka aiki baya tasiri. Karki manta da labarin fauziyya daya bamu mana. Tana son dauda amma ba wata tsayayyar magana tsakaninta dashi. Data je wajen malam ,yace ze mata aiki akan shi ,ya Kuma gayamata dokokin tace ta amince. Ba bata lokaci malam ya fara doka mata yasin, cikin wata biyu dauda ya kawo kudin gaisuwar ta. Ya rage takaiwa malam kudin sadaka. Saboda kinsan baya karban kudin ka se idan yama aiki Aikin yayi kyau. Fauziyya tazo ta rasa abun kaiwa Malam. Taje akayi zina da ita ta samu kudi ta kaima malam ,kina jin yadda yace mana a lokacin wata shidda kenan da kawo kudin gaisuwarta amma magana tsit kuma har yau ita ake magana ba labari ,ita duk a tunanin ta malam baze gane bane ohon mata..."


Wani kallon rainin hankali Smatcher kebin Binafa dashi tace

"Dalla malama karki raina wa kanki da wayo ,yo kedin me kike inba kici kudin maza aci ki ba. Wani shegen ne ze dinga kashe miki kud'i haka ba tare da kina bada abun nan ba. Mtsss" taja wani guntun tsaki.

Itadai Binafa bata rabata dako kala ba jin ma zata bata rai yasa tace

"Kinga ni ban iya gaddama ba. Bacci zanyi seda safe" ta k'arashe maganan tare da figan hang bag dinta ta wuce daki ,seda tadan watsa ruwa tayi sallah ,karatum Qur'ani tadan taba kafin tayi addu'a ta rage wutan dakin ta kwanta.

Smatcher na nan inda Binafa ta barta da tarin tunani a ranta ,tasan tabbas abunda Binafa ta fad'a haka tsarin malam yake ,wani abun ma da Binafa ta manta dashi shine ,idan ya fara ma aiki baka canza Malami ,amma ita ta canza malamai sama da ukku. Can kasan makoshinta ta furta

"Tabbas nasan halin yarinyar nan. To amma ita din me take idan ba bin mazan ba. Nasani sarai akwai wata a kasa"...

Da wannan tunanin Smatcher tayi bacci na seta gano wani irin sirri Binafa ke boye wa, taci alwashin seta hako sirrin boye.


Washe gari da asuba Binafa ta fara farka wa, bata yi mamakin ganin Smatcher a kusa da ita ba. Toilet ta shiga tayi alwallah, ta fito ta tada sallah. Seda ta idar sannan ta tashi Smatcher dakyar ta mike tayi sallah. Addu'o'i Binafa ta shafa sannan ta zare hijabinta tare da fita daga dakin.

Kitchen ta wuce ,ruwan zafi ta fara Dora wa na tea ,daya ji kayan kamshi ,sannan ta fere doya ta dafa ,ta soya musu. Cikin 30mins ta kammala ta dauka ta koma dakin ganin Smatcher tayi ta koma bacci ,bata bi ta kanta ba ganin lokaci na tafiya.
Wanka ta shiga tayi ,ta fito ta shirya cikin school uniform farare tas da suka ji Karin guga ,batayi wata wata na ta zauna ta had'a tea me kauri tasha ,bata wani ci doyan ba Dan tsakura tayi ta mike tare da hamdala ga ubangiji. After dress dinta ta zura tare da daukan Jakarta, kamar bazata tashi Smatcher ba se kuma tayi tunanin be kamata ta fita bata sanar da itaba.

Wani duka ta sakar mata a kafa ,Smatcher ta bud'e ido tana mika ,tace

" ni zan tafi asibiti, idan kin gama kwanan laushin ga break fast dinki nan." Ta k'arasa maganan tana saka takalmi. Taci gaba da cewa


"Ki shirya idan na dawo karfe biyu zaki rakani kasuwa siyayya Dan gobe nake so in tura kayan"

"Adawo lpia Hajiya nurse" shine abunda Smatcher ta fad'i tare da maida kanta ta kwanta. Binafa ta amsa da

"Ameen" lokacin da take ficewa daga dakin


A asibiti sosai suke jin dadin aiki da Binafa ,kowa yabon ta yake ,a nutse take gudunar da abubuwan ta cikin kwarewa. Dan idan kaga yadda take aiki a wajen ba zaka taba cewa practical tazo ba. Kai kace ma'aikaciyar wajen ce. Babban likitan asibitin ma ,seda ya roke ta cewa Dan Allah yana so idan ta kammala karatun ta tazo tayi aiki dasu.



Karfe biyu binafa ta dawo ,ko gidan bata shiga ba tama Smatcher waya ta fito su wuce. Smatcher tace mata

"Abinci fa?"

"Idan mun dawo naci, nidai kiyi sauri". Ta bata amsa tare da yanke kiran.


Siyayya tawa Umma kamar yadda ta saba. Smatcher se Binta take kamar jela. Sun tsaya wani babban shago ,Binafa ta dubi Smatcher tace

" inace kema kince siyayya kika zo?"

"Eh.eh amma"... Smatcher ta amsa ta kamar Mara gaskiya. Binafa basarwa tayi se kuma tace

" kije ki duba abubuwan da kike so" ta k'arashe tana duba wasu material. Ganin harta kusa kammala wa Smatcher bata dau wani kayan kirki ba ,yasa taje ta dinga daddaukar mata, itadai Smatcher se Binta take da ido ,a haka har suka k'arasa siyayyan ,Binafa ta biya kudin. Na Smatcher kawai wajen dubu saba'in da wani Abu ta kashe. A haka aka sa yara suka kai musu kayan mota. Seda ta biya ta bada sakon kayan Umma sannan suka koma gida.


Suna hira Smatcher ke cewa

"Amma dai Binafa kayan nan kin bani ne insa riba na akai idan na siyar inturo mk da kudin ko?".

Binafa dake danne danne a waya tace

" aah bana buk'atar komai a wajen ki. Na baki ne kema kije ki tsaya da kafafunki ,ki kuma yi watsi da wannan shashancin".

Godia Smatcher ta fara mata ,ta katse da


"Ni bansaki kimun godia ba ,na miki ne Dan Allah"
A haka suka ci gaba da hirarrakin duniya.


Bayan sati biyu Smatcher ta koma ,kamar bazata tafi ba saboda taji dadin zama da Binafa. Binafa ta shiga wata na had'u a asibiti. Honourable kuma be dawo ba, se idan sunsa ranar dawowa a kara tura musu wani Aikin. Sako akan kari Binafa najin alert. Ga salim daga damanta ,hankalin ta a kwance zuciyar ta a nutse. Dikda cewa ya koma amma suna yawan waya akai akai.
A haka harta kammala practical dinta. Randa taje musu sallama wasu nurses din hadda hawayen Sabo. Alkhairi suka mata sosai cikin kewa suka rabu.


*BAYAN SHEKARA DAYA*


Binafa ta kammala karatunta. A yanzu kam ba abunda ta nema ta rasa a rayuwa. Azziki Kuma yaci uban Nada. Ana gobe alhamis za'a musu walimar graduation dinsu. Ranar laraba taja wata qawarta Wanda course mate dinta ce ,taje tazo ta rakata office din director. Bata kawo komai a ranta ba ,suka nufi office din ,knocking suka masa ya basu izinin su shigo.


Gaishe shi sukayi ya amsa sannan Binafa ta gyara zamanta tace

"Sir nazo in maka godia ne abisa dikkan taimakon Dana samu a makarantan har Allah ya nuna mun na kammala lpia. Naji dad'i sosai Dan banida bakin dazan gode muku". Jakarta ta bud'e ta d'auko naria duba Dari biyu da aje mai akan table dinshi tace

" wannan kudeden makaranta ne da ake bina gashi Allah ya hore na biya". Tana kainan ta fice daga office din ,billy tabi bayan ta. Seda suka fito billy ta kalleta rai abace tace

"Gaskiya binafa baki kyauta ba ,banjin dadin abunda kikayi ba ,meyasa zaki bama director kudi ,bayan kinsan kyauta kike karatu a school dinnan tun lokacin da suka ji labarin ki"...


Murmushi binafa tayi Wanda yafi mari ciwo tace

" billy nasan abunda nake yi. Sedai ya kamata ki fahimta ,binafan da ke Neman taimko ,amma binafan yanzu sedai ta taimakawa wasu". Ta k'arasa maganan muryanta na rawa. Kan kace ma kuka yaci karfin ta. Billy taji duk tausayin Binafa ya kamata ,lallashin ta ta shiga yi ,dakyar ta samu ta tsagaita kukan...







har kullum
*SIDIYA* ✍

💖💖💖💖💖

*BAN YI NADAMA BA*

💖💖💖💖💖

Has been change to

💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖



*Note: zaku ga cewa na canzawa littafin suna daga BAN YI NADAMA BA zuwa BINAFA. Nayi hakan ne badan wata manufa ba sedan samun maslaha. Kasancewar naga wata marubuciyar ta fara littafin the same da sunan nawa. Hakanne yasa nace bari in canza nawa Dan kar ayi confusing readers. Da fatar hakan bazai rikitar da masu bibiyar wannan littafi ba. Masoyan wannan littafi ako ina kuke kuna raina. Kuci gaba da kasancewa tare dani SIDIYA dan jin yadda kayataccen labarin BINAFA ze cigaba da antayo muku. Karku manta da sauran tafiya. Nagode*


*Gift to my beebah (marubuciyar ZARAH). Thanks 4d advised tawan. Hakika ke din ta daban ce. Ina yinki over over. Lodi lodi .Luv u wujiga wujiga. 💋😂*



*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)




*PAGE1⃣9⃣➡2⃣0⃣*




A haka suka k'arasa ciki. Washe gari akayi walimar graduation din su Binafa. Ba kadan ba sunyi kyau ,dan kuwa anko sukayi na material yello da bakin head. Dikkan su ba baya ba musamman mutuwar ,dan ita alkebba ta dora a sama .


Walima akayi Wanda manyan mutane da yawa suka hallara. Ga 'yan uwa da abokan azziki. Dan har umman Binafa ma tazo taga abuja ,se nan 'yan uwanta na Kano duk sun halarci taron. Walimar yayi jama'a anci ansha abun ya qawatar se Wanda ya gani. Sun samu kyaututtuka daga manyan mutane daban daban ,ba kamar Binafa dake da daukan hankali. Lokacin da aka zo gabatar da taron ita ta bud'e taron da addu'a se 'Yar takaitaccen nasiha data gabatar, itace MSS president na makarantan. Ba kad'an ba nasihan ta ya shiga mutane domin kuwa tayi tunatarwa ne akan wuta da aljanna ,se shagaltuwa da duniya. Wanda taja ayoyi na alqur'ani da manyan sahihan kuma ingantattun hadisai. Ba kad'an ba yanayin yadda tayi gabatarwan ya burge mutane. Wasu hadda en guntun hawayen su na taqawa.


Ba'a tashi ba se wajejen azuhur. Umma ba kad'an ba taji dadin yadda 'Yar tata ta samu karbuwa ,
Banda kyaututtuka data samu ,banda zunzurutun kudi. Ga kyautan admission da honourable Alh Adamu fagge ya bata ,idan tana da ra'ayin ci gaba da karatu. Ga kyautan mota da comrade junaida ya bata kirar corolla. Umma bata san lokacin data fara hawayen farin ciki ba .


Bayan taron haka manya manyan mutane suka dinga zagayawa wajen director-n makarantan suna tambayan numbern Binafa. Director be so ba amma haka yakai zuciya nisa ya basu. Dukda binafa bata so ba ,amma kuma hakan ba k'aramin dad'i ya

Please Login or Register in order to submit comment