Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kwashe k'arya da Gaskiya ta fad'a masa. A zafafe ya fito yayo kan mu da sunan duka ,nan take ya fara tari dak'yar aka rik'e shi aka maida shi d'aki, se ranar na gano wai Ashe Abba Nada ciwon zuciya saboda tsabar bak'in hali daya d'orawa kansa. Duk se naji banji dad'i ba ,ba yadda banyi ba da Abdallah akan yazo muje mu bashi hak'uri amma yace shi baze je fa ,nima d'in kamar baza niba ,sedai na kasa sukuni ,haka na shiga d'akin shi da sallama, a kwance na tarar dashi idon shi a lumshe kamar me bacci ,amma a zahiri ba bacci yake ba. Magana na fara murya a dasashe ,amma yayi shiru kamar besan na shigo ba. Ganin yak'i yace mun yasa na k'arasa har kusa da inda yake kwance na tsaya daidai kanshi ,sunan shi na kira a sanyaye "Abba!!!" Amma kasan me? A maimakon inji ya amsa kawai se jin nayi ya fara tari ,a hankali tarin se k'ara karfi yake ,nan fa hankali na ya tashi, na fara jijjiga shi ,ana cikin wannan yanayin ne Sega bela ta shigo , azato na zata zo mu taimakawa Abba ,amma a mamaki na base bela tasa ihu ba ,wai gani nan zan kashe Alhaji ,ihu take bataji bata gani ,nan take ta Tara mun jama'a ,se rantse rantse take wai wllh ta ganni ina shak'a masa wani Abu a hanci , kowa se tambaya na yake meya faru ,amma mamaki ya hanani magana jin irin sharrin da bela keson laqqana mun na kisa!!! Kisan ma wai mahaifi na, aiduk abunda ke tsakanin mu ban taba wannan bahagon tunanin ba...

Hankali na be k'ara tashi ba seda aka kai Abba asibiti likitoci suka tabbatar da lallai an shak'a mai guba... Nan fa hankalin kowa ya sake tashi ,dukda ansan halin bela ba abunda bazata iya aikatawa ba amma kuma lamarin ya saka tunanin kowa a kokonto... Kai in tak'aice maka zance case d'in seda aka shiga kotu.

Tun shigar mu kotu na farko alqali ya bada umarnin a ajiye ni a cell har a gama shari'a... "Yan gidan mu kowa se kuka yake ,duk yadda suka so abasu dama suyi magana dani Sam aka hana su ganina. Umma a cikin kotun ta yanke jiki ta fad'i ta samu...


Shari'ar bata wani d'au lokaci ba saboda akwai manaqisa a cikin ta ,ranar k'arshe alqali ya tabbar da cewa dikkan wani sheda da ake nema akan wacce ake zargi an samu ,sukayi amfani da kalaman da Abba yace na " bashi bani..." Wai saboda haka ne yasa nake so in kashe shi. Aka buk'aci bela da tayi rantsuwa da Qur'ani ,aiko bako tamtama ta rantse. Nan alkali ya yanke mun shekara d'aya da rabi a gidan kaso... 'Yan uwa na da abokan azziki kowa se kuka yake mun ,saboda daidai gwargwado an shedeni ,dabba wannan ban tab'a kashewa ba balle mutum kuma ma mahaifi na. Nan aka bama 'yan uwa na suje suyi sallama dani. Kowa se addu'an Allah ya sakamun yake ,niko saboda tsabar firgici ,tsoro da kuma mamaki daya kamani k'ala na kasa cewa ,inbanda Aikin kuka ba abunda nake. Lokacin da aka basu na magana dani ya k'are nan aka samun ankwa a hannu za'a tafi dani ,kuka su umma keyi kamar ransu ze fita ,rik'e ni umma tayi tana kuka tana fad'in 'Ku kyale mun 'ya ,'yata batada lefin komai kawai makirci ne aka shirya mata...." K'ank'ame ni umma tayi kamar zata maida ni ciki ,su Abdallah suma kukan suke suna rik'e ni, da k'arfi da yaji 'yan sanda suka b'anb'aro ni , wajen gaba d'aya se koke-koke ake ,umma na ganin da gaske tafiya za'a yi dani a take ta fad'i nan nak'uda ya taso mata. Ina ji ina gani aka saka ni a mota ,aka rabani da umma na da 'yan uwa na...

Munzo daidai gate din fita Sega anty Hindu ta shigo da kukan ta ,hannu ta dinga wa 'yan sandan alamar su tsaya amma ina ,haka ta dinga bin motan da gudu tana kuka ,bata ko San an kawo titi ba ,machine naga ze bankad'eta inaso in mata magana amma baki na yayi nauyi ,shahhhh... Me machine ya kwashe anty Hindu...








Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE4⃣9⃣➡5⃣0⃣*




Haka nayi rayuwa a gidan yari na tsawon lokacin da aka ibar mun. Koda yaushe cikin damuwa nake ,na lalace na rame kamar bani ba, ba komai bane a raina se ummana da 'yan uwa na ,da kuma mamakin abunda mahaifi na yamun ,Dan ita bela ko kad'an bana kawo ta a raina ,kuma ko kad'an banyi mamakin abunda ta aikata mun ba Dan wannan kad'an ne daga cikin masifar da Bela zata iya aikatawa kenan. Na shiga damuwa da k'unci Dan ko a gidan yarin haka na zauna yau ciwo gobe lpia ,damuwa ta samu gindin zaman a zuciyata da tunani nake kwana dashi nake tashi ,kuma shine abokin hira na , dukda cewar duk sati umma na takan kaimun ziyara ,had'e da abinci amma bana iya cin komai ,duk lokacin da tazo tana kuka ina kuka haka muke rabuwa...
Akwana atashi ba wuya a wajen Allah ,lokacin fitowa na ya cika, ranar Dana fito murna agun ummana da 'yan uwa na ba'a magana masoya da abokan azziki fal a kotu wasu hadda hawayen tausayi na...


Bayan na fito ne nake samun labarin Abba ya sake sakin habi bayan ta sake haihuwa ,imran da Abdallah kuma sunyi nasaran samun scholarship harma sun wuce turkey anan babban birnin ISTANBUL, Fatima kuma saboda azabar bela ta gudu kusan wata shida sannan aka gane cewa tana lagos ne can wajen 'yan uwan umma.
Dama bela da zata tafi bata bar 'ya'yan ta ba Dan dama ta fad'a tace duk randa Allah yayi tabar gidan mu bazata iya barwa bela 'ya'yan ta ba, saboda kwata-kwata bela batada isash-shen tarbiyan dahar zatace zata yiwa 'ya'yan wasu.. Umma na ta haifi twins duk maza sultan da suhail, bayan ta haihu ne ta koma can gidan su na Abuja tare da musaddiq ta tafi ,a tak'aice dai bela kad'ai ce gidan take cin karanta ba babbaka, a lokaci d'aya kuma ciwon mahaifa wato (fibroid) ya kama bela sakamakon zubadda ciki da take yawan yi da batasan ze haifar mata da matsala ba ,kuma ko kad'an bata damu ba saboda tasan tana cikin daula kuma ba kowa a gidan daze takura mata. Makaranta ma da take zuwa ta tattara ta watsar.
Shi kuma Abba tun lokacin da yaga kowa ya watse yabar shi ya fara rashin lpia ,,damuwar dayasa a ranshi ne yayi sanadiyyar haifar masa da hawan jini...


Bayan na fito daga gidan yari ne, director-n makarantan mu ya nemi akan in dawo inci gaba da karatu a kyauta,,,,dukda cewa mate d'ina har sun kammala ...

ban so komawa ba ,musamman idan na tuno da rashin nasihar daya mun a fakaice. Saboda lokacin Dana samu matsala da Abba ,a lokacin naga karatu na ya soma samun matsala ,haka naje nayita rok'on director d'in mu akan su banni inci gaba da karatu har zuwa lokacin da zan samu kud'i inbiya kudin makaranta na amma k'iri da muzu director yayi k'irmashe-she ya hana ,ana cikin haka nema sega masifar shiga na gidan kurkuku...


Kafin in koma seda umma tayita bani hak'uri akan in koma ,shima director yayita kirana yana bani hak'uri ,hatta malaman makarantan haka suka dinga damuna a waya suna bani hak'uri akan indawo ,sannan ne fa nakoma. Sanadin wulaqancin da director yamin ne akaro na farko yasa ana gobe zan kammala karatu na naje na biya duk wani kud'i Dana San shine hakkin su ,badan kuwa ya buk'aci hakan ba, kawai ni wulaqanci ne banaso ,sannan na nuna masa ne, lokacin da suka d'auki nauyin karatu na babu ne ,bani da shi ,amma kuma daga baya alkhairin Allah ya sauka...


Bayan na koma makaranta ne ,umma ta saida kayan d'akin ta aka fara saro mata kaya tana turo mun ina saida mata a makaranta... Ta haka ne muka fara warwarewa.


Lokacin da nake kukan babu ,na rasa yadda zanyi da rayuwata ,bani da komai inba rai ba shima na aro ne, Zeey smasher k'awata ce sosai sedai wasu halayen nata sam basu min ba. itace wacce tadan fara seta ni a layi ,sedai bada sanin taba na goce a layin.
Da dadewa smasher na yawan taya mun harkan ta amma ko kallo bata ishe niba. Smatcher ta k'ware a bin maza, kai matan ma bata bari ba ,bugu da k'ari ga d'an banzan shaye-shaye kamar ruwa...


Dakaina na samu zeey nace mata inaso zan fara harkan nan ,sosai taji dad'i tace mun duka ko d'aya kawai zan tab'a? Sanin data mun na bana son raini yasa ta gane mayataccen kallon danake Binta dashi ,kuma sarai sak'o na ya isa gare ta.
A haka muka je wajen malam musa me farin allo ,zeey tayi masa bayani akan tanaso a had'a mun na farin jini. Koda mlm musa ya duba taurari na ya sanar da zeey cewa ta bamu wuri, nan yake sheda mun taurari na Nada kyau ,bana buk'atar wani hadin farin jini ,kuma yayi alqawarin taimaka mun duba da labari na dayaji.
A nan ne yake fad'a mun sharud'od'in sa na bayawa mazinata aiki ,sannan kuma shi baya tsafi ,nayi mamakin jin sharad'in shi na farko ,se nayi ta mamakin to idan baya ma mazinata aiki ,ya zanyi kenan ,nida na zo da niyyan karuwanci. Ganin da yayi kamar kad'an shiga damuwa yasa yace in kwantar da hankali na, nan ya bani wani Turare ,yace mun duk lokacin da namiji ya nuna yana so yayi lalata dani inshafa shi a k'asan Mara, a take mutum zeyi releasing ba tare da ankai ko inaba ,da kuwa yayi releasing to magana ta k'are, sosai naji dad'in hadin da mlm musa yamin,,,, sannan yamun kakkab'a na duk namijin Dana ke tare dashi ya dinga sakarmun kud'i kamar ba gobe ,haka kuwa akayi...


Nayi amfani da wannan daban wajen koyawa maza hankali. Kuma bana huld'a ta seda 'yan siyasa ,koda masu hannu a shuni. Babu namijin daya tab'a kusanta ta, saboda ni gwana ce a iya gamsar da maza ta hanyar romancing,... Wato a fagen tab'e-tab'e ,lashe-lashe ,murje-murje da kuma yak'ushe-yak'she... In short na iya sarrfa namiji a gado ta hanyar jagwalgwala shi da yamutsa shi cikin kissa da salo ba tare da ankai ga babban aiki ba....

Na kuma Tara dukiya fiye da tunanin ka, na mallaki k'addarori kama daga gidaje ,motoci da kuma filaye duk nawa na kaina...


Cikin sanyin jiki binafa ta kalli umar faruk sannan tace

wannan shine labari na,,,,"""...



*CIGABAN LABARI*


Wani nannauyen ajiyan zuciya Umar faruk ya sauke ,gaba d'aya jikin sa yayi sanyi ,jin abun yake kamar alma-ra, zuciyar shi cike take fal da tausayin BINAFA ,wanda hadda 'yar k'wallan sa.
A b'angare d'aya kuma yaji sonta na k'ara ratsa ko wani b'argo da jijiya na cikin shi ,a lokaci d'aya kishin ta ya dinta fizgar shi kamar ze ci kanshi saboda tsabar kishinta daya ke ,nan take zufa ya fara karyo masa, nan take ya sauya kammani ,takaici ne ya cika shi ya kasa cewa komai...


Binafa ganin yayi shiru yasa ta kira sunan shi sunan shi cikin wani irin murya me shiga jiki.

"Me sunan manya!". Har cikin k'wak'walwan shi yaji yadda ta kira shi. Kai ya d'ago yana kallon ta itama shi d'in take kallo.

Yrrrrrrrrrrr,,,, suka ji wani shock ya saukar musu tun daga cikin kai har babban yatsan su na k'afa, lokaci d'aya Zuciyoyin su suka tsananta bugawa... Ko wannen su na karanto tsantsar madaran so da qauna daga idon d'an uwan shi. Se suka samu kan su da sakarwa junan su wani kayataccen murmushi Wanda ke k'arawa fuskokin su haiba da kwarjini...


Kunya ce ta kama Binafa ganin wani mayataccen kallo da umar faruk ke binta dashi , ga wani bak'on yanayi data tsinci kanta a ciki ,tayi saurin sadda kanta k'asa tana wasa da zara-zaran yatsunta...
Shi d'in ma kunya ce ta kama sa ,yaso yayi magana ,amma Dan kar Binafa ta nazarto halin da yake ciki ta raina shi yasa ya waske...


Can k'asan mak'oshin shi ya furta

" masha Allah Ashe na tako a sa'a"!!!….. A zaton shi bataji meya ce ba. Wani kallo Binafa ke binsa dashi na me kace? ,ganin irin kallon data ke mai yasa shi d'aga mata gira alamar me tagani? Hannu ta d'aga masa alamar bakomai, kai ya gyad'a mata shima sannan ya basar...


Dikkan su se zancen zucin su suke... "Hmmmmmm!!!"shine abunda ko wannen su ya furta kamar had'in baki... A take suka sa dariya...



SIDIYA ma dai dariyar take😂lolz...






Comments
&share




Taku har kullum

*SIDIYA* ✍
💖💖💖💖💖💖💖💖💖

*BINAFA*

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*STORY & WRITTEN BY : SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION®* 📚
(On ward 2gether)



*PAGE5⃣1⃣➡5⃣2⃣*



Bayan kwana2 Binafa ta koma Lagos Umar faruk kuma ya wuce abuja ,da cewar nanda sati d'aya zeje ya nemi izinin Auren ta...

Umar faruk cikakken namiji ne tsaye dakyau zaune dakyau, yana da hak'uri da kuma kawar dakai ,sedai idan aka kunna shi bayada sauki, mutum ne me zurfin ciki,,,, yana son yara sosai ,ga son 'yan uwa. A b'angaren halitta kuwa ,zan iya cewa Umar na cikin sahu na biyu a tsarin taruman mazan da ko wacce macce ke kwad'ayin mallaka a matsayin miji. Yana da tsayi ,jikin shi kuma d'an daidai ne ,yana da haske amma ba wani cancan ba, amma duk da haka ze d'anfi Binafa haske Dan ita baza a kirata da fara ba ba kuma baka bace sedai a kira ta da wankan tarwad'a ,se sufar kanshi daya kwanta luf har ya kusa had'ewa da gashin girar sa kamar de na larabawa ,ga tsinin hancin shi daya ke k'ara fito da kyawun fuskar shi, lab'b'an bakin shi jawur daya dace da fuskar shi ,baya da manyan ido sosai ,,,,yana da dogon hab'a Wanda ke zagaye da gashi. Fuskar shi d'auke take da saje da gemu bak'i sid'if se walk'iya yake da alama yana shan gyara, Umar faruk mutum ne me yalwar gashin jiki ko ina na jikin shi gashi na kwance. Duk lokacin da zeyi dariya se fararen hak'oran shi sun bayyana wanda suka d'au sahu a jere, ga wushirya daga tsakayi me k'arawa fuskar shi cikar zati...
Kai iya had'u wa Umar faruk ya had'u matakin farko ,yadda kuka San d'an Sudan haka zubin shi yake...



Lokacin da Umar faruk yaje wada hajiyar sa da zancen Binafa sosai tayi murna had'e da masa addu'an Allah yasa a dace ,Dan kusan so biyu yana aure amma matan basa zama... Hajiya karime itace mahaifiyar Umar faruk ,ita da Umar kamar an tsaga k'ara kusan kamar su har ta b'aci ,sedai ta fishi haske sosai ,kuma ita tana da k'aramin jiki ,shi kuma gogon nawa a tsaye yake kamar Doki.


Binafa bayan komawar ta legos sosai suka tarbe ta ,asibitin kowa se yaba mata yake ,musamman MD daya ke jin kamar ya had'iye ta Dan tsabar farin ciki, gagarumar walima suka shirya mata na murnan nasaran da aka samu na lashe seminar a karo na 16 shekaru da dama da suka shud'e...
Bayan an kammala ne ta nemi a bata Hutu taje gida tad'an Hutu ,ba musu MD yace taje ,duk lokacin da ta gama hutun seta dawo. Godia ta masa sosai sannan ta fara shirin komawa abuja.
Wani abunda MD be sani ba shine ,Binafa bada niyyan Hutu kawai zata tafi ,hadda niyyan ajiye aiki gaba d'aya. Koya MD zeji idan ya samu wannan mummunan labarin na cewa binafa zata bar aiki koma nace tabar aikin oho...
Bayan kwana2 ta dira babban birnin tarayya ABUJA...


Sosai taji dad'in yadda ta samu gidan ,Dan kusan ba matsalar komai ,harkoki se dad'a bunqasa suke. Washe garin zuwan Binafa ne take bama umma labarin Umar faruk da yadda suka had'u kai har harin da b'arayi suka kawo musu a hotel d'in ,Binafa bata ragewa umma komai ba. Sosai umma tayi murna taji dad'i sosai Dan kusan abunda take ta jira ta gani kenan a rayuwar ta, nan take ta shiga kiran 'yan uwa da abokan azziki tana sanar musu...



Ranar da Umar faruk yazo gaishe da umma ,sosai yaji dad'in tarbar da aka masa ,duk yadda yake ganin kirkin Binafa se yaga umma ta zarce ta. Su twins se haye masa jiki suke suna ja masa gemu ,dariya abun ya dinga bashi ,yaji a ranshi inama ace 'ya'yan shine ,har tambayan Binafa yayi wai Dan Allah ta tambayar masa umma idan sukayi aure yana so a bashi su twins, abun dariya ya bama Binafa cikin ranta take cewa ,

"Kaji baho ,ba d'anda za'a baka haka kawai a cuce ni a hana ni more rayuwar aure na, cabdi ai umma ma tafi so taga hanjin cikin ka Dan bata had'a su twins da komai ba... " Yadda take ta faman dariya da gaske ba k'aramin burge Umar faruk yayi ba Dan be tab'a ganin dariyarta irin nayau ba, hankalin shi ya maida gaba daya kanta ,ya kafe ta da ido se murmushi yake ,ganin irin kallon da yake Binta dashi ne yana ta fara tsagaita dariyan ta. Wani iska ya furzar me zafi kafin yace a sanyaye


"Komai naki mekyau ne farin ciki na ,kina sanya ni nishadi a duk lokacin da nake tare dake ,wani sabon natsuwa na saukar mun!!! Inason ki BINAFA, ina matuqar matuqar kaunar ki ,sannan ina rok'on Allah daya aramun tsawon randa zan ci gaba da kasancewa dake"...

" Ameen " shine abunda BINAFA ta furta ,tana jin yadda kalaman Umar faruk ke fasa ko wani bangon jini


Yinin ranar kusan tare suka wuni se dare Umar faruk ya wuce gida..
A yanzu shak'uwar dake tsakanin Binafa da Umar faruk ya zarce tunanin me karatu ,koda yaushe suna nan mak'ale da juna a waya. Soyayya suke gudanarwa Mara sirki ,datti ko gauraye a ciki ,abun su gwanin sha'awa se Wanda ya gani.

Bayan sati biyu da zuwan Umar faruk gidan su Binafa ,ya buk'aci yana so za'a zo Neman masa izini , Binafa ta sanar da umma akan magabatan Umar zasu zo , a cewar ta wajen malam zubairu za'a tura su, amma umma tace a'ah baza'a yi haka ba ,can kubau za'a tura su wajen dangin mahaifin ta ,a cewar umma wannan shine siyan girma da mutunci saboda asan 'yar tata nada asali ba daga sama ta fad'o ba.
ko kad'an umma batayi tunanin aje Neman Auren Binafa gun mahaifin taba ,tasan Binafan ma bazata amince ba.
Ba yadda Binafa ta iya haka ta sanar masa zancen umma cewa suje kubau, address din family house d'in su na kubau ta tura masa da komai da komai ta yadda bazasu wani wahala ba wajen gane gidan...



Bayan sati d'aya Umar faruk da yayyen mahaifin sa suka je kubau Neman Auren BINAFA kamar yadda suka yi alqawari ,basu wani sha wahala ba wajen gane gidan kasancewar ba b'oyayyen gida bane ,ba lefi an musu tarba ta mutunci ,sosai dangin mahaifin Binafa suka yaba da kirkin Umar da kuma gidan dattakon daya fito, su kansu dangin Umar faruk sun yaba sosai da tsatson da matar d'annasu ta fito, haka aka gudunar da komai cikin tsari kamar yadda shari'a ta tanadar.. A tak'aice dai su Umar basu baro kubau ba seda suka kammala komai ,an yanka musu sadaki Naira dubu 50 sun biya a take ,Dan kuwa hadda d'orin wasu dubu hamsin d'in suka bada na rabawa dangi. An saka ranar bikin su nanda wata biyu masu zuwa, ba kad'an ba abun yawa Umar da dangin sa dad'i jin yadda aka gudanar da komai ba tare da and'au wani dogon lokaci ba...

Kwanan su Umar d'aya a kubau suka kama hanyar komawa gida Abuja...


Sosai umma taji dad'in yadda hajiyar Umar ta kirata ta dinga yabon dangin Binafa da kuma dattako irin nasu...

Tun lokacin da akasa ranar Auren Umar da BINAFA umma tasa Hajiya turai (kawar umma ce 'yar sudan ,aure ne ya kawo ta nigeria ,gwana ce wajen gyaran amare), ta fara gyaran 'Yar tata Dan kuwa ma daga k'arshe Binafa gidan Hajiya turai ta koma da zama ,gyara take sha bana wasa ba, idan kaga binafa wata d'aya daya wuce ka ganta yanzu bazaka gane taba ,saboda yadda tayi haske ,tayi k'iba ,fatar ta se wani shek'i take...

Ga lectures d'in da Hajiya turai kewa Binafa na safe daban na rana daban na dare daban... Wani abun idan Binafa taji sedai kawai tayi dariya Dan ta Riga da tasan wannan, itama ba kanwar lasa bace., Binafa macece datasan kanta ,ta kuma tanadi dikkan wani nau'in mataki na cikarta 'ya mace...


A hankali lokacin bikin su se k'ara k'aratowa yake. Yanzu saura sati ukku bikin, wanda se a lokacin umar ya kaiwa binafa lefe na gani na fad'a akwati goma sha biyu, na atamfofi daban ,na lace daban, na material daban ,kayan bacci da english wears ba'a magana ,ba abunda yafi sawa da yawa irin dogayen riguna dan yaga binafa tafi yawan sanya su.
Umar mutum ne da bayason bidi'a ,dan haja daya tashi kawo lefen da kanshi ya kawo yasa yara suka shigar dasu ,babu abunda besa masa ba ,da yawan kayan ma and'inko su. Tsayawa Fad'in had'uwar lefen Binafa b'ata lokaci ne...


Umar ba kad'an ba ya shiga damuwa ,saboda Hajiya turai ta masa Katanga da ganin amaryar sa ,ko nan dacan bata barin ta fita.


A kwana a tashi saura sati biyu bikin Umar da Binafa. Yanzu kam Binafa ta koma gida ganin lokacin bikin ya k'arato ,se a lokacin Binafa taga irin dukiyar da Umar faruk ya kashe mata a lefe ,se santin lefen take ,godia ta masa sosai...

Basu wani yi rabon I.v ba ,ta waya duk suka turawa 'yan uwa da abokan azziki...

Ko wani b'angaren sun fara bak'i ba kamar gidan su binafa, anty Hindu ma ta iso da yaranta hud'u Khausar itace babba ,Khalipa me sunan Abban su Binafa ,Mahmud sannan auta hydar cewar anty Hindu...



Jama'a Baku tambayi oga salim ba🤔

A b'angaren salim tun lokacin daya samu labarin Auren Binafa duk yabi ya gigice ya rame kamar bashi ba ,ya koma kamar wani zautacce ,a halin yanzu ma yana kwance a asibiti, duk wani motsi da Binafa zatayi kamar a kunnen shi Dan kuwa Ashe security yasa mata...



Saura sati d'aya biki ya kan kama, bak'i a gidan su Binafa ba masokar tsintsiya ,haka a gidan su Umar 'yan Sudan ma duk sun iso. Umar na zaune wayar shi tad'au k'ara ,wata sabuwar number yagani ,nan take gaban shi ya fad'i ,kamar baze d'auka ba se kuma ya d'auka tare dayin sallama...


Daga cikin wayan kuwa shek'ewa akayi da dariya ,seda ta d'an tsagaita dariyan sannan tace cikin dakakkiyar murya

"Umar faruk ango"../ gaban shine ya tsananta bugawa danko ba'a fad'a masa wacece ba yasan latifa ce ,can k'asan ranshi ya furta " innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, a ina kuma kika samu labarin zanyi aure?"

Kamar taji abunda yace ,ta katse masa tunani da

Please Login or Register in order to submit comment