Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan numbern 08168187344 ko ta ACC dina

6321481778
,Sadiya Said Sidi,
fidelity bank...


Sena jiku
Nagode...💖🤓💖








Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SIDIYA ) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



Assalamu alaikum warah matullahi wa baraka tuhu. Masoya en uwa da abokan Azziki ina me farin cikin sanar daku na dawo da izinin Allah zamu d'ora daga inda muka tsaya, da alkawarin zaku dinga ji na akai akai, sedai kunsan d'an Adam da ajizanci, se a hada min da uzuri ...🥰🤝


Idan Baku manta ba mun tsaya a Shafi na 75-76 yanzu zamu d'ora daga inda muka tsaya. Gamai buk'atar tun daga Farko ze iya tuntub'a na insha Allah nagode.



*PAGE* 7⃣7⃣➡7⃣8⃣





BINAFA na tsaye da hoton a hannunta umar ya k'a raso fuskarshi dauke da annushuwa. Ganin binafa yasa shi ya kara Fad'ad'a fara'ar shi. Karasowa yayi yana mata sannu da zuwa, nan ya sallami Duk ma'aikatan dake kai kawo. Sannan ya maida duban shi gare ta.

"yadai madam yau ba magana?"

D'an murmushin yak'e ta k'ak'aro tare da tattara nutsuwarta. A kasalance ta furta

"barka da wuni babban me gida, ya gajiyan aiki?"


"Alhamddulillah! Gajiya ai ya warware tunda naga farin ciki na, me Jin tausayi na kuma uwar baby na".


Dikkan su murmushi ne dauke a fuskokin su gwanin ban sha'awa. Ko kadan hankalin umar faruk be kai ga hoton dake hannun BINAFA ba, dukda cewa ta juya hoton ba lallai ya iya gane wani hoto bane a hannunta. Hannunta ta ya rik'o tare da cewa


"matar umar dan Allah muje Ki bani abinci inci, yunwa na nema ta kassara miki miji". Yanayin yadda yayi maganar a shagwabe ya bata dariya, wanda ya bayyana dimple d'in ta. Hannu umar yasa a tsakiyar dimple din yana wasa dashi tare da cewa

"dimple na miki kyau matar umar. haka nake so Ki haifa mun baby me dimple kinji?". Ya karashe maganan yana shafa cikin ta.

Maganar shi yayi daidai da motsin dan cikin ta. Dagowa yayi yana kallonta

"kinji baby nama naso ko?" shafa cikin ya shiga yaci gaba da cewa

"karka damu babyna idan momma bata haifo mun kai da dimple ba idan kazo zaka tayani mu mata bulala"...

A Karo na biyu cikin ya sake motsawa.

Umar faruk yace
" kinji ina magana da baby na ko? "


Dariya dikkan su suka sa. BINAFA tace

" nidai muje kaci abinci, karku ishe ni da shirme kaida babyn Naka "

Dan ja baya yayi yace

" au kice mun kawai kinji haushi? To maza Ki xauna risho "

Murguda masa baki tayi tare da cewa

" can da yawar Ku. Oya muje kaci abinci Wannan lokaci nane bana babynka ba, seka jira babyn Naka idan yazo se kuyita shiriritan kaga ka samu aikin Ki seka aje Wannan baban baby. "


Yace
" yes gani! "
Ya k'arasa maganan yana wani daga ka fad'a

Dikkan su suka sa dariya. Zaunar dashi tayi, sannan taje ta wanko hannunta a wash Basin dinda ke cikin office d'in.


Zuba abincin ta fara yi a plate. Nan wani k'amshin dad'i ya daki hancin umar faruk. Wani lumshe ido yayi tare da furta

"Ni'imal bint... Ni'imal bint...ke matar umar wllh ai dai lobiyuu"

"I lobiyuu too mijin BINAFA"

Wani dariya suka sake sawa, kafin ta dawo kusa dashi ta zauna, basmala tayi, sannan ta shiga debo abincin da hannun ta tana bashi a haka har seda ta tabbatar ya koshi sannan ta tsiya ya masa kunun ayan data zo dashi wanda Yaji kayan kamshi, ta bashi, umar be dauke kai ba seda ya tada kofin sannan ya furta


"alhamdulillahi! Samun mata ma data iya kunun wake ba kunun alkama ba abun alfahari ne" ya ida maganan yana wani dogon mika.

Cikin dariya binafa tace

"ba lefin ka bane!"

Yace
"to lefin waye?"

Tace masa
"ah! Lefin Masu noman ayar ne mana".


Wani dariya suka fashe dashi. Ranar dai haka suka wuni cikin raha da kaunar junan su. Basu suka tafi gida ba se yamma.



Da daddare Bayan sun yi shirin kwanciya. Binafa ke tambayar umar hoton data gani a office din shi. Wanda dama ta kagara su dawo gida ne tazo mishi da tambayar, ko a dazun abunda ya hanata tambayar shi, ganin shi data yi cikin fara'a da walwala, bata so ta bijiro da wani abunda ze bata musu Wannan moment din.


Ta maimaita tambayar yafi so a kirga. Umar faruk se dafe kai yake yana Jin tambayar har cikin k'ahon zuciyar shi, Jin binafa taki sarara masa da tambayoyin ta Masu kara hargitsa tarin farin cikin daya Dade yana tsarawa.


Cikin Wata dakakkiyar murya me kada 'ya' yan hanji wanda bata San shi da ita ba.


Binafa bata lura da sauyawar yanayin saba, seda ya daga yana binta da wani gigitaccen kallo me alamar tuhuma.


Nufo ta yayi gadan gadan kamar ze doke ta ya shiga nuna kanshi da yatsa yana Fadin

"mene miki fatima? Me na miki da kike son ganin Bayan farin ciki na? Anya ma kina sona kamar yadda kike cewa? Meyasa Wannan ranar tazo mun a haka?"



Shane! Sega hawaye nabin kuncin sa. Nan fa hankalin binafa yayi mugun tashi, ba shiri itama ta fara Kuka, tana data sanin bijiro masa da Wannan tambayar dukda cewa tana da buk'atar sani.


Girgiza shi tashiga yi tana so ta furta kalman lallashi, Amma bakin ta ya mata nauyi.

Rike shi tayi tana so ta masa magana, Amma ya fizge jikin shi daga nata yabar Dakin jikin shi har wani tsuma yake, kafafuwan shi na nema kasa daukar shi.


Nan binafa ta zube a kasa ta fashe da wani Kuka me tsuma zuciya...




*************


Shin ya labarin laure? 🤔A

bangaren gidan alh Ibrahim arille kuwa(mahaifin binafa)...











Muje zuwa yanzu aka fara wasan... 💃🏻

Taku har kullum
SIDIYA ✍

Magana
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 7⃣9⃣➡8⃣0⃣






A b'angaren gidan alh Ibrahim arille (mahaifin binafa), yanzu komai ya k'are, laure ta tattara dikkan dukiyar shi ta kwashe ta fara kasuwanci, ya koma summas sabila yassara, ba taro ba sisi, GA Rashin lpia dake damun shi na hawan jini Amma ba kudin zuwa asibiti, idan yace takai shi asibiti se ta fara masifa da bambami,, tana fad'in bata aje ba bata ba wani ajiya ba, Itace komai na gidan, nan fa gori ze tashi, idan kuma yace ta kira Mai su abdallah su turo Mai se Tace ai ko ankira baya shiga, idan ta fita kuma seta zagaya ta kira in suka turo kudin kuma ta dena. A takaici dai Bela Itace mijin alh ya koma matar, Abu kadan da yayi se fada da masifa kamar tana yi da dan ta...


Yau ma alh Ibrahim ne ya shigo gidan, dauke da sallama, Bela na tsakar gida tana kwasar farfesun kayan ciki, tana dangwalawa da biredi. Har alh Ibrahim ya kawo daidai kusa da ita bata daga ta kalle shiba.

Da murmushi akan fuskar shi, yace

" hajiya hutawa Ake?"

Tayi banza dashi, ganin hakan yasa ya kama bakin shi yayi shiru, Dan yasan ba karamin aikin ta bane idan ya Dame ta tamai zagi na uwa na uba...

Seda ta cinye tass, ta dago tana lashe hannu, sannan ta turo Mai gaban shi,

"gashi nan seka Dauka ka ida lashewa tsohon maye do, Dan nasan abunda ya tsaida ka Kenan"... Ta karashe maganan tana mikewa tare da cewa


" idan ka Gama ka hada da sauran kwanukan ka wanke mun su, GA kuma kaya na nan a daki na wanki, idan ka Gama se kayi shara ka d'ora mun girki, danni idan na fita se dare, kasan yau talata, yau ake sauke min dila."

"adawo lpia" shine kadai abunda alh Ibrahim ya iya furtawa...




*************



Tun daga ranar da binafa ta tambayi umar waye Salem?, bata sake gane kanshi ba, yazo ya dena zama a gida, abinci idan tayi ta aje Mai idan ta fito da safe haka zata taradda shi kamar yadda tabar shi ba'a taba ba. Kafin ta tashi da safe kuma ya shirya ta tafi aiki, binafa ta rasa meke mata dad'i a duniya, ga umar yaki sauraren ta. A haka ta Yanke shawarar data je ta sanar da hajiyar shi halin da ake ciki, batayi Kasa aguiwa ba, ta karbi shawarar da zuciyar ta tazo mata dashi dari bisa dari...


Da yamma likis ta, ta gama shiri, tasa babah dije ta hada mata dan abinci mara walaha, sannan ta biya tayi dan siyayyan tsaraba, wanda zata rabawa ma'aikatan gidan.
Da kanta taja motar, bata taka burki ba se farfajiyar gidan su umar faruk. Tun daga gate Masu aiki keta murnar ganin ta, se zuwa gaishe ta suke yi. Duk Wanda yazo da tsarabar shi yake tafiya, se saka mata albarka suke.


A haka ta rantaya ta karasa cikin gidan. A babban parlour - n gidan taci karo da hajiyar umar. Da murna ta tarbe ta, nan danan tasa aka kawo mata kayan lashe-lashe da tand'e-tand'e. Gaisawa sukayi cikin girmama juna, sannan suka dan taba hira kadan, kafin binafa ta gayama hajiyar abunda ke tafe da ita.


Gaban hajiyar umar ne ya fadi Jin zancen da binafa tazo dashi, nan take wani tsufa ya fara karya mota.
Zare glasses din da ke idonta tayi, sannan ta kure binafa da ita na tsawon mintuna talatin kafin ta janyo wayarta dake gefen ta. D'an danne danne tayi kafin ta mika wa binafa wayar, kallon ta binafa keyi alamar bata gane ba, hajiya ta mata nuni data karbi wayar, jiki a sanyaye binafa ta karbi wayar, hotu na ta gani na salim da umar tun suna kanana, bin hoton tayi da ita, kamar ance taja wayar Sega wani hoton ya bayyana, sedai Wannan karon ba suka dai bane a hoton hadda wani kyaky-kyawan saurayi, wanda kusan dik kamannin su daya da umar, haka tayita ganin hoto kala-kala, dukda cewa ita bata gane me hakan ke nufi ba.


D'agowa tayi ta kalli hajiya, hajiyar ma ita take kallo, murya can kasan makoshi hajiya Tace mata

"akan salim kike Tambaya ko?"


Gaban binafa ne ya shiga dukan uku uku, bata iya bude baki tayi magana ba sedai ta amsa mata dakai.


Tashi hajiya tayi ta shige daki. Binafa na zaune a parlour, tun binafa nasa ran fito war hajiya, har taga kusan awa biyu ba hajiya ba labarin ta, tashi tayi ta nufi Dakin, a mamakin ta se taji kofar gam a kulle, tayi knocking shiru...



Mamaki ne sosai ya cika ta da fargaba, a gefe daya kuma tsoro ya lullube ta.


Ta daukar wa kanta jin koma menene matsalar dan haka ta Yanke shawaran kwana a gidan.


Idon ta biyu har asuba tana sa ran ganin hajiya, Amma shiru...


Me aikin part din hajiya ta buk'aci ya bata extra keys na part din, ba bata lokaci kuwa ya dauko mata akwatin makullan. Haka tayi ta gwadawa har Allah yasa ta samu na Dakin da hajiyar ke ciki.




Tura kofar Dakin tayi, ta shiga da salama dauke a bakin ta...










Taku har kullum

SIDIYA ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 8⃣1⃣➡8⃣2⃣






Tsantsar tsoro ne ya bayyana akan fuskar BINAFA, ganin hajiya data yi Duk ta fita a hayyacin ta, fuskar ta ta kumbura tayi jajir abunka da farin mutum, da alama Kuka ta kwana yi.

Ba shiri BINAFA ta k'arasa gefen gado inda ta hango hajiyar a rakub'e. Wani marayan Kuka ta fashe dashi tana jijjiga hajiyar...

"hajiya mena muku da kuke so Ku jefa ni cikin mawuyacin Hali? Ashe Baku dauke ni kamar yadda na dauke Ku ba? Ashe Bamu zama daya ba kamar yadda kika sha fadi ba? Ashe ban yi banyi matsayin da zansan komai naku ba? Shin hajiya menene lefi na idan naso Jin damuwar Ku? Hajiya Ki tuna fa ni fatima ba abunda na boye muku dan gane da Rayuwa ta, Kin ga kuwa ban cancanci Ku boye mun naku ba,,, hajiya komai d'acin labarin da kuke boye mun baze kai labari na ba na tabbatar da ha... "


Bata k'arasa ba hajiya ta rufe mata baki , tana girgixa kai, cikin yanayin Kuka da disash-shen murya take magana


" A'a BINAFA, karki kuskura Ki furta hakan, da kinsan munin abunda muke boyewa da baki danganta kanki dashi ba... Da kinsan Shekara nawa da kuma yadda mukayi kokarin kawar da Wannan damuwar da bakiyi kokarin Jin Wannan haramtacce kuma k'azamin labarin ba...

Tabbas kin zama mu mun zama ke, baki cancanci mu boye miki komai ba, sedai Ki sani ba munyi hakan bane da wani manufa shi Allah ya sani, A'a munyi hakan ne dan samawa kan mu da dik wani na tare damu mafita, maslaha da kwanciyar hankali, Amma tunda kin matsa se kin ji "...


Wasu siraren hawayen bakin ciki hajiyar umar ta goge sannan ta soma Bama BINAFA labarin su kamar haka...



" nasan BA'ISH (sunan da hajiya ke Kiran umar dashi Kenan na yaren Sudaniyya), ya sanar dake asalin mu da kuma dan abunda ba'a rasa ba dan gane da rayuwar mu, sedai nasan ko ze fada miki komai baze sanar dake labarin mahaifin su ba, hakane?"

Kai kawai BINAFA ta iya gyad'awa.


Wani murmushin takaici dayafi mari ciwo hajiya tayi, wanda be hana kyawun manyan tanta fitowa ba dukda yanayin data ke ciki a yanzu.


A jiyan zuciya tayi, sannan taci gaba kamar haka...


"mu 'yan asalin k' asar Sudan ne, karatu ne yakai mahaifin su BA'ISH garin mu nan cikin FARSANDA har Allah ya kulla alaqar aure a tsakayin mu.


Auren mu bada jimawa baban su BA'ISH ya fara harkan shiyasa wanda raina be so ba, haka dai yayita kwantar mun da hankali har hakura.


Bayan munyi aure muna zaman lpia daidai gwargwado, sedai Duk lokacin dana samu ciki ya Allah baya zama, tun abun baya damu na har na fara damuwa, sedai ko rabin damuwar baban su BA'ISH banyi ba, Dan kuwa Duk inda Yaji magana seya karbo mun, kuma seya tabbatar na Gama Amfani Da maganin, hakan yasa na rage damuwa ganin yadda mijina ke iya bakin kokarin shi a kaina, sedai yin angwada angwada ba'ayo sa'a ba.

To a lokacin iyaye na nada rai, kuma kinsan tausayi da irin son d'a na iyaye, haka suka dage da aiko mun da magani, har Allah yasa cikin zauna, sannan suka gargad'eni akan karna sake na sake shan wani magani matuqar basu bane suka aiko mun. To a hakane har na haifi 'ya ta ta Farko FAREESA, dangi en uwa da abokan Azziki kowa yayi murna ba kamar mahaifin ta dako fita ya dena saboda ya kula da ita. Soyayya da gatan duniya FAREESA ta ganshi agun mahaifin ta dama Duk wani dan uwa nawa. Dukda cewa' yan uwan shi Bama wani ga maciji dasu, musamman kanwar shi ZINNURAT Duk a ganin su Nike hana dan uwan su zuwa wajen su, Dan shi mutum ne da baya son zumunci, baya kuma shiga mutane, Na masa fada na masa nasiha Amma ba wanda yayi aiki, a haka harna hakura na kyale shi...


To Allah dai da ikon shi, shekaran FAREESA daya da Wata biyu tayi Zazzabin kwana uku, ta Amsa Kiran ubangiji, dik da cewa yarinya ce Amma akwai ta da shiga rai, ba wanda be ji mutuwar nan ba, musamman mahaifin ta dahar da Rashin lpia yayi na Rashin ta...


Na dauki dangana nabar wa Allah. Wata shidda da rasuwan ta, Na kara samun wani cikin, sedai banyi daukin shi dan gani nake abunda ya faru akan FAREESA hakanne ze sake faruwa, a haka na raini cikin harya Isa haihuwa, gashi ba karamin jigata nake ba a wajen haihuwar, hakanne ma yasa mijina ya karbo mun maganin Wannan matsalar, alhamdulillahi ban wani sha wahala ba kamar lokacin haihuwan FAREESA, sedai d'an Kuka daya yayi tarihi ya maimaita kan shi.


A haka seda nayi haihuwa tara, wasu Bayan na haife su darai suke mutuwa, wasu kuma basa na zuwan darai. Abun ya ishe mahaifi na, musamman ya shirya ya tafi kuwaiit dan gane inda matsalar take, saboda kawo yanzu kowa da abunda yake sakawa a ransa.


Bayan yaje kuwaiit wajen wani babban aminin sa, shiya kai shi wajen wani malami , anan ake sheda wa mahaifi na mijina na cikin kungiyar asiri, dana maita, wanda Duk b'arin da nayi a baya da 'ya' yan dana ke haihuwa basa zuwa darai shine sanadi.



Sosai mahifina ya girgixa, anan dai malamin ya bashi magani a kawo mun, wanda zanyi Amfani dashi Duk lokacin da na samu ciki.



Mahaifi na ya shiga taraddadin ta wace hanya ze iya sanar dani Wannan mummunan labarin...



A hanyar shi na dawo wa daga kuwaiit, Allah ya kaddara Mai hatsarin jirgi su talatin da bakwai a jirgin ba wanda ya fita darai... "





Taku har kullum

SIDIYA ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY: SADIYA SIDI SAID (SADIYA) ✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE* 8⃣3⃣➡8⃣4⃣






Hajiya karime taci gaba da cewa

"iya tashin hankali da barazana mun fuskan ce shi, alhaji ba kadan ba ya nuna matuqar damuwa akan rasa mahaifi na danayi, Dan kuwa ko mahaifin shine iya damuwar daze shiga Kenan. Haka muka Gama jima mi muka hakura.

Kad'an Kad'an dai muka dinga rasa 'yan uwa da makusantan mu, ciki hadda mahaifiya ta, mahaifiyar shi alhajin, kanwar shi ZINNURAT, gashi mutuwar kusan iri daya ce. Ba k' ananan maganganun da ba'a zo mun dashi ba akan miji na Amma bana sauraren Masu kawo mun, a dalilin haka kowa ya guji gida na, babu me mu'amala dani ni kuma bana yi da kowa, bana zuwa hidiman kowa bame zuwa nawa, gida na ya dawo tamkar kurkukun fursuna.


Ni kaina a tsarge nake kwana a tsarge nake tashi a gidan, bana iya bacci, yadda naga safe haka nake ganin dare, gashi Duk wasu alamomi daza su tabbatar min da tabbas mijina na cikin kunyi yar asiri, Na fara ganin su, Dan baya dawo wa gida se tsakar dare, idan ya shiga daki ya kulle kan shi baya fitowa, se ya share sama da sati daya be fito ba, idan kuma ya fice, bana sake sashi a Ido har na tsawon Wata guda, Duk kuma randa ya neme ni a shimfida a d'ari-d'ari nake zuwa, badai zance a'ah ba dan kar in kwana cikin tsinuwar Allah dana mala'iku....


A haka harna samu cikin su umar faruk (BA'ISH), da d'an uwan shi Ahmad salim(SHA'IB).
Na shiga taraddadi da fargaba da wuce misali, gashi banida kowa bani komai se Allah, babu wanda xan iya tunkara da alfarman ya taimaka mun dan kowa ya guje ni, koda yaushe ina kan dadduma safe, rana, dare, ina gayawa Allah damuwa na. Tsabar damuwa da tsoron mezai biyo baya yasa Duk nabi na rame na k'warjane, abincin kirki bana iya ci, a haka harna haifi su umar, cikin iyawar Allah na raine su, koda yaushe cikin addu'o'i da nema musu taimako nake, aikuwa inji Allah har su umar suka fara wayo Allah be d'ora uban su akan suba.



Kowa yayi mamakin dahar su BA'ISH suka fara girma suka yi wayo babu abunda ya same su. Wata rana ina bacci na manta ban kulle kofa ba, Dan tun lokacin dana haife su bana barin su kwana ba tare dani ba, haka sena tabbata na rufe part dina na kuma tofe su da addu'o'i.


Ranar rabon ayi ne, da kuma afkuwan kaddara yasa na manta ban rufe dakin ba. Cikin bacci kamar an tashe ni, Na farka koda na duba gefe na BA'ISH kawai nagani ya d'unk'ule, jikin shi se karkarwa yake, a firgice na yaye bargon dana rufa mana, Dan taba jikin nayi, naji shi rauu kamar garwashi, tsoro ne ya kamani na Rashin ganin SHA'IB da banyi ba, tashi nayi, mirgino BA'ISH ke da wuya naga bakin shi na fitar da kumfa, a gigice nake jijjiga shi ina tambayar shi ina SHA'IB??? Amma ya Kasa mun magana se nuni yake mun da k'ofa, ba shiri nabi inda yake nuna mun...




Sauri-sauri, gudu-gudu nake yi har nakai part din mahaifin su inda nake jiyo hayaniya sama-sama, nan bugun zuciya ta ya tsananta bugawa, Na Kasa k'arasa ciki, d'an malek'in dake jikin kofar tanan na leka kozan iya hango meke faruwa...


Tsabar firgici ne da tsoro ya taru ya tsaya min a kahon zuciya, ganin abunda nake ji akan mahaifin su yau na tabbatar na kuma zama shahida ganau ba jiyau ba, mutane nagani kowannen su sanye yake da Jan kaya, ga SHA'IB a tsakiya suna zaga ye shi, suna surutan su na matsa fa, ganin mahaifin su nayi yaba wa SHA'IB wani Abu a k'warya, yana Gama shanyewa ya fadi a Kasa yana kakarin mutuwa, ganin hakan yasa ba shiri nabar wajen...




Gudu nake bana ko kallon gaba na, ina kaiwa dai dai daki na banka k'ofa, kudin da zamuyi Amfani dashi mubar kasar kawai na iya Dauka, ba shiri na sungumi BA'ISH na d'ora shi a kafad'a ta, fitowa nayi ina ta waige waige, nayi sa'a kuwa ban hadu da kowa ba, a haka harna samu na fice daga makeken gidan...





Gudu nake cikin dare ba qaqqautawa, seda nayi nisa da gidan ne, na hadu makocin mu alh. Sabitu da taimakon shine muka baro kasar a washe gari.




Haka nayi ta sana' o'i ciki har na, ga aiki, wanke mota, sharan titi da sauran su wanda ni kaina bansan adadin Sana'o'in da nayi ba. Na nemar wa BA'ISH magani harya warke muka ci gaba da zaman mu anan cikin rufin asirin Allah, har nasaka shi a makaranta...


Ban kara tunanin komawa Sudan ba. Ban kuma San SHA'IB na raye koya mutu ba, a haka ne naji labarin rasuwar mahaifin su, wanda ya sabawa umarnin kungiya a karo na Farko.


A yadda labarin yazo mun, ance mutuwar zana yayi mutuwar kaskanci, gawar shima Kasa taki dauka, sedai aka kona shi. Mutuwar shi da kwana biyu, gidan shi na tsafi ya kama da wuta ya k'one k'urmumus..."




Wani ajiyan zuciya hajiya karime ta sauke tare da goge siraren hawayen bakin cikin da ya zubo mata. Sannan ta kalli BINAFA dake daskare a waken kamar an

Please Login or Register in order to submit comment